Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 49

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 49

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 49: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 49. "Wato ni da nake da ikon a kan abincin ban isa na…

3,373 words

"Wato ni da nake da ikon a kan abincin ban isa na gindaya magana ba sai kin yi jayayya ko?" Ta yi raurau da ido na kissa ta ce

"Shikenan ni bani da kima da daraja a idanunka ka saka ƙannenka za au rainani, Husna ta ɗaga hannu ta mareni amma babu wani mataki da ka ɗauka sannan har naushina ta yi fa, ai da ƴar gwal aka taɓa Sadiya da tuni kana tada jijiyoin wuya, kuma wallahi bashi suka ci indai ni ce wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha mu zuba ni da su ɗan halak ka fasa!."

Nasir ya ce

"Mari ne kin yi an rama, to ya kuke so in yi da raina, kuma wallahi idan kika sake wani abu ya biyo baya ni da ke ne sannan ki saka mata ledar wannan su tafi"

Jin haka sai ta ƙara harzuƙa ta saki ledar tare da ɗaga hannu za ta wankawa Husna mari Husna ta yi saurin durƙushewa Meenal ta mari iska, shi kuma hakan ya yi daidia da hannunsa da ya miƙa ya cafe hannun Meenal. Baki sake take kallonsa tana tunanin wanna wace irin baƙar rana ce, lallai zama bai ganta ba dole ta tashi ta ƙwatarwa kanta ƴanci don ba za ta yarda ta zauna ba a haka a ce ana mulkarta ba wannan rayuwar ta tsarawa kanta ba. Yana riƙe da hannunta yake faɗin

"Idan kika sake kika mare ta wallahi daga yau na soke zuwansu miki girkin safe, yaran suna yi kansu da ƙafarsu amma kina raina musu" Jin ya faɗi haka ta gane zai aikata tun da ta ga take*tkensa ita kuma ta fi so a ce yanzu aka fara wasa wato idan har suka daina zuwa aiki komai zai canja domin za su tashi daga mulkarsu da takr sannan ba za ta ci gaba da samun damarmakin da yake fatan samu ba wanda za ta ambula musu ƙasa a ido su d uwarsu.

Baki ta dantse da haƙori ta ce.

"Ai abin bai kai haka ba, sannan karka manta ba fa ni kaɗai suke yi wa bautar ba har da kai sannan har da kansu da kuma mahaifiyarsu, kuma ai a ganina harshe da haƙori ma ana saɓawa a ci gaba da zama"

Bai tanka mata ba don ya matsu ya je ya ƙarawa wankansa Sadiya kuwa dama tuni ya kama gabanta, kallon su Hibba ya yi ya ce su yi tafiyarsu, sai dai Meenal ta ci alwashin rama abin da aka mata.

Ko da suka tafi a hanya suna ta maganar abin da ya faru, suna zuwa gida suka rattabawa Hajiya abin da ya faru tsabar haushi da takaici ta yi ta tsinewa Meenal har da uwarta ma. Sai dai da ta ji cewa Husna ta wanka wa Meenal mari sai ta ji da dama dama wai kibiya a ido amma dai tabbas ta lura yarinya ƙarama tana juya su, sannan ko da su

Hbbar suka ba ta labarin cewa Nasir ya shiga ɗakin Sadiya har ma yana mata faran faran sai ta nuna jin haushi har da cewa a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta!.

Meenal sai da ƙawarta ta zo gidanta washe gari sanann ta ari wayarta ta saka ta kira alajin ta da ya mata alƙwarin kuɗi don haka sai ta masa ƙorafin abin da ɓarayi suka yi na ƙwace kuɗi da kuma wayarsu. Ko da ya ji hakan sai ya ce idan zai yiwu ta zo su haɗu yau a hotel ta karɓi sabuwar waya dadal a kwali. Don haka tare suka fita da ƙawarta Safiyya ganin Nasir ba ya nan ya tafi kasuwa, sai da ta gama sheƙe ayarta ta dawo gidan amma kafin ma lokacin dawowarsa ya yi ta dawo, tana dawowa ta saka sabuwar wayarta a caji da sim ɗinta wani da take da shi a ajiye kafin ta yi welcome back na wancan.

Rashin ishashan kuɗi ya hana ta zuwa su koma wajen boka, ita da Momi sai dai hatta wayar ta faɗawa Nasir Momi ce ta siya mata don ba ta bari ya san ma an mata satar waya ba. Ganin yanzu adalci yana neman wanzuwa a gidan hakan ya sa ta ci alwashin tarwatsa duk wani abu da yake alaƙa da farincikin Sadiya a cikin gidan, don yanzu babu laifi suna samun kulawa ita da Kalifa saɓanin baya da ake nuna musu watiyar launin fata.

Ƙaryar da Meenal ta tsiro shi ne ta ringa zazzaɓin ƙarya ta amai, ko da ya ce ta je asibiti ta ce ba ta son zuwa Safiyya ta kawo mata tsinkena gwajin ciki da ake yi da fitsari wato PT wanda wata ƙawarsu ta auna tana da ciki domin kuwa ya nuna layi biyu ɓaro -ɓato. Shi ta yaudari Nasir da shi ta faɗa masa tana da ciki, abin mamaki sai ya ɗora rai a kan cikin yake ba ta kulawa tun da yanzu yana ƙoƙarin daidaita adalci. Meenal ta ci alwashin sai ta nunawa Sadiya ita ba kowa ba ce a wajen Nasir kamar yadda take a baya.

Babban abin da Meenal da Safiyya suka shirya shi ne daƙile duk wata soyayya da kulawa da Sadiyar take samu ba ta kowacce hanya ba sai ta hanya guda ɗaya wacce suke ganin idan har abin da suka shirya ya tafi daidai to tabbas Sadiya za ta tsinci talatar ta a laraba!.

Yau ya kama asabar a yau ne suka gama shirin aiwatar da komai hakan ya sa Meenal sanya idanu a dukkan motsin Sadiya domin kawo ƙarshen zamanta a gidan, sannan yau ya kasance ranar girkin Sadiyar. Yau ko da ya fita da wuri ya dawo saboda sun shirya za su je duba baban wani abokinsu hakan ya sa ya yi wa Sadiya sallama ya tafi. Sadiya tana zaune a ɗakinta sai ta tashi ta shiga banɗaki ta bar Kalifa a ɗakin yana bacci. A lokacin ne kuma Nasir ya kira Meenal yana tambayerta ya jiki sannan ta faɗa masa tana son ya taho mata da jan apple. Sadiya tana fitowa daga banɗaki ta shige ɗaki ita kuma Safiyya ƙawar Meenal tana can ƙofar gidan Sadiyar ta maƙale a jikin wata katanga, sai kuma Nasir wanda yake dab da ƙarasowa gidan.

Sadiya a bakin gado ta zauna, zamanta ke da wuya kenan tana ɗan hakin tafiyar da ta yi sai kawai ta ji Meenal ta ƙwala wani gigitaccen ƙara, Sadiya gabanta ne ya yanke ya faɗi domin abin da ya fara zuwa zuciyarta shi ne ko dai mciji ne ya sari Meenal ɗin ko dai wani abu mai kama da haka domin ƙara ya yi kama da na mai neman ɗauki da gaggawa. Gabanta ne ya faɗi ta taso tana ɗan tura cikinta, sai kuwa ta ji ta sake ƙaran a karo na biyu, sai kuma kiran sunan Sadiyar ya biyo bayan ƙaran da ta saki, Sadiya a kiɗime ta fito daga ɗakinta da zuciyarta ɗaya domin zuwa ta taimaka mata tun da dai ta san tun da her Meenal ta kira sunanta to tabbas tana neman taimako.

Kiran sunan Sadiya take hakan ya sa Sadiyar nufar ɗakinta a kiɗime. A ƙofar gida Safiyya da take laɓe ta hango motar Nasir ta shawo kwana da sauri ta fito daga maɓoyarta ta fara tafiya tamkar yanzu ta zo layjn take tafiya, yana ƙarasowa tana ɗaga ƙafarta za ta shiga gidansa ya fito suna gaisawa a daidai nan ne suka ji wani irin ƙara da Meenal ta saki, har rige rige suke wajen shiga gidan don ganin abin da yake faruwa.

A can cikin gidan kuwa bayan Sadiya ta nufi ɗakin Meenal tana zuwa sai ta ga Meenal kwance a kan kujera saman fuskarta ɗauke da filo sai jujjuya kai take tana ihu, da sauri Sadiyar ta ƙarasa wajen ta miƙa hannu za ta ɗauke filon kenan sai Meenal ta sake sakin wani ƙaran wanda ya yi daidai da shigowar Nasir da Safiyya wanda shi Nasir ko takalmi bai cire ba tsabar kiɗima da ruɗewa. Shigowarsu ya yi daidai da faɗin da Meenal take cewa

"Don Allah karki kasheni Sadiya wallahi indai Nasir ne zan bar miki shi, a yau zan bar gidan nan" Wannan furucin ne ya sanya Sadiya da ta miƙa hannu biyu kan filon da yake saman fuskar Meenal za ta ɗauke mata ta dakata gananta yana faɗuwa jin furucin ta, jikin Sadiya ne ya ɗauki karkarwa ganin Nasir da Safiya suna zarw ido suna faɗin

"Innalillahi wa inna ilahi raji,un" Da sauri Nasir ya ɗauke filon saman fuskar Meenal wacce ta haɗa uban gumi, har ture Sadiya ya yi lokacin da zai wuce sai a sannan Sadiya ta fahimci ta faɗa tarkon kishiya ba ta gama gane tuggu ba ne aka haɗa mata sai da Nasir ya ɗago filon ta ga ashe filon ra ne wanda yake kan gadonta nan da nan ƙwaƙwalwarta ta shiga tunanin ta yaya filonta ya zo ɗakin? Tana cikin wanann halin ta ji muryar Nasir yana faɗin

"Kisan kai Sadiya?"

Meenal da Safiyya juna suka rumgume suna fashewa da kukan kissa. Sadiya kai ta hau girgizawa ta rasa ma abin da za ta faɗa...

*Saura page 1 mu gama Book 1 dama na faɗa muku a page ,30 za mu gama book 1 sai kuma mu shiga book 2 wanda shi ne zai kaimu har ƙarshen labarin. Ga wanda yake da buƙatar book 2 naira ,500 zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222. Sai dai akwai turka turka akwai cakwakiya, faɗi tashi sadaukarwa haɗe da ƙalubale da kuma sakamako a book 2 sai dai wanda ya karanta har ƙarshe zai gane hakan kun san dai alƙalamin maman afrah ba ya rubuta shirme. Daga ɗari biyar babu ragi domin 700 ne sai na rage muku don a samu sauƙi idan na kammala book 2 800 ne*

https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1

*RUWA CIKIN COKALI*

(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*

*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*

*09025576222*

BOOK 1

PAGE 3️⃣0️⃣

*End of book 1*

SADIYA

Gabɗaya ta ma rasa wane tunanj za ta yi kanta ya kulle sannan mamaki haɗe da al,ajabi suka mata dirar mikiya lokaci guda, idanunta taf da hawaye take kallon yadda Meenal da Safiyya suke kuka wiwi bayan kuma ta san sharri ne aka ƙulla mata, tabbas ta yarda da kishiya mai makirce sai ta ɗaura maka sharrin da za ta sa ka yi gidan kaso!.

Furucin da Nasir ya yi ne ya ƙara hauhawar farashin tashin hankalin ta da ya ce

"Sadiya yanzu rashin imani har ya kai ki dannawa abokiyar zamanki filo za ki kashe ta? Ki tako tun daga ɗakinki ki biyo ta har ɗakin ta ribar mai za ki samu idan kin ida nufinki a kanta? Shin ke duniyar kika ƙauro?" Bakinta ne ya shiga karkarwa ita a rayuwa ko kaza ba ta jin za ta iya kashewa bare kuma ɗan adam ta yaya Nasir zai yi wannan furuci kenan shi har ya yarda, ɗagowa ta yi ta kalle shi yana riƙe da filon ta ga yafda fuskarsa ta sauya ya haɗe rai ɓacin rai tsantsa ya bayyana a tate da shi cikin sanyin murya ta ce

"Wallahi Abban Kalifa ban yi yinƙurin kisan kai ba ka yarda da ni" Ta faɗa cike da ɗari-ɗarin da ya sa ya ƙara zarginsa a kanta.

Cike da ɗaga murya yakr magana tamkat zai kai mata bugu ya ce

"Tun wuri Sadiya karki yi zaton zan yarda da wannan marairaicewar taki, wannan magana ba fa ƙarama ba ce babba ce magana ake ta kisan kai kuma ba faɗa mini aka yi ba da idona na ganki shin kuma wace magana za ki yi wane furuci za ki yi da zai sanya har na ƙaryata abin da idanuna suka gaskata?!.

