Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 38

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 38

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 38: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 38. "Ki fitar min a ɗaki!" Meenal da mamaki take kallon…

3,358 words

"Ki fitar min a ɗaki!" Meenal da mamaki take kallon yadda Sadiya ta haɗe rai hakan ya sa ta taɓe baki ta juya ta fita, tana fita Nasir ya juya zai bi bayanta Sadiya taku ɗaya biyu ta yi ta sha gabansa ya tsaya da mamaki yana kallonta tana hucin ɓacin raj ta ce

"Duk abin da kuke mini a gidan bai isheku ba har sai kun biyoni har ɗakina khna ci mini fuska?" Ta faɗa tana kafe shi da idanunta. Ganinnya sha jinin jikinsa ya kasa furta komai ta ci gaba da faɗin

"Yaushe rabonka da ka shigo ɗakin nan matsayina na matarka? Ni da ɗanka mun zama saniyar ware? Ka na ba amaryarka cimar da take son ci mu kuwa ko oho, hatta abincin da za a tsakura mana wanda va zai isa ba ake bamu babu mahaɗi sai dai no in nema, shin wnanan shi ne adalci? Allah cewa ya yi ku aura mata biyu biyu, uku uku ko huɗu huɗu in ba za ku yi adalci ba ku aura ɗaya, amma ka san ba za ka kwatanta adalci ba ka aura biyu ka zo kana tauye haƙƙin ɗaya?

A zafafe ya ce

"Ya isheki Sadiya wai yaushe har kika ga makwancina da kike daɗa mimi maganar da ta zo bakinki? Haƙƙin me na tauye miki? Idan har haƙƙin kwanciyar aure kike magana ke ba taimakonki na yi ba a wannan jikin naki kina fama da tsohon ciki za ki iya ɗaukan ɗawainiyar miji? Mai za ki iya taɓukawa daga wannan haƙƙin sai wanne aka tauye? Ita baka ganin sabuwar amarya ce komai za ta ɗauke ke kuwa ki ji da fama da kanki mana" Tsabar mamaki ma ta rasa mai za ta ce sai binsa da ido take ganin haka ya ce

"Idan baki da abin faɗi zan tafi" Ganin ya juya tana shirin tafiya ta ce

"Ita kuma nepar da aka ware ɓangarena aka yanke fa ko ita ma duk tana cikin tsohon cikin da nake ɗauke da shi?"Ta faɗa tana kafe shi da ido. Rasa mai zaj ce ya ce

"Kuɗin wuta ne bakya biya ya kamata tun da kina samun kuɗi kike biyan wani kaso daga kuɗin nepa" Kallonsa take rana son tantance abin da yake faɗa cike da mamaki ta ce..

"In ke biyan kuɗin wuta saboda ina sana,ar firjin, shin nauyina ne na biya kuɗin nepa, duk abubuwan sa nake ɗaukan ɗawainiyar su wanda Allah bai wajabta mini ba har da witar nepa kuma? Shin baka san ko da a ce mace za ta tara kuɗin duniya misali a ce tana da miliyan ɗari mijinta yana da dubu ɗari shi ne zai ɗauki ɗawainiyar ta Allah bai wajabta mata ɗaukan ɗawainiyar kanta ba ko da ta fi mijin kuɗi sai dai idan ita ta ga dama bisa kyautatawa... Katse mata hanzari ya yi da faɗin

"Dalla dakata malama wa,azi za ki mini? Wa ya ce ana buƙatar kuɗinki, ko an ce miki an lura ma da wannan taro sisin da kike samuto ke kika ɗauki wannan kuɗi ki riƙe babu mai neman komai a wajenki, sanann tun da baki da abin faɗa ni zan tafi" Ya faɗa yana juyawa ya fice daga ɗakin, Sadiya sai ta jiyo muryar Meenal tana faɗin

"Baka dai amince a mayar mata da wutar ba?" Sadiya da sauri ta fito tsakar gidan ta gansu tana zuwa ta ce

"Bai yarda ba ya ce sai ina biyan kuɗin nepa hankalinki ya kwanta?" Kawai sai ta ƙyalƙyale da dariya har da tafa hannu ta ce

"Wannan ai tsakaninku ne kun fi kusa baki da haƙori ke ai uwar gida saraitat mata ce" Ta faɗa da gatse Sadiya ta kalle ta ta ce

"Sau da dama ko in ce a koyaushe ana maimaita karin maganar CIWON ƳA MACE NA ƳA MACE NE, sai dai duk wannan furucin a baki ne kawai domin kiwa a zahiri CIWON ƳA MACE BA NA ƳA MACE BA NE saboda mata mu ne matsalar kanmu da kanmu, da a ce kowacce mace za ta yi tunani da dogon nazari a rayuwa da bata zama sanadin zubar hawayen ƴar uwarta mace ba, idan miji ne mace ƴar uwarki ce za ta yi sanadin samar da rashin zaman lafiya a tsakaninku, ko da kuwa ke baki tare mata komai ba, idan ƴaƴa ne duk da su babi ruwansu a kishin da take amma sai wata ta gurmata musu rayuwa ta kore ki daga gidan bayan ta yi silar fitarki sannan ba za ta riƙe miki ƴaƴan ba. Idan saurayi ne yake son ya auri wata macen da yake so uwarsa ce za ta yi uwa da makarɓiya ta hana wannan auren ba don koɓai ba sai don ita take iko da shi ko da ta bari an yj sai ta dawo ta sakawa matar ɗan nata ido mai ya mata mai yake mata. Idan namijin ne ƴar uqarsa ko mahaifiyarsa tana gani yana wulaakanta matarsa maimakon a bashi shawara ya daina a nuna masa muhimmancin iyali a,a sai dai a aara rura wutar kawai saboda ƴar wani ce ta kowane fanni mata mu ne matsalar kanmu da kanmu. Idan saurayi da vudurwa ne suke soyayya ata ce za ta yi ƙoƙarin janye hankalinsa ya koma gareta ya zaman ta yaudari waccan ta shiga halin ƙunci ko da kuwa ita wacce ta yi wwacen saurayin ba aurensa za ta yi ba...

Meenal ce ta yi sanadin dakatar da Sadiya daga maganar ta hanyar ɗaga mata hannu Sadiya ta yi shiru duk da tana faɗar maganar ne daga ƙasan zuciyarta, domin kuwa ta san tabbas kaso tamanjn cikin ɗari ƴa mace ita take silar assasuwar faruwar qasu abubuwa domin ita shaida ce gashi nan tana ganin yadda mahaifiyar Nasir ta tsane ta sanann suke take zuga ɗan nata duk da sun san yana tauye ta amma ba za ta tsawatar ba sai dai ma ta ƙara nuna masa hanyar sa zai musguna mata, haka zalika su Husna su ma mata ne kuma suna mantawa watarana su ma za su je gidan auren basa tunanin a musu abin da suke yi mata domin faɗar ma,aiki S.A.W ma ne kama tudinu tudan duk abin sa ka yi sai an maka, haka zalika gashi nan abin sa Meenal ta mata duk da bata taka ta zubar mata ba amma ta zo tana zuga mijin a kan ya tauye mata haƙƙin ta.

Meenal tana kallonta ta ce

"Wannan damuwarki ne ke ya shafa ni bai shafe nj ba, ni idan zuciyata ta yi fess bani da damuwa a wajen miji zuciyar uban kowa ta yi baƙiƙƙirin" Tana faɗar hakan ta buga cinya ta juya ta nufi ɓangarenta Nasir ta take mata baya ko waiwayen Sadiyar bai yi ba, tana juyowa ta ga Kalifa a tsaye a bayanra ta ƙirƙiri murmushin yaƙe ta kama hannunsa suka koma ɗaki tana tunanin wannan abubuwan da ake mata ba komai ba ne domin ta san watarana sai labari sannan wani lokacin sai take ji a jikinta kamar idan da sauran numfashin ta za ta yi farinciki watarana!.

Washe gari ko da ta tashi wayarta ma babu caji don yanzu ta saya wata wayar ba waccan wacce take amfani da ita ba ce, ko da safe da ta tashi suka yi kiciɓis da Nasir a tsakat gidan zai je kicin ɗaukan abu, bayan su Husna sun zo sun yi break fast Meenal ta tsakura musu kamar kullum sun tafi, ta bi bayansa ta tsaya a ƙofar kicin ɗin ganin bai fito ba sai ta shiga ta ce

"Ina kwana"

Ya amsa da lafiya" A taƙaice

Ta ce

"Dama ina so in tambaye ka nawa ne kuɗin nepar da za a mayar mini ka san ina siyar da abu ba na son kasuwar ta tsaya" Kamar ba zai furta komai ba ya juyo ya ce

"To sai mai idan kasuwar ta tsaya? Ba taƙamarki kina samun kuɗi ba ke ma har kin yi bakin da kike kallon tsabar idanuna kina faɗa mini son ranki, to ki sani mayar da nepa ba yanzu ba ko da kuɗin naki sai kin gane muhimmancin wutar sannan da kike batun kasuwa shin kayan sanyin da kike siyarwa su kaɗai ne sana,arki? Ita kuma Meenal da bata siyar da komai fa? " Yana zuwa nan ya raɓa ta gefenta zai wuce sai ta tare hanyar a daidai nan Meenal da ta ji shiru bai dawo ba daga ɗaukan kofi da ƙaramar wuƙar cokali ta biyo shi, tana kwala masa kira kamar wani ɗanta, yana daga kicin ɗin ya amsa yana faɗin

"Gani nan fa" Ita kuma dama tun da ta fito ta ji dirin maganar Sadiyar a kicin shi ne dalilin da ya sa ta ƙarasa domin ta yi alƙarin ta ringa yi wa Sadiya kissa da kisisina har sai ta fitar da ita daga gidan don tana so take watayawa a gidan samarinta na banza suke zuwa suna ɗaukanta sannan ma idan ya tafi kasuwa Nasir tana kawo su gidan suna holewa abinsu. Kicin ɗin ta ƙarasa Sadiya ta juyo ta kalle ta sanye take da wasu kayan bacci masu net riga ce mai siririn hannu kuma ko ciniyarta bata rufe ba, sai ƙaramin wandon rigar wanda kaɗan ya fi panta kanta babu ɗankunne kallo ɗaya Sadiya ta mata ta ɗauke kai saboda bai ma dace Meenal ta fito a haka ba idan shi mijinta ne ita duk da tana mace bai dace ta ganta a wannan shigar ba, uwa uba wannan idan gidan yarana ne zai ɓata tarbuyar yara domin ta ga sau tari sai namiji ya ƙara aure idan amaryar ta je gidan ta tarar da yara amma hakan ba ya hana ta saka kaya masu fitar da tsiraici a ganinta maijinta take yi wa kwalliya bayan kuma yaran suna ankare da komai, wasu ma hatta wata runguma da sumbata sai su yi wa mijin a gaban yaran wannan ba daidai ba ne yana ɓata tarbiya, su kuma mazan suna ganin ana yi ne don a faranta musu sai ya zamana basa ma iya yin kataɓus wajen hanawa ko dai don jin daɗinsu ko kuma don tsoron zuciyar amaren.

Tana zuwa ta kama tsantsa ta ce

"Wato ma cin amanata ake a kicinta" Cike da diriricewa Nasir ya ce

"Amana kuma Meenal wace irjn cin amana"

Tana ƙirƙiro ƙwallar kissa tare da yin muryar kuka ta ce

"Daga ɗakko kofi da wuƙa za a yanka biredi shikenan ka ƙi dawowa ashe dai kuna kicin kuna cin amanata bayan ka san girkina ne" Sadiya kawai baki ta dantse da haƙori ita da ba a ma shiga ɗakinta mai ta ce sai ita ce har take da bakin magana bakin maganar ma sharri ne.

Baki ya buɗe zai yi magana ta tari numfashinsa tw ce

"Tun da na taho daga windown kicin na hangoku rungume da juna" Da sauri ya juya ya kalli Sadiya nufinsa Sadiya ta furta wani abu ma,ana ta musanta zargin da Meenal ɗin take yi sai ka ce ita ba matarsa ba ce. Ganin Sadiya ta kauda kai gefe bata ce komai ba sai ta shiga rantse rantse yana cewa ko yatsan Sadiya bai taɓa ba.

Meenal ta ce

"Wallahi ba zan yarda ba tun da dai haka ne sai dai ka kira a mata kicin ɗin langa-langa ni ta kwashe kayanta ta bar mini wannan kicin ɗin tun da dai idan ka shiga kicin bin bayanka take kuna cin haƙƙina" Ta faɗa tana sanya hannu ta rufe fuska tare da rushewa da wani kuka kamar an faɗa mata mutuwa. Cike da son ganin ya lallashe ta da gudun ɓacin ranta ya ce

"Shikenan an gama yau za a buga mata kicin ɗin langa -langan sai ta bar miki wannan ɗin hakan ya miki" Kai ta gyaɗa tana share hawayen da ta kirkira. Sadiya da sauri ta kalle shi jin furucinsa tana kanne ido tsabar mamaki kafin ta furta wani abu ta ji Meenal ta ce

"Ka ga daman kicin ɗin langa-langa ya fi dacewa da ita tun da a gawayi take girki ni kuma da nake amfani da cooker gas wannnn ne ya fi dacewa da ni"Ta faɗa tana fakar idonsa ta yi wa Sadiya gwalo tare da mata wani kallo mai alamta mu zuba mu gani.

Kallon Sadiya ya yi ya ce

"Bani hanya in wuce, sannan ki fito da duka abin da kika san mallakin ki ne daga kicin ɗin ki ajiye a gefe guda, daga an gama haɗa miki naki kicin ɗin sai ki mayar can" ,Yana kaiwa nan ya raɓa gefenta ya wuce, ita kuma Meenal ta saƙala hannunta a kafaɗarsa shi kuma ya saƙalo hannunsa wanda babu kofin ya riƙe ƙugunta suka tafi ɓangaren Meenal ɗin.

GIDAN SU ZALIKA

Gabaɗaya Mamy ta gigice hankalinta ya tashi ji take tamkar zai gushe mata domin abu ne da take gani tamkar ba a zahiri ba addu,a take a zuciyarta Allah ya sa mafarki take, domin sai hakan ya fi mata sauƙin rayuwa a ce wannan abin a zahiri ne. Juya kwallin take a hannunta tabbas pills ne, wato maganin hana ɗaukan ciki. Hannunta yana karkarwa ta buɗe kwalin ta ga duk an ɓalli maganin alamar an sha kenan wato an yi amfani da shi.

A fili ta furta

"Allazina iza asabathum musibatun ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un"A take ta ji wasu hawaye masu zafi suna zubowa daga kwarmin idanunta zuwa dakalin fuskarta, kuka take sosai marar sauti ko ta ji sauƙin abin da take ji a ranta, yau ita ce da matsalolin gidan miji sannan mijinta ya yi watsi da ƴaƴansa tamkar ba ya raye, ya bar mata ragamar komai kuma duk da tana iya bakin ƙoƙarinta amma sai da aka fara samun tangarɗa a lamarin tarbiyar a fili ta furta

"Ina godiya a gareka ya ubangiji da wannan jarabawar, ya Allah ka bani ƙarfi da ikon rungumar duk wata jarabawa da za ka jarabceni da ita, na san ka na ji kuma kana gani ya rabby ka kawowa baiwarka mai rauni ɗauki bani da tsumi bani da dabara" Ta faɗa tana rushewa da wani sabon kukan, ta jima tana kuka har sai da ta ji zuciyarta ta ɗan saki, duk da ta san abu ne mawuyaci wannan mummunan dafin ya fita daga zuciyarta amma dai tana fatan Allah ya yaye mata domin shi babu abin da ya gagare shi.

Maganin ta je ta sanya a drower ɗinta, ta dawo ta ɗauki jakar ta mayarwa Zalika ɗakinta wace har lokacin tana ta shan bacci abinta.

Da safe ta je ɗakin Zalika ta same ta ta fito wanka kana zaune gaban madubi tana shafa mai sannan ga kayan da ta fitar za ta saka a kan gado a ajiye. Ta rufe ƙofar ta je ta samu waje ta zauna bayan ta yi sallama Zalikar ta amsa tana cigaba da abin da take.

Mamy ta ce

"Zalika wajenki na zo ina son magana da ke" Zalika tana shafa powder ta ce

"Ok Mamy" Sai da ta kammala ta zo ta saka kayantw sannan ta zauna a kusa da Mamy tana danna waya.

Mamy ta ce

"Bani jakar can taki zan yi wani abu" Gaban Zalika ya buga kasancewar ta san akwai maganinta a ciki kuma ba za ta so Mamyn ta gani ba. Tana ɗan nuna alamar tambaya ta ce

"Mamy jakata kuma mai za ki yi da ite?" A nan ne Mamy ta ji wani abu kamar kibiya ya caki zucuyarta, domin kuwa hakan yana nuni da cewar maganin ne Zalika bata so ta gani, hakan yana nuni da cewar Zalika tana neman maza, duk da Mamy ta san a jakartw ta gani amma zuciya irin ta uwa gani take ba maganin hana ɗaukan cikin ba ne duk da ta san haka ne amma so takr ta buɗe idonta ta ga mafarki ne hakan zai zama mafi sauƙi ga ruhinta.

Mamy tana danne abinda take ji ta ce

"Mene ne a jakar da na ga kin razana? Ba handout ne da biro da wasu abubuwan amfani na makaranta ba, mene ne baƙo a ciki, ko kin manta tun kina nursary ne nake haɗa miki school bag ɗinki idan kin dawo ma ni nake adana miki ita yaushe abubuwan suka sauya kuma" Zalika tana ɗan diriricewa ta ce

"No babu komai Mamy kawai dai ina sauri ne na je na yi break fast sannan ina da lacture ne ba na son na makara" Idanun Mamy suka cika da ƙwalla tana kallonta ta fito da kwalin hannunta da ta ɓoye ta buɗe tafin hannunta gaban Zalika ne ya buga da ƙarfi tana kallon kwalin hannun Mamy inda jikinta ya ɗauki karkarwa tana ƙoƙarin baɗa laɓɓanta don ganin ta ce wani abu sai dai gabaɗaya alamomin rashin gaskiya sun bayyana a gare ta a inda Mamy ta gama fahimtar cewa tabbas ba mafarki take ba Zalika dai ƴarta tallin tal guda ɗaya ƴa mace wacce daga ita bata da wata ƴa macen sai Mubin ita ce ta san namiji, namijin ma ba mijin aurenta ba namijin titi shin zarginta gaskiya ne ? Idan ba gaskiya ba ne da mai zalika za ta kare kanta?

A take zuciyar Mamy ta shiga raya mata

'Lallai akwai aiki ja a gaban iyaye mata wajen sanya idanu a rayuwar ƴaƴansu yanzu a ce har yarinya tana iskanci a waje amma uwarta bata ankara ba, shin ina fitar budurci da ake gane cra wannan ne karo na farko da yarinya ta fara sanin ɗa namiji? Amma a ce uwa bata lura ba duk da kasancewata uwa mai sanya idanu a rayuwar ƴaƴana amma har abu ya yi nisa ban sani ba, kenan wayon ƴaƴan yanzu har ya kai su ɓoye abin da babba zai kasa ganewa!

Mad about you

Delina de merly

My way intense

Gucci guilty men

Vanilla 28 kayali

Khamrah

I want choo

Creed aventus

Amber oud

Sugar baby

Club de nuit

Olympea

Stronger with you

Reef 33

Dior sauvage

212 VIP man

Blue de channel

Pink shiffon

Jadore

Bombshell

Pure seduction

Versace bright crystal

La vie est belle

Versace Eros man

*🎉 PROMO NA ƘARSHEN SHEKARA GA MATA! 🎉*

*Ki bar tsohon shekara da matsala, ki shiga sabuwa da gyara!*

Mun yi sabbin kaya don nuna soyayya da kulawa ga wanda suke son mallakar ɗaya daga cikin waɗannn abubuwan ko kuma duka.

*Ga kayanmu masu inganci da kike bukata:*

1️⃣ *Maganin Matsi Gam-Gam* Don matsi 1500 maimakon 2500

2️⃣ *Maganin Sanyi* Yana kawar da dukkan nau’in infection da wari, ƙaiƙayi, ƙuraje rikicewar al,ada 2500 maimakon 4k.

3️⃣ *Sabaya 3 in 1* Gyara breast, hips sannan tana gyara jiki 5k maimakon 7k.

4️⃣ *Maganin Gyaran Breast* Yana ciko da breast, ga masu shirin yin yaye da kuma wanda breast nasu yake buƙatar gyara 3k maimakon 4500.

5️⃣ *Daka* Tushen ni’ima 1500 maimakon 2500.

🎁 PROMO NA MUSAMMA

Ranar ƙarshe 31 ga Disamba, 2025

Ki gyara jikinki, ki faranta ran mijinki, ki shiga sabuwar shekara da armashi.

MAMAN AFRAH

09025576222

https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1

*RUWA CIKIN COKALI*

(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*

*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*

*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣4️⃣

JIDDA

Da matuƙar tashin hankali a tattare da ita take faɗin

"Lafiya mai ya faru?" Ta faɗa duk ta diririce saboda yadda ta ga mijin nata hankalinsa a tashe. Bai bata amsa ba don hankalinsa yana ga wayar da yake amsawa sai ta ji yana faɗin

"Gani nan Mummy" Yana gama wayar ya yu hanyar fita daga ɗakin cikin sauri lura da ta yi kamar hankalinsa ya bar jikinsa ta yi saurin riƙo rigarsa ta baya, tare da yin sauri ta sha gabansa suna fuskantar juna tamkar za ta saki kuka ta ce

"Ina tambayarka ko lafiya amma shi ne baka faɗa min ba" Kallonta ya yi sai kuma ya ga ta bashi tausayi hannunsa ya kai ya shago gefen fuskarta ya ce

"Ki yi haƙuri hankalina ne ya tashi, Mummy ce ta ce Daddy ya yanke jiki ya faɗi " Cike da tashin hankali ta ce

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ƙofar ya buɗe suka fito dagaɗaya ta ga ya fice a hayyacinsa, suna sakkowa ƙasa ya nufi hanyar fita Jidda ta ce

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull