Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 48
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 48: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 48. Umma tana nan yashe a kan tabarma, jin wayarta ba za…
3,360 words
Umma tana nan yashe a kan tabarma, jin wayarta ba za ta bari ta huta ba ta tashi tsaye za ta ɗakko wayar ta amsa, wani bugar jikin ƙofar gidan da aka yi hankali tashe Umma ta yi cikin ɗakin zaninta da ya suɓuce ya faɗo ko ta kansa ba ta bi ba haka ta yi cikin ɗaki daga ita sai ƙaramin siket da ake sakawa a ciki. Ko da ta shige ɗakin a guje ta banko ta saka sakata ta jimgina bayanta da jikin ƙofar tana numfarfashi. Tunanin ta ko Malam Kallan ne ya sake biyo ra har gida idan haka ne har ta fara tunanin yau sai dai bango ya tsage ta shige!.
Barar da almajirin ya fara rafkawa a tsakar gidan, shi ya ankarar da Umma almajiri ne ya bugi ƙofar. Wani wawan tsaki Umma ta ja tana mai tashi tsaye ta buɗe ƙofar ta fito tsakar gidan tana luƙawa almajirin zagi wai duk ya kasa bara a bakin ƙofa sai ya zo yana bugar ƙoga kamar za a yi yaƙi.
Susum almajirin ya fice daga gidan, ita kuma ta hau masifa tare da sunkuyawa ta ɗauki zaninta a fili tana cewa
"Wannan ai shashanci ne ka zo ka ruɗawa mutane ciki, dama ni da nake a ruɗe ka zo ka ƙara ruɗani nake tsere ni kaɗai a tsakar gida, har ina yada zani wallahi ka ɗauki alhakina" Ta faɗa tana ɗaukan zanin ta ɗaura, daidai na kiran ya sake shigowa a fusace ta ɗauki wayar don haushin Aliya take ji ba ta san irin rijiyar da ta tsallake ba, rijiya mai gaba miilyan ma ba gaba dubu ba. Ɗagawa ta yi sai kuwa ta ji Aliya tana faɗin
"Umma aka ce Malam Kalla na unguwar nan ya rasu, ina ta kiran ki in ce ki shirya rangaɗaɗau ki je ki ɗura masa aganin nan a hanci ko kakarmu ta yanke saƙ... Ba ta ƙarasa ba Umma ta ce
"Aliya na je gidan Malam kalla"
Aliya ba ta gama.jin ba,asi ba ta carara uwar guɗa don tunaninta aiki ya kammala. Umma kuma tsabar takaici sai ta kasa magana sai da ta gama guɗa da ife-ife ta ce
"Allah ne kaɗai ya aan karatun kurma Umma, a yau ba sai gobe ba zan nemi takardar saki a wajen Kasim, ni ba don mutane ƴan sanya ido ba da wallahi babu wata idda da zan zauna yi kawai sai in auri Ibrahim ɗin, don na ƙosa fara gasawa Jidda baƙar aya mai tsakuwa a tafin hannunta yanzu ne za mu nuna mata dama mu asalin maƙiyanta ne ƴar daular da ta afka ciki ce ta aanya mu ka sassauta tuƙin gangancin ƙiyayyar da muke yi wa rayuwarta...
Umma jin batutuwan da Aliya take ba su da alamar ƙarewa ita kuma ta san ba a zo wajen wannan maganar ba domin an samu saɓanin abin da ita Aliyar take zato, cike da muryar mai ɗankaren sanyi ta ce
"Aliya aiki fa bai kammalu ba, don na je har ɗakin gawar Malam Kalla amma wallahi magani dai bai samu shiga hancinsa ba... Tun Aliya ba ta gama jin komai ba hawaye suka yi wa fuskarta tsinke ba komai ne ma ya ɓata mata rai ba sai yadda Umma ta samu damar da ta yi wasa da damarta don ta ce har ɗakin gawar ta je kuma dai ta san bokanya ta bata maganin da za ta barbaɗawa mutanen gidan su sume kenan idan har kowa ya suma sannan ta shiga ɗaki mai ta tsaya yi ba ta aiwatar da aikin ba?. Cike da muryar kuka mai nuna tsantsar takaici da baƙinciki ta ce
"Haba Umma da kin san ba za ki iya ba wallahi da ni na yi, ni fa ɗazu Amatullahi ta kirani take ce min Malam Kalla ya mutu tsabar farincikin an samu sabuwar gawa ta namiji kuma a unguwar sai da na nuna jin daɗina da har Amatullahin ta kusa harbo jirgina domin ban faɗa mata aikin da za ki yi a kan gawa ba kin san ba komai ne kake kwashewa ka faɗawa mutum ba duk da ta san komai"
Umma maganganun Aliya sun sosa ƙoƙon ranta haka ta fara magana cike da masifa ta ce
"Aliya ni za ki cewa ba zan iya ba, ai da kin zo ke kin je kin zuba, da kin san irin rijiya da bayan da na tsallake wallahi da baki yi wannan furucin ba, ni da gawa ta riƙe min hannu da ƙafa muka ringa rigima da gawa" Ƙirjin Aliya ta dafe da hannu ɗaya tana zare ido a take ta ji tsoro ya baibaye ta ta ce
"Umma dama bai mutu ba ne? Mun shiga uku Umma kar dai asirinki ya tonu?"
Umma ta ce
"Ai shi ya sa ake aso mutum ya fara jin ba,asi kafin ya yanke hukunci, to da asirina ya tonu ai da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, wallahi ban san mai ya sa wannan gawar ta mini haka fa ke ƙarshe da na matsa sai na gudu haka na janyo gawar nan ƙiiii wallahi har bakin ƙofar gidan Aliya, amma yadda kika san ana saka mini maganaɗisu ko kuma a saman iska haka aka ɗagamu daga ni har gawar aka mayar da mu" Umma ta faɗa tana kwashe komai ta faɗa mata.
Tsoro duk ya mamaye Aliya ga shi Kasim bai dawo daga masallaci da ta fita ba sai ta ji gidan gabaɗaya ya mata girma, amma saboda zuciya marar kyau da kuma mugun ƙuduri wannan abin da Umma ta faɗa bai zame musu aya ba sai ta ce
"Amma ai da sauran maganin ko Umma?" ,
Umma ta ja tsaki ta ce
"Sai ki yi kuma Aliya, an ce miki muna ta fafatawa da gawa guntun na ledar ya kife iska ta ɗaga ledar ma ni ba zan ce ga inda ledar take ba to ana ta kai wa yake ta kaya? Wallahi da a ce ke ce kika ganki riƙe a hannun gawa kuma gida babu kowa ta riƙe ki gamgam har da su shaƙe wuyan hijabi da tuni kin suma" Aliya ta yi shiru tana jin ɓacin rai tare da tunanin shin mai ya sa ba ta da sa,a a rayuwa mai ta sa duk aikin da aka bada a yi a kan abubuwan da za su saisaita rayuwar ta sai an samu akasin lissafi sai komai ya rushe, kenan ita haka za ta dawwama a talauci Jidda a daula, Umma ba ta ankara ba ta ji Aliya da ƙarfi ta ce
"Ba zai yiwu ba, ba zai taɓa yiwuwa ba, akwai wanda yake saka mana hannu a aikin nan ina zargin Jidda ce in ba ita ba ya za a yi a ce duk abin da za a shirya a kanta ko kan mijinta abu ba ya yiwuwa in har ba saka hannunta ba ya za a yi a ce gawa ta yi motsi har ana kokawa wananna abin da sake kuma wallahi duk ranar da nufina ya cika sai ta wulaƙanta iya wulaƙanta a wajena" Ta faɗa tana rushewa da kukan baƙinciki.
Suna cikin wayar Abba da ya dawo saga masallaci ya yi sallama, da sauri ta ce
"To madalla Aliya ka gaishe da Kasim ɗin, to zai ji Abban naki ai ga shi nan ma ya shigo" Ta faɗa don ta ankarar da Aliya Abba ya dawo haka ta datse kiran tana ɗan wayincewa ta tattaro nutsuwarta amma gabanta yana faɗuwa game da Abba tana jiran ta ji kanun labarai shin Abban ya gano ta je gidan mutuwar ko kuwa kowa ma ya sani tun da ba ta san yadda aka ƙarƙe ba.
Ganin jikinsa sanyi ƙalau tun kafin ya ƙarasa zama ta ce
"Kai Allah sarki Malam Kalla lokaci ya yi!" Ta faɗa cike da jimantawa, ya gama zama ya ce
"Wallahi ke dai bari Lubabatu na ji mutuwar bawan Allahn nan, duniya ba matabbata ba, watarana mu ma haka tamu mutuwar za ta risƙemu" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke jin babu wani batu bayan na mutuwa hakan ya sa ta zage suka ci gaba da jajantawa. Ko da dare ya yi ta zo kwanciya sai tsoro ya mamaye mata zuciya daga ta rufe ido sai take ganin kamar gawar za ta zo mata haka ta kwana idanu a buɗe don ba ta so ta rufe idanun sai take hangar gawar kamar ta zo gidan, haka ta kwana a firgice.
Da safe sa ciwon cikin ƙarya ta tashi amma tana ta nuna za ta tafi sutura Abba ya ce tun da ba ta da lafiya ta zauna, daɗi ya cika ranta don ita ba ta so ma ta je suturar gawar da ba ta da tabbacin ta mutu. Ko da Abba ya tafi suturar ya dawo haka ta ce
"Oh duniya ba tabbas har an binne shi ko, rayuwa kenan, yanzu mutum an jima gawa rayuwa kenan, duniya kenan yau kana tafiya a saman ƙasa watarana kuma kana ƙarƙashin ƙasa"
Abba ya ce
"Bari ke dai ai muna rayuwa ba mu san rana da lokacin mutuwarmu ba bare yanzu da ake yawan mutuwar nan ta bagatatan mutuwar fuju,a yanzu za ka rabu da mutum an jima ka ji an ce babu shi" Umma dai ba ta ji amsar tambayarta ba hakan ya sa ta ce
"Wallahi kuwa Allah sarki marigayi Malam Kalla su tasu ta ƙare saura tamu tun da sun shiga kabari"
Abba ya ce
"Kai ina tsoron mutuwa ranar da zan ganni ga ni ga mala,ika, ranar da za a saka ni a kabari ranar da zan ganni a cikin kabari, ya Allah ka rabamu da duhu da azabar kabari da nauyin ƙasa"
Umma ta takarkare ta ce
"Amin" Amma duk ranta ya ɓaci ita so take ya ce an binne shi don tana tsoron ya faɗi abin da ya faru tun da tana ganin bai mutu ba. Har ta yi shiru sai ta ce
"Ko ba a yi suturar ba ne"
Abba ya ce
"Haba ke kuwa sutura ta nawa kuma tuni ma da an dawo mai zai dawo da ni gida in ba a kai shi makwancinsa ba, dama dawowa na yi idan na karya sai na koma idan na ɗan jima wajen karɓar makokin sai na dawo na shirya na tafi kasuwa"
Umma ta ce
"Haka ne" Ta faɗa tana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya.
Aliya kuwa tun da ta ji bayanin da Umma ta mata ta gane cewa Abba ne ya dawo, Umma tana datse kiran wayar ta ajiye kawai take kuka wiwi don rashin cikar burinta kuma tana tunanin yadda za a samu wani kuɗin aikin.
Ko da Kasim ya dawo sai da ya fahimci ta sauya amma sai ta nuna masa kanta ne yake ciwo shi kansa haushinsa take ji ta gaji da sakar masa fuskar da take ta gaji da nuna masa tana zaune da shi ne da zuciya ɗaya, bai san cewa da wata manufa take zaune ba burinta yana cika zaman gidansa ya ƙara don ta fi ƙardin zaman aure da talaka, talakan ma mata -maza. Ko wayar ta da ya gani sabuwar ta nuna masa Jidda ce ta saya mata duk da ta fahimci bai ji daɗi ba amma haka ta make abinta tun da ta san shi dai koyaushe cikin fafutukar na abin da za a rufawa kai asiri yake ita ba ta taɓa hango masa zai taka matakin masu arziƙi ba duk da an ce arziƙi kashi ne amma ita ba ta hango arziƙi a tare da wannan mata mazan ba gani take a haka zai ƙare ita kuma ta fi ƙarfin zama da shi yadda take kyakkawa ajin farko da gidan daula ta dace, gidan daular ma ba kowane iri ba.
Bayan nan suka ringa waya da Umma saboda tana tsoron ta je gidan su haɗu da Abba saboda ba ua son yawan zuwa gida babu dalili, shi yawo ba ya yi wa mace kyau a wajensa a ce yau tana can gobe tana can ko da budurwa ce kuwa bare matar aure, ya tsani fita babu dalili. Haka dai suka shirya suka je wajen bokanya don sanar da ita abin da ya faru. Ko da suka je bokanya ta ɗauka za su faɗi kyakkyawan labari amma sai ta ji saɓanin haka, mamaki ya kamata hakan ya sa ta yi wani surkulle ta ɗakko wani ganye tana karkaɗawa tana ambaton wani suna, zuwa can sai suka ji magana ta karaɗe ɗakin ana cewa
"Ya ke bokanya mai kike buƙata a aiwatar miki?" Bokanya ta ce
"Ina so sanin dalilin da ya sa gawar da za a sakawa maganin da na bayar ta motsa har ta riƙe wacce za ta yi aikin"
Mai maganar bisa muryar tsoro ya sheƙe da wata dariyar da har sai da su Umma suka razana sai da dariyar ta lafa ya ce
"Akwai wani abokin aikin ki boka Naladidi wanda sa,insa ta shiga tsakaninku a watan da ya wuce har ya ci alwashin sai ya ɓata miji duk wani aiki to shi ne yake kan bakansa, shi ne ya yi komai" Cike da rashin fahimta ta ce
"Mai ya yi"
Muryar ta ci gaba da cewa
"Ya aika aljani ɗan ƙundalo ya je ya ture Daddyn Ibrahim ɗin da kika yi wa asiri a cokali, shi ne aka kira Ibrahim ɗin aka sanar da shi a lokacin da zai ci abinci wannan dalilin ya sa bai ci abincin da cokalin ba bare har aikin ya ci, sannan shi ya aika aljani gidan gawar Malam Kalla, aljanin ya ɗauke gawar mamacin ya kwanta a wajen da aka ajiye mamacin bayan ya sauya kamanni irin na mamacin ai ba gawar ba ce aka yi ƙoƙarin sakawa maganin ba aljanin ne, da shi suka yi kokawar har sai da ya ga komai bai yi ba a aikin sannan ya koma ya sanar da bokan cewa ya cika aiki hakan ya sa ya ƙara cin alwashin duk aikin da za ki yi sai ya san yadda ya yi ya ɓata aikin bai yiwu ba" Tun da ya fara bayani jikin Umma yake karkarwa musamman idan ta tuna cewa wai da aljani ta yi fafutuka jiya ashe aljani ne ta ja hat zaure duk sai ta ji tsoro ya baibaye ta a ganinta har gwara gawa mutum ce a kan aljani. A neman duniya za ta je ta yi abin da aljannun ma za su ɗauke ta a banza.
Daga haka bokanya ta sallami aljanin da ya mata bayani don har wasu ayyukan da ta yi wa mitane aka samu akasi sai da ya faɗa mata dalili duk aikin bokan Naladidi ne. Tsaye ra miƙe rai a ɓace tana surutai da cin alwashi a kan bokan, nan ta ce idan su Umma sun samo kuɗi su dawo za ta musu maganin da ba a isa a saka hannu ba, don ta ce gabaɗaya wwaɗancan maganin da ta musu duk da an nuna matsalar rashin dacewar aikin daga gare ta ne amma ba za ta musu wani maganin ba sai sun sake biya shi ne Umma ta faɗa mata babu kuɗi sai ta ce su je in sun samo kuɗaɗe masu nauyi su dawo haka suka taho jiki babu ƙwari a hanya Umma ta ce
"Oh ni Lubabatu yanzu ashe da aljani na fafata, ashe ɗauke gawar aka yi kenan da na tafi sai aljanin ya dawo da gawar kai jama,a lallai sai a bar aikin aljannu, ai ni dai na daddara da aikin matar nan"
Aliya ta ce
",Kenan Umma sai dai na haƙura sa cikar burin nawa?"
Umma tw ce
"Sai dai idan an samu kuɗin mu tuntuɓi wani wajen don wallahi ba zan ke zuwa muna danbarwa da aljannu ba wataran ma su ji haushi su ɗauke i su kaini matattararsu, tun da ni da naci in ce sai na yi aikin ko na gawar ma ba nacewa na yi ba kin ga da akwai tsautsyi sai aljanin ya ɗaukeni, amma ni dai tun da bokanya tana da abokin adawa suna faɗa mu cire kanmu daga zuwa wajenta"
MEENAL
Kafin ta sauke hannunta Husna ta ɗaga nata hannun ta kifa mata marin duk da abin ya zo mata a bazata amma sai ta dake ta dafe kunci da hannu tana rushewa da kuka, zuwan Nasir sai ya kasa fahimtar mene ne tun da ya ga an yi kuma Meenal ya ga an mara sai dai marin da Husna ta yi wa Meenal a kan idanunsa da na Sadiya, sai dai ita Sadiya kasancewar a gaba take ta ga marin da Meenal ɗin ta zabgawa Hibba. Meenal kunci ta dafe da hannu ɗaya ɗayan tana riƙe da ledar dankalin amma kuma yana dafe a cikinta.Tana rayawa a ranta cewa Husna ta taɓo gidan rina din sai ta mata sharrin da ba za ta fitar da kanta ba tun da har ta iya saka hannu ta mare ta, Nasir kuma yana mamakin faruwar abin don ya san dai ya ji an ambaci ɓarayi kuma ya fito ya ga saɓanin abin da kunnuwansa suka ji. Don haka bai tambayai ba a si ba sai ya ce
"Husna mene ne hakan? Matata kike mari a cikin gidana?" Husna da Hibba sun buɗe baki za su yi magana sai Meenal ta ce
"Darling wai fa kawai don na ce ihu ɓarayi shi ne ta naushe ni a ciki kuma ta mareni, dama tun ranar nan suke cewa ban isa in haihu a gidan nan ba tun da dai har na saka kake sakawa suna zuwa suna mini aiki" Baki suka saki jin wata kissar da ta musu sannan a yanayin yadda suka ga ya nuna a fuskarsa kamar dai ya yarda da maganganunta, sai dai kafin ya yi magana sai Sadiya ta ce
"Ya kamata ka fara tambayar abin da ya faru kafin ka ɗorawa ɓangare ɗaya laifi ka fara yin bincike domun tabbatar da abin da idanunka ba su gani ba karka yanke hukunci da abin da idanunka suka gani...
Tun kafin ta kai aya Meenal ta ce
"Malama tun da ba da ke ake ba ki yi shiru mana kuma ai zuwa da kai ya fi saƙo sannan gani ya kori ji shi da idanunsa suka ga abin da ya faru tamabayar mai zai yi"
Nasir shu takaicinsa ɗaya ma da suka saka ya fito da kuma a jikinsa ko wanka bai gama ba, shi ua rasa wannan wace irin rayuwa cw kuma wace irin cakwakiya ce a ce kullum sai sun zo nan za su dafa abin da za su ci hakan ya sa ya ce
"Meenal mai ya sa kika musu ihun ɓarayi?"
Meenal duk da ta ji haushin tambayar ganjn kamar ma ita yake son ɗorawa laifi sai ta ɗago masa ledar ta ce
"Dankali Hibba ta sata suka saka aljihu shi ne Allah ya toni asiri su na gani"
Hibba sai ta ji duk kunya ta kamata shi kuma sai ya ma rasa abin cewa sai Husna ta ce
"Yaya dankalin ne fa takr bamu kaɗan ba ya isarmu kullum sai dai mu yi kashi kamat wasu mararsa galihu, shi ne muka ƙara yawan dankalin da muka soya muka kwasa yadda zai ishemu" Ya ɗanyi shiru ya ce
"Kuma sai ku ɗauka bakwa cewa ta ƙara muju wanda take baku ba ya isa"
Hibba ta ce
"Ka ga fa ɗan wanda take bayarwa bai fi cikin mutum ɗaya ba"
Ganin dankali ransa ya ɓaci kamar wanda aka roƙa ganin yana neman yarda da maganrsu Mrenal ta ce
"Ƙarya suke munafukai ne wallahi a kicin suke tsayawa su cin iya cinsu sai su kai ɗan kaɗan gida, amma ya za a yi na zuba musu wannan" ,Gabaɗaya ma sai ya rasa maganst wa zai ɗauka su kuma su Hibba suna mamakin sharrin da take ƙullawa da kuma tsabar iya kissa.
Ɗan jim kawai ya yi ya ce
"Bani dankalin na ledar" Miƙa masa Meenal ta yi sai ya miƙawa Husna ya ce
"Gashi nan ku juye a cikin wannan ɗin ku je ku tafi gida"
Meenal ta doka uban tsallw tana masifa da kumfar bakin ya goyi bayan ƴan uwansa ta kama ledar hannun Husna ta riƙe ta ce babu wanda ya isa ya fita da dankalin daga gidan tun sa ita ba ta basu ba.
Nasir ya ce