Kenza eBookz

Sakon so complete Novel - Chapter 12

Sakon so complete Novel - Chapter 12

Sakon so complete Novel Chapter 12: Sakon so complete Novel Chapter 12. 7 daidai Abee ya shigo gidan saida ya gaida Hajiya sannan yataho sama dakinshi…

2,859 words

7 daidai Abee ya shigo gidan saida ya gaida Hajiya sannan yataho sama dakinshi yawuce batare daya kalli daidai da kofar dakinta ba sake wanka yayi yashirya cikin wani black suit na italian yasa black takalmi sai kamshi yake yafito rikeda wayanshi a hannu harya wuce kofan dakinta kaman wanda yatuna wani abu yadawo wannan karan bai knocking ba yabude dakin zaune yaganta kan dadduma sanye da milk hijab tadaura kanta akan gado tana bacci, daganan kofa yakirata. “Kee!” Firgigit tabude idanunta kaman taji muryan mala’ika mikewa tayi zumbur hakan yasa towel dinta yay kasa hijabin yawani kama jikinta dayasa zaka iya ganin komi dauke kai Abee yayi saikawai yajuya yafita batare dayace mata komiba. Kokarin hawa gado tayi ta kwanta but jin fatar jikinta kaman ma danko danko yake mata yasa tacire hijabin tawuce bayi, da ruwan sanyin hakanan tai wanka dawani sabon soso da shower gel datagani abayin mai kamshin dadi sai ihu take tana sauke ajiyan zuciya sabida sanyin ruwan, daura towel tayi tafito har rawan sanyi takeyi sosai tawuce takashe AC sannan taje gaban madubi wani cream datagani awajen na QEI tadauka tabude dan shima sabone tashiga shafawa sabida sanyin ya barta gama shafa man tayi ganin taki daina jin sanyi yasa takoma bayin tacire towel din ta wurga washing machine datagani abayin tadauko wani towel din tadaura tafito, zama tayi jin sosai takejin sanyi yasa tasake mikewa tai wajen gadon tashiga gyarawa sabida tadainajin sanyin daidai tana gama gyaran ana sallama tareda bude kofan dakin hakan yasa da sauri takalli kofan da kodaddun idanunta dasunsha kuka Anty Samira ne tace “gyaran gado kikeyi Lujain”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali tace “ina kwana”? Murmushi sosai Anty Binta tayi tace “muntashi lafiya ya Kwanan sabon waje”? Shiru Lujain tamata batare dabata amsaba karban bargon hannunta Anty Binta tayi tace “kawo natayaki ninkewa naga yamiki nauyi kaman ma kin wanka ko”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali, Anty Binta tace “to je saka kaya duk suna cikin wardobe atampopinki ma yau tela zatazo ta aunaki, yi maza sa kayan musauka kasa”? Gyadamata kai tayi hankalinta na kara kwantawa wannan datace su sauka kasa that means zata kaita gida kenan, wardrobe din tabude dogon rigan da hannunta yafara tabawa tadauka wani nakine amman yanada gold stone dake sparkling, dan juyawa tayi tadan kalli Anty Sam ganin hankalinta gabaki daya nakan bargon datake gyarawa akan gado yasa ta dauki cotton pant data gani awajen Babba aka sayo da kananu babban tadauka tasaka yamata cip tasaka underskirt, sannan tazare towel din ta ijiye tajuyama Anty Samira baya tadau wani white singlet tasaka daya kamata bam dan ko kadan batason tasaka bra tadauki rigan tasaka dayawani haskata da kaman dan ita akayi, dan kwalin abayan tadauka zata yafa dasauri Anty Sam data gama tana kallonta tace “noo kifara gyara gashinki” dan zaro idanu tayi ahankali tace “ban iyayi ba Gwaggo ke mini” yanda tai maganan saida Anty Binta tai murmushi ganin yarinyar nada shagwaba komi nata ashagwabe takeyi dan yamabi jikinta tace “zauna kiga” zama tayi akujeran gaban dressing Anty Binta tacire ribbon din tana kallon tsayin gashinta sannan tadauki man kitso tashafa mata tareda tsage gaban kan sannan ta tajemata ahankali tai parking gashin dayawani kwanta tai parking tsaf tana kallon fuskanta tagaban madubi tace “idanunki sun kode da yawa sa kwalli saimu sauka muyi breakfsat ana jiranmu” kwallin tadauka tasaka ahankali sai idanun sukai kaman na aljanna gyalen Anty Binta ta karba tayafa mata aka sannan tace “tashi mujeto” tashi tayi Anty Binta tai gaba tana biyeda ita abaya suka fice daga dakin sukai stairs kanta akasa, kowa na nan, Hajiya na zaune tasanya wata atampa blue mai kyau, sai Abee dake zaune kan one sitter dake facing stairs din, sai Kausar na zaune akasa wajen kafanshi rikeda littafi da byro a hannunta tana rubutu, sai Abdallah yana zaune kusada Hamza da Ibro duk suna kallon stairs din sai Sajida da Zainab da Maman Aneesarh duk suna zaune suma tareda matan Ibro ga yara akasa suna zazzaune, kallo daya tama falon da mutanen ciki tasauke kanta kasa hakanan kawai gabanta nafadi dum dum dum, ko Anty Binta ta lurada hakan ne kamo hannunta tayi suka karasa sauka kasa har zuwa gaban Hajiya tace “ga Maman mu nan gabadaya dudda jiya dakika ganta kinata kuka but itane Maman Mu Hajiya Babba dakanta” dakuwa Hajiya tama Binta tace “kinci gidanku Binta” sannan takalli Lujain da kanta ke kasa tace “Mun tashi lpy Lujain” Gyadamata kai Lujain tayi ahankali murya chan kasa tareda dan dukawa kaman yanda take gaida Baba tace “ina kwana Hajiya” murmushi Hajiya tayi tace “lafiya lau, to har yanzu boyemana fuskan akeyi ne” kara noke fuskanta tayi kasa, kusada ita Hajiya ta nuna mata tace “zoki zauna to” kasa zama tayi kusada Hajiya ahankali ta zauna akasa kaman zata fashe da kuka daidai nan Aneesarh dake wasa akasa tawani rarrafo dagudu zuwa jikinta tana kokarin magana na yara tana kallon fuskan Lujain din kaman yanda yara keyi irin taga bakuwan fuskan nan sai kowa na dakin ya tsaya yana kallonsu, ware idanu Lujain tayi for the first time dawani kalan sauri tasa hannunta tadauki Aneesarh ahankali tace “Fine babyyy” washe baki Aneesarh tayi tana dariya tanajan gyalenta ahankali gyalen abayan ya zame kasa gashinta da Anty Binta ta gyara mata yawani bayyana for the first time Lujain tawani saki murmushin dayasa dimples nata duka biyun suka lotsa ganin yanda Aneesarh keja mata gyale daidai lokacin Abee yadan kallesu.EPISODE 2️⃣0️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Breakfast aka fara kawowa cikin falon dan Hajiya tace ita barata dinning ba, Maman Aneesarh tace “Aneesarh taho kisha cerelac dinki kibar Anty Lujain tayi breakfast” sauka daga jikin Lujain Aneesarh tayi ahankali mikewa tayi kaman zataje wajen Mamanta saikuma da gudu tai wajen Abee zatahau jikinshi takasa, daukanta yayi ahankali yana kallon fuskanta ahankali yace “you don’t want to eat”? Gyadamai kai tayi da sauri tana kallon Coffee dayake sha, dan murmushi yayi yakai bakinta kurba tayi kadan jin daci yasa ta tabe baki tasauka daga jikinshi tawuce wajen Mamanta.

Lujain na zaune inda take akasa atisha yazo mata hannunta takai kan fuskanta tayi tanajan hancinta saiga nabiyu yazomata shima tayi tace “Alhamdulillah” na uku na zuwa, Hajiya tace “sannu Lujain” na hudu ne yazomata shima tayi dayasa kowa ya kalleta banda Abee dake kokarin kurban coffee shi, Hajiya tace “kin kwana da AC ne Lujain”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali, hakan yasa Hajiya tace “bata farfesu da shayi tasha Binta, sannu mura keson kamata” shayi Anty Binta tahada mata mai kayan kamshi, bala’in yunwa takeji jikinta har rawa yasoma ganin shayi, Anty Binta nagamawa dasauri tadauki cup nashayin takai bakinta ta kurba wani kalan zafi dataji yasa batasan lokacin datasaki cup dinba shayin sai cinyanta wani kalan ihu ta kurma dayasa har Abee saida ya kalleta. “Wayyoooo Allah na zafi, Gwaggo” tai maganan tana kokarin kwaye doguwan rigan sama tana yarfe hannu tana kuka, Hajiya tace “daga gani bata sabashan shayi mai zafin nan ba Subhanallahi sannu ya isa daina kuka” Anty Binta ganin shirin dage rigan take yasa takai hannunta ta taba inda shayin yazuban mata tace “sannu sannu, jeki cire kayan zan biyoki da breakfsat din sama” Gyadamata kai tayi tana share hawayen daya zubomata tawuce sama da sauri tana tafiya ahankali su Sajida suka bita da harara, Anty Binta tashiga hada mata breakfsat nata a tray tace “Kausar zo dauka ki kaimata” dan turobaki tayi sannan ta tashi ahankali tazo tadauka tawuce sama daidai Abee ya mike yakalli Hajiya yace “natafi Hajiya” ahankali tace “tom Allah bada sa’a Imran” wucewa yayi yafita daga dakin suma su Hamza da Abdallah suka fice daga falon Sajida da kaman jira take su fice tace “tsakani ga Allah wlh da auren wannan yarinyar kaman buhu gwara rashin aurenta, wanan shirmen za’a bama Ya Imran a matsayin mata ai wlh ancuceshi haba mana” Zainab tace “mugun an cuceshi ma bakiga ko kallo bata isheshi ba, yarinya banda haske babu abinda ya ceceta sai shegen kiba, taga shayi jikinta har rawa yake sabida son abinci” Matar Ibro ne dake wajen tace “wlh irin kibar yarintan nan ne, nima akwai kanwata Ummie haka tun tana karama takeda irin wannan kiban kaman ana hurata tashi daya kuma ta zazzage kiban tass kaman ba itaba itama zata rame ne, kwanan nan ma tunda duk damuwa yamata yawa” cikeda kulewa Sajida tace “ba wannan ake magana ba kekuma Matar Ibro mu bama sonta amatsayin Matar Ya Imran ne, mezaiyi da yarinyar da Kausar ta girma wannan ba cuta bane” daidai nan Kausar tasauko tace “ni wlh na tsaneta Allah ya kyauta Abee dina yay rayuwa da wacce na girma amatsayin mat…..” wani mugun kallo da Hajiya tama Kausar yasa takarasa maganan tace ”zoki saka Hijabinki kibar gidan nan kitafi makaranta nasan Hamza na mota yana jiranki” ba musu ta taho hijabi ta dauka da jakanta tafice Hajiya takalli su Sajida tace “kuzo kubarmini gida babu ruwanku da yarinyar nan, babu abinda ya shafeku da ita dan haka ku kiyayeta, bansonjin wani yakara maganan ta agidan nan, ban yarda kuci zalinta ko zarafinta ba, babu ruwanku tsakaninta da mijinta Imrana shine mai ita shine mai iko da ita, koni ba zamana takeba zaman mijinta take agidan nan, koba komi I expect dukanku ku girmamata amatsayinta na Matar yayanku dan haka ku kiyaye” duk shiru sukayi Hajiya tamike tawuce dakintaEPISODE 2️⃣1️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Abee na zaune a office nashi wuraren 2:30 aka tura kofan office dinshi batare da anyi knocking ba aka shigo dago kanshi yayi kallo daya yama Musty dake sanye da manyan kaya yana kalllonshi yana wani makirin murmushi yadauke kai yacigaba da abinda yakeyi, maida kofan Musty yayi yarufe yakaraso gaban table yace “Ango Ango kai kaga wani glowing dakakeyi ne irin na amarcin nan” dan dariya yayi ganin ko kallonshi Abee baiyiba Musty yace “no bama wannan ba tell me everything about the first night” wani mugun kallo da Abee yamai yasa yawani kalan kyalkyace da dariya yace “inda kallo na kisa da yanzu idanunka sun kasheni yafi sau dari” dauke kanshi Abee yayi yacigaba da duba papers din dake hannunshi yace “idan abinda yakawoka wajena kayi kenan kabarmin office please” hadiye dariyan Musty yayi yakalli Abee yace “to ka ijiye takardun ka kallen mana muyi magana” dan ijiyan zuciya Abee ya sauke ya ijiye takardun ahankali yakalleshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda tsokana Musty yace “yaushe zaka komarda Amarya gidanka? Kasan gidan Hajiya bazai barka kai amarci da kyau bako”? Akufule Abee yatashi pappers din yashiga tattarewa yabar wajen yakoma kan lumtsetsen couch na office din yazauna ahankali yacigaba da abinda yakeyi anatse shikuma Musty yana zaune inda yake yana kallonshi yakai kusan 10min sannan yatashi shima yazo yazauna kusadashi batare da Abee yakalleshi ba yace “zan barmaka office din gabaki daya fa Mustafa” murmushi Abee yayi yace “nasan zaka iya, all jokes apart magana nazo muyi Imran look at me” yanda yay sounding serious yasa Abee yadago idanuwanshi ahankali yakalleshi alamun ina jinka. Ahankali Musty yace “Nasanka to be someone da kana taimako kana tsayama wayanda bama kasansu ba kabi musu hakkinsu ka kwace yancinsu, yaran dakai sponsoring education nasu bansan iya adadinsu ba saisa yauma is still on that matter nakeso nida kai muyi maganan fahimta best friend” shiru Abee yayi still yana kallonshi anatse Musty yace “I know bakason auren nan and you don’t consider this girl your wife” daukekai Abee yayi hakan yasa dasauri Musty yace “hear me out mana Imran bawai inaso nace you should consider her matarka bane wlh ko daya I accept that take as long as u want kafin kai accepting nata kokarkayi accepting nata ni duk dayane awurina but as your friend reminder na musulunci nazo namaka” shiru Musty yakarayi sannan yakalli Abee yace “I know you better than anyone nasan yanda kake idan bakason abu yanda kake wulakanta abin, banso kama dat small innocent girl that kind of treatment Imran, bance kai accepting nataba as your wife but inaso ya zamto ka kiyaye hakkokinta na musulunci, lafiya, ci, sha, sutura and respect, duk kabata kaga idan ka wulakanta yarinyar nan and neglect her mutanen gidanku kap haka zasu mata suma, remember bata tareda dan uwanta ko daya, remember kaman yanda su Kausar basuda mama itama batadashi su Kausar sunma fita gata in the sense sunsan mahaifiyarsu banda haka kaga ga all your sisters and family sun taso cikinsu itako has only her grandma! Just grandma, inaso kajata ajiki be nice to her please Imran, saikuma second abu dazan fadamaka is school idan all this issue yakara sanyi saika nemi wani good school kasata since school datake sun koreta saita fara wani sabo mai kyau kaji Imran that’s the only abu da dama zan maka magana akai kaji”? Dan dauke kai Abee yayi kaman bazaiyi magana ba saikuma chan yace “naji” murmushi Musty yayi yace “to hurry ka karasa abin nan gashichan ana kiran salla muje muyi saimu wuce gida”. **

Koda takoma daki kayan tacire tashiga bayi tana wanke kafanta wajen dan ja yayi dan bawani konewan kirki bane towel ta daura tafito tana kallon kulan abinci da tray shayi dataga an kawo mata dabatasan waya kawoba, zama tayi tahada shayin dakanta ta shanye tass sanan tacinye duka chips da egg dake kulan ta shanye farfesun shima tass rabonta da abinci tun jiya hawa gado tayi ahankali sai bacci koda Anty Binta tashigo ganinta kwance kan gado da towel yasa ta murmushi ta kwashe kayan abincin tafita, wajajen azahar ta tashi tashiga bayi da ruwan sanyin still takara wanka tafito tana atishawa hijabi tasa tai salla sannan tazauna kawai tai shiruu tana kallon dakin, duniyan kawai yamata ba dadi, komi ya tsayamata chak, gidan yamata wani kala kawai sai hawaye sosai tayi kuka jin ana taba kofanta ana magana yasa tashare hawayenta da gudu, Anty Binta ne tashigo tareda wata mata kallo daya Anty Binta tamata tagane tai kuka amman tai kaman bata saniba tace “anzo aunaki tashi to” tashi tayi ba musu matan ta aunata tsaf sannan suka fice itada Anty Binta chan saiga abinci wata Yar aiki takawo mata dauke kai tayi wasu hawayen sun sake zubomata that means bara’akaita gidansu ba kenan, tsanan abincin taji tayi jin ana kiran la’asar yasa tawuce bayi tadauro alwala tazo tai salla, jin dakin yamata wani kala sotake tama danga hasken rana babu yasa ahankali ta tashi tai wajen window ta yaye labulen tareda bude window wani kalan iska ne yabuge fuskanta ahankali tasauke ijiyan zuciya tadade tsaye wajen sannan tajuyo akwatin da aka kawo mata tai wajensu tabude duka, robobin daddakkun magungunan ne daban daban da sauri ta maida tarufe dan barata shaba magungunan nan da badadi dayan tabude ganin su chocholate minti biscuits da yogurt daya cika akwatin yasa batasan lokacin datai murmushi ba tawani fashe da kukaba takifa kanta kan kafa ahankali tace “Gwagooooooo” sosai take kuka da sunan Gwaggo, chocholate guda uku ta dauka sannan tarufe akwatin tasaka wani white slippers pink dake dakin masu kyau daidai kafanta tabude kofa ahankali tafito tana mamaki dataji gidan tsit babu ko muryan yara bin ko’ina take da kallo hartakai stairs tafara sauka tana bude chocholate dinta wata Yar mata tagani afalo tana shara matan jin tafiya yasa tadago kanta dan murmushi tayi ganin Lujain tace “ina yini amarya”? Dan turobaki Lujain tayi jin ankirata da amarya takarasa saukowa ahankali tace “ina masu gidan”? Murmushi matan tayi tace “duk sun fice nan makota yau ana sunan matan Kamal” shiru Lujain tayi sokawai take tafita waje juyawa tayi tafara tafiya zuwa kofa itadai Yar aikin tacigaba da sharanta tana mamaki ina Amaryan gidan nan zata daga ita sai towel akirji babu ko hula, bude kofa ahankali Lujain tayi tana kallon babban tsakar gidansu dayaji flowers ahankali tashiga sauka dagakan dakalin tana kallon gate dababu kowa awajen wani zuciyan nacemata tawuce tabude tafice abinda ta tafi gida wani zuciyan kuma nacemata karta fita kotaje gida daga Gwaggo har Baba zasu kara dawo da itane, tafita ma mutane su ganta ayita kallonta ana kiranta Yar iska tunda yanzu duniya gabaki daya sun santa, hawaye taji sunzo mata tunawa datayi abinda yasa tamazo gidan nan in first place, karasawa tayi wani wani plastic chair dake wajen flowers na compound din ta zauna takai chocholate nata baki ta balla tana taunawa still tana kallon gate din, kaganta kaman wata aljana fatarta fari kal kaman jini zai fito idan katabata ga pink towel da slippers ajikinta she looks so adorable and very cute.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull