Rayuwa da gibi na batul mamman - Chapter 50
Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 50: Rayuwa da gibi na batul mamman Chapter 50. Tashin hankalin da ya sake bayyana a fuskar Hamdi har yafi na farko.…
3,360 words
Tashin hankalin da ya sake bayyana a fuskar Hamdi har yafi na farko. Tana so tayi ihu, kuka ko ƙorafi amma duka ta kasa. Zuciyarta ce kawai take harbawa fiye da ƙa'ida. Taj duƙar da kai yayi ƙasa don bai ma san me yake ji ba a lokacin.
Sai shiru ya mamaye wajen na ƴan daƙiƙu sannan Hamdi ta iya samun damar yin magana da dashashiyar murya.
"Da izininta aka ɗauka?"
Umma tayi gaggawar amsawa "Sosai. Mu bamu ma san ita ce donor ɗin ba sai da aka yi."
A hankali Hamdi ta ɗaga kai ta kalli Alhaji. Yayi mata kwarjini amma dole tayi masa tambayar dake ranta.
"Alhaji don Allah ba tursasata aka yi ba?"
Raunin muryar Hamdi a yayin da take kwaɗayin samun amsar da zata sassauta raɗaɗin zuciyarta ya shiga jikin kowa. Taj kam gabansa faɗuwa yayi. Idan amsar bata yi daɗi ba me zai ce da Hamdi?
"Baiwar Allah ni nafi cancanta ki yiwa wannan tambayar."
Kowa ya kalli Mal. Salisu. Cikin tausasan kalamai ya sanar dasu yadda komai ya kasance har aka yi aikin. Abu na ƙarshe kuwa shi ne kunna musu audio ɗin Yaya. Kuka kuwa har su Inna da ba yanzu su ka fara ji ba. Ita dai Hamdi zuciyarta kusan tsayuwa tayi ma. Kukan kuma ya ƙi zuwa balle ta sami salama.
"Idan kuna son sake tabbatarwa zan iya kai ku a nuna muku CCTV. Jiya sai da muka kalla tare da Dr. Hadifi wanda ya jagoranci aikin." Ya ƙarƙare da cewa " Malama Khadija ita ta kawo kanta asibitin nan da ikon Allah."
"Ya Allah. Ya Allah Ka basu lafiya. Allah Yasa anyi aikin a sa'a." Hamdi ta shiga furtawa.
Mamaki ya turnuƙe Alhaji da sauran mutanen. Ji wani irin tawakkali a tattare da ƙaramar yarinya. Domin ta ɗan sami sauƙi ya sanar da ita tahowar Abba Habibu wanda bata da masaniya. Ko a lokacin da ya faɗawa su Zee hanasu sanar da ita yayi. Ya san halinta. Bagarar da ita akan kada ta tsawaita tambaya zai fi wahalar da shi fiye da ƴan uwanta.
Abin da kawai ta ce shi ne "Allah Ya kawo shi lafiya. Mungode."
Daga nan bata ƙara magana ba kuma bata yarda ta haɗa ido da kowa ba. Bata so ainihin damuwarta ta bayyana. Cike take da fargabar me zai faru da Yaya. Me ya hanata farfaɗowa? Idan gudan ƙodar ta sami matsala yaya zata yi?
Hanyar banɗaki ta tambayi Yaya Kubra ta nuna mata. Taj yayi saurin tashi zai bita sai Ahmad ya sha gabansa har ta fara nisa.
"Kuka zata je ta kuma yi" ya faɗi yana ƙoƙarin kaucewa Ahmad ɗin dake tare duk hanyar da ya bi.
Tausayi Taj ya bashi sai dai a ganinsa Hamdi tana buƙatar ɗan lokaci ita kaɗai a wannan yanayin tunda babu kowa daga gidansu a kusa. A tausashe ya yi masa magana.
"Allow her Taj. Let her cry."
Taj ya girgiza kai "she needs me. Don Allah ka bari na bita."
"Ɗan uwanka aka sakawa ƙodar mahaifiyarta fa Taj. Kamal ya farfaɗo amma ita tunda aka fito bata buɗe ido ba. So kake tayi ta murmushin ɗan uwanka zai tashi ko kuwa tayi kukan mamanta a gabanka? Give her that space ko na minti goma ne to sort her feelings please."
"Amma.." ya soma cewa cikin damuwa.
Alhaji ya ɗora hannu a kafaɗarsa sai yayi shiru ya juya yana kallonsa "ka bi umarnin yayanka."
Haƙura yayi ba don ya so ba.
***
A cikin banɗakin, Hamdi ƙulle kanta tayi ta fashe da kuka mai matuƙar ban tausayi. Tana yi jikinta yana rawa. Idan Yaya bata tashi ba ina zata saka kanta? Me ta taɓa yiwa iyayenta na kyautatawa da zata iya dogara dashi taji salama a bayan su? Wai ma wace magana suka yi ƙarshe? Wane hali Abbansu zai shiga? Tambayoyi birjik a ƙoƙon kanta. Tayi kuka sosai har sai da taji kamar hawayen ya daina fitowa sannan ta buɗe ƙofar ta fito.
A inda take tsaye daga bayanta ƙofofi ne na toilet guda takwas. Gabanta kuwa dogon sink ne da kawonan famfo da madubi. A gaban madubin ne taga wata mata wadda da alamu balarabiya ce sai dai bata iya ganin komai illa idanunta. Sanye ta da abaya da niqab harda safar hannu. Hamdi ta kasa ƙarasawa gaban sink ɗin saboda kunya da taji tunda ta san dole matar ta gama jin kukan da tayi. Ga mamakinta matar sai ta ɗage niqab ɗinta. Ba yarinya bace. A ƙalla tayi hamsin a ƙiyasinta. Matar kawai buɗe hannuwanta tayi ta matso ta rungume Hamdi. Kamar tana jira ta ƙanƙame wannan complete stranger ɗin ta sabunta kukanta. Tana yi matar tana bubbuga mata baya har tayi mai isarta ta ɗago kai a kunyace.
"Am sorry"
Da turancinta irin na larabawa matar ta tambayeta "You lost someone?" (Rashi kika yi?)
"No, my mother is in the ICU" (Mamana tana icu)
Matar ta ce mata ta duba Husnul Muslim akwai addu'a sahihiya daga Manzon Allah SAW da ya ce musulmi su dinga karantawa a yayinda su ke cikin damuwa ko tashin hankali.
(La'ilaha illallahul Azimul Halim La'ilaha illallahu Rabbul arshil Azim La'ilaha illallahu Rabbus samawati wa Rabbul ardi wa Rabbul Arshil Karim.)
Da murmushi matar ta ƙara da cewa "Na rasa kalmomin da zan nuna miki alkhairi da albarkar dake cikin yi wa Allah kirari da wannan addu'ar. Ki yita da yarda, aminci da imani. In sha Allah za ki faɗawa wani a gaba. Allah Ya yaye miki damuwa."
Ba tare da musayar suna ko wani information game da juna ba suka rabu. Hamdi taji wani irin ƙwarin gwiwa tamkar Yaya ta tashi ta gama. Ta yabi Allah, tayi Masa godiyar haɗata da wannan mata sannan ta buɗe wayarta ta duba Husnul Muslim ta buɗe addu'ar ta fara yi. Da yake kuma ta ssnyawa zuciyarta cikakken yaƙini, nan da nan taji salama a ranta. In an cire jajaye kuma kumburarrun idanunta, za a iya cewa tafi kowa dauriya da ta koma cikin su Yaya Hajiyayye.
Ko zama bata samu tayi ba Ahmad yace su tashi domin shirin tafiya Umra. Wasu cikin ƙannensa suka so kawo turjiya wai sai Kamal ya tashi zasu tafi.
A fusace Umma ta daka musu tsawa ganin an kiransu ɗaya bayan ɗaya suna noƙewa kamar ƙananan yara.
"Kai dalla can ku tashi. Na zata kuna da hankalin sanin cewa nacewa ibada ake yi idan ana da buƙata a wajen Allah SWT."
Babu shiri suka fara tashi. Ta harare su "in kuma zaman ku ka fi so sai a bada himma amma ba a nan ba. Yanzu ma alfarma suka yi mana aka bamu wajen zama."
Shi dai Alhaji yana kallonsu har suka fice bai ce uffan ba. Zuciyarsa gabaɗaya ta shiga tunanin da fuskar da zai kalli Abba Habibu idan ya iso. Ya ɓoyewa iyalinsa yadda suka yi da likitoci akan rashin farkawar Yaya da wuri. Amsar guda ce. Ta zubar da jini sosai a lokacin aikin. Duk da an saka mata wani, amma jikinta bai daidaita ba har yanzu.
"Ya Allah, Ya Allah Ka rufa min asiri Ka bawa wannan baiwa taka lafiya" ya faɗi a hankali iya laɓɓansa.
***
"Kin san Allah Yaya Zahra yau zan tafi gida. Na gaji! Ba zan iya ba."
Zahra ta kalli ƙanwarta Ilham dake tsaye ta sanya hannu ta riƙe ƙugu tana faman yin ƙwafa da motsa kai hagu da dama cikin ɓacin rai.
"Ki gaishe da su Mama"
Zahra kawai ta iya cewa da sanyin murya ta sami waje ta zauna akan kujera a falo. Alamun gajiya ta kowacce fuska sun bayyana a tare da ita. Da gani bata cikin nutsuwa.
Ilham sai taji kunyar abin da tayi. Cikin jin nauyi ta zauna a kusa da yayarta ta ɗan dafa ta.
"Ki yi haƙuri. Kawai gani nayi kina ta wahala da matar da ba wani mutumci ne da ita ba."
Da sauri Zahra ta kalli hanyar ɗakin Salwa inda Mami take kwance yanzu. Ilham ta gane tana tsoron kada Mamin taji ne. Sai dai ita ko a jikinta. Mami ta sirewa kowa a gidansu saboda ire-iren rashin mutumcin da ta dinga yiwa Zahra. A haka ma don ba gari ɗaya suke ba.
"Na rasa me yasa Mama tace ki cigaba da kula da matar nan bayan ƴar cikinta ma ta gudu. Shima kuma Daddyn Hayat yayi tafiyarsa ya barki." Ta taɓe baki "kada ki ji haushina amma Allah na tuba wace Umra zai tafi alhalin ya bar mahaifiyarsa a wannan halin?"
Zahra ta girgiza kai "Ilham indai kin gaji ki tafi kawai."
Ilham ta sami waje ta zauna a kusa da yayarta. Jikinta yana bata akwai wata gagarumar matsalar a gefe wadda tasa dole Ahmad yayi nisa da gida a yanayin da ake ciki.
"Yaya Zahra me yake faruwa ne don Allah? Ban kai matsayin da za ki faɗa min damuwarki ba?"
Sai da Ilham ta zubar da hawaye kamar yadda Zahra take yi bayan ta sami amsar tambayarta. Cikin kuka ta sanar da ita abin da yake faruwa a gidan surukinta.
Tayi mata bayanin tsaka mai wuya da Ahmad yake ciki wanda indai bata tausaya masa ba, bai kamata ta ƙara masa damuwa ba. Ga Maminsa a wannan yanayi. Ta sami labarin an saki su Salwa a wajen Ahmad amma har yau bata dawo ba. A gefe guda kuma ga Kamal a kwance, sun samu da ƙyar jiya anyi masa transplant amma daga nan ba za ta ɗorar da komai ba.
"Amma Yaya Zahra su da suke da yawa don dai shi kaɗai ya dawo saboda mahaifiyarsa ai bai kamata ya zama laifi ba."
"Alhaji ko sunan Mami baya son ji. Kuma kinga abubuwan da Salwa ta janyo musu. I know he feels responsible shiyasa na tabbata nauyin faɗa masa yake ji. Sannan komai na gidansu shi yake sakawa a matsayinsa na babban ɗansa namiji. Wannan ma zai iya contributing." Cewar Zahra a sanyaye.
Ilham ta jinjina kai a hankali sai kuma ta kama dariya tana cewa "lallai aure ibada ne. Duk takurar da kike ciki amma kina auna komai ta fuska daban daban da yadda zai yi affecting mijinki." Ta murmusa "na ɗauki wani gagarumin darasi. Na san dole yana alfahari dake"
Zahra tayi murmushi "za ki cigaba da tayani zama?"
Ilham ta zumɓura baki ta koma ta kwanta akan kujera alamun dai ta fasa tafiyar. Zahra kuwa ta daddage ta kai mata duka a ƙafa sai da tayi ihu.
"Me nayi miki kuma?" Ta tambaya tana murza ƙafar.
"Tayar min da hankali mana. Wai ni kike yiwa barazanar komawa gida ƴar rainin hankali."
Ilham ta tuntsire da dariya "sai ga Yaya Zahra an kwantar da kai ana marairaice murya." Wani dukan Zahra ta kai mata ta miƙe babu shiri ta gudu.
A cikin ɗaki, Mami ke kukan zuci ita kaɗai. Ga ƴan uwa, ga ƴaƴa amma babu kowa a kusa da ita!
***
A wulaƙance Alh. Usaini yake duban Salwa. Tana durƙushe a gabansa ta fita kamaninta saboda tsabar naci. Shi ko ganinta baya son yi saboda yadda yake jin haushinta. Makauniyar soyayyarta ta janyo tonuwar asirinsa da lalacewar aikinsu gami da korar da mahaifinsa yayi masa. Da azal ta hau shi kuma ranar da aka sako su a titi ya ganta tana tafe tana jan ƙafa. Ya tsaya rage mata hanya da manufa guda...ci mata mutumci akan asarar da ta janyo masa. Sai aka yi rashin sa'a ashe ƙarfen ƙafa ya kwaso. Wani hotel ya tafi da ita yana ayyana azabar da zai gana mata. Ashe ita za ta gana masa.
Salwa ta nace lallai sai ya kaita wajen malaminsa. Tana da tabbacin za ta sami kan Taj tunda ta shaida da idanunta yadda wancan maganin ya birkita masa lissafi. Ba don iyaye sun shigo ciki ba da yanzu ƙarshenta an fara shirye shiryen rufe Happy Taj.
"Zan yi maka biyayya Alh. Usaini. Duk abin da kake so zan baka banda mutumcina." Murmushi ƙayatacce ta saki sannan ta ɗora da cewa "Taj nake tanadarwa kaina."
Wani kallon banza yayi mata yana ɗage hanci kamar tsohuwa zata tsallake lambatu "Wai ke wawiyar ina ce? Ana so dole ne? Banda masifa irin taki waye ma yake ta soyayya yanzu? Life is all about money, money and more money."
"Ba za ka gane ba. Wallahi ni Taj ne rayuwata. Idan ban aure shi ba zan iya rasa raina."
"Ƙaryar banza. Me ya hana ki mutuwa tuntuni?" Ya ɗan sassauta murya "kinga ki zo ki tafi gidanku don Allah. Hotel ɗinnan sun hana ni fita saboda ke. Naje checking out ance sai mun fito tare don kada na bar musu liability."
"Ka taimaka ka haɗamu. Nayi maka alƙawarin ba za ka ƙara jin ko da suna na ba."
Wani baƙinciki ya tokare masa wuya. Ya tashi kamar zai kai mata duka sai ya fasa. Baya son janyowa kansa wata sabuwar rigimar. "Wayyo Allah na. Salwa ki tafi kada na illata lafiyarki."
"Zan jure. Wallahi ko me zaka yi min zan jure. Ka taimaka min."
A hasale ya zauna. Magana da mahaukaci ɓata lokaci ne. Ba don Allah Yasa mata basa gabansa ba da tuni sunan Salwa sorry. Ita ko tsoro bata ji ba take zaune da shi a hotel a ɗaki guda. Safe, rana da dare duka zancen ɗaya ne. Idan yana so tayi shiru sai dai in yana waya. To gashi ta ƙare masa. Duk wani wanda zai roƙar masa mahaifinsa ya yafe masa ya zare hannu a kansa. A halin yanzu bashi da tudun dafawa. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka kashe masa gwiwar yi mata wani abu. Tunani da damuwarsa sun shallake ƙaramar lalurar Salwa ta son maso wani.
Abin da bai sani ba shi ne akwai wata ƙanwar kakarsa ta wajen uwa da ta saka baki akan maganarsa. Ga tsufa ga lalurar ƙafa amma a haka tasa aka kaita gaban mahaifinsa har gida ta bashi haƙuri a madadinsa. Ganin girmanta yasa shi yafe masa. Bayan ta tafi ya saka aka binciko masa inda ɗan nasa yake. Bayan nan aka tabbatar masa da cewa tunda ya shiga hotel ɗin bai fita ba. Abin ka da ɗa da mahaifi. Sai ya tashi da kansa yace ƙanin Usainin ya kai shi. [4/2, 11:37 PM] +234 803 761 4669: RAYUWA DA GIƁI 38
Batul Mamman💖
Nagode da karamcin ku. SonSo
***
Addu'a kam babu irin wadda bakunan ƴaƴan Alh. Hayatu ba su yiwa Yaya ba ta samun lafiya cikin ibadarsu. Hamdi ta zauna ta dinga yi wa Allah SWT kirari tana faɗin buƙatarta. Da ƙyar ta iya baro masallacin saboda shauƙin kasancewa a waje mafi tsarki kuma inda take da tabbacin karɓuwar addu'arta. Sai bayan isha su ka koma Jedda. Ana yi musu tayin tafiya masauki amma kowa ya ce sai sun ga isowar Abba Habibu. Ahmad da yake tracking tafiyarsu ya sami bayanin tsaiko da aka samu da su ka tsaya transit a Egypt sakamakon hazo da ya lulluɓe garin. Haka su ka kasance jugum-jugum ana ta tasbihi a zuci da fatar baki.
A can Bauchi kuma mahaifin Salwa bai san me yake faruwa ba sai da Ahmad ya kira shi a waya. Keɓewa ya yi daga ƴan uwansa ya sami wuri ya kira shi. Abban nata bai ɓoye masa rashin jindaɗinsa ba kuwa.
"Haba Ahmad. Kai da nake yabon hankalinka, ta yaya za ka bari har a kwashi waɗannan kwanaki kafin ka sanar dani?"
Ahmad bai yi mamaki ba. Dole ko wane ne yaji babu daɗi. Shi yasa ya zauna yayi masa bayanin dukkan abin da yake faruwa da gidansu. Baban Salwa ya jajanta masa ya kuma yi masa uzuri. Musamman da yace ya dakata ne daman yana jiran ganin ko zata dawo, kada yayi saurin tayar masa da hankali.
"Babu komai. Zan nemeta a waya. Idan ban samu ba ma akwai wani ɗan ƙanwata da zai iya yi min tracing ɗin layinta."
"Allah Yasa a dace. Nima zan cigaba da kiranta."
Suna tsakar sallama Baban Salwa ya dakatar da Ahmad ya yi masa nasiha mai ratsa zuciya.
"Ana canja abokin zama amma kaga iyaye? Iyayen ma musamman uwa, sai dai haƙuri kawai. Na san kana ƙoƙari kuma kana haƙurin amma ka ƙara domin neman albarka ba don ita Mamin taku ba."
Ɗacin abubuwan da Mami ta aikata waɗanda suka kawo su wannan lokaci ya dawo masa amma basu bari ya ƙi amsar shawarar ba. "In sha Allahu. Nagode"
Da haka suka yi sallama. Ahmad ya koma cikin ƴan uwansa a inda suka taru suna jiran isowar Abba Habibu.
***
Daga lokacin da Abba Habibu ya sauka daga jirgi zuwa yanzu da yake fitowa da ƴar jakarsa a hannu, gabansa ya faɗi sau ba adadi. Tunani iya tunani yayi amma ya kasa samun abu guda da zai iya cewa shi ne yake jin ya sami Yaya. Haka ya fito da sassarfa yana jan addu'o'i daban daban. Yana sako ƙafarsa waje ya ɗaga kai yana waige-waige. Abokin Ahmad ya sanar da shi cewa Alh. Hayatu zai turo a ɗauke shi. Shi yasa yake baza idanu ko zai hango guda cikin yaran nasa. Sai dai abin mamaki maimakon ƴaƴan, Alh. Hayatu ya gani da kansa yana tunkaro shi.
Wani irin abu mai zafi yaji ya tsirga masa daga tsakiyar kai har tafin ƙafa. Ƙafar ta zaɓi wannan lokacin taƙi motsawa kwata-kwata ma. Yana gani Alh. Hayatu ya cigaba da nufo shi amma ya kasa ɗaga ko da ɗan yatsa har ya iso gaban shi ya tsaya.
Da rawar murya Abba Habibu ya ce "Tun a waya na ce da Ahmad ya faɗa min gaskiya yace min da ranta."
Alh. Hayatu ya gyaɗa kai da sauri "da ranta Habibu. Iyalin ka tana nan da rai."
"To me ya same ta? Ni na san gagarumar matsala ce kaɗai za ta sa ka zo tarba ta a nan." Abba Habibu ya furta helplessly.
Alh. Hayatu kasa magana ya yi, sai wata uwar kunya da ta mamaye shi. Abba Habibu bai yi ƙarya ba. Haka nan me zai kawo shi tarbarsa? Mutumin da yake ƙyama yau a dalilin matarsa yana yi masa kallon mafi girman daraja a cikin mutanen da yake tare da su.
Kafaɗar Abba Habibu ya dafa ya nuno masa motar dake jiran su "Zo mu tafi Habibu."
"Kayya da dai ka faɗa min me zan tarar da nafi samun nutsuwa." Ya kalli Alh. Hayatu da yanayi da yasa dole ya ƙara jin tausayinsa. "Ganin ka a nan da tausasa kalaman ka a gareni sun fi faɗar min da gaba fiye da wayar da Ahmad yayi min jiya. Don Allah ina zamu je? Ko dai da gaske ne an kama ta cikin masu nakasar dake taho wa bara?"
Ba a nan Alh. Hayatu ya so sanar da shi ba. A wannan yanayin na tsananin firgici da yake gani a wajen Abba Habibu bai dace ya tsorata shi ba. Gudun tarwatsa labarin a bakin yara shi ne musabbabin tahowarsa. Sai dai kuma har ƙasan zuciyarsa shi ya san babu wani lokaci da ya dace ayi breaking mummunan labari ga makusancin wanda abu ya shafa. Ana faɗa ne kawai idan dama ta samu tare da addu'ar haƙuri da tawakkali. Ba tare da jan rai ko kwaskwarima ba ya sanar da shi gaskiya.
"Ƙoda ta bawa Kamal. Tana kwance a asibiti yanzu haka muna jiran farfaɗowarta."
Ko cikakken sakan Abba Habibu bai ɗauka ba wajen fahimtar kalaman Alh. Hayatu. Sun yi masa dirar aradu mai ƙarfi. Ga wasu irin tambayoyi suna tsaruwa a kansa cikin karo da juna wurin son fara fitowa. Amma duk da haka sai ya kasa furta ko ɗaya a dalilin tunawa da wayar da Yaya tayi masa tana neman izini.
"Yaya jikin Kamal ɗin?"
Mamakin wannan tambaya Alh. Hayatu ya yi kafin ya iya cewa da sauƙi a hankali.
"To mu je" Abba Habibu ya ɗaga ƙafa yana mai danne tsananin tsoron da ya taso masa.
Sai da suka shiga mota Alh. Hayatu ya kasa daurewa ya ce "Ba ka tambaye ni lafiyarta ba?"
"Ka manta ka ce min ana jiran farfaɗowarta?"
"Haka ne." Ya faɗi yana jinjina kai "to amma ba ka tambayeni komai ba?"
"Za ta bani amsa da kanta idan ta tashi in sha Allahu." Abba Habibu ya jingina bayansa da kujera cikin yaƙini. A yayin da wani ɗaci ɗaci ya dinga taso masa na tsoro sai ya dinga faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal Wakeel".