Kenza eBookz

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 13

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 13

Sanadin caca book 2 complete Chapter 13: Sanadin caca book 2 complete Chapter 13. Kinsan mai na tarar bayan naje ƙasar england,Muhammad yanada mata,juliat…

3,046 words

Kinsan mai na tarar bayan naje ƙasar england,Muhammad yanada mata,juliat amma ta musulunta ta koma Amina,saboda soyayyarsa yasa ta zama ɗaya daga cikinmu,shikuma ya aureta ne yasaka ta a ƙarƙashinsa gudun kada ta sake komawa gidan jiya.. Baƙar fatace ƴar garin benue,karatu ya kaita can ta haɗu da Muhammad,anan ta ƙwadaitu da musulunci amma saidai in zai aureta yazama tana ƙarƙashin ikonsa,saboda iyayenta bazasu karbeta ba. Daya zo wa abbanmu da zancen bai ja ba ya amince masa,ganin niyyarsa na inganta rayuwarta. Lokacin danaje naga part biyu a gidan tana ɗaya naji tsoron zama da itah,kuma nayi mamakin yanada aure ba'a sani ba,ashe mu yaran gidanne kawai bamu sani ba. Bayan sati ɗaya na zuwannawa na saki raina ,ganin tanada mutunci sosai,sabon addinin nata kawai tasaka a gaba sai kuma karatunta na medicine da takeyi. Nima a makarantar da take na samu gurbin yin masters wato oxfort. Muhammad ne yake ajiyemu a makarantar kana ya wuce wajen aiki. Zamane mukeyinsa na mutunta juna,kowa yana harkar gabansa,a bangaren mijinmu kuma muna samun soyayyar sa fiyeda tunanin mai tunani,domin shiɗin mutum ne da sai an bincika kafin a samu tamkarsa wajen bawa mutum haƙƙinsa. Kwanci tashi har munyi shekara guda da aure,ita kuma amina tayi shekara biyu. A lokacinne kuma aka zo auren zainab,murna ta komawa ciki tayi,saboda a lokacin ba dama naje ina project na gamawa ta. Sai Muhammad ya tafi shida Amina,dama tunda tayi aure bataje ba. Satinsu ɗaya suka dawo,zainab har kuka tayimin akan banje ba,amma sai haƙuri na bata. Tare suka dawo da hajiya Mammah akan zatazo taga ɗakinmu. Itakam daman hajiya Fatima bazata zo ba tana kunyar dan fari irinna fulani. A ranar da suka dawo na tashi da zazzabi, dan ma Muhammad na ɗakina,domin nasha wahala sosai da daddare,amai ga zafin jiki. Washagari da safe ya kaini asibiti,Amina Da hajiya Mammah basu sani ba suna sashen Aminan. Gwajin farko aka cemin inada ciki na wata uku,nayi murna sosai musamman dana shafe shekara guda daman babu komai.. Shima Muhammad yayi farinciki fiyeda ni,ganin bayan shekara biyu da aure zai samu ɗa ko ƴa. Da safen Muhammad ya tashi su hajiyah Mammah ya faɗamusu,itakam Amina ana faɗamata a take ta rungumeni tana lelleƙani,har ta bani tausayi,saboda ni kaina shaidace akan son yaranta,don abinda take karanta ma kenan a bangaren karatunta. Itama hajiyah Mammah kabbara tayi tareda ɗaga hannu sama. Waya Muhammad ya ciro akan zai ƙira gida,amma hajiyah Mammah ta hanashi,a cewarta ya barta takai wanann albishir ɗin gida. Da farincikinsa ya amince da maganar ta. Tun daga wannan lokacin nafara ganin gata a wajen Muhammad,Amina kuwa ko ban nuna alamar komai ba saita gwadani. Satin hajiyah Mammah daya ta tafi gida. A haka nikuma na cigaba da rainon a cikina,akan cewar idan cikina yazo haihuwa zan koma gida na haihu. Naji daɗin hakan sosai lokacin danaji Muhammad ya faɗa. A ranar dana shiga wata na tara muka kamo hanyar dawowa gida,murna a wajena bazata boyu ba. Bayan mun sauƙa mun kai kaman minti biyar ba motar datazo daukarmu,nikamma harna gaji,saida suka samamin kujera na zauna,Amina sai sannu takeyimin. Munan nan zaune wata mota ta zo baƙa,wani mutum haka gajere ya fito daga motar, wannan kuma wanene,bansanshi a gidan ba ko sabon driver ne. Nidai tun kafin su ɗakko kayanmu na ja jiki zuwa cikin motar,dama na gaji. Tafiya muke amma maimakon hanyar gida sai naga suna wani waje daban,Muhammad ne ya fara ƙoƙarin yiwa drivern magana,amma sai ya shaqa masa abu a hanci. Ganin haka yasa muka saka ihu nida Amina,domin abin ba ƙaramin razana mu yayi ba. Duhune ya fara lullube ganinmu,yayinda hankalin mu yake neman hanyar fita daga cikin kanmu. Kafin idona ya ƙarisa rufewa naga drivern ya saka facemask,yana kuma magana da wani ko wata a waya. Ruwa aka watsamana,shine sanadiyyar buɗe idanummu muka ganmu a cikin wani cell. Wajen kaman kango yake,amma a rufe kirif domin badan hasken da aka kunna na za'a samu duhu a wajen.. Jijjiga ƙarfen bakin ƙofar nake ina kuka tareda ƙiran Muhammad da zainab,a zatona basa wajen,sai can bayan wani ɗan lokaci tukunna naji tarin Amina,ƙiran sunanta nafarayi sai can ta amsamin a galabaice,mai suka mata? Ina Muhammad yake shi. Kafin na samu mai bani amsa naji takun sawun mace yana tahowa. Wata mata ce ta rufe kanta da baƙin ƙyalle,bana gane wanne irin kallo takemin saboda bana ganin fuskarta sosai.. Batayi min magana ba,sai bada umarni da tayi da yatsun hannunta. Kaman abin tsafi haka naji ihun muryar Amina da kuma Muhammad.. Zare ido nayi tareda fara jijjiga ƙarfen wajen,wayyo wacece ita mai takeyi musu da hannunta?. Maganar data gefenta tayi yafi komai ɗagamin hankali. "Ranki ya daɗe sun ƙarisa mutuwa a yanzu" "Ku sakata a wajen ajiyar gawa,shikuma ku kaishi bakin hanya daidai inda za'a ganshi" Mutuwa mai take nufi,kashesu tayi kenan meyasa?? Ƙara na sake mai cikeda firgici,wanda sanadiyyar hakan ya haifar min da yankowar ruwa ta ƙasa na,nishi na fara cikin kukan,wanda bazan iya tsaidashi ba.. Jin kalar nishin danake fitarwa ne yasakata itada matar juyo da hankalin su gareni. Nan ma kaman abin tsafi ƙofar cell ɗin danake ciki ta buɗe,jan hannuna mataimakiyar tata tayi zuwa wani ɗakin daban,duk da halin danake ciki amma sai duka nake kaimata zan ƙwace,shikenan sun kashemin mutane biyu kenan danake rayuwa dasu,shikenan bazan sake ganinsu ba. Wayyo mijina,zan haihu batareda yana wajen ba,dukkuwa tsananin muradinsa na son ganin gudan jininsa. Saboda tashin hankalin danake ciki hankalinnawa ya gushe lokacin da jaririn ya faɗo daga jikina. Ihun sane ya dawo dani cikin hayyacina.. Duk halin da nake ciki hannuna na rawa na miƙa hannun zan dauke,amma haka naga wani hannun dayafi nawa hanzari ya ɗauke. Binta nayi da ido ganin yanda ta riƙe a jaririn a hannunta tana jijjiga shi da jininsa da komai. Hanyar fita daga ɗakin naga ta nufah,da gudu na bita a baya har ina faɗuwa saboda rashin ƙarfin jiki,domin a zatona kasheshi zatayi kaman yanda ta kashemin mijina. Inda ta kawoni nagani,babban falone amma ba komai ne a cikinsa ba banda wata kujera,wazan gani a kai matar nan ce mai hula wacce ta kashemin miji. Baƙin ciki naji da fargaba lokacin danaga matar tasaka mata yarona akan hannunta,bai kamata zuwansa duniya kenan ya hau kan hannun waɗannan azzalumanba. "Maryam" Naji ta ƙira sunana,muryar tayimin kaman nasan wacece,amma kuma mai zai kawota nan wajen,mata kamilah mai ɗumbin ilimi. "Nasan kin gane muryarta,kina shakkane kawai da tunanin nice kokuma ba nice bace,to niɗin ce dai wacce ƙwaƙwalwarki ta baki" Saka hannun tayi ta zare hular kanta,"hajiyah Mammah" shine abinda na faɗa cikin mamaki da ƙarfi. Dariya ta sheƙe dashi tareda cewa. "Karkiyi mamakin hakan,komai ya faru ke kika jawo ba kowa ba,san kanki ne dana mahaifinki ya jawo komai. Ɗana ya nuna miki so,nima na nuna miki so amma haka kika tsallake kika tafi taki rayuwar,shi kika barshi a cikin duhu. Duk wanda zan nuna wa kulawa da so ƙarshe wajen fatima yake komawa,ni a barni dagani sai ƴaƴana,shikansa Hamma ko ƙafarsa zan tsugunna na lasa haka zai take harshena ya tafi wajenta. Dan haka wannan ya ƙare, duk sainaga bayan kowa amma bandake ke kaɗai. Kinsan meyasa? Saboda kece soyayyar Aliyu ta farko,amma akan idonsa yarasata aka bawa Muhammad saboda son kai,kukayi ta murnar biki da shagali,nikuwa babu wanda ya kulada ni da ƴaƴana,ina ji ina gani yabar gida amma babu wanda ya tsaida shi bare yayi masa abinda yake so. Har lokacin da kikayi aure inada yaƙinin kashe aurenku,ba yanda banyi ba abu yaƙi yiyuwa,ƙarshe ma wai harda ciki gareki. Hakanne yasa nayi muku gabaɗaya,yanzu dolene ki auri Aliyu tunda Muhammad ya mutu" "Bazan aure shi ɗin ba,badai kisane aikinki ba to ki kasheni nima amma bazan aure shin ba" Dariya tasake tuntsirewa da itah. "Mai kike nufi,dama nasan ai zaki ce haka,zan baki zabi guda biyu. Ko kiƙi amincewa na kasheki,na kuma kashe wanann yaron. Ko kuma ki amince da ƙudurina,nikuma zan bar ɗanki da rai,amma da sharaɗi duniya bazata shaidashi a matsayin ɗanki ba,saboda bazai yiwu ki auri ɗana zaki haifamin jikoki yazamana kuma wanann yana ranki ba. Dan haka zai shiga alhalin Hamma ne a matsayin amina,dama already na faɗa musu cewar itace da ciki bake ba" "Kutt mai kika ce, itace da ciki bani ba?" "Da mai kike nufi,har abada bazan bada wannan lbarin ba,ke din dan Aliyu aka halittoki ba Muhammad ba,dan haka bazan taba bada albishir na kinada cikinsa ba sam. Yanzu zabi ya rage ga naki. Zan baki wata biyu ki zauna anan ki gama bawa ɗanki soyayya,daga nan kuma dole tsana zaki dunga nuna masa,ke zaki raineshi amma raino na azaba,duk ranar da soyayyar sa ta ɗarsu a ranki to sunansa matacce,saiki zaba ko ceton jinin Muhammad na ƙarshe dayake muradin gani,kokuma mutuwarsa da taki da kuma ta dukka ƴan uwanki da ubanki? Wanann shine hukuncinki da butulcin da kikayiwa soyayyar ɗana,kuma haka zaki girbeta har ƙarshen rayuwarki. Sannan kada ki manta,dukkan ahalin gidan suna ƙarƙashin ikona ne,kuskure kaɗan zai kaiki ga yin dana sani marar misali"......

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2* ...22...

Hajiyah Maryam tana zuwa nan da labarin muryarta da ƙyar take fita saboda kuka. Yayinda nikuma a nawa bangaren badan kukan da take ba bazan taba yarda hakan ya faru ba. Cigaba tayi da maganar wanda zuwa yanzu tana zaune tabas a tsakiyar ɗakin.. "Soyayyar yarona wanda ko zafin haihuwarsa bangama ji ba,ita tasakani amincewa da kuɗurinta,a tunanina idan yana raye ko bana nuna masa so to ba matsala,ashe vansan jure ganin ɗanka yana wahala bakada ikon taimaka masa hakan yafima mutuwar zafi,koba komai Muhammad da Amina su sun huta. Haka na shafe wata guda ina kulada ɗana wanda nasaka masa suna Ahmad,bayan wata daya ya ƙare nasake roqarta ta ƙaramin wani watan. A ƙarshen wata na biyunne na miƙa mata yaron,yayinda wata nurse tayimin allura yanda alamun haihuwar danayi zasu gushe. Ina kuka ina komai haka tasaka wani dattijo data cikashi da kuɗi ya kaini gida,akan wai tsintata yayi a sume a gefen titi inda mukayi accident ,dan cewa tayi wai ƴan uwan Amina ne suka kashe Muhammad ita kuma suka tafi da itah. Kowa sai tsinemusu yakeyi,harda marigayiya Amina wacce bataji ba bata gani ba. Kukan mutuwar Muhammad ne ya dawo sabo saboda bayyanata,kowa na cewa ana ta ƙiran number Amina amma bata shiga da gangan dama ta gudu. Bayan sati biyu da faruwar hakan har sannan ko magana banayi,saboda kewar yarona da kuma mutuwar abokan zamannawa wanda na saba dasu. A lokacinne kuma wata mata tazo ƙofar gida ta ajiye ahmad ta daddare haɗeda wasiƙa ta tafi. Wasiƙar tana ɗauke da cewar wai ɗan Amina ne ta mutu su kuma bazasu riƙe jinin Muhammad ba,dan haka ga ɗanmu nan,sunansa Ahmad. Abinnan yayimin ciwo sosai amma ba yanda zanyi,kowa bayyi na'am da Ahmad ba,saboda baƙin Amina da suke gani,sai hajiyah Mammah wacce ta rungumeshi tamkar jikanta,hakanne kuma yasa tasake fari a idon mutanen gidan,sai a sannan nagane ashe abinda take kenan. Kwanci tashi bayan yaye har hajiyah Mammah ta yaye Ahmad kowa ya manta abinda ya faru,nikuma saboda bana kula Ahmad yasa aka faramin ganin kaman dan bani na haifeshi bane,haka na toshe kunnuwana badan komai ba saidan kare lafiyar yarona,duk da nasan kularda take bashi na munafurcine amma dai yanamin daɗi. Ana cikin hakanne Aliyu ya dawo,wanda nasan duk matsawar hajiya Mammah ne,lokacin da aka tada zancen aurenmu kowa ya amince,harshi da dama sona yana zuciyarsa,inaga kumani da daman munyi yarjejeniyah da itah. Auren bayyi wani armashi,bansan kosu yayi musu ba,amma nikam jinake kaman an ɗauramin mutuwa,kulawar dayake banine ma da zuciyarsa ɗaya,tunda nasan shi bashida laifi shiyasaka ni barin wani abun ya wuce,tunda nasan ƙaddarata ce. Bayan aurenmu da sati ɗaya zainab tazo gidana ina kuka na faɗamata mai yake faruwa,shima kuma dan ta faramin faɗane akan kiyayyar danake nunawa Ahmad. Bayan na faɗamata saida na gargaɗeta tayi shuru amma sai taƙi. Lokacin tana goyon Neelah, tazo gida wunin arba'in,wannan magana dana faɗamata nayi dana saninta yafi cikin kwando,domin a daren tana shirin faɗawa hajiya Fatima bakinta ya manne,tayi tayi tai magana abu ya gagara,haka aka bari akan saida safe za'a kaita wajen magani. A daren aka nemeta sama da ƙasa aka rasa,tun masu magani suna cemana tana gari kaza har muka daina nema muka zubawa sarautar Allah ido. A sannan ɗin ban daddara ba naso ɗaukar mataki amma banyi nasara ba. Ƙarshe ma wani abu hajiyah Mammah tasakamin a jikina,duk lokacin danayi yunƙurin bata mata shiri sai naji kamar yana zuqar jinina ta ciki. Haka nacigaba da fama da wannan yanayi babu wanda ya sani har na haifi Maimuna,koshi Aliyu bai san mai yake faruwa. Tun bana ganin laifin Aliyu da su Aina'u har yazamo ya fara shafarsu,kuma a lokacin ne na nemi aiki na fara saboda ya ɗaukemin hankali. Shekarar mu biyu da aure muka tare a sabon gidan Aliyu,wanda shine wannan,a sannan ne kuma aka bashi muƙamin general. Naji daɗin dawowar wani gun kuma banji daɗi ba,saboda ninake kulada Neelah,sannan ina kallon Ahmad duk da bana kulashi,amma kuma koba komai na daina ganin hajiyah Mammah a kusada ni. Dan babu ɗan adam dana tsana a rayuwata kamarta. A haka rayuwar tacigaba da tafiyah harna haifi su Saleem inada cikin Fatee. Lokacin na zama babbar lawyer,shikuma Aliyu yazama air marshall a shekarar,wanda duk da saka hannun abba nah,saboda rashin Muhammad yasa yake ganinsa tamkar magajinsa. Can you imagine wani kisan raini hankali wai su abba Hamma da hajiya Fatima sun dawowa daga umarah tayar motarsu ta kunce motar ta ƙone. Ko qur'ani aka bani na danna nasan aikin hajiya Mammah ne,amma ya zanyi toh shikenan suma ta gama dasu. Lokacin da abban nah yaji wannan labarin shima ciwon zuciyarsa ya tashi,dama ba lafiyace dashi sosai ba,yamayi retire. Bayan wani lokaci Aliyu ya damu sai ya dawo da hajiyah Mammah gabansa,saboda ita kaɗaice dukka yaran gidan sunyi aure. Mariya kamma watan haihuwarmu kusan ɗaya,ta haifi Mulaifah tanada cikin na biyu. Ita a haihuwa ta rasu ɗan shima ya koma,nikuma na haifi Fatee aka sakamata sunan hajiyah Fatima. Neelah kuma saboda babu hajiyah Fatima saina kaita gidan marayun dana ke kuladashi,lokacim ma ba babba bane,amma tunda bazan iya riƙeta kusada ni ba gudun cutarwar hajiyah Mammah gwanda na kaita inda zata dunga ganin yara sa'anninta,kuma atleast zan dunga ganinta kullum. Batayi ko wata ɗaya bama Aliyu ya kaisu india itada Ahmad wajen amininsa zasuyi karatu a can. Kasancewar lafiya suke yasa na kwantar da hankalina na cigaba da kulada wanda suke gabana. Ana nan har akayi auren Maimuna,itakuma Neelah bayan sun gama makaranta ta dawo gida tana training ɗinta a nan abuja,amma bata zauna a gidan ba saita zauna a barrack,shikuma Ahmad bai dawo ba sai daya gama komai. A tunanin sa kokuma nace tunanin da aka saka masa kuma yake gani,nafi kowa tsanarsa a duniya,nan kuwa a kaff rayuwata dana tashi na tsinci kai na a uwa,kullum banda lissafi saina suwa yake tareda su,cutar dashi suke kokuma ahah" Kukane ya kubce mata wanda nima yasakani kukan,dama abinda yake faruwa kenan, tabbb lallai idan kaga mutum ya kabarshi,wato kenan ita kura ce da fatar akuya tazo ta labe anan wajen. "Kenan matar dana gani da wata ta shige jikin bango ranar danaxo gidannan......." Ɗago ido hajiyah Maryam tayi tareda ɗaga min kai. "Ita kika gani ba kowa ba,itada wanann shegiyar Raheenan,wacce ta ɗaukemin yaro lokacin dana haifeshi,su ne kika gani inda sun san kin gansu da tuni bakya numfashi,shiyasa nake cemiki kiyi taka tsantsan kada ki maimaita kuskurena." "Wannan hoton dana gani shine baban Ahmad,amma kince bai san Ahmad ba,ya na ganshi kuma a hoton?" "Bada shi akayi hoton,ni kaɗai nayi hoton ranar sunansa,wanda na roqi hajiya Mammah ta barni nayi,shidin bayarwa nayi aka hadamin kamar yana cikin hoton" Uhm jijjiga kai nayi tareda jajanta lamarin,shin waye zayyi tunanin abinda yake faruwa kenan idan ba gani yayi ba,lallai in kuwa hakane akwai aiki a gaba. "Akwai wani aikin da zakiyimin Sumaimah" Hajiyah Maryam ta faɗa tana tafa ƙafaɗa tareda jan majina,wanda tafito saboda yawan kukan data sha. "Please ki zauna dashi a wannan kwanakin,na ɗago cewar shiba ɗan Aliyu bane,dole za'a faɗamasa waye ubansa,kuma ace shi ɗan tubabbiyane wacce ƴan uwanta suka kashe ubansa,daganan wanda bai sani bama zai sani,dan haka be with him" "Ammm........amma taya zan zauna dashi bayan baisan ni wacece ba, bayason ina yin kusada shi alhalin yana ganina a matsayin wacce ba muharramarsa,saida nayi miki alƙawarin zan taimaka miki wajen ganin mai yake faruwa,sannan daga gobe zan fara aiki a sashen hajiyah Mammah,saboda gano wani abun" "Ahah bazan sakaki wannan aikin mai hatsari ba idan tagano wacece ke bazatayi tunani na biyu ba zata kasheki,ta kashe ɗanki. Kinsan ke wacece yanzu haka a wajenta kuwa......? Matsafanta sun nuna mata wacce zata kawo ƙarshenta matar ɗan data raba da iyayensa ne wato Ahmad. Sannan matar dazatayi sanadiyyarta itace uwar ƴaƴan sa. Abinda bata sani ba ya riga yayi auren,da ta sani bazata hana Mulaifah aurensa ba,hasalima ita zata ƙarfafa hakan. Shiyasa kada ta gano matsayinki ba yanzu ba tukunna" "Nasan da hakan kuma zan kiyaye,amma ki sani nima rayuwar ɗana data mijina nake dubawa" "Shikenan kije ki kwanta dare yayi zanyi tunani akai zuwa safiya."

Da haka na bar sashen hajiyah maryam ɗin zuwa namu sashen,duk da banida waya a hannuna amma nasan dare yayi sosai,dan tsitt kakeji babu motsin komai a gidan. Daidai nazo farfajiyar gidan zan wuce sashenmu naga mata guda da alkyabba,wadanda dai nagani farkon zuwana gidan. Yanzu kaman wancan lokacin ta jikin katanga suka wuce,daidai inda naga wannan zanen. Jijjiga kai na nayi tareda cize baki,wannan karon ko ɗar na tsoro banji ba na wuce. "Aradu kaman yanda kika gama taggunki to sai ya karye,kodan saboda rayuwar mijina dana ɗana bazan saurara miki ba sai asirinki ya tonu,wanda kike tsoron karsu gane kuma kike komai dominsu wato ƴaƴan ki,saisun gane wacece ke"

To fah Sumaimah in action.......let go!!!.

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2* ...23...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull