Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 37

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 37

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 37: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 37. A falo Aliya ta tashi sai ta sunkuya za ta ɗauki…

3,370 words

A falo Aliya ta tashi sai ta sunkuya za ta ɗauki jakarta, a daidai nan Saude da take ɗauke da kofuna biyu da cokali a cikin kowanne ta zo za ta ajiye kawai sai idanunta ya sauke a ƙirjin Aliya nan ta hangi cokali kane-kane a cikin bireziyar Aliya, idanu ta zaro gabanta yana faɗuwa da sauri ta kawar da idanunta ta ajiye kufunan ta juya za ta bar wajen daidai nan Aliya da ta ɗauki jakar tata ta ɗago cikin kaushin murya ta ce

"Keee!" Amma Saude ko gizau bata yi ba bare ta juyo ma ko nunawa bata yi akwai wata halitta a wajenta ba ta yi tafiyar ta tana dab da shiga kicin Aliya ta sake cewa

"Ke Saude aba da ke nake magana ba" Juyowa ta yi cike da nuna rainin hankali ta ce

"Au wai dama da ni kike? Ai na ji kin ce kee ni kuma da aka yanka rago Saude aka raɗa mini" Ran Aliya ne ya ɓaci hakan yansa ta yi jifa da jakar a kan kujera ta nufi Saude a fusace tana zuwa ta damƙi rigar Saude daga kafaɗa ta ce

"Ke ni kike faɗawa hakan?" Saude ta yi shiru batance komai ba don dama fitsararriya ce ta ajin ƙrshe don ta ga aiki take shi ya sa bata zaƙewa. Aliya ta kalle ta cike da tuhuma ta ce

"Tun yaushe kike cikin kicin" A fili ta ce

"Lokacin da Aunty Jidda ta dafa kafaɗarki kuna tsaye a can lokacin ne na zo na shiga" Ta faɗa tana nunawa Aliya inda suka tsaya ɗazu sai Aliya ta ji daɗi don hakan ya nuna bata ganta ba a zuciyarta ta ce

'Tun lokacin da kika haye sama'

A daidai nan Jidda ta fito daga ɗaki sai Aliya ta ƙirƙiri dariya tare da sakin riƙon da ta yi wa Saude ta ɗan buga kafaɗar Sauden da wasa tana cewa

"Kina birgeni Saude" Saude ganin barikin da Aliya ta yi sai ita ma ta yj dariya tana cewa

"Na kuwa gode Aunty Aliya bari na kawo muku sugar" Juyowa ta yi ta dawo falon Jidsa tana riƙe da wayarta tana dariya don ita sai ta ga sun birgeta tana ta mamakin sakkowar Aliya yanzu ta zama mai sauƙin kai sai take ganin hakan ne ya dace domin dama duniyar kanta nawa take da mutum zai ke ɗagawa da girman kai.

Ko da ta kawo musu sugar suka sha kunun Aliya ta ce tafiya za ta yi Jidda ta saka direba ya kaita gidan, tun da ta san Jidda ta ji Kasim ya kira ya kusa dawowa sannan kuma tun da bata faɗawa Kasim ta fita ba duk da ta san idan ma ya san ta fita ɗin ba wani abu zai mata ba amma kuma dai tun da lallaɓawa take ta samu cikar burinta za ta daure ta kuma cije!.

Ta haɗa mata sha tara ta arziƙi tana cewa sai ta kawo mata nata wunin, ko da ta rako ta bakin motar bayan ta saka dogon hijabia sai Aliya ta ƙame a gefe ta ce direba ya fito daga mazaunin direna ya buɗe mata haka ya fito ya buɗe ta shiga ya rufe wani daɗi take ji lalai mulkar wani akwai daɗi dole ta baza iko iya iko idan ta karɓi ragamar gidan Ibrahim. Da suka zo wucea mai gadi ya buɗe musu get sai da ta buɗe glass ta wurga masa uwar harara.

Ana kiran magriba direba ya kaita ƙofar gidanta ya buɗe mata ta fito tana wani shan ƙamshi tana riƙe da ledar da Jidda ta bata wanda bata ma san mene ne a ciki ba sai kuma jakarta, tana jin ranta fari ƙal don ta yi aikin da ya kaita gidan.

Tana shiga suka ringa waya da Amatullahi suna ta murna Amatullahi har da guɗa Aliya za ta zama matar manya, sai dai kuma sai ta ji tana baƙincikin cewa Aliya ta yi aure ta barta a gida sannan yanzu za ta ƙara yin wani auren ta shiga gidan arziƙi ita tana nan samarin kullum ta ce su fito sai su fita da gudu.

A gidan Ibrahim yana shigowa gidan shi ma ana kiran magriba alwala ya yi ya wuce masalaci, lokacin da ya dawo suka haura sama ya ce Jidda ta zuba masa abincin haja ta zuba masa yana cewa

"Idan na cinye sai kin ƙara mini domin kin san ina son tuwo" Dariya ta yi ta ce

"Ai idan ka cinye na fulas ɗin ma sai a ƙaro maka a kicin" Dariya ya yi ya ce

"Mai kika sanya mini idan na cinye?"

Tana kallonsa ido cikin ido ta ce

"Mai kake so in sanya maka kuɗi ko mota?"

Ɗan ɓata rai ya yi ya ce

"Kuɗi abin so ne, saboda da su ne ake abubuwa na rayuwar yau da kullum, mota kuma wani abu ne na ƙawa a duniya sai dai ba dole sai da ita ake rayuwa ba, kamata ya yi ki saka mini abu mai muhimmancin da ya fi wannan" Da alamar mamaki take kallonsa ta ce

"Kamar me?" Kafe ta ya yi da idanunsa wanda take jin suna yawo a duka jikinta tamkar yadda jinin jikinta yake zagayawa a cikin jijiyoyinta ya ce

"Jiddarh,?" Ta ce

"Na'am"

Ya ce

"Kamata ya yi ki bani kyautar kanki ina nufin ki saka mini kanki a cin abincin nan sai na fi ci da yawan da zan baki mamaki" Wani murmushi ne ya ƙwace mata wanda bata yi zato ko tsammani ba ta ce

",Banda abinka ni dama ai taka ce"

Hanunsa biyu ya miƙa ya tallafo gefen fuskarta ya ce

"Na sani Jidda dama ke tawa ce amma ki ce za ki rayuwa da ni za ki kasance da ni rayuwa ta har abada, za ki zauna da ni a runtsi da duk wuya, duk halin da na tsinci kaina ba za ki taɓa guje min ba Jidda, da ke nake rayuwa kr ce sanyin idaniyata na faɗawa Mummy ke ar aljanna ce Jidda na faɗa mata in har miji ne yake ɗaga ƙafa matarsa ta shiga aljanna Jidda ki saka kanki cikin sahun matan aljanna, aljannar ma firdausi" Ƙwalla ce ta taru a idanunta kafin ta cika idanun sai kawainta gangaro saman kumatunta da sauri ya saka manyan yatsunsa ya goge hawayen don ba ya son ganin kukan Jidda.

Muryarsa ce t bayyana cikin rauni ya ce

"Mai ya sa kike kuka Jidda? Wallahi ba na son zubar hawayenki" ,Ƙasa ta yi da idanunta don ta ga damuwa ƙarara a fuskarsa sannan idanunsa sun yi ja, tana ta tunanjn duk da ana cewa a farkon aure ana bada kulawa da nuna damuwa sai tafiya ta yi tafiya zama ya yi zama sannan zaman ya koma zaman haƙuri amma gaskiya a yadda Ibrahim yake nuna mata soyayya da kulawa bata jin har iya numfashin sa zai canja mata.

Muryarta tana rawa ta ce

"Na ji kana min kalamai ne wanda suke nuna kamar kana mini ban kwana ne tamkar dai kalamai ne masu alamta kana mini sallama sai dai ban san wace irin sallama ba ce"

Murmushi ya yi don kauda damuwar fuskarta wacce har ta sa ta zubar masa da hawayenta ya ce

"Kawai dai ina nuna miki girma da muhimmancin Jidda a rayuwar Ibrahim ne" Ɗagowa ta yi ta kalle shi ya gyaɗa mata kai alamar gaskata maganar.

Idanunta ta juya ta ce

"Muhimmancinka a zuciyar Jidda tamkar alaƙar gangar jiki da numfashi ne, idan aka cire rai a jikin gangar jiki to gangar jiki ta zama gawa ba za ta amfanu ba sai cikin ƙasa wato kabari haka kake da girma a zuciyar Jidda" Yana kallonta shi ma ya ce

"Allah ya dawwamar da soyayya da ƙaunar junana har abada ina fatan na riga ki barin wannan duniyar domin idan kika fara tafiya Allah ya sani ni dai rayuwata za ta tagayyara ne"

Jidda ta ce

"Ni ma hakan take" Hannuwansa ya ɗauke daga fuskarta ya mayar wuyanta tare da kai fuskarsa ya ɗora goshinsa a kan tana goshin hancinsa yana kan nata hancin ya ce

"Tare za mu rayu kuma tare za mu mutu, don sanarwar mutuwar ɗayanmu shi zai sa zuciyar ɗayar ta buga shi ma a take ya bi ɗan uwansa sai a sakamu a kabari ɗaya" Su duka suka ƙyalƙyale da dariya don wannan ne buri da fatansu kar ɗaya ya mutu ya bar ɗaya baka jin komai a ɗakin sai sautin dariyar su sannan ya koma ya zauna.

Plate ɗin ta tura masa gabansa ya ɗauki cokalin yana gyara zamansa, gutsiro tuwon ya yi a cokalin ya ya saka miya tare d ambaton

"Bismillah" Nufar bakinsa ya yi da tuwon sai dai ƙaran wayarsa ya katse masa Jidda da wayar take kusa da ita ta furta

"Mummy ce take kira" Ta faɗa tana ɗakko wayar ta miƙa masa. Da hannun hagu ya karɓi wayar hannunsa na dama yana riƙe da tuwon a cokalin, ya danna ok tarw da kai wayar kunnensa.

Kukan Mummy ne ya saka ya saki cokalin hannunsa tare da tashi tsaye yana faɗin

"Mummy lafiya?" Jidda ma tsaye ta tashi gabanta yana faɗuwa ganin hankalinsa ya tashi...

*Na muku promo na kayan maganin mata a zo a mini ciniki* 💃💃💃💃💃

*🎉 PROMO NA ƘARSHEN SHEKARA GA MATA! 🎉*

*Ki bar tsohon shekara da matsala, ki shiga sabuwa da gyara!*

Mun yi sabbin kaya don nuna soyayya da kulawa ga wanda suke son mallakar ɗaya daga cikin waɗannn abubuwan ko kuma duka.

*Ga kayanmu masu inganci da kike bukata:*

1️⃣ *Maganin Matsi Gam-Gam* Don matsi 1500 maimakon 2500

2️⃣ *Maganin Sanyi* Yana kawar da dukkan nau’in infection da wari, ƙaiƙayi, ƙuraje rikicewar al,ada 2500 maimakon 4k.

3️⃣ *Sabaya 3 in 1* Gyara breast, hips sannan tana gyara jiki 5k maimakon 7k.

4️⃣ *Maganin Gyaran Breast* Yana ciko da breast, ga masu shirin yin yaye da kuma wanda breast nasu yake buƙatar gyara 3k maimakon 4500.

5️⃣ *Daka* Tushen ni’ima 1500 maimakon 2500.

🎁 PROMO NA MUSAMMA

Ranar ƙarshe 31 ga Disamba, 2025

Ki gyara jikinki, ki faranta ran mijinki, ki shiga sabuwar shekara da armashi.

09025576222

https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1

*RUWA CIKIN COKALI*

(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*

*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*

*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣3️⃣

SADIYA

Ta jima abin yana bata mamaki sai dai bata san wa za ta faɗawa ba ma tun da abu ne da vai taɓa faruwa da ita ba. Ta so ta tambayi Meenal mai ya sa ita akwai nepa a ɓangarenta ita kuma babu sai dai gudun abin da zai je ya zo ko kuma a bata amsar da za ta mata ciwo sai ta ja bakinta ta tsuke. Meenal kuma dama ta yi hakan ne don ta turawa Sadiya haushi amma abin mamakin sai ya ga bata ga ko alamar damuwa a fuskar Sadiyar ba bare ta kai ga furtawa hakan ya sa ranta ma ya ɓaci ta taso a fusace lokacin Sadiya ta fito ta ɗaurawa wata maƙocoyarsu curry da ta saya curryn nan mai kyau da kala ga ƙamshi wanda ta auna wajen maman afrah, hakan ya sa Meenal faɗin

"Sadiya wai ni ke wace irin ishashshiya da mai ce? Wato saboda girman kai da nuna ɗagawa ke ba jinin sarauta ba amma shi ne koke zaune ɓangarenki babu wuta ko ki tambaya tun da ni ai gashi nan kina jin ƙaran TV a ɓangarena" Ta faɗa tana jifan cikin jikin Sadiya da wani mugun kallo. Matar ta lura da kallon tsanar da Meenal take jifan Sadiya da shi hakan ya sa ta jinjina al,amarin amma sai ta g Sadiya ta yi murmushi irin murmushin nan da ake kira da sa kishiya haushi, ta ce

"To ai na ga ba zaman kaina nake yi ba zaman aure nake, sannan ke ɗinma zaman auren kike ni da ke babu wanda yake zaune a ƙarƙashin wani, don haka nake jiran shi wanda shi ne ginshinƙin gidan sai in ji ta bakinsa" Kallon ashe ke ma dai kin yj baki Mrenal ta mata kafin ta taɓe baki ta ce

"To shiknan zan nuna miki ni nake iko da mijin da kike taƙamar kina zamansa kuma zan nuna miki ni ƴar halak ce matsawar kina son ci gaba da neman taro da sisi da firjinki dole ki biyo ta hannuna ko ki dawwama babu nepa a ɓangarenki" Tana faɗar hakan ta juya fuuuu rai a ɓace, sai matar nan ta ce

"Sadiya ki yi haƙuri don Allah karki tanka mata, ki bari har Nasir ɗin ga dawo" ,Tana faɗar hakan ta ɗan dafa kafaɗar Sasiya sai kuma ta juya za ta tafj muryar Meenal ta katse ta da faɗin

"To almunafunfun, dama ku ne baƙaƙen munafukan unguwa masu haɗa kishiyoyi faɗa saboda gulma da tsugudidi"

,Kallo ɗaya matar ta yi wa Meenal ta ce

"Ke idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri don wallahi ni jna danne banza in lakaɗa miki na jaki in yi gaba" Bata jira cewarta ba ta kaɗa kai ta tafi don ta san ta turawa Meenal ɗin haushi. Matar tana fita Sadiya ta shige ɗakin ba tare da ta kula maganganun da take ta yadawa a tsakar gidan ba, duk da abin ya mata ciwo a ce tana uwar gida amma amarya tana neman yin iko da ita, amma dai mai haƙuri yana dafa ditse watarana har ya sha romonsa.

Tun da ta shiga ɗaki take waya da chartong da samarinta har la,asar jefi ,-jefi tana yin baƙi su gaisa a tsaitsaye su tafi.

Yanzh ta fara tunanin yadda za ta fara fita ci gaba da barikinta tun da dai yanzu zaman ya fara kankama ita kuma ta saba da bin maza tana ganin Nasir shi kaɗai ba zai wadace ta ba.. Sai dai gida ne ba ita kaɗai ba bata san ya za ta yi da Sadiya ba duk da ta san ba lalai ta kai ƙaranta wajen miji ba sai daj ido mudu ne.

Lokacin da Meenal ta ji ƙaran motar Nasir da sauri ta ƙirƙiri kukan ƙarya har ya shiga ɗakinta ya ganta zaune a bakin gado ta takarkare tana ta sharɓar kuka hankalinsa ya tashi ya ma rasa ya zai yj sanann lallashin duniyar nan da kumambada baki ya yi amma ko gizau bata yi ba bare ya saka ran za ta amsa masa.

Sai da ya sha fama kafin ta ce

",Tun da ƴan nepa suka zo na basu kuɗin nan suka yanke ɓanbaren Sadiya shi ne fa matar nan ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, baƙaƙen maganganu sai da na yi da na sanin zuwana cikin gidan nan har da wata maya da ta zo siyayya wurinta suka haɗu sika ci mini mutunci, wai baƙincikin san,a nake mata saboda ni ba na siyar da caass bare asss" ,Cike da mamaki Nasir ya ce

"Ita Sadiyar ce da ɗanyen aikin wannan ita bata san albarcinki take ci a gidan nan ba ba don ke ba da tuni ta cikawa rigarta iska fa," Wani daɗi ne ya cika zuciyarta tana rayawa a ranta indai tuggu ne da kutungwila ai sai ta gane shayi ruwa ne.

Meenal ta ce

"Ina fa ta sani wai har da ce mini zaune gari banza ce ni wai ina zaman kashe wando bana sana,ar komai, wai Nasir ɗin ma ba ya jin maganata wai ban isa in saka kaki mayar mata da nepa ba" ,Nasir jin tana magana cikin muryar kukan da ta yi wa muryarta ado da shi ya sa ya miƙe zumɓur yana faɗin

"Zo mu je ni ba na son munafurci" Tun daga ƙofar ɗakin Meenal yake kwaɗa mata wani mahaukacin kira, amma bata amsa ba tana jinsa dama riga take sakawa kasancewar jo ta yi rigar jikinta ta ɗame ta duk bata jin daɗin yadda ta kamata shi ya sa ta gwammace ta cire ta duka. Tana jin baloƙoƙon da yake amma bata tanka masa ba ko kiran bata amsa ba so take ya shigo ɓangarenta.

Sai da ya kira sau uku a na huɗu ta amsan tana fitowa daga ɗaki ta samu kujera ta zauna a falon tana cewa

"Shigo mana Baban Kalifa" Ransa ne ya ɓaci jin wai shi take kira ma wato ita ba za ta je ta zama ɓarjajjiya da mai. Fuuuu ya taho Meenal ta take masa baya domin so takr ta ga ƙwaƙwaf sannan tana so ta nunawa Meenal ita ce da gida ba Nasir ba.

Yana shiga falon a faɗace ya ce

,"Yanzu kenan sai na zo ke ba za ki iya zuwa ba" Sadiya ganin Meenal a bayansa ta shigo mata ɗaki sa ta sauya akalar murya da ta fuskarta ta ce

"Ayya sorry Baban Kalifana na taho zan zo sai kawai ƙafata ta riƙe shi ya sa na dakata" Ta faɗa tana kallallame murya don ta luta in bata zama ƴar bariki ba kishiya za take kissar haɗa ta da miji wannan yana daidai da kashe mata aure yanayin yadda ta yi magana sai ya ji zuciyarsa ta ɗan sauka, ba kamar lokacin da ya taho a fusace ba. Meenal ganin bai yi magana ba sai abin ya bata mamaki Sadiya ta yi saurin faɗin

",Sannu da zuwa ya kasuwa"

Kawai sai Meenal ki ta yi ya ce.

"Kasuwa sai godiyar Allah" ,Ya faɗa yana ɗan sassauta muryarsa Meenal jin zuciyarsa ta sauka ba kamar da ba sai ta karkata murya cikin ɗan jan hanci ta ce

"Ni ma Allah zai bani abin yi Sadiya, kowa rabonsa yake samu kuma sana,a ma lokaci ne yadda Allah ya baki jari nima zai bani watarana!". Tana faɗar haka ta juya za ta tafi Nasir ya riƙo rigarta ya ce

"Haba Mrenal ai zan yi mata magana" Sadiya kuwa tana tunanin maganar mai sai kuwa ya tsuke fuska ko kula Kalifa da yake faman kiransa bai yi ba ya ce

"Sadiya a kan mai za kike mata gorin sana,a har kike cewa wai ita ce mai zaman banza" Kallon ni kika yi wa haka Sadiya ta yi wa Meenal sai dai kuma sanin tuggun mace ya sa ta ce

"Ka yi haƙuri ni ban yi da wata manufa ba"

Nasir ya haɗe girar sama da ƙasa ya ce

"Ai in har dai nepa ce to ba za a mayar yanzu ba sai na nuna miki Meenal ma ta isa a gidan na kamar yadda kike matata haka take ita ma don haka ki kiyaye a kan Meenal komai yana iya faruwa" Ganin ya juya zai tafi Sadiya ta ce

"Ina son magana da kai " Ya juya ya kalli Meenal da ta kashe masa ido ɗaya ya ce

",Ki faɗa a nan kawai don ko a bayan idanunta kuka faɗa tamkar a kan idonta ne don da ni da ota mun zama tif da taya" Meenal fakar idon Nasir ta yi ta aikawa Sadiya gwalo Sadiya kuma sai ta yi kamar bata gani ba don bata yarda ta nunawa Meenal cewa hakan ya mata ciwo ba.

Danna ɗacin da ya ziyarce ta ta yi ta ce

"Dama ina son zuwa gidan Noor ne gobe" Cike da mamaki ya ce

"Kuma shi ne za ki faɗa min tun yanzu tun da dai ai na san ba yau za ki je ba...

Meenal ta yi karaf ta ce

"Ka san da yake yanzu bata da ranar girki shi ya sa da ta ganka yanzu ta faɗa maka don karka suɓuce mata ka san fa ko wayarta in kana ɗakina ba ɗagawa kake yj ba" ,Abin ya yi wa Sadiya ciwo duk da ta san ko ma mene ne ba laifin kowa ba ne illa na Nasir shi ya sa Meenal take ɗaukanta ba a bakin komai ba duk da ta san shi ɗin ma ba komai ba ce a wajensa.

Ɗan murmushi ya yi ya ce

"Kuma haka ne fa, gaskiya amarya da zafinki kika shigo fa"

Meenal ta ce

"Ai ƴan magana sun ce da zafi-zafi ake dukan ƙarfe ko ka ga laifina" Ya amsa mata da a,a suka ƙyalƙyale da dariya, wato sun mayr da Sadiya kamar wata mahaukaciya, hakan ya sa ta miƙe tsaye ta kalli Meenal tana nuna ta da yatsa cikin ɗaure fuska ta ce

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull