Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 25
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 25: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 25. Idanunsa suna a kan fuskarta bacci ya ƙara wartarsa,…
3,353 words
Idanunsa suna a kan fuskarta bacci ya ƙara wartarsa, bayan wani lokaci kaɗan Jidda ta ɗan yi motsi sai kuma ta runtse idanunta da ƙarfi kafin ta ɗan buɗe su, ata musu masauki a ko ina ba sai a kan Ibrahim da yake bacci, ita kanta ta ba kanta dariya domin kuwa sai da ta ji gabanta ya ɗan bada rass sakamakon ganinsu a gado ɗaya sai sannan ne ta tuna ashe fa sun yi aure!. Murmusawa ta yi a lokaci guda tana tuno da ƴar uwarta Aliya tana rayawa a ranta cewa Aliya ma ta kwana cikin wannan shauƙin mai wuyar fassaruwa. Zaune ta tashi tana son ta sauka ƙasa don zuwa ta samar da abin da za a yi break fast da shi, tana zura ƙafafunta ƙasa Ibrahim da tun tashin ta zaune motsin ta ya katse masa baccin. Tana dab da sauka sai ta ji an riƙo mata hannu wata kunya ce ta turnuƙe ta tana ta tunanin da wane ido za ta kalle shi, sai ta ji ya ce
"Haka ake tashi daga kan gadon miji babu sanarwa? Ko dai sai na koya miki yadda ake kula da miji?" Ya faɗa yana kama ɗaya hannun nata ya juyo da ita suke fuskantar juna amma yana daga kwance, ita kuma duk kunya ta lulluɓe ta sai kawai ta sunkuyar da kai tana kallon ƙasa sai dai yanayin fuskarta yana nuni da mrmushin da take da alama maganar da ya yi ce ta bata dariya.
Bai jira mai za ta ce ba ya ce
"Ai ni in baki iya kula da ni ba sai na koya muki yadda za ki kula da ni, amma sai kina buyana albashi duk wata" Bata san lokacin da dariya mai sauti ta suɓuce mata ba, bata san mai ya sa su maza basa jin kunya ba. Tana cikin wannan dariya ta ji ya ce
"Wato dariya na baki ko? To tayani in tashi zaune, kin san yana daga cikin ba mijin kulawa matarsa ta kama hannunsa ta tashe shi zaune" Idanu ta runtse ta ma rasa ya za ta yi ko dai ta furta masa da bakinta cewa kunyarsa ta mata shamaki da furta komai sai dai laɓɓanta sun ƙi bata haɗin kai. Yana riƙe da hannuwan nata ya tashi zaune sai dai bai sakar mata da ƙarfinsa ba, sai da ya zaune gwiwarsa tana jingine da jikinta ya ce
"Kar ma ki ce ke kika ɗagani domin ni na tashi kaina, ai ni yanzu na gane bani da gata ita ma Mummy ɗazu da ta kira ni sai faɗa take kar na bar mata ƴa da yunwa, Allah sarki ni babu mai kulani sai dai ko Daddyna" Idanunta a ƙasa ta ce
"Shi ɗin ma Daddyna ne" Bakinta ya ƙurawa ido yadda ta yi maganar tamkar ba daga bakinta maganar ta fito ba, sakin ɗaya hannun nata ya yi ya saka hannunsa ɗaya ya ɗago haɓarta idanunsu suka sarƙe da na juna duk wanda zai ga yadda kallon yake wakana haƙiƙa zai gane soyayya ce mai cike da ƙaunar juna, kulawa sadaukarwa haɗe da tsantsar yarda da juna ce a tattare da masoyan, sun daɗe a haka kowane ɗaya daga cikinsu ba ya son ya ƙifta musayar kallo ne na soyayya yake afkuwa, kowa ya tsinci kansa a yanayin ne ba tare da shiryawa hakan ba.
Ɗaya hannun ya kai ya riƙe gefen fuskarta ya ce
"Jidda ina ƙaunarki da dukkan zuciya da ruhi, hatta gaɓoɓin jikina kowace gaɓa ta san da zaman soyayyarki Jidda" Murmushi ta yi ta ce
"Ni ma ina ƙaunarka" Bata ankara ba ta ji ya saki riƙon fuskarta da ya yi da kuma tallafo haɓarta sai gani ta yi ya ɗaga hannu sama yana godewa Allah, ita ma sai ta tsinci kanta da ɗaga nata hannun tana maimaita duk wata godiya da kirari da ta ji yana yi wa ubangijin talikai.
