Kenza eBookz

Sakon so complete Novel - Chapter 13

Sakon so complete Novel - Chapter 13

Sakon so complete Novel Chapter 13: Sakon so complete Novel Chapter 13. Tana nan tanacin chocholate din tana kallon gate aka bude karamin gate dasauri aka…

3,353 words

Tana nan tanacin chocholate din tana kallon gate aka bude karamin gate dasauri aka shigo mai gadi ne baima lurada itaba key gate yacire da saurinshi sannan yashiga bude gate din sai zare idanu take innocently tana kallo tanakai chocholate bakinta tana balla. Ana bude gate din daga Abee har Musty dukansu hangota sukayi zaune kan plastic chair daga ita sai towel babu dan kwali akanta hannunta rike da 3 different chocolate data bare tana ballansu all at the same time, da sauri Musty yadauke kanshi yaciro wayanshi yana dannawa kaman baiga komiba shikuma Abee kuri yayi yana kallonta yanda tadage tana kallon wajen gate din har mikarda wuya take kaman wata jimina tanacin chocolate kaman akwai abinda ta ijiye waje, jan motan yayi ciki tabi motan da kallo batare data gane waye aciki ba dan bata iya gani mai gadi yashiga kulle gate din. Ta glass Abee ke kallonta batare daya fito ba kozata tashi tashige ciki amman ko gezau sai kallon gate din dama tacigaba da yi tanacin chocholate dinta, dan kallo Musty yayi ganin yana danna wayanshi yasa batare daya kashe motanba yace “I need to get something for Hajiya bari na karbo prescription din mutafi” “okay” Musty ya amsashi atakaice hakan yasa Abee yabude kofa yafito tanacikin kallon gate taji karan bude kofan mota hakan yasa takalli wajen da sauri hada idanu sukayi itada Abee dake mata wani kalan kallo wani kalan faduwa gabanta yayi takasa cigaba da tauna chocholate din datakeyi takasa tashi takasa zaune takasa komi, sai kirjinta dake bugawa dum! Dum! Dum! Daidai Abee yakai gabanta batare daya kalleta ba babu alamun wasa a voice nashi yace “follow me” yay gaba tashi tayi hakanan kawai taji jikinta yafara rawa falon itama tashiga amman taga haryay stairs hakan yasa tabishi abaya agaban dakinta taga ya tsaya yay folding hannunshi akirji yajuyo yana kallonta, jitayi legs nata are shaking amman haka tadaure kanta akasa takaraso ahankali gaban dakin ta tsaya tana watsa da yatsunta cikin sanyin murya da yet zaka jishi a zafafe yace “bakida kayan sawa ne”? Girgizamai kai tayi batare data dago kanta sama ta kalleshi ba, cikeda dan zafi Abee yace “then why are you sitting outside da towel”? Dan tabe baki tayi irin na masu shirin yin kuka jin yanda yake mata magana kaman zai daketa ahankali tace “ai kaya tsungulina sukeyi, haka nake zama awajen Gwaggo naa” wani mugun kallo yamata yace “look up” ahankali gabanta na racing tadago idanunta dahar sun cika da kwalla sosai takallai, babu wasa kan kwayar idanunshi yace “this house yamiki kama da gidanku?” Girgixamai kai tayi daidai hawayen na zubowa sharrr yace “then this should be the last time dazaki daura this thing kifito waje understood”? Gyadamai kai tayi ahankali saikuma tajuya da sauri tabude kofan dakinta tashige tareda fashewa da kuka sosai tafada kan gado, yakai kusan 1min tsaye wajen yanajin karan kukanta yadanja tsaki yawuce dakinshi yarasa mesa yakemata magana with anger he’s so pissed of ne wlh. Wanka yayi ya shirya tsaf cikin jeans da Riga yadauki wasu jersey yahada awani karamin workout bag dan yanaso yabuga kwallo bayan magrib yafito batare daya kalli kofan ba yawuce yasauka kasa..EPISODE 2️⃣2️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram; https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Wajen motanshi yayi yabude yashiga ciki yana jefa jakan daya dauko baya yatada motan Musty na kallonshi baicemai komiba saidan murmushi dayayi tareda gyara zamanshi, ganin ba hanyar pharmacy sukayi ba sai barrack dasukayi zuwa filin kwallo yasa Musty kawai murmushi yace “maganin Hajiya fa” changing room Abee yawuce batare daya amsashiba Musty yabishi abaya suka shiga shidayake Musty nada kayan chanzawa a locker shi na changing room shiryawa sukayi suka fito suka shiga field sosai suke buga kwallo team na Abee daban nasu Musty daban Abee saicin kwallon yake kana gani kasan ya iya kwallo sosai ya kware, saida aka fara kiran sallan magrib sannan suka tashi wanka sukayi suka maida kayansu sannan suka wuce mosque.

Saida akayi isha’i sannan yadawo gidan kashe mota yayi yafito yana magana da waya akan kunnenshi, yashiga falo anan ma yake gani suma basu dade da shigowa ba, samin waje yayi yazauna yakarashe wayan dayakeyi sannan ya amsa gaisuwan kannenshi daidai nan Hajiya tafito daga dakinta da charbi a hannunta tace “waini tunda nashigo banga Lujain ba, ke Kausar tashi kije ki kiramini ita nasata a idanu” tashi Kausar tayi ahankali tawuce sama, Hajiya takalli Abee tace “dazu fa kaman nace itama ta shirya tabimu sunan saikuma dai na bari dan bangaya maka ba” shiru Abee yayi baice komiba dan baimaso anamai magananta daidai nan Kausar na saukowa tace “tana wanka Hajiya” amman nafada mata daidainan Anty Binta takawoma Abee shayi zubamai tayi a mug tabashi karba yayi ahankali tace “Yaya nakawo maka dinner”? Girgixa mata kai yayi yace “no” saida ya shanye shayin tass sannan yatashi yace “Hajiya bari naje daki” “to Imrana Allah bamu alkhairi” wucewa yayi yahau stairs yayi sama yana gab da karasawa gaban dakin Lujain Lujain tabude kofan tadakinta tafito tana sanye dawani doguwan riga black tana rawa rawan sanyi dan bala’in sanyi takeji gashin kanta ya dan hargitse ga lema leman ruwa tagaban gashin, juyowa tayi bayan ta maida kofan tarufe karaf suka hada idanu da Abee dake tahowa yana tafiya one one kaman wani sarkin kasa, wani kalan mugun faduwa gabanta yayi dawani kalan sauri har hannunta na rawa tabude kofan dakin takoma cikin dakin dasauri tareda maida kofan tarufe daidai wani atishawa na zuwan mata tayishi, bin kofar dakin nata Abee yayi da kallo yawuce yashiga corridor yabude dakinshi yashiga.

Ahankali tazauna kan gado tai shiru tadade zaune ahaka saikuma ta tashi tacire rigan tadauko towel tadaura tasake dawowa ta zauna bakin gado tasakeyin shiru tanajin wani kalan yunwa, wani kalan kwanciya tayi kaman marainiya tana kallon kofa bude kofan nata akayi aka shigo saida tadan firgita ganin Anty Binta ne yasa dasauri ta tashi Anty Binta tace “kince ma Baba baki kara zama da towel amman kinata zaman ko” sauke kanta tayi ahankali kasa tana wasa da yatsanta batare datace komi ba, Anty Binta takaraso gaban gadon tace “Hajiya na kiranki mesa bakizo”? Dago kanta tayi ahankali takalli Anty Binta saikuma takalli kofan dakin takasa cewa komi, kallon kofan Anty Binta tayi itama ganin kofan take kallo saikuma ta kalleta tace “Ya Imran yahanaki fitowa”? Gyadamata kai tayi ahankali hawaye na gangarowa daga idanunta wani kalan mugun tausayi Anty Binta taji tabata hakan yasa gently tazauna bakin gadon bama tasan mezata ce ba tace “ki yakuri kinji Lujain” kaman jira Lujain take fadawa jikin Anty Binta tayi ta kankameta sai kuka, dan lunshe idanu Anty Binta tayi tabudesu zatama Hajiya magana tagayama Ya Imran yanemi makaranta yasata tun wuri kan wani abu yasami yarinyar mutane gashi babu mai kulata daga ita sai Hajiya ke kulata yanzu idan ta tafi next week yazatayi, tadade tana kuka sannan Anty Binta tace “Ya isa to” Anty Binta takai hannunta kan fuskanta tana sharemata hawayen tana mamakin taushin fuskanta da kumatunta kaman fuskan Yar jaririya, ahankali Anty Binta tace “kinajin yunwa ko”? Gyadamata kai tayi cikin kuka, murmushi Anty Binta tayi tace “to bari naje nakawo miki abinci da shayi, stop crying now konai fushi” hadiye kukan tayi tana kallon Anty Binta, murmushi Anty Binta tayi tajuya tafita daga dakin bata wani jimawa suka dawo itada Kausar daketa kumbure kumbure tadauki tray na kayan shayi itakuma Anty Binta tadauki flask guda biyu Kausar na ijiyewa ko kallonta batayiba tajuya tafita itakuma Anty Binta ta ijiye tace “to sauko kici” ahankali tasauko tana dake goge hawaye.

Zaune yake gaban desktop nashi yana wani aiki dagashi sai singlet dawani dan gajeren wando wayanshi ne yay kara hakan yasa yadauka ganin Hajiya ne yasa yakai wayan kunnenshi yana mamakin meyafaru take kiranshi. “Ka sameni adakina Imrana” ta katse wayan, ijiye wayan yayi yatashi tareda daukan jallabiya yasaka sannan yasa slippers yafito batare daya kalli kofan dakin Lujain dayake iyajin maganan Anty Binta aciki ba tana mata fira wucewa yayi yasauka kasa Hamza da Abdallah yagani a falo suna buga video game suna ganinshi duk suka natsu dakin Hajiya yawuce da sallama yabude kofan yashiga Hajiya na zaune bakin gadonta tana kallonshi hakan yasa yakarasa ciki yazauna kan lallausan carpet na tsakar dakin ahankali yace “gani Hajiya” karasa jan charbi datakeyi tayi ta ijiye sannan takalleshi tace “Imrana” dan dago kanshi yayi yakalleta yace “na’am Hajiya” ahankali tace “I promise not to meddle with affairs naka dana matarka but I think akwai somethings that I can overlook a matsayina na babba” Hajiya tadanyi shiru saikuma tace “banson damuwa yama Yar karaman yarinyar nan yawa Imran, kaiba kulata kake ba kannenka ma haka, Binta ne kawai ke kula da yarinyan nan agidan nan nikuma baran iyaba dan kafafuna ba barina zasuyi ina hawa saman nan ina saukowa kullum ba” Hajiya takarayin shiru sannan tace “inaso gobe kafin katafi aiki ka dauki yarinyar nan ka kaita makaranta mai kyau kasata, islamiyya kuma zaka sata wanda su Kausar ke zuwa asabar da lahadi, amman dai gobe yarinyar nan tafara makaranta kaga karatu nata wuce ta, tunda bawai wani abu take agidan ba banda zaman kadaici da kuka dan haka ka kaita kasata a makaranta mai kyau kaji ko Imrana” gyadama Hajiya kai yayi yace “to” Hajiya tabishi da kallo tace “tashi katafi to Allah bamu alkhairi” ahankali yace “Ameen” yatashi yafita daga dakin tareda maida mata da kofan yarufe, sama yakoma daidai lokacin Anty Binta tafito tareda Lujain din da hijab ke jikinta black dayawani kalan haskata, ganinshi yasa tasauke kanta akasa tashige bayan Anty Binta ahankali tana wasa da yatsunta, Anty Binta ma sauke kanta kasa tayi ganin yanda yake kallonsu da wannan idanun nashi dabaka jurewa, kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace “where to”? Ahankali Binta tace “dakina zamu ta kwana awajen Ya Imran wai bata iya kwana ita kada…….” wani mugun kallo yama Anty Binta yace “bacemin daga nan” dawani kalan sauri Anty Binta tawuce tayi hanyar dakinta, wani kalan kuka Lujain taji yazomata batare data kalleshi ba tajuya ahankali takoma cikin dakinta ko tsayawa kulle kofan ma batayiba da gudu tafada gado sai kuka, yadade awajen tsaye sannan yakarasa gaban dakin nata batare daya kallo ciki ba yasa hannu yajawo kofan yarufe yawuce dakinshi.EPISODE 2️⃣3️⃣

Wanka yashiga yafito ya shirya cikin wasu milk pajamas masu bala’in kyau yazauna kan gado, drawer jikin gadon yajawo yadauko wani babban english novel na UK mai suna the soulless love, wani akwati yabude na glasses yabude yaciro wani white glass yasaka sannan ya jingina da gadon tareda kashe wutan dakin yakunna wutan side lamp kadai ya jingina da gado tareda jan bargo ya lullube kafanshi yabude book din yafara karantawa yanajin kukanta sama sama dan daga nan dakinshi yakanji abinda ke faruwa acikin dakinta, almost 2hrs yayi yana karanta book din sannan ya maida yarufe ya ijiye saman drawer ya kwanta ahankali yanaso yay bacci amman baya iyawa kuma bayaso yanashan magungunan shi, dan lumshe idanu yayi yabudesu jin ko’ina tsit that means tayi bacci kenan, wayanshi yadauka ahankali yabude wani locked folder hotunane aciki na wata black beauty mata maidan jiki kaman yanayin girman Anty Binta, kaganta kamanninta da Kausar daya sak kaman tayi kakin Kausar ta tofar, lumshe idanunshi yayi ahankali yabudesu yasake daurawa akanta yatsanshi yakai kan fuskanta yana shafawa murya chan ciki yace “I’ve missed you Muna, why did you have to go and leave me alone at this stage of life” shiru yayi tareda lumshe idanunshi again yaja wayan yakaishi kirjinshi ya rungume tsamtsam.

Karfe uku daidai kaman wata mayya tabude idanunta sabida azababben yunwan datakeji kaman wacce ta kwanta bataci abinci ba tsabagen yanda tasaba cin abinci tsakar dare, ga kanta dake wani kalan sarawa hancinta taji yatoshe da majina hakan yasa dabaki take numfashi ma, ahankali tabi dakin da kallo dan wutan dakin a kunne yake, saukowa tayi daga gadon dasauri zuwa wajen kulolin dake dakin tashiga budewa amman babu komi cikinsu dan tas tacinye komi jiya da daddare, mikewa tayi tsaye tana kallon kofan dakin gabanta na faduwa saikuma ahankali tai wajen kofan gabanta nawani kalan mugun faduwa bude kofan dakin tayi kadan ta leka wutan corridor a kunne hakan yasa tafito da sauri tana gyara daurin towel din kirjinta kanta ba dan kwali, waigawa tayi takalli falon saman gabaki daya babu kowa ko’ina tsit, tafiya tafara ahankali tana taba cikinta da har wani ciwo ciwo yake mata yanadan kugi sabida yunwa stairs tayi tafara sauka tana kallon falon da wutanshi akashe yake gabanta nawani kalan fadi har hadiye yawu take tana sauke ijiyan zuciya takarasa sauka tana tafiya sadaf sadaf kaman wacce zatai sata tayi dining area dayake akwai dan haske dake haskowa daga wutan falon sama, ahankali kaman mai sata tashiga bubbude warmers na abinci dake kan dinning table din tana dubawa ganin akwai naman kaza soyayye dayawa dakuma rice a warmers din yasa tajuyo ahankali zata dauki plate daka cikin dankin wankakkun plate din dake kan dinning table din, mutum tagani tsaye abayanta yay folding hannunshi akirji kaman gunki, wani kalan zaro idanu tayi tawani kalan bude baki zata kwala ihu danta bala’in tsorata cikin zafin nama Abee yawani kalan fizgota tawani fado jikinshi taredakai hannunshi kan bakinta yarufe gam dan yasan tana ihu Hajiya zata farka dan batada nauyin bacci ko kadan tafito tagansu anan and that’s the last thing he needs now, cikin wani kalan low voice kaman mai whispering yace “don’t you dare scream” wani kalan zaro manyan cat eyes dinta take tana kallon fuskanshi dadan haske kadan din dake wajen wanda yazo daga falon sama jikinta ko’ina rawa yake jin gabaki dayan jikinta na manne danashi banda fuskanta dake facing nashi takasa kwace kanta gashi yataushe mata baki kamshin dayake narawa ni ratsa mata hanci, wani kalan kallon kwayan idanunta data zaro yake dudda the place is dark amman harwani kyalli suke, yanda yake kallonta batare daya zare hannunshi daga bakinta ba yasa taji wani kalan natsuwa nashiganta ahankali jikinta yadaina rawa hakan yasa tasaukar da idanunta kasa ahankali danta kasa jure idanunshi akanta, kaman wanda yatuna wani abu zare hannunshi yayi dagakan bakinta dasauri tareda tureta daga jikinshi tangal tangal tayi zata fadi tabuge da table kaman wacce batada stamina dasauri yakama hannunta yarike hakan yasa bata bugeba adan kufule yace “what are you doing here”? Dan kallonshi tayi adan tsorace akuma hankali cikeda sigan shagwaba tace “I am hungryyyy” tai maganan tana kokarin kwace hannunta daya kama dayasa taji hannun yamata wani iri, sakin hannun yayi shima dasauri strictly yace “go back to ur room” kwabe kwabe tayi da fuska kaman zatai kuka saikuma tawuce dasauri batare datace komiba takoma sama kanta na bugawa sosai, shiga dakin tayi batare data kulle kofanba dan tsoro takeji takoma gado tazauna tana dafe kanta dakemata ciwo sosai tana numfashi da baki, kugin da cikinta yayi na yunwa yasa ta kwanta ahankali kan gadon tareda kife cikinta tajuyayar da fuskanta tana kallon mirror ta hakan yasa tajuyama kofan baya ahankali tana lumshe idanu wasu zafafan hawaye na sauko mata daga idanu sabida shegen yunwan datakeji gashi yakorota ciki, almost 5min tana kwance ahaka kaman daga sama taji kamshin turaren mai dadi nashiga hancinta dudda muran datake hakan bai hanata jin dadin turaren ba, ahankali tajuyo da kanta batare data tashi zaune ba dantaga waye yashigo dan ko kadan bataji alamun tafiya ba, Abee tagani tsaye bakin kofanta dauke da tray a hannunshi yana kallonta ba yawo ba fallasa, dawani kalan sauri takai hannunta tashare hawayen dasuke kwance kan fuskanta sannan ta yunkuro ta tashi zaune dan dafe kanta tayi tareda yatsine fuska sabida ciwonkan dataji kaman kanta zai tsinke yafadi, daukekai yayi daga kallonta batare daya shigo dakin ba yace “tashi kisa kaya” babu musu ta tashi gaban wardrobe taje tabude wani dogon rigan bacci tadauka sannan tajuya tadan saci kallonshi ganin yana tsaye inda yake har lokacin yasa ahankali tazo tawuce bathroom tamaida kofan tarufe, towel din jikinta ta cire tayi hanging sannan tasaka rigan baccin peach ne very decent ya tsaya mata iya knees dinta rigan yamata kyau sosai gadan katon tebanta daya fito daga rigan, gashin kanta dukya kara hargitsewa sabida yanda tasaka rigan dagaka, bude kofan tayi ahankali taleko cikin dakin, baya dakin amman ya ijiye mata tray abincin akan carpet, jellof rice ne da naman kaza kusan 5 akai sai tururi suke alamun yamata microwaving sai goran ruwa akan tray mara sanyi da spoon, da wani kalan sauri tafito har murmushi take ganin abincin zama tayi tadauki spoon dasaurinta zata fara ci daidainan aka sake bude kofan dakin dasauri tadaga kanta daidai tanakai rice bakinta hada ido sukayi da Abee dake rikeda kwalin magani guda biyu a hannunshi, ahankali tasauke kanta kasa tana ijiye spoon na abincin dazata kai baki tarasa mesa dazaran taganshi she use to become restless yatsunta tashiga wasa dashi batare dako motsin kirki takarayiba, karasowa cikin dakin Abee yayi har zuwa gabanta ya tsaya tareda ballo paracetamol biyu da actifed guda daya murya chan kasa kaman wanda bayason yay magana yace “take” dan kallonshi tayi ganin kallonta yake ba wasa kan fuskanshi yasa kaman wata yar yarinya tabashi hannunta, palm dinta yafara kallo sannan yasamata pills din aciki raurau tayida idanu tana kallon magungunan babu abinda ta tsana arayuwanta kaman magani, bottle water daya kawomata mara sanyi yadauka yabude yabata hannu tasa takarba shima sannan tadan kalli fuskanshi kaman mara gaskiya awani irin hankali akuma tsorace tace “in sha?” Wani mugun kallo yamata yace “no kishafa” raurau tasakeyi da idanu, sannan ahankali ta daura pills din kan cinyanta tadauki guda daya rak acikin guda ukun tana kallo sannan takalli fuskan Abee adan tsorace ganin ita yake kallo yasa dasauri ta dauke kanta takai maganin ta wurga baki taredakai ruwa ta kurba wani kalan kakarin amai tahau yi Abee dake kallonta yace “kikamin amai anan saikin lasheshi tass” yay maganan yana fizge ruwan daga hannunta ganin tana shirin zubarwa, sauran pills din yadauka daga kan cinyanta yarike a hannunshi sannan yakai ruwan bakinta ahankali yace “open your mouth” babu musu tabude bakin zuba mata ruwan yayi aciki sannan yace “raise your head” daga kanta sama tayi sannan yadan matso kusada ita faduwa gabanta yashigayi sosai amman tadaure, watsa mata pills din acikin bakin yayi dasauri tahadiye tana wani kalan tabe fuska da baki kaman taci kashi tadauki spoon tadebi rice dasauri takai bakinta tanaci hawaye yayi fall acikin idanunta, AC dakin yakalla ganin akashe yasa yakalleta har lokacin tabe fuska take irin na wanda yasha magani yace “da ruwan sanyi kike wanka”? Kaman daga sama taji tambayan, dan kallon fuskanshi tayi saikuma ta gyadamai kai ahankali kafin tadauke kanta tace “ban iya kunna ruwan zafi ba” dan shiru yayi yana kallon yanda take magana, jin baice komiba yasa tadago kanta hada ido sukayi dasauri tadauke kai, mikewa tsaye yayi yawuce bathroom nata yabude ya tsaya daganan bakin bayin yana kallon ciki bayin is very clean towels ne kusan guda 5 ta shaya ajikin hanger juyawa yayi yakalleta ganin tana zaune inda take bata tashiba yace “sainace kizo zakizo” dago kanta tayi tadan kalleshi saikuma ta taso ahankali dauke kai yayi yashiga bayin tabiyoshi ta tsaya daga nan bakin kofa nuna mata yanda zata kunna hot water yayi sannan yajuyo yace “kingane”? Gyadamai kai tayi ahankali kanta akasa ganin yana tahowa yasa tafice daga bayin dasauri takoma wajen abincinta tazauna tafaraci shikuma yafito daga bathroom din yawuce yafita daga dakin.

Tass tacinye abincin da naman tasha ruwa sannan tahau gado sai bacci. 4:30 Abee yafito cikin jallabiya yatada mutanen gidan batare daya shiga dakin Lujain ba, yawuce masallaci. Wuraren 7 nasafe Hajiya tafito falo taxauna kan kujera daidai Kausar dake cikin kitchen tafito da kula zata ijiye kan dinning Hajiya tace “Kausar jeki cema Auntyn ki Lujain tashirya tsaf ta sauko Babanku zai kaita yasata a makaranta yau” Gyadamata kai Kausar tayi tawuce sama.EPISODE 2️⃣4️⃣

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull