Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 45
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 45: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 45. "Malam ko mu yi kuka ko kar mu yi wannan ƙaddarar ba…
3,371 words
"Malam ko mu yi kuka ko kar mu yi wannan ƙaddarar ba mu isa mu kankar ta ba, kai da Allah ya tseratar da kai da iyalanka babu wanda wutar ta ƙone ai an ci ta varka, baka ga ko gidan jaje aka je ba idan iya dukiya ko amfani wuta ta ci ba har barka ake yi wa mutum saboda ba ƙaramar ni,ima ba ce saboda ubangiji yana iya yin komai amma ya tsayar iya haka wato ya taƙaita"
Yana kallon ta da jajayen idanunsa ya ce
"Barka fa? Kika ce a yi barka to duk wanda ya tako gidan nan ya yi mini barka sai ya cire masa ƙafa" Mama Habiba ta ce
" Kenan baka godewa Allah da wannan abin da ya maka ba, da ka gode masa sai ya dawo maka da abin da ka rasa ta inda baka yi zato b... Kafin ta ƙarasa ya ce
",Rufe mini baki Habiba ai ina ga ma ke ce kika mini baki, da kika zo riƙona in bada abinci a dafa baki da kuɗin da za ki sayi abin da za ki ce wataƙila ma sanadinki ne gobaear ta kama, ni ban san ma wace jarabar ce ta sa nae zaune da ke ba har yau Habiba, to mace ke dai ba haihuwa kike ba sannan kawai dai ni ne nake ciyar da ke don haka kawai ina ga zan hukunta ki...
Mama Talatuwa ta katse shi da sauri da faɗin
"Haba Malam kaima ka san wannan dai son zuciya ne kawai ka yarda da ƙaddara saj ka samu sauƙi a zuciyarka, amma wannan zargi ne kake hakan kuma zai saka maka kokwanto a zuciyarka baka yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko...
Ƙasa ya dafa ya miƙe tsaye duk da ƙafafunsa karkarwa suke saboda gabaɗaya abin da ya faru ya ruɗa shi.
Da yatsa ya nuna Mama Talatuwa ya ce
"Idan akwai shegen da zai faɗa min yadda zan yi a rayuwata sai in gani, don haka ni nake da damar yin abin da na so a lokacib da na so"
Mama Habiba tun maganar da ya faɗa ta gorin da ya mata hawaye ya daɗe da wanke mata fuska a zuciyarta tana addu,ar Allah ya bata haihuwa watarana, Baba ya kalle ta ya ce
"Habiba ki je na yanke igiya ɗaya daga cikin igiyoyin da suke tsakanina da ke" Mama Habiba ta ɗago fuskarta sharkaf da hawaye ta ce
"Tohm Malam ina roƙon Allah ya sa haka ya zama mafi alkairi a garemu" ,Bai tanka mata ba sai Mama Talatuwa da tar rafka salati, ita kuma Mama Bilki da take jiyo abin da suke daga ɗakinta ta leƙo ta tsaya a ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa ta ce
",Allah ya yanke miki wahala Habiba, yo ai ke gaba ta kaiki gobarar titi, zaman gidan nan ai jarabawa ne, duk lokacin da Allah ya yanke maka sai ka gode wataƙila gaba ta fi ba ya yawa!" ,
Baba ya ce
",To mai bakin reza, wato ke ishashshiya da mai to ai hausawa sun ce riƙon mahaukaci sai sarki, kuma wallahi kika cika baki kafin ta isa gidansu ke ma kin kama hanyar naku gidan" Baki sake take kallonsa.
Mama Habiba ba ta tanka musu ba ya wuce ɗakinta jiki sanyi ƙalau ranta duk bau daɗi tana tunanin ashe dama shi ya sa ubangiji ba ya son saki duk da abu ne halactacce, saboda gabaɗaya ta ji wani ɗaci a ranta lallai ta tabbata saki ba shi da daɗi.
Kayanta ta haɗo a jaka ta fito ta zo ta yi wa matan da yaran gidan da suka fito sallama ta kama hanya ta fita.
Tana fita Baba ya ce
"Yawwa yanzu kuma na ragewa kaina wahala amma dai ba zan gushe ba ina son ɗa namiji ko kan gararre ne sai ranar da na haifi ɗa namiji dole ne ma yanzu in samu budurwa ko sakin wawa in auro" ,Yana faɗar hakan ya ja ƙafafunsa yana yin ɗan kukan takaicin ƙonewar kayan abincin sa. A tsakar gidan kuwa Mama Talatuwa ce kaɗai take cike da jimamin barin gidan da Mama Habiba ta yi sai dai tana fatan ta samu sauyi mafi alkairi tun da ta lura rashin haihuwar ne kaɗai yake saka Baba yake mata yadda ya so.
Washe gati da maƙota suka riƙa shigowa gidan suna jajantawa Baba. Duk magidancin da ya shigo sai Baba ya ce
",Kun ga dai yadda Allah ya jarafceni da ƙonewar kayan abincin, wannan lamari ne da yake buƙatar taimako da tallafin jama,a sannan kamata ya yi mutanen unguwa su yi gangami a yi meeting a sanar a masallaci ake haɗa kuɗin tainakon da za a bani wataƙila kuɗin su zama silar warakata dagaa baƙin talaucin nan" ,Duk wanda Baba ya faɗawa haka sai ya nuna ya yi na,am kuma hakan abu ne mai kyau sai dai babu wanda ya zauna ya ce a yi shawarar haɗa masa kuɗin domin Baba bai san cewa kaf unguwa babu wanda bai san halin da gidansa yake ciki ba, ya manta cewa yanzu kiwo na mutum ake yi ba dabba ba.
Ko da Mama Talatuwa ta kira Sadiya a waya ta sanar da ita abin da yake faruwa ta yi jimami sosai kafin daga bisani ta fawwalawa Allah komai dama ai ta san halin mahaifinsu na rashin wadata iyali wanda bai san hakan cewa ba iyalinsa kaɗai yake tauyewa ba hsr da kansa yake tauyewa domin sai ya sauke nauyin haƙƙinsu ne Allah zai ƙara buɗa masa, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan gani yake rashin wadatarwar shi ne zai haɓaka arziƙinsa.
Ko da ta je gidan ta jajanta masa sai da ya ce
"Sadiya kin faɗawa Nasir ɗin na samu gobara komai na kayana abincina ya ƙone? Na kira wayarsa sau biyu bai ɗaga ba kuma bai biyo kiran ba, ai kin ga a matsayinsa na surukina ɗaya ƙwallin ƙwal ya kamata ya kawo ɗan wani abu mana, don na ga jama,ar unguwar nan babu niyya ango ya kwana da wando, tun jiya an gagara kawo ko ƙwayar gero bare a saka ran kawo shinkafa, ni wallahi na ɗauka zuwa yanzu an tara buhun shinkafa ƴar gwammani buhu bakwai a lalace na hatsi biyar dawa huɗu amma har yanzu shiru maƙatau, ko dah taimakon ƴan siyasa zan nema ne?"
Sadiya ta danne takaicin da ta ji ta ce
"Baba wataƙila ko yana kasuwa lokacin da ka kira shi, amma dai maganar kawo tallafi dama ba lallai ba ne tun da yanzu rayuwar ce sai a hankali kowa ta kansa yake...
Hannu ya ɗaga mata ya ce
"Ke dalla rufewa mutane baki, ba ta kai ba idan ma ta ƙafa ake ai ba za su rasa amfanin abinci a gidansu ba a lalace ko kwano biyar biyar ce mutum in zai zo jaje sai ya taho da shi, amma don asara sai su taho babu komai kowa haka zai shigo hannu yana dukan cinya su zo su ishi mutane da cewa, ka yi haƙuri malam Bala haka Allah ya ƙaddara Allah mayar da alheri" ,Ya faɗa yana kwaikwayon yadda mutanen suke faɗa in sun zo masa jajan tare da jan wani dogon tsaki yana muzurai. Haƙuri ta shiga bashi ta ɗakko dubu goma ta ba shi, ya karɓa ko godiya bai mata ba bare ya saka albarka, saboda shi yanzu wasu kuɗaɗe masu kauri yake so su faɗo masa.
Kamar zai yi kuka ya ce
"Wllahi shi ma limamin nan na masallacin nan ba shi da tausayi ina ga ma in daina sallah a masallacjn nan in koma wani, mutumin nan yana kallo tun kan ladan ya kira assalatu na fita na je masallacin nan na ringa sallar nafila ina ɗaga hannuwa sama idan na idar ina ta addu,a amma na ɗauka da aka idar da sallar asubar zai yi sanarwa a lasifika cewa a taimaka mini amma shiru maye ya ci shirwa, haka da aka idar da sallar azzahar na kifa kaina da gwiwoyin ƙafata wai duk don a fahimci ina cikin damuwa da halin ƙaƙanika yi amma babu wanda ya bi ta kaina"
Haƙuri dai Sadiya take ta ba shi, bayan ta jo sallamar mutane a zaure ta amsa suka shigo don Baba yana jin sallamar ma ya ƙi amsawa ya rage murya ya ce
"Sadiya da kin ƙyale su, don ba wata tsiyar suka kawo ba in banda zance" Ita dai ba ta amsa ba haka suka shigo Baba kuwa ya haɗe fuska yana muzurai don dakyar yake amsa jajan da ake masa.
Sadiya sai da suka keɓe da Mama Talatuwa take faɗa mata sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba, salati ta yi hankali tashe tana jimanta abin, don ita da ta shigo ta ga ɗakin Mmar a rufe ta ɗauka ko unguwa ta tafi cike da damuwa a fuskarta ta ce
"Mama wai su maza haka suke ne?"
Mama ta ce
",Kamar yaya?"
Sadiya ta ce
"A yadda na fahimta yawancinsu ba su da uzuri, sannan duk daren daɗewa suna manta halacci, kuma su babu ruwansu da daɗewar da mace ta yi tare da su da sadaukarwa da taimakonsu da ta yi a rayuwa, haka kawai wani namijin sai ki ga an ce sun kwashe shekaru da matarsa tun ba shi da komai tun suna gidan haya, wani ma ko aikin yi ba shi da shi, sai ya fita ya nemo za a samu a ci watarana ma a haƙura idan bai samo ba, wani kuma matar ce za ta ciru ta ƙullu ta ciyar da gidan wata rana, wata ma bashi za ta ci, wata kuma ta haka jarinta da take juyawa zai salwanta a wajen taimaka masa, amma daga ya samu dama sai ya manta da duk abubuwan da suka faru a baya, sai ki ga bai mata halacci ba, sai ki ga tukucin da zai mata shi ne rabuwa da ita sai ya sake ta, ya auri wata ya ci gaba da rayuwa da waccan ɗin wacce ta zo ta samr shi cikin arziƙinsa wacce ba ta san wahalarsa ba amma ita za ta ji daɗin ita wacce ta sha wahalar sai ki ba ba ta da darajar da za ta zauna a gidan nasa ma mai ɗan mutunci shi ne wanda zai zauna da matar bai sake ta ba, amma dai wata duj da tana gidan sai ki ga wulaƙanci yana biyowa baya" Cewar Sadiya tana hawaye.
Mama ta ce
"Eh maganrki tana kan hanya Sadiya duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba"
Sadiya tw ce
"Ni ma ai wasu na ce Mama, dimin wasu sun san halacci wani ba ya taɓa mantawa da halaccin, wani yana darajawa da mutunta matar ko da a ce ya auri wata matar to fa ya san darajar waccan da suka sha wahalar tare"
Mama ta ce
"Ai wasu mazan sai addu,a domin wani namijin a ya riƙe alƙawari amma mafi yawanci ƴa mace ta fi yin halaccia a kan ɗa namiji, mace ta fi riƙe alƙawari duk da su ma mazan akwai masu tsananin riƙe alƙawari"
Sadiya ta ce
"Mai ya sa?"
Mama ta ce
"Saboda za ki ga ƴa mace ko mijinta ne ba shi da lafiya wato duk tsananin jinya za ta zauna ta kula da shi, sannn ko da nakasa ya samu sai ki ga ta ƙarar da ƙuruciyarta wajen kula da shi, babu ruwanta da sai ta je ta auti wani ta ci gaba da rayuwa da wanin, amma ita kuma macen idan bata da lafiya ko zazzaɓi ne ya yi tsananin sai dai a kaita gidansu iyayenta su yi jinya, idan ta warke sai ta dawo gidan mijin"
Sadiya ta ce
"Kenan lafiyarta ce a bar amfana?"
Mama ta ce
"A,a ina faɗa miki yawancin abin da yake faruwa amma akwai wasu mazan da suke kula da matansu fiye da tunaninki" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke amma dai ta ji ɗacin sakin da Baba ya yi wa Mama Habiba.
Ko kiran magriba ba a yi ba ya ringa ƙwala mata kira yana faɗin ta ɗakko Kalifa su zo su tafi gida.
ZALIKA
Tana karkarea take kallon kwalin duk ta diririce tunanin ta ya tsaya cak sai faman haɗo tunanin take amma hakan ya gagara, ta ma rasa abin da za ta shirya don ta kare kanta don ta ji ƙwaƙwalwar ta da kuma yanayin da jikinta ya nuna suna neman ƙin bata haɗin kan da zai taimake ta, domin ganin ta kawar da zarginta a kan wannan mummunar ranar da za ta fallasa asirin da take ɓoyewa, duk da ta san saɓon ubangiji ne sanna duk lokacin da za ta aiwatar da saɓon ta manta cewa shi wanda ya haramta hakan hakan yana ganinta, kuma duk abin da ka ɓoyewa wani mutum ba za ka ɓoyewa Allah ba, haka kuma duk wani abu da kake ɓoyewa don kar mutane su sani akwai ranar da ubangiji zai tona maka asiri duk daren daɗewa kuwa sai an sani!.
Maganar da Mumy ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta kai ziyara na ɗan daƙiƙu, da kuma zillon da zuciyarta take yi ta ji Mamy ta ce
"Zalika ki amsa min da bakin ki cewa mene ne wannan? " Mamy da gabaɗaya hawaye take kwaranyowa daga idanunta ta faɗa cike da tsananin damuwa Allah ne kaɗai ya san damuwa da firgicin da yake cikin ranta, sai take jin anya duk iya uƙubar da take ciki dangane da zaman aurenta ta taɓa jin raɗaɗin baƙinciki irin wannan ba, sai yau take jin makamancin raɗaɗin da uwa take ji dangane da abin da ya samu budurcin ƴarta, ta sha ji a rediyo ta sha ji a social media ana labarin an yi fyaɗe ga wasu ƴaƴan wasu ma ba ƴanmata ba ne wasu yara ne ƙanana masu ƙarancin shekaru amma ake samunwwasu mararsa imanin suna raba su da mutuncinsu, ashe haka kowace uwa take jin wannan raɗaɗin? Ta san da ciwo amma bata zaci ciwon har ya kai haka ba, ciwo ne mai tafe da rashin nutsuqar zuciya, duk da nata ciwon ya sha bamban da sauran ciqukan da sauran iyayen mata suke ji domin su sauran fyaɗe ne wato abu ne da ya faru da su ba da amincewar su ba, amma nata fa?
Nata abu ne ba tsautsayi ba hasali ma alamomi da dama sun tabbatar mata da cewa tata ƴar da amincewarta tun da ga shi har tana yawo da maganin tsarin iyali wanda bai dace a ganshi a wajen macen da bata da aure ba sai dai mace mai aure!.
Zalika tana jin tashin hankali ta yi ƙoƙarin dannewa tare da saita kanta don hakan ya bata damar linke mahaifiyarta ma,ana domin ta faɗa mata abubuwan da zai sa ta yarda da ita abin da ake kira wasa da hankali da tunani
Cikin sanyin murya ta ce
"Mamy mene ne ya sa za ki zubar da hawayenki a kan abin da ba gaskiya ba? Mai ya sa za ki shiga tashin hankali a kan abin da zargi ne? Wannan abubuwan fa gbaɗay zargi ne sannan yanayin yadda kika tunkareni da maganar ya sa na shiga cikin ruɗu" Mamy wani sashe na zuciyarta yana mata albishir da cewa duk abin da ta sanya a zuciyarta ba haka ba ne shaiɗan ne yake mata linzami, shi kuma wani sashen yana faɗa mata cewa Zalika rainin hankali take mata sannan ta yi hakan ne don ta yi wasa da hankalin ta.
Durƙusawa Zalika ta yi ta saka hannuwanta biyu ta dafe gwiwar Mamy ta yi raurau da idanunta ta ce
"Mamy ni ce fa Zalikar ki da kika yarda da ni, ni ce fa wacce kika bani tarbiya kika kula da motsina da dukkan komai na, a kan mai zan ci amanar wannan abubuwan da kika min a rayuwa? " Ta faɗa tana runtse idanunta hawaye suka zubo wani yana bin wani. Mamy kawai kallon fuskarta take ta rasa ma matakin da za ta saka wannan al,marin, amma dai ta dakatar da zucuyarta zuwa lokacin da za ta ji abin da za ta faɗa mata duk da zuciyarta tana gargaɗinta a kan kar ta yarda, don yanzu Zalika ta goge mata hadda ta sanya tana jin tsoronta.
Ta ci gaba da faɗjn
"Mamy akwai wata abokiyar karatuna matar aure ce sunanta Fatima Abdulƙadir to ita ce ta saka maganin nan a jakata ta manta da shi, ni kuma abin da ya sa na tsorata da kika nuna min saboda na san zai yi wuya ki fahjmce ni, amma dai ina kyakkyawan zato a kanki mahaifiyata na san ko da duniya za ta zargeni a kan aikata wani abu marar kyau, ke kaɗai ce za ki shaide ni yanzu Mamy idan baki bani shaida mai kyau ba waye zai miki shaidar Zalikar ki?" Ta faɗa tana ɗago kai ta saka idanunta da suke zubar hawaye ta saka a cikin na Mamy da take yi wa Zalika kallon da take son gane iya gaskiyarta.
Jin Mamy ba ta ce komai ba sai Zalika ta fahimci kalamanra suna tasiri a wajen Mamy duk da ba ta gama gansuwa cewa Mamyn za ta yarda da abin da take faɗa ɗin.
Ta ci gaba da faɗin
"Tana tafiya da maganin ne school saboda time ɗin shan maganin nata lokacin muna makaranta ne, ba ta so lokacin ya wuce ya zamana sai ta dawo daga makaranta za ta sha, shi ya sa take zuwa da shi tana ɓalla tana sha, yau da ta ɓalla shi ne ta saka a jakata lokacin muna sauri za mu shiga lacture ni kuma da muka fito sai na manta ita ɗin ma ina ga mantawar ta yi"
MAMAN AFRAH
09025576222
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 2️⃣8️⃣
MEENAL
Ihu take da iya ƙarfin ta tana ɗaga hannu kamar makauniya neman ɗauki take don a ƙwace kuɗin nan duk da ba halaliyarta na ne wato ba da guminta ta tara ba. Momi kuwa sai juyi take a tsakiyar hanyar gabaɗaya jikinta ya yi busu-busu da ƙasa ita ihun ma ba ta iyayi sosai saboda nauyin da bakinta ya mata.
Su duka kuka suke jina-jina domin sun doku sosai sai dai son zuciya bai bari kowacce daga cikinsu ta fahimci cewa alhakin wacce aka sacewa kuɗin ba ne da ta tara da gumin ta. Meenal tana yin wani juyi ta ce
"Momi sun gudu da kuɗin wayyo na shiga ukuna" Momi maimakon ta furta wata kalma kawai sai ta ɗaga hannuwa biyu tana kaɗawa tana yi wa Meenal zancen bebaye, wani takaici ne ya ƙara rufe Meenal ɗin ta ce
"Haba Momi yanzu duk wannan halin da muke ciki amma sai kike mini zancen kurame?"
Momi tana ɗan ƙoƙartawa wajen ganin ta tashi zaune saboda yadda jikinta yale tsananin ciwo tsabar dukan da ta ci, ganin tashin ba zai iyu ba ta buɗe bakinta da ya kumbura suntum saboda naushin da ya sha kamar ana saka ƙaton ƙuli-ƙuli daga cikin kumatun ta ce
"Haba Meenal baki ga yadda na daku ba kamar sakawara a turmi, wannan yara mararsa imani a ce ko tausayin shekaruna ba su ji ba suka nakaɗa mini na jaki... Shiru ta yi sai da ta ɗan huta saboda yadda take jin ciwo in tana mganar tamkar an saka gishiri a ciwo ta ce
"Ai tsakanina da su Allah ya isa!"
Meenal ta ce
"Haba Momi yanzu ta dukan da kika sha ma ke kike yi, bakya ta maƙudan kuɗin da suka ƙwace wanda ko bokan ba a kaiwa ba ya yi maganin, kuma sia magana kike kamar kin cika baki da abinci"
Tsaki Momi ta ja dakyar ta ce
"Wane shege ne ya ce miki ban damu da kuɗin ba amma ai lafiya ta fi komai, kuma da kike maganar na saka abinci a baki ba gwara in saka abinci sai dubu a bakin ba da wannan masifaffan dukan da na sha, baki ya kumbura suntum ai wannan sai na nemi mansileta" Ta faɗa tana ƙara bajewa a tsakiyar hanyar domin tana jin idan ba kama-kama aka mata ba to ita dai ba za ta iya tashi ba.
Meenal ta ce