Sanadin caca book 1 complete - Chapter 10
Sanadin caca book 1 complete Chapter 10: Sanadin caca book 1 complete Chapter 10. Samun waje yayi ya zauna yana kallonsu suna kewaya gidan,banda ihu babu…
2,970 words
Samun waje yayi ya zauna yana kallonsu suna kewaya gidan,banda ihu babu abinda suke,abinka da yara har tausayinsu ya kamani. Bakiti na ɗauka bayan gama yimasa sharar ɗakin da kuma tsakar wajen,kayan da za'a wanke na zakuɗo a ɗakinnasa masu ɗan banzan datti,duk sun rine ga hamami kaman zan yi amai.. Ta gabansa na wuce na nufi hnayar waje ɗebo ruwan,haka kawai sainaji gidan yamin duhu rana ɗaya,ashe gaji nafila ce akansa. Tunda nazo gidan yaune ya taba kaiwa har zuwa yanzu yana gidan.. Dana kawo bakin ƙofar gidan tsayawa nayi ina kallon wajen,nasan mutane zasuyi ta kallona suna maganganu akai,shiko kunya bayaji ace matarsa zata ɗebo ruwa,ko yara mata basa ɗiban ruwa balle matan aure,hmmm nice ma nake mutunta auren,shi mutumma baya mutuntawa ballantana wani aure a wajensa. Tafiya nake kaina a ƙasa na nufi wajen ɗiban ruwan,Allah ya taimakeni ma babu nisa daga gidan.. Ban taba tunanin fitata tafarko a gidan ɗiban ruwa zanje ba. Sau uku nayi randar tasa ta cika,saniyar dayake faɗa itama na kai mata ɗaya,saina sake ɗebo wasu guda biyu na wankin kayansa,nima saina haɗa da nawa ma na wanke.. Duk ɗiban ruwan danake ta gabansa nake wucewa,har sannan izaya yake yiwa yaran gaji bai gama ba,tabb lallai gaji tana tsoron goje,duk abinda yake shiru taƙi yin magana,yanda take da ƴaƴan nan kaman rayuwarta amma tayi shuru? "Kutashi ku tafi,gobema ku sake tafiyah ta rashin ladabi,kuje ƙofar ku ku ƙiramin atika yanzunnan" Yana cewa ya sallamesu da gudu suka shige ƙofar tasu suna kuka. Can kaman bayan mintuna Kursiyyah ƴar babbar tafito daga ƙofar tana matsar hawaye. "Yayah goje wai inji gaji batanan bata kwana a gida ba" Dariyar gefen baki yayi yana jijjiga kai. Ɗaga murya yayi yanda gajin zatajishi. "Ke gaji,wato ni zakiyiwa iya shege koh,makaho kika mayarni komai,yarinyar ba ita nagani cikin dare tashigo gidaba?. Kinsan Allah kafin na ƙirga Uku kota fito kokuma nazo da kaina na ɗauketa,abin kuma bazayyi muku kyau ba" Ƙirgen zai fara,ganin abin zai baci nida kwainane cikin rawar murya nace. "Uhmm....bata ƙofar inna gaji" Wani kallo da yatsomin da ɗazu nasamu ya manta da shafina. "Tana ina toh,ohh daga zuwanki gidan kema har an fara munafurci dake ko?" "Ahah ahah wlh ba haka bane,kawai ina kwance ne da daddare tace na buɗe mata shine......" Bai bari na ƙarisa wanke kaina ba ya buɗe muryarsa yana ƙiran atika. "Ke Atika wlh in baki fito daga ɗakinnan ba idan nazo saina yayyaga ki" Yana gama magana kiriff saiga Atika a waje tana rarraba ido,duk da tana ƙoƙarin boyewa amma kana ganin rawar da jikinta yake kasan tsoron karonnata dashi take. Da hannunsa ya nuna mata gabansa taje ta tsugunna. Sunkuyar dakai tayi takasa haɗa ido dashi. "Uban me kukaje yi keda Sageer A asibiti jiyah?. Wato ciki kukayi tare saboda ku ga tantirai shine kuka zubar koh,kowa a wajen sai faɗa yake cewar ke ƴar gidanmuce,saboda ki jawo min raini a gari koh. Ku a hakan har shegune gu da zaku iya kashe rai,ko ni bana ɗaukan rai sai mutum yamin laifi,shi cikin da kika yi fadamin wane laifi yayi." "Wayyo dan Allah yayah goje kayi....." "Shuru kada ki kuskura ki faramin wannan Kalmar da banaso ɗin. Kinsan mandotary ne sai kin Kwashi naki kason,shima abokin shan shagalinnaki yana can wajen yarana suna morewa,ke kuma anan zan miki naki a gida. Ke wakike kujera koh a sunan na yaran manzo(kursiyyah)je ki ɗaukomin wani cable na birkin keke yanan a maƙale a gefen ɗakina" Jijjiga kai Atika tayi tana kuka jin abinda za'a ɗauko,da alama dama kaman tasan karo. Ni da bani za'a duka bama nima karkarwar nake,wankin nake da sauri ina gurzarsa kar a haɗa dani. Wacce aka aika ɗin ta tafi saigata da dawo kuwa,miƙa masa tayi yana karba tabar wajen,ƙofarsu ta shiga,da alama taje faɗawa uwarta abinda yake faruwa ne. Mummurɗa shi yayi yai masa tuka,iya ƙarfinsa ya zage ya tsula mata a cinyah,wani ihu ta kurma wanda nasan ana jiyota a maƙwantansu,innalillahi yanda nake zatonsa ashe ya fi haka. Tsula mata yake tana burburwa saida yayi mata Goma kafin ya dakata,nishi take tana maida ajiyar zuciya kafin ta tashi ta zauna,tana kaiwa hannun ta bangarori da dama na jikinta,inda duk zafin dukan yake ratsata. "Kinsan dukan danayi miki na menene koh?" "Jijjiga kai tayi alamar ba ta saniba" Ohh baki ma san mai kikayimin ba,zaton ki dan kin sheqe ayar kine kaɗai zan bata lokaci na wajen yimiki haka,kinada wannan darajar,ai ba sheqe ayah ba in kinaso kije kasata ma bai dameni ba,amma gonata da kika shiga shiyasa nake miki hukunci saboda karki sake shiga. Meyasa kukaje asibiti kukace cikina ne a jikinki,wani na turoku bana son a sani kar asirina ya tonu. Koba haka kukace ba keda bunsurunnaki?" "Eh.....eh haka muka ce" "Meyasa to kuka ambaci sunana a sharholiyarku,wato saboda kun rainani koh,kin taba ganin nayi irin wannan ƙarƙantaccen aikin?" "Ahah baka taba,sunƙi zubar mana da cikinne wai sai mun kawo shaidu,shine mukace naka ne,kace kuma idan kazo abin bazayyi kyau ba. Wlh ba hakan muke nufi ba,kawaidai mun faɗa ne dan suyi mana aikin" Wata dariyah yasake yi ta gefen baki,kana ya sosa ƙeyarsa da kan cable ɗin.. "Lallai yarinyar nan kin dakeni da mamakinki,yanzu da badan yarona yazo ya faɗamin ba saboda ya jiku,saidai ayi ta faɗan na miki ciki a cikin gari,a zubarmin da mutunci. Ni bansani ba ashe so kike na miki ciki,toh shikenan bazan miki ba ni nafi ƙarfin haka,amma in hakan kikeso zan saka a sake yimiki wani,idan kikaje zubarwa kice goje ne yasaka ayimin,shine kuma,ya turo yace ya zubarmin....barinaje na dawo na kaiki cikin maza biyar su yayyagaki,wannan da kikayi ba iskanci bane ai" Oh dama wannan laifin tayimasa shiyasa yake jibgarta,nifah nayi zaton ma bayaso ta dunga iskanci ne,tabbb lallai Atika ma tanada kasada sosai. Wani ihu tafara tana haɗa hannaye,roqonsa take bilhaqqqi,amma saima ya rufe ido. "Dan Allah dan ya rasulullahi Yaya goje kayi haƙuri,wlh bazan ƙaraba na tuba,gaji kizo kI ceceni wayyo gaji." Tunda ake ƙwallon ball da ƴaƴan nata bata yi ko tari ba sai yanzu ta fito,haba a matsayinta na uwa kuma tana jin kukansu dole abin yayi mata zafi. Da goje suka haɗa ido lokacin data fito ɗin,kana ganin fuskarta kasan in ranta dubu ne to duk ya baci. "Amma dai goje tunda ka daketa tabaka haƙuri ai shikenan zance ya wuce ko" "A tunanin ki? Har yanzu banji muryar kaina tace na barta haka ba,kee tashi kije ranar can ki zauna" Filin tsakar gidan ya nuna mata wanda yayi zafi zau da rana,ki saka gwiwoyinki a wajen ki tsaya haka,karki tashi har sai nazo na ce hakan. Ban gama dake ba tukunna,zanje ba sallami wancan abokin aikinnaki ne" Har zai fita ya kalli gaji ya kalleni,wani dumm naji mai kuma nayi yanzu. "Ban yarda ta tashi ba kokuma abata ƙwayar abinci ko ruwa,idan kika bata...naji labari saina sakaki a ɗaki da karnuka sun yayyagaki. Ke kuma idan ta bata abinci kokuma ta tashi a wajen baki faɗamin ba,nasamu labarin ke zan yiwa abinda na faɗa zanyi mata" Ya ƙarisa maganar yana tabbatar min,ɗaga kai na fara ba tsayawa har ya fita ban dainaba. Shanyar kayan dana wanke nake,sai ji nayi gaji takama kafaɗata ta jefar dani ƙasa,tohh ni kuma mai nayi,wato yakama dukan ƴaƴan ta tashaqa bari ta huce akaina ni marar galihu. Kallonta nake da mamakin mai kuma nayi ni,ƙasar da take bakina nake sharewa,saboda yanda na kifu a bakin. "Nikuma gaji mai nayi miki" Yau ko inna ma bance ba,dan na kula matar batada darajar daza'a mutuntun tata,kuma ƴaƴan ta ma ai haka suke ƙiranta. "Ohh baki ma san mai kikayimin ba koh? Nakula hadda wani sanja murya ma kike,dan kinga mijinki yayiwa ƴaƴana fata fata shine hakan yamiki daɗi koh?" "Taya za'a duka wani mutum yaji daɗi,indai bashine marar imani ba,kuma dai naga kina gani wanda yayi dukan nima ba ƙyaleni yayi,bare kice nina zigashi" "Zigo? Kima zigashin mana,kekam ai a tafin hannuna kike in shi ya gagareni,nasha neman maganin tanƙwasashi abu ya gagara,saboda asiri baya kamashi,amma kekam ina ba irin jikinsa ne dake ba koh. Wato saboda ke ga munafuka hadda faɗamasa atika a ɗakin mairo ta buya koh,ke a dole zakiyi gwaninta a wajen wadda bai ɗaukeki mutum bama ballantana kuma matarsa,saboda kallon kuɗin caca yake miki,ko saniyar daya ciyo a kalankuwa tafiki daraja a wajensa,ganinki kike mace amma keba mace bace,wacce namiji yakasa ɗaga ido yakalla za'a ƙira mace,kuma batun Atika yanzu zan dauketa a wajennan,inkin isa ki faɗa ki gani. Abinci kuma zanga wanda zai sake baki a gidannan,aiki kuma babu fashi saikinyishi" Maganganu taci gaba da gasa min masu zafi,haushine ya turnuƙeni zuciyata tana zafi,ina na ɗebi iya inda zan iya ɗauka,dolene na fesar mata da sauran. Kallonta nake tana ƙoƙarin isa inda atikan take. "Hmmm wai gaji saboda kina matsayin matar ƙanin baban mijina,matsayin uwata aka baki ne,ke baki san in kinkai mutum bango ki dakata bane? Harda zaki ƙirani ba mace ba,shiyasa ai naga ƴarki da take kasa darajarta a waje kowa ya ɗauka kaman karya za'a ƙirata da mace koh,kokuma ke da bakisan soyayyar miji ba yanacan gidan karuwai a can yake wuni,ke bakida aiki sai dafawa ki ciyar masa da ƴaƴa za'a ƙiraki da macen. In kincika macen kema da ki hanashi zuwa wancan ƙazamin gidan mana.Ai gwanda ni ba mata yake biba ya ƙyaleni,ra'ayine bayayi,kekuwa fah yanason matan amma mai yasa ya tsallakeki. Sannan dakike cewa wai inna isa na faɗamasa zatonki idan kin ɗauketa a wajen zanyi shuru ne? Wlh saina faɗa,haka kawai ki ceceta nayi shuru ya gano ya fatattakani bai dameki ba ko,nina aiketa yawon sharholiyar komai. Abinci kuma kada ki bayar,nima kuwa bazan sake miki komai na gidannan ba,inkin ban abinci nayi miki,in baki bani ba nima bazanyi ba,inji ce ni saida mai nayi aiki" Ina gama faɗin haka nakama hanyar ɗakina da sauri,saboda kada ta biyoni ta fatattaka ni kaman yanda ta naga tana huci,cike kuma da mamakin irin furucin dana yi. Haba ai dole nayi,ko damo aka matsa ai dole yayi cizo,wanka zanyi na kwanta,nasan dole goje zai dawo basai dare ba,saboda ya ajiye atika a tsakar gidan. In yaso saina tambaye shi naje gidan su Shareefah,nasan zan samu abinda zanci a gidan.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977 Auwal Sadiya First bank
Ko katin mtn ta nan 09035784150
VTU ta nan 2347068390570
Shaida kuma ta nan 09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[15]
[Goje a mahangar gani]
Har na fita daga gidan rai na bai daina zafi,lallai wannan yarinyar wuyanta yayi kauri. Lokacin danaji maganar nan baƙaramin baci raina yayi ba,kaman ni....nine zatace nayi mata ciki,kai barima na koma nasake tattaka ta dan ubanta. Juyawa nayi gidan,har nafara shiga na hango gaji ta jefar da Sumaimah a ƙasa,wato akan ta zata huce saboda na daki ƴar ta ko. Maganganu gajin tafara faɗawa Sumaimah,wacce kana ganin fuskarta kasan abinda take faɗamata ba ƙaramin zafi suke mata ba. Kai mata mata.....shiyasa fah ni banason shirgi dasu,wato rashin shiga harkarta da banayi shima abin magana ne da har za'ayi mata gori dashi. Niyyar ƙarisawa nayi,ganin gaji tana shirin ɗauke Atika daga inda nace ta tsugunna,dama nasan hakan zata faru,tsoratar da Sumaimah zatayi ta ɗauketa daga wajen,musamman data ganta wawiyah ce batada wayo. Siririyar maganar ta naji,cikin sanyi take amayarwa gaji duk maganar data fesa mata,dama ta iyah magana haka,nida nayi zaton ma kurmiyace. Tun bata kai haka ba muna yawan cin karo da ita a hanya in zata makaranta,sai ta juyah da gudu kaman taga aljani,tun abin yana bani mamaki har na daina. Amma yanzu ta dawomin da mamakina,ina ganinta wawiyah ashe tanada wayo,ehh tunda gaji tasaka wannan magana da alama takaita bango ne. Fitowa nayi daga gidan na tafi inda su Tunga suke hukunta Sageer,har na isa wajen da tunanin faɗan matan a raina. Lokacin dana isa wajen sun mammaujeshi sun ɗaure shi,a zaune suke suna taɗin siyasa,na wani chairman paty dayake so muyi masa aiki. Ina isa wajen sukayi shuru tareda bani gaisuwa,amsawa nayi kana na samu waje na zauna. "Ogah goje gashi nan mun ɗan tabashi kaman yanda ka nema. Iya shegen ma ya iya kawai,ashe ƙaramin ɗan iskane,daga dukan farko fah ya rojaye kaman wata ƙanƙara" Ragarus ne yafaɗa yana cigaba da jujjuyah sandar hannunsa. "Hmm ku sunceshi ku kaishi ƙofar gidansu,duk ya isheni bana ma son ganinsa,ku tabbatar kun bar masa jan gargaɗi a rubuce na saka hannuna" Dama duk masu bin matannan suna lalatasu yanda kasan ƴan daudu haka suke,sai shegen surutun tsiya da ƙarya,matan ma sun fisu ƙwari. Ko mai ma matan suke gani a jikinsu oho. Jawabin da chairman party yafaɗa suka maiyarmin,akan yanaso muyi masa aiki,saidai suyi masa badai ni ba,dan inada wani aiki da zamu fita da ƙungiyar DC,Jiyah suka turomin takardar inda zan samesu da daddare,za'a tattauna yanda plan ɗin zai tafi,nasan bazai wuce sati ɗaya ba samu fita aikin.Bazan faɗawa sauran abinda yake faruwa,iyah Tunga ne kawai yasan zancen. Yau ma nake shirin naɗashi shugaba mai riƙon ƙwaryah kafin na dawo,bazayyi yu dan bana nan na hanasu yin aiki ba,musamman kuma dana san zasu samu kuɗi sosai idan sunyi ɗin. "Bakomai za'ayi masa aiki,duk da bananan a lokacin,amma zan yimasa gargaɗi kaman ina nan. Zanyi tafiyah maybe wani satin,zan iyah kaiwa satin ban dawo ba,dan haka Tunga zai zagorance ku idan bana nan. Basuji daɗin abinda nace ba,sannan nasan dole zasuso sanin ina zanje,amma koda zasu sani ba yanzu ba tukunna. Jeji na nufah Ina riƙe kai,wannan ciwon kan narasa daga ina yake zuwa,duk sanda nafara jinsa saina dunga jin kaman ba nanne yakamata na kasance,kaman inada wani wajen bayan nan,kaman akwai wata rayuwar bayannan danake da itah. To amma a ina take,yaushe zan bar wannan masifaffen ciwon dayake juyar da rayuwata,haka nake kwana na tashi,amma tunda nake bantaba jin nutsuwa ba,kullum acikin duhu nake,lokaci lokaci ko a bacci ina hango wani haske ɗan ƙarami a can nesa,sai nayi gudu nayi gudu inaso na kamoshi sai ya bace ya ƙyaleni ni kaɗai. Ƙarisowa wajen bukkar tawa tacikin jejin nayi,da sanina nayi mata fenti baƙi,saboda a baƙin wajen kawai nake iyah bacci ,hakan ma nafison cikin jeji,shiɗimma ba cikin salama ba,sai an kai ruwa rana,kowa ka tambayeshi yasan ba ƙalau nake ba,akwai abinda yake cin rayuwata da kaɗan kaɗan. Bani na tashi daga baccin wahalar daya ɗaukeni ba sai a kusan la'asar. Tashi nayi naga abinci Tunga yakawomin,dama hakan yakasance al'adarsa,bansan mai nayi masa ba ya damu da rayuwata,shin mai nakeyi daya kamata a damu dani?. Banci da yawa ba na ajiyeshi nabar bukkar. Kai tsaye gida na nufah,nasan waccar sheɗaniyar yarinyar ba lallai ne ta tashi ba tana wajen. Duk hanyar danabi yara guduwa suke,wasu nayi ƴar dariya wasu kuma na jijjiga kai,amma dai hakan yana min daɗi,naga ana tsorona,koba komai zan jini tamkar sarki. Pa kwance na ganta luff a inda nace ta tsugunnan,inuwa har da kusa iso inda take. "Keee...." Firgitt tayi tatashi zaune,jikinta sai rawa yake na azabar data sha,kaman wacce tayi wanka da rairayi,ƙasa take kallo,amma kana iya gano bushasshen hawayen daya haɗu da ƙasa a fuskarta. "Tashi ki tafi,gobe ma ki sake sakoni cikin sabgarki" Yunƙurin tashi tayi,mangar mangar tanufi ƙofar su,wato sai gida an doki kare aka,da sanda yaje satar kajin gidan basu sani ba kuwa. Takardar da aka aikomin nake karantawa,abinnan yana bani mamaki,yaushe inna ta sakani a makaranta ne,kwata kwata bana tuna shigata makaranta,amma kuma ina karanta abinda aka rubuta da hausa da kuma turanci,ko yaren turanci akayi sainaji inajin mai akace,har naji inason na maida amsa kuma da yaren. Ƙarar motsin tafiyar mutum naji,hakanne yasa ajiye takardar ina jira naga wanene zai shigo. Sallamar Sumaimah naji a bakin ƙofar,saida tazo bakin ƙofar naga kayan dana bata wanki ne a hannunta. A bakin ƙofar ta tsaya,ita bata shigo ba ita kuma bata koma ba,ganin abin har yafara bani haushi yasa nace. "Idan bazaki shigo ki ajiye ba toki koma dasu" Da sauri kaman jira take ta tsallako cikin ɗakin,a gaban akwatina ta tsugunna,dayake can take kallo sai hakan yabani damar kallon bayanta. Atamfah ce a jikinta sabuwa,tunda nake ban taba kallonta da sabon kaya ba sai yanzu.. Zuge akwatin tayi ta jera kayan a cikin tass kafin ta mayar ta rufe. Kallon ɗakin nake sai a sannan ma na kulada gyaran da tayiwa ɗakinsa,harda yanar gizon da take jikin ɗakin duk ta cireta,nayi ƙarya idan nace bayyi kyau ba. Tashi tayi zata fita saikuma ta tsayah,kallonta nayi anan nagane abu takeso tace,ganin yanda bakinta yake motsi. "Menene" Na tambayeta saboda na hutasar da itah,nasan in dai a hakanne saimu wuni batace komai ba,so nake kuma ta tafi tabani waje akwai abinda zanyi. "Uhmm ......uhmm dama inaso nake gidan su Shareefah ne ƙawata,babu nisa kafin magriba zan dawo" Shuru nayi ina nazarin maganar tata,shin dama na taba cewa karta fitane,intanaso da koma gidansu ma mana,yau ubanta yabani kuɗina yace ƴar sa ta dawo gida ba riƙeta zanyi ba,wani salon munafurci ne hakan ko mai?. "Shin dama tunda kikazo gidannan kinji nace kada ki fitane?" Saurin jijjiga kanta tayi tana wasa da ƙasan rigarta,sai tayi kamar an tare bera a buhun daddawa. "Ahah ba haka bane,Allah ya hani mata da fita daga gidan mazajensu batareda izinin mazajen ba,idan kuma mace ta aikata hakan to mala'iku zasuyi ta tsine mata har taje ta dawo,shiyasa idan mace tanason gujewa hakan to ta tambayi izinin mijinta a duk lokacin dazata fita waje" "Tohh wata sabuwa,da ba'a garinan kike ba sai nace a ina kikaji,jeki idan zaki wata anguwar ma kada ki sake zuwa kimin wannan iyayin" "Toh nagode" Bata jira na bata sake cewa komai ba ta fita da sauri daga ɗakin.
••∆∆∆••