Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 40
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 40: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 40. Zaune yake da kwanon tuwonsa a gabansa yau a tsakar…
3,318 words
Zaune yake da kwanon tuwonsa a gabansa yau a tsakar gidan yake a zaune tun da ya kai lomar tuwon farko ko taunewa bai yi ba bare a samu damar haɗiyewa da sauri ya dawo da ita yana tofara kamar wanda ya ci kashi. Hannunsa ya tsame ya shiga ƙwalawa Mama Bilki da ta yi zaman dirshan a tsakiyar ɗakinta tana cin tuwonta bayan ta barbaɗa masa maggi dunƙule jin kiran ya ƙi ƙarewa ta fito tana suɗe hannu ta ce
"Haba Malam kira sai ka ce makaho ai ya kamata kake numfasawa"
Baba ya ce
"Abin da ya fi numfasawa zan yi, ke yanzu wannan ba abin kunya ba ne ki ɗauki wannan tuwon naki ci karka mutu ki kaiwa miji, ban da rashin tunani kina zaune gidan kishiyoyi uku ke ta huɗu amma baki iya tattalin miji ba? Bari ki ji mata wanda suka gama karantar hakayyar maza a kwanon mazan suke samun gurbi a zuciyar miji" Kallon sheƙe ta masa ta ce
"Wane gurbi kuma Malam ai gurbi ina ga an riga an cike in dai a zuciyarka ne" Sanin halinta ya sa ya ce
"In ji wane shegen?"
Ta ce
"Ah to ka tuntuɓa dai amma na san babu gurbin zama a zuciyarka"
Tunaninsa ko ta fara sakkowa ne da vayanin nasa dama tunaninsa bai wuce ta ringa masa lafiyayyan abinci ba hakan ya sa ya ce
",Wallhi tsaf mace za ta saye zucuyata in dai ta harkar abinci ne, ai ki dafa shimkafa miya ta ji nama wallahi kin kasa kin sayar a zuciyata" Da dariya ta bushe ta ce
"To ni yanzu an ce maka neman wajen zama nake, to ai ko ni kake kawo mini abincin da naman gurbin zama zan baka w tawa zuciyar" Jin furucinta ya gane nasa furucin bai samu shiga ba hakan ya sa ya saka ƙafa ya haure kwanon miyar ta tu tsure a wajen ya shiga ƙwalawa Hafsa kira ta fito ya ce
"Ki duba idan akwai mai da yaji ki mini kwaɗo da tuwon nan in samu in kashe yunwar cikina wanna uwar taki bata neman albarkar gidan aure, a ce maggi mace ba za ta saya ta saka a miya ba"
Har ta juya za ta tafi ta juyo ta ce
"Kai daniya hatsi ko masara kake badawa wataran ma ka ce hatsi ya di tsada ka auna ka kai kasuwa ka siyar ka ɗauke canjin saman ka saka a aljihunka sai ka auno masarar ka kawo, mace za ta bada kuɗin surfe ta biya na niƙa sannan ta saya kayan miya ta maka miyar haba ai wannan macen ko banki ce ita ka gama daƙushe ta" Jin haka ya miƙe yake masifa yana faɗin ya rasa lokacin da suka fara daina tsoronsa har kowa yana da bakin mayar masa da martani!.
Bayan kwana biyu sai ya tsiro da wani abu wani daga yau ya daina basu hatsi ko masarar tuwon ma don ya ga neman ake a kassara shi tun da har yanzu ƴaƴan babu wata wacce ta fito da miji hakan ya sa ya ce iyayansu mata ne suka ɗaure musu tsantsa, don haka sai dai su suke ciyar da su amma shi dai kam ya daina bada ko ƙwayar hatsi.
Tun daga ranar ya ƙara haɓaka kayan store ɗinsa daga ya ji wani ya matsu zai sayar da hatsi haka zai je ya saye ya zo ta libga a store iyalinsa ko oho, watarana ya je yana ciniki da wani maƙocinsa daga yamma sai mutumin yake cewa ai buhun hatsi da zai sayar iyalansa zai aunawa masara sun ce sun gaji da cin tuwon hatsi, shi ya sa ya ɗakko buhu ɗaya daga ciki zai musu canji tun da shinkafa iya ta rana ce kaɗai ake yi. Buɗar bakin Baba ya ce taɓ amma kai wahalalle ne ai ni nan na gama gane idan ka biyewa iyali sai sun ga ka yi gawa don komaj naka sai ya ƙare saboda kullum sai an ce ka kawo abinci. Shi kuma yake faɗa masa cewa ai wannan nauyi ne da Allah ya ɗorawa mutum ko bai sauke ba sai Allah ya tambaye shi, amma Baba bai ji ba haka ya saya ya je a jibge shi kuma mutumin ya siyowa iyalansa buhun masarar don ya faranta musu.
A washe garin ranar da ya sayar sai Allah ya buɗa masa ta hanyar da bai zata ba.
Store ɗin Baba ya cika da shinkafa da hatsi dawa da masara, ko masakar tsinke babu, amma nauyin iyali an ƙi a sauke, kullum haka za suke zaune cikin yunwa ƴaƴan sai dai kowa ya je ya yi buga buga masu roƙon samari su roƙa, masu bada mutuncin su a basu kuɗi su bayar wanda kuma za su ɗauka ma ba a basu ba a wani waje sai su ɗauka don duk su saukewa kansu nauyin haƙƙin da ba nasu ba, haka matan ma wata sai ta kwanta da yunwa idan bata da kuɗi yanzu dai kowa shi yake ciyar da kansa.
Kullum da asuba sai ya je ya buɗe store ɗin kafi ya tafi masallaci, ya ga komai lafiya domin yanzu kwaɗon da yake datsewa ba ya buɗuwa da kowane mukulli sannan idan ya dawo daga masallaci ma a store ɗin zai yada zango yana kallonsu yana murmushin jin daɗi yana ganin arziƙi gashin hanci ne, sai dai ya manta da karin maganar bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema.
Yau ya kama litinin yana zaune da azzahar yana ganin waccen ta jiƙa garin kwaki, wancan ta shigo da awara kowa da abin da yake, shi kuma yana zaune da a ce wani zai miƙo masa da karma zai yi.
Mama Habiba ce ta zo ta ce
"Mallam don Allah ka bamu hatsi a yi tuwon nan, wallahi jiya ma da yunwa na kwanta kasancewar bani da kuɗi da safe ma ban karya ba ga rana ta yi yanzu, wallahi... Kafin ta kai aya ya katse ta yana masifa yana faɗin ko ƙwayar hatsi ba zai bayar ba, tashi ta yi jikinta babu ƙwari ta kama hanyar ɗakinta, kamar daga sama kamar almara sai Baba ya fara hango hayaƙi yana fitowa daga jikin ƙofar store ɗinsa kafin ƙiftawar ido gabaɗaya store ɗin ya kama da wuta sosai gobara ta kama..
SADIYA
Har suka shige tana tsaye bakinta a sake, tana jin ana cewa maza suna juyawa uwayen gidansu baya idan suka samu wasu matan ma,ana idan suka ƙara aure duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, amma daj kam abin na Nasir ya fara wuce gona da iri, domin ta lura shi babu ruwansa ma da wani adalci in ba rashin adalci ba da rashin sanin muhimmancin matarsa uwar gidansa ta yaya za a yi a ce wai ita ce za ta ɗauke kayanta a mata kicin na langa langa saboda ita bata da ƴanci sannan bata da wani galihu a cikin gidan.
Duk da ta san idan ɓera da sata to daddawa ma da warinta, ma,ana idan har da laifin Nasir wajen mayar da ita ba komai ba a cikin gidansa to da laifin iyayanta musamman mahaifinta, da shi babu ruwansa da ƴanci ko kwanciyar hankalin ƴarsa a gidan aure shi kawai burinsa a riƙe masa ƴarsa a ɗauki ɗawainiyarta, kowane namiji kuwa ya ga babu wanda ya damu da kai hasalima iyayan so suke a ɗauke musu nauyinka dole sai yadda ka gani don wulaƙanci an saya maka shi kwando -kwando.
Abin takaicin ma shi ne mahaifiyarta duk da ta san mahaifiyarta bata isa da Baba ba amma dai ya dace a ce ita a matsayjnta na mace tana tausaya mata da sauraron halin da take ciki, ba wai ta yi watsi da damuwarta ba in ta zo za ta faɗa ta ƙi saurarenta, kuma rashin amayar da damuwar ne yake ƙara daskarar mata da damuwa a zuxuyarta, gashi saboda cikin da take ɗauke da shi ba ta son take saka damuwa a ranta sai dai shi faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi.
Kicin ɗin ta shiga Kalifa yana buye da ita ta shiga kicin ɗin, jin ƙafarta ta ƙara riƙe mata sai ta samu waje ta zauna a kan kujerar katako irin ta mata ta tsakar gida, tana zama kawai da takaici ya cika mata zuciya bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba,bata ankara ba sai ta ji hannun Kalifa a kumatunta tana share mata ya ce
"Momma ki daina kuka" Ya faɗa cikin muryarsa ta yara sai lokacin ta ankara da abin da take da sauri ta saka hannu ta ƙarasa goge hawayen, domin ko kaɗan bata son Kalifa yake ganin zubar hawayensa idan ya tashi da haka lokaxin da ya yi wayo zai iya fahomtar abin da ya saka ta zubar hawaye a baya. Abu na gaba idan har yaro yana ganin hawayen mahaifiyarsa koyaushe yau da gobe zai sa ya ɗauka su hawayen ba wani damuwa ba ne idan ana zubar da su, hakan zai zamana ya saba gani nan gaba ko da a ce ya girma idan zai ga hawayen mahaifiyarsa hakan ba zai zama damuwa a garesa ba wanda zai sa ya ji wani iri domin ya saba gani, idan har yara suna ganin hawayen zai zamana basa ɗaukan kukan uwa da muhimmanci, basa ɗaukan zubar hawayen mahaifiyrsu a bakin komai.
Murmushi ta yi tw ce
"Ba kuka ba ne yaji ne ya shiga idanuna" Ta faɗa tana kama hannuwansa biyu ta riƙe tana dariya, shi ma dariyar ya yi ya ce
"Yaji ne Momma?" Ta ce
"Eh" Daga haka ta yunƙura ta tashi tsaye don sai da ta dafa ƙasa ma ta tashi. Kayanta na kicin ɗin ta shiga haɗawa domin hanyar lafiya a bi ta da shekara domin idan da ita kaɗai ce matar Nasir yanzu sun zama su biyu in har ta yi wani abu da zai yi sanadin Nasir ta kaita gida, to ta san Baba haƙuri wataƙila har sai ya durƙusa wannan kuma abin kunya ne a gareta kishiya ta san waye mahaifinta mene ne matsayinta a gidansu duk da ta san waccen kaita gidan da ya yi har sai da Nasir ɗin ya ba Meenal haƙuri.
Haka ta ringa fito da kayan Kalifa ma yana ɗakko ƙananan abubuwa har suka kwashe tass. A waje guda suka tattara lokacin Nasir ya fito daga ɗaki Meenal tana biye da shi, haka Meenal ta wuce ta gabanshi ta nufi kicin ta riƙe da plate mai ɗauke da kofuna kicin ɗin ta je ta ajiye tare da rufo kicin ɗin ta juya ta kalli Sadiya ta ce
"Ko ke fa" Tana faɗar hakan ta zo ta tsaya gabansa tana masa magana cikin kwarkwasa amma Sadiya sai ta ba bango ajiyarsu kamar ma bata san da zaman su a wajen ba.
Bayan ya fita Meenal ta kalle ta ta ce
"Ya kamata ki fara shirin haƙura da wasu abubuwa da dama daga cikin gidan nan domin ni da ke za mu yi wani zama da ba lallai ki jure ba, amma zai fi kyau ki haɗa kayanki ki nufi gida don sai hakan ya fi zamar miki kwanciyar hankali, amma a shawarce idan kuma kin ga za ki jure to ga fili ga mai doki...
*Idan Allah ya sa muna raye a page 30 za mu gama Book 1 sai mu tafi book 2 wanda shi ne za mu yi har ƙarshemkn labari, sai dai tafiyar tamu tana da nisa, domin labarin yana da ɗan tsayi sannan akwai sarƙaƙiya da abubuwan mamaki al,jabi tausayi dasussa, sai wanda ya bibiyi labarin ne zai gane abin da nake nufi.*
MAMAN AFRAH
*09025576222*
https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 2️⃣5️⃣
ALIYA
Zaman dirshan ta yi a tsakiyar dalon tana kuka haiƙan, gabaɗaya duniyar ta mata matsi da ƙunci ji take tamkar ta kashe kanta ta huta wannan wace irin ƙaddara ce a cw Ibrahim wai ko ɗanɗanar tuwon bai yi ba don baƙinciki da takaici ma a ce wai wurgi ya yi da cokali me ɗauke da asirin a jiki kawai saboda an faɗa masa rashin lafiyar ubansa zai shikenan zai jiƙa mata aiki. Bayan ta sha wuya da kuma kasada wajen zuwa ta sauya cokalin da kuka mai ƙarfi ta rushe tana faɗin
"Na shiga uku na lalace Allah ya isa tsakanina da uwar Ibrahim da ta kira shi ta faɗa masa rashin lafiyar ubansa har ya yi sanadin fasa cin tuwon da ya yi, daman ma uban nasa mutuwa ya yi mu ga tsiya" ,Ta faɗa tana haura ƙafafu duk ta cakuɗa gashin kanta, ɗifff ta yi kamar ruwa ya ci tw, tana saƙa da warwara ranta in ya yi dubu a ɓace yake gabaɗaya sai tsanar mijinta Kasim mata maza ya turnuƙe mata zuciya tana tuno irin yadda ta bashi haɗin kai a gadon su na sunna a daren jiya duk don tana cike da ɗoki da farincikin cikar burinta na auren Ibrahim ashe dai bata san tufkar da ta yi an warware mata ita gabaɗaya ba!.
Sai da ta sha kukan takaicin ta tsagaita sannan ta janyo wayarta ta kamo sunan Umma ta doka mata kira Umma tana ganin kiran ta ɗauka cike da murmushi ta ce
"Tilon ƴata ki ce aiki ya kammala yanzu za mu fara baza capacity, wallahi naira sai ta ci ubanta a wajenmu, motoci da gidaje masu kyau sai sun san mun yo kuɗi mun kerewa wulaƙanci!" Ta faɗa tana jiran Aliya ta fara kora mata bayani Maimakon ta ji muryar Aliya cikin farincki tana mata bayani sai ta ji Aliya ta fashe da kuka Umma hankali tashe ta ce
"Kukan me kike Aliya? Buɗe bakin ki ki faɗa min wallahi gabana faɗuwa yake kar dai ki faɗaa min mummunan labari mai ya faru?"
Aliya cike muryar kuka ta ce
"Umma bai ci tuwon ba" Umma tana zare ido tamkar kwarton da aka kama ta ce
"Bai ci tuwon ba to uban mai ya ci ko dai Jidda ce ta yi wani mugun tuggun da ya sa bai ci ba, ko dai ta harbo jirginki Aliya ke kike haukarki?" Ta tambaya cike da zaƙuwar son jin dalilin.
Aliya ta ce
"Wannan tsohuwar tasa ce ta masa waya wai ubansa bashi da lafiya ya yanke jiki ya faɗi shi ne ya jefar da cokalin tsabar ruɗewa a sibiti ma ya kwana tuwon ya lalace an zubar" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Umma da take jin ɓacin rai tamkar ta yi ƙaramar hauka, sosai ranta ya ɓaci ta ce
"Ki daina kuka Aliya in har ina numfashi a doron ƙasa saj kin cika burinki, ko ma in ce burinmu sannan a shirye nake na yi fatali tate da tarwatsa aniyar duk wani wanda zai kawo tsaiko a lamarin nan" Aliya sai ta ji ta ɗan samu ƙwarin gwiwa hakan ya sa ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya nan Umma ta yi ta bata baki a kan cewa ta kwantar da hankalinta in dai gidan Ibrahim ne ta gama shiga ta gama.
Sun yi sallama bayan sun jajantawa juna Aliya saboda takaici ko da Jidda ta ƙarasa asibitin ta kira ta don ta ce ɗazu suna magana basu gama ba ta daina jin ta amma sai Aliya ta ƙi ɗaukan kiran don yanzu kawai haushin Jidda take ji.
Washe gari Umma ta kira Aliyar tana faɗa mata tare za su je ajen bokanyar don ta faɗa musu abin da ya dace a yi domin ita yanzu ta gwammace ko salwantar da rayuwar Jidda ne a yi in har za a samu biyan buƙata duk da tana son a bar Jidda a rayw domin su ƙunsa mata baƙinciki irin baƙincikin da za ta gwammace gwara mutuwarta amma in hakan zai zama matsala gwara ta bar duniyar ma su su ci tasu duniyar da tsinken tsire mai tsini. Daga Abba har Kasim babu wanda aka faɗawa fitar hanya suka sata suka tafi yana kowane ya fita kasuwa. Ko da Amatullahi ma ta tambayi Aliya sai ta faɗa mata da Umma za su je wannan karon.
Suna isa bokanya ta musu izini suka shiga. Bayan Aliya ta gabayar da Umma a matsayin mahaifiyarta sai kuma ta shiga rattabo mata bayanin yadda al,amura suka kasance wato yadda ba a dace da cin abinci da cokalin da aka yi asirin nan ba. Ta yi mamaki kuma ta jimanta abin domin tana tabbatar musu cewa da a ce ya ci abinci da cokalin nan da matsalar su ta kau har abada!. Sai dai matsalar idan aka yi aiki ba a maimaitawa sai dai a yi wani sabo. Nan Umma tw ce kawai a yi wani aikin.
Bokanya ta yi jim ta ce
"Aikin da za a yi yana da hatsari kuma yana da ci, domin idan aka yi har sai ya fi na cokali zafi sai dai shi wannan aikin ana faɗar ladan da za a biya na aiki a nan take ta sanar da su za a biya kuɗin aiki dubu ɗari biyu. Daga Umma har Aliya kallon kallo ake domin kaf cikinsu babu mai dubu goma ma ta kansa a halin da ake ciki dai yanzu babu kuɗi sannan kuma suna buƙatar a yi aikin da gaggawa.
Bokanya ta basu kwana biyu a kan cewar idan an kawo kuɗi za a yi aiki. Tun da suka taho suka shiga zulumi da tunanin yadda dubu ɗari biyu za ta fito, idan suka yi hasashen kuɗin da yawa sai kuma su tuna tasirin da aikin zai yi, tun da idan Ibrahim ya shiga hannunsu sai sun fanshe abubuwa da yawa.
Sun rabu a kan cewa za su yi waya bayan sun tsara cewa Umma ce za ta kai wa Jidda kukan buƙatar kuɗin tun da suna ganin tana gidan daula ba za ta rasa kuɗi ba.
Washe gari aka sallamo Daddy daga asibiti ya ware tass sai dai ɗan abin da ba a rasa ba. Jidda tana zaune a bakin gado Ibrahim ya zo ya zauna ya ce
"Habibty rufe idanunki" Wani kallon ƙasan ido ta masa sai kuma ta murmusa haɗe da runtse idanun, ya ce ta buɗe hannunta haka ta buɗe hannun sai da ya ajiye mata mukullin a kan hannun sannan ya ce
"Buɗe idanun" Tana buɗewa ta ga mukulli a hannunta mukullin mota, nan ta shiga tambayarsa ya sanar da ita cewa Abba ya siyawa mota, don dama yana da niyya. Wata iriyar runguma ta masa tana ta murna tare da jero masa wasu addu,o,i masu daɗi hakan ya sa ya ji matsayinta ya ƙara ƙaruwa a zuciyarsa. A ranar ne ta shirya domin zuwa ta isar da saƙonsa zuwa ga Abba bayan magriba tare suka je a motar direbansa yana biye da su don haka yana ajiye ta ya bata mukullin ya shiga motar da dirwban ya zo da ita ya ce an jima zai dawo ya ɗauke ta.
Da sallama ta shiga gidan lokacin Abba bai dawo daga masallacin ishsha,i ba. Umma da take zaune a tsakar gida a kan tabarma ta buga uban tagumi ko da ta ji sallamar ma sama sama ta ji sai da ta ɗago ta amsa duk a diririce musamman da ta ga Jidda cikin shuga ta alfarma cikin shigar manyan hajiyoyi wani dakkaken leshi wanda ya amsa sunansa leshi da ƙaton mayafinta da ya rufe mata dukkan ilahirin jikinta, sai takalmi da jaka masu aji sarƙoƙin gwal ɗin da ta saka suna walwali su ne suka saka Umma jin zuciyarta har wani ɗaci-ɗaci take, ita kuma Jidda ba ita ce ta ɗakko kayan ba gabaɗaya Ibrahim ne ya ɗakko mata a cewarsa gwara ta je gida a ganta a ce ya iya kiwo sannan ya riƙe amana haka ya faɗa mata cikin wasa lokacin da ya ɗakko mata kayan.
Umma dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta ce