Kenza eBookz

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 9

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 9

Sanadin caca book 2 complete Chapter 9: Sanadin caca book 2 complete Chapter 9. A hankali ɗabi'unta sai sanjawa suke,abin mamaki kuma na gaza cireta a…

3,267 words

A hankali ɗabi'unta sai sanjawa suke,abin mamaki kuma na gaza cireta a rayuwata kaman sauran mutane idan naga basuda amfani a gareni,kallon kawai idan tayimin saina tsinci kaina da masa yimata abinda nayi niyya. Ɗazu da baccin wahala ya ɗaukeni ban taba tsammanin zan tashi naganta a gefena ba,nayi zaton kaman ko yaushene lokacin danake yaro,bana samun kowa a gefena a duk sanda nake buƙatar taimako. Dana ganta a gefennawa abin sabo yazame min,kuma saina tsinci kaina da jin daɗin hakan. Amma kuma abin tambayar mai take anan wajen,yaushe ƴar aiki zatazo kawai ta zauna da wanda takewa aiki dan bashida lafiya. Abinda yake haɗani da ita shine bata riƙe mutuncinta a matsayinta na mace,amma kuma nafara kula ni kaɗai takewa hakan,ko Saleem da suke magana bata bari suzo daf da juna,ko yaushe tana gefe idan suna magana,kuma ta takure jikinta. Amma ni kaman ɗakin iyayenta haka take shigomin ɗaki,yanzu harda banɗaki ma. Har nazo shiga banɗaki maganganun da take suka tsaida ni cakk da sake ƙara ɗaga ƙafata. Shin mai ya haɗa rayuwata da tata da ta damu saita taimakamin,kuma hakan ma wai ba'a matsayin mai aiki ba,har tana roqon na yarda da itah,wanda kafin ta faɗa ma na tsinci zuciyata da fara hakan. Maganar ta ƙarshe ta sakani jin babu daɗi,a tunanin ta baƙin cikin abinda za'a bata a albashi wai nake? Akan meyasa toh. Wata zuciyar tacemin saboda ka koreta mana,kaman yanda kakewa sauran masu aiki a lokacin baya,shin kasan mai suke shiga idan kayi sanadiyyar barin aikinsu? Amma ai ba laifina bane,sune suke abinda bai dace ba. Abinda ya ban mamaki kuma wai tana da ɗa. Kenan tanada aure ko ta taba aure?. Koma dai menene zan bata dama nagani. Lokacin dana fito kafin nayi wani tunanin ƙamshin abinci ya buɗemin hanci,ohh tun lokacin dana dawo ƙasar nan Abbah yabani sashennan ban tabajin ƙamshin abinci a cikinsa ba sai yanxu. Sai kuma naji kamar duk tsawon lokacinnan sai yanzu yayi numfashi ya zama rayayye,a da tamkar matacce haka yake. Ina nan zaune kallo kawai nake amma hankalina yana kan son sanin wanne irin abinci take. Dayake tunanina yana kan kirchen ɗin ina ganin leƙowarta kafin ta koma ta fito da abincin. Ɗan murmushi nayi,tanada yarinta saidai daga gani batasan tanada itaba. Bayan takawo abincin ta ajiye magana take yi,ina jinta amma narasa mai zance da itah,kalmomin bakina dukka sun gudu sun buya. Nasan zataji babu daɗi ganin har ta gama maganar ta zuba abincin ta fita bance mata komai ba. Runtse ido nayi tareda jan ƴar ƙaramar tsuka,tayimin abubuwa dayawa yau ɗinnan,ko nuna damuwarta ma da tayi akaina abune ta ban fiya samunsa ba,atleast ta cancanci godiya. Na ɗau fork ɗin kenan nayi loma ɗaya,idon rufe inajin danɗanon yana ratsani naji takun samun Saleem ya shigo. Shikenan yazo bazai bari naci a salama ba. Bai tsaya tambayar komai ba yaja na kular kagabansa yafara ci. Da mamaki nake kallonsa. "Daga zuwa ba'a maka tayi ba saika fara cin abinci?" "Nima fah kaman kai yunwar nakeji,sakacin rashin kulada lafiyarka tasa ban zauna ba,waccar mai aikinnaka tasakani a gaba da ido cikeda hawaye. Sannan a yanda ka rufe idonnan kana karbar saƙon girki bakada alamar yimin tayi nan kusa,ballantana ma mai abincin tace naci ai. Shiyasa na bawa kaina kafin a bani. Wow to ya gaji abincin yamda yayi wani ɗanɗano?" "Uhm ba laifi kam yayi daɗi,nafada ina sake kaiwa wata lomar" Dariyar danaji ya sheqe da ita yasakani saurin kallonsa. "Yadai kake dariya kamar zararre,wai yaushe mutane suka fara sakewa dani ne har suke kawomin shirme" "Easy bro ba zarewa nayi ba,da kake faɗin haka kaima ai ka sauya sosai ba kaman da ba" "To meyasa kake wannan dariyar?" "Uhmm naga ka zage sai loma kake ne,mai cewa baya iyacin plate na abinci gashi yana shirin tashi dashi" "Ohh nima nayi mamakin hakan,maybe yanada nasaba da rashin cin abinci a gidane saboda abinda ya faru, cin abinci a waje kuma ba wani sonsa nake ba,idan nayi take away kuma ina isowa gida sainaji na kasa ci" "Ehh lallai ina Sumaimah tazo taga yanda target ɗinta ashe zai kamaka,har take damuwa da tunanin ba zayyi aiki ba" "Wane target,wani abu kuke shiryawa?" "Ahah ba komai bane,kawai nayimin magana ne akan nasa a kawo kayan abinci nan sashennaka,wai dama ta daɗe da gyarashi. Shine nace to tayi list ɗin abinda take buƙata,ina can ta turamin ta message na faɗawa plazar,yanzu hakama nasan suna hanyar kawowa" Cikeda mamaki nake kallon Saleem kaman nasamu hoto,yaushe sukayi wannan maganar duk ban saniba "Yanzun kana nufin kace masu kawo abinci suna zuwa,meyasa baku faɗamin ba to kafin ku aikata,yaushe na zama ƙaramin yaron da zaku dunga juya rayuwarsa da muhallinsa?". "Yah Ahmad bafah dan mun rainaka bane,hasalima ni bani na kawo shawarar nan ba,itace tace zatayi da kanta,saboda jikinka yafi buƙatar abinci marar nauyi,sannnan kuma akai akai. In mutum yanada case da abincin irin haka na siya bazayimasa,kaikuma bakacin abinci a gida. Shiyasa tace tunda da kitchen a sashenka a kawo komai da komai nan zata tunga yi maka. Yah Ahmad serious bansan mai yake cikin zuciyar Sumaimah ba,amma nuna damuwa da kulawar da take akanka baya min kamada wai so kaɗai,kuma wai kana matsayin ubangidanta,akwai wani abun bayan haka. Bugu da ƙari abinda tafaɗa ɗazu yabani mamaki" "Mai tace?" "Danayi mata maganar bakada lafiya,saboda ciwon dayake cikinka kafin nace komai tace wai,wannan ciwon dakaji shekaru biyu baya,dama tasan dole zai jawo matsala saboda yanada zurfi. Nayi mamakin a ina tasani. Dana tambayeta a ina tasani sai tacemin a gidan taji,ban yarda da amsarta ba amma koma menene da alama bataso a sani. Na zargeta da sanin wani abu akan ka,amma a raina ina kyautata zaton batada mungun nufi akan ka. Shiyasa nayi tunanin ka barta tayi aikin,koba komai zamanta kusanka zaisa ka sake gane wani abun." "Hmmm inaga tanada labarin abinda ya faru dani,Allah yasa itama ba yarinyar hajiyah maryam bace kaman sauran,shikenan zan barta tayi aikin domin na gano mai tasani gameda ni,sannan waye ya faɗamata" Muna cikin maganar ƙira yashigo wayar Saleem ya tashi ya fita,naji yana cewa su shigo gidan ta wajen sashena ƙofar baya,da alama masu kayan abincinne. Kaman yanda ya faɗa na yarda da bayaninsa,duk da ina ƙi amma rayuwata sai sanjawa take,tana shigomin da wasu mutanen da banyi tsammanin shigowarsu ba. Saleem ne ya shigo da bandir a hannunsa,bayan ya ajiye ya sake komawa. Nima binsa nayi na fara ɗaukowa daga cikin motar. "Bakada wani ishashshen lafiya,da ka bari ma zan shigar dasu dukka" "Uhm ba matsala naji sauƙi ma,waye ya siyo kayan,a matsayin na gida ka karbo kokuma kaine ka siya?" "Bro kabar wannan zancen,idan so kake ka siya menene na sauri,ina wanne waje zaka siyo inka ja girki" Na tambayane kawai,nasan shine ya siyo kuma bazai faɗamin shiɗin bane. Kaff a gidannamu daga shi sai Mammah su kaɗaine muke zama muyi maganar kirki,Maimuna ma wani lokacin muka yi hirar bincike idan mun haɗu,ita ɗin ma jefi jefi ne,saboda batada doguwar magana kamarni. Kallon kayan abincin nayi sun cika kitchen ɗin. "Yanzu wannan taya zasu zauna a nan wajen?" "Zuba ido kaga idan tazo yanda zata shiryashi,bakaji akace wani kayan sai amale ba,Aikin wani kuma wasan wani" Ehh to hakanne nan ɗin tamkar fadarsu ce,su sukasan yanda zasu shirya komai. Ohh ko wacce irin rayuwa zamuyi?"

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2* ...15...

Sumaimah (POV)

"Tambayar ki nake,meyasa yau baki yimin aikiba,kuma ance kin shigo,to me kikayi bayan shigowar?" Shuru nayi ina kallonta,daga baya na sunkuyar dakai,shin mai zan ce mata ne ma,ni dai ba nace na shigo nayi mata bincike ba. Ohh wayyo Allah nah. "Uhm Hajiyah nashigo amma kafin na fara aikin sai nace barina fara yiwa Yallabai tukunna,to kuma danaje bashida lafiya saina manta ban dawo ba. Kiyi haƙuri hajiyah" Tunda na fara maganar kafeni tayi da ido,da alama bata yarda da abinda nake faɗa ba sam. "Yaushe kika zama mahaifiyarsa da idan bashida lafiya bazakiyi wani aikin ba uhm?" "Uhm kiyi haƙuri hajiyah,dan Allah za'a iya bani iya aikin sashensa kawai,in yaso a ragemin albashina sai a ɗau wata" Banida zabi daya wuce na faɗi hakan,duk da nasan hakan kasada ce,tunda banyi aikin da nazo yi ba,shi ya riga ya koreni banida albashinsa,iyah na hajiyah maryam ne,to ita kuma idan na haɗa da aikinta bazan samu damar kulada sashensa ba sosai. "Meyasa kikace haka? A tunanina iya shara da goge goge kike yimasa,a kaf ma'aikatan gidannan ke kaɗaice mai aiki kaɗan,amma a hakane zaki rasa time na yimin aiki,lokacin da kikazo fuskarki ya nuna buƙatar kuɗin aikin ki muraran,amma yanzu kina cewa kin yarda a rage kuɗin aikinki saboda aiki a bangare ɗaya?. Ɗazu ance kin haɗu da hajiyah Mammah har tayimiki magana,alamu ya nuna ta yaba da hankalin ki. Koda kin bar yimin aiki to inaso na sakaki a sashenta,zaki dunga yimata goge goge da shara,zan sauya mai aikinta" Meyasa zata sauya mai aikinta ta sakani,nace banason nayi mata kuma tasake turani wani wajen?. "Amma hajiyah....?" "Kince bazaki yimin aiki ba na yarda toh,amma wannan ba wai turasasaki zanyi ba,ahah ina roƙonki ne kiyimin wannan aikin,saboda dake kaɗai na yarda a kaf cikin gidannan. So nake kiyi mata aiki amma ki zama idona da kuma kunnena a sashen. Amma idan kinje karki sake ki nuna nina kawoki kokuma kinada alaqa dani, idan hakan ya fito kina cikin hatsari. Ki kuma yi taka tsantsan da komai,kije inada abinyi yanzu,gobe zaki fara yimata aiki" Tana gama faɗin hakan ta shige banɗaki,jan numfashi nayi tareda kallon hnayar da tabi ɗin,wannan matar mai take nufi,kota kula nayi mata bincikene shiyasa take ƙoƙarin turani wajen waccar dattijuwar kai. To amma meyasa naga tarin damuwa a idonta lokacin da take roqona,babu wannan jiji da kan da kuma ɗaga kai,tayimin kama da wacce takeso ta kare wani abu nata. Ƙarar shigowar message nagani a wayata,da bazan duba bama,domin a zatona mtn ne zasuyimin tujarar bashin danaci. Ba sunan mtn nagani ba,wata number ce babu suna,hakan yasa na tsaya na buɗe. _zama dashi yasa kin fara mantawa da halin da kike ciki da kuma shi,ki kusa dashi amma kiyi taka tsantsan,sannan duk rintsi karki bayyana masa matsayinki a wajensa,yin hakan a yanzu hatsari ne gareki da kuma ɗanki_

Zaro ido nayi tareda maimaita saƙon akai akai har bansan adadi ba.. Waye yasan wacece ni,waye yasanni a gidannan bayan inna ladiyo ita kuwa batada waya bare ta turomin saƙo,ba kuma Saleem bane,domin shima bai san wacece ni ba. Shin na yarda da gargaɗin kokuma na watsar,idan da gaskene nima na fara zargin Ahmad yana cikin hatsari a gidannasu,to amma waye yake haddasa komai,ina zargin hajiyah Maryam,amma kuma a raina ina jin kamar ba ita kaɗai bace akwai wata. Ajiyar numfashi na sake tareda wucewa sashenmu,naso zuwa sashensa a yanzun nayi masa abincin dare,bashshi kawai sai gobe naje.

........

Tana maganar dama daƙyar takeyi,saboda wani abu da takeji yana taso mata a zuciya,shiyasa tun kafin ta sallameta tayi saurin barin ɗakin ta shiga banɗaki.. Kai tsaye bakin sink ɗin ta nufah tareda fara sheqa aman jini mai kauri harda guda guda,ta daɗe tanayi kafin ya tsagaita mata kaɗan. Komawa tayi ta zauna akan bahon wankan dayake banɗakin,haki takeyi numfashinta yana sama sama,riƙe ƙirjinta tayi tana runtse ido. Ta daɗe a hakan kafin ta miƙe cikin dauriya ta fito daga banɗakin. Wayarta ta ɗauka akan gado ta danna ƙira,bata ce komai ba har wacce ta ɗauki ƙiran ta gaji ta kashe. Zama tayi a bakin gadon har sannan hannunta yana kan ƙirjinta. Banko ƙofar akayi da sauri,Neelah ce amma cikin tashin hankali ta shigo ɗakin. Gaban hajiyah maryam ɗin taje ta tsugunnawa,idon ya cika ta ƙwallah,ganin yanda hajiyah maryam ɗin tayi fari soll kaman fatalwaa. Cikin rawar murya da fara magana cikeda damuwa. "Mmm....ommy har yaushe zaki cigaba da wannan abun,ya isa haka don Allah,kinsan muna buƙatarki bai kamata ki dunga bada rayuwarki ba,ya isa haka,kiga fah yanda jikinki yayi,muje kiƙara jinin inyaso saimu dawo idan ya ƙare" "Ahah Neelah nagaji da wannan irin rayuwar,wahala da kuma gudura ne gareta,idan har ban tsayar da auren sa da kowacce mace ba hakanne zai cigaba da faruwa,nikuma na gaji da takurawa rayuwarsa Neelah,na cutar dashi da yawa,ya isa haka,sun tabbatar min idan har banyi wani abun ba to kona mutu bazasu tabamin ƴaƴa ba,dan haka Neelah zan ɗau komai a kaina na tafi. Koda na tafi don Allah kici gaba da.........." "Ahah nikam,nikam dan Allah ki daina wannan maganar,bazan jita ba banason ma na jita,baki cancanci haka ba,su ya kamata su cutu bakeba,kin juri azabarsu tsawon shekara da shekaru,bai kamata kici gaba da jurarta ba har yanzu,dole ne muyi wani abun,karki damu zanji da komai. Zanyi iya ƙoƙarina wajen kin cika abinda suka ce ɗin,badai waccar shegiyar Mulaifan suke tunani ba,to Inshaallah bazai aureta ba,dama bata dace dashi ba ko kaɗan. Yanzu dai ki tashi muje asibitin nayiwa Dr Mus'ab magana yana jirnmu ma yanzu haka" Tashi neela tayi tareda zan hannun hajiyah maryam ta tashi. Amma taƙi koda motsawa. "Yanzu Neelah haka zan dunga zuqe jinin mutane a jikina yana ƙarewa,aikina kenan" "Ahah ba iya aikinki ba kenan,kinyi abinda wasu ma bazasu taba iyawa ba,you deserve it" Da ƙyara Neelah ta samu ta yani hajiyah Maryam ta tashi zasu fita,jikinta duk ya shiga kaman wacce tayi shekara tana jinya,numfashinta ma daƙyar yake fita. Mayafinta ta yafa mata suka buɗe ƙofar baya,ta kusan sashen masu aiki ta baya. Lokacin ana ta ƙiran magriba a masallatu. Daidai fitowarsu zasu wuce sai a kan idon Sumaimah wacce ta kayan wankinta da tayi tun safe,ta manta bata debe ba. Zaro ido tayi ganin Neelah ta riƙo hannnun hajiya Maryam suna tafiyah,yanda take takawar kaman matar data fito daga labour,yanzunnan fah ta rabu da itah kafin magriba?. Kayan da ajiye a jikin ƙarfen fence ɗin lambu ta lallaba zuwa ta bayansu. Hanyar wajen mota taga sun nufah,to amma in batada lafiya mai yasa suka fito ta ƙofar baya,hakan ma a boye saida kowa ya tafi sallah. Jijjiga kai tayi da alama hankalin ta bai kwanta da wannan fitar ba.. Tsayawa daga sunyi,hakanne yasa ta bar tunanin ta tattara dukkan nuturwarta akan sanin mai zai faru ko yake faruwa. Yunƙuri daga Hajiyah Maryam tanayi kaman mai shirin amayar da abin cikinta,zaro ido tayi ganin yanda maimakon amai ya zubo jini ne yake zubowa. "Hasbunnallahu menene haka" Sumaimah ta faɗa tana saka hannunta a baki. Saurin ƙarisawa motar Neelah tayi da itah ta rufe ƙofar.. Dawowa tayi ta ɗau wani bokiti a wajen ta tari ruwa ta sheqa. Lalleƙawa tayi ko zataga wani yana binta,ganin babu kowa yasa ta shiga motar suka zasu. Cije yatsa Sumaimah tayi,ranta cike fall da son sanin shi mai yake faruwa ne.. Ganin suna shirin fita daga gidan yasa ta tashi ta bisu a baya. Neelah ce tafita ta buɗe get ɗin gidan,dayake mai remote,ana kunnawa yake buɗewa kuma kaman abin haɗin baki babu kowa a wajen. Binsu tayi a baya ganin da gaske fita zasuyi. Babu kowa a bakin titin sai napep kaɗan kaɗan da suke wucewa,ga motar su hajiyah maryam tana yin nisa. "Hajiyah wani wajen zakije ne naga kin tsaya kina leqa hanya?" Wani mai taxi ne yayi mata magana. Kallon kayan jikinta tayi,doguwar rigace saita ɗaura dan kwalinta. Sinceshi tayi tareda yimasa yafin gyale. Ƙofar motar ta buɗe tareda faɗawa ciki. "Waccar baƙar motar zaka bi don Allah,kayi sauri kada su bace dare yafara yi" "To shikenan" Tada motar yayi yabi bayan su Neelah. "Mommy ki daure mun kusa isa" Raba hankalin ta tayi biyu,ɗaya na kan hanya ɗaya kuma yana kan hajiyah Maryam wacce take nishi ɗaɗɗaya.. Ma'aikatarta ta marayu suka nufah,kasancewar babbace sosai akwai part na abubuwa kala kala a ciki,har asibiti. A bakin wajen mai motar ya ajiye Sumaimah,anan gizo yake saƙar batada kuɗin mota. "Hajiya kuɗinki ɗari biyar" Wuri wuri tayi da ido,domin batasan ta inda zata samo kuɗin ba sam. "Mallam kayi......." Tun kafin ta gama maganar wata ta miƙama ɗari biyar. Karba yayi yaja motarsa ya tafi. Cikeda mamaki ta juya ta kalli matar data biyah kuɗin,wata dattijuwa ce amma ba sosai ba,murmushi tayiwa Sumaimah tareda cewa. "Neelah ce tacemin akwai wacce ta biyosu naje na biya kuɗin taxi ɗin,tasan baki ɗakko kuɗi ba daga gida" Sororo tayi tana kallonta,kenan dama sun san tana binsu,mai yasakata yin wannan garajen hakane,duk ta makance akan neman gaskiya,ji inda ta tsinci kanta da daren Allah. "Mai kika tsaya yi,tace na shigo dake inda suke,suna bangaren asibiti na nan wajen,koba tare kuke ba kai?" "Ahah ......uhmm tare muke" "To biyoni na nuna miki,suna saurine shiyasa basu jiraki ba inaga,ciwon hajiyanne ya tashi,naga na yau ma yafi na kullum tsauri,Allah sarki tana shan wuya wannan baiwar Allah" Cikeda tausayi tayi maganar,jin abinda ta faɗa yasa Sumaimah tambayarta.. "Batada lafiyane hajiyan?" "Ohh baki sani ba? Ai kusan duk wata saita sha ledan jini,wani ciwo ne da ita yake zanye mata jini" Hmmm ko basu san tana shigewa da bango bane,nasan yanzu haka shine yake zuqe mata jini. Wacce na ganta da ita kuma yanzu haka wannan matar ce tasuka zo tare,dama ina yawan ganinta tashiga sashenta ta ƙofar baya. Gashi na biyosu sun ganni,sunsan ina bibiyarsu. Anya kuwa bazan gudu ba,kar naje na shiga a ɗau nawa jinin a saka mata . tunda suka biyamin kuɗin taxi zasu fanshe a jinina,koma mai sukamin nina jawowa kaina,tunda ƙafata ce ta kawo ni. Wannan tunanin Sumaimah take tayi a cikin kanta sinka sinka,yayinda a zahiri kuma take ɗaga ƙafarta tana bin matar duk lungun data bi,kaman wanda aka ɗaura mata igiya akace saita je. "To mun iso wajen,waccen ɗakin zaki shiga suna ciki,nasan an fara ɗaura mata jininma" "To ki rakani mana meyasa zakice na shiga?" Jijjiga kai tayi tareda cewa. "Bana son ganinta a wannan yanayin,bama haka ba kuma ba'a son mutane da yawa wajennata harsai ta tashi tukunna" "Nikuma an yarda na shiga?" "Ehh Neelah tace ki shiga,domin cewa tace na taho dake idan na biya kuɗin taxi ɗin,sannan batace ki tsaya a waje ba,kinga kuwa tana nufin ki shiga kenan,sai anjima barinaje kar yaran danake kula dasu su nemeni" Tana gama faɗin hakan ta bar wajen. Aka bar Sumaimah ta tunanin ta tura ƙyauren ɗakin tashiga kokuma ta juyah.

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull