Kenza eBookz

Sanadin caca book 1 complete - Chapter 13

Sanadin caca book 1 complete - Chapter 13

Sanadin caca book 1 complete Chapter 13: Sanadin caca book 1 complete Chapter 13. Gyara tsayuwa ta nayi bayan sun gama tafin. "To nagode shugaba da wannan…

3,248 words

Gyara tsayuwa ta nayi bayan sun gama tafin. "To nagode shugaba da wannan karramawar,amma batun rijiya ni dama dana so yin tsalle ba nufina zuwa wajen rijiyah ba,kaine ka kaini wajen rijiyar,dan haka yin tsallena na faɗa rijiyar ma duk yana wajenka. Mun tafi akan zamuyi sati ɗaya,gashi munyi sati biyu bamu koma gidaba" "Karka damu da wannan zaku kowa zai iya tafiya gidansu,aikinnan ya gamu saurna kuma nagaba idan yataso. Kuɗin da kuka samu nasarar ɗakkowa kungiya bazata karba ba an bakushi ku raba,su ɗau kashi ɗaɗɗaya su baka kashi biyu." Naji daɗin kuɗin tunda dama abinda yakawoni kenan ,amma nayi mamaki da banjisu a cikin raina sosai ba. Mota DON3 ɗin yabani kyauta,saidai nace masa banaso,danna kula a ɗan tsorace yake dani karna yi masa tawaye kaman oganmu,amma ni bashine a gabana ba sam,so nake naje naga wacce wainar su Tunga suke toyawa. Madadin haka wani na ɗauka a mutane wajen ya tuƙoni zuwa garinna mu wanda yake district ɗin gwagwaladanne. Da daddare na iso,ban wuce gidaba sai kawai na nufi madakatarmu,babu kowa dan haka kai tsaye ɗakina dayake cikin jejin na nufah. Jakar kuɗin na ajiye kawai nayi kwanciyata,saboda narama baccin wahalar da banyi ba kwana da kwanaki. Hasken ranar daya hudo ta rufin ɗakinne ya haske ido na,wanda hakan yasakani yin miƙa na tashi na zauna. Fitowa nayi daga cikin bukkar na nufi kogi,wanda yake a ɗan gangare idan mutum yayi ƴar tafiyah. Wanka nayi kana nayi alwala,salloli biyu ake bina,isha asuba da kuma azahar wacce akayi yanzu.. Ina cikin yin sallahr Tunga ya shigo bukkar,ganin ina sallah yasa ya tafi.Nasan abinci zaije ya kawomin. Bayan na gama jakar kuɗin danazo da itah na buɗe buzun dayake tsakiyar ɗakin,kuɗin na zuba a ciki sauran kuma na barsu a jakar. Jakar kayan aikina ma bazan koma da itah gidaba duk anan zan barsu. Shigowa yayi yana cikin rarraba kuɗin a kan buzu,kallo ɗaya yayi musu ya kawar idonsa tareda miƙamin kwanon abincin daya riƙo. "Ogah ga abinci,ka dawo kuma babu magana sai kawai naganka a jeji" "Kamawa tayine,a gajiye nake shiyasa banshiga garinnan ku ba,ya aikin dana barku dashi ya tafi?" "Yatafi yanda ake so,kawaidai kuɗinne bai bamuba,ana wannan matsalar sanjin kuɗin" "Ga wannan ka bi kan kowa da rabonsa,ni barina wuce gida na sanja kaya" Kuɗin na miƙa masa dami masu yawa,cikin fara'ah da washe baki kuwa ya karba. "Ogah ta samu kenan,shiyasa fah mukeyinka,inka samu kana yaga mana,ba kaman tsohon kwarkwaroncan ba daka gama dashi" A ƙaramar jaka na saka sauran kuɗin wanda zanyi amfani dasu na fitoh. Hanyar gida na nufah,kaman kullum kowa ya ganni sai ya sanja hanya. Ina shiga ƙofar tawa na ganta kaca kaca,yanda na tafi haka na dawo na sameta babu abinda aka taba. Buɗe ɗakin nayi na shiga,shi da alamar anyi masa shara kaman sau ɗaya dana tafi,cije baki nayi ina jijjiga kai,lallai ma yarinyar nan ta rainani. Cire kayan jikina nayi na zubasu gefe. Gajeren wandona da singlet nake nema,amma banga waɗanda nake son sakawar ba,nan na tuna su na cire lokacin dana tafi. Fitowa nayi na nufi kewayen saniyata,tana kallona tafara jujjuyawa,gabanta ƙwaraff babu abinci ko kaɗan. Saidai kuma amma babu rama a jikinta,to yaushe kenan take bata abinci,kodai ba ta bata kai?. Ƙofar innan nashiga a zuciye,mai zan gani kaya nagani a cikin bokiti an jiƙasu. Kuma indai ba gizo idanuna yakeminba kayana nagani a jiƙe a cikin bokiti,wannan kuma wanne wari suke fitarwa haka. Nasan dai kayana duk dattinsi bazasuyi wannan warin ba. Dan takaici bansan lokacin dana bankaɗa labulen ɗakin innan ba na shiga. A kwance take sai sharar bacci take hankalinta kwance,wani cije baki nayi tareda runtse ido,zuciya ta tafarfasa take,yayinda ƙwaƙwalwata ke kwaranyomin wanne nau'in hukuncin dazanyi mata.

Fita nayi daga ɗakin naƙira su durwa wanda na barsu a wajen Tunga,ɗazu da suka ganni a hanya suka biyoni,bokitin data jiƙamin kayannawa na ɗauka na shiga dashi cikin ɗakin shima......hmmm yau waye zai hanani hukuntaki,na daɗe banga wanda ya rainamin hankali kamar ta ba.

[Sumaimah a mahangar gani]

Bayan na gama cinye tuwon inanan kwance naji kursiyyah tashigo ɗakin. "Sumaimah wai kizo inji gaji kiyi wanke wanke,ko bakisan hadda kwanukan yin awara ba a ciki?" "Kije kice mata yau baxan iya yin aiki ba banida lafiyah" "Chabɗi wlh ba wani rashin lafiyah,bakida lafiyar ne zaki cinye kuma tuwon dana kawo miki? Ai wlh saina cewa gaji wai kince bazakiyi ba ne" Tana gama faɗin hakan ta fita daga ɗakin,runtse ido na nayi lokacin da cikinnawa yayi wani danƙa kaman zai cire taciki. Tun safe nake juye juye akan gadon,bani na samu bacci ba sai wajen azahar tukunna. Baccin duk da yana cikeda yunwa amma yana min daɗi sosai. Kaman a sama naji sauƙar ruwa a jikina,wata ajiyar zuciya nasaki tareda tashi na zauna ina rarraba ido. Warin kashin shanu naji a cikin ruwan haɗe da warin soda. Tofarwa wanda yashiga bakina nake ina tari. Har sannan ban dawo hayyacina naga waya aikatamin hakan ba,amma nasan ba maiyyimin wannan aika aikar sai gaji. Juyowa nayi,saidai maimakon naga gajin,da fuskar kare muka haɗa ido yana min gurnani,saikuma wasu ƙafafu a tsaye. Binsu nayi da kallo zuwa sama,har idanunnawa suka haɗu dana goje,wanda ƙasumbarsa ta ƙara yawa,ga idonnan kaman na zaki yaga abin farautarsa. Ihu nakeson yi kozan tashi daga mafarkin danake,amma kuma nasan ba mafarkin bane zahiri ne.. Matsawa nake da baya har nakai jikin gini akan gadon,tunda nasan shine ban ɗaga idona na sake kallonsa ba. Magana yafarayi da wannan maganar tasa mai diri. "Yaushe nayi wasan dazaki rainani,shin abinda nasakaki kenan dana tafi,nace miki kada ki karya ɗaya daga cikin ayyukan dana sakaki,amma wani abin takaicin ko guda ɗaya daga cikinsu bakiyi ba,wato duk abinda zanyi nayi koh?" "Dan Allah kayi haƙuri wlh" Fizgo hannuna yayi ya jefani a tsakiyar ɗakin,jikina banda karkarwa babu abinda yake,saboda razanar danayi jinina ya tsinke sai zuba yake duk ya bata kan gadon da kuma jikina,nasan yagani amma ko a jikinsa,Allah yasama yasan menene. "Ki rufemin baki,kada ki kuskura ki ambaci wannan kalmar da na tsani jinta in anyimin laifi wato haƙuri,saboda bana haƙurin" Since sarƙar jikin karen hannunsa yayi,da alama banni dashi zayyi ya fiffigani,aikuwa hakanne dan sunshe shi yayi yana shirin barin ɗakin. Wani takaici ne gamida baƙin ciki suka tokare min maƙoshi,take kuwa sukayi nasarar kawarda tsoronsa dayake cikin zuciyata,yazamana haushinsa da kuma mamaki irin na halinsa sunfi gaban tsoron danakeyi masa. Wannan ba mutum bane,taya mutum zai dunga jin tsoron halitta irin wannan ma. "Dakata kada ka fitah" Nikaina nayi mamakin umarnin dana bashi,yaushe nasamu wannan jarumtar haka? Tsayawar kuwa yayi bai fitan ba,ba wai danna isa ne yasakashi tsayawar ba,saidan mamaki daya cikashi. Juyowa yayi tareda ɗaga gira yana kallona,yayinda nima na ɗaga nawa idon nasaka su a nasa,saƙo nake son isarwa da ruhinsa bawai shi ba,saƙon kuma bazai kai inda nakeso ba idan ba idonsa nake kalla ba. "Badai kasheni kakeson yi ba,idan kasheni zakayi ka kasheni da kanka,basai kasaka halittar da batayiwa Allah komai ba ɗaukar rai,Naga abubuwa da yawa a rayuwata sannan duk da banda galihu a duk ina naje,amma hakan bashi zai saka nakasa tsarewa kaina darajata wanda Allah yabani na ƴa mace. Bana fatan labarin mutuwa ta ya yaɗu cewa karene ya yayyagata a ɗaki har ta mutu,gwanda mutane suce mijinta ne ya yankata,wanda bai san cinta ba,baisan shanta ba,baisan ya ta kwana ko ta tashi ba,dabbarsa ta fita daraja,Dan kawai yayi tafiyar da bata san ya tafi ba,yadawo yaga batayi aikin daya sakata ba,bai tambayi dalili ba kawai sai ya yankata. A wannan tafiyar bai ajiye mata abinci ba ko kuɗin magani,sannan bai bata izinin tafiyah ko ina ba,shin dutse ya ajiye kamai,saniyar sa ya damu da itah akan a bata abinci,amma matar da ajiye ko oho. Duk da hakan tayi iya koƙarinta wajen ganin cika umarnin daya bata,amma ƴan gindasu sunƙi barinta ta cika ɗin,shikuma bai biɗi sanin daliliba hukunci kawai ya iya zartarwa na son kansa." Kukane ya kufcemin na abubuwan da suka faru a gidan wanda suka dawo cikin kaina. "Indai wannan rayuwar ce mai kamada ta bautar mutanen farko to wlh ka kasheni goje bana tsoro,duk hukuncin dazaka min na daɗe da sanin kwatankwacinsa,kaya da kake faɗa kuma ƴaƴan gaji ne suka zuba a kewayen saniya,na kasa wankewa ne saboda hannyena ciwo ne dasu......bazan iyaba ka ɗau raina kawai kaman yanda kake iƙirari ko yaushe,ka ɗauka kawai na huta,dama tunda nake mai na tsinta na farinciki a duniyar ne??? Kullum zullumin mai zai faru. In baka kasheni bama yunwar cikina zata kasheni,gaji bazata sake bani abinci ba nasan,saboda bazan iya yimata aikin da innayi take bani ba. Dan haka ni gwanda ka kashenin ma kafin yunwar da kasheni" Rarrafawa nayi na riƙe ƙafar wandonsa,har raina ni na gaji da wannan zaman rayuwar. Jikina karkarwa yake na wuyah,dakuma kukan danakeyi,karen dayake gefena sai gurnani yake,amma ba tashi nake ba,na daina ma tsoronsa,mai jiran mutuwa wanne tsoro zaiji ne" "Tashi .....ki tashi nace" Abinda yakeson nayin nasan bazan iya ba,amma barina gwada nagani. Miƙewa nayi daga rarrafen inaso na tsaya akan ƙafata,wani juuuuu jiri yaɗebeni,kafin idona ya rufe sai naji ni a hannun mutum ba tsakar ɗaki ba.

Nauyi idanuwan sukayimin,amma haka na dage na buɗeshi,akan farin cilin idonnawa ya sauƙa,fanka tanayi walwal a samana. Gefe na kaikaita kaina na kalla,window nagani na glass ga kuma farin fenti,tunani na fara na shin a ina nake ne. Yunƙurin tashi nayi sai naji hannuna a ɗaure,hannayen na kalla duk an ɗaɗɗauresu da bandeji,da alama magani aka shafamun to waye yayi min. Allura na gani a ɗayan hannun wata igiya tayi sama ruwa yana shiga jikina,Asibitine wai?? Na tambaya a raina,gyaran murya naji hakanne yasa na kalli mutumin dayake kan kujera a zaune,tun ɗazu yake kallo na ban kulaba. Ƴar razana nayi ganin ya kafeni da ido. "Meyasa kika taba abinda kinsan jikinki bayaso?" "Soda ce" "Ban tambaye ki menene ba,cewa nace meyasa kike amfani da itah,bayan kinsan jikinki bayaso,Tunga ya faɗamin cewar yabaki dubu biyu,mai kika siya toh?" "Uhm na ajiye banganshi ba,wanda na siya kuma......" "Ƴaƴan gaji sun sace,sannan sun ɗauke wanda kika siyah" "Uhm" "Sannan kayana ma sune suka saka a wajen saniya" Nan ma ɗaga masa kan kawai nayi,tunda hakanne kuma ya riga ya gane. "Wajibine na gyara saitin gidannan,ke kuma kina zaune suka miki hakan ke ga asararriyah koh?.tunda kin tashi barina je na dawo,ga nan abinci a gefen gadon kici ki gyara jikinki zan dawo na maidaki gida inna gama abinda zanyi" Ɗaga kai nan ma kawai nayi, "Bakya magana ne,ɗazu ban tambayeki ba kikayi da faɗi ba'a tambayeki ba,yanzu kuma kinkoma kurmiyarki" Daga haka cikin tafiyarsa ta isashshe ya fita. Mamaki ne yakamani anya kuwa ba mafarki nake ba,wai asibiti ya kawoni?" Ledar daya kawomin na buɗe,maltina ce a ciki da kuma peak na madara,sai magani a ciki. Ɗaya ledar kuma indomie ce aka soya ta da ƙwai. Toh ikon Allah....Sumaimah zataci daɗi kenan.. Nafaɗa a raina bansan sanda murmushi ya ƙubcemin.

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977 Auwal Sadiya First bank

Ko katin mtn ta nan 09035784150

VTU ta nan 2347068390570

Shaida kuma ta nan 09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number. +227 97 21 16 15 ----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh 09035784150 Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES* FACEBOOK PAGE:Sadisakhna WATTPAD:@SAKHNA03 AREWABOOKS:@sadeesakhna PHONE NO:09035784150 ________________________________ *Book 1* Chp[20]

Zamana na gyara a tsakiyar gadon na saka wannan kayan daɗin a gabana,saida na cinye indomien tass kafin na buɗe peak ɗin,itama gamawa nayi da itah na ɗauko itama maltinar. Saidai ita ban sha dayawa ba na ajiye,dan batayimin daɗi sosai ba kaman wancan madarar. Wata nurse ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da littafi tana rubutu. "Mrs goje ruwanki ya ƙare koh?" Tafaɗa tana kallon hannuna na hagun,oh ni na manta da ruwan dayake shiga jikinnawa ma. Matsawa kusa dani tayi ta zare ruwan,iyah canular kawai tabari a jiki. Murmushi tayimin da muka haɗa ido. "Hhhh kin burgeni wlh,bakida lafiya amma kin cinye abincinki tass" Kunya ce ta kamani,hakan yasa na sunkuyar dakai,hmm batasan rabona da abinci ya isheni bane shiyasa. "Karki damu babu wata matsala,tunda kina cin abinci basai an sake saka wani ruwan ba,ga magunnan dazaki dunga sha da shafawa duk ya siyo ɗazu,saiki dunga kulawa sosai karki ƙara taba abinda jikinki bayaso" Ɗaga mata kai nayi alamar na fahimta. Har tazo fita saita sake dawowa, "Yawwa ya kawo kaya akan ki sanja,dan haka idan kin gama kizo office ɗinmu daga kin fito ta gefennan kiyi wanka,yace yana zuwa yanzu" "Ohh nama gama bari kawai mutafi" Binta nayi a baya a hankali har muka isa office ɗin nasu da tace,a matsayina nasan bankai har a kaini wajen ma'aikatan jinya nayi wanka ba,ya danganta ne da wanda ya kawonin shiyasa ka. Bayan nafito daga wankan bandegi da sake sauya min na hannunsa,wanda na ga ashe sun cire fatar jikin hannun ne. Doguwar riga ta miƙomin maroon mai kyau da mayafinta,sai pad dakuma pant. Karba nayi na koma banɗakin na shirya kafin na sake fitowa. Kasancewar ban iyah surutu ba musamman da wanda bansani ba,shiyasa na zauna nayi shuru. Muna nan zaune kaman kurame naji muryar gojen suna magana da wata nurse,lokacin ana ƙiran magriba a wasu masallatan. Yana shigowa dani muka haɗa ido,nayi saurin sauƙar da kai,wai karfa in mukaje gida ya casa ni,dana tuno rashin kunyar danayi masa jiyah. "Oh sainace ki fito tukunna zakizo mu tafi,ko baki ganni ba kai" "Uhm naganka" Binsa nayi kaman jela a baya ina ta kakkare jikina saboda mayafin bashida girma,dan ma dare ya ɗan fara shiga. Wani mashin naga mun nufah sabo irin bajaj ɗinnnan mai babban mazauni a baya. Saida ya hau yafara diri kafin na hau bayan,dadumeshi nayi ƙanƙam,saboda ban taba hawa mashinba. Nasan yajini dan har ƴar tsuka yayi amma baice komai ba. A hankali yake tafiyah wanda nasan saboda nine har muka iso gida. Sauƙa nayi daga kan mashinɗin ina rarraba ido. "Nagode" Nafaɗa a hankali,bai kalli inda nake ba ballantana ya amsa,duk da nasan yajini sarai. Kafe mashin ɗin yayi ya nufi cikin gidan,nima binsa nayi a baya,mamaki yabani ganin ba hanyar ɗakinsa yayi ba. Ɗakin ya shiga ya tattaro kayansa wanda ya juyemin su a jikina,harda zannuwan gadon wanda ya nabata da jini da kuma ruwan daya zuba duk ya tattaro ya fito dasu waje. Ɗakinsa ya sake nufah sai gashi da bargonsa da zanin gadonsa nan ma. Dukka zubasu yayi a gabana,nidai ina nan tsaye ina kallonsa,jikina har yafara karkarwa,kaddai yana nufin a darennan zan wanke duk uban kayannan kai?. Wuceni yayi ya shiga ƙofar gaji,can sai gashi ya fito Atika tana binsa a baya, itada kursiyyah.Taci kwalliya da alama fita zatayi a daren. A tsayawa suka yi a gefe dani suna kallonsa. "Ku ɗauki wannan kayan ku wanke su a darennan,idan har suka kai gobe baku gama ba wlh kunji na rantse sai na ɗaureku na tsawon satin bakuga rana ba. Sannan idan kungama ku cikamin randa ta da ruwa" Sakin baki mukayi haddasu muna kallonsa,hanyar ƙofar sa ya nufah hankalinsa kwance. Bayan ya tafi juyowa atika tayi tana kallona. "Wannan aikinkine ko,kema nan tantiriya ko,wato bari ki juyashi shikuma ya juyamu,toh baki isa ba,dan kuwa ke zaki sha wahala ma idan hakan za'ayi,ina zai tafi ya barki a gidan" "Menene me naji ana cewa ne? Kekam ba fita zaki bane mai kike anan,ko ta dawone dama ba mutuwa tayi ba da mukaga ya fita da itah" Kallon gaji nake tasaka wani figalallen hijabi,da wani zaninta mai kama da three quarter na wando,wai a hakan sallahr magriba da dungura,wato da suka ga yafita dani ɗazu so sukayi ace na mutu.....hmmm mai nayiwa waɗannan mutanen suka tsaneni ne? Ganin gaji tafito yasa Atika rushewa da kuka tana bubbuga ƙafa,kaman ba itace take magana yanxu ba cikin tsiwa.. "Gaji kiji wani sabon salon iskanci,ɗazu da kikaga yafita dai itah,ashe suman ƙarya tayi,suka fita taje ta kitsa masa munafurci,yana shigowa ya jibgo wannan uban wankin wai mu yi shi a darenann,nida ko nawa ma bannayi shine zaice wai muyi mata wankinta da nasa??? Nikan wlh gaji bazan iyaba,Allah gaji ki ɗau mataki" Atika ta faɗa tana rushewa da kukan munafurci. "Ke ƴar nan mai kikecewa,ayi mata wanki,akan uban me za'a maida ƴaƴana bayinki,ƴar gwamna ce ke ko ƴar sarki,toh wlh baxai yiyuba komai za'ayi saidai ayi,kuma kwanon abincin ki a gidannan babu shi,idan yunwa zata kasheki ma saidai ta kasheki" Nidai ina nan tsaye in jinsu,ganin jiri yana ɗibana yasa na juya zan shiga ɗaki. Gaji ce ta jawoni baya ina shirin faɗuwa,da ƙyar na tsaya akan ƙafafuna. Hannu ta ɗaga zata shararamin mari,da sauri na rife ido ina jiran naji da wanne waje zai saƙƙo. Naji ƙarar marin amma kuma banjishi a kuma tu na ba. "Kambuuu nika mara goje ina matar kawunka zaka mareni,saboda kai......" Wani marin yasake kifa mata ta ɗaya kuncin daidai buɗe idona,kutt dama goje gaji yamara,kai matar kawunnasa?..na faɗa a raina ina zare ido. "Kona daɗa miki ne,kukuma saboda kun rainani nasakaku aiki maimakon kuyi shine kuka tsaya kuna zage zage koh,ku faɗamin Nida na sakaku kuke zagi kokuma itah. Duk ina sane da abinda kuka aikata bananan,har kayana kuka ɗauka kuka saka a wajen kashin shanu ko?....daga kyau aikin gidannan kaff nasake ganin wanda yasakata tayimasa,saina cire masa ƙafafu da hannaye,in yaso ayi masa aikin da dalili" Ƙwafah yayi mai ƙarfi yafita waje yana huci. Oh ni inaganin ta kaina a gidannan,ko ina ba sauƙi. Ɗaki na wuce na barsu a wajen,duk yadda zasuyi ma suyi. Can wajen goman dare har nayi bacci naji ana buga ƙofar tawa. Buɗewa nayi muka haɗa ido dashi,ledar dayake hannunsa ya miƙomin,hannu nasaka na karba ya bar wajen.. Bayan na koma ɗakin zama nayi na buɗe ledar,soyayyar doya ce da ƙwai sai balangu,ikon Allah mai ya shiga kan gojene yake siyomin waɗannan abubuwan. Bandai sake kawo tambaya tabiyu ba nafara kaiwa cikina.

___***___

*Overall military security headquarter division in barrack*

...ABUJA...

Tashi yayi tsaye cikin bacin rai ya buga hannunsa akan desk ɗin,wani tafarfasa zuciyarsa takeyi na bacin rai. Ga girma yazo masa amma common case ɗaya ya gagara gamawa dashi ya huta?. Runtse ido yayi tareda cije fatar bakinsa ta ƙasa.. Kallon Gen Saeed yayi wanda yake gabansa a Tsaye. "Kana nufin kacemin har yanzu baku gano sansanin Wannan ƙungiyar BC ba" "Eh ranka ya daɗe,har yanzu bamu gano daga inda suke ba,Banida cikekken bayani sosai akan su har yanzu,gashi cibiyar tsaro ta ƙasa Civil security headquarter tana buƙatar karban aikin,saboda wannan a harinnasu na ƙarshe a gwagwalada sunyi babban ta'adi sosai" "Ta bincike akan su yana tafiyah normal,meyasa yanzu ake samun matsala akai?" "Ranka ya daɗe kafin na karba Gen Ahmad Aliyu Hamma ne yake jan ragamar binciken,to tunda ya rasu kuma......" Shuru yayi yana kallon fuskar Air mershall Aliyu Hamma,saboda ambaton ɗan sa dayayi kar abin ya kasance cikin matsala,saidai kuma ya kula hankalinsa baya kansa sam. "Shirya min koma gida David,kafin na dawo Ka tabbatar kaida jami'anka kun samo wani abu gameda su,domin banason wanann aikin yabar Military ko kaɗan,Civil security bazasu iyah da wannan abinba sam,zan nemi yin magana da president akan lamarin" Yana gama faɗin hakan ya dashi ya fitah. Babban mutum ne yafara manyanta,amma kuma kasancewar a ƙuruciya ba'a zauna ba,jikin yana nan kaman bana dattijai ba,duk da daman bawai tsoho bane ba. Combo ɗin motocine a ƙofar office ɗinnsa,yana fitowa ta tsakiyan ya shiga,suka ja zuwa gida. Babu nisa gidannsa dan haka da wuri ya isa katafaren gidannsa wanda yake da kwarjininsa kaman an jefoshi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull