Sanadin caca book 1 complete - Chapter 12
Sanadin caca book 1 complete Chapter 12: Sanadin caca book 1 complete Chapter 12. Da safe ina zaune naji muryar hamisu ƙanin Shareefah,tashi nayi na fito…
3,315 words
Da safe ina zaune naji muryar hamisu ƙanin Shareefah,tashi nayi na fito daga ɗakin na karbi kwanon hannunsa. Godiya nace yayiwa ummansu da Shareefah kafin koma daki na rufe ƙofah. Ƙosai ne a ciki mai zafi sannan aka soyah,da murnata na zauna na cinye tass nasha ruwa. Gado na koma na sake kwanciyah ban fita ba kaman koyaushe,dan dama haka na kimtsa zanyi ɗin. Can wajen kaman shaɗayan rana naji ana ƙira sunana,muryar namiji ce amman ba goje bane. Saurin tashi nayi zaune na mutstsike idanuwana na fito. Da tunga muka haɗa ido yana can ɗan gefe da baranda a tsaye. Muna haɗa ido murmushi yayimin kana ya kauda idonsa. "Ina kwana matar ogah" Uhm wai matar ogah manya,na faɗa a raina,a fili kuwa ɗan murmushi nima nayi tareda cewa. "Lafiyah kalau Tunga ya zirga zirga" Amsa wa yayi a taƙaice kafin yafaramin bayanin abinda ya kawoshi. "Uhm gashi wannan ki riƙe a wajenki,nasan ba lallai yabaki wani abun ba dazai tafi" Mamaki yabani ganin ya miƙomin dubu biyu. "wannan kuɗin fa na menene" "Ko zaki siya wani abun idan buƙatar hakan ta taso,yace bayan ya tafi na kula da duk al'amuransa,baice da harda iyalansa ba amma kuma ninaga kema yakamata a baki wani abin a kuɗin da muka samo,koba komai bazaki rasa abin siya ba" "Kulada al'amura,tafiyah yayi ne?" Na tambaya cikeda mamaki. Shima saida ya zaro ido jin irin tambayar danayi masa,yo ba dole yayi mamaki ba,yaji mata batasan mijinta yayi tafiyah ba. "Ohh bakisan cewar yayi tafiyah,wani aikine ya taso wanda ya samu bada daɗewa ba,shine suka nemeshi jiyah akan zai fara aikin,yacemin dai na kula masa da komai sati guda zayyi ya dawo. Laah kuma hakane ba lallai ki sani ba,dan yace na faɗamiki kada komai da kike na aikinki ya sauyah,kiyi shi tamkar yana nan" Ɗaga kai nayi a zahiri,yayinda ta baɗini kuma zuciyata tayi baƙiƙƙirin,wato zayyi tafiyah amma bai faɗamin ba,saima aikowa dayayi akan nacigaba dayimasa gyare gyare,tunda yake baisan cina ko shana ba saidai nayi masa aiki koh? Idan dan yana ganin ya sameni ne ta sanadin caca ai Ko dabbarsa ma ta sanadin wasan kalankuwa ya samota,amma yana kulada ita sosai,sai nice wato zai maida goruba koh?. Ɗagawa Tunga kai kawai nayi,dan bansan mai zance masa bama. Allah ya dawo dashi lafiyah,shine abinda nasamu cewa bayan Tunga ya tafi. In kulada shi yaso ya bani haƙuri,ganin banason hakanne yasa ya tafi. Ina nan tsaye a wajen naga gaji ta fito daga ƙofarta,wajenda kayan wanke wankenta suke,ƙuda yabisu yabisu har sun bushe saboda daɗewa a wajen. Tsayawa tayi a gaban kayan tana kallonsu, kursiyyahce ta kawo kwanon dataci awara zata ajiye a wajen. "Ke kursiyyah kije ki ƙiramin kawule ya debomin ruwa kuyi wanke wanke" "Wai nikam gaji wlh bazanyi ba,haka kawai naga tun safe aka ce Atika tayi tace bazatayi ba,saini za'a saka" Ƙofar tashige tana wani wantsala kamar tarwaɗa. Nidai ina nan tsaye ina kallonsu. Da rana ma hamisu ne yasake kawomin abinci,amma sannan kam nace masa kada ya sake kawowa. Dan kafin ya kawomin kursiyyah ta kawomin shinkafa da wake mai da yaji,wai gashi inji gaji nacigaba da aikina na safe. Murmushi nayi ganin kwana ɗaya kawai harta daddara ta dawo hanyah. Ban musa ba na karba,danni ma daman hakan nakeso,banason kawomin abincin da ake daga gidan su Shareefan. Ɗaukar daya nayi daga cikin abincin naci,ɗayan kuma na ajiye na yamma. Washagari da safe ɗumame kaɗan ta gaji tabani,duk yadda naso abin ya tafi yanda zamuyi zaman lafiyah nasan hakan bazai faru ba sam,dan haka tunda nice mai son mu daidaita dole ni zanyi haƙuri da itah,kaman yanda naga inna tana yi da itan,gobe inna zata yi sati guda da tafiyh,sauranta sati ɗaya ta dawo kenan. Kuɗin da Tunga ya kawomin na ɗako dubu ɗaya a ciki.Soda ta kawomin nayi wanke wanken,sabulun danakeyi dashi ma dama yaƙare wanda inna tasiyamin,nayiwa goje wanki dashi. Hijabina na saka wanda nake sallah na fito waje ko zanga wani a cikin yaran unguwa ya sayomin sabulu da omo. Na ɗan daɗe a tsaye kafin na samu wani almajiri da robarsa a hannu yana wurgawa sama. "Dan mallam dan Allah zo na aikeka mana" Na fada ina ƙirnsa da hannuna,tahowa yayi da hanzarinsa,kayan jikinsa na kalla,duk sun yayyage sunyi daƙan daƙan dasu,yana dosoni sai zarnine yake tashi. Wai rayuwa kenan,wato idan kaga rayuwar wani dole ka godewa Allah. "Iyah ta gani" "Yawwa dan Allah omo zaka siyomin da sabulu a wancan shagon" "Tah" Karba yayi ina kallonsa ya nufi shagon,kasancewar ba nisa ina hangoshi har yaje ya dawo. Hamsin na dauka a kuɗin na bashi,ya karba yana godiyah ya tafi,nikuma na shigo gida. Ƙofar gaji na shiga siyan awara,tunda nasamo sanji. Sallama nayi ta amsa ciki ciki,bata huce ba kenan. "Gaji a bani awara ta ɗari" Nafaɗa ina miƙamata gudan ɗari biyar ɗin da aka bani a canji,tsayawa tayi tana kallon kuɗin naɗan lokaci kafin ta karba. "Tohh amarya an fara samun kuɗine a wajen miji?" "Amarya bazata samu kuɗi ba dole sai in miji ne yabata?" "To ba cass bare ass,kana kuma babu jiyarar ƴan uwa,ai dole mu tambaya" "Akwai wasu marasa cass da ass ɗinma a gidan dasuke siyan kayan masu cass da ass ai" Hmm tace kawai kafin ta ƙirgamin awarar,dan tagano da Atika nake ƴar ta,shigar kaya a gidannan wanene ya kaita,kuma ba sana'ar fari bare ta baƙi,kuɗin jikinta sunfi na jarin awarar ma. Canjina ta miƙomin na ɗari huɗu da kuma awarar tawa. Karba nayi bansake cewa komai ba na bar ƙofar,zama nayi na cinye tass nasha ruwa kafin na fito yin wanke wanken. Ga ɗiban ruwa ma yana jirana na randa ta data goje,da kuma saniyar can,dan dai kar a ɗaure dabba a hanata abincine tausayi ma bazai barka ba,da wlh bazan sake bata komai ba sai ranar dazai dawo,hmmm ga gyaran ɗakinsa ma,shima bazanyi ba sai ana gobe zai dawo inyaso. Wani satinne ina? Kafin sannan ma idan nayi sa'a inna tadawo lokacin.
__**__
"Toh sabon salo lallai yarinyar nan in banyi da gaske ba tsoronta zan faraji a gidannan..a ina tasamu kuɗi haka hadda sanja ɗari biyar,naga siyayya tayi na sabulu da omo ma a leda" Buɗar bakin kursiyyah wacce take zaune a gefe sai cewa tayi. "Ai inna Tunga ne wannan abokin yahya goje ya kawo mata kuɗin,dan ina banɗaki naji yana cewa wai,gashi ta rike kafin gojen yadawo. Tafiya yayi kuma zayyi sati bai dawo ba" "Ke ƴar nan,kenan baya garin? Haba biri yayi kama da mutum,shiyasa ban ganshi ya shigo gidan ba har zuwa yanzu,wato kuɗi aka kawo mata ta dunga kashewa kafin ya dawo koh. Kuma ta rasa mai zatayi sai siyan omo da sabulu?" "Wanke wanke zatayi mana dashi" "Naga na aika ki kaimata sodar wanke wanken,wanne iyayine sai tayi da omo,kaman wata ƴar gayu,kowa ma ai da sodar yakeyi" "Ohh gaji baki sani ba,ranar naji tana faɗawa inna wai intayi da soda hannunta tsatstsagewa yakeyi" Barin ƙirga awarar gaji tayi tana kallon kursiyyah,wacce tagama shirin fita tallen safen. "Oho dama hakane,ya akayi bansan zancen ba kuwa,ni inacan ina tunanin banza,ga hanya mai sauƙi wajen kamata da hannuna,sai nayi mata abinda da ƙafarta zatazo har wajena ta tsugunna,badai ni take mayarwa magana ba" Gaji ta ƙarisa maganar tana murmushin mugunta.
Oohp anan zan tsaya fah sorry baikai sauran ba da shafi huɗu,wlh na gaji ne shiyasa🙏🏼 muhaɗu gobe kawai.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977 Auwal Sadiya First bank
Ko katin mtn ta nan 09035784150
VTU ta nan 2347068390570
Shaida kuma ta nan 09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[18]
Nafito kenan daga ɗaki naga ɗan gaji kursiyyah tana wanki da sabuluna,mamaki abin yabani sosai. Da sauri na ƙarisa wajen nace. "Kursiyyah me kike da sabuluna,bakuda shi ne saikin ɗau nawa?" "Bamudashi ya ƙare,shine gaji tace na ari naki taga kin sayo rannan" Jimmm nayi ina jinta cikeda takaici,wannan wacce irin rayuwa ce,ace mutum bashida katabus na rayuwarsa,kallon sabulun nayi a hannunta ya kusa ƙarewa saura ƙiriss,gashi gobene cikar sati guda da goje zai dawo,inna ma a satin gaba nake saka ran ganinta. Miƙa mata hannu nayi ta bani sabulun,bance komai ba na nufi ɗaki,kuɗin dana ajiye dubu ɗaya a wanda Tunga yabani na tafi zan ɗauka,dan omon danake wanke wanke dashi shima ya ƙare,saina siyo dukka. Kwanon na jawo a cikin carbet ɗin inna inda kuɗin yake,amma mee.....ina buɗewa dubu ɗaya tace ɗaukeni a hankali. Wata razana nayi ina jijjiga kai,ahah ahah haka bazai faru ba samm,meyasa toh meyasa hakan zata faru? Waye ya ɗaukemin kuɗi,sannan a wanne dalili? Hawayene suke zubomin ina kallon kwanon,amma sam na gagara taresu ballantana na hanasu fitowa. Saida nayi mai isata kafin nayi shuru,nasan babu wanda ya haɗa abinnan sai gaji,wato ita dai duk hanyar dazaya wulaƙantani in bata bi ba batajin daɗi koh?. Tunani natafi meyasa toh ta aiko ƴar ta ta ɗaukemin sabulu,sannan kuma suka sace min kuɗin,kaddai gaji ta gane banason wanke wanke ko wanki da soda kai?? Inkuwa hakane wannan kam shine dalili. Tunowa nayi da kayan goje da ban wanke ba akan sai yau tukunna,ga kuma gyaran ƙofarsa shi ba na tashi sam. Guntun sabulun na ɗauka nafita waje,wankin kayan zanyi kafin lokaci ya ƙure. Basuda yawa kayan dan haka sabulun ya isheni na wanke su tass,ina gamawa ƙofarsa naje na gyara itama kafin na dawo ɗaki na kwanta. Sauran wanke wanke shikuma ya zanyi dashi,shine hanyar abincina kaɗai,dan haka dole nayi,kuma ko a shari'ah tafita tunda tabani abinda suma dashi suke wanke wanken. Shareefah ce tafaɗomin a raina,amma nayi saurin kawarda tunanin ta,ahah bazayyiwu dan naga tana taimakamin shikenan daga matsala ta tasomin saina tunkareta ba,rayuwata ce gidan aure na ne,dan haka dolene na maganceshi da kaina basai wani ya taya ni ba. Ina nan kwance ina duniyar tunanin kirsiyyah tashigo da kwanon abincina,dayake na kula bashine target ɗinta ba hanani abincin,koban je ba tana kawomin. Ajiyewa tayi a tsakar ɗaki,harta tashi zata tafi nace. "Ke kursiyyah a cikinku waye ya shigo ɗakinnan ya ɗauki dubu a cikin kwano?" Dafe ƙirji tayi tareda zaro ido,daga nan kuma saita zunduma ihu ta fita da gudu tana kuka kaman na zare mata rai. Da kallo na bita bakina a sake,anya waɗannan yaran mutanene,yara ƙanana daku amma duk kuna fanɗare,tashi nayi na zauna,dan nasan gaji tana zuwa. Aikuwa hasashena bai tafi a banza ba,in gama zama najiyo sababinta tana tahowa. "Dan tsabar munafurci da samun wajen zama,har kin samu bakinda zaki ƙira ƴaƴana barayi,uban me kika taba kamasu sun ci miki tunda kike?" Har ɗakin tashigo ta riƙe kunkumi tana tayi,nidai kallonta nayi sau ɗaya kafin na ɗauke idona. Ta inda tashi ba tanan take fitaba harta gama wanda ya isheta tafitah. Wani hawayennne naji yana shirin zibomin na takaici,kai.......shima bai isa ba,yayi ta jiƙemin fuska Kenan,ya isheshi haka yayi rabonsa. Kwanon abincin na ɗauko na cinye,dama ban taba ƙoshi dashi ba,cikina har ya saba da wannan. Alwala na ɗauro nayi sallah,daga nan kuma sai bacci,dan shikam babu laifi ina samunsa a gidan,bakaman gidanmu ba. Ban daɗe da kwanciya ba kukan saniyar goje ya tasheni,da sauri na fito daga ɗakin na nufi kewayennata,kar itama a sace ta kamar kuɗina,goje yazo yace nina sayar ta,inada a ranar kwanana ya ƙare a duniyah. Bayan mutum naga yana jujjuyata,gabana ne yayi rass,ban saduda ba dai nayi ta maza na leƙa. Da Tunga muka haɗa ido,aikuwa sai na sauƙar da ajiyar zuciyah himmm. Shima daya fuskar tawa saida yayi murmushi. "Ohh kinace barawo ne,in banda abinki wanene a cikin garinnna sai saci sanuyar goje?" "Uhm to duk da hakan dai" "Dama nazo gyara wajennata ne,wataƙila gobene zai dawo,duk da yace ki kulada ida amma nasan ba lallai ki iya gyara wajen ba." "Hakane kam nagode sosai tun......uhm wai menene ainihin sunanka ne?" Danni banason waɗannan sunayen haukar dasuke sakawa kansu.. Jimm yayi kaman mai tunani,can kuma sai yace. "Sunana Al'amin" "Suna mai ma'ana amma ka boyeshi,nagode al'amin barina tafi to tunda naga kaine" Ohh a zuciyata ji nake kaman nace masa su gaji sun ɗauke kuɗin daya bani,amma nasan hakan ba abune mai yiyuwa ba,bazan iyah faɗaba sam. Haka na bar wajen na nufi ɗakin inna. Tun ana gobe goje zai dawo har an kwana huɗu babu shi babu alamarsa,inna ma dazata dawo tun jiya bata dawoba. Ko bazasu dawo bane guduwa sukayi suka barni,ni bata goje nake bama,in yanaso kar ya dawo tacan tacan huta roro,amma inna ji nake kaman mahaifiyata ce ta tafi tabarni. Jiya bacci dan barawone shiyasa yasamu damar ɗaukata,tunani sunyimin