Safiyya cikin muryar kukan kissa ganin Nasir ya hau keken ɓeran da suka ɗora shi ta ce

"Ni dama waya ta min ta ce min ba ta jin daɗi ashe dai rabon idanuna su yi mugun gani ne, Allah ya sa ma ka zo gidan wataƙila da babu namiji a kusa ta haɗa ni da Meenal ɗin mu baƙunci lahira" Kallon ki ji tsoron Allah Sadiya ta yi wa Safiyya kafin muryar Meenal ta karaɗe falon da faɗin

"Ni dama bacci ne ya ɗauke ni sai kiran Nasir ya tashe ni bayan mun gama wayar sai na ji idanuna suna rufewa alamar baccin ne bai isheni ba kawai sai na ji kamar daga sama an rufa min wani abu a fuska ina ta ƙoƙarin janyewa abu ya gagara numfashina ma babu wajen shaƙa don an fi danna abin a saitin hancina, Allah ya kawo ku kuka ceceni ni ban taɓa zaton ma mace ce ba wallahi na ɗauka namiji ne ashe dai mace ce macen ma Sadiya, shi ya sa bahaushe ya ce makashinki yana tare da kai" Ta faɗa hawaye suna tseren fitowa daga idanunta Safiyya ma tana taya ta.

Nasir kansa ne ya kulle ya fara jin wata tsanar Sadiya yana ganin zama da wanda zai iya kisan kai ba shi da wani amfani shi dama tun ba yau ba yake son yakice ta daga rayuwarsa kawai dai wannan uban nata ne yake maƙala masa ita sannan dai ya san kawai lokaci ne bai ƙare ba na zamansu tun da duk son ka da rabuwa da mutum in har zaman bai ƙare ba babu yadda za ka yi sannan idan har kana son zaman da mutum in zaman ya ƙare dole sai rabuwa ta gifta.

Sadiya ta ce

"Allah shi ne shaida kuma zai bayyana gaskiya" Gabaɗaya sai su Safiyya suka kalle ta tun da dai sun san babu wani da zai bada shaida a gidan tun da daga ita sai ita.

Ta ci gaba da cewa

"Ni ba zan iya kashe mutum ba kuma na san duk wani abu da mutum ya yi a ɓoye zai bayyana watarana, don Allah ba ya barin zalunci, sannan ni dai na san fitowa ta daga banɗaki kenan na koma ɗaki na ji Meenal tana ƙara tare da kiran sunana

, hankali tashe na taho don in taimaka mata, don ni duk tsakanina da mutum in har yana neman taimako zan taimaka masa duk da ba wata jituwa ce tsakanina da ita ba. Ina zuwa na same ta kwance da filo rufe a fuskarta tana jujjuya kai, da hanzari na nufe ta zan cire mata a lokacin ne ku kuma kuka zo, wallahi ni ban lura filona ba ne ma sai da kuka shigo" ,Ta faɗa tana share hawaye, Nasir ɗiff ya yi domin ƙwaƙwalwarsa ta karɓi caji ya rasa wane tunani zai yi duk da Sadiya tana maganar ne a rikice alamar har lokacin a tsorace take amma hakan bai hana shi gano ƙamshin gaskiya ba sai dai ya san an ce mata suna da tuggu da kuma kissa wannan ya sa ya kasa gane a ciki waye mai gaskiya Meenal ko Sadiya?.

Zama Meenal ta yi ta ce

"Lallai ɗan adam wato yanzu ni kike son ɗorawa laifi?" Ita ma da Nasir ya tsura mata ido sai ya ga babu shakka ko alamun rashin gaskiya hakan ya sa ya gane aikin sai mai shi wato shari,a sai sai al,ƙali.

Wuri ya samu ya zauna tare da dafe kansa ya rasa ta ina zai fara baka jin komai a falon sai sautin kukan Meenal da Safiyya.

Sadiya ce ta ɗaga hannu sama ta ce

"Ya Allah kai ne mafi ji da gani, kai ne sarkin sarakuna, iko da mulki naka ne, Allah kai kaɗai ka san mai gaskiya ya rabbi ka bayyna gaskiya ka wanke ni daga zargin da ake mini" Gaban Meenal ne ya buga da ƙarfi jin wannan addu,ar da Sadiya ta yi sai kuma ta raya a ranta cewa kawai dai Sadiyar tana faɗa ne amma dai ba ta da shaida.

Muryar Nasir ce ta katse da faɗin

"Wannan maganar ba ƙaramar magana ba ce tana buƙatar a saka manya a ciki" Jin wannan furucin nasa ya sa Meenal ta ji wani takaici ita ta so ya saki Sadiya a lokacin in ya so koma mai zai biyo baya ihu ne bayan hari, din haka sai ta yi tunanin wata dabarar ko hakan zai sa Sadiya ta amsa laifin hakan ya sa ta ce

"Ai dama babu wanda zai yi laifi ya ce shi ne ya yi, kuma wannan magana ba zan yarda ba sai na yi ƙara, domin yunƙurin kisa ba ƙaramin abu ba ne" Ta faɗi hakan ne ko Sadiya za ta saduda ta karɓi laifin dimin idan ta amsa laifin ta san Nasir zai fusata ya saki Sadiyar in ya so sai ta ce ta fasa ƙaran. Amma sai ta ga Sadiya dai tana kan bakanta.

Safiyya ta ce

"Wannan laifin dama ai sai an dangana shi ga hukuma don a yi hukunci saboda ƴan baya ma su hankalta" Waya Meenal ta ɗauka ta kira Momi tana labarta mata tana kuka duk da dama ta sanar da Momin abin da za ta aikata. Ba a ɗauki lokaci ba sai ga Momi a firgice ta shigo gidan saboda ta nuna ta firgita ta lamarin takalmi ma da ta zo zauren gidan tsayawa ta yi ta cire ta saka shi hagu a dama dama a hagu tana zuwa ta rungume Meenal tana hawayen kissa ta kalli Sadiya kallo na ƙasƙanci ta cr

"Ƴar tawa guda ɗaya to in har suniya kika so ta bari ba sai kin biyo ta haka ba, da kin faɗa ma cewa kina neman raba ta da ranta da tuni ta bar miki gidan, ba dai a kan namiji ne za ki yi kisan kai ba, ku mata sai shishshigi komai ku aikata a kan maza wasu mazan ma ba su damu da ku ba, to ni ina ƙaunarta iya kaɗai gareni sannan sai kin fuskanci hukunci domin ba za mu bar wannan maganar ba" Nasir sai haƙuri yake ba ta amma ko gaisuwarsa ba ta amsa ba tana ta masifa wai za a kashe mata ƴa bai ɗauki hukunci ba.

Sadiya tana ta rantse rantse amma kuma sai harara take samu da tukuicin masifar Momi.

An fito tsakar gidan Momi tana riƙe da hannun Meenal saboda ta ce ma ba ra jin ƙarfin jikin ta Momi ta ce

"Wannn cikin da kika samu ne ake miki hassada ba a so ki haihu a gidan wato sai ita ce za take haihuwa shi ya sa ta yi tunanin raba ki da duniya" Nasir dai ɗakin Sadiya ya nufa domin ya tabbatar da cewa filon natan ne suna tsaye a tsakar gidan sai Momi ta ce gabaɗaya za a shiga ɗakin Sadiya haka suka shiga yana gaba suna biye da shi sai dai da aka zo bedroom ɗin za a duba filon a tabbatar sai ga hula a tsakar ɗakin da sauri Nasir da ya ga hular ya ce

"Meenal wannan ba hular ki ba ce?" Ya tambaya domin ya gane hular tata ta net ce kuma da zai fita lokacin tana kwance hular tana kan ɗayar kujerar falon a ajiye ta ce ya miƙo mata ya karɓa ta saka a kanta wannan dalilin ya sa ya gane hular. Idanun kowa na ɗakin suka sauka a kan hular inda Meenal gabaɗaya ta rikice har ta kasa haɗa haruffan da za ta bashi amsa, amma saboda ƙarfin hali sai ta ce

"Lah hula ta ce" Ta faɗa da mamakin ganin hular tana mai miƙa hannu ta taɓo kanta, tana sake cewa

"Ikon Allah mai kuma ya kawo hulata ɗakin nan hular da tana kaina na yi bacci ɗazu" Momi ta yi karaf ta ce sato ta aka yi za a shirya miki wata maƙarƙashiya, wataƙila malami ne ya ce a kawo hular da take kanki zai yi wani aiki," Wani daɗi ne ya cika Meenal jin mahaifiyarta ta kawo mata haske, duk da gabanta ya faɗi da ganin hular kuma ta tsorata da lamarin, saboda ko kaɗan ba ta san hular ta faɗi daga kanta ba lokacjn da ta zo ɗaukan filon.

Safiyya ta ce

"Lallai maso abinka ya fika dibara, ban da ƙarfin hali ɓarawo da sallama hula a kankam a je a ɗauke kai zaman kishi sai ka shirya zama da kishiya gaskiya ba wasa ba ne"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull