Kenza eBookz

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 8

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 8

Sanadin caca book 2 complete Chapter 8: Sanadin caca book 2 complete Chapter 8. Tafiya nake a sunkuye,duk ƙara taku danayi jinake kaman nakoma…

2,632 words

Tafiya nake a sunkuye,duk ƙara taku danayi jinake kaman nakoma wajennasa,amma kuma komin naci na ya zanyi,yace baya buƙatata. Daga idona nayi na hango dr Saleem a lambu,har nayi niyyar sharewa saikuma na sanja ra'ayi,ko ba komai wani abin ba laifinsa bane nawane,shi baisan ni wacece ba,nikuma ban sanar dashi ba. Ƙarisawa nayi inda yake da sauri fuskata ɗauke da damuwa.. "Ahh malama Sumaimah ya na ganki haka cikin bacin rai?" "Uhm .....uhm daman Yayankane bashida lafiya yanata nishi yana riƙe ciki,na tambayeshi menene yaƙi faɗamin" Zaro ido yayi tareda tambayata. "Ciki kikace ya riƙe?" "Ehh cikinsa ya riƙe,menene wani abune a cikin nasa?" "Shin yau kinga yaci abinci?" "Ahah ni ban taba ganinsa ya ci abinci ba" "Ohhh shit wai yah Ahmad meyasa yake hakane, maza jeki haɗomasa abinci a cikin gida yanzunnan,kodayake mtsw ba lallai yaci ba don bayacin abincin gidan. Kinga jeki ɗakko ruwan zafi haka ko shayine ya sha akwai maganinsa a drawer bari naje . kiyi sauri" Tunda ya fara maganar kamar hoto haka nake kallonsa,kenan wani ciwone dashi a ciki,nikuma na dau abin kaman wasa. Inason tambayarsa mai yake damunsa,amma dai duk ba yanzu ba. Cikin gidan na shiga da sauri,kai tsaye kitchen na nufah. Daidai zan shiga kitchen ɗin naji nayi gware ta mutum,ban tsaya kallon waye ba na wuce da sauri. Muryar danaji ta dakamin tsawane yasa na tsaya cak. "Heyy ke jahilar inace zaki bugeni ki wuce kamar kin buge itace?" "Am sorry sauri nakene kiyi haƙuri" "Ina ruwana da saurinki,kiga yanda kika 'batamin jiki a cerelac" Saida tayi maganar na kulada gaban pink ɗin rigartata yanda ya baci da yellown abin. Ohh ƙifta idona nayi,na kwafsa kam. "Me kike kallo ki dauko mopa ki gyara wajennan,sannan kizo ɗakina ki karbi kayan ki wanke" "Okay to ina zuwa" Nafaɗa zan zuya da sauri zuwa daukar ruwan zafin. "Ke mikike nufi,ina zaki je" "Kiyi haƙuri anty Mulaifah kaman yanda na faɗamiki wani abun zanyi da gaggawa,idan na gama zan zo na gyara" "Kutt lallai ma yarinyar nan kin rainani" Hmmm ji saikace tafini,ina jinta tana bambaminta amma nayi cikin kitchen ɗin,komai zatayi ma daga baya kenan,yanzu mijina yana buƙatata urgent. Allah ya taimakeni ina zuwa naga inna ladiyo ta ɗora ruwan zafi,diba nayi a wani jug. A gurguje na haɗa shayin na zuba a wani flask na ɗau kofi na fita da gudu. Duk abinda nake inna ladiyo tana kallona amma batace uffahn ba. Har nazo na wuce ina jiyo masifar Mulaifah wanda har yanzu bata gama ba. Magana ta ƙarshe danaji shine wai ta koreni a aiki na tattara na tafi. Lokacin dana isa sashen babu kowa da falo,daki na shiga dannasan suna can.. A kwance yake akan gado,Saleem kuma yana gefensa. Yanzun baya nishin amma daga ganin yanayinsa mutum zai tabbatar yana jin jiki. Sallama nayi da flask ɗin a hannuna,da shi muka haɗa ido,nasan yayi mamakin dawowa ta bayan ya koreni. Ɗauke kaina nayi tareda ajiyewa a gaban Saleem. "Sorry na dade ban dawo ba,mun ɗan samu gwarene da Mulaifah a hanya ya jikinnasa?" "Uhm to gashinan zuba masa tea ɗin yasha ko yaya ne sai yasha maganin" To nace tareda zuba tea ɗin a kofi,ya ji madara kuwa da bornvita sai ƙamshi yake. Saleem na miƙawa kofin ya karba. "Idan ka gama ina jiranka a lambu,uhm Allah ya sawwaƙe" Tashi nayi na ɗau kofin na fita,ina kallon Ahmad yana kallona amma na ɗauke kaina. Wajen dana tunkuɗewa Mulaifah abinta na gyara kafin na nufi sashennata domin na karbi rigar,duk da cewar naji tace wai saita koreni,amma ai ba ita ta ɗaukeni aiki ba. "Yau dama nake niyyar sanarwa Abbah yakamata a ɗago zancen aurenmu da yah Ahmad,tunda ya huta ai,shekara biyu fah?.......aiki bari kawai za'a sha shagaline na musamman,wannan maganin an tabbatar min da innayi amfani dashi daidai to abbah bazai cemin ahah ba,shikuwa Ahmad bana tashi,saboda nasan indai Abbah yace masa ya aureni aiki ya gama. Kudai ku zuba ido Kuga yadda zata kaya,Gen Ahmad hamma dan Mulaifah aka yishi".. Hannun ƙofar na riƙe sosai saboda jirin daya ɗebeni,no wonder ashe shiyasa take ta masifa data ganni a sashen Ahmad,kuma ko yaushe cikin hantara ta take saboda ina aiki a sashensa. Kan ubancan,mutumin da kowa yake gudunsa haka na tunkareshi,na zauna dashi har yazama mutum. Lokaci daya subucemin nasha wahalar rashinsa,yanzu kuma na sameshi ina shirin dawo da hankalin sa gareni tace wani nata ne ita kaɗai,hadda wani dan ita aka yi shi. Cije bakina nayi dana tuno furucinta na ƙarshe,hmmmm ai kuwa Mulaifah zan nuna miki wannan furucinnaki ba haka yake ba,in dai harna barmiki Ahmad ke kadai to saidai bana numfashi,nida Sayyid muna buƙatar sa,we deserve him no matter what. Sakin handle ɗin nayi zan bar wajen,na fasa ma yi mata wankin rigar. Har na juya zan tafi naji muryar ta a bayana. "Ke kuma me kike min a bakin ƙofah?" "Babu kawai na manta hanya ne" "Hanya??ba riga kika zo karba ba?" "Uhmm da itace amma na fasa?" "Kin fasa?" "Ehhh" Na faɗa ina juyawa muna kallon juna,idona cikinnata babu alamar zan sauƙe,zicuyata ƙuna take da turirin kishi dayake cina,jinake komai ma zanyi a yanzun. "Ki wanke kayarki kokuma ki bawa masu aikin da suke yin wanki,niba aikina kenan ba" Ina gama faɗin hakan na juya nabarta a wajen baki buɗe. Duk abinda muke wata dattijuwa tana kallonmu,inaga itace hajiya Mammah da suke faɗa,danni bansan ta ba mu taba haɗuwa ba. Murmushi tayimin lokacin danazo daidai fita daga sashen,kunya ce ta kamani ganin takama ni a matsayina na ƴar aiki inayiwa jikarta kuma ƴar gida rashin kunya. Rusunawa nayi tareda gaisheta kaina a ƙasa. Ba yabo ba fallasa ta amsa min cikin dattako. Tana sanye da farar riga dakuma lullubi shima fari. "Sannu yarinya,amma ke baƙuwa ce domin ban saida ki ba" "Ehh hajiyah satina guda kenan da zuwa" "Ayyah ya sunan ki toh?" "Sunana Sumaimah hajiyah" "Mashaallah Allah ya taimaka toh,karki damu da sabaninku fah da Mulaifah kin burgeni ma da baki raga mata ba,faɗanta yayi yawa da mutane. Inkin samu lokaci kizo muyi hira kinji?" "To shikenan hajiyah ba matsala nagode" Daga haka na ra'beta na wuce,ina mamakin halinta,inaga to itah su Saleem suka iyo rashin wulaƙanta mutanen. A lambu na zauna na tsirawa wani waje ido,inda ruwa yake bi abin sha'awa,a zahiri mutum zai ɗauka wajen nake kallo,amma a ciki tunanin abinda naji Mulaifah tana faɗa nakeyi. Zabura nayi tareda juyawa jin wani abu a jikina,ɗaga ido nayi naga ashe fulawa ya wullomin kan cinyata. "Sarkin tunani mai kikeyi haka,ko duk damuwar ubanginnnakine kai?" "Uhm ya jikinnasa ciwon ya lafah,yasha maganin,tea ɗin fah shima yasha?" Cikeda zumuɗin son sanin ya yake har ban kulaba na fara zayyano wannan tambayoyin,sai bayan na gama furtasu danaga yanamin kallon mamaki kafinna juyar dakai ina wayancewa. "Shin miyasa kika damu jinyarsa kaman haka,tsakaninku bayamin kamada iya mai aiki da ubangidanta" Shuru nayi domin banida amsar dazan bashi a wannan maganar. Shima ganin ban amsa ba yasa ya sauya maganar. "Karki damu zai samu sauƙi idan har ya kiyaye. Ya taba samun raunine a cikinsa kuma da alama ba'a kulada wajen yanda ya kamata ba,makamin da aka soka masa kuma yanada dadi,duk da an karya ƙarfinsa amma ya tabashi sosai,to sanadiyyar haka yasa hanjin wajen bashida ƙarfi,dole sai yana cin abinci akan kari kuma marar nauyi sosai,saboda karya motse dayawa kuma kar ya ɗame da yawa" "Wajen da yaji ciwo na cikinsa shekara biyu baya kake nufi,haba daman nasan bazai tsaya iya haka,ace wai ya warke shikenan,ciwon akwai zurfi sosai" Magana nake nayi zaton a azuciyatane,ashe Saleem ya kafeni da ido cikeda mamaki,saida na gama yayimin tambaya. "Ya akayi kikasan ciwon shekara biyu baya ya jishi,kuma yanada zurfi sosai?" "Uhmm am labarin naji a gidannan,kuma um......na taba ganin tabon a cikinsa" Runtse ido nayi lokacin dana faɗi hakan,Allah ya taimakeni ma shi mutum ne da baya bin ƙwaƙwaf. "To amma taya kake ganin za'a sakashi ya dunga cin abinci akai dan gudun faruwar haka. Mai zai hana a dungayi masa girki a sashensa tunda bayason na gidannnan" Murmushi yayi tareda gyaɗa kai. "Ehh hakan yayi,saidai bana tunanin zai yarda" "Zai yarda,kawai bai saniba a saka kayan abinci a kitchen ɗin" "Waye zai dunga girka masa toh,iyah gyaran sashensa ne aikinki,bai kamata ki ɗaurawa kanki wani abinba daban" "Karka damu dr,indai har hakan zayyi amfani a shirye nake dayi,yanzu zan iya ganinsa?" Ohh Allah yasa yace ehh. "Ehh to ni bansani ba,tsakaninku,tunda kince zakiyi kimin lissafin komai da komai da akeda buƙata saiki bani,Inshaallah za'a kawo" "Nagode sosai" Daga haka na tashi na tafi,sashenmu na shiga nayi sallah na taba abinci sama sama,kafin na fito na nufi wajen ogan ƴan tsarin. Kaina tsaye na shige ɗakinnasa,yana kwance akan gado,daga ganin kwanciyar bacci yake.. Gaban gadon naje na zauna tareda tsareshi da ido. Nafi minti goma a haka ina kallonsa ko ƙiftawa banayi,tun ina kallon fuskarsa da take gabana harna fara hasasho goje nah,mai sona da kuma ƙaunar farincikina,nayi kewarsa sosai. "Lafiya kikazo gaba kika kafeni da ido kaman zaki cinyeni,hadda wani kuka kaman wanda aka ce na mutu?" Dawowa nayi daga duniyar tunanin ina kallonsa,kama da gangar jiki suka haɗa,amma wannan sam ba goje nah bane. Shafa kumatuna nayi sai a sannnan naji ruwan hawayen dayake magana akai. "Niba kai nake yiwa kuka ba,nasan ai baccin kake ba mutuwa kayi ba,kayi sallah kazo kaci abinci kasake shan magani" "Yaushe kika fara bani umarni,wani kekam banace kada ki sake dawowa sashennna ba" "Ka faɗa amma na dawo,yanzu babu wani zancen kora,domin ba'a matsayin ƴar aikinka na dawo ba,ƴar aikin mai roƙarka inka koreta to ta tafi,wannan nice amma da banbanci da wancan" "Mai kike nufi,ana yiwa mutum aiki dolene,nace na koreki" "Naji ai ka koreni kuma bance maka ban koruba,in ma na kuɗin aikin daza'a vani wanda zan taimakawa rayuwar ɗana da kuma da ƙanwata da innata kakemin buƙulun samu to naji na gani. Amma yanzu ka sani ba'a matsayin mai aikinka nake ba,a matsayin wacce zata taimakeka nadawo. Ruwanka ka karba kokuma akasin haka,amma ni zan taimaka maka saboda hakan..........(jan hanci nayi tareda saita muryata da take rawa)......buƙata ta ɗaya ka yarda dani,banida nufin cutarwa a gareka,in ka amince kayi sallah kafito kafinnnan na gama abinci" Inagama faɗamasa hakan na fito daga ɗakin na nufi kitchen,na ɗauko kayan abinci daga kitchen ɗin gidan,wanda zan dafa kafin dr Saleem ya kawo kayan abincin kaman yanda yace.

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2* ...14...

Jallof ɗin taliya nayi da ice fish,saina markaɗa ayah nayi kunun ayah mai kauri. Abinda yasa nayi na kula ko lokacin da yana goje yanason a sarrafa masa taliyah.. Ina yin abincin amma gabaɗaya tunanina ya rabu gida biyu,shin zai ci kokuma ahah,idan bai ci ba yazanyi?. Na sauƙe abincin kenan ina sakawa kunun ayan ƙanƙara naji motsinsa falo.. Leƙowa nayi a hankali kaman munafuka,a zaune yake a akan kujera yana kallon wani labarai a bbc. Komawa nayi da baya ina kallon kwanukan abincin dana shirya. Ta maza nayi tareda yin shahada na ɗauki tiren nafito zuwa falon. Har na ajiye akan center table bai kalleni ba,nima kuma ban fasa ba. A flate na zuba masa sai ƙamshi takeyi,dan murmushi nayi ganin yanda ya haɗiyi yawu ta gefen idona. Tura masa nayi gabansa bayan na saka fork akai,shima kunun ayan na zuba a kofi na miƙa masa. "Bismillah gashinan na gama,kaci koda kaɗanne saboda yanayin da kake ciki,barina tafi idan kagama zanzo na ɗauke" Yajini sarai amma bai kalleni ba sai kace gunki,a raina nace wannan inaga da a gidan sarauta aka haifeshi bazaiyi magana ba ma. Tashi nayi daga durkushen danake nafita daga sashen. A bakin ƙofa na haɗu da Saleem zai shigo. "Ahah Sumaimah ya mutuminnaki ne?" Ƴar dariya nayi kafin nace. "Ehh to bazance komai ba,nayi masa abinci dai,amma har na fito bai yimin magana ba" "Iyee kafin kayan abincin suzo harkin fara girkin,toh nima cikinnawa bai ɗauka ba,barina shiga na tayashi. Am yawwa naje na kaimusu list ɗin abinda kike buƙata,zasu kawo a motar shagonnasu in anjima zuwa yamma" Jagayeni nayi ya shige ciki hana murza hannu,hakan da yayi sai ya bani dariya. Shikam babu ruwansa kaman ba ɗan gidan ba. Sashenmu na nufa,inyaso in an kawo kayan na dawo. Ina can inata kulada shi ashe ni banci abinci ba tun safe. Cikina sai ƙiran ciroma yakeyi. Ina shiga akan kwanon abincin na dura babu tsayawa. "Kina can kina aikin da ba'a sakaki ba,saida kika ɗebo yunwa kafin kikasan da nan koh,nayi zaton ai kinci abincin a can" Ummi ce tayi maganar tana fitowa daga banɗakinmu,fuskarta da ruwa,da alama alwalar la'asar tayi. "Kinci abinci ne?" "Meyasa kika tambaya,mai zan jira?" "Saboda naga ranar dana daɗe ban dawo ba bakisan natafi siyayya da umaru driver ba kinyi zaton bata nayi,ko abinci baki ci ba" "Waye yace miki,ni ban nemeki ba kawai dai banajin yunwa ne,yanzun tun ɗazu a ina kike,nasan dai a kin daɗe kikai Azahar" Tana maganar ne bayan ta saka hijabi tana shimfiɗa sallaya. Kallonta nake da mamakin halinta,a yanzu in wani ya ganta zaice tafi kowa tsanata,amma allah ne kaɗai yasan tunani da tayi da bana nan. Fuskar damuwa na ɗora akan fuskata bayan na rufe kwanon abincin na turashi gefe.. "Hmmm bashida lafiya ne,ni bansani ba saida dr Saleem ya faɗamin ashe ciwon yayi tsanani sosai,matuƙar bazai dunga cin abinci akan kari ba to ciwon zai tashi. Gashi wai bayacin abincin gidannan" "To miye naki a ciki,ƙaramin yarone da sai an faɗamasa lokacin da zaici abinci saboda kada yayi masa illah? To yanzu da kike faɗamin mai zakiyi akai,sufah masu kuɗinnan duk da suna burgeni to kuma suna bani haushi" Kallonta nake yanda ta zage tana ta masifah,nayi zaton bataganin laifin masu kuɗi sai talakawa ko ƴan ƙyauye,to ashe ba haka bane,kowama bata barshi ba,duk da cikin zuciyarta ba hakan bane. "Na yanke shawarar zan dungayimasa girki a sashensa,dan haka bazan dunga dawowa da wuri ba" "A nawa zaki dunga yimasa kuma" "Wannan ba zancen kuɗi bane,nice na saka kaina bashi yace nayi ba" "Tabɗi kyauta kuma,ina kanki ya shiga,ko kema sonsa kike kaman sauran wanda sukayi masa aiki a baya kai?" "Ahah ba haka bane,bazaki gane bane ummi amma......" "Kinga bazan gane ba,ba kuma saina gane ɗin ba,dan haka karki takurawa kanki wajen yin bayani,barikiga nayi sallah kar lokaci ya ƙuremin. Ohh yawwa nama manta,in kingama aikin saka kan kada ki manta hajiyah Maryam na nemanki,yau baki gyara mata side ɗin ta ba,bayan kuma kinshiga sa safen" Dumm gabana ya buga,sai yanzu na tuna abinda ya faru,tabbas na shiga kaman zanyi aiki,amma sainayi bincikena kawai na fito. Runtse ido nayi tareda jijjiga shi,Allah gani gareka.

Ahmad (POV)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull