Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 5
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 5: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 5. Ƙwalla mai zafi ta shiga saukowa Taj a yayinda yake jin kamar da gayya…
3,209 words
Ƙwalla mai zafi ta shiga saukowa Taj a yayinda yake jin kamar da gayya mahaifin nasa yake tauye shi. To amma ko zai hana saboda baya son a haɗa ɗan cikinsa da sana'ar girki me yasa ba zai duba cewa rashin zuwansa zai salwantar da mafarkin cigaban ɗan marayan da bashi da gata ba.
"Alhaji ka yiwa Allah..."
"Na gama magana" Ya furta da izza sannan ya fuskanci Ahmad "ka canja mana booking idan akwai jirgi mu tafi yau da ƙanin naka. Takardunsa kuma ka tsaya ka karɓar masa."
Hankalin Taj tashi ya yi ya miƙe da sauri "Alhaji na rantse maka ba don ni zani ba. Idan ban je ba za ayi disqualifying ɗinsa."
"Wannan nauyin sai ya zame maka darasin rayuwa a gaba ta yadda ba za ka sake marmarin saɓawa umarni na ba."
Inna da Mama har ma da Ahmad saka baki su ka yi wajen lallashin Alhaji akan ya amince amma ya yi biris da su. Taj kuwa kuka yake tamkar yaron goye. A wannan yanayin wayar Wakili ta shigo masa. Alhaji da kansa ya ce ya ɗauka kuma ya faɗa masa ba zai je ba.
"Happy Taj yi haƙuri na kira ka da sassafe." Ya yi magana da ɗan jin nauyi.
"Kada ka damu na riga na tashi."
Wakili ya yi ƴar dariya "jiya wanda mu ka gaisa ka ce yayanka ne ko?"
"Eh." Ya amsa da sanyin murya.
"Breakfast na haɗa masa nake neman address ɗin ka. Na rasa da me zan karramaka. Ko a wannan matsayin mu ka tsaya kai ne sila. Zan so yin aiki tare da kai nan gaba." Ya sake dariya "kana burgeni ne. Ina son koyon girki kamar kai."
Kasa cewa komai Taj ya yi sai ruwan hawayensa da ya ƙaru. Daurewa ya yi ya ce da Wakili zai tura masa address ɗin yanzu. Bayan ya ajiye wayar ya dubi Alhaji da ya gama jin komai.
"Ka gani ko Alhaji? Yana da kirki kuma maraya ne. Cutar shi zan yi idan ban je ba."
Gajiya Alhaji ya yi da magiyar dukkaninsu ya ɗaga murya ya ce ce "Ku fitar min daga ɗaki gabaɗayanku."
Iko da izzarsa ba tun yau su ke damun Mama ba. Amma wannan ya fi ɓata mata rai. Wace irin zuciya ce da shi da za a dinga roƙonsa akan tallafawa rayuwar wani ya turje a kai. Sannan da girmansu ya haɗa su da ƴaƴan cikinsu ya yi musu kora irin wannan ta ƙasƙanci. Ta dubi hawayen Inna wanda ko ba a faɗa ba ta san na son share damuwar ɗanta ne. Bata cewa kowa uffan ba ta fita ta koma ɗaki inda ta baro wayarta. Kimanin minti goma ta ɗauka wurin yiwa mijin yayarta wanda ya kasance babban wa ga Alhaji ta fayyace masa komai.
"Zan kira shi yanzu. Kashe wayar." Kawai ya ce bayan ya gama jin bayaninta.
Da ta koma ɗakin yadda ta fita ta barshi haka ta same shi. Saboda halin da Alhaji ya sanya jama'ar ciki hatta iskar ɗakin bata daɗi. Shigarta ke da wuya Alh. Jafaru ya kira shi kamar yadda ya yi mata alƙawari.
"Hayatu."
"Na'am" ya amsa da ladabi domin ya yarda da aka ce babban wa uba, musamman wanda ya riƙe matsayin da gaskiya da amana irin yayansu.
"Ni Jafaru na bawa Tajuddin izinin fita yaje ya ƙarasa abin da ya fara. Sannan ina mai umartarka da ka zauna har a sallame su daga makaranta ku taho tare."
"Yaya Babba?"
"Idan ban isa ba kana iya take umarnina ka ɗora naka."
Bai bashi damar sake cewa komai ba ya kashe wayarsa. Alhaji ya kalli Mama da wani irin ɓacin rai mara misali. Sanin bata da gaskiya sai ta sadda kanta ƙasa kawai.
"Tashi kaje wurin gasar."
Iya abin da ya ce kenan ya fice daga ɗakin ya barsu. Taj bai ma gane dashi ake ba sai da Mama tayi masa magana. Ya kalli agogo yaga takwas saura mintuna ƙalilan. Gashi da ƴar tafiya zuwa makarantar. Tunanin wanka ko kusa bai zo masa ba ya fita da gudu-gudu ya sauka neman abin hawa. Ya isa tara saura minti bakwai. Har an gama shirya komai sauran teams biyun sun tsaya suna jiran lokaci. Wakili kuwa shi kaɗai ne a can gefe yana ta baza idanu cikin tashin hankali.
Taj na shiga wurin aka kaure da ihu da tafi. Ashe ba Wakili kaɗai ke jiransa ba. Masu mara musu baya da dama sun shiga fargabar makomarsu da aka ga bai zo ba. Tara daidai aka buga wata ƙatuwar ganga wadda ta bawa participants ɗin damar farawa. RAYUWA DA GIƁI 6
Batul Mamman💖
***
Kyakkyawan envelop Yaya Babba ya miƙawa Alhaji ya kuma bishi da kallo a tsanake don son karantar yanayinsa. Kamar yadda ya yi tsammani duk wani annuri da walwalar da yake tare da ita a farkon zamansu tsaf ya kau. Duhun da yake zuciyarsa ya sami damar nuna kansa a fuskar. Disappointment ɗinsa akan Taj ya kashe masa jiki da zai yi magana.
"Kawo maka ya yi?" Da Yaya Babba ya gyaɗa kai sai ya ce "to me yake so?"
Kallon tausayi Yaya Babba ya yi masa. Mutum mai kafiya irin ƙaninsa yana da wuyar sha'ani. Wani zubin ya tabbatar yana sanin cewa ba a kan gaskiya yake ba amma don kada ya sauya baki sai ya cigaba da riƙo da hujjojinsa masu rauni. Sai dai a yau ya ƙudiri niyar amfani da girmansa karo na biyu ya tanƙwara ƙanin yadda yake so.
A nutse yadda zai fahimta ya labarta masa zuwan Taj gidansa kwanaki uku da su ka wuce. A lokacin sun kusa wata biyu da dawowa daga India. Sakamakon gasar girkin nan ne Wakili ya taho masa da certificate ɗinsa na ɗaukar na ɗaya. Sannan ga admission letter kamar yadda aka yi alƙawari. Shi ne ya kai masa ya gani amma ya roƙe akan kada ya sanar da kowa domin ko iyayensa mata bai nuna musu ba. Ya kawo ne saboda ya nuna masa godiya akan shige masa gaba da ya yi har ya sami damar ƙarasawa. Sai kuma Wakili da ya nuna son zuwa ya gaishe da iyayensa kafin ya wuce Minna. Shi ne ya kai masa shi inda aka yi masa tarba mai kyau. Da yaji daɗi har mahaifiyarsa sai da ya haɗa da Yaya Babba su ka gaisa.
Alhaji ya gama jin zancen da bai gamshe shi ba ko kusa ya ce "mece ce manufar nuna min tunda ya ce baya son na sani?"
Yaya Babba dakewa ya yi babu alamun wasa ya ce "ina son ka sanya masa albarka ne domin idan Allah Ya kaimu lokacin fara karatun ni zan mayar dashi da kaina."
"Kada mu yi haka da kai Yaya."
Alhaji ya furta da ƙaramar murya yana jin wani irin yammm a sassan jikinsa. Yana matuƙar ƙaunar Taj sannan burinsa a duniya yaron ya gaje shi. Idan hakan bai samu ba ya yi zarra a duk sana'a ko aikin da ya nema amma banda GIRKI. Yadda rayuwar Habibu ta sauya salo a kan idanunsa ba zai taɓa lamuncewa ɗansa ya faɗa wannan hanyar ba. Shi fa ko duk jikinsa kunnuwa ne ba zai yarda girki ba wani nau'i bane na daudanci.
"Idan Allah Ya bamu yara masu biyayya, amfani da ƙarfin iko wurin hanasu farinciki ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba Hayatu."
"Haka ne."
"Ka amince?" Yaya Babba ya tambaye shi yana murmushi.
"Ai ka ishe shi uba Yaya Babba. Ba za ka taɓa faɗin magana na musanta maka ba in sha Allahu."
Da zuciya ɗaya Yaya Babba ya miƙa masa hannu su ka yi musabaha cike da farinciki. Bai san cewa magana ce mai harshen damu Alhaji ya yi masa ba.
"Allah Ya ja kwana baban Tajuddin. Nagode da karamcin nan da kayi min. Da yardar Allah sai mun yi alfahari da zaɓinsa."
"Uhmm" kawai Alhaji ya iya cewa don bakinsa ya bushe kamar an shanya a rana. Samu ya yi ya bar gidan kamar babu abin da ya riƙe a ransa.
Bayan fitarsa Yaya Babba ya kira Mummy (Ɗaharatu) matarsa kuma yaya ga Mama ya sanar da ita anyi nasara. Ta kama murna tana cewa hakan shi ne daidai.
"A neman haram ake yin fito na fito da burin ƴaƴa. Yadda Taj ya rame ya sanya abu a ransa ko ya zauna ba daɗinsa za su ji ba. Allah Yasa matakin nasara da samuwar alkhairi mu ka ƙulla."
"Amin" Yaya Babba ya faɗi yana gyara zaman gilashinsa.
Duk cikin zuri'arsu shi da wata ƙanwarsu Jamila ne ake yiwa laƙabi da ƴan boko. Matarsa ɗaya da yara biyar waɗanda huɗu sun yi aure saura namiji ɗaya. Mutum ne da ya yarda da displine ɗin yaron da ya kauce hanya amma sam bai yarda a tauye haƙƙinsu ba. Ita kuwa ƙanwar tasu da yara ke kira Amma likita ce. Sai da ta gama karatu tayi aure har ana ganin da gangan taƙi yi tun farko. Mijin mazaunin Amerika ne a can yake aiki. Bayan aurensu da ta bi shi ita ma ya sama mata take aikinta a wani asibiti. Yaransu biyu mata.
***
Ɗaki Alhaji ya kira Taj bayan ya koma gida. Ya yiwa ɗan nasa kallo na ka bani kunya sannan ya miƙa masa envelop ɗin. A take kuwa jikin Taj ya kama rawa.
"Ba da wata manufa na kai masa ba Alhaji."
"Ka ji na ce wani abu ne?"
"A'a."
"Madalla" ya gyara zama "Yaya Babba ya ce ka haɗa kayanka ka koma gidansa kafin lokacin fara karatun naku."
"Wane karatun? Ba service zamu tafi ba?" Ya tambaya da faɗuwar gaba.
A ransa Alhaji gani yake rainin wayo ne kawai Taj yake son yi masa amma ya san komai. Ƙarshenta ma shi ya roƙi Yaya Babban da ya taimaka masa ya sami komawa makarantar.
"Idan ka dawo sai ka zo kayi service ɗin. Ina yi maka fatan samun nasara da alkhairi. Allah Ya yi maka albarka. Tashi ka tafi."
Kansa sake ƙullewa ya yi amma babu halin tambaya. Sai ma ƙarin bayani da Alhajin ya yi masa cewa ya bari jibi zai kai shi da kansa don ya sami damar hađa kayansa.
"Ba na kuma son jin zancen nan a bakin kowa har matan gidan don na san za su so hanaka tafiya."
"To Alhaji" ya amsa a ladabce.
Kamal kaɗai ya sanarwa abin da yake faruwa. Da taimakonsa ma ya gama haɗa kaya. Ranar da za su tafi Alhaji ya faɗa masa zai dawo daga kasuwa da azahar sai ya kai shi.
"Happy" Kamal ya kira Taj suna zaune a ɗaki "ba ka mamakin chanjin ra'ayinsa?"
"Ni fargaba ce ma tafi damuna. Naga ko kaɗan bai nuna fushi ba duk da Allah Ya sani ba da wannan manufar na kai wa Baba Yaya takardun ba."
"In sha Allahu ma babu komai. Dama tsoron da naji da ka ce wai ya ce kada a faɗawa kowa."
Bugun ƙofa gami da sallamar Bishir ce ta hana Taj sake yin magana. Saƙon Alhaji ne yana jiransa a mota.
A take yaji gabansa ya yanke ya faɗi. Ya tashi jiki a mace sai Kamal da Bishir ɗin ne su ka ɗauko masa kayansa. Kowa yaga ana loda kaya a booth ɗin Alhaji sai ya yi mamaki amma an rasa mai tambaya don babu fuska.
"Ka shiga ka yiwa uwayenka sallama." Alhaji ya umarce shi da ya fito.
Inna bata gida. Sai su Hajiya. Su ka biyo shi waje kuwa su na tambayar Alhaji me ya faru Taj zai koma gidan Yaya Babba. Cewa ya yi su koma. Idan ya dawo zai yi musu bayani.
A mota haka su ka tafi ko numfashi mai sauti Taj baya iya ja. Kamar tare su ke don ana buɗe musu gate su ka ga Yaya Babba yana fitowa daga mota. Dawowarsa kenan daga office. Yayi mamakin ganin Alhaji kaɗai ko direba babu da Taj. Sai dai wannan ba komai bane a yayin da yaga ya buɗe booth Taj na sauke kaya.
"Hayatu me yake faruwa ne?" Ya matso kusa dasu don jiran su gama su shigo ciki ma ba zai iya ba.
Alhaji ya dubi ɗan uwansa yana mai baƙincikin yadda yayi masa katsalandan a cikin harkar gidansa. Shi kuwa Taj yana jin haka wani irin tsoro ya kama shi. Kenan Baba Yaya ba shi ya nemi ya dawo gidansa kamar yadda Alhaji ya faɗa masa ba.
"Ga Taj nan. Suna na ne kawai addini bai halatta min cire masa ba amma daga yau na bar maka shi."
Yaya Babba ya girgiza da furucinsa matuƙa. Fuskar ƙanin nasa a haɗe take kamar baƙin hadari.
"Me ya yi zafi? Don na ce zan mayar dashi makarantar da yake so?"
"Ai ban hanaka ba tunda ka isa. Shi ma da na isa dashi ina mai umartarsa kada ya dawo min gida."
"Hayatu bana son rashin hankali." Yaya Babba ya fara faɗa.
"Ai kuwa bai kamata ka kira biyayyata gareka da rashin hankali ba." Ya cigaba da magana kai tsaye babu tauna lafuzza don yau dole ya amayar da ɓacin ransa "saboda gudun shiga haƙƙi ban taɓa yiwa kowa iko da ɗansa ba. Amma sau biyu Yaya kana bawa yaron nan abin da nake son hanawa. Hakan ba komai zai janyo min ba illa baƙin jini daga gare shi. Koda yayi min biyayya zata zama bisa tursasawa ba don son rai ba. Maganin kar ayi, kar a soma. Tunda ka nuna masa za ka iya bashi abin da na hana sai ka riƙe shi na bar maka."
"Ni kake faɗawa magana Hayatu? Ashe zumuncinmu bai kai nayi umarni ko hani ga tsatsonka ba tare da ka ɗaga kai ba?" Yaya Babba ya faɗi yana mai jin ciwon maganganun da kunnuwansa ke ji.
Musayar yawun da suke ba ƙaramin tadawa Taj hankali tayi ba. Ya durƙusa a ƙasa yana kuka yake roƙonsu da su yi haƙuri.
"Wallahi ba zan sake tada zancen nan ba har abada. Ku yafe min don Allah."
"Baka isa ba! Karatu ko ba kyauta aka baka ba sai kayi shi. Tunda ka iya raina ƙoƙarina akanka ka haɗani da ɗan uwana dole ka cika burinka."
Taj na kuka ya riƙe ƙafar mahaifinsa yana roƙon yafiyarsa. Yaya Babba ma idanunsa sun kaɗa sun yi ja. A haka ya ja girmansa don gudun rigima ya bashi haƙuri.
"Kayi haƙuri. Ban yi zurfin tunani ba, da ban shiga huruminka ba. Don Allah ka ɗauki ɗanka ku tafi."
"Na gama magana. Wallahi daga yau Taj ya bar gidana..."
"Kada ka rantse." Ya yi nufin dakatar dashi sai dai ya makara.
Suna ji suna gani Alhaji ya juya ya shige motarsa yayi gaba. Taj ya bi motar a rikice kafin ya sami wuri kusa da akwatinsa ya zauna cikin wani irin yanayi na rashin kuzari. Zuciyarsa wani irin ƙunci kawai ke yawo a cikinta. Bai san lokacin da aka kwashe kayansa ba. Sai hannuwa da yaji na ɗan uwansa, ƙaramin ɗan Yaya Babba wanda ya kasance sakonsa ya tayar dashi. Da ƙyar ya yarda ya shiga gidan. Mummy tana kuka tana bashi baki tare da alƙawarin gobe Yaya Babba zai mayar da shi.
***
A wannan rana ko gyangyaɗi Taj bai samu ba. Kuma haka ta kasance a ɓangaren Baba Yaya da Alhaji da Inna. Don bayan ta dawo gida da ya sanar dasu hukuncin da ya ɗauka har suma tayi. Gidan ya rikice da koke koke. Iyalin Alh. Hayatu su ka taru su ka juya masa baya daga matansa har ƴaƴansu. Hakan kuwa bai yi masa komai ba face ƙara tsanar turbar da Taj yake son bi. Da kuma abin da Yaya Babba yayi masa.
Washegari duka ƴaƴan Marigayi Alh. Sule su ka taru a gidansu dake Soron ɗinki inda mata guda ɗaya da ta rage musu a matsayin uwa take. Ita ce mata ta uku cikin matansa. Zama irin na da yasa ita da ƴaƴan sauran abokan zamanta su ka cigaba da zumunci tamkar lokacin da mahaifinsu yake da rai.
Ita Yaya Babba ya kaiwa ƙarar Alhaji tun a jiya. Tasa aka kira mata kowa dake kusa. Amma ma dake nesa dama ta iso kwana huɗu da su ka wuce hutun shekara. Tana Abuja da niyar tahowa bayan sati guda. Amma kiran Gwaggo yasa ta biyo jirgin ƙarfe tara na safe.
Bayan an zazzauna Yaya Babba ya mayar da iya abin da ya faru ta ɓangarensa. Tun daga wayar da Mama ta yiwa Mummy da suna India har zuwa yadda ta kasance jiya. Aka tambayi Alhaji sai kaɗa baki ya yi ya ce bashi da abin sake tofawa.
"Yanzu Hayatu har kayi girman da za ka nuna mana iko akan ƴaƴanka?" Yayarsa mace mai bin Yaya Babba wadda daga ita sai shi tayi maganar da ƙwalla a idonta "na zata za ka yi farinciki da zumuncin da muke dashi wanda mu ka ɗora ƴaƴanmu da jikoki. Kai ba abin alfaharinka bane ace ɗanka yaje neman sauƙi a wajen ɗan uwanka? Shi kuma bai bashi kunya ba ya share masa hawaye."
Ransa sosuwa ya yi da har suke ganin laifinsa. "A cikinku akwai wanda zai bar ɗansa namiji ya ɓata lokaci a jami'a yana koyon girki da yadda ake sarrafa kayan abinci?"
"Me zai hana tunda ba haramun bane" wani ƙaninsa ya amsa kai tsaye. Wasu duk su ka amsa da za su iya.
"Wallahi ƙarya kuke yi. Ni ban taɓa ganin namiji a arewa mai sana'ar abinci ba wanda baya abin mata."
"Saboda al'adar bahaushe ta mayar dashi aikin mata kaɗai ba. Amma a kudu da sauran ƙasashen duniya maza nawa ne su ka yi fice da girki kuma in ba faɗa su ka yi ba sai ka rantse ma ƴan dambe ne."
"Ni yanzu me kuke so daga gareni?"
Gwaggo ta dube shi. Haƙiƙa akwai ciwo wurin iyaye idan ƴaƴansu su ka ƙi bin umarninsu. Gashi mutum mai aƙida wanda baya son ko yaya aga gazawar nasa. Kuma dole yanzu yaga kamar an haɗe masa kai. Don ko ita idan zata yi rantsuwa ta san babu kaffara da matuƙar wahala in ka cire Yaya Babba da Amma a sami mai barin ɗansa namiji ya yi wannan karatun.
"Hayatu kaje gidan Jafaru ka ɗauko ɗanka maganar nan ta mutu daga yau."
"Ai nayi rantsuwa Gwaggo. Akan Taj wallahi ba zan yi kaffara ba."
Cikin fushi Yaya Babba yace "Nima kuma wallahi ba zan zama silar raba ɗa da iyayensa ba. Idan rashin albarka ya bishi a dalilinka duniya ni za ta zaga."
Gwaggo dai gajiya tayi da basu baki ta kama hawaye tana cewa don babansu baya duniya shi yasa su ke yi mata haka.
Amma da bata ce uffan ba tun farkon zamansu ce ta katse musayar yawun da suke.
"Gwaggo ki zama shaida. A gaban kowa duk sun yi rantsuwa ba za su zauna da Taj ba. To ni ina so kuma dashi zan koma. Zan taƙaita hutuna mu baku wuri ku sha iska."
Kallonta kowa ya kama yi kafin kuma mazan su nuna a gidansu zai zauna.
"Jamila zai bi domin babu amfanin ya zauna a nan kowa yana yi masa kallon wanda uba ya kora." Gwaggo ta kashe maganar.
"Gwaggo ina so ki min shaidar ƙarshe. Yadda kowa baya son a shiga abin da ya shafe shi da đansa to nima kada wanda ya shigar min gonata. Zan yiwa Taj abin da zan yiwa ɗan cikina tsakani da Allah."
Kafin kowa ya sake magana ta tashi ta fice daga gidan gabaɗaya.