Sanadin caca book 2 complete - Chapter 10
Sanadin caca book 2 complete Chapter 10: Sanadin caca book 2 complete Chapter 10. Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai…
3,064 words
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
*BOOK 2* ...16...
Tun zuwanta tab da bakin ƙofar kafin ta tura take jin nishin hajiyah maryam a cikin ɗakin. Cire komai dayake ranta tayi ta afka cikin ɗakin,ma'aikaciyar jinya ce sanye da kayan likitoci,sai ɗayar kuma kayane haka a jikinta,sai kuma Neelah da take tsaye a wajen kan hajiyah Maryam,wacce take kwance tana lumshe ido sama sama. Sumaimah tana shiga da Neelah suka haɗa,wacce kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kanta,domin hankalin ta yana kan hajiyah Maryam. Kaman munafuka take takawa har taxo daidai tsakiyar ɗakin,daidai lokacin da hajiyah Maryam tayi wata ƙara mai cikeda firgici,fizge fizge tafarayi tana ƙoƙarin yage ƙarin jinin dayake shiga jikinta,yayinda suma suka ƙara ƙaimi wajen rirriqeta. "Innalillahi kuyi wani abun zasu cire min zuciya,wannan karon kam da ita zasu tafi,kucewa ƴaƴana su yafemin wayyo Allah nah" Mai sanye da kayan likitanne ta kalli Sumaimah da take tsaye, tayi suman tsaye. "Baiwar Allah miƙomin allurar can nayi mata,da alama zafin ciwone yasakata....Neelah ki riƙeta sosai fah,karki bari ta cire igiyar" "Ai ba igiya take ja bama,anty indo,da alama ƙirjinta takeson tabawa" Neelah ta faɗa cikin tausayawa kaman zatayi kuka,daidai kuma lokacin da Sumaimah ta miƙawa matar allurar. Ƙarba tayi da sauri ta zuba a jikin carnular,kafin tacigaba da shafa kanta. Sun daɗe a hakan kafin ta daina jijjigar,jikinta ya shika baccin wahala ya ɗauketa. Saketa sukayi sauran matan biyun suka bar ɗakin,yayinda itakuma Neelah har yanzu batayi motsiba tana nan a zaune gefen hajiyah maryam ɗin. "Mai yake damunta haka?" Sumaimah ce tayi maganar cikin kiɗima da kuma ɗaure kai,don abin duk wanda ya gani kam sai ya tausaya mata. "Uhmm nima bansan sunan cutar ba ballantana nayimiki bayani akanta,yanda kika gani a yanzu haka nake gani nima tun tashi na. Nida hajiyah Maryam mun daɗe da sanin kina bibiyarmu da abinda muke,kece mutum ta farko data san abubuwan da su kansu ƴaƴan ta basu san dashi ba. Kaman yanda muma munsanki mun san wacece ke fiyeda yanda ƴan gidan suka sani" Zaro ido Sumaimah tayi tareda kafe Neelah da kallo. "Kina nufin......." "Ehh nasan ke wacece,daga garinda kike,da ɗanki wanda yake ɗa a wajen Ahmad duk munsan komai,saidai shi mijinnaki bai san da hakan ba,wanda kuma hakan shine ya fi a wannan lokacin" "Kece kika turomin wannan saƙon kenan,na karna faɗawa Ahmad wacece ni?" "Uhm nice,amma hajiyah Maryam ce tace na turamiki,abinda kikeyi na bincike nasan kinayi ne domin kare wanda kikeso,amma ki sani zai kasance ɗayan biyune,ko kiyi nasarar kare wanda kike so,kokuma ki akasin haka,wanda sakamakonsa shine zaki cutar da masoyanki fiyeda yanda kike zato,zabi ya rage gareki wanne zaki zaba" Dumm Sumaimah ta tsaya tana kallon Neelah,yayinda kunnunwanta suka buɗe suna jin abinda take faɗamata,kenan duk tsawon wannan lokacin sunsan wacece itah,da kuma abinda takeyi to amma meyasa basu koreta kokuma su cutar da ita ba,indai har da gaske hajiyah Maryam tana ƙin Ahmad to meyasa tasan tasirinta a rayiwarsa amma ta ƙyaleta,maimakon haka saima cewa da tayi karta bayyana ko ita wacece. Kai dole akwai wani abu ƙulalle dayake kai kawo a cikin wannan lamarin. Buɗe bakinta tayi,wanda yayi mata nauyi kaman an ɗaura mata dutse a kansa. "Kun san wacece ni,kuma kunsan na ganku a abubuwa da dama,to amma meyasa kuka rabu dani,yanzu ma kunsan ina biye daku amma maimakon ku gujemin saima biyamin taxi da kikayi,kikace a shigo dani a har ɗakinnan,menene dalilin hakan?" Ɗan murmushi Neelah tayi na ƙarfin hali kafin tace. "Sumaimah karki kuskura ki shaidi littafi daga bangonsa,ki bari saikin buɗe cikin kinga mai ya ƙunsa tukunna,idan kuma ki ƙi,a sanadiyyar hakan zakiyi nadama da tafi cikin kwando" Kafin Sumaimah ta buɗe baki tace wani abu sukaji tarin hajiyah Maryam. Dukkansu a tareda suka waiga inda take. Itama kallonsu take tareda ƙoƙarin tashi ta zauna. "Sumaimah ke kuma menene dalilinki na bin mutum waje kawai dan kinga ya fita cikin dare,idan wajen halakane kenan haka zaki kai kanki ki cutu,miye amfanin hakan kenan?" Duk da muryarta tana ɗan rawa saboda rashin ƙarfin jiki,amma cikin dakewa take yiwa Sumaimah magana. "Kiyi haƙuri" Shine abinda ta faɗa tana sunkuyar dakai. "Uhm shikenan ya wuce,amma abinda Neelah ta faɗamiki gaskiya ne,kidaina jefa kanki cikin abu kai tsaye ba tareda ƙwaƙwƙwaran shiri ba,kada ki manta keɗin uwace sannan kuma kinda waɗanda suka damu dake. Neelah tashi ma mutafi gida dare Yayi sosai" Tun kafin Neelah tace wani abun ta tashi daga kan gadom zata saƙƙo,tana miƙewa hajijiya tace jira nake,tayi taga taga kaman zata faɗi ƙasa,a tare Neelah da Sumaimah suka riƙeta. "Mommy baki samu ƙarfin jiki ba har yanzu,bazayyiwu mu tafi gida ba,za'a iya zargin wani abun,ki baridai ko zuwa safiya" Zaunarta sukayi a bakin gadon tana haki tareda riƙe ƙirjinta. "To shikenan naji,amma ki maida Sumaimah gida kada a ga batanan,ke ma kuma kije ki huta,indo zata kulada ni" "Ahah babu wanda zai nemeni,dama ni ƴar aiki ce,kawai zance na rakaki wani wajene zan riqemiki wani abun" "Ni a wajena keba ƴar aiki bace,hasalima baki taba zama ƴar aikin a wajena ba,ko ita wacce ta turoki tasan bazan taba ganinki a mai aikiba,kuma tasan zan kulada ke shiyasa bata damu ba ta turoki gidannan,amma duk da haka akwai abinda bazan iya ba,dan haka kibi Neelah ta maidaki gida,sannan koba niba kada ki sake ganin anfita yin wani abun kisaka kanki a ciki batareda zurfin tunani ba" Cikin faɗa take maganar,da alama tsoro da kuma fargaba sun kamata a lokaci guda,wanda hakan yasa suka haifar mata da yin faɗan da bata shirya ba. Komawa tayi ta kwanta,alamar ta gama bayani kenan bazata sake jin abinda suke faɗaba. Fitowa sukayi daga ɗakin,har suka shiga mota suka kamo hanya babu wanda yace kowa komai. A bakin ƙofar gidan Neelah tayi burgi bata shiga ba,kallon Sumaimah tayi alamar ta fita. Hakan yasa ta tura ƙofar motar zata fita. "Nasan kinason kisan gaskiyar mai yake faruwa,amma sanin hakan bazai miki komai ba sai sakaki a hatsari,amma in kinga zaki iya ji to ki tambayi hajiyah maryam da kanki,zata sanar dake komai" Ɗaga kai kawai Sumaimah tayi,zata sake fita a motar. "Kin yarda da itah?" "Ahah koda na faɗa a cikin raina to hakan bazai zama gaskiya a raina ba,saidai kuma zarginta da nake na yanke kusan rabi a cikinsa. Ni zan shiga ciki nagode ki gaisheta Allah ya sawwaƙe"
Sumaimah (POV)
"Sumaimah yau ba baccin asuba ne,mai yake damunki naga ko da daddarema duk sanda na farka saina ganki kina juyi" "Uhm ba komai ummi,ki koma baccinki kawai banajin yin baccinne yau" Tashi nayi daga kan sallayar har rana ta fara fitowa saboda daɗewa da nayi a zaune. Hijabin na cire na yafa ƙaramin gyale akan rigar jikina na fita. Gidan tsitt yake babu kowa, sai kukan tsintsaye a lambu. Leƙawa nayi ruwa yana gangarawa wajen tsirran da suke gurin.. Haka kawai ban sani ba na tsinci kaina dayin murmushi, domin Allah yayini da son Yanayi(nature). Zama nayi a kan dutsen danake yada zango ko yaushe idan naje wajen. Kasancewar da ɗan duhu ma bana ganin wajen sosai. Jiya kam nayi wani abu waishi tunani,tareda neman mafita na lamarin danake ciki. Wani bangare na zuciyata nason yarda da hajiyah Maryam dakuma abinda nagani,yayinda wani bangaren kuma yana gargaɗina da yardar,duk abubuwan dana gani har yanzu saina cigaba da abinda hankali bazai ɗauka ba?. Tunowa nayi da ashe an kawo kayan abinci a sashen Ahmad,bamma je nagani ba,ga kuma ƙarin aikin sashen hajiyah Mammah da zan dungayi,duk da ma shi ba mai yawa bane. Mariya ce in jisu da faɗa take mata abinci,saboda tafison na gargajiya. Ni gurbin wacce take ɗan tayata da aikace aikace zan maye,sai goge goge. Tashi nayi daga wajen na nufo sashen sa,ƙofar falon na tura na shiga,nasan dama ba rufewa zayyi ba bayan ya dawo daga masallaci. Kai tsaye kitchen ɗin na nufa,yana cikeda kaya kowanne da gindinsa suka ajiyeshi. Kama kunkumina nayi tareda jijjiga kai, maza dai sai a gaishesu dan ma Allah ya taimakeni na gyara kitchen ɗin. Kayan nafara ciccirewa,kowanne ina sakashi a wajen daya dace dashi,na fridge na sakasu. Har sun fara tsami,musamman kayan marmarin da kuma kaji. Saida na gama gyara kitchen ɗin tass kafin na ɗaura girki. Sandwich nayi da kunu gyaɗa,saboda naga harda garin kunun suka kawo. Bashida bata lokaci dan haka da wuri na gama,ina cikin goge goge na inda yaɗan baci naji motsin mutum a bayana. Juyawa nayi da sauri muka haɗa ido da Ahmad,vest ce a jikinsa sai 3 quarter,shima zabura yayi daya gannin, domin bayyi zaton nazo ba. Saurin sauƙe ido nayi da muka haɗa ido,yayinda shima yafara kame kame ya rasa abin cewa. To mainene ma ni ɗin na wani sunkuyar dakai. Ɗaga idona nayi na kalleshi kafin na gaisheshi a taƙaice,har yanzu kaina a cunkushe yake,aikin ma inatayi duk rabinsa a tunani ya ƙare,har a garin yin kunun saida na zubar bansani ba. "Meyasa kikazo da sassafennan?" "Saboda nagama da wuri kafin ka fita aiki,sannan hajiyah Maryam ta ƙaramin wani aikin,inason inna gama wannan na tafi" To kawai yace da kansa,kafin yaje inda fridge yake sai ɗau ruwa,ina gani ya tsaya yayi jimm yana kallon cikin wajen,nasan bazai wuce yanda yaga na cika wajen da abubuwa ba,komai da nasa wajen. Ɗaukar ruwan yayi zai fita,har yaje bakin ƙofa nayi masa magana. "Nagama abincin,a falo zan ajiye maka kokuma na shigo dashi ɗaki?" "Ahah ki saka a dining ma ya isa" Daga haka nacigaba da goge gogena shikuma ya fita. Jera abincin karyawar nayi a dining kaman yanda yace, daga nan kuma na fara gyara falon. Fitowa yayi sanye da kayan aikinsa na uniform,dayake kalar yanada duhu,sai yayi masa kyau sosai,dana kalleshi wata faɗuwar gaba ce ta riskeni tareda mararin jina a jikinsa,saidai nasan hakan bazai yiwu ba,koma zai farun banan kusa ba. Dan haka shiyasa na binne komai a ƙasan zuciyata nacigaba da aikina. "Uhm da kika gama kallonnawa ai ba aikin zaki cigaba ba,saiki zo ki zubamin abincin koh?" Ajiye mopar nayi na nufi gabansa,dama na gama da falon. Buɗe plate ɗin nayi kawai,saboda bamma sakashi a cikin warmer ba. Fork na saka masa a gabansa,tareda zuba mata kunun a kofi shima na miƙa mar. Saida naga yaɗau fork din zai faraci kafin na tafi. Ɗakinnasa nashiga,nan ma saida na tattare kayansa komai nasaka shi a muhallinsa kafin na share. Daga wannan sai wannan nakebin aikin daki daki,dan yanzu inaga ko idona rufene to zan iya yin komai. Lokacin dana gama na fito daga ɗakin ya riga ya fita,dan haka zama nayi naci abincin a wanda ya bari na kai kwanukan kitchen. Bayan na wankesu nasakawa sashen turaren wuta na fito,saikuma da yamma idan na daidaici yakusa dawowa. Nafito kenan mukaci karo da hajiyah maryam,shigowarta gidan kenan da alama,amma ba kayan da tafita dashi bane jiya a jikinta kokuma nace aka fita da ita kai. Wasu kayanne daban masu kwarjini da suka boye faɗawar da fuskarta tayi,saikuma abin hannu shima daya boye ƙofofin tabon carnular da take hannunta a jiyan. Amma fah hakan zai boyune kaɗai ga wanda baisan mai yake faruwa ba,bandani da naga komai. Gaskiya na jinjinawa ƙarfin halin matar nan,ta tsaya ƙyam akan dogon takalmi cikin izza,kaman ba itace take nishi da ƙyar ba jiya. Kallo ɗaya tayimin ta ɗauke kanta,nima banyi niyyar tacemin komai ba ai. Duk da kuwa zuciyata cike take da zumuɗin son sani mai yake faruwa,domin ta hakanne kawai zan ga wanne irin taimako zan bawa uban ɗannawa.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
*BOOK 2* ...17...
"Fatee ina zakije" Hajiyah maryam ta faɗa a dake lokacin dataga Fatee ta dosota da alama fita zatayi. Da mamaki tayi turuss tana kalon mahaifiyar tasu sai kuma ta cuno baki. "Mommy dama bakya gida,nifa banyi zaton yauma a,wajen aiki kika kwana ba?" Da Mamaki na kalli fateen,tayini a haife amma wai har yanzu a ƙaramin hankalin ta uwarta takwana tanashan jini batada lafiya,amma wai bata sani ba? Hmmm dole mutane su dunga cewa rayuwar masu kuɗi akwai wuyar sha'ani,koda yake itama hajiyah maryam ɗin na kula tana son ƴaƴan ta dayawa,amma kuma koda wasa bata nuna hakan a gaban idonsu,komai yasa oho. "Ba wannan na tambayeki ba,wannan wacce irin shigace kike shirin fita da itah?" Ta faɗa tana nuna riga da wandon jikinta,wanda rigar ƙaramace bata rufe wandon sosai ba,sai kuma gyale shima iya wuya. Yanayin shigar yayi kyau sosai,amma fita dashi a matsayinta na ƴar musulmai kuma hausawa bayyi tsari ba. "Uhm uhm mommy mota fah zan shiga,ba a ƙafa zan tafi ba,kuma ma........" "Jeki cire wannan kayan ki saka wasu" "Amma mommy......" Tafaɗa kaman zatayi kuka harda buga ƙafah. "Nace jeki ciresu koh!!!" Wannan karon da ƙarfi tayi maganar,kana gani kasan dukkan ƙarfinta na lokacin ta tattaro tayi amfani dashi. Cikin fushi kaman zatayi kuka tabar wajen da gudu. Tana tafiya hajiyah maryam ta tsugunna a wajen tana kama ƙirji. Saurin matsawa nayi kusada itah na tallafi hannunta na dama,ɗago idonta tayi a hankali tareda zubasu a cikin nawa. "Taimakamin na shiga ɗakina kafin wani yazo ya sameni a haka,musamman su fatee" "Kina fama da ciwo amma meyasa bazaki bari iyalanki su sani ba" Cikin rashin fahimtarta tayi mata wannan tambayar,shin abin kunya ne mutum yayi jinya,da bazata iyah bayyanawa ba. Dariyar ƙarfin hali tayimin kafin ta jijjiga kai. "Hmmm bazaki ganeba Sumaimah,muje" Daga nan hanyar ɗakinnata muka nufah,a bakin gado ta zauna,har Sannan haki takeyi jikinta babu ƙarfi. "Kona kawomiki abinci kai?" "Abinci kuma,masu girki sun farane da sassafennan?" "Uhm akwai wanda nayiwa Ahmad a sashensa,to ko ruwan tea ma" Na faɗa inason kawar da zancen farkon. Ƴar dariya tayi tana kallon yanda nayi diri diri. "Menene na sauya zance Sumaimah,nasan zaki fara yimasa girki ai,hakan yanada kyau sosai,domin bai warke ba amma kullum yana cikin saka rayuwarsa cikin hatsari.....hmm marayan Allah. Nagode Allah da kikaso rayuwarsa" Kallonta nake ganin yanda take maganar cikin damuwa kuma daga ƙasan zuciyarta,shin yaushe zan gane wannan matar ne. "Ke ba kishiyar mahaifiyar Ahmad bace,kinayin kaman keɗin uwace data nisanta kanta da ɗanta,kuma take cutuwa dayin hakan" Saurin zabura tayi ta kalleni,da alama maganganun da take ɗazun tana zaton a zuciyarta take furtasu. "Taya kika san hakan?" Bayan ta faɗi hakan sake ganowa tayi tasake kwafsawa a karo na biyu,diriricewa tayi da alama tayi matuƙar razana ganin yanda sirrin dayake ƙarƙashin zuciyarta ya fito fili. "Sumaimah zaki iya tafiya inason na jini ni kaɗai" "Toh" Shine abinda nafaɗa nayi hanyar fita daga ɗakin. Naji maganar ta. "Duk da cewar abinda kika gano ɗin gaskiya ne amma ba yanda kike tunani ba.....Sumaimah har yanzu baki yarda dani ba,kuma baki shiga har yanzu matakin danake so kikai ba kafin ki san mai yake faruwa,duk ƙoƙarina na nabarki cikin duhu batareda kinsan komai ba kaman sauran mutanen gidan,amma abu yaci tura,kina cigaba da gano abinda zai iya vaki wahala. Wannan wacce irin ƙaddara ce.......koma dai menene kada kowa yaji abinda muka tattauna dake a yanzu,ki barshi a ranki kada ki fitar" Daga haka ta kishingiɗa a kan gadonta,da alama ta gama maganar tata. Jan ajiyayyen numfashi nayi tareda fitowa daga ɗakin na rufe. Kitchen na nufah na ɗora ruwan zafi,da farko tayi kamar zataci wani abun,maganar da mukayine tasakata sauya shawara,dan haka nasan a wahale take. Idan ma abinda nagano gameda itane yasakata yin hakan da ta daina,menene abin wahalar rashin ganewar,tunda muka haɗu abinda take nunawa tayi kamada wacce take hora kanta wajen yin abinda bashine a cikin zuciyarta ba,gabaɗaya rayuwarta a wasan kwaikwayo takeyinta,ciki kuwa harda ƴaƴan ta. A fili ta nuna musu halin ko inkula,a baɗini kuma sune a ranta har lokacin da numfashinta zai fice,Musamman ma Ahmad,duk wata damuwar sa da komai nasa tasani,sannan koyaushe cikin kareshi take kota saka a kareshi daga wani abun,sannan duk sanda aka kawo zancensa inaganin nadama da rauni a idonta sosai. Wannan za'a ƙira da tsana,soyayyarsa ce a idonta irin na mahaifiya. To amma ya haka? Mai yake faruwa a wannan kurman gidanne,idan har ba itace take cutar dashi ba to wanene,duk da itama ban yarda da itah har yanzu ba,amma kuma zuciyata tana bani,akwai wani wanda yafita dayake aikata waɗannan ayyukan,kuma yake tilastata akan horon da take bawa jininta bada son ranta ba. Amma koma waye mai yasa batayi maganinsa ba,kuma ta miƙashi an hukuntashi,ina matsayinta na wayayyiyar mace kuma mai sani akan shari'ah.
Chapter notes and social links
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare