Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 39
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 39: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 39. "Ka jirani in ɗakko hijabina" Bata jira cewarsa ba ta…
3,309 words
"Ka jirani in ɗakko hijabina" Bata jira cewarsa ba ta yi hanyar ɗakinta sai gata ta ɗakko hijabi a hannu a falon ta shiga sakawa tana gama sakawa sai ta ga Baba Kuluwa riƙe da plates za ta shiga kicin ta buɗe baki ta ce
"Baba zan fita za mu je gidan Mummy" Baba Kuluwa ta ce
"Lafiy Hauwa'u" Jidda ta ce
"Daddy ne ba ya jin daɗi" Fatan samun lafiya ta masa Jidda tana juyawa sai ta ga Ibrahim ɗin ba ya nan da sauri ta fita ganin ya bar ƙofar ma a buɗe. Ko da ta fita ta same shi har ya shiga mota, tana zuwa ta ce
"Ka ba direba ya kaimu na ga kamar ba za ka iya tuƙin ba" Cikin sanyin murya ya ce
"Zan iya" Bata sake magana ba ta buɗe ta shiga mai gadi da suke zaune suna hira da sauran ma'aikatan gidan ya tashi buɗe musu get kowa yana ɗaga musu hannu cike da girmamawa suka fita, gidan Mummyn suka kama hanya ko magana Ibrahim ba ya yi kasancewar jin muryar mahaifiyarsa da ya yi tana kuka a waya ƙaran wayarsa da take ajiye a gefe ne ya sanya Jidda ɗaukan wayar ta miƙa masa ganin sunan Mummy da sauri ya danna ya kara a kunnensa, ji ya yi Mummy tana faɗa masa sun tafi asibiti adirshin asibitin ta faɗa masa don haka ya juya kan motar suka kama hanya.
Ko da suka zo asibitin sun je ɗakin da aka kwantar da Daddy yana kwance lifet kamar gawa sai likita da yake sanya masa ruwa a hannu Mummy tana zaune a gaban gadon ta kifa uban tagumi idanunta jajawur. Haka su ma suka tsaya suna ganin ikon Allah. Bayan likitan ya gama abin da zai yi sai ya ce da Ibrahim su je office suka fita aka bar ɗakin daga Mummy sai Jidda da take ta faman ba Mummy baki.
Mummy ta ce
"Jidda lafiyarsa ƙalau fa, babu abin da yake damunsa, muna hira kawai miƙewar da zai yi ya yanke jiki ya faɗi sumamme" ,Jidda ta ce
"Subhanallah ki yj haƙuri Mummy in sha Allahu zai samu lafiya" ,Mummy tana share hawayen da ya gangaro mata ta ce
"Allah ya sa amma na tsorata da lamarin nan, gaskiya rayuwa abin tsoro ce "
A haka Ibrahim ya shigo direban gidan Mummy yana biye da shi riƙe da ledar magunguna sai kuma katan ɗin ruwan roba.
Har lokacin Daddyn bai farka ba don dai yanzu numfashin sa ya dawo kawai dai bacci yake, Ibrahim ya ce zai je masallaci ya yi sallah direban ma dama yana ajiye ledojin ya fita Jidda ma sallar ta yi ita dama Mummy tana hutun sallah ne
Wajen ƙarfe tara da rabi Mummy ta ce au tafi gida saboda Jidda sai Ibrahim ya ce zai kaita gidan ya dawo ita ma Jidda ta ce a asibitin za ta kwana amma Mummy ta ce a kaita gida..
Suna tafiya tana ta kwantar masa da hankali ga tausayinsa ya kamata, ko abinci bai ci ba ga rashin lafiyar Daddy mai gadi yana buɗe musu get ya shiga da motar mai gadi yana rufe get inda mai ba flowers ruwa ya taho da sauri ya zo yana ƙoƙarin buɗe masa motar cikin girmamawa amma sai ya dakatar da shi yana faɗin ba fitowa zai yi ba. Jidda ce ta juya ta kamo hannunsa ta sanya cikin nata ta matsa yatsunsa tare sa rausayar da kai ta ce
"Annurin zuciyata idan fuskarka ta zama babu walwala sai na ji komai ya sare mini, sannan sai na ga gabaɗaya duniyar ta mini ƙunci tare da yi mini wani irin duhu" Iska ya fesar daga bakinsa ya riƙe sitiyarin motar da hannu ɗaya duk da ba tuƙi yake ba, ya saka ɗaya hannun da take murzawa ya riƙe nata gamgam ya ce
"Ki bari har na dawo daidai Jidda yanzu damuwar Mummy da halin da Daddy yake ciki ya rufe komai amma ki sani zuciyata a buɗe take tana sane da ke sannan da ke take rayuwa"
Kallonsa take yadda fuskarsa ta yi fayau ta ce
",Plss mu shiga ciki na haɗa maka shayi mai ɗan kauri ka sha" Kai ya shiga kaɗawa alamar ba zai sha ba, amma ganin ta shagwaɓe fuska sai ya ji yana so ya faranta mata hakan ya sa ya yi na,am sai suka fito a tare tana riƙe da hannunsa suka shige cikinm gidan, a falon ƙasa ta masa masauki a kujera ta nufi kicin ko hijabin bata cire ba, shayi ta haɗo masa ta ɗoro a ƙaramin kofin tamgaran da ɗan ƙaramin plate ɗin kofin ta zo tana juyawa da tea spoon.
Ko miƙa masa bata yi ba ta shiga bashi a baki har sai da ta ga ya shanye tasss sannan ta ajiye a ƙasan kafet tsaye ya miƙe yana mata sallama ya juya zai fita yana dab da fita daga ƙofar falon ya juyo sai kuwa ta ƙarasa da sauri ya buɗe mata hannunsa ta shige ya rungumeta sannan ya yi kissing goshinta ya ce
"Ni zan tafi sai Allah ya kaimu gobe" Amsa masa ta yi ya ɗaga mata hannu alamar bye-bye ita ma ta ɗaga masa ya fita.
Tsakiyar falon ta koma ta aunkuya za ta ɗauke kofin shayin sai ga Saude ta zo ta karɓa ta je kicin ta wanke ta ajiye, ta fito sai ta ga Jidda zaune hakan ya sa ta mata ya mai jiki bayan ta faɗa mata da sauƙi sannan ta masa fatan samun sauƙi.
Sama ta haura jim kaɗan ta fito da kayan tuwon nan bayan ta ɗauke cokali da tuwon da Ibrahim ya gutsiro zai ci lokacin da Mummy ta kirashi wanda kiran ya yi sanadiyyar rasa nutsuwar zuciyarsa sanadin rashin lafiyar mahaifinsa. Tana sakkowa ta yi kiciɓis da Saude hakan ya sa ta ba Saude kayan tuwon ta ce ta kai kicin, karɓa Saude ta yi Jidda tana komawa sama Saude ta shiga kicin har da rufe ƙofa ta tsaya ta ƙarewa tuwon kallo tana ganin gurbin da akamcire a jikin tuwon wanda da alama cokali ɗaya ne kuma ga gutsuren lomar nan a gefen plate ɗin, wata ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala don ta san akwai abin da Aliya ta yi a saman, wanda tana zaton hakan zai kasance wani abu ne ta barbaɗa a miyar tuwon sannan zarginta da take ta rayawa a ranta cewar cokali duk da ba za ta iya hasashen ainihin abin da ya yj silar ganin cokali a bra ɗin Aliya ba amma kawai ta gwammace ta salwanatar da cokalin haka ta juye tuwon duka da miyar a baƙar leda ta wanke kwanukan ta gyara kicin ɗin. Ta fita da wata doguwar wuƙa a hannunta da kuma ledar da ta sauye tuwo da miyar sai wannan cokalin. Sai da ta je garden ɗin gidan can tsakanin wata bishiya ta haƙa babban rami ta jefa ledar da cokalin ta yi addu,a ta mayar da ƙasar ta rufe wajen sai da ya yi kamar ba a taɓa tona wajen ba, sannan ta bar wajen tana jin wani shauƙi.
Ko da ta yi shirin kwanciya ta saka kayan bacci pink colour masu laushi sosai ta shafa turare, ta hau gadon ta kwanta sai ta ji gabaɗaya ɗakin da gadon sun yi mata girma kasancewar babu tauraron zucuyarta Ibrahim.
Filonsa da yake kwanciya ta janyo kusa da ita tana shaƙar ƙamshin turarensa tana jin tamkar tana kusa da ita tun da basu taɓa nesa da juna ba tun da suka yi aure.
Daga ƙarshe ta ɗakko ƙafafunta ta sakko ƙasa ɗakinta ta nufa ta je ta kwanta a ganinta za ta samu sauƙi salama da sasaauci na tunanin Ibrahim da take ji tamkar shekara suka yi ba sa tare da shi.
Aliya tun da ta gama waya da Amatullahi sai ta kira Umma tana sanar da ita cewa aiki ya kammala, Umma ta ringa rawa da juyi a ɗakinta tana jin daɗin yau sun hau turbar zama masu arziƙi. Ko da Kasim ya dawo shi kansa ya yi mamakin ganin yadda fuskarta take a washe bata sai wani nan nan take da shi, bai san cewa tana yin hakan ne don ta hango tsantsar wata dama da za ta samu a rayuwa. Indomie ta dafa masa yau don badangarci da hannunta take bashi a baki ba ma da fork ba. Gabaɗaya daɗi ya cika Kasim ya kalle ta yana murmushi ya ce
"Haƙiƙa ni a cikin maza ɗan gata ne a wajen matata, matata tana sona!" Ya faɗa yana buɗe baki ta bashi indomie ɗin. A fili ta ce
,
"Idan miji bai zama ɗan gata a wajen matarsa ba a ina zai zama" Ta faɗa tana kallonsa.
A zuciyarta kuma ta ce
'Wanda dai nake so da muradi yana can sai dai very soon zai dawo gare ni tabbas zan murza kan naira har sai ta tabbatar ta zo hannun da za a bata wahala" Suna ta hira har suka kammala don ita ko a bakinta ta ce a ƙoshe take wani irin farinciki take ji irin farincikin nan mai hana ka cin komai duk da dama bata tare da yunwa.
Ko da suka zo kwanciya ma bayan ta sha maganinta a ɓoye na hana ɗaukan ciki tana rayawa a ranta cewa ta kusa daina shan magani da zarar ta auri Ibrahim za ta yi ban kwana da shan magani domin ta je inda za ta saki jiki ta haihu ta zubar da ƴaƴa yadda za su ci gado son ransu, tamkar dai sun ƙauro duniya.
Ranar Kasim ya san ya yi aure domin kuwa zagewa ta yi ta nuna masa kulawa ta musamman a wajen mu,amala, sai ta sa yake jinsa na miji sak babu sirki kamar yadda ake kiransa mata maza. Duk bai san tsabar farincikin da take ciki ba ne.
Washe gari da safe har ta matau ya fita ya bar mata gidan saboda tana son dara shirin barin gidan saboda ta san abubuwan da bokanya ta faɗa mata na cewa Kasim zai sake ta sannan za a rufe bakin Abba da duk wani ɗan tsurku da zai kawo tsaiko a lamarin. Yau Kasim shiga ya yi ta musamman son yau jinsa yake tamkar aabon angon da aka ɗaurawa aure a ranar, ko da ya zo mata sallama ma ya daɗe tana ta furzo mata kalaman soyayya tana amsa masa a fili amma a zucuyarta wani haushi ma yake bata.
Yana fita ta doka wani uban tsaki ta koma ɗaki ta zauna tana duba waya don ganin lokaci so take ta kira ta tabbatar amma kuma ganin ƙarfe goma sai ta ba zuciyarta haƙuri a ɗan jima domin kar a zargi wani abu. Ahawara ta yanke ta kira Amatullahi ta ce
"Ƙawata ya ne?" Amatullahi ta faɗa tana jiran kanun labarai duk da zuciyarta tana cike da zulumiin jin labarin tana jin babu daɗi don ta ita ma ta matsu ta samu miji ta yi aure ƴan unguwa sun ishe ta da tambayar aure da kuma masu faɗa mata magana a fakaice wato gorin aure tamkar dai a kansu take ko kuma su suke ciyar da ita da ɗaukan sauran ɗawainiyarta, mutane basa tunanin cewa shi aure lokaci ne idan har mutum bai yj aure to lokaci ne bai yi shi ma ba a son ransa ba, don wasu ƴanmatan ana sakawa suke jjn tamkar su kai kansu ɗakin miji saboda yadda ake nuna musu habaici da gorin auren, bayan auren nan ba farilla ba ne sunna ne kawai me ƙarfi. Wasu kuma in suka samu miji sai ɗagawa da girman kai su dole matan aure suke nunawa wanda basu yi auren ba tamkar su suka hana kansu auren.
Aliya ta ce
"Wallahi ni kaɗai na san irin farincikin da na kwana da shi, ai hatta Kasim ya dangwali albarkacin farinciki da nake ciki"
Amatullahi ta ce
"Shegiyar uwa sai bukka wato dai shi ala dole ya ɗauka faranta masa aka yi bai san abin ne hawan hawa ba,, to yanzu mene ne kanun labarai?" Ta tambaya cike da fargabar jin amasar tambayarta
Aliya sai da ta yi wata dariya mai haɗe da shewa ta ce
"Babu tantama kuma babu wani tunani tabbas na san aiki ya kammala saura abu ya dara aiki don a yadda na fahimta mutumin mayen tuwo ne kin ga kuwa ai tuni ya antaya tuwon nan cikinsa sauran kuma ya fara fuskantar mulkin mallaka daga gareni ke hatta Jidda wallahi sai ta gane ni asalin maƙiyarta ce don sai ta gwammace kiɗa da karatu domin matsawar na samu wata dama a kan Jidda wallahi sai na gasa mata aya a hanhu sai na sa ta wulaƙanta!" Ta ƙarashe maganar tana haɗe rai tamkar dariya bata taɓa kai ziyara fuakarta ba.
Amatullahi ta ce
"Kin min daidai ai wallahi kowa ya samu dama kar ya yi wasa da damarsa"
Aliya ta ce
"Ke dai bari ai abin yana min cuwo a ce Jidda ta mallaki abubuwan rayuwa ban mallaka ba wai har ni ce zan koma tamkar ƴar maula a wajenta wato tana ɗakko kuɗi ta bani wai ni Aliya kyakkyawa me aji da jiji da kai ni ce Jidda ta bani kuɗi wai da kuɗin Jidda na saya waya taɓɗi!".
Sun jima suna tattaunawa suka yi sallama ta ce duk yadda ake ciki za ta sanar da ita. Tana kashe kiran sai kiran Umma da shigo ta ɗaga Umma jin muryar Aliya fess cikin shauƙi tun bata gama jin kanun labaran ba ta carara guɗa, ita ma Aliyar guɗar ta ɗauka kafin daga bisani suka ɗauki shewa kamar wasu sa,annin juna ba uwa da ƴa ba.
Umma tana gyara ɗaurin ɗankwali ta maido da shi gaban goshi ta ce
"Wallahi ba ke kaɗai ba Aliya hatta ni zan tsula tsiyata musamman idan aka rufe baki da ƙwaƙwalwar wanann uban naki, dama shi yake taka min birki yana hana ruwa gudu"
Aliya ta ce
"Bari dai Umma sirikar Ibrahim ai an buga an barki sai kin zama zakaran gwajin dafi a cikin sirikan masu kuɗi" Suna ta tattunawa suka yi sallama Aliyar tana faɗin bari ta kira Jiddar ta ji za ta zo ta kira Umma ta faɗa mata yadda ake ciki.
Sunan Jidda ta kamo ta shiga kiranta, lokacin Jidda tana tsakiyar falon ƙasa tana sanya hijabin ta za ta tafi asibiti don har ta faɗawa direba kuma ta ji ya fito da motar jiran fitowarta yake, duk da sun yi waya da Ibrahim ya ce Daddy ya farfaɗo sai dai rashin ƙarfin jiki da kuma gefen bakinsa ma da ya ɗan karkace don yana da hawan jini. Sai ta ce za ta taho asibitin ya mata na,am don yana ta so ma ya koma gidan ya yi wanka amma ya kasa tafiya duk da damuwar Mummyn ma ta ragu.
Saude ce sunkuye a gabanta tana jera kwanukan a cikin kwandon da za a tafi da abincin asibitin, Saude tana ɗauke da kwandon tana biye da ita sai ga Baba Kulu ta fito tana cewa ta yi wa mai jikin sannu amsawa ta yi cikin girmamawa domin tana ganin Baba Kulu tamkar uwa a gare ta saboda Jidda ta san muhimmacin furfura.
Baba kulu ta juya ta koma tana ci gaba da abin da take yayin da wayar Jidda ta shiga ruri tana dubawa ta ga sunan Aliya ɗagawa ta yi tana faɗin
"Barka da safiya ƴar uwa rabin jiki fatan kin je gida lafiya" Aliya da ta koma ta kwanta a doguwar kujera haɗe da ɗaga ƙafafu sama ta ɗora daga can saman kujerar, hannunta ɗaya yana tallafe da wuyanta tana yatsina fuska ta ce
"Lafiya" Ta faɗa a takaice don har ta fara wulaƙancin da za ta gara Jidda tun daga yanzu, don duk tunanin magani ya ci
Bayan sun gaisa Jidda take faɗa mata Baban Ibrahim ne ba lafiya a asibiti ma ya kwana yanzu ma can za ta tafi, Aliya ta ce
"Amma jiya baki faɗa min ba"
Jidda ta ce
"Ai rashin lafiyar jiya da dare ne" Aliya ta yi shiru tana son jin kanun labarin yadda aka ci abinci da cokali sai dai ta rasa ta ina za ta fara zuwa can wani tunani ya faɗo mata hakan ya sa ta ce
"Allah bashi lafiya, ki masa sannu sannan ki wa Ibrahim ɗin ya mai jiki"
Jidda ta ce
"Zai ji in sha Allah ai a can asibitin ma ya kwana"
Aliya ta ce
"Ayya bawan Allah sarkin son tuwo" Ta faɗa haɗe da sakin kunnuwa don jin abin da Jiddar za ta ce, ƙirjin Aliya yana sama yana ƙasa duk da ta san ba za ta ji wani labari makamacin wanda take tunani ba, amma dai sai ta ji tan fargabar jin amsar, domin ta san tabbas ta yi furucin da za ta samu amsar tambayarta.
Jidda ta ce
"Wallahi kuwa ke dai bari ai duk ƙaunarsa da tuwon nan jiya sai da ya gutsura zai kai bakinsa aka sanar da shi rashin lafiyar Daddyn wallahi tsabar ruɗu bai san ya saki cokali mai ɗauke da tuwon ba, tuwon da ko a bakinsa bai ɗanɗana ba jiyan"
Dummm dududummmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi a take ta ji numfashinta yana neman barin gangar jikinta, bata san ya aka yi furucin ya fito ba ta dai ji bakinta ya furta
"Bai ci tuwon ba? Ko a bakinsa bai ci ba kika ce Jidda?" Ta taɓbaya a ruɗe tana tashi zaune cike da firgici, Saude kasancewar wayar ana iya jiyo maganar kuma tana tsaye ne daga gefen Jidda tana riƙe da kwandon a kan kunnenta ta ji maganar Aliya da take yi a gigice cikin diriricewa fakar idanun Jidda ta yi ta kauda kai gefe tana sakin dariyar gefen baki tana danne dariya mai ƙarfi da take son ƙwace mata, domin ta gama harbo jirgij Akiya ai dama ta san Aliya ba za a yi abin kirki da ita ba ta gama fahimtar cin duduniyar Jidda take.
Jidda kuwa duk da ta ji yanayin da Aliya ta mata tambayar sai bata kawo komai ba, tunanin ta ko yadda ta ji an ce yana son tuwon kuma bai ci ba shi ne take jimantawa, amma ai a ganin Jidda lafiyar mahaifi ta fi komai.
Baki ta buɗe ta ce
"Wllahi ko ɗanɗanawa bai yi ba ai tuwon ma ya lalace an zubar an wanke kwanon" Aliya bata ce komai ba illa sakin wayar da ta yi ba tare da ta sani ba, taimakon ta da Allah ya yi a kan kujera ta faɗi tsaye Aliya ta miƙe cike da tashin hankali tana tunanin abin da Jidda ta faɗa mata. Jidda kuwa da ta gaji da faɗin hello hello sai kawai ta datse kiran ta shiga mota Saude ta ba direban kwandon ya saka a a motar aka wangale musu get suka fita daga gidan.
Tsaye Aliya ta tashi hannu biyu a kanta, hatta ɗankwalin kanta tuje shi ta yi tamkar mahaukaciya sabon kamu haka ta koma, tana tuna irin tarar aradu da ka da ta yi wajen isar da cikalin wannan sannan yanzu ita idan har an kwatsa cokalin a cikin ƴan uwansa cokula ba za ta taɓa sheda shi ba wataƙila ma asirin jikin ya karye, tunanin ta ɗaya idan ta je ta sanar da bokanya abun da ya faru kar ta ɗakko mata jan aikin da ba za ta iya ba, tun da a ranta tana raya babu gudu babu ja da baya!
BABA
Ya yi baƙincikn rasa gutsuren tsumman rigar da ya gutsure a jikinnrigar ɓarawo da a tunaninsa da ita zai riƙe matsayin sheda ko wataran za a ga wanda ya saka yagaggen kayan sai ya gane amma dai ya sanya a ransa idan kere yana yawo zabo yana yawo watarana za a haɗu. Bai san cewa ƴaƴansa ne suka ɗauke yadin ba sannan aka haɗa aka ƙone da wanda ya gutsure ɗin da kuma gutsuren saboda tsaro ba don tsoro ba.