yawa barkatai,ga kuma ciwon ta hannyena sukeyi na yin amfani da soda. Da ita ake amfani a komai na gidan,har wanka ma saita aiko su kursiyyah waisu kawomin,saboda tsabar munafurci da mugunta. Duk matakan danake bi wajen bata taba hannuna sosai ba dole saida tayimin illah a ƙarshe,kwana biyar ne kacal dana fara amfani da ita,amma sai kace an saka hannyena a wuta matar ta tashi haka suka koma. Shi kansa abincin ma bata bani wanda zai isheni yanzu,banda karkarwa babu abinda jikina yakeyi wani lokacin. Gunwa zanjene ma da matsalata,gidanmu zanje wanda sunsan dama da hakan suka kawoni dan su rabu dani,kokuma ƙawar tawa da banida aiki sai ɗora mata wahala. Gaskiya hakan da kunyah,zanyi haƙuri na zauna,idan har ajalina kenan Allah yasa na cika da imani. Warware hannyen nayi da tsumman danake sakawa indai zan taba ruwa,ko kuma abu wanda zamemin illah. Hanyar wajen saniyar sa na nufah domin zuba mata abinci,da inajin haushin sakamata abinci,amma yanzu itama tausayinta nakeji,wai a yanda nake ɗinna ita kuma dani ta dogara na zuba mata abinci,nida ko bani nawa ya isheni ba'ayi. Kwanonnata na ɗauke zan ɗebo mata dusa,saidai me.....da kayan goje na haɗa ido a cikin kewayen saniyar,duk ta takasu sunyi duƙu-duƙu kaman basu taba ganin ruwa ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Shine dai kaɗai abinda bakina yakeda ƙarfin amsabatawa. Ɗiban kayan nayi na taho dasu zuwa ƙofarmu. Sakasu nayi a gaba inda kallonsu,harda singlet ɗinsa da komai ma na kayansa aka zuba a wajen,sai zarnin fitsarin saniyah sukeyi. Yanzu shin taya zan fara wanke kayannan,kayana ma bana wankewa bazan iya ba,hannaye na bazasu iya gurzawa su fita ba,inaga kuma waɗannan harda su jeans,na iyah wankewa. Sakasu nayi a cikin ruwa na zuba sodar akai na ajiyesu,idna suka jiƙa saina wanke. Tun da rana har dare,idan naje wankewar ina fara mitstsikawa in ciwo ya ratsani saina ajiye na tafi,naga ta kaina nikam a gidannan,taya zan rayu da haka?. Da daddare haka nayi yarfe hannu har bacci ya ɗauke,yanzu yakai ko tafasu a sallah banayi,inaga idan naje asibiti yankesu zasuyi suce sun rube,inaji ina gani za'a maidani kuturwa???? Gaskiya gobe dole nasan abinyi..... Washagari da safe na tashi zan yunƙura kenan naji zuutt a marata..wata sabuwa kenan inji ƴan caca. Wayyo shima ciwonnan wannan watan kam da yayimin uzuri mana,kenan wasa wasa na kusa wata a gidannan. Yunƙurawa nayi na tashi zaune ina cije baki,saboda riƙewar da marata tayi gamm. Banɗaki na lojana naje,daga nan na dawo ɗaki na kwanta,shigowar kursiyyah nagani da ajiyemin ɗumame. Yauda masifa kenan,na faɗa a raina. Cinye tuwonnan zanyi bazan barshi ba,idan kuma ta gano naci tuwonta banyi wanke wanke ba bansan yazamu ƙare ba. Duk da ciwon danake ji haka na daure na sauƙa ƙasan ɗakin,buɗe kwanon nayi mukayi ido da ido da karin tuwon guda ɗaya. Dama kullum ɗaya take sakamin kaman rai.. Miyar babu daɗi haka na suɗeshi,jinsa nake kaman nama saboda yunwa. Amai nafaraji yana tahomin,dan dama ko a gida haka nakeyin al'ada da wuyah,kowanne wata saina sha wahala a ranar farko. Komawa nayi kan gadon inna,nayi rigingine ina kallon sama,saboda amai ɗin ya koma. Idan na bari tuwonnan ya su'buce daga cikina bansan lokacin dazan samu wani abincin ba a yau.
[Goje a mahangar gani]
Kwana goma kenan tunda muka tafi wajen aikin,fasa banki mukaje yi a gwagwalada,to bayan munyi da alama ƴan sanda da sojoji sun sani da wuri,hakanne yasa aikin ya baci,aka kashe wasu daga cikinmu,wasu kuma aka kamasu. Mudai bamufi mu huɗu ba muka tsira a cikin mutum sha biyar . Jeji muka furma da guda har sannan kuwa bamu jefar da kuɗin da muka ɗebo ba yana wajenmu. A jejin muka buya tsawon wannan lokacin,saboda neman da jami'an tsaro suke mana. Munsha baƙar wuyah muka dawo sansanin ƙungiyar. Masu jiran ƙofar ne suka buɗe mana muka shiga,bayan sun gama bincike mu tukunna. A gajiye muka wuce inda ogan yake muka jefa masa jakunkunan kuɗin. Saida ya ƙaremana kallo saikuma ya tuntsire da dariyah yana nuna mu da hannu. Yayi kaman daƙiƙa biyar yana wannan dariyah kana kuma yayi shuru yana goge hawayen da dariyar ta sakashi. "Ku kalleku sai kace birirrika,da kyau da kyau,ni banyi zaton ma zaku tsira ba wlh,danaga baku dawo ba inace na kasheku ne" Numfashina sama sama yakeyi saboda baƙinciki,yayinda zuciyata ke rayamin na kasheshi kawai ya daina numfashi. Saidai haka na danni zuciyata nayi masa tambaya. "Meyasa kake tunanin zamu mutu?" "Saboda nina ƙira ƴan sanda da sojoji na faɗamusu zakuzo yin fashi a banki. To ya kaji toh,duk lokacin dana ɗebi sabin yara haka nakeyi musu,tahaka nake gwada jarumtar su,shiyasa bamuda mutane dayawa sai jarumai. Ya kaji salo.........." Tun kafin ya gama maganar nakai masa wani farmaki,fitt na so yanke maƙogaransa,saidai dayake ya san dabarun faɗa yagoce da sauri na sameshi a jijiyoyin wuyan sa na dama. Ihu yasaka yana dafe wajen,yayinda jini yafara tsartuwa yana wanke rigar jikinsa.. Yaran dazuke wajen da gudu suka ɗaukeshi zuwa wani wajen da bansan inane ba,yayinda nikuma wasu suka rirriƙeni zuwa wani ɗaki mai kama da prison. Idona a tsaye yake gamm babu alamar tsoro ko kuma nadamar abinda nayi masa,hasalima takaici naji da ban yanke maƙogaronsa ba. Ina nan a cikin cell ɗin har tsawon kwana uku,waɗanda suka kawoni wajenne suka fito dani. Kaya suka miƙomin iri ɗayah da wanda ogan yake sakawa,cikin girmamawa suka miƙamin kayan tareda yimin alamun na biyosu. Wani ɗaki suka nunamin nashiga,akwai gado a ciki da kuma banɗaki,ba laifi yayi kyau kam. Wanka nayi na wanke wannan ɗauɗar jejin,duk da ma ni ba gwanin tsafta ba,amma naji daɗi sosai. Kayan da suka bani na saka kana na fito. Cigaba da sakeyi da binsu har mukazo wajenda aka taramu da farko. Maimakon ogannmu yanzu wani mutumine sanye a suit akan kujerar. Bashida suffar ƙarfi amma kuma yana da suffar sanin duniya akan fuskarsa,sannan kuma kana ganinsa kasan kuɗi ya zauna masa. Murmushi yayi kana ya min alamar na matso,ba musu kuwa cikin nima nuna isata na ƙarisa wajen. "Goje kake da suna koh? Ka burgeni sosai ka burgeni da jarumtar daka nuna jiyah,wanda hakan yasa na baka matsayinsa,shiyasa ka ganka da waɗannan kayan. Saidai ba tsallen da kayi ya kawoka tabb da rijiyah,idan ka sa ke yin wani to zaka jika a ciki tsundummm,wanda zaka iya yin dubu baka fito ba. Nine shugaba na ukun da ake cewa zaku haɗu dashi in kuka tsallake aikin farko,a samana akwai shugabanni biyu,ni nabiyun nasani bansan na farkon ba,shigaba na biyune yasan wanene na uku. Dan haka barkanka da zamowa na hannun damana" Tafi yafara yayinda sauran ƴan kungiyar ma suka fara,lallai wajennan akwai haɗari,jiya na lahanta shugabansu har sun maidani a matsayinsa??.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977 Auwal Sadiya First bank
Ko katin mtn ta nan 09035784150
VTU ta nan 2347068390570
Shaida kuma ta nan 09035784150
Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------
Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150
*Duk wanda shafinnan yamasa daɗi yayi comment please,finally dai Sumaimah tah............ku karanta ku gani dai........*🤣🤣🤣 ________________________________ *Book 1* Chp[19]