Kenza eBookz

Sanadin caca book 1 complete - Chapter 9

Sanadin caca book 1 complete - Chapter 9

Sanadin caca book 1 complete Chapter 9: Sanadin caca book 1 complete Chapter 9. Cikeda borin kore kunya ya kaɗa rigar sa yabar gidan,amma kana ganin…

2,973 words

Cikeda borin kore kunya ya kaɗa rigar sa yabar gidan,amma kana ganin fuskarsa kam kasan abin ya dameshi. (Hmm baka ga komai bama) Ammi tana shiga ƙofar tasu taji ihun inna rammah a ɗaki. Ƙarisawa ɗakinnata tayi da sauri dan ganin mai yafaru. Leƙawa tayi ta samu aljanar da aka ƙira da Deejah ta kafa haƙoranta a cinyar inna ramm,irin wanda tayiwa kazarta ɗazu. Ammi ce tashiga ɗakin ta janye ta daga jikinta,jini sai zuba yake a wajen. "Wayyo na shiga uku,cinyeni zatayi nima kaman yanda ta cinye kazata,wlh bazan zauna ba uwaisu ya kawo abinda zai halaka ni ya halaka ƴaƴana" A bangaren Deejah kuwa ammi tana banbareta daga jikin rammah ta koma kan gadonnata tasake kwanciyah luff kaman ba ita tayi ba. "Rammah mai kika mata ta cije ki?" "Ammi ganemin wannan masifar,tace a ɗakina zata zauna na kawota,wai kawai dan taga ɗana akan gado saita jefoshi.Aradu badan na cafkeshi ba a ƙasa zai faɗi,haushin hakanne yasa na mareta,aikuwa tafara wannan gurnanin,wai ba'a dukanta,kannaceme naji ta maƙare a jikina tana yakushi na. Muna haka zanina ya kunce,tana ganin cinyata ta gasa min cizo.Wani zafine ya jiyarceni shiyasa na zuba ihu. Dan Allah Ammi ki taimakeni na fitar da ita a ɗakina" Deejah tana jin abinda rammah ta faɗa ta ɗago idonta. "Idan kukayi yunƙurin ta'bani saina bunkawa ɗakinann wuta na babbakeshi,ke kuma idan kika sake shiga in muna fada to ɗakinki zan koma da zama. Zanyi bacci kafin na tashi ku sama min abinci,idan ba haka ba kaza ta gaba ce abincin na,sannan duk ɗan daya shigo ina bacci saina karya ƙafarsa". Tana gama faɗin haka ta koma ta kwanta. "Kinji koh ammi dan Allah........" "Ahah dakata bakyajin abinda tacene,ko bakiga yanda tayiwa kazarki ba kai,bazaki ɗau darasi daga haka ba. Ni kinga tafiya ta ba dani ba. Takaicine ya ishi rammah,hakanne yasa ta fito filin ƙofar tasu tana safa da marwa,burinta kawai uwaisu ya shigo gidan ta direshi da masifah,a jima ta leƙa ɗakinnata,duk sanda ta hango Deejah a kwance tana birgima akan gadonta sai wani takaici ya jiyarce ta. Tun tana tsammanin jiran uwaisu shuru shuru har yamma tayi,bata manta ba kuwa yana shigowa tasha gabansa. "Allah ya shigo dakai,maza kasan yadda zakayi ka fitarmin da waccar halittar daga ɗakina,dan wallahi bazan zauna da itaba,saidai na bar gidannan akan haka" "To yanzu ykk so nayimiki kenan,shigowata kenan tun fitata,baki bani abinci ba kuma kece da abinci" "Abinci zancen abinci ma kake kenan,to ni tunda ka kawo wannan masifar ko ruwa ban saka a bakina ba,kanace wasa nake koh,koka fita da ita kokuma nayi gidanmu. Kalli inda ta cijeni fah har yanzu jini bai tsaya ba" Masifa rammah take kan gari ya gari,akan koya fitarda Deejah a ɗakinta kokuma ta tafi gidansu. Ganin abinnata bana sanyi ne nan kusa ba yasa uwaisu ƙirna mazan gidan akan su fito da Deejah a cikin ɗakin. Ubaidu aka ƙira yaran gidan maza kaman su biyar akan su fito da itah. "Haba baba kace yarinya ce ƴar shekara sha biyu,miye kuma sai an ƙiramu kusan mu biyar,saikace wani gardi" Ubaidu yafaɗa da sanda a hannunsa yana dariya rainin hankali" "Uhm uhm ubaidu kudayyi a hankali,bakuga yanda tayiwa kazar rammah bane ɗazu,nan da nan fah ta cinyeta a gabanmu,kuma itama kanta ramman data cijeta saida fatar da ɗaye" Ammi tafaɗa cikeda tsoro. Duk cikin mazan babu wanda ya yarda da zancen ammi,amma dai basu ajiye sandan ba suka shiga dashi. Deejah tana ganin shigowar mazan da sanda ɗakin ta tashi ta zauna. Kallonsu take kafin idonta ya sauƙa kan rammah da uwaisu waɗanda suka shigo daga baya. "Mazakuyimin da waɗannan sandunan,ke kika turo su ko dan kawai zan zauna a ɗakinki? Kaikuma dan kawai nace na yarda ka zama ubana na biyu shine zaka saka a dakeni" Cikeda mamaki bawai na tsoro ba take kallon su dukka,baƙincikine yasake shaƙar rammah,musamman data gano inda dejah ta kwanta,tajiƙe wajen jaraff da fitsari,hmm dama yaushe za'a raba wannan da fitsari,da batayi kashi bama.

Yakuke ganin shin Deejah zata fita daga ɗakin ramma kuwa????

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977 Auwal Sadiya First bank

Ko katin mtn ta nan 09035784150

VTU ta nan 2347068390570

Shaida kuma ta nan 09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[13]

"Ehh nina ɗakkosun su fita dake,au harma mamakin hakan kike,da a tunaninki zan zauna dake ne a ƙarƙashin rumfah ɗaya,kalli fah yanda kika jiƙemin gado,abinda ko ɗana baya yimin ƙatuwa dake. Ubaidu kuyi ta dukanta,shegiya aljana kawai" Ubaidu ne yakai hannu zai zawota daga kan gadon ta goce. "Ohh dama ta gaske kuke,naga aljanuma ai da basaso na zauna a jejinsu mun daidaita ballanta na kuma ku,nafiku iskanci bari ku gani. Kekuma da banyi niyyar yi miki komai ba,amma tunda kika nunamin kalarki bari kiga tawa" Tana gama faɗin hakan ɗakin yakama da uwa ta ko'ina,tsakiyar gadonne kujera ne,cikin ƙankanin lokaci hayaƙi ya turnuƙe ɗakin. Fita sukayi da ciki kowa yana toshe hanci saboda numfashinsa daya shaqe,rammah kuwa sai ihu take tana neman agaji na ɗakinta dayake shirin zama toka. Ruwa aka fara zubawa,jama'a tana kawo ɗauki daga waje,daƙyar aka samu wutar ta lafah,kayan ɗakinta kam saidai wasu idan tayi. "Jama'a ku taimaka ba kwa ganin ɗakina ne,komai na fah yana ciki,wayyo Allah na" Burburwa rammah take tana birgima a ƙasa,sai riƙeta ake zata faɗa cikin wutar,gidan yacika da mutane da kuma hayaniya. Har dare yayi gidan bai lafa ba,rammah kam ita akayiwa,babu abinda ta tsira dashi a ɗakin sai ginin kawai,zuwa lokacin tama daina magana sai bin mutane da ido.

___***__

[Sumaimah a mahangar gani]

Jiya harna kwanta inajin hayaniyar su Tunga a ƙofar goje,bansan lokacin dasuka tafiba har bacci ya ɗaukeni. Ko a nan suka kwana ma oho. Yanzu dayake ni kaɗai ce a ƙofar innan kaman kullum bayan nayi sallahr asuba komawa bacci nayi,bani na tashi ba saida safiya tayi. Kuɗin koko nah na miƙa ta katanga maƙwantanmu yaranta suka miƙomin,bayan na shanye na haɗa kayan wanke wanke nayi. Yau dawuri nagama ba kaman koda yaushe ba,mai yafaru gaji basa 'bata kwanuka da yawa ba yau?. Bayan nagama vanyi shara ba,saboda gidan bayyi dattiba shima kaman koyaushe,sai a sannan na tuna ashe ƴaƴan ta basu kwana jiya gidan ba,suna can gidan kakaninsu. Har na zauna goje ya faɗomin a rai,koya fita ko yana nan oho. Tashi nayi a hankali na nufi Ƙofar tasa,zuciyata ta kasu kashi biyu,ɗaya nacewa kar naje,yayinda ɗaya kuma take cewa na kawar da tsoro na naje na duba. Shurun danaji ne yasaka na kula babu mutum a ƙofar ya kulle ma da makulli. Saidai kaman yanda Tunga yafaɗa kam anyi taro,dan wajen kaca kaca yake kaman kasuwa. Kalle kalle na fara a ƙofar,banma san haka take ba sai yanzu,ba laifi tanada ɗan girma.. Banɗakin na tura shi a buɗe yake,saida na razana dan yadda yahaɗa uban datti na ganyen bishiyar dayake zubowa a maƙwantai.ga kuma kaya daya jibga a cikin banɗakin na wanki. Komawa ɗakin inna nayi na ɗauko tsintsiyah,na yanke hukuncin share wajen,koma mai zayyimin saidai yayi,wahala bata kisa indai ba kashenin kuma zayyi ba. Tsakar ƙofar na fara tattarewa dattin na share,kana na koma kan banɗakin. Kayan daya tara himmm a na ɗebe,har ƙwari sunyi gida a ƙasansu saboda daɗewa da sukayi a wajen. Banyan shima na gama shareshi kayan na ɗebo na fito dasu zuwa ƙofar inna. Dama inada sauran sabulun da inna tabarmin dashi na wanke kayan tass,nasha wahala kam kafin su fitah,saboda dauɗar da sukayi ba kaɗan bace. Bayan nagama shanya su nan da nan suka bushe,da sauri kuwa na ɗebe su na naɗe. A bakin ƙofar ɗakinsa na ajiyesu na dawo da sauri saboda kar yazo ya taradda ni a wajen. Daga ƙofar tasa bayan na fito wajen gaji na shiga na ɗora mata girkin rana,dan indai tace zata bani abinci kaman na jiya bazai isheni ba. Kaman kurame tsakanina da itah haka muka gama girkin,ta zubamin nawa na ɗauka na dawo. Bayan naci nayi wanka na nai bacci,gidan shuru babu wanda zanyi magana dashi,nayi kewar inna sosai. Da daddare har na rufe ƙofah naji ana bubbugawa,ban buɗeba sai nace wanene?. Shuru naji babu amsa,har gaba ya buga,can kuma sai naji kamar muryar Atika tana nishi. Buɗe ƙofar nayi na sameta a tsugunne a bakin ƙofar tana riƙeda ciki,sai fidda wani numfashi take na wahala. "Atika lafiya mai yafaru naganki a nan da darennan?" "Ni in zaki matsamin na shige ki matsamin,wayyo cikina sai tsage wayyo na shiga uku,Sageer ya cuceni yagama dani" Matsawa gefen nayi kaman hoto na bata waje ta wuce,duk yadda akayi akwai wata a ƙasa,kuma da alama batason gaji ta sani. Bayan na bita zuwa ɗakin gani nayi ta ciro tsumma a ƙasanta ta ajiye,duk ya baci da jini,jikinta sai rawa yake amma dan dauriyar zuciya haka ta gyara jikinta a daren,zanin inna ta ɗauka da ta saka kafin ta dawo ɗakin. Nidai har sannan ina zaune kaina yayi murfi da wannan lamari,yau mai nake gani haka a kan idona ni Sumaimah. Gadon da nake kwana lokacin da inna tana nan ta nufah zata kwanta,bayan ta ciro wani magani a jakarta tasha. Kasa jurewa nayi hakan yasa nayi magana,ko bazata kulani ba saina tambaya.. "Atika menene haka yake faruwa,kaddai......" "Ehh shine,abinda kike tunani ba shiɗinne dai wato ciki. Ciki na zubar saboda banaso gaji tasani shiyasa ka na shigo nan,ko zaki faɗamata kai?" Maganar tata ta dakeni sosai,wai anya kuwa tasan girman laifin data aikata kuwa,har take da bakin wannnan ƙwarin gwiwar?. Nida bani na aikata ba har yanzu jikina rawa yakeyi,wai wannan wane irin zamani ne Allah ya kawo mu ne haka,ace irin wannan babban laifi yazama ruwan dare kowa yi yake? Cikin sassanyar murya ta jan hankali na fara yi mata magana. "Atika kinsan irin tarin girman laifin da kika aikata kuwa,kinsan shin wane muni ne dashi dakuma matsayinsa a musulunci harda mahaliccinki. Sannan kinsan irin wuƙar da kika ɗauka kike da'bawa kanki saboda wannan halayyar. Inda kinsan me waɗannan abubuwan suke nufi da bazaki aikata abinda kike ba,koda kuwa anyi yunƙurin tursasaki ne,amma kuma wai da saninki kike aikatawa,kisa fah kikayi atika naran da bai yiwa Allah komai ba. Abinda Allah maɗaukakin sarki yace. ”daka ɗauki ran bawansa wanda ya kasance bai aikata komai ba ko mumini,gwanda ka yaye sama da ƙasa idan har zaka iyah” "Amma ke kin aikata hakan hankalinki kwance kinzo nan wai kin 'boyewa gaji kada ta ganki saboda kina tsoronta ita ta haifeki,shikuma wanda ya halicceki a gabansa kikayi komai batareda kina tsoron yana ganinki ba. Kuma a hakan ace za'a ga daidai a rayuwa?" Tunda nafara maganar shuru kakeji bata ce komai ba,sai can naji alamar sheshshekar kukanta.. Shin magana ta ce tasakata kuka ko kuma ciwo takeji oho. "Hmmm Sumaimah kenan,a zatonki ni banajin zafin rayuwar dana tsinci kaina naganni a ciki.Ni bazanyi aure ba,banga wata fa'ida da yinsa ba,indai aure irinna iyayenmu ne gwanda banyi ba. Mace na buƙatar namiji da kuma kayan more rayuwa,wannan yake kaini wajen maza" "To idan kuwa hakane yake kaiki wajensu akwai fa'idar yin aure kenan,tunda abinda kika lissafo suma suna cikin aure,sannan batun bazakiyi aure ba saboda kinga rayuwar iyayenki hakan ba hujja bace dazata baki lasisin yin zina da kuma kashe rai Atika" Zuwa yanzu raina ya baci da furucinnata,wannan wane irin son raine mu mutane muke da shine. "Kinga Sumaimah dan na barki kinyi wannan maganganun kuma kinga sunyi tasiri akaina bashine zai baki damar faɗamin maganganu ba,rayuwa tawa ce,nikeda ikon yin abinda naga dama da itah. Banga abinda zaisa nabar ciki a jikina kam na haifeshi na shege,saidai in narasa yanda zanyi,ai hausawa suna cewa da kunyar duniya gwanda ta lahira" "Allah koh,zamuga in muka je ko hausawan zasu ƙwaceki ai,Allah ya shiryeki dami gabaki ɗaya" Ina gama faɗin hakan na haura gado na kwanta,ita sani ai duniya ce ta ishi kowa riga da zani harda na yafawa ma. Da asuba tayi ni kaɗai na tashi nayi sallahta,atika nasan ko wannan abun bai faru bama ba sallahr asuba zata tashi ba,inaga kuma ta samu dalili. Bayan nayi sallahr ban komaba saina cigaba da karatu,ina jinta tana tsuka na dameta,bance mata komai ba ban kuma daina ba har na gama. Na gama rufe ƙur'anin kenan naji muryar goje a bakin ƙofa,wani daram naji wanda duk sanda nayi arba dashi sai hakan ta faru,ko yaushe zan saba da wannan mutumin oho. Da sauri na jawo ƙafata na fito wajen,muna haɗa ido dashi na sunkuyar da kaina. "Keee wacce irin mai kan tumakai ce ke? Tun shigowarki gidannan nace ba ruwanki da shirgina amma bakiji ba koh,wato kilaroro zakiyimin irinna ku na mata,an zugaki kidunga shiga harkata koh?,meyasa kika tabamin kayana dasuke banɗaki,nasan ba inna bace tun da bata nan" "Kayi haƙuri tunda bakaso hakan bazai sake faruwa ba,naga wajen yayi dattine kayan ma kuma sun daɗe a wajen,shiyasa na gyara saboda na samu ladan yiwa miji aiki" "Hehehe miji? Tanan kika bullo,saboda kinga gidanmu ɗaya shine har nake magana kina mayar min koh. To tunda miji zaki yiwa aiki kizo sashena na baki aikin miji ki dungayi,ba aikin miji kikeso ba,zaki samu ai akwaishi da yawa" Yana gama faɗin hakan ya shige ƙofar tasa yana tafiyar isa,jikinnan a murɗe kana ganin hakan ta jikin ɗamammiyar rigarsa. Nashiga uku ni Sumaimah mai yake nufi da zai bani aikin miji,ni mai yasama na shiga shirginsa ne bayan ya hanani,yanzu gashi na jawowa kaina,ko mai zai faru oho?. Haka ina ji ina gani na kawar da waɗannan zullumin na nufi sashennasa kaman yadda yace. Wannan shigar har nafijin tsoro akan shigar danayi jiyah,ga sanyin safiya sai karkarwa nake. A zaune yake akan wani tsohon bokiti na ƙarfe a tsakiyar filin wajen,duk sanyinnan da ake daga shi sai singlet da three quater na wando. Wayyo nikam ko maza haka banason ganinsu a irin wannan shigar ballantana wannan mai suffar dodannin.. Jan ƙafafuna nayi har gabansa na tsugunna,gudun kada na tsaya ma na gamu da wani laifin akan wanda nayi. Ƙaremin kallo yake kaman mage tasaka bera a gaba,saida yayi ya isheshi dan kansa kafin yayi wata ƴar dariya. "Tunda kin zabi shiga rayuwata,duk da cewar na gargaɗeki to ba komai zan barki ki shiga,da farko dama ina neman sabon yaron dazai dunga kula da saniyar can,tunda gaki tazo gidan sauƙi,zaki dunga ɗebo ruwa a rijiyar ƙofar gida kina min wanki da kuma bawa saniyah kina cikamin zan dunga bar miki makullin ɗakina ki dunga gyarawa,komai yazamo yanda nake sonsa,idan har naga kuskure guda ɗaya daga cikinsu toh ki saurari hukuncinki a matsayinki na wacce takasa cika ayyukan miji" Yanda kake faɗan mijin kasan abin wasa ma ya maida kalmar,wai harda saniyah zan kulada itah,babu wanda ya fi batamin rai ma kaman ɗiban ruwan,saboda kawai ya tozarta ni bazai iya bawa yara su ɗebo ba saini? Menene laifina dan nayi masa wanki nayi masa shara,ni wanne irin mutum ne haka Allah ya hadani dashine kam. Allah ka dubeni ka fitar dani daga cikin wannan ƙaulin.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977 Auwal Sadiya First bank

Ko katin mtn ta nan 09035784150

VTU ta nan 2347068390570

Shaida kuma ta nan 09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[14]

Har na gama aikina na yau ko yaushe a gidan da safe,Ƙwalƙwalwata ta gagara barin Tunanomin abinda gojen yacemin,tabbas kam yanzu na yarda ba daidai yake da sauran mutane ba,wai a hakan ma yanda nake tunanin zayyi min bai yimin ba. Na ƙara tabbatarwa bazan taba samun matsugunni a wajensa ba ballantana nayi wani tasiri a cikinta,amma kuma ta wani wajen a zuciyata yana cemin wataƙila tunda har ya yarda na taba kayansa zan iya samun nasara koda watarana ne. Duk da cewar ayyukan daya bani mutum ko ƴar sa ne bazai saka ba ballantana kuma matarsa,koda yake mai yasa hakan zai dameni,nasan dama bazan samu wannan matsayin ba,ga kuma..... Firgit nayi na dawo daga duniyar tunanin jin an wullomin abu a jikina,ɗaga ido nayi caraf sai a cikin na goje,wanda yake min kallo mai haɗe da harara. Saurin sauƙe idona nayi,ananne naga ashe makulli ya wullomin,na dakinsa ne kenan,na faɗa a raina. "Kije kewayen can saniya ta tana ciki,daga yau kulada ita yana hannunki,akwai abincin ta a gefen wajen,sannan ki cikamin randa ta kullum da ruwa,ki gyaramin ɗaki waɗancan yaran sun wargaza shi,amma ki tabbatar komai yana muhallinsa,naga kin iya wanki akwai kayana suma ki wanke su" "Toh shikenan" Har yakama hanyar fita waje sai kuma ya dawo,. "Ko ɗayane ya kuskure vakiyi ba.......saikinyi ɗiban ruwa sau ashirin kina yiwa gidannan ban ruwa,idan kuma ya wuce ɗaya baki cikaba sai na rufeki a ɗaki da su durwa,basai na faɗamiki abinda zasuyi ba kinsan menene" Yana cikin maganar ne ƴaƴan gaji suka shigo gidan da gudu sun dawo cin ɗumame daga makaranta,gudu suke basu kulada wanda yake gabansu ba,aikuwa suka bangajeshi zasu wuce basuma kulaba. Har sun kusa isa ƙofarsu ya daka musu tsawa. "Kaiiii.....dukku ku dawo nan ku zube" Wata karkarwa suke amma ba bakin magana,su haɗune,ƴar babbar itace mai bin atika,sai kuma ƙannenta biyu maza ɗaya mace,ƙaninta ne gaji take goyo ta yayeshi. "Dan Allah yayah goje kayi......" Kallon da yayi matane tayi shuru bata ƙarisa ba. "Jeki ƙofata ki ɗaukomin bokitin danake zama,dama tunda kuka dawo babu wanda na saita a cikinku koh,ita kanta uwartaku dama na kula ta mantani har maganata take ina jiyota daga ɗakina. Ku fara tsallen ƙwado kuna zagaya gidannan,kuga ƴan iska koh.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull