Kenza eBookz

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 7

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 7

Sanadin caca book 2 complete Chapter 7: Sanadin caca book 2 complete Chapter 7. A tsaye yake a gaban mutumin wanda kamanninsa suka sauya baka gane komai a…

3,184 words

A tsaye yake a gaban mutumin wanda kamanninsa suka sauya baka gane komai a fuskarsa saboda wahala da kuma dukan dayasha. Ɗayane daga cikin ƴan kungiyar BC wanda aka kama shekara biyu baya,duk yadda za'ayi dashi yayi magana amma yaƙi,da haushi ya ishi masu tambayar sukayi masa lahani sosai. Yanzu ma cewa yace a kawo masa shi ko zai iya gane wani abun,duk sun tabbatar masa da yazama mahaukaci ai da daɗewa,shikaɗai sai yayi ta dariyah yana cizon baki. Anyi kimanin awa guda kenan Gen Ahmad yana gabansa,amma yaƙi cewa komai. "Kai ɗago ka kalleni shin ka sanni?" Amma shuru kaman yana magana da kungi,wani yashigo wajen tareda sara masa,kana yafara da cewa. "Gen Neelah da Eemran suna neman izinin shigowa,tun ɗazu suke waje" "Kace musu su shigo" Neelah ce tafara shigowa kana Eemran,gaisheshi sukayi kafin Neelah ta miƙa masa wani file.. "Yallabai ga bayanan da muka samu a asibitin,bayan tsawon bincike bamu samu komai ba,saida muka duba files na hotunan marasa lafiya har na shekara biyun kafin muka gano naka." Tun kafin ta gama bayanin ya buɗe file ɗin yana kallo. Hotone kawai a jiki sai suna ta sign. "Gojee???" Shine abinda Ahmad Ya faɗa cikeda mamaki.. "Miye kuma goje,narasa sunan da zanyi amfani dashi sai goje?" "Eh goje ƙwarai kuwa goje,shine shugaba ai na yanzu goje baaa" Mutumin dayake gabansu ne yafara faɗa yana wasa da babyn robar da take hannunsa. Da sauri Ahmad ya tsugunna a gabansa tareda cewa. "Eh shi kasanshi?" "Hhhhhhhh goje bindigar roba ba" Tsuka yayi ya tashi tareda sake kallon su Neelah. "Shikenan iya abinda kuka samo,waye to ya kaini asibitin,ƙungiyar BC ce?" Jijjiga kai Neelah tayi kafin tace. "A yanda suka faɗa mana kuma kaga wannan saka hannun,sunce matarka ce ta kawoka asibitin,itace ma take zaune a wajenka har ranar daka tafi. Sannan bayan ka tafi tasuma suka karbeta a asibitin,har sukayi mata test na juna biyu....bayan sun sallameta kuma basusan ta da kuma daga inda take,amma sunce jininta ya hau sosai ga yaron ciki,da ƙyar idan batayi barin sa ba" Zaro ido Ahmad yayi yana kallon Neelah kamar ya samu madubi,mata da kuma ciki nasa wai? Abin takaicin kuma bai tuna komai ba? Tabbas daya tashi kam yaga wata mace a gefen gadonsa a kwance,kaico da bai tasheta ba,yasan da duk baisha wannan wahalar ba. "Taya zakuce to babu sunanta da kuma garin da take,wannna ba abune da hankali zai ɗauka,kuxo muje asibitin ina buƙatar duk wani bayani daya shafeta" "Am sorry sir,amma mun iya ƙoƙarinmu amma bamu samu komai ba,ƙarshe ma sai suka ce wai anyi musu kutse waccar shekarar,to a lokacin sun rasa data da yawa na bayanai" Wani gumi ne ya yanko masa,bai san lokacin daya samu waje ya zauna ba yana dafe kai,wannan wane irin abune ne haka. Tashi yayi zai fita,har yaje bakin ƙofa mai kulada wajen yayi masa magana. "Sir ya zamuyi da wannan mutumin?" "Zai warkene?" "Ahah ƙwaƙwalwarsa ta lalace ba lallai va" "To kuyi duk yanda zakuyi dashi,kai Eemran ran ka rufemin office ɗina bazan koma ba,gida zan tafi" A hanyar zuwa motarsa yaji wayarsa tayi ƙara,shareta yayi harta katse,saida aka sake ƙira kafin ya fito da itah ya duba. Hajiyah maryam ce take ƙiransa,har bazai ɗaga ba saikuma ya danna ɗauka. "Har haka na zama a wajenka saikaga dama ka ɗau ƙirana?" "Shin me kike buƙata?" "So nake kazo inda nake akwai maganar dazamuyi?" "Inada........" "In kanaso kaji sunan matarka da kuma a wanne gari take to kazo inda nake,sannan kayi abinda nace" Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar,sauƙe wayar yayi a kunnensa tareda runtse ido,abin bai wani bashi mamaki,domin hakan ba shine farau ba. Yarigada yasan bashida wani mutum ɗaya daya yarda dashi wanda ba nata bane.

Ƙofar motar ya buga tareda jingina kansa a jiki. Yakai aƙallah minti biyu a haka kafin ya buɗe motar ya shiga. Kai tsaye ma'aikatar data buɗe ya nufah,ransa badan yaso ba saidan bashida zabi. Get ɗin aka buɗe masa ya shiga,mutane sai zirga zirgarsu sukeyi,a ransa yace hankalin su kwance kaman basu san da wacce suke zaune ba. Bayan yayi parking kai tsaye makeken office ɗinta ya nufah,babu sallama kawai ya saka kai. A zaune take a kan kujerar da take gaban makeken wani tebur,magana sukeyi da wata. Ta gefen ido ta kalleshi kafin ta cigaba da maganar ta. Shikuwa ganin haka yasa yakama wata kujera a gefe ya hakimce akanta. Fuskarsa babu yabo ba fallasa,duk tururin dayake cikin zuciyarsa amma haka ya shanye shi ya bayyana tamkar a nutse yake a zahiri. Bayan matar ta fita zuyawa hajiyah maryam tayi akan kujerarta tareda ƙare masa kallo daga inda take zaune. "A tunanina ba ƙirana kikayi domin ki ƙaremin kallo ba,dan haka ki tafi kanki tsaye maganarki,mai kike buƙata?" "Nima a nawa tunanin ko baka ɗaukeni uwaba,naci darajar na haifi yakai,kokuma na amsa sunan matar ubaka koh.....dan haka ba gaisuwa ne malam Ahmad?". Ɗauke da murmushi akan fuskarta tayi maganar,inba wanda yasan abinda take aikata masa ba ko shi kansa,mutum zai ɗauka a yanzun ba kallon tsana take aika masa ba sai na ta raina wayonsa,ta guma dariyar yanda ya tsime fuska shi a dole kada ta rainashi.

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2* ...12...

"Okay let's go to the deal,(Aha bari muje yarjejeniyah),zan faɗamaka wacece matarka,sannna kuma a ina take,amma da sharaɗin saika daina binciken da kakeyi a yanzu na ƙungiyar BC,duk cewar nasan idan na kacigaban babu abinda zaka samo saidai ka sake saka rayuwar a halaka karo na biyu. Dan haka ka ajiye case ɗinnan ka kama wani daban,idan kayi hakan ka tsira kuma zaka san inda matarka take" Wani kallon kinsan mai kike fada Ahmad yayiwa hajiyah maryam,saida tagama bayanin kafin yayi ɗan murmushi. "Amma da kikayi wannan maganar ke kanki kinsan idan zan yarda da ita kokuma akasin haka, babu abinda zaisa na daina wannan aikin matuƙar ba kama wanda suke da hannu da shuni a ciki nayi ba. Batun sanin inda matata take,dama bawai saninnata ne maƙasudin abinda yasa nake nemanta ba,bazaki san dalilin ba kuma,dan banyi maganar da kowa ba bare ki sani" Tashi yayi cikin bacin rai zai fita daga office ɗin,magana tasake yimasa hakan yasa ya tsaya da fita. "Bazaka daina ba....koda kuwa na kusada kai zasu cutu akan hakan,koda kuwa abinda zaka tono ɗin bazai maka daɗi ba?" "Ban damu da daɗinsa da kuma rashinsa ba,indai zanyi nasara hakan ma kaɗai ya wadatar" "Hmmm yaro man kaza,kanada masoya a boye,haka zalika kanada maƙiya ma a boye,abinda yake zai bayyana maka maƙiyanka amma kuma zai cutar da boyayyun masoyanka,tunda kace kaji ka gani na amince da zabinka,i like to see you try" Ƙarisa maganar tayi tana ɗan sosa biro a goshinsa,bayan ya fita ajiyar zuciya tayi tareda lumshe ido. "Shin ya zanyi da yaronnan ne ni maryamu,gabaɗaya narasa taya zan juya akalarsa daga kan abinda yake shirin yi" Ƙirane ya shigo ta wayar office,hakan yasa ta ɗaga da sauri. "Halle jikin nasreem ne?" "Eh ranki ya daɗe,yanzu haka ma ana nemanki da gaggawa" "Ohk ganinan zuwa" Tana kashe wayar tafita daga office ɗin da gaggawa,wani corridor ta bi da gudu har tana tuntube. Ɗaki na biyar a bangaren hagun ta shiga. Likitocine guda biyu akanta,da kuma wasu mata masu uniform ruwa kalar omo. Ɗaya daga cikinsu ce taga shigowar hajiyah maryam ɗin,da sauri ta matsa domin bata damar kallon yarinyar da take kan katifar. Cije cije take da fizge fizge,gaba ɗaya bata cikin hayyacinta,fatar bakinta duk tayi jawur saboda cizonta da take kaman zata cireta. Ƙarisawa gabanta tayi a hankali daidai lokacin da likitar tayi mata wata allura.. Sauke numfashi tafara tana jan nishi kaman mai alamar fitar rai,can kuma sai tayi shuru kaman wacce ta mutu,da alama bacci tayi. "Naga tayi bacci da wuri,kenan yau da sauƙi ba kaman jiyaba da muka kai dare?" Hajiya Maryam tayi maganar cikin tausayawa,kaman ba itace take izza ba. "Ehh hajiyah mun samo allurar da tayi daidai da jikinta yanzu,Inshaallah zata samu sauƙi" "Mashaallah hakan yayi, aikinku yana kyau,ya dai sauran marasa lafiyan,da fatan suna samun sauƙi" "Eh suma da sauƙi,mai siyo maganin ma yanzu zai dawo,jariran har yanzu jikinsu da zafi" "Bakomai kada ku damu,kudai kuyi abinda ya dace,duk abinda ake buƙata ba matsala bace" Tashi tayi tasake kallon wacce take kwance akan gadon cikeda tausayi. "Hmmm wanda sukayi raping ɗinki saisun biya ba ɗaukar bashi,babu wanda zai sha idan yashiga gonata" Lokacin da tayi maganar ta dawo ainihin kalarta,fita tayi da sauri kanajin takun takalminta ƙwass ƙwass harta bar wajen. Wani sashen tasake shiga,wanda su kuma duk yarane a wajen suke wasa. Suna ganin tashi go suka fara rige rigen isa wajenta,da alama su basa tsoranta kaman sauran mutanen waje.

..........

Yau banje sashen Ahmad gyara da wuri ba,yayi fadan har ya gaji amma ko a jikina,dokokinsa indai ba wasu muhimmai ba babu wanda nake bi a ciki. Tafiya nake ina kalla kalle,nazo daidai wuce na shiga sashensa kenan naji murya dr Saleem yanamin magana. "Malam Sumaimah barka da safiyah,ko nace safiya,da naga shabiyu ta kusayi" "Ahh habadai da saura,ya naganka a gida baka tafi wajen aiki ba" "Uhm na dawone,abu na ɗauka yanzu zan koma" Uhm kawai nace fuskata ɗauke da murmushi na wuce,shikam ya fita zakka a gidannnan a kirki. Fulawar dana yanka nake murzawa a hannuna harna isa sashen,kaman nawa kai tsaye na wuce. Babu wani datti sosai saboda gyaran dayake samu daga gareni,sannan kuma ba zama ake ba sosai. Sama sama na gyara ko ina kafin na dawo falon ina kallonsa,kana gani kasan bana mace bane,ga waje har waje amma fayau babu abubuwan daukar ido a ciki. Fita nayi lambu na cinko fulawowi wanda suke cikin tukunya na saka a ƙofar inda ya dace. Labulayenma sanjasu nayi daga farare zuwa jajaye,irin carpet ɗin falon. Yaraf na zube a kan kujerar falon ina maida numfashi,nikaina gyaran yayi min kyau ba kadan ba. Gumi naji yana yankomin saboda motsa jikin danayi,gashi bangama ba inason saka room fresh da turaren banɗaki. Yunƙurawa nayi na tashi na shiga ɗakin. "Fadi ba'a sakani ba,sai gwanintar da ba godewa nake. Ohh kodayake zan samu lada a matsayinsa na mijjna. Bayan na gama komai har zan fito daga banɗakin sainaga yayimin kyau sosai. Wata zuciyar ce tace nayi wankana kawai a nan basai na tafi ba,uh uhm anya kuwa.'kiyimana da sashen mijinki ne ba laifi kikayiba. "Uhm mijin da bai san daniba? Baridai na ɗana naji mai akeji,wannan sabulan daga gani zasuyi ƙamshi" Hannuna na miƙa na murɗa wata makunna dannaga ko tana aiki,ban zata ba saiji nayi ruwa daga saman banɗakin ya yimin wankan rashin shiri daga sama har ƙasa. Ahhh ajiyar zuciya naja,ina kallon yanda kayana suka jiƙe jaraff. Wayyo ni wlh ba haka naso ba. Cire kayan nayi na matsesu na shanya a jikin glass ɗin inda aka zagaye domin wanka. Ruwa na haɗa mai ɗumi nayi wanka a cikin bahon,ina ciki idona yana kallon sama inda wasu ƙofofi suke,gabaɗaya bantaba kulada su ba sai yanzu dasukamin wanka. Bayan na gama fitowa nayi daga cikin bahon,towel ɗinsa da nagani a lanƙaye na saka,hankalina kwance na fito daga banɗakin ina kallon goge gashina da hannun towel ɗin,ɗayan kuma na riƙeshi a ƙirjina. Nama bushe dan tun ɗazu naketa yarfe kayan su samu su bushe,dan ma nasan ba dawowa zayyi yanzu ba sai an yamma. Dana shigo ɗakin kaina a sunkuye yake bamma kula da mutun dayake tsaye a dakin ba yanamin kallo ido buɗe. Daga ido nayi na kalleshi nace. "Ohh harka dawo yanzu,banyi zaton zaka dawo da wuri haka ba" Ganin bai bani amsa ba kuma yana kallon jikina da mamaki yasa na tuna mai yake jikina saida na kalla,narasa meyasa nakasa tsintar kaina da jin kunuyrsa,kodan nasaba da ganin a haka dayake a baya?. "Shin kekuwa mutum ce,kirasa inda zakiyi wanka sai a sashena,hakanma ki saka min towel,sannan na shigo ko a jikinki cewa ma kike wai nadawo da wuri,babu ko damuwa a ranki?" "Am sorry kayi haƙuri,wani waje na murda bayan na gama aiki,shine sai ruwa ya zubo ya jiƙemin kaya,tun ɗazu nake yarfesu amma basu bushe ba, shine na ari towel ɗinka,kuma na fito hakanne saboda nasan bazaka dawo yanzu ba" "Ohh yaushe aka saka min dokar bazan dawo ba sai lokacin da kika dibamin" "Nibance karka dawo ba" Wata harara ya zabgamin tareda nuna min ƙofa. "Zoki fice daga sashennan,dariya yabani ganin yanda yake iya ƙoƙarinsa wajen bai kalli inda nake ba,nikuma sainaji kaman nayi amfani da hakan. Jin shuru banzo na wuce ba yasa ya ɗaga ido ya kalleni,kaman mai tsoron kar a kamashi yana kallona ɗin. "Ba magana nake miki,wanne wane irin salon karuwanci ne?" Dumm gabana ya buga yayinda wani ƙululun baƙin ciki ya turnuƙeni,karuwanci ni ya ƙira da karuwa. "Karuwanci, nika ƙira da karuwa???" Hawayene suka cicciko a ido na,yayinda muryata tafara rawa. "Uhhhh karuwanci....bakaga karuwanci ba ai,bari kaga ainihinsa" Sakin zanin jikinnawa nayi ya faɗi a ƙasa,wanda kuma akan idonsa,runtse ido yayi tareda juyawa gefe. Takawa nake cikin ƙunan rai naje tagabansa zan wuce,dagani sai pant. Hannuna naji ya damƙo daidai lokacin dana kai hannuna zan buɗe ƙofar ɗakin na fita. Manta komai ai ba hauka bane,kuma nima ba dutse bace,abubuwan sun fara isa ta haka. "Ke bakida hankali ina zakije a haka?" Duk da naji haushin maganar daya yabamin amma ta wata fuskar naji sanyin ganin duk da bai tunoni ba amma yana kishina..dama kuma abinda nakeso naga yayin kenan bawai fitar zanyi ba. "Zan fitane nayi karuwanci wanda kace inayi" "Mtsww ki koma kisaka kayanki,Idan ma so kike a ace daga wajena kike to hakan bazayyi aikiba" Juyowa nayi na kalleshi,wanda yayi saurin ɗauke hannunsa daga damtsena yana ja da baya. Har sannan baya kallon inda nake,dama bawai burina kenan ba a yanzun. "Zan saka towel din amma da saiKa yarda zaka banni na zauna har sai kayana sun bushe,kokuma ka tambayomin ummi tabani kayana. Inkuma kanada kayan mace toh?" Bai bani amsa ba sai zuwa inda towel yake da yayi ya ɗakkoshi,dawowa inda nake yayi ya rufashi a jikina,cikeda bacin rai yake kallona tareda yin magana a kusan fuskata. Kisaka kije ki ɗebo kayanki Ga nan dryer kiyi amfani da ita ki busar dasu. Yana gama faɗin hakan ya fita daga ɗakin. Juya ido nayi tareda komawa banɗakin na ɗauko kayana. Atampa ce riga da zani,dayake cotton ce har yanzu a jiƙe suke. Ɗakkosu nayi na dawo ɗakin na kunna dryer,ni bamma kawo wannan tunanin ba.

Ahmad (POV)

Tunda na fito daga ɗakin yaraff nayi akan kujera,dama ga gajiyar dana ɗebo . Wai inada mata maybe hadda ɗa,maganar ta dokeni sosai ban taba tsammanin hakan ba. Ga kuma itama waccar matar abban,shin mai na tarewa matar nan ne a rayuwarta,da im bata shiga rayuwata ba bata jin daɗi. Idan har da tayi nasara wannan lokacin kam bazai taba yiyuwa ba,dolene sai na binciko laifukanta a fili ta karbi hukuncinta. Mtsww tsuka naja da hotunan waccar suka fara walƙiya a cikin kaina,shin kanta ɗaya kuwa a abinda tayi. Amma alamunta bai nuna tanada tabin hankali ba,gabaɗaya nakasa gane yanayinta guda ɗaya,wani lokacin taji kunya,wani lokacin tsoro,a wani yanayin kuma kulawa,yanzu kuma na nunamin rashin tsoro da kunya. Wato ta zefar towel bata ma ɗaukeni namiji lafiyayyeba,ko a jikinta. Wani abun mamakin kuma batayi kama da wacce take kasa jikinta a titi,duk da abinda tayi amma hakan yagaza sakani jin tsanarta,meyasa to mafita ɗaya ce inaga na koreta kawai. Buɗe idona nayi a hankali jin ƙarar bude ɗaki. Tasaka kayannata yanzu,saidai muna hada ido ta tasakar min wani kallo najin haushi.. To mai laifina a ciki,tayi abin karuwai na faɗa kuma yazaba abin faɗa. "Kizo ki fita,na koreki kada ki sake dawowa,sannan koda kin roƙeni hakan bazai amfani ba" Ga mamakina bata ban haƙuri ba kuwa tayi hanyar waje. Yunƙurawa nayi zan tashi sai naki cikina yayi zafi kaman an tsinkamin hanji. Hakan yasakani sakin ƙara mai ɗan karfi.

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki Small 14k Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

*BOOK 2* ...13...

Sumaimah (POV)

Hmmmm daman nasan zancen gizo bai wuce na ƙoƙi,banda korar babu abinda ya iya. Har naje bakin ƙofa zan fita naji ƙararsa,da sauri na dawo tareda nufar inda yake a kiɗine,duk da inajin haushinsa amma kuma muradin ganin ko lafiya yake shiya rinjayi zuciyata. Hannuna na saka ina daga kafaɗarsa,ganin ya sunkuya yana riƙe ciki. Jijjiga shi nafara ina tambayarsa mai yafaru,amma shuru bai bani amsa ba saima ture hannuna da yayi. Ɗagowa yayi idonsa yayi ja ya kalleni. "Ke miye damuwarki ne,banace ki tafi ba?" Tsuke fuskata nayi tareda tashi daga kan kujerar,hanyar waje nayi batareda na sake jiyaba nasan. (da kallo ya bita cikeda mamakin wai tafiya tayi kuwa,duk da a fili yace ta tafin,amman wani bangare na zuciyarsa sai yaji kaman ya tsaida itah.)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull