Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 24
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 24: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 24. "Subhanallahi Allah rabamu da tashin hankali ni fa…
3,322 words
"Subhanallahi Allah rabamu da tashin hankali ni fa dama jiya ganin kina kumbure-kumbure shi ya sa ban tsaya yi miki sallama ba, saboda na ga sai ki mini rashin m... Aliyanta katse ta da faɗin
"Amatullahi Kasim mata maza ne" Amatullahi zaune ta tashi daga kan doguwar kujerar da take kwance a falon gidansu tana mai saka hannu ta toshe bakinta ta ce
"Mata maza fa? Ke yanzu Aliya duk bita da ƙullin da kike yi wa mutumin nan sai kin bishi da sharri?" Aliya cike da haushi ta ce
"Wai sharrin mai kike nufi? Ina miki maganar tsakani da Allah mata maza ne Kasim amma kina wani batu" Amatullahi ta ce
"Innalillahi mun shiga uku, kuma kika zauna a gidan Aliya?" Aliya ta ce
"To ya zan yi?" Amatullahi ta ce
"To ke ba shikann ba kin samu maƙalar rabuwa da shi sai ki ce ya yaudare ki bai sanar da ke ba in ya so kin ga kin samu hanuar yakice shege daga rayuwarki dole ya sake ki tun da babu wacce za ta zauna da mata maza, kin ga burinki yana dab da cika na auren mijin Jidda tun da ba uwa kuka haɗa da ita ba, sannan ba uba kuka haɗa ba bare a ce ya hakan ya haramta" Dididim gaban Aliya ya buga a take ƙwaƙwalwarta ta fara mata safa da marwa lokaci guda wani abu ya ɗarsu a zuciyarta, sai dai furucin Amatallahi ya katse matq hanzari in da ta ce
"Ina fatan dai babu abin da ya shiga tsakaninku, don mar a je yin abu sau ɗaya ya ɓata miki abubuwa dubu!" Aliya cikin rashin fahimta ta ce ban gane ba?"
Amatallahi ta c
"To idan yi ɗaya an samu ƙaruwa fa kin ga ko sakin ki ya yi ya barki da jelar goyon ciki da reno"
MAMAN FRAH
09025576222
[11/7, 9:00 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/GTq4oSxwxZfLKU7Amx5My1?mode=wwt
*RUWA CIKIN COKALI* (Ya ishi mai hankali wanka)
*NA*
*MAMAN AFRAH*
BOOK 1️⃣
PAGE 1️⃣6️⃣
Wannan grp ni
MAMAN AFRAH na buɗe shi ne domin masu soh saya kayan sallah su yi adashe, za ka zaɓi abin da kake so ka zuba kuɗinka ya danganta da yadda kake so. Duk abin da ka zuba a rubuce yake daga ka gama za a baka kaya.
1-Leshi 4-abaya
2-Atamfa. 5-kayan yara
3-shadda 6-Mayafai
7-Takalmi da jaka
8- Takalman yara
Da sauransu idan har kin san ba yi za ki yi ba karki shiga min grp don cire ki zan yi, ba wasa ya taramu a ciki ba.
Maman afrah
09025576222
*SADIYA*
Tun da suka ɗauki hanyar gidan gabanta yake faɗuwa, tunaninta ɗaya kar Nasir ya yi wa Baba tijara a gabanta domin ba za ta ji daɗin hakan ba, duk da shi Baban yana ganin yana musu ruwan kuɗi amma da alama har yau bai san waye Nasir ko kuma dai ya sani takewa yake yi. A ɓangare ɗaya na zuciyarta yana cike da fargabar ko dai Nasir ya sawwaƙe mata ne babu laifin fari bare na baƙi duk da cewa ita ba tsoron sakin take yi ba kawai tana shayin halin Baba ne yadda yake da son aurar da ƴaƴa tamkar rai da mutuwa. Duk da yanzu ta samu sassauci na zaman gashin ƙumar da Nasir yake mata a cikin gidansa kuɓa ba komai ba ne ya kawo mata wannan sauƙin sai sana'ar da take yi don ta lura da cewa idan har kana da sana,a to baka ma jin zugin ɓacin rai idan an maka saboda wani sa,in rashin zaman lafiyar da yake wanzuwa tsakanin wasu ma,auratan har da ganin matayensu basu da sana,a bare aikin yi, suna ganin duk wata ɗawainiyar mace su za ta ɗorawa amma ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wani namijin ko kina sana,a ko aiki babu ruwansa da harkar kuɗinki kuma zai yi abin da ya dace da ɗaukan gabaɗaya ɗawainiyarki da sauke haƙƙinki da ya rataya a wuyansa. Wani namijin kuma shi yana jin daɗi ya ga matarsa tana da abin yi wato ta tsaya da ƙafafunta har ma da kansa zai ke ƙara mata ƙarfin gwiwa, wani kuma sai dai ma ya san duk yadda zai yi domin ganin ya murƙushe komai don kar ki ci gaba saboda yana baƙjn ciki wani kuma yana tsoron ki samu wani ci gaba ko ɗaukaka ki fi ƙarfinsa kowa dai da yadda ya ɗauki rayuwa kuma da yadda yake kallon ta.
Sadiya bata san sun shigo layin gidan nata ba domin ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula maganar Baba ce ta katse mata tunanin har hakan yansa mai napep ɗin jan wani uban birki don ya tsorata da furucin Baba ya ɗauka ma wani gagarumin abu ne ya faru, jin Baba ya ce
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wannan furucin da ya yi da ƙarfi tamkar wanda ya hango wani gagarumin haɗari ya tunkaro su,shi ne ya sanya Sadiya dawowa hayyacinta a kiɗime tana ciccira ido domin ganin abin da yake faruwa, shi kuma mai napep har da sauri kashe kiɗan da ya ƙure ya tsayar da napep ɗin tare da juyowa ya ga abin da ya faru. Baba kuwa kuwa babu ruwansa da kiɗimar da ya saka su bai yi bori da sanyin jiki ba ya ce
"Wai don Allah mai ya sa Nasiru yake son tona mini asiri ne? Ya zai mayar mini da ƴa gida kuma ya garƙamawa gidan mukulli gidan uban wa ya tafi to?" Ya faɗa ya ɗorawa Sadiya Kalifa a cinya, ita Sadiya sai lokacin ta lura da gidan a kulle kuma ta gane duk wannan ɗaga jijiyar wuyan da Baba yake saboda gidan a rufe ne da yake ma basu gama ƙarasowa gaban gidan ba, dogon wuya Baban ya yi ya hango.
Baba kuwa fita ya yi daga cikin napep ɗin duk ya gama tada hankalinsa sai baza uwar babbar riga yake tana neman taɗe shi, Sadiya ta ma rasa bakin magana ikon Allah kawai take kallo, shi kuma mai napep da ya gane mai Baban yake yi wa baloƙoƙon sai ya ja wani ƙaramin tsaki ba tare da kowa ya ji ba. Baba kuwa ƙarasawa bakin ƙofar ya yi ya taka matakalar ƙofar gidan ya taɓa kwaɗon (Padlock)Ɗin da aka rufe gidan cike fa faɗa ya ce
"Sadiya wai ni kika rako ko kuwa ke na rako da kika zaune a adaidaita sahun? " Cikin sanyin jiki Sadiya ta fito tana cewa
"Baba gani na yi gidan a rufe" Yana harararta ya ce
"Kuma don gidan a rufe sai ki zauna a ciki kamar wanda dai so kike ki koma gidana" Bata tanka masa ba ya tsaya tare da kama ƙugu yana hangen ta inda Nasir zai fito. Mai napep kuwa ya wani sako ƙafa waje ya ɗauki mataji(Kumb)Ya ɗan taja gashin kansa cike da tantiranci ya ce
"Yallaɓai karka manta dai duk tsayuwar da nake yi a wajen nan a kuɗi take don haka yawan jiran da zan yi yawan hauhawar farashin kuɗina" A zuciye Baba ya ce
"Abin da ya fi hauhawar farashin kuɗinka, sai ka ce sata kana tsaye ba tafiya kake yi ba bare ka ce mai kake ƙonawa amma kake batun kuɗi yo ba zan biya ba, bayan ma zuwan nawa babu biyan buƙata" Wani irin durowa ya yi daga napep ɗin ya tsaya Baba yana jifansa da wani kallo, mai napep ya waiwaya ya ga layin ba kowa yana ɗaga rigarsa sai ya zaro wata zarɓeɓiyar wuƙa soke a jikin wandonsa, da sauri Baba ya matsa a kiɗime har yana zamewa ya surmiyo daga saman dakalin ƙofar gidan, mai napep ya ce
"Bani haƙƙina, in ba haka ba in farɗe maka ciki daga kai har ƴaƴan naka" Da sauri Sadiya ta ƙanƙame Kalifa cike da tsoro dama ita sai ta ga ma tamkar wani ɗan shaye-shaye ne Baba hannunsa yana rawa ya saka a aljihub babbar rigarsa sai ga kuɗi ya fito da su ƴan dubu-dubu kusan dubu ɗari biyu bakinsa yana rawa yake faɗin
"Nawa ne kuɗin naka har na jiran da ka yi" Mai napep ya ce
"Dubu da ɗari biyar" Baba hannu yana rawa ya ce
"Ga dubu biyu ka riƙe canjin" Karɓa mai napep ɗin ya yi ya mayar da wuƙar ya koma cikin napep ya ɗakko ɗari biyar ya jefawa Baba ya ce
"Ni da kake ganina haƙƙina nake nema, babu ruwana da sai na karɓi haƙƙin wani shi ya sa ba na sata, na gwammace duk runtsi na nemi na kaina na kaucewa wulaƙanci, kuma ni da kake gani ko akuya ban taɓa kashewa ba ita ce dai dabba bare kuma mutum kawai barazana ce saboda masu ci da haƙƙin wani" Yana gama faɗar hakan ya shiga napep ɗinsa ya tada ya kunna waƙa ya yi kwana ya bar wajen a guje.
Baba ɗari biyar ɗin ya ɗauka ya zauna a kan dakalin yana faɗin
"Wasu yaran zamanin fitsararru ne, ashe ma duk bige ne ba iya caka wuƙar zai yi ba, ai wallahi da na san haka ne da dubu ɗaya zan bashi" Ya faɗa yana haɗa kan kuɗin ya mayar aljihu, Sadiya kawai kallonsa take da mamakin kalamansa duk da babu wani abu sabo a lamarin Baba.
Ranta ƙuna yake bai dace a ce ya yi mata abin da ya mata ba, ta yaya za a yi a ce mijinta ya kaita gidan ya tafi ahi kuma ya dawo da ita. Waje ta samu ta zauna take ganin ikon Allah sun kwashe ya fi minti arba,in amma babu alamar Nasir sai mutane da suke wucewa, Baba sai hamma yake a jere can da ya gaji ya ce
"Tashi mu je gidan mahaifiyarsa ki zauna w can ki jira shi, ai in ya dawo ya je can ya ɗakko ki" Wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata, jin wai gidan sirikarsa zai kaita, sirikar da ita ce silar duk wasu abubuwan da suke faruwa, sannan ta yi imani da Allah sai sun yi wa Baban wankin babban bargo sannan kuma ya bar mata abin gori na cewar ubanta ne ya dawo da ita. Kamar daga sama ƙwaƙwalwarta ta kai mata wasu tunani a take ta zaɓi ta yi wa Baban ƙarya don tsira da daraja da mutuncin ta, duk da ƙarya ba ɗabi'arta ba ce kuma ba halayyar ta ba ce.
Cike da danne abin da ya ɗarsu a zuciyarta ta ce
"Baba ai Hajiyar bata gari ta yi tafiya" Kamar wanda ta faɗa masa saƙon mutuwa ya ce
"Subhanallahi bata gari kuma? Amma ai ba za a rasa sauran ƴaƴan nata a gidan ba" Da sauri ta ce
"Tare suka tafi" Ya numfasa ya ce
"Kai ni dai na ga ta kaina wallahi yaron nan yana son tada mini hawan ruwa, to ke dama baki ɗauki mukulli ba" Sadiya ta ce
"Shi ya datse gidan da kansa"
Baba ya ce
"Dama ya shirya shuka tsiyar nan amma dai mu je gidan, kuma wallahi sai dai mu tafi a ƙafa ba zan biya kuɗin adaidaita ba" Yana faɗa ya fara tafiya, haka Sadiya ta bi bayansa tana ɗauke da Kalifa a kafaɗarta, ranta har ya mata daɗi ganin Baban bai zubar mata da mutunci a wajen Nasir da mahaifiyarsa ba, duk da ta san da wuya ne idan bai faɗa masa cewa ya rakata gidan a rufe ba.
Suna tafiya yana masifa wayar Nasir kuwa ya kira ya fi a ƙirga amma bata shiga, ko da suka koma gidan ɗakinsa ya shiga ita kuma ta je ɗakin Mama Talatu.
Mama ta ce
"Sadiya yankuka dawo har gabana ya faɗi ko dai dama yaji kika yi shi ne kika yi ƙaryar tare kuk?" Kai kawai ta girgiza.
Sai a ɗakin Mama Habiba suka kwana saboda Sumy ta kafa rashin mutuncin Kalifa ba zai kwamta a katifa ya musu fitsari ba, shi kuma ɗakin ƴanmatan dama bata ma tarki zuwa ba saboda ta san rashin kunya za su mata.
Baba washe gari bai je kasuwa ba, ya kasa fita saboda gani yake tamkar igiyar Sadiya ce za ta tsinke idan ya bar gidan, wato kamar in baya nan Nasir zai dawo ya kawo takardar saki, amma idan yana nan ko da ya zo da niyyar sakin zai roƙe shi ya fasa sakin. Har wajen goma wayar bata shiga, wayar Arfat Baba ya karɓa ya saka lambar Nasir ya hau doka masa kira sai kuwa ya ɗauka da ta kusa katsewa.
Nasir ya ce
"Hello" Baba ya ce
"Buɗe muryarka da kyau Babanka ne mahaifin Sadiya" Da sauri Nasir ya cire wayar daga kunnensa ya duba ya dai tabbatar da numbar Baba ba ce dona ya san ya saka duka lambobin Baba a black list. Jin haka sai Nasir ya ce
"Hello ba na ji" Ya faɗa yana ciro wayar daga kunne ya shiga hura iskar bakinsa da ƙarfe, yadda Baban zai ji, Baba jin haka ya buɗe baki yana faɗi
"Baka ji na Nasir" Nasir da sauri ya katse kiran, yana shirin saka lambar a black list sai kiran ya sake shigowa haka ya ɗauka Baba ya ce
"Nasir mai ya sa ka kawo Sadiya gida" Nasir yana taɓe baki ya ce
"Laifi ta yi" Baba ya ce
"Amma wannan an yj shegiyar yarinya amma ta ce babu abin da ta yi ka kawota" Nasir ya ce
"Ruwa ai ba ya tsami banza" Nan Baba ya shiga bashi haƙuri duk da bai ji laifin da ta yi ba yana cewa zai saɓar mata Naair ya ce
"Baba kawai a kan maganar matar da zan aura za ka ja mata kunne, ta ce bata son raini in ya so yanzu zan kira wacce zan aura ɗin sai na faɗa mata ka bani haƙuri in ta haƙura to" Baba tsabar son zuciya bai ma ji zafin maganar Nasir ba ya ce
"Amma Sadiya an yi sakarai kishiya ai abokiyar zama ce, kuma ita a gidan ubanta ba mata huɗu ta tashj ta gani ba, ka bata haƙuri za a ja mata kunne" ,Nasir ya amsa yana kashe wayar, don dama jiya daga gidan Baba gidan Hajiya ya je ya faɗa musu komai sai dai su Husna suka ce kar a sake ta saboda gwara ta zauna ta ƙunshi baƙin ciki. Haka Nasir ya kira Meenal ya bata haƙuri yana faɗa mata wai Baban Sadiya yana bashi haƙuri don kamar ma a muryarsa kuka ya ji yana yi, saboda tsabar ƙarya irin ta Nasi, iya kuma Meenal kanta ya mata girma jin ana bata haƙuri kuma yanayin yadda aka ce Baban Sadiyar ya bata haɗuri hakan na nufin Sadiyar bata da wani galihu a wajen ubanta, domin haka ya sa ta ƙara ɗaura ɗamarar yin duk yadda ta so idan ta shiga gidan, don mayar da Sadiya gida da ya yi ba ƙaramin matsayi ta gane tana da shi a wajen Nasir ba don har Hibba ta kira ta tana faɗa mata yadda aka mayar da Sadiyar gida, sosai abin ya faranta mata, sai dai abin da bata sani ba shi lamarin duniya yau naka ne gobe na ɗan uwanka, in dai namiji yana wulaƙanta matarsa to indai ita wacce bata shigo gidan ba tana da hankali to ba murna ya kamata ta yi ba illa jajantawa kanta, tun da duk abin da aka yi wa ta cikin gidan ke ma wataran zai iya miki.
Mama Habiba wacce ta shigo ɗakin Baba ta same shi yana waya ta ce
"Wallahi abin da kake baka kyautawa, kai ba za ka ƙwatawa ƴarka ƴanci ba sai dai ka zubar mata da kima a gidan aure, baka san wannan zubar mata da daraja zai yi a wajen miji da kishiya kai har ma da dangin mijin ba, ai kamata ya yi ka nuna musu ita ma ƴa ce ka nuna ƴarka ta fi ƙarfin wulaƙanci, ka nuna masa tana da gata tana da galihu sannan kuma ko yau ya sakar maka ita za ka iya riƙe ƴarka, amma ya kawo ta gida ya tafi ka kasa samunsa a waya ka ɗauke ta ka matar da ita yanzu ka ari waya ka kira shi yana maka maganar banza. Ai ita mace tana da kima da daraja, kuma kamata ya yi a kowane lokaci a sauarari kukanta a ji matsalolinta da take ciki na gidan aure, a maganace mata matsalarta a ƙalla wannan shi ne gatan da za ta samu, kuma mijin ma ya gane ba shi kaɗai ne gatanta ba anuna masa ta fi ƙarfin wulaƙanci, amma kai da ya maka laifi ya dawo maka da ƴa babu wani dalili me ƙarfi ka zo kana bashi haƙuri shin wannan kaɗai ba zai saka gobe ma ya ƙara ba?K... Miƙewar Baba tsaye a zafafe ya hana ta ƙarasa maganaryana kumfar baki ya ce
"To uwata Habiba faɗa mini yadda zan yi tun da ke ce mijin ni ne matar" Mama Habiba ta ce
"Ni dai ban ce ba amma ita gaskiya dama ɗaci ne da ita" Baba ya ce
"Kin zo kina ta tada jijiyoyin wuya, shin ke kin san ciwon ɗa ma? Ke da baki taɓa sanin zafin ɗaukan ciki da naƙuda ba baki san ya son ɗa yake a zucuyar iyaye ba har kika zo kina wata maganar banza" Jin furucinsa ta tashi tsaye ba tare da ta ce komai ba ta juya ta fice a ɗakin ra saka takalmin ta ta tafi.
Baba kuwa Nasir ya ƙara kira sai Nasir ɗin ya ce babu komai, don dama ita ma Meenal an gama zugata a kan cewa kar ta yarda a saki Sadiyar ta bari su zo su jera don Sadiyar ta fahimci ruwa ba sa,an kwando ba ne.
Hakan ya sa Baba ya ji daɗi a ransa a ƙalla dai daga ƙarshe Sadiya za ta koma ɗakinta tun da ba sakinta aka yi ba, Arfat ya ba wayarta ya je ya samu Sadiyar ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, yana ta batun kar ya sake jin an kawo ƙaranta a kan ta yi wa matar da Nasir zai aura wani laifi don haka ta saka a ranta ba da ita kaɗai zai rayu ba sannan ko bayan an yi auren idan ma cewa Nasir ɗin ya yi take gaishe da matar tasa to take yi ai durƙusawa wada ba gajiyawa ba ne kuma zama lafiya ya fi zama ɗan saki.
Ƙirjinta tamkar an saka dutsi haka take jin zafin maganganun Baba amma ta danne ta amsa masa, saboda yin biyayya ya zama dole tun da bai saɓawa addini ba.
A take ya saka ta shirya ya ce ta kama hanya ta tafi har da bata kuɗin napep ɗari biyar. Tana fita ya tafi kasuwa, ita kuwa dama gidan maƙota ta shiga ta saka yara suna duba mata ana cewa ya tafi ta dawo gidan, sai da la'asar sannan ta tafi saboda Mama Habiba ce ta ce ta yi haka kar ya ga ta koma da safen wani rainin ya biyo baya duk da dai babu rainin da Baba bai ja mata ba.
Babu wanda ma ya kawo ta a ka bare har a faɗa masa cewa bata tafin ba.
JIDDA
Har ya gama waya da Mummy amma Jidda ko motsi bata yi ba bare ya sa ran za ta tashi, ƙara gyara filonsa ya yi ta hanyar daidaita kansa bisa filon, hannunsa ya rungume a ƙirjinsa idanunsa ƙirrr a kan kyakkyawar fuskarta da yake jin babu wata mace da ta kai masa Jiddansa kyau, sosai yake jin sonta da sabuwar ƙaunar ta da ta ƙara dasawa a zucuyarsa a daren jiya yana ƙara huda masa zuciya, lallai ya yarda babu abin da ya fi ga ɗiya mace sama da ta kai mutuncin ta gidan aurenta, saboda hakan ba ƙaramin daraja yake ƙara mata ba wacce ba za ta yanke ba har abada a wajen mijin nata, domin yau sai ya ji kima da darajar Jidda ya wuce na koyaushe a zuciyarsa sannan alƙwari ne ya ɗaukawa kansa cewa zai kula da ita sannan ya mutunta ta don ta sadaukar da komai saboda shi, idan ya ce komai ciki har da aurensa.