Sanadin caca book 2 complete - Chapter 11
Sanadin caca book 2 complete Chapter 11: Sanadin caca book 2 complete Chapter 11. Sashen hajiyah Mammah nayi bayan na kaiwa hajiyah maryam abincin danayiwa…
3,187 words
Sashen hajiyah Mammah nayi bayan na kaiwa hajiyah maryam abincin danayiwa Ahmad,bataci sandwich ɗin bama,iya kunun gyaɗar kawai tasha. A hanya naci karo da wani soja a ƙofar sashen,yana ɗaya daga cikin masu kulada security na gidan. "Am gud morning,please can you send this to hajiyah Mulaifah?" Yafaɗa yana miƙomin wani akwati irinna package ɗinnan. Karba nayi kafin nace wani abun har yabar wajen. Banso ba haka na nufi ɗakinnata,Allah yagani banason duk wani abu dazai dunga haɗani da waccer matar. Tura ƙofar ɗakinnta nayi bayan na shikenan sashen hajiyah Mammah,ko ƙwanƙwasawa banyi ba. A buɗe kuwa yake bata rufe ba. Wata irin kwanciya tayi akan gadon kaman wata ƴar bori,hararta nayi tareda ajiye abin akan drawerta,har na juya zan tafi naji maganar ta cikin magagin bacci. "Ke rainin naki har yakai kishigomin ɗaki kai tsaye kaman wadda muke sharing dake?" Tsayawa nayi amma ban juyo ba,wai dama idonta biyu? "Ga waɗannan kayan naɗeminsu kafin ki tafi" Cije bakina nayi,amma ya zanyi,banason yazamo koyaushe muna samun sabani da itah. Juyawa nayi wajenda take maganar,a hankali nake takawa har naje gaban wardrop ɗin,ina buɗewa kaya suka wani sako kai zuwa ƙasa. Saida na tsorita domin banyi zato ba. Zaro ido nayi ganin kusan duk ilahirin kayanta a cunkushe suke babu tsari. Wai a hakan zata ƙira kanta mace,kuma maison mallakar wani namijin. Fitowa nayi da kayan cikin tass nafara jerawa da ɗaɗɗaya. Wayar tace tayi ƙara,saida tayi ƴar ƙaramar tsuka kafin ta miƙa hannu ta ɗauka. "Hii padush ykk" "Ƙalau ke ya akayi jiyanne,abin yayi aiki" "Hmmm ai nake faɗamiki fiyeda yanda kike zato ma,yace haka ne kam tunda abune da aka farashi,kuma yayi alƙwarin haɗashi yanzun bazai gagara ba. Yau ma zayyi magana da Ahmad akan zancen,zuwa gobe kowa zai shaida shirye shiryen aurena da Ahmad" "Amma bakya ganin shi Ahmad ɗin ya ƙi amincewa" "Nima nayi wannan tunanin amma hakan bazayyiyu ba,domin Abbah bazai taba daina yimasa zancen ba idan har ba auren aka yiba,shikuma kinsan wancan karon ma,baya iya tsallake maganar abban. Dan haka kisha kuruminki ki saurari mai zai faru" Dariya suke sunata maganganunsu wanda sukayi amanna dasu kuma suke yi musu daɗi.. A yayinda gefe ɗaya kuma ni suke ƙonamin rai fiyeda yanda mai tunani zai tuna,wai dama matar nan da gaske take,mijina take son mallaka hakan ma kuma ta hanyar mallakar magani,bawai da son ransa ba?. Rigar da take hannuna na jefar na tashi na tafi,kunnuwana bazasu iyah jin waɗannan maganganun ba,in kuma nace zan cigaba da saurarensu to za'a samu cikyakykyen mishkila. Ina jinta tanamin magana amma nayi banza da itah nabar sashen. Kai tsaye sashen hajiya Maryam nayi,saidai tun kafin na shiga nake jiyo maganar ta,da kuma muryar babban mutum,nasan babu makawa babansu Fatee ne. "Wai bakida lafiyane naga duk kin sauya,kin rame ba kaman da ba" "Ohh dama ka damu da hakan,sai yanzu kasani? Kafaɗamin menene yake tafe dakai da har kazo sashena i yanxu?" Shuru naji ya gibta,har zan juya na tafi saboda bai dace na zama kullum mai jin abinda wasu zasuce ba,hakanma kuma sabgar ma'aurata wanda bai shafeni ba. Turus nayi tareda komawa baya,abinda naji ya faɗa ya shafeni. "Akan maganar auren Mulaifah da Ahmad ne,tazo tasameni akan maganar jiya da daddare...kinsan kuma daman abune da har an farashi wancan tsautsayin ya gibta. To yanzu tunda komai yalafa yakamata a yi auren. Yanzunnan daga office nake,nazo ɗaukar abune nace barina yi miki maganar,shima Ahmad munyi magana dashi ɗazu kuma ya nunamin amincewar sa." "To mai yasa kake faɗamin,a matsayina nawa a wajensa" "Maryam mai yasa kike hakane,wainikam yaronnan mai ya taremiki ne,da kullum kike nuna haka?" "Abban Fatee mai nayi kuma,shin nasake ƙoƙarin kashe maka ɗa ne yanzun,da kake min wannan zancen. Naji abinda kace,Allah ya taimaka ya kaimu ranar auren,yaushe ka saka?" "Wani satinne idan komai ya daidaita,yakamata yayi aure zuwa yanzu,kuma babu amfanin sake wani shirye shiryen bayan wanda akayi a baya" "Uhm" Shine kawai abinda na iya faɗa kafin nabar wajen,nikam mai yasa kullum kunnuwana sai sun jiyomin zancen wasu ne wanda zai tabamin zuciya?. Dafa bango nake jikina yana rawa na bar wajen. Itama ta yarda da auren,shima uban gayyar ya yarda da auren,shikenan daga ƙarshe sun zabi jininsu zasu haɗashi da ita,dama nasan yafi ƙarfina tun ranar danagano wanene shi,kawai son zuciyane da yarda da abinda bazai yiyu ba yasa nake ganin watarana zai waiwayeni. Kukane ya kufcemin mai matuƙar ƙarfi a corridon da zai fitar dani zuwa sashenmu. Kasawa nayi,na kasa ƙarisawa na gaza,komai yayimin duhu. Nakasa dawowa dashi a cikin rayuwata,shin dama bana cikin ransa tunda ko kaɗan,da gushewar tunani kaɗai zai shafeni tass daga cikin kansa?. Dan ban faɗamasa ni wacece ba shikenan koda da sau ɗaya bazai iya cankar wacece ni ba? Idan ta ɗaukeshi wane uba zan bawa ɗana kenan,shikenan yanada uba amma kuma tamkar bashida shi_? SANADIN CACA ne yahaɗani dashi, na tsorata dashi,na ƙyamaceshi amma kuma na daure na amince dashi,na yarda dashi na taimakeshi na kuma bashi kaina da amanata,batareda na duba mai yayimin a baya ba kokuma waye shiba a baya. Amma shi mai yasa yanzu yakasa gani na,ya kasa tuno ni,yakasa karbata a rayuwarsa. Shin mai zanyi nan gaba wanda zai dawo dashi cikin rayuwata?.
"Wayyo Allah mijina,Allah ka dawomin dashi bada wayona ba kokuma dabarata, zan iya bin son zuciyata na faɗamasa ni wacece kai tsaye,amma hakan mai zai faru......zan rushe abinda hajiyah Maryam ta daɗe tana ginawa,zan bayyana ni wacece a idon maƙiyina. Sannan shima zan sakashi cikin ha'ula'i. Amma kuma idan na kawar da zuciyata gefe shin zan iya rarrashin zuciyata taga masoyinta tareda da wata?? Ohh ni Sumaimah naga ta kaina.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
*BOOK 2* ...18...
Saida nayi wanda ya isheni kafin na tashi daga wajen na nufi bakin famfo,fuskata na wanke wacce tayi ja ta kumbura. Kai tsaye part ɗinmu na nufa domin na kwanta,abubuwan sunyi mini yawa. Da Sameer naci karo wanda ya fito daga mota zai shiga cikin gidan dana fito ɗin. Karo muka kusan yi,hakanne yasa na dan ja da baya ina kallonsa,shima kallon mamakin yake bina dashi. Bamu taba haɗuwa dashi ba a gidan,kasancewar lokacin dana zo an turashi wani aiki,idan ya dawo kuma baya daɗewa yake tafiyah. Ni na ganeshi saboda kamarsu ɗaya da saleem,kalar jikinne kawai da ɗaure fuskar ba iri ɗaya ba. Ganin kallon dayakemin ya wuce na misali yasa na raba zan wuce,jinayi yayi min magana wanda banyi zato ba sam. "Wacce ke,amma dai ke sabuwa ce a gidannan koh?" "Uhm" Shine kaɗai amsata,ohh wata tambayar na kuma jin ya sake jefa min. "Miye Sunanki" "Sumaimah" Daga hakan nayi wufff na bar wajen gudun wata tambayar,nasan zayyi mamakin hakan,in halinsu ɗaya ma da Mulaifah har yace na rainashi. Amma abinda bana ɗauka shine ƴar aiki ba baiwa bace,tanada ƴan cinta da kuma ganin dama akan rayuwarta.
Bayan la'asar shine fitowata daga sashenmu,tun ɗazu nake gardama da zuciyata kan bazan yiwa Ahmad girki ba,amma kuma wani bangaren na zuciyata ya hanani amincewa da ƙin yin. Koba komai nina ce naji nagani zanyi,sannan kuma bai kamata daga yin ɗaya na bariba. Koda yake nasan idan yayi aure ma bazan sake ganinsa sosai ba. Kitchen ɗin na shiga na fara haɗa kayan abincin dazanyi amfani dasu. Jallop ɗin shinkafah zanyi masa da wake,mai kifi da manja. Ba abincin ƴan gayu bane amma na marmarine,bansan ko zai ci ba. Bayan na gama juice kawai na ɗauko masa a fridge na ɗora akan tiren. Kaina a ƙasa yake nake tafiya wajen dinning ɗin,hankalina kuma baya jiki na sosai,ya tafi duniyar tunani. "Mai kike gani haka kina shirin buguwa da table?" A lokaci guda na dawo hayyacina,na kalli mai maganar kana kuma na sake juyawa na kalli table ɗin. "Ohh kayi haƙuri" "Banine wanda zaki bawa haƙuri ba ƙafarki ce inaga,karki ajiye kawomin nan" Saida yayi magana nakula ashe ba kayan aikine a jikinsa ba,har yayi wanka ma da alama,tunda ga nan damshin ruwa a jikinsa. Kawowa abincin nayi na ajiye a gabansa,daidai lokacin da yake sanja tashar tv. "Yau ka dawo da wuri" A hankali nayi maganar,banyi zaton ma zaiji ba. "Uhm" Naji yabani amsa. Daga nan shuru ne ya gibta harna gama zuba masa abincin na miƙamasa. Karba yayi kafin na ajiye yasaka a gabansa. Yanda ba bata lokaci yafara saka abincin a bakinsa har saida yabani dariya,amma a yanzu banida wannan mood ɗin. "Me yake damunki?" "Ehh!!" Bansan lokacin dana bashi wannan amsar ba,tambayar tasa ta razanani,ni yake tambaya wai me yasameni? "Ehh haka nace mai ya sameki,yau naga yanayinki ya sauya ba kaman kullum ba,bakida lafiya ne?" "Ahah babu komai,zan iya tafiya idan baka buƙatar komai?" Jin shuru baiyi magana ba yasa na ɗaga kai na kalleshi,ashe kallona yake tsawon lokacin. Kuma kallone mai ɗauke da alamar kulawa,ban taba ganin ya bini da irin wannan kallon ba sai yau. Garamm mukaji shigowa cikin falon kaman an jefo bauna. Ɗaga ido nayi na kalleta cikeda takaici, gabaɗaya wannan kuwa tasan mai ake ƙira da hankali. Barima na tashi na tafi,domin bazan juri wani tension ɗin ba. "Ka gama da abincinne?" Na tambayeshi har Sannan fuskata ɗauke da damuwa. Ɗaga min kai kawai yayi,har sannan bai daina bina da kallon tambaya ba. Kwanukan na ɗebe na nufi kitchen,ta gefensa na wuce tana tsaye ta naɗe hannaye,batamin magana ba bayan hararar dayayimin,nima kuma dama hakan nake so ai. Juye sauran abincin nayi na wanke kwanukan,tun daga kitchen ina jiyo maganar Mulaifah,amma dai banajin abinda take cewa sosai. "Haba D mai yasa kakemin hakane, karka manta fah har an kusa aurenmu wancan abin ya faru,kasan kuwa irin halinda na shiga. Dana jure sai gashi komai ya wuce. "Wai nikam banaji ance kinyi aure ba,maiyasa kika kashe shi?" "Saboda bazan iya zama da wani ba idan bakai bane" "Shine kawai hujjarki" Ba kunya ta ɗaga masa kai kuwa. "Hmmm ki tashi ki barmin sashe,karki ga don na amince da aurenki kiyi tunanin cewar domin ke na amince,hakan bazai sauya komai ba daga kallon danake miki" "Karka ce haka D nasan zaka soni idan muka fara zama tare ina ƙarƙashin ikonka." Daga haka ta tashi tabar falon,duk da maganganun daya faɗamata amma ko kaɗan basu wani dameta ba,tunda burinta na zama matarsa zai cika.
Da daren ma yau bamu huta ba,ummi sai mita takeyi,gwara suma sunsan ana hakan a gidan,nida bansani ba fah. Idan akwai abinda za'a tattauna daman ana ƙiran family meeting irin haka. To ranar dukka masu aiki zasu haɗu suyi aikin,ayi dinner tare a babban falo kowa ya tafi bayan an tattauna. "Mtsww ko akan me za'ayi wannan meeting ɗin kuma oho" Ummi ta faɗa wacce take zaune a kan kujerar kitchen ɗin.. Kallo ɗaya nayi mata na ɗauke kaina tareda cigaba da zuba fried rice a cikin warmer. Muryar inna ladiyo mukajiyo tana shigowa. "Kun shirya komai da komai kuwa,kowa fah ya hallara yakamata akai abinci zuwa yanzu" Cikin sauri na ƙarisa zuba abincin na ɗauka na fita. Kaina a ƙasa na ajiye abincin a tsakiyar table ɗin. Suna zaune a can tsakiyar falon,ban da hayaniya babu abinda sukeyi. Dama haka sukeda ɗan yawa. Amma duk yawanci ƴan uwan hajiyah Mammah ne,sai ƙanwar babansu wacce take aure a maiduguri da ƴaƴan ta manya haka,Hajiya Aina'u sunata hira itada Maimuna. Sai Fatee kuma da suke kallon abu a waya itada wacce naji ƴar hajiyah Aina'u ce Muneerah. Bayan mun gama jejjera komai da ɗaɗɗai da ɗaɗɗai suka fara zama a dinning ɗin.Wajen ya cika har Alhj Aliyu ma yazo da hajiyah Mammah. Kowa sai gaisheta yake ana mata ya jiki,saboda ƙafarta tana ciwo abinka da jiki ya sha miya. "Ahh how sweet,ba'a tabayin family meeting da zayyi min daɗi ba sai wannan" Mulaifah ce ta faɗa wacce take zama a kujerar da babu kowa akai. Blue material ne a jikinta yanata sheki,kaman wanda aka cemata yaune bikin. Bayan an zazzauna iya manya masu wayo ne kawai a wajen,ƙananan yara kuma inna ladiyo da mai aikin hajiyah Mammah inna kareema sun tafi dasu. Shuru wajen yayi naga kowa ya juya yana kallon ƙofah,nima waiwayawa nayi ina zubawa hajiyah Maryam abinci. Caraf idona ya sauƙa a cikin nasa,don tunda ya shigo wajen idonsa akaina yake. Inda nake ya nufo kai tsaye,mai kuma zayyimin ya taho wajena. Kujerar danake gabanta naga yana shirin ja,hakan yasa na jamasa ya zauna kana na matsa. Fuskar mutanen wajen na kalla,dukkansu kowa yayi mamakin zuwan Ahmad wajen da alama,banda Alhaji Aliyu dakuma Mulaifah wacce take ta washe baki kamar gonar auduga. Plate ɗin gabansa na ɗaga zan saka abinci,wani kallo yayimin nasan na gargaɗi ne,amma sai nayi kamar ban ganshi ba. Zuba masa nayi na tura gabansa,haɗa ido mukayi amma bansan ya akayi ba na samu kaina nuna masa babu komai da idona. Sauƙar da kai yayi tareda jan abinci gabansa kamar wanda akayiwa yaro dole.
Duk wajen babu wanda ya kulada abinda ya faru sai hajiyah Maryam,Saleem da kuma Sameer. A tare nida ummi muka bar wajen,ganin yanzu lokacin sune na tattaunawa. "Kai nifah masu kuɗi suna bani mamaki,to shi wannan zama a ci abincin menene amfaninsa ne?" Ƴar dariya nayi kafin nace. "Uhm kowanne ɗan adam yanada tsarin yanda Allah yayi masa rayuwarsa ummi,su wannan ce hanyar da suke bi wajen haɗuwa da ƴan uwansu,bakya ganin waccar ƙanwar babannasu har daga maiduguri tazo?" "Uhm ummi dan Allah zoki kai wanann yarinyar tana ta kuka mana" Lokaci guda ta haɗe fuska, "Haba inna ladiyo kinsan fah banason shiri da yarannan,ita ɗin menene bazata rike yarinyar nan,su waɗannan masu kuɗin malalata ne" Kallon yarinyar nayi wacce take ta tsala kuka gata ƙarama. Da kuma ummi wacce take zuba mita. Kodan nima uwa ce,haka kawai na tsinci kaina da jin tausayin yarinyar. "Inna kawo ta na kaita,tanata kuka bakinta har ya bushe" Daidai shigata cikin falon najiyo muryar Alhaji Aliyu. "Dukka nayi magana dasu kuma sun amince,kuma tunda ba abune na fari ba,kuma akwai halin yin na yanke wani satin za'a ɗaura musu aure" "Sati ɗaya yayi kaɗan,a matsayina na matar gidannan kuma mai iko da komai to ban yarda ba" Kowa kallon hajiyah Maryam yayi,jin yadda tayi maganar a dake. "Meyasa zakice haka,menene dalilinki na ƙin amincewa" "Maimuna ta yimaka zancen akwai wanda suka daidai ta zaizo wajenka,sai kace sai kayi tunani,haka Fatee kafi kowa sanin soyayyar da suke da Sadeeq amma baka bawa abin hankalin ka. Meyasa sai wannan da bawani damuwa yayi da abinba kake ƙoƙarin saishi zakaga kawai yayi iyalansa?" Sakin baki Alhaji Aliyu yayi,ya rasa meyasa hajiyah Maryam take masa irin wannan tsanar,yana zure cin zarafinta in suna su kaɗai amma a bainar jama'a abin da cin rai. Cikin fushi Aina'u ta ajiye cokalinta tareda fuskantar hajiyah Maryam.. "Wai Maryam mai yake damunki,meyasa bakya iya boye zafin kishinki da hassadarki akan rayuwar Ahmad,kodan saboda kinga shine babba ba ƴaƴan ki ba shiyasa?" Ƴar dariya hajiyah Maryam tayi kafin tace. "Baƙin ciki da kishi,na me kenan. Inda ɗansa ne shi da saiki cemin zanyi kishi kokuma nayi baƙinciki,amma babu wanann tunda ba ɗansa bane." "What maryam wannan wane irin shirme kikeyi haka?" "Shirme haka kike gani shirme nake? Ahmad ba ɗan Alhaji Aliyu bane, Maimuna itace ƴarsa tafari,idan kuma baki yarda ba ga nan uwarki da kuma yayannaki ki tambayesu. Dan haka batun nayi masa baƙinciki ki ajiyeshi a gefe,in kinga yaci gadon Alhaji Aliyu to ƴaƴana ne dukka suka mutu" Tana gama faɗin hakan ta tashi daga kan kujerarta hankalin ta kwance ta bar wajen. Idone ya koma kan Ahmad,wanda ya rumtse cokalin dayake hannunsa ƙam kaman zai maidashi cikin hannun,bakinsa yana rawa ya kalli AM Aliyu da jajayen idanuwa. "Abbb......abba shin dagaskene abinda matarka take faɗa?" Runtse ido shima AM Aliyu yayi,saboda bashida ƙarfin gwiwar kallon idon Ahmad ɗin ya tabbatar masa da abinda yakeson sanin. Kuka hajiyah Mammah ta rushe dashi tareda saka gefen zaninta tana sharewa. Tunda naji abinda hajiyah Maryam ta faɗa na zama tamkar gunki a wajen,shin ni wannan matar wacce iri cene. Gaba da gaba muka tsaya da taxo zata fita daga falon. Wani shu'umin murmushi tayimin bayan ta dafa kafaɗa kafin tabar wajen. Juyawa nayi nabi hanyar data bi da kallo. Bangazata naji mutum yayi yafice daga wajen,iya bayansa kawai na samu gani,tafiya yake kaman zai tashi sama don sauri.. Ohh dagani har shi sai wahala muke sha a bangare mabambamta,shin yaushe komai zaizo da saukine?. Hankalina yayi gaba ji nayi an fizge yarinyar data ke hannuna tana kuka. Hanyoyi biyu na kalla wanda suke hannun riga. Wajenda Ahmad yayi da kuma wajenda hajiyah Maryam tayi. Shin ita zanbi naji mai yake faruwa,kokuma shi zanbi domin na tausheshi akan halin da yake ciki? Ku fadamin a comment shin wacce hanya kuke ganin yakamata tabi a ciki?😄😄
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
*BOOK 2* ...19...