Wanka suka ƙara yi da ruwa mai ɗumi bayan sun fito yana shiryawa sai suka ji horn hakan ya sa ya gane saƙon Mummy ya iso, yana jin lokacin da me gadin ya buɗe ƙofa.
A saman ta baro shi yana shiryawa ta sakko ƙasa bayan ta saka kayan da ta cire, Ɗakin da aka kaita ta shiga, ita sai yanzu ne ma take ƙarewa falon kallo tamkar a wata ƙasa take da ban. Bayan ya gama shiryawa cikin farar shadda gezna sai sheƙi take tana ƙamshi ga turaruka masu aji da ya feshe jikinsa da su. Nocking ya ji a bakin ƙofar ya sakko cikin nutsuwa yana ɗaura agogo a hannunsa, yana buɗewa mai gadi ya gaishe da shi cikin girmamawa, amsawa ya yi ya karɓa kwandon da ya kawo yana sanar da shi direba ne ya kawo daga gidan Mummy. Faɗwa mai gadin ya yi cewa ya san da zuwan nasa shi kuma ya juya Ibrahim ya rufo ƙofar ya dawo ya nufi kan dining ya ajiye kwandon amma a ƙasa a gaban dining ɗin.
Ɗakin ta ya nufa lokacin tana gaban drower ɗinta bayan ta bar gaban madubi inda ta tsaya shafa kwalakca da humra da sauran body spray da shuwa masu bala,in ƙamshi don kan madubin ya sha jere tamkar an je shago, drower da ta buɗe yadda kaya suke a jere sai da ta ji wani iri yau ita Jidda ce wacce Umma take ƙwace mata duk wasu kaya masu kyau da nagarta idan Abba ya ɗinka musu amma gashi komai ya zama tarihi tun da gashi yanzu kaya masu tsadar da bata tama tunanin ko a mafarki za ya saka irinsu ba.
Tabbas komai na rayuwa idan ka yi haƙuri zai zama tarihi watarana!. Yanzu gashi komai ya wuce, yana sako kanshi ɗakin tsabar ƙamshin turarukan da suka bugi hancinsa hatta sallama suɓuce masa ta yi, kasancewar tamkar wanda aka yi ɓarin turare a ɗakin abin birgewar ma ba za ka taɓa gane wane irin ƙamshin turare ba ne. Jin alamun mutum ya sa ta waiwayo kasancewar tana ɗaure da towel da yake da ta shigo kayan ta cire ta ɗauki wani towel sabo ta ɗaura, ganin ya tsaya a rungume hannunsa yana mata wani kallo bata san lokacin da ta ce
"Sannu da zuwa" Maganr tata ta bashi dariya sai ya ce
"Kin manta kin gaisheni ɗazu yanzu kuma sannu da zuwan ta mene ne?" Bata amsa ba din ita kanta ta ba kanta dariya. Bata ankara ba sai ta ganshi ya zo dab da ita ya kama dantsen hannunta duka biyu sai gani ta yi ya janyo ta ya zaunar da ita a bakin gado, wucewa gaban drower ya yi ya tsaya yana ta ƙarewa kayan ciki kallo amma sai ta ga ya rufe, wata ya buɗe sai kawai ta ga ya ɗakko wata riga daga gani ba za ta wuce gwiwa ba sannan sai aka mata ƙaramin hannu, daga gaban rigar akanyi hoton heart babba daga ƙara aka rubuta GIRL da manyan baƙi.
Miƙo mata kawai ya yi ya ce
"Ita nake so ki saka" Karɓa ta yi a ranta tana cewa
"Ka ji kaɗan ka ji da yawa, ni Jidda dama a gidan auren miji ne yake zaɓa maka kayan da za ka saka?" Ta tambayi kanta sai ta ji yana cewa
"Ba zan ɓoye miki ba Jidda tun da na shigo ɗakin nan na tsinci kaina a wani yanayi mai wuyar fassara, sai dai ina tausaya miki kasancewar daren ki na farko ne kuma na yi dogon zango amma ba don haka ba, da sai kin mayae da ni ruwa" Kallon rashin fahimta ta masa ya ɗora da faɗin
"Ina shigowa da na shaƙi ƙamshin turaren nan sai ya sakani a wani yanayi, tabbas turare yana taka muhimmiyar rawa wajen haifar da yanayi a tsakanin mace da namiji, shi ya sa aka haramtawa mace ta saka turare ta fita waje maza suna jin ƙamshin, dalilinnda ya sa ake rubuta mata alhakin zina saboda ƙamshi yana tada sha'awa ne duk wani namiji idan ya ji ƙamshin turaren zai ji sha,awarta" Kai kawai take kaɗawa bayaninsa yana shigarta duk da mafi yawan mata sun yi watsi da wannan maganar suna cin karensu babu babbaka, musamman da ya kasance yanzu har kabbasamata suke yi a kayansu, su gama turara kaya su saka su fita sun manta da haramcin hakan.
Yana faɗa mata ya buɗe ɓangaren bra da panties ya ɗakko mata fararen set ya bata, bra ɗin pant ɗin, ganin tana wani juyawa kamar kunya take ji sai ya fita yana dariya, ta saka tare da ɗora rigar da ya zaɓo mata, jin yana kiranta ta fito tana amsawa wani mugun kyau ya ga rigar ta mata hakan ya sa ya ga tamkar dama don ita aka yi rigar tabbas aure rahma ne, Allah azurta kowa da mace da kuma miji na gari.
ALIYA
Wani irin bugawa da ƙarfi zuciyarta ta yi har numfashin ta yana barazanar mata wahalar shaƙa, jin furucin Amataullahi, a take bakinta ya bushe babu ko ɗigon lemar da za ta sanya laɓɓanta da suka yi gaggawar bushewa su jiƙu. Bata san tana da zafin nama ba sai da ta ganta tsaye ƙiƙam a kan ƙafafunta da zuwa lokacin sun fara karkarwar gaza ɗaukar gangar jikinta ba komai ne abin da ya razana ta haka ba illa furucin Amatullahin da ta ce tarayyarta da Kasim sau ɗaya zai ruguza mata abubuwa dubu, sannan in har a tarayyar da aka yi an samu ƙaruwa hakan yana nufin zai barta da jelar ciki da reno ma'ana shikenan ya yi sanadin rugujewar burikanta ciki kuwa har da mallakar Ibrahim matsayin miji da kuma zama kishiyar Jidda don ta mata gashin ƙuma!.
"Hannunta yana dafe da ƙirjinta ɗayan kuma tana riƙe da wayar da take kunnenrta ta ce
"Na shiga uku Amatullahi, wallahi ya yi tarayya da ni" Amatullahi ta ce
"Wato ya kalamance ki da kalamansu na maza ko har kika yarda ya karɓe budurcin, kenan daman jiya duk burin kunyar ƙarya ne kike yi?" Cike da takaici Aliya ta hau labarta mata cewar ita fa ba wai da saninta ba, gabaɗaya ma vata cikin hayyacinta abubuwan suka faru. Nana Amatullahi ta ce
"To kuwa ba a bori da sanyin jiki, za ki iya ƙwatarwa kanki haƙƙi, tun da wannan ai an yi zamba cikin aminci, an sakanyaudara a lamarin tun da an rufe ku, ta yaya za ki auri mata-maza Aliya, duk kyau da ajinki amma ki ƙare a mai mafitsara biyu, Allah dai ya sa ma dai bashi da breast a ƙirji a toh don idan mun zo gidan kar muke kasa bambance tsakanin aya da tsakuwa, ma'ana muke kasa gane ki da kuma shi tun da baku da bambanci a halitta" Kuka Aliya ta fashe da shi ranta yana ƙuna tana jin tsanar Kasim ta ce
"A yau ba sai gobe ba Kasim zai sakeni!. Ba zan zauna da shi ba, wannan ai yaudara ce tsantsa, ko kotu na kai shi ya cancanci kowane hukunci" Tana maganar tana kuka, ita kuma dama tana jin haushin Aliya ta yi aure ta barta hakan ya sa ta ringa zuga Aliya don ta kashe auren su zama ɗaya.
Sai da ta gama ɗora Aliya a tamfa sannan ta kashe wayar Aliya ko kiran Umma bata tsaya yi ba, ɗaki ta nufa a sukwane ta saka kaya kala biyu a kit ɗinta ta ɗauki hijabi ta saka, hannu ta miƙa za ta ɗauki wayarta da ta ajiye wani takaici ya sake cikata ganin screen ɗin kwatsa-kwatsa tana tuna cewa wai yanzu ita Aliya ce da wannan ƙazamar wayar Jidda kuma da bata isa komai ba mummuna ita ce mai iphone, sannan ita tana wannan ƙazamin gidan Jidda tana katafaren gida, daɗin abin haushin shi ne Jidda lafiyayyan namiji take aure ita kuma mata-maza tabbas wannan yana nuni da cewa ba ƙaramar tazarw ba ce a tsakaninsu.
A zuciye ta ɗauki wayar kamar ta buga ta a bango sai dai ta lallashi zuciyarta don ta san yanzu dai bata da wata wayar sai wannan, fitowa ta yi lokacin tana tsakar gidan ta ga kiran Umma yana shigowa hakan ya sa ta kashe wayar ma baki ɗaya, don ta ƙudurta a ranta sai dai Umma ta ganta a gida, duk da cewa wata zuciyar tana bata shawarar kar ta je gidan saboda kar ta fusata Abba ya ɓata mata rai, amma kuma in ta tuna cewa lamarin mata-maza saj ta ga ba magana ce da za a yi sanya ba, watsar da shawarar zuciyarta tata ta yi kan maganar zuwa gidansu Kasim don ta fi so ta je gidansu in ya so idan Abba ya zo ya ji abin da yake tafe da ita sai ya yi magana da mahaifin Kasim a kawo mata takarda, don ta yi imani da Allah babu wani wanda zai do ƴarsa ta zauna da mata maza ga shi uwa uba ma ƙin sanar da ita da aka yi kafin auren.
Kasim da suka gama waya da Salis sai ya shiga wani shago da yake gefe yana son sayan alewa ya yi sadaka, domin wannan lamarin na Aliya sai da sadaka, shigewarsa shagon ya yi daidai da fitowarta don haka ko ƙofar gidan bata karo ba ta bar masa ita a buɗe wayam. Ɗaya ɓangaren ta yi ba inda shagon da Kasim ya shiga ba, don haka bai ganta ba, tana riƙe da kit ɗin tana tafiya kamar za ta ci da ka ta matsu ta ganta a gida ko ta amayar da abin da yake bakinta don bata gane cewa a babbar matsala take ba sai da ta yi magana da Amatullahi hmmm wai ita Aliya da ta gama shirya rayuwar gidan aurenta ta jin daɗi da holewa ita ce ta ƙare da auren mata maza har ana cewa wai ba za a bambance su idan yana da breast a ƙirji!.
Napep ta samu ta tsare suka kama hanyar gidan. A can gidan kuwa Umma lokacin da ta ƙule a ɗaki tana dokawa Aliya kira tana so ta bata baki, bayan Abba ya fita amma kuma sai ta ji an katse wayar a ƙarshe ma ta ji wayar a kashe. Fitowa tsakar gidan ta yi duk baƙi an karya wato an ci abinci, wasu suna hira wasu kuma suna wankan yaransu don suna cewa tafiya za su yi yau.
Wata daga ciki ta c
"Lubabatu an aurar da ƴaƴa yau an yi bacci fa munshari kowace ta shiga ɗakinta lafiya" Umma ta ce
"Wallahi kuwa, ai mun yi waya ma da su ɗazu, ai kam duk wanda ya kai ƴa mace ɗakin miji kam dole ya yi bacci da munshari, saboda fargabar tarbiyar ƴa mace duk da cewa duk tarbiya ɗaya daga ta yarinya mace har ta yaro namij" Nan aka shiga yin hira ana ta yaba gidan Jidda wanda hakan yake haifarwa da Umma wani ɓacin rai kamar ana soka mata ƙahon ƙarfe a zuciya. Tsayuwar napep a ƙofar gidan sai kuma shigowar wani yaro ƙarami yana cewa wai a ba mai adaidaita kuɗi, kafin su samu damar bashi amsar wanda ya aiko shi, kukan Aliya da ya fara ratsa kunnuwansu tamkar an yi mutuwar da ba a ɗauke gawa ba ya saka gabaɗaya idanun kowa ya koma can...
MAMAN AFRAH
*Ina manyan matan? Na buɗe muku adashe mai so ga link nan ya shiga grp, ko a min magana pc idan kin san ba yi za ki yi ba bana son harkar ɓata lokaci.*
*ABUBUWAN DA ZA A YI ADASHEN SU NE*
*Leshi, atamfa jaka, takami kayan yara, takalman, yara, abaya, mayafai na shago, mayafai beadwrk, adire, kamfala, shadda, shaddales sai kuma kayan kicin da zanin gado ga mai buƙata* .
*Amfanin yin adashen domin samun sauƙin siyan abu idan kana zuba kuɗin da kaɗan zai baka damar samun abin da kake so saɓanin za ka ga wahalar siye a dunƙule, Allah sa mu fara a sa,a mu gama cikin nasara.*
[11/13, 12:45 PM] 😍: https://chat.whatsapp.com/GTq4oSxwxZfLKU7Amx5My1?mode=wwt
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1️⃣7️⃣
*ALIYA*
Gabaɗaya kowa baki sake hankali tashe yake binta da kallo, kowa da abih da ya fara rayawa a zuciyarsa, wasu suna raya cewa ko mijin ne ya mutu, wasu suna tunanin ko dai bata kai masa mutuncinta ba ne shi ya sa ya mata shegen duka a koro ta, saɓanin Umma da tuni ta harbo jirgin abin da ya maido da Aliyar gida. Umma a take ta ji wani abu yana juyata tabbas ta san yau Aliya ta gama kunce mata zani a kasuwa ta tona mata asiri ita da take son komai ya zama na sirri amma ta kwaso ƙafa ta taho gida tana ɓare baki kamar dai an sanar da ita mutuwar wani shaƙiƙi nata.
Umma tamkar ta saka kuka haka ta ji don ta fara tunanin yadda za ta ɓoye matsalar nan amma da alama matsalar ba za ta ɓoyu ba, tun da dai gashi nan ta yi wa kanta fallasa auren bashi. Salatin da matan suka kwasa shi ya dakatar da Umma daga saƙa da warwarar jin ana ta jerawa Aliya tambayar lafiya? Sai dai kukan Aliyar ya hana ta bada amsa hakan ya da zargin da yake ran kowanne ya ninku fiye da farko, maganar yaron nan ta sake katse musu zulumi da ya ce
"Wai mai adaidaita sahu ya cw a bashi kuɗin" Umma da wasu kuɗi suke gefenta ta ɗauki ɗari biyar ta cillawa yaron ya ɗauka ya fita da gudu, Aliya ƙarasawa kan baranda ta yi ta zauna zaman dirshan cike da kuka ta ce
"Wallahi Umma ba zan zauna da shi ba" Kowa sai ya matso don jin ba,asin maganar don furucin ta ya nuna ba ita ce da laifi ba kamar yadda zuciyoyinsu suka saƙa musu a farko, kowa sai ya buɗe kunne don jin dalilin.
Umma ji ta yi kamar ta dannewa Aliya baki don kar ta faɗa domin ta san muddin ta yi maganar to kuwa shuka za ta yi a idon makwarwa don kowa sai ya ji labarin matsalar gidan aurenta, sani ne Aliya bata yi ba yanzu zancen duniya iya faɗawa baba ne, wuyar ta ka yi furuci sai ya bazu wani ma sai ya gama ƙara gishiri da maggi a maganar don ta yi armashi idan zai bada labari.
Umma ta rasa ma mai za ta ce duk da tana ta ƙoƙari wajen ganin ta dakatar da Aliyar daga abin sa take son faɗa, amma Aliya duk yadda Umma ta kai ga mata magana da ido amma ko idanun Ummar ma bata kalla ba,ɗaya daga cikin matan ta ce
"Aliya dama auren ƙiyayya ne aka miki?
Kafin ta bata amsa wata daga cikinsu rai a ɓace ta ce
"Ko auren ƙiyayya ne a kan mai za akai ta gidan miji ta taho gida? Ko ma mene ne ba sai ta zauna a magance matsalar ba, amma ta kamo hanya ta dawo gida wannan ai tonon asiri ne kuma dole idanun mutane ya dawo kanta, tun da yanzu kiwon mutum ake yi ba dabba ba"
Aliya cike da muryar kuka ta ce
"Ba dole in taho gida ba, mutuminnda yake ɗauke da mugun abu" Salati akam kwasa Umma kuwa kai ta ɗauke gefe tana jin kamar ta tsinewa Aliya don takaici gashi bata son ta dakatar da ita su ce bata ɗauke su a matsayi iyayen Aliyar ba tun da daga dangin Abba sai kuma nata ƴan uwan. Wata ƴar uwar Abba da ta zo daga ƙauye tana dafe ƙirji ta ce
"Wayyo Allah, mun shiga uku Allah sa bai kwanta da ke ba Aliya" Matar ita tunaninta mugun abun da Aliya ta ce tana nufin cutar HIV ita kuma Aliya sai ta ji zuciyarta ta ƙara karaya sannan ta ji daɗina ranta a ƙalla ta san dai wannan babban batu da za a raba auren tun da ta ga ana batun bai yi tarayya da ita ba, tana murje idanu ta ce
"Wallahi ganin idanuna na ga wajen facin da aka masa, ba don na gani ba da ba zan taɓa yarda ba" Umma a ƙufule ta ce