Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 2

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 2

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 2: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 2. Hannu Sadiya ta saka ta ƙara goge hawayenta duk da…

3,283 words

Hannu Sadiya ta saka ta ƙara goge hawayenta duk da hakan bai hana wasu zubowa ba, ta ja hanci tare da ru tse idanu tana cije bakinta a hankali ta buɗe baki za ta yi magana, kukan da Kalifa ya saki saboda ya tashi, shi ne ya hanata ƙarasawa. Da sauri Mama ta kai hannu ta rufe masa baki, cikin raɗa-raɗa ta ce

"Kin san dai Malam bai san kin zo gidan nan ba, ina dai gani takalmanki ma sai a bayan ƙofar ɗaki na saka su, saboda yana ganin takalmi a ƙofar ɗakin zai fahimci kina nan, kuma daga ni har ke ranmu in ya yi dubu sai ya ɓaci" Da sauri Sadiya ta ɗaga kalifa zaune tana ɗan jijjiga shi ya yi shiru, yana buɗe udanun ya wartsake ya ce

"Momma abinci" Shiru Sadiya ta yi tana tunanin abin da za a bashi, sai Mama ta matsa ta ɗakko wani ƙaramin filas da yake can gefe ta buɗe ta ce

"Wannan kashin ɗumamen Sumayya ne na safe ta ajiye sai ta dawo daga makaranta za ta ci, bari a tsakura masa" Sadiya ta ce

"Mama kin san dai yarinyar nan ba kunya gare ta ba, kina gani da muka zo ma sai da ta yaɓa min magana, ni ban san Sumy wace irin yarinya ba ce" Mama ta ce

"To Halima saboda rashin kunyarta ai ba a ƙi ba yaron nan abinci ba, kuma kin san dai kuka zai yi idan Malam ya ji kukansa kuwa zai gano kuna gidan nan kuma dai kin san ƙarshen zancen, ita kuma Sumayya sai dai na ci gaba da mata addu'a kina gani dai yarinyar nan bata raga mini ko kaɗan kamar ita ce uwar ni ce ƴar ta raina ni wallahi" Cewar Mama tana ɗakko ƙaramin plate ta ɗaukawa Kalifa tuwon aka saka ruwa aka goge masa fuskar ya karɓi tuwon yana ci.

Mama ta ce

"Ni dai abin da zan faɗa miki Halima ki yi haƙuri da lamuran rayuwa" Mama ta faɗa don ganin ta dakatar da Sadiya daga maganar da take son furzarwa daga bakinta. Idanu Sadiya ta ɗaga tana kallon mahaifiyarta a ranta tana tunanin ita sai yaushe ne za a ɗauki lamarin gidan aurenta da muhimmanci an san tana cikin damuwa da matsaloli amma sai a hanata furta komai ake bata haƙuri, basu san irin ƙangin da take ciki ba a ƙalla ko ba za a sama mata mafita ba ai a saurari damuwarta hakan zai rage mata nauyin zuciya.

Cikin sanyin murya ta ce

"Mama wai mai ya sa a kullum bakya sauraren damuwata, kin san irin zaman uƙubar da nake a gidan aurena kuwa? Koyushe na zo da matsala sai dai ki dakatar da ni ki ce in cigaba da haƙuri"

Mama ta ce

"To Halima in ban baki haƙuri ba mai kike so na ce miki, kin san dai aurenki kamar auren zobe ne ba mutuwa zai yi ba don mutuwar aurenki daidai yake da mutuwar nawa auren, ko ma in ce daidai yake da mutuwarki, kin san dai duk cikin ƴaƴa gidan nan ke kaɗai ce mahaifinki yake alfahri da mijin da kika samu kika yi aure, ni ma ke ɗaya nake dakar ƙirji in ce kina ɗakin miji, kina dai gani har kishiyoyi haushin aurenki suke ji suna ganin nasu ƴaƴan basu samu miji ba"

Sadiya ta ce

"Mama wallahi wani auren da shi gwara babu, na san ba za a ce ni kaɗai ce a cikin halin da nake ciki ba dole za a samu mata da yawa da suke cikin damuwa a gidajen mazajensu amma dai wallahi da wannan auren gani nake gwara na dawwama babu...

Katse ta Mama ta yi a daidai nan kalifa ya turo plate ɗin da aka tsakura masa tuwon, har ya cinye dama ba yawa ne da shi ba ya ce

"Momma abinci" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke, Mama kuma gabanta ne ya faɗi, saboda ta lura so yake a ƙara masa kuma dai ta san idan aka tarki ƙara masa tuwon ba zai yi saura ba, kuma dai ta san tabbas ƙarewar tuwon nan matsala ne. Filas ɗin ta ɗaga ta juye masa sai Sadiya ta ce

"Mama ya kika juye masa?" Mama ta ce

"To ya zan masa Sadiya yanzu dai kin san idan ba a ƙara masa ba kuka zai yi kuma dama cikin ɗan yaye akwai cin abinci"

Sadiya ta ce

"Ai kuma ni Sumy nake tsoro ta zo ta yi wa mutane tijara" Mama ta ce

"To mene ne baƙo a wajenmu sai ta zo ta yi abin da za ta yi"

Sadiya ta ce

"Mama wallahi Mama zaman gidan Nasir kamar zaman kurku yake a wajena, wulaƙancin yau daban na gobe da ban kuma iyayena kamar wanda suke sa,anninsa wallahi idan kin ga abin da yake min kare ma ba zai ci ba" Ta faɗa hawaye yana malalowa daga idanunta.

Baba da ya fito daga bayi ya yi alwala, ya ɗauki babbar rigarsa ya saka ya gyara zaman kuɗaɗensa a aljihunsa, ya fito zai fita masallacin azzahar ɗin ƙarfe biyu ya ji wata yarinya tana tallar awara, kiranta ya yi ya bata ɗari biyar ta zuba masa a leda ya ƙulle ledar ya kai ɗaki ya ajiye ya kulle ɗakin ya saka mukullin a aljihu, ya fito yana gyara zaman rigarsa ya fita zuwa masallaci, a ƙofar gida suka haɗu da Sumy wacce dawowarta daga makaranta kenan, kallon ta ya yi ya ce

"Sai yanzu kika dawo?" Ta ce

"Sai yanzu dai aka tashemu"

Ya ce

"Amma mai ya sa Aisha ta riga ki dawowa bayan ku duka a S.S 3 kuke?"

"Eh Baba ni ai a A nake ita kuma B na tsaya ƙarasa kwafar rubutu ne"

Ya yi ɗan jim kaɗan har ya fara tafiya ya juyo ya ce

"Kuma babu wani saurayi da kika haɗu da shi a hanya wanda ya ce yana sonki zai zo gidanku ya aure ki" Ɗan zumɓura baki ta yi a ɓoye sai ta ce

"Ni babu wanda na gani"

Ya ce

"Zan dawo ai akwai maganin farin jini naki da na Aisha zan baku gwara ku yi ku tashi" Ya faɗa yana yin gaba ita kuma a ranta ta ce

"Wai hanyar makaranta ma sai an tambayi mutum ya haɗunda saurayi, wai mu yi ku tashi sai ka ce wasu jiragen sama" Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan.

Ko sallama bata yi ba a tsakar gidan dama Mama Sa'ada kawai ta gani tana alwala ita ma Mama Sa'ada da ta san cewar Sumy bau ta ido ta ɗauke kanta saboda ta san yanzu sai ta mata rashin kunya yarinyar da hatta uwarta bata ƙyale ba. Labulen ɗaki ta bankaɗa ko sallama babu daga Mama har Sadiya suka ɗago suna kallon ta buɗar bakin Sumy sai cewa ta yi

"Kam bala'i wane ishashshe da man ne ya ɗauka min tuwo ya ba wannan ƙwalamamman yaron?" Ta faɗa tana ƙarasowa tsakiyar ɗakin ta kama tsantsa tana musu wani kallon fitsara.

Mama ta buɗe baki cikin sanyin murya ta ce

"Ki yi haƙuri Sumayya ni ce na ɗauka na bashi, ke da ɗanki yunwa yake ji...

Sumy ta yi saurin katse Mama da faɗin

"Wallahi in na yarda shegiya nake, kuma wallahi ni kar a ƙara cewa wannan ɗana ne, a toh ɗana dai a gaba zan haifa"

Mama ta ce

"Allah ya baki"

Sumy ta ce

"Wallahi yanzu ba sai anjima ba za a biyani tuwona, tun da dai ubana ne ya nemo don ya fita kunyata ya ciyar da ni haƙƙin da Allah ya ɗora masa, shi mai ya hana shi a zauna a gidan nashi uban a bashi"

Sadiya ta ce

"Wallahi Sumy ki kiyayeni bana son rashin mutunci sa'arki ce ni?" Cewar Sadiya da jajayen idanunta, dama tana cikin damuwa yanzu kuma za a ƙara mata.

Sumy ta ce

"To ƙarya na yi ne? Na ce ƙarya na yi, ai babu wani rashin kunya in kinaso ki ja wa kanki guntun mutunci to ki zauna a ɗakin mijin naki" Tsaye Sadiya ta tashi ta ɗaga hannu za ta sharara mata mari sai Mama ta shiga tsakani ta ce

"Haba Sadiya ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala ke yanzu za ki biyewa wannan sakaran"

Buɗar bakin Sumy sai ta ce

"Wallahi dai Mama kike jin tsoron Allah ji daina nuba bambanci a tsanin ƴaƴa dama ai na san kin tsane ni saboda ni ban yi aure ina kawo miki abin duniya ba, kuma ki biyani kuɗin tuwona da jikanki ya cinye" Ta faɗa cike da tsiwa, ran Mama ne ya ɓace ta ce

"Idan na biyewa zuciya sai na miki baki Sumayya amma ki bi duniya a sannu ni mahaifiyarki kike ɗagawa murya kina magana da ni kamar wanda kike magana da sa,arki ke kullum ba za ki gane annabi ya faku ba, kuna manta matsayin mahaifiya da ɗawainiyar da ta yi da ku?" Mama ta faɗa tana ɗaukan ɗari huɗu ta cillawa Sumy ta ce

"Ga kuɗin tuwon naki nan" Babu kunya ta ɗauka ta shige bedroom don faɗan da Mama ta yi ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.

Komawa Mama ta yi ta zauna daɓas ranta duk yana mata ƙuna. Sadiya ta ce

"Mama ki yi haƙuri da halayyar Sumy wallahi ko kaɗan bata ma ɗaukan abin da ake faɗa mata"

Mama ta ce

"To ya zan yi da ita Halima ai haƙuri ya zama dole in ba haka ba halayyar Sumayya sai ta saka zuciyata ta buga, dama an ce a ƙarshen duniya kuyanga za ta haifi uwar gijiyarta kuma gashi nan alamomin sun fara bayyana, tun da za ki ga ƴaƴa suna yi wa iyayensu abu kamar dai su ne iyayen"

Sadiya ta ce

"Allah shirye ta ta ganar da ita"

Zayyanawa Mama irin abubuwan da Nasir yake mata ta yi, amma Mama ta dakatar da ita hakan ya sa Sadiya ta shiga kuka tana cewa

"Mama wai mai ya sa ba za a warware min matsalolina ba, shikanan ni a haka zan ci gaba da rayuwa? ga matsalar miji ga ta dangin miji, ƙannensa sun raina ni mahaifiyarsa bata ƙaunata wallahi Mama hatta Kalifa da babu abih da ya tare musu basa son yaron nan kamar wanda agola ne sgi ba ɗan gidan ba" A daidai nan Baba da ya dawo daga masallaci zai wuce turakarsa ya fara jin tashin magana da ya ƙarasa jikin ƙofar sai ya saurara ta haka ya gane muryar Sadiya ce sai dai ba ya iya gane mai take cewa.

A fusace ya bankaɗa labulen, sai kuwa ya fara tozali fa ruwan hawayen Sadiya, gabansa ya yanke ya faɗi, Mama kuwa sosai ta shiga ɗimuwa na ganinsa babu zato babu tsammani, Sadiya kuwa jikinta ne ya ɗauki karkarwa. Baba idanu ya ƙanƙance yana yatsina fuska ya shigo ɗakin ko takalman ƙafarsa bai cirw ba saboda tsabar ɓacin rai ya tsaya yana bin Sadiya da kallo tare da jefa mata wani mugun kallo a harzuƙe ya ce

"Uban mai kike yi a gida Sadiya? Ko Nasirun ne ya mutu?" Ya faɗa yana jiran jin ba'asi Sadiya a zuciyarta ta ce

"Ni da zai mutu ma da na huta da wannan halin da nake ciki, in banda rashin kwanciyar hankali a ce mace tana jin tamkar da mutuwa mijinta ya yi. A fili kuma ta buɗe baki cikin ladabi ta ce

"A'a Baba yana nan lafiya ƙalau, dama zuwa na yi na kawo muku wuni...

Saurin katse ta ya yi da faɗin

"Sadiya mai ya sa kike da tada zaune tsaye ne wai? A kan mai na siyar da akuya za ta dawo taje cinye mini danga? Har ki ɗakko ƙafa ki taho ga ke ga ɗanki wuni guda cur, " Ya faɗa yana maida kallonsa kan Mama ya jefa mata tata tambayar ta hanyar faɗin

" Kukan uban mai take yi?" Mama inda-inda take yi sai ya katse ta da faɗin

"Ba magana nake miki ba? Ko wani sabon munafurcin ne hallaw kika saka yarinyar nan a gaba kina mata tambayar munfurci so kike ki kashe mata aurw ta dawo ta zauna a gida na samu na kawar da ita ina ƙoƙarin kawwar da sauran ƴan uwanta amma kw kina neman jiƙa mini aiki, to wallahi duk ranar da auren yarinyar nan ya mutu ki yi kuka da kanki" Ya faɗa yana nuna Mama da yatsa. Mama kai ta sunkuyar ya ƙara kallon Sadiya ya ce

"Kukan mai kike?"

Sadiya ta ce

"Wallahi Baba ko kaɗan ba na jin daɗin gidan Nasir kawai yana ta gana mini azaba da gasa mini aya a hannu... Katse ta ya yi ta hanyar dakatar da ita.

Ya buɗe baki a faɗace ya ce

"Ke banda rashin hankali wane shegen ya ce miki aljanna tana samuwa da sauƙi? Ko ana nemanta ta daɗi to ki buɗe kunnuwanki ki ji Nasiru ko yankan namanki zai ke yana ci ɗanye ba zan taɓa ganin laifinsa ba saboda rage mini aiki ya yi duk wanda zai auri ƴarka ya rage maka ɗawainiya da ita, to haƙiƙa ya gama maka komai a rayuwa, ki zauna a ɗakin ki duk runtsi ƴan uwanki gasu nan barkatai ban da maganin farin jini babu abin da nake ɗirka musu ko sa samu miji ma" ,Tun da ya fara magana kanta a sunkuye kuka kawai take shi kuma Kalifa sai suɗe plate ɗin da ya cinye tuwon yake.

Sai da ya numfasa ya ce

"Ki tashi a kan sawunki ki koma ɗakin mijin ki" Da toh ta amsa masa tana tashi tsaye ta ɗauki Kalifa ko hannu bata wanke masa ba a haka ta saɓa shi a baya, siyam - siyam kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta nufi bayan ƙofa ta ɗauki takalmin dakyar ta iya furta

"Na tafi Mama" Mama kuwa kai kawai ta shiga gyaɗa mata, raɓa gefen Baban ta yi ta fito duk abin nan da ake Sumy tana jin su zaune take a tsakiyar bedroom ɗin ta yi ɗai-ɗai da ƙafafu tana cin doya da ƙwai sai yankakkiyar gurasa a gefe wanda wani saurayi da ta gaɗu da shi a hanyarta ta dawowa daga makaranta, daga ya tsare ta yana tambayar sunanta da kwatancen gidansu shikenan sai ta ce ya saya mata, dama tana ta tunanin cin ɗumamen tuwon da ta ajiye. Ya siya mata ta saka a jaka bayan ta kwatanta masa gidan nasu, dama tana da abin da za ta ci amma ta kafa tijara sai da Mama ta biya ta kuɗin ɗumamen da aka ba ɗan ƴat uwarta Kalifa saboda rashin mutunci.

Tana fita tsakar gidan Baba ya fara sababi yana faɗin

"Saura in ga kin kwaso min ƙafafun ki a kwana kusa kin dawo min gidan nan, idan ba dubiya ko wani gagarumin dalili ba" Ya faɗa yana ɗaga murya, hakan ne ya ankarar da mutanen gidan zuwan Sadiya don lokacin da ta zo kowa yana ɗaki, amma yanzu kowa ya san ta zo.

Mama Bilki da take zaune a ɗakin ta tana cin garin kwaki da suga jin furucin Baba ta sheƙe da dariya ta ce.

"Wato ƴar da ake tunƙaho ta samu miji wasu basu samu ba, ita ce ake yi wa kashedin dawowa gida hummm a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta, da yake mijin ma ɗan tijara ne ba wani mai hannu da shuni ba ne da mai kuɗi ne in sau ashirin za ta zo gidan ai ba za a gaji da ita ba saboda an san nauyi za ta rage in ta zo, amma da aka san talaka ne mijin ita ma Allah baku mu samu ce ai gashi nan da tsakar rana ana korarta" Ta faɗa tana dariya Aisha da take danna waya bata ce mata komai ba.

A can tsakar gidan Sadiya ta juyo ta ce

"Baba don Allah ka barni in an yi la'asar rana ta yi sanyi sai in tafi, amma rana a buɗe kuma wallahi gori yake min duk ranar da na koma gida da wuri bare yau da tsakar rana"

Baba ya ce

"Ya miki goriba ba gori ba, ba mijinki ba ne ai in baki sani ba ki sani baki da gidan da ya fi gidan mijinki"

Haka ta juya ta tsaya a zaure ta goge hawayen duk da kowa yana ganinta zai gane ta yi kuka, gashi Baba ya ƙi barin ta zauna a gidan ma bare ta yi ɗan zance nauyin zuciyarta a ragu. Baba kuwa har bayanta ta bi sai da ya zo har ƙofar gida ya tsaya ya hange ta ta kama hanyar gidanta duk da akwai tazara sosau daga gidansu zuwa gidan nata. Cikin gida ya koma ta ƙara zuwa ɗakin Mama Talatu ya ƙara kora mata kashedi sannan ya buɗe ɗakinsa, ruwa ya ɗauka tare da awararsa ya zauna ya shiga ci.

A zuciyarsa yana faɗin

"In banda abin Sadiya ke da Allah ya dube ki a haihuwar fari ya baki ɗa namiji yanzu wannan yaron yana tasowa ba kin huta ba, zai ke ɗaukan ɗawainiyarki, ni ba gashi nan ba sau mata rigis nake haifa"

A ɓangaren Sadiya tun da ta kama hanya take ta zancen zuci, ta san yau sai dai ta tashe kunnuwanta don Nasir sai ya yayyanka mata baƙaƙen maganganu, ya faɗawa iyayenta maganar da take sosa mata rai kwata-kwata bai san darajar mutane ba. Gabaɗaya ta gaji a haka ta ƙaraso unguwar tasu, tana shawo kwanar gidan nata, sai ga Nasir a bayan mashin za su wuce ta, da alama daga gidan yake, amma kallo ɗaya ya musu ita da Kalifan ya ɗauke kai tamkar bai san su ba, kai tamkar ma babu wata alaƙa a tsakaninsu, a nata ganin ko da ita bai nuna ya santa ba, ai ya nuna ya san ɗansa tun da jininsa ne, duk da ta san ɗan nasa ma ba wani son sa yake ba.

Haka ta daure ta cigaba da tafiya ga zafin rana, jikinta tana jin yadda gumi yake zuba a bayanta duk rigarta ta jiƙe. Da yake a ƙofar gidan nata akwai matakala guda biyu wanda sai ka taka sannan za ka buɗe ƙofar gidan, har sai da ta taka matakalar tana tsaye a ka ta buɗe jakarta pose wacce mukulli ne kaɗai a ciki ta zaro mukullin tana shirin saka mukulli ta buɗe jamlock ɗin amma sai ta ga wani abu a jikin ƙofar wanda ya yi matuƙar bata mamaki...

MAMAN AFRAH

09025576222

[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/IQU3wL7NUTCCqrbtxkJaaz?mode=ems_wa_t

*RUWA CIKIN COKALI*

(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*

*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*

*09025576222*

BOOK 1

PAGE 3️⃣

Fitowarsa kenan daga wanka jikinsa ɗaure da towel inda kansa yake tsane ruwan da yake jikin kwantaccen gashin kansa, ƙarasowa ya yi tsakiyar ɗakin har lokacin yana goge gashin kan nasa gaban madubi ya ƙarasa ya ahiga shafawa fatarsa mayukan da suka dace da ita mayukan da suke jibge da turaruka a kan madubin tamkar an buɗe shago.

Ibrahim kenan ɗa ɗaya tilo a wajen Alhaji Sule wanda yake kira da Daddy ɗa kuma a wajen Hajiya Faty wacce yake kira da Mummy. Fari ne dogo sannan ba siriri ba ne faffaɗa ne mai yalwar kwantaccen gashin kai, yana da manyan idanu wanda suka ƙawatu da zara-zaran gashin ido da gashin gira yana da ƙaramin baki pink lips, sai dai bashi da hayaniya.

Ɗan gata ne na ajin ƙarshe a wajen iyayensa mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne kuma tsohon ɗan siyasa, iyayen Ibrahim suna matuƙar son sa, basa son ɓacin ransa, sai dai bashi da mata hatta budurwa ma bashi da ita, tun da ya dawo daga ƙasar america da ya kammala karatunsa yake kula da kamfanonin mahaifinsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull