Sanadin caca book 2 complete - Chapter 14
Sanadin caca book 2 complete Chapter 14: Sanadin caca book 2 complete Chapter 14. Gudu gudu sauri sauri tayi parcking motar a ƙofar wani gida,kaman an…
3,117 words
Gudu gudu sauri sauri tayi parcking motar a ƙofar wani gida,kaman an turata ko gama saita ta batayi ba ta buɗe ƙofar ta faɗa gidan fa gudu. Hannunta na kan bakinta,kana ganinta kasan kuka take tarewa da hannun. Kai tsaye wani sashe ta nufah a gidan ba cikin gidan ta shiga ba. Domin gidan kana kallonsa da alama na haya ne amma na masu aji. Banke ƙofar tayi ta shiga farlon,ba kowa a ciki dan haka ɗaki ta shige. Wata matashiya ce mai matsaikacin a jiki a kwance akan gado fanka na seseta tata tana bacci. Gadon ta hau tareda ɗaga mata duka a hips ɗinta. Wata zabura mai baccin tayi tareda kallon Mulaifah cikeda mamakin ganinta da tsakar rana a gidanta. "Ke lafiya na ganki kaman an jefoki iyanzu,daga ina haka?" Maimakon ta bata amsar maganar ta saima kuka data kece dashi da danasani da kuma takaici. 'Magana nake miki Mulaifah amma kinyi shuru vakicemin komai ba" "Padush na shiga uku shikenan rayuwata ta ƙare nikam wayyo Allah nah" "Wai maiya farune?" Wata takarda da take hannunta ta jefawa padush ɗin,wacce take ɗauke da sunan asibiti. Da sauri hannunta har yana rawa ta buɗe takardar,zaro ido tayi da alama ta karanta abinda ya saka Mulaifah kuka. "Ciki..... Omg how,garin ya hakan ta faru mai kike tunani?" "Nima bansani ba besty,kuma fah ina amfani da magani yanda ya kamata" "Uhm na waye to a samarinki,nasan bazai wuce useey ba koh" Ɗaga kai tayi kawai ba tareda ta bata amsa ba. "Ya sani amma?" "Yasani dashi ma mukaje asibitin" "To kuma miyasa kuka dawo ba'a zubarba?" "Hmmm sunce wai zan iya rasa raina idan natakura saina zubar,saboda mahaifata batada ƙarfi,nayi amfani da magani sosai,ga kuma abortion danayi sau biyu,idan nasake wai zan iya samun bleeding mai tsanani. Duk da hakan ya takura akan sai an zubarmin shi bai shirya karbar dan shege ba yanzu,wai sunan iyayensa zai baci,musamman da yana neman minister. Nikuma sai naƙi a zubar ɗin,dan gaskiya ban shirya mutuwa yanzu ba. To akan hakane mukayi fada dashi ya tafi,yace kuma idan nasake nemansa sai ya batar da rayuwata. Padush ina cikin tsaka mai wuya,dan Allah ya kikega zanyi yanzu?" "Uhmm badan badan ba akwai wata shawara,cikin wata nawane" "Two month ne fah,munje yin gwaji ne na kowanne wata aka ganshi" Wani juya ido padush tayi tareda gyara zama, "Badama kince har yanzu baki haƙura da auren Ahmad ba?" "Eh ban haƙura ba amma yanzu kam kinsan bazai yiyu ba ai,tun bayan da aka ce shiba ɗan abba bane zance ya watse,bama ko magana dashi ma fah yanzu wata biyu kenan,shine ai na koma wajen usseey rage zafi,kinga abinda na jawowa kaina nan" "To mai zai hana ki maida cikin na Ahmad inyaso,i think kaman zayyi,kinga idan ya san cewa nasane to a gidan za'a saka dole sai ya aureki,shima kuma zai dunga kulawa dake tunda yana tunanin abinda ya aikata miki. Tunda kince cikin two month ne to definatly a wata bakwai nan gaba zaki haihu kenan... Sai mu kasheshi muce ɗan bakwaine batareda kowa ya ganshi ba,kinga ke kuma daga kin warware sai ayi muku aure" "Wow wannan labarin yayi daɗi,amma taya zai kasance,sanin kanki ne ko karen haukane ya ciji Ahmad to bazai nemi mace ta wannan hanyar ba" "Tsiyata dake gidadanci,to dama haka kawai zamu je masa,maganin tada ƙarfaffa sha'awa zamu saka masa,wanda ko shi robot ne to bazai iya riƙe kansa ba,saikin tabbatar yasha yafara aiki tukunna saiki je sashennnasa,daga nan ki ɗau wayarsa ki ƙira numberki. Idan komai ya wakana da safe saikiyi kukan ƙarya,kice masa ƙiranki yayi,to da kika zo bakisan mai yake faruwa ba kawai ya afka miki,gashi da ƙarfi ya farmakeki har kika kasa ƙwatar kanki......haka haka dai nasan dole zaice ki boye abin yazama sirri,daga nan sai ki nuna masa alamar kinada ciki,saiki kai maganar wajen su Abbah. A lokacin vashida zabi daya wuce ya aureki'" Tun kafin padush tagama bayanin Mulaifah ta rungumeta saboda tsananin murna,ganin lokaci guda tasamu mafita akan matsalarta. Daga haka suka cigaba da tsara yanda plan ɗin zai tafi musu a cikin nasara. Basu tashi ba saida suka ƙira wani doctor saurayin padush ɗin akan a ina zasu samu maganin amma mai ƙarfi sosai.
Sumaimah (POV)
A tsawon wannan watanni biyu da faruwar zancen auren Ahmad da Mulaifah mun samu ɗan kusanci kaɗan fiyeda na da nida Ahmad. Wanda kowa idan ya kalla yasan soyayyata ce tashiga zuciyarsa,kokuma nace zuciyarsa ta ganeni,ƙwaƙwalwarsace dai har yanzu bata ganeni ba. Ni abinma wani lokacin har dariya yake bani,idanna ga yana hade rai idan ya ganni da Saleem ,bama ya Sameer wanda shima ya dawo daga aikin daya rafi yi,shikamma har kalmar so ya furtamin, a amma lokacin nace masa yayi haƙuri ni matar auece,lokacin dana faɗamsa bai yarda ba saida na rantse masa tukunna.Tundaga lokacin muke mutunci dashi,amma shi Ahmad bai sani ba,gani yake kaman soyayya mukeyi,nikuwa ban taba faɗamasa gaskiya ba,shima ya ɗanɗana yaji yanda naji kokuma nace nake ji. Shima Sameer yanzu nice nake yimasa abinci a gidan, shikuma Saleem in yana nan a sashen Ahmad yake ci. Sameer ma abinda yasa baya zuwa don basa shiri da Ahmad ɗinne,har yanzu yana zarginsa a cewar shiya gani a wajen satar da akayi shekara biyu baya. A bangaren hajiyah maryam kuwa yanzu har raina nake ɗaukarta tamkar mahaifiya ta,yayinda itama take ji dani tamkar ƴar ta,amma yawanci mukanyi zancene a sashenta inna je yimata aiki,duk da ta hanani ma amma nice na nace akan zan dunga yimata. Yanxu ma a kitchen nake na dukka gidan ina yin abincin karyawa,Ahmad bayanan yaje Kaduna jiya,da yamma zai dawo. Dan haka shi yau bashi a abincin safen,iyah Sameer ne kawai da hajiyah maryam,wanda don ita ma na tashi dawurin saboda zata sha magani,jiya a gidan marayunta muka wuni an ƙara mata jini. Duk lokacin danaga tana wahala yanxu haushin hajiyah Mammah nakeji,don nasan itace ummul aba'isin na duk abinda yake faruwa a gidan. Jallof ɗin taliya nayi mai ruwa ruwa tasha sardine,a warmer na sakawa Sameer nasa,ita kuma a plate na zuba saina kife da wani. Saida na kai masa nasa kan dining table kafin na wuce sashen hajiyah maryam. Neelah bata nan tare suka tafi da Ahmad dan haka nice kaɗai mai kulada itah,tunda ni kaɗaice nasan abin dayake faruwa. Bata ɗakin,amma akan gadon akwai alamun bata daɗe da tashi ba,kenan tana banɗaki. Ajiye abincin nayi na yaye zanin gadon,ganin alamar jini jini daya bata gadon,wanda nake tunanin inaga daga jikin carnular ta yafito. Bayan na cire ina shimfiɗa wani tashigo ɗakin jikinta da ruwa,wanka kenan tayi. Gaisheta nayi tareda yimata ya jiki,ta amsa cikeda fara'ah,ta samu ƙarfin jikinta ba kaman jiya ba. A bakin gadon ta zauna na miƙo mata abincin,kana na buɗe drawerta na miƙomata magani. Bayan ta gama ɗan zance mukeyi wayar ta tayi ringing,Neelah ce taƙira taji ya jikinta. Sun fara magana kenan na dauke kwanon na basu waje. Dan yanzu babu wani zance labe na rigada nasan bazata taba cutar da Ahmad ba,kuma bugu da ƙari nariga da nasan wacce take aikata komaiɗin. Lokacin dana maida plate ɗin ummi harta fara wanke wanke,banyi koƙarin tayata ba dannasan batason hakan. Ina ajiyewa ma naga wayata tana ƙara. Yau wace rana nace a raina,yah Musbahu ne yake ƙirana. Sun fito daga wajen aikin kenan,kai mashaallah dan dama ƙiranmu na ƙarshe dashi tun kafin nazo gidanann,wai an turasu wani waje aikinsu na farko,kuma wajen ba service,harsu gama ba waya. "Yah Musbahu kaine dagske?" Dariya yayi kafin yace . "Nine mana mai kika gani?" "Wata huɗu fah kenan kona ce biyar" "Uhm Alhamdulillah mungama ai,jiya na dawo gida da daddare,naje gidanki akace wai bakyanan kin tafi aiki abuja.....Sumaimah meyasa,aikatau fah akace kinayi?" Shuru nayi na kasa bashi amsa,nasan dama dole sai yaji babu daɗi. Hawayene naji yana shirin zubomin nayi saurin maidashi. Inata garauniya na manta ashe inada wanda suka damu dani. "Lahh yah Musbahu karka damu ba wani aiki bane fa sosai,bawata matsala. Ina su ammi,kaje gidana kace yasu deeja da Sayyid da inna". "Duk suna nan ƙalau,banida lokaci gobe zan koma kaduna da nazo na ganki,amma karki damu bayan mungama da kaduna abuja za'a turamu headquarter indai an tabbatar da ƙwazonka,Inshaallah idan na dawo abuja zaki bar wani aikin aikatau" "Tom Sheeshah Allah ya kaimu yah Musbahu nagode" "Ameen ya Allah" Cikin sanyin jiki na sauƙe wayar,zai dawo abuja? Kuma zai hanani aiki,idan bangama abinda zanyi a gidan kafin sannan fah,hajiyah maryam bazata iyah cigaba da yi ita kaɗai ba,don wannan jinyar da take ma ƙoƙarin taimakon Ahmad tayi ta hanyar bashi wasu bayanai akan mahaifinsa. Saboda har yafara zargin kansa a matsayin ɗan wacce ta kashe masa mahaifi. Wannan abin na kana ganin gaskiya kayi shuru yafi komai sosawa hajiyah Maryam zuciya. Dan a ranar da hajiyah Mammah ta zauna tamkar matar arziƙi tana zayyano masa labarin ƙaryar hajiyah Maryam kuka tayi ta rabza a ɗaki,musamman da taga halin da Ahmad ɗin ya shiga,da saida yayi yunƙurin nemo dangin Amina,injishi dangin mahaifiyarsa. Da ƙyara aka shawo kansa ya haƙura,shiMa bawai dukka ba,yabarine saboda case ɗin dayake handling. "Ohh ya zanyi idan yah Musbahu yazo gidannan,komai fah zai iya wargajewa kenan." Sashenmu na nufah domin na kwanta,dan yau bazanje sashen Ahmad ɗin bama sai yamma idan yakusa dawowa.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...24...
Hankalinta kwance ta haɗa komai a hankali,don tasan tunda yace bada wuri ba,wataƙila ma sai wajen magriba su ganshi. Bayan ta gama komai jawowa sashen tayi amma bata kulle ba,tunda tasan babu mai shiga idan ba itaba kokuma wani inya gayyaceshi. Tafiya take tana ƴar waƙa,tamkar babu abinda ya dameta,tana shiga sashensu banɗaki ta faɗa domin ta ɗauraye jikinta,don tun ranar farkon da Ahmad ya kamata tayi wanka a banɗakinsa bata sakeyi ba,tanaso ya yarda da itah,idan zatayi nasara to sai ta haɗa da kiyaye irin waɗannan abubuwan.
∆∆∆∆ A bangaren Mulaifah kuwa tun safe aka kawomata maganin da zatayi aikin dashi,(sildenafil viagra). Tana tsugunne a garden taga shigewar Sumaimah ta dawo daga sashennasa, Hakanne yabata damar itama shigewa sashen. Bayan ta shiga kunkumi takama tareda yamutsa fuska jin yanda ƙamshin turare yakama falon sosai. Takawa tayi zuwa kan dining inda Sumaimah ta jera kayan abinci,saida ta buɗe tagani kafin ta fito da maganin. Gorar ruwa ta buɗe ta zuba overdose,yanda zayyi aiki yanda yakamata,kuma ta sanshi sarai idan bai gusar masa da hankali ba to zai iya riƙe kansa.. Murmushin mugunta tayi tareda rufe komai kaman bata tababa ta juya ta tafi. Tana fitowa daga falon ta ƙira padush tareda labarta mata. Lokacin har an fito daga sallahr magriba.
∆∆∆
Bayan Sumaimah tayi sallahr magriba bata tashiba saita fara karatun ƙur'ani har akayi sallahr isha ta tashi tayi,tana nan zaune akan daddumar taji wayarta tayi ƙara,sunan Ahmad tagani,ya dawo kenan ta faɗa a ranta. Ɗagawa tayi tareda yin sallama. "Ka dawone ya hanya?" "Lafiya ƙalau,shin kin rufe min drawer ne?" "Ehh na rufe" "Ina kika saka key ɗin,zan ɗauki wani document ne akwai abinda zan duba da darennan a ciki" "Waii ai na taho da key ɗin a jikin wanda ka vani na sashenka,amma ina wanda yake wajenka" "To na wajennawa ne yafaɗi ai banganshi ba,kuma ma yanzu zaki bani ki tafi,nasan daren yayi ai" Daga haka ya kashe wayar tasa,kallo Sumaimah tabi da wayar tareda tashi daga kan sallayar,wato ya ɗebo gajiyarsa yanason hucewa akan ta. Da hijabinta na sallah a jikinta ta ɗauki key ɗin ta nufi sashennasa. Ta baya tabi bata shiga ta cikin gidanba,duk da ba komai zatayi ba amma kada su zargi wani abun. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi shuru,har tagaji ta buɗe ta shiga,a wajen dining ta ganshi,a gorar ruwa a hannunsa,a ƙasa kuma ya zubarda juice ɗin da ya haɗa. Juyar da ido tayi tareda miƙa masa key ɗin,wani lokacin mamaki yake bata idan yana abu kamar yaro. Ɗauke jug ɗin tayi a ƙasan ta rufeshi,hanyar kitchen ta nufah zata ɗauko mopa,maganar sa ce ta tsayar da itah. "Mai zakiyi a kitchen yanxu?" "Wannan wajen zan gyara mana kafin gobe ya bushe,kuma da alama sai iya shiga ƙasan kujera" "Amma dare yayi ki gyara nan wajen kuma......" "Karka damu yanzu zan gama na tafi" Ɗaga mata kai yayi tareda shigewa ɗakinsa. Bayan ta ɗauko mopar hijabinta ta cire ta ajiye akan kujera. Tazo matsar da gorar ruwan dayasha sai taga abu ya taru a ƙasan robar,abinne ya bata Mamaki,mai ya kawo wani abu cikin gorar ruwa kuma. Ɗagawa tayi tana jujjuyawa,kaman an ce takai idonta ƙasa saita hango ƙwayar magani a ƙasan table ɗin,tsugunnawa tayi da sauri ta ɗauka tana jujjuyata,tabbas ɗazu ta gyara wajennan bataga komai ba. To kennan waye yashigo ya ajiyeta a wajen,da alama kuma irinta aka saka a cikin gorar ruwan,wani abin tashin hankalin wanda aka hara da koma mai nene yariga da yasha. Hannayenta ne suka fara rawa kana da dukka ilahirin jikinta. Saurin tashi tayi kaman an tsikareta tayi ɗakin Ahmad ɗin da gudu. A bakin gado ta ganshi ya kifah kai,hannunsa kuma yana kan cikinsa ta ƙasa,babu riga a jikinsa daga shi sai gajeren wando. Ga drawer ya buɗeta ga kuma kayansa a gefe.. Da gudu ta nufeshi tareda zama a gefensa. "Wayyo dan Allah kada ka mutu ka tashi muje asibiti,wayyo Allah mai kayi musu zasu kasheka" Riƙo hannunta yayi gam,hakan yasakata tsayawa da yin kukan ta kalleshi. Shima itan yake kallo,idanunsa sunyi jawur tamkar garwashin wuta. Magana yakeson yi,amma fatar bakinsa rawa takeyi,kana gani kasan yaƙi yakeyi da wani abu dayake son tasowa a cikin jikinsa. "Ki......kitafi.....ki rufe ƙofar kada ki kuskura ki dawo..." "Meyasa mai kake nufi,wanine yasaka maka abu a cikin ruwa Kasha,kuma da alama mai illah ne,inaga ma guba ce tunda tasaka maka ciwon ciki,dan Allah ka tashi muje asibiti" "Nace. ....kkkkitafii Sumaimah,meyasa bakyajin magana,Ko so kike na rasa tunanina na aikata miki abinda dukkanmu zamuyi danasani....." Shuru tatsaya tana kallonsa,dan har yanzu bata gano mai yake faruwa ba,saida ya daka mata tsawa kafin ta tashi ta fita tana share hawaye. Harta fita daga sashennasa sai kuma tagano alamar motsin mutum yana tahowa zuwa inda take. Gabanta ne yafara bugawa,don a zatonta ko hajiyah Mammah ce zatayi siddabarunta. Komawa tayi a hankali zuwa falon ta rufo ƙofah tana leƙowa ta glass ɗin ƙofar. Saida ta matso kusa kafin taga Mulaifah ce,tana tafiya tana waiwayawa tamkar munafuka. 'To ita kuma mai haɗinta danan wajen zatazo goman dare.' Shine tunanin da Sumaimah tayi wacce take kallonta ta glass ɗin ƙofah. Ganin sashen Ahmad ta nufo zata shiga,hakan yasa Sumaimah tayi saurin saka key wanda yake hannunta,saboda kada ta shigo ta ganta a ciki itama da daddaren,amma kuma Ahmad yana buƙatar taimako. Kai amma ba a wajen wannan ba. Murɗa ƙofar tayi ta jijjiga amma shuru,kaman zatayi kuka tayi,duk Sumaimah tana kallonta. Wayarta ta ɗauko ta danna ƙira,can bayan an ɗauka tace. "Padush ya rufe ƙofar bayan ma,tayi ta bugawa har mai gadi na yaci yaji,amma shi bai buɗe ba,kumafah bai daɗe da shiga ba,baici maganin ya fitar masa da hankalin sa ba zuwa yanzu,kuma hakanne ma zaisa ya buɗe da wuri ai.........ohh padush yazanyi ne,idan bai buɗe ba asirina zai tonu in aka gane inada ciki a gidannan..........najira menene,ni haƙurina ya ƙare,idan bai buɗe ba yakwana bayyi releasing ba maganinnnan zayyi masa illah,karnaje nayi silar hakan,kinsan ina sonsa..........wayyo nashiga uku,yanzu duk plan ɗin dana wuni ina haɗawa ya vaci,shiya sani yasan yadda zayyi,in wani abuma ya sameshi babu wanda zaisan nice" Bayan ta kashe wayar juyawa tayi kaman zatayi kuka,duk abinda take kuma take cewa Sumaimah tana kallonta. Wani ƙululun baƙin cikine da kuma na tashin hankali suka haɗu mata a cikin ƙirjinta. "Oh dama kece,kuma abinda kika saka masa kenan a cikin ruwansa,sai yanzu na kamo bakin zaren,wato so kike ya kwanta dake ba'a cikin hankalin sa ba,saboda ki laƙaba masa cikin da kika iyooo" Hannu Sumaimah tasaka a ha'barta tana jinjina lamarin.. Ta ɗan daɗe a wajen,saida ta tabbatar Mulaifah ta tafi tukunna kafin itama ta murɗa zata fita. Har ta saka ƙafarta a waje saikuma maganar Mulaifah ta dawo cikin kunnenta. Cewar in ya kwana batareda mace ba ya samu matsala shiya sani. Maida ƙofar tayi ta rufe bayan ta dawo cikin falon. Safah da marwa tafara tana tunanin abinyi,itadai in tace zata samo makarin maganin dayasha a daren to tayi ƙarya,sannan shin wa zata nema yabata shawara akan ya zatayi. Wayarta ta ɗata ta danna ƙorna Neelah. Can kaman ringing biyu ta ɗaga,muryar tarau take da alama batayi bacci ba. "Hello anty Neelah kina jina?" "Ehh ina jinki,yadai jikin mommy ne ya tashi?" "Ahah daman............" Kaff ta zayyane mata abinda yake faruwa,ajiyar zuciya tasake bayan ta gama jin abinda yake faruwa. "Kai amma wannan yarinya akwai shegiya,wai su bazasu barshi ya huta bane? Kinsan miye,yanda ta faɗa gaskiya ne zai iya yimasa illah,tunda tace overdose tabashi,sannan ni bana nan ina kaduna bare na samo masa maganin dazai karya wanda ya sha. Abinda za'ayi tunda ke matarsa ce dole kene zakiyi masa magani,kuma dama hakan haƙƙinki ne......saidai kiyi haƙuri zakiji jiki sosai tunda baya hayyacinsa....." "Bakomai dama nayi tunanin hakan,na tambayi shawararki ne kar hakan yazama kuskure,musamman da rayuwarsa ke cikin hatsari" "Shikenan kiyi haƙuri kikuma jure,komai zaizo da sauƙi Inshaallah" Kashe wayar Sumaimah tayi tareda kasheta,hanyar ɗakinnasa ta nufah cikin sanyin jiki. A hankali ta murɗa ƙofar ɗakin,yana nan a inda ta barshi,saidai yanzu daga inda take tana hango yanda jikinsa yake rawa. Ƙarar maida ƙofar da tayine yasakashi ɗagowa ya kalleta,zuwa yanxu kam ya sanja kamanni. Takawa take a hankali tana nufar inda yake,yayinda shikuma yake binta da wani mayen kallo mai cikeda fassara,gabanta dukan tara tara yake har ta zauna a bakin gadon. Hannunta ta ɗaga zuwa kannasa hannun,wanda jijiyarsa suka fito raɗa raɗa,tausayinsa ne ya tsirga mata har cikin ranta,wanda hakan yasakata fashewa da kuka. "Kayi haƙuri ka yafemin,nasan hukuncina bazayyi maka daɗi a gobe ba,amma kayi haƙuri dan Allah" Tana gama faɗin hakan takai bakinta saitin nasa,kaman dama riƙewa yake,amma yanzun ƙarfinsa ya gaza control ɗin ƙishirwar da take cikin ransa,hakan yasaka mai makon yaji haƙurin da take bashi,saima sumbatarta daya farayi a zafafe. Kuka take tana cize baki jin yanda yake yamutsata,tun tana jin da ɗan ƙarfi a cikin jikinta harta daina ji. Ta daɗe tana ɗanɗanar azabar,har saida maganin yasakeshi jikinsa ya sake laraff baccci ya ɗaukeshi,kafin itama tasamu damar runtsawa.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...25...