Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 26
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 26: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 26. "Facin ubanki Aliya, shegiya sai ka ce wata tayar…
3,356 words
"Facin ubanki Aliya, shegiya sai ka ce wata tayar mota za ki ce faci wallahi ki kiyayeni" Ta faɗa tana tashi tsaye tana gyara ɗaurin zanin ta da yake barazanar barin jikinta, tana jin kunya kamar ta nutse don kunyatawa dai yau Aliya ta kunayata ta a bainar jama,a.
Baki aka hau ba Umma ana faɗin ta mata a hankali ai babbar magana ce ta sanyata baro gidanta, Aliya buɗar bakinta sai ta c
"Kuma wallahi da na san mata-maza ne ba zan aure shi ba, wajen ɗinkin tabon nan ba zai taɓa ɓacewa ba har ya mutu, da shi zai koma kabarinsa, ni ba zan ma je in ke haihuwar mata maza ba" Wasu sun ɗauki abin da girma don suna tunanin a mata maza Kasim ɗin ya fi ƙarfi ne ta ɓangaren mace basu san ma namiji ba ne kawai tsanarsa ce ta ƙoƙon ran Aliya har take ganin za ta rabu da shi.
Umma ɗaki ta shige jin kamar za ta nutse don kunya, tsayuwar nape a ƙofar gidan da kuma sallamar Abba da ya yi kana ganinsa ka ga wanda hankalinsa yake a tashe shi ya dakatar da ɗaya daga cikin matan da take ba Aliya baki.
Abba wanda maƙocinsa ya kira shi a waya yana tambayarsa lafiya ya ga Aliya an sauke ta a a daidaita sahu tana kuka ta shiga gida. Nan Abban ya nuna masa bai san ma da dawowar tata gidan ba, tsabar ruɗewa ma kasa kiran Umma ya yi a waya shi ya sa ya kamo hanya ya dawo.
Ransa a matuƙar ɓace ya kalle ta ya ce
"Aliya mai ya dawo da ke gida" Gabaɗaya sai ta ji shakkar Abban ta kamata sannan sai ta tsinci kanta da kasa faɗa masa asalin abin da ya dawo da ita gidan, kallon mutanen wajen ta yi ko wata za ta ari bakin ta ta ci mata albasa amma sai ta ga kowa ya yi shiru hakan yana nuni da ana son waƙa a baki mai ita domin ta fi daɗin ji. Wani irin tsoron Abba ne ya lulluɓe ta tsoron da bata yi tunaninsa ba lokacin da za ta taho don yanayin yadda ta ga fuskar Abba ya nuna mata bai ji daɗin abin da ta yi ba sai dai ya za ta yi a nata ganin bata da wani zaɓi da wuce hakan, wata tsawa da Abba ya duka mata wacce sai da fitsari kaɗan ya ƙwace mata jin ya ce
"Ba magana nake miki mai ya rabo ki da ɗakin mijinki a kwana ɗaya tak da kika yi a gidansa" Ba Aliya ba hatta Umma da take ɗaki maganar yadda ya yi ta cikin ƙaraji ya hargitsa ƴaƴan hanjinta.
Aliya cike da fargaba bakinta yana rawa ta ce
"Abba, ma...ta...ma...za... ne Ka...sim...ɗin" Ta faɗa a tsorace tana danne kuka mai ƙarfin da yake son ƙwace mata, tana fatan ta samu goyan bayan Abba a kan maganar nan. Abba wanda ko kaɗan bai fuskanci abin da ta faɗa ba kasancewar a rarrabe ta yi maganar, juyawa bayansa ya yi ya ga wani bokiti wanda aka yi wanki aka ajiye ya ɗakko zai kwaɗa mata, aka shiga bashi baki yana tada jijiyoyin wuya cike da ɓacin rai ya ce
"Za ki faɗa min sakarcin da ya sa kika baro gidanki ko sai na sauya miki kamanni?" Aliya bata san lokacin da ta ce
"Abba Kasim ɗin ba namiji ba ne sak!." Sai da ta yi furucin sannan ta ji wata kunya ta lulluɓe ta, maganar ta ɗaurewa Abba kai ya fara tunanin to ita Aliya a ina ta san namiji da har za ta ti ikirarin shi Kasim ba namiji ba ne, bayan jiyan ne ranar farko da ta kaɗaice da na miji ba ma wannan ne abin mamakin ba yadda har ta baro gidan miji a kan wannan ƙaramar matsalar don iya hasashen sa dai kamar tana nufin bashi da wani kataɓus a wajen aiwatar da sunna ma'ana yanayin jikinsa ba zai gamshe ta ba.
Ba kallon ita ba hatta Abba sai da ya ji kunya amma dai ɓacin ran da yake ciki ya danne kunyar Aliyar ya ƙara buɗe baki yana ƙwalawa Umma kira, sai ga Umma a sukwane zaninta riƙe a hannu don yau an damalmala mata lissafi damuwa da takaicinta in ta tuna mummuna Jidda tanaa can hankalinta kwance ita kuma da kyakkyawar ɗiyar ta suna nan hankali tashe, ƴar tata ta since musu zani a kasuwa. Umma tana fitowa ya hau ta da faɗa duk da haƙuri da kawar da kai na Abba amma yau kam ta gane shayi ruwa ne don a yanayin yadda yake faɗa tamkar babu abin da zai hana shi kai hannu ya ce
"Saboda ban isa ba yarinyar ta baro ɗakinta a kasa samun wanda zai kira ni a waya ya faɗa mini, sai dai daga waje a sanar da ni, yanzu wannan abin kunyar ina za a kai shi a ce wai saboda wani dalili marar tushe saboda Aliya ta raina mutane ta kamo hanya ta dawo gid" Umma da sauri baki yana rawa ta ce
"Baka fuskanci abin da take hufi ba Kasim ɗin ne yake da halittar mata maza" Ɗan shiru Abban ya yi yana tunanjn ya aka yi daga ɓangaren Kasim ba a sanar da su da wannan babbar larurar ba, amma dai babu yadda za a yi a ce ta baro ɗakinta ba tare da ta sanar ba wannan shi ne abin da ya ƙona masa rai.
Abba ya ce
Mai ya sa baki yi waya kin faɗa ba za ki kamo hanya ki taho bakya bari a je can a sulhunta" Aliya ta ce
"Abba ni ba sai an sulhunta ba na haƙura da shi kawai" Abba hannu ya ɗaga ya wanke fuskar Aliya da mari ba tare da ya ce komai ba ya juya a ƙufule ya fita waje, Umma duk kunya da takaicin mutanen wajen ya kama ta amma dai gwara a warwate matsalar ita bata ma ƙaunar Aliya ta dawo gida da zama a nata ganin da Jidda ce za ta yi kwantan rashin miji sai gashi yanzu tata tilon ƙar tana neman yin kwantai don a ganinra kwana ɗaya a ɗakin miji ma ai zai karya lagon ƴanmatancin Aliyar don ta san ma ai tuni ta zama bazawara idan ya sake ta sannan bata da tabbacin ba a samu rabo jiyan ba tun da dai ta san tun da har Aliyar ta ga halittar da yake ɗauke da ita to tabbas an aiwatar da sanna.
Abba yana fita ya ɗaga waya ya kira Baban Kasim yake labarta masa abin da yake faruwa, nan da nan ya sanar da Abban cewa gashi nan zuwa gidan Abban. Baban Kasim yana kashe waya sai ya shiga kiran Kasim don jin ba a sin yadda aka yi ya bar matarsa sabuwar amaryar kwana ɗaya tak ta tafi gida, tun da wannan abu ko shi ne aka yi wa ƴarsa hakan ba zai ji daɗi ba don wannan abin kunya ne abin takaici ka kai ƴa ɗakin miji ta dawo gida.
Kasim da yake shirin fitowa daga shagon nan kiran Babansa ya katse masa hanzari yana ɗagawa Babansa ya ce
"Kasim mene ne dalilin da ya sa ka bar matarka ta taho gida? Kai baka mata bayanin cewa tun kana ƙarami aka maka tiyata cewa kai ba mata maza ba ne kuma mata maza suna iya rayuwa kamar kowa su haihu kamar kowa, sannan suna da dama kamar kowa ba?" Baban Kasim da ya katse gaisuwar da Kasim yake kawo masa ya faɗa cike fa hargagi har Babar Kasim da take kicin ta jiyo abin da yake faɗa, hakan ya sa gabanta yankewa fa faɗi a nata ganin ta aurar da ɗan nata amma kuma wata wutar tashin hankali yana tunkaro su. Kasim a take ya ji bakinsa ya bushe wani tashin hankali ya saukar masa maimakon ya ba Babansa amsar tambayar da ya masa sai ya ce
"Gani nan zuwa Baba" Baban nasa kuwa ya yanke kiran, shi kuma Kasim ya yi hakan ne son kawo ƙarshen maganar saboda yana mamaki da tantamar anya Aliya ta tafi gida kuwa? Tun da ya san a gidan ya barta.
A rikice ya yi cikin gidan yana ƙwala mata kira, amma shiru ko ƙutarta bai gani ba banɗaki ya nufa amma bai ganta ba, kicin ma haka duk da ba ya saka ran ganin ta a kicin ɗin saboda ya san babu abin da za ta je yi, yana komawa ɗaki da ya je bedroom a nan ya tabbatar da maganar Babansa don ya ga alamar hargitsa kaya da Aliya ta yi.
Bai yi wata-wata ba ya fito daga gidan sai da ya zo ƙofar gida ya tuna bai ɗakko mukulli ba ya koma ya ɗakko ya fito yana cikin datsewa ya ji wani yana cewa
"Ango ka sha ƙamshi" Yana juyawa ya ga wani abokinsa ne, hannu kawai ya iya ɗaga masa ya tsare mashin ya hau don ya lura idan ya tsaya zai iya gane ba ya cikin hayyacinsa. Suna cikin tafiya kiran Babansa ya shigo yana ɗagawa Baban nasa ya ce
"Kasim ka zo gidan Abba muna can" Gabansa ne ya hau dakan lugude yana fatan kar wannan zaman da za a yi a saka ya warware igiyar aurensa da Aliya.
SADIYA
Da kamar ta nufi gidan Kaka amma sai ta daure ta ƙarasa gidan, tana zuwa sai ta ga babu mukulli a ƙofar gidan mamaki ya kama ta kenan mai yake a gidan bai fita ba ko dai ya dawo daga kasuwar ne ko kuma mene ne dalili da wannan saƙe-saƙe ta shiga gidan tana jin babu daɗi a ranta na wunin ranar yau bata sayar da kayan sana'ar ta ba bayan ta saba kama kuɗaɗenta. Tana shigowa ta fara sallama amma shiru ba a amsa ba sai dai ta ga takalminsa a ƙofar ɗakin sai da ta yi sau uku amma babu alamar zai amsa haka ta shigo ta ɗaga labaulen falon ta shigo dama Kalifa bacci yake a bayanta a ranta tana raya ko ina motar tasa kuma tub da baya ganta a ƙofar gida ba.
Ko da ta shiga ɗakin yana gaban madubi yana idaidaita hula a kansa amma ko kallo bata isheksa ba, kamar dai ba a yi ruwanta a wajen ba. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi wanda take fatan hakan ya narkar da takaicin da yake danƙare a ƙirjinta. Ta ɗan daure ta ce
"Barka da yamma" Bai amsa ba illa ya saki hular tasa ya riƙe ta da hannu ɗaya saɓanin lokacin da ta shigo hannuwansa biyu suka riƙe suke da hular, ɗaya hannun marar hular ya yi amfani da shi wajen ɗaga mata hannu alamar ta dakata hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru tana kallon ikon Allah duk da bata san dalilin dakatar da ita ɗin ba. Ya kusa minti huɗu yana daidaita hular har sai da ya ga ta masa yadda yake so ita kuma tana jira ta ji abin da zai ce. Da ya gama gyara hulae bai juyo ba yana kallon madubi sai da suka hala ido ta cikin madubin ta ji ya ce
"Ki daina kalle mata kwalliyar" Cike da mamakin furucinta da kuma rashin sanin inda maganar ta dosa sai kuma ya ce
"Na ji kina mini barka da yamma ke ai ya kamata a yi wa barka ko?" Da nuna alamar tambaya a fuskaryta ta ce
"Ban gane ba barkar mai?" Ya ce
"Barkar dawowa ɗakin ki mana, ai nan Baba ya kirani a waya yana ta bani haƙuri, na ce bari na tambayi Meenal ɗin in ta haƙura sai ki dawo" Har sai da idanunta suka ciko da ƙwallah tsabar ɗacin da maganar ta mata wato dai Baba ya zubar mata da mutunci da kima a ce ya kaita gida amma saboda ta zauna a gidan aure yake bada haƙuri gashi yanzu ya ja mata raini har ana mata barka da dawowa ɗakinta, wato ta ga samu da ta rashi ɗan kawar da kai gefe ta yi tana danne abin da ta ji ta ce
"Allah sarki Baba yana son ƴaƴansa su yi zaman aure ne ai sannan mutum ne mai son zaman lafiya ba ya son tashin hankali shi ya sa ya zaɓi ya bada haƙuri a kan ciccira magana" Ta ce tana jin kamar mai.
Wata ƴar dariya ya yi wacce ta yi kama sa ta yi kama da ta raninin hankali ya ce
"Allah ko?" Bata tanka masa ba ta zaɓi ta bar ɗakin don ta ga abin cin fuska ne. Tana dab da fita daga ɗakin ya ce
"Da farko na dakatar da ke ne da kika min mafana saboda ina saka hula bana so ta karkarce kin san idan za a yi wa amarya kwalliya abin a tsara ne don a birge ta" Murmushi ta yi ta ce
"Wannan gaskiya ne" Bai jira ta ce wani abu ba ya ce
"Na ce kina kalle mata kwalliyae ne saboda ta ce mini kar in bar ƴan mata su kalle mata ni" Maganar ta ɓata mata rai amma sai ta zaɓi mayar da martani cikin ruwan sanyi ta ce
"To ai ƴanmata ta ce ka ga bata ce har matarka ba kenan matarka ta fi damar ta kalle ka don halaliyarka ce" Tana faɗa ta juya ta fita. Shi kuma ya murmusa don yana ganin Baba ya ƙara bashi damar wulaƙanta ta tun da yana nuna dole sai ta zauna a gidan, tun da yana faɗa masa sauran ƙannenanta suna nan babu mashinshi ni.
Tana zuwa falon ta sauke Kalifa ta ɗora a kan kujera ta fara shirin gyara gidan, sallamar wata yarinya da ta zo siyan manja ya sa ta fito daga ɗakin ta je ta bata ta dawo, tsintsiya ta ɗakko bayan ta kunna gawayi don yin tuwon dare. Fitowarsa daga ɗaki yana buɗaɗa ƙamshi ita shaddar ma kanta aabuwa ce dal yau ya fara sakawa hatta hula da agogon duk sabbi ne yadda kayan ya masa kyau tamkar ranar ɗaurin aure kamar abin arziƙi ya ce
"Sadiya baki tambaye ni ina mota ta ba" Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce
"Na ga bata waje to tunanina ko ka ba wani ne ɗani" Ta faɗa cikin zolaya. Washe baki ya yi ya ce
"Kamar kin sani kuwa ai Meenal ce suka karɓa aro ita da ƙawarta za a koyawa Meenal ɗin mota" Ɗan jim ta yi tana tunanin ba ya ma gudun matsala sai ta ce
"Ma sha Allah, Allah ya tsare ya sa a koya a sa'a" Da amib ya amsa yana saka takalmi ya fita a daidai lokacin kuma suka ji ƙaran tsayuwar motar ya waiwayo yana cewa
"Kin ji ƴan halak suna dawo" Ita dai bata amsa masa ba ganin ya zama wani sauna a kan mace duk don ya ga bata nuna damuwa a kan lamuransa shi ya sa har yake faɗa mata komai ya zo bakinsa yana ganin ba za ta ji ciwo ba.
Yana fita ya rufo ƙofar Sadiya ta cire takalmi ta yi saɗaf-saɗaf ta je zauren ta shiga leƙawa daga wata ƙaranar tulla da take jikin ƙofar, tana ganin lokacin da suka fito daga motar wata farar budurwa wacce fuskarta har wani jaja take saboda bikicin ita ce ta fito daga mazaunin direba ita kuma Meenal ɗin daga mazaunan mai zamana banza. Suna ta dariya shi kuma ya harɗe hannu a ƙirji yana ta kallonsu, Meenal ta zunɓura baki tana magana cikin ɓaci ta ce
"Ka ga ko, ta kusa jefa maka ni a kwata" Ƙawar tana dariya ta ce
"Ka ji ni da mata za ta min sharri wai ni ce ma zan jefa ta a kwata to ita ce ta kusa jefa mu a wata ƙatuwar kwata, ɗazu ma kaɗan ta kaɗe wani tsoho" Gabaɗaya aka yi dariya, kafin ita ƙawar ta shiga baya ita kuma Meenal ta shiga gaba shi kuma ya shiga ya tada motar da yake a jiki ta bar mukullin, haka suka bar layin duk abin da suke a kan idanun Sadiya sai da suka tafi ta juyo ta dawo cikin gidan ta fara aikin gabanta.
Yau saura sati ɗaya biki Nasir duk ya mayar da hankaki kwacakwam kan lamarin bikinsa sai hidima yake daga shi har su Hajiya da ƙannensa tamkar dai wannan ne karon farko da zai taɓa aure. Duk da Hajiyar ta faɗawa Sadiya cewa su a wurinsu wannan ne auren fari da Nasir ɗin zai yi, kuma wannan ne auren da suke gani za su yi biki na kece raini, maganganu maarar sa kai da ƙafa dai Sadiya ta ji su sai dai tana toshe kunnuwanta ta yi kamar ba ta ji ba, saboda Hajiya ita tana ikirarin biki biyu za ta yi wato ɓangaren amarya da na ango abin ta tuwona maina.
Tun da aka zo aka yi jere ake ta kulle ƙofofin ɓangaren amarya, sannan duk wanda zai shigo gidan cikin nuna halin ko in kuka yake ga Sadiya hatta gogan yanzu ta rasa kansa da ƙafarsa babu wani abu da yake shiga tsakaninsu ba ya cin abincin gidan kwata-kwata sannan idan ya fita ma wani lokacin sai dare. Ita yanzu ko ya zo ma baya yake juya mata a kan gadon, domin ta lura gabaɗaya zumuɗin son kasancewa da sabuwar amarya yake ɗibansa, komai ya mayar da shi ga amarya, ana saura kwana biyu ɗaurin aure ya haɗa kayayyakinsa ya kwashe rabi da kwata ya kai ɗakin amarya, duk wasu abubuwa na amfaninsa to ya mayar ɗakin amarya, tamkar dai cewa aka yi ita Sadiyar ba matarsa ba ce duk da ayyukansa ya nuna cewa da alamar hakan amma dai ita ta bashi lokaci.
Ko naira biyar bai bata ba a matsayinta na uwar gida bare ta saka ran wani kayan da ake yi wa uwar gidan duk da malamai suna ganin hakan ba wajabci ba ne sai dai sun faɗa hakan kyautatawa ce sannan kowace rai tana son a kyautata mata amma Sadiya bata samu hakan ba. Ita ma ganin da kuɗinta hakan bai wani dame ta ba, tun gabatowar bikin a littafin maman afrah ruɓaɓɓiyar igiya ta ɗauki lambarta ta kira ta ta faɗa mata tana son atamfofi lokacin ana saura kwana biyar biki ne. Nana maman afrah ta ce ta mata magana ta whatsapp ta tura mata atamfa da les da takalmi da jaka, sai kayan Kalifa kala biyu ta bata acc no ta saka kuɗi sai ga mai napep ya kira ta a waya ya ta faɗa masa unguwar ya kawo mata, sun yi kyau sosai kamar yadda ta gansu a hoto haka suke shi ne ta bayar aka mata ɗinki. Sai aka mata buɗaɗɗe kasancewar tsufan da cikinta ya yi.
Ko bayan ya kwashe kayansa daga ɗakin tana gyara masa drowersa ta ga ya ajiye wasu magunguna na maza hakan ya sa ta gane tanadin amarya ne murmushi ta yi abinta tana musu fatan wanyewa lafiya.
A ɓangaren amarya Meenal kuwa ta saya magungunan mata ciki kuwa har da wani na matsi mai suna gamgam wanda take fatan ma dawo mata da budurcinta ba tare da angon nata ya farga cewar ta yi fatali da mutuncin da ake fata da burin kowace mace ta kai gidan miji.
Yau za a kawo amarya bayan an yi gagarumin bikin kece raini kamar yadda Hajiya ta buƙata, Sadiya ma ta yi ɗan taro na maƙota da ƙwayenta, ta saka atamfarta poplin da ta ɗinka da yake ɗinkin doguwar riga ne sai ya mata cif abinta. Dirin tsayuwar motoci a ƙofar gidan ya ankarar da kowa ƙarasowar amarya, kasancewar akwai nepa, ife-ifen yara da guɗar manya ita ce ta karaɗe unguwar, sai yi suke suna maimaitawa Sadiya da ta fara jin faɗuwar gaba ta shiga ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagisu aslihli sha,ani kullahu wala takilni ila nafsi ɗarfata ain.
Haka suka shigo kamar da gayya suna ƙara guɗa, su kuma maƙoa suka shiga musu sannu da zuwa amma sai suke yi wa Sadiya da mutanenta kallon ƙasƙanci. Babu wansa ya ƙara tanka musu, suka nufi sashen amarya. Bayan kowa ya watse an yi wa Sadiya sallama tare da bata haƙuri hatta wasu saga cikin ƙannenta ma sun zo.