Sanadin caca book 2 complete - Chapter 15
Sanadin caca book 2 complete Chapter 15: Sanadin caca book 2 complete Chapter 15. Yaji dai kaman ya tasa kai da wani abu mai tudu,amma bayyi masa kamada…
3,374 words
Yaji dai kaman ya tasa kai da wani abu mai tudu,amma bayyi masa kamada pillow ba,buɗe idonsa yake a hankali saboda nauyin da yayi masa kafin ya sauƙe akan cikin Sumaimah. Ɗaga kansa yayi sai a sannan yaga ashe kan ƙirjinta yasaka kansa,mai ya kawota ɗakinsa kuma kan gadonsa,sannan ba sutura a jikinsu. Abinda yafaru jiyane Yafara kwaranyowa cikin ƙwaƙwalwarsa. Saurin zabura yayi ya tashi zaune tareda ƙarewa yanayinnasu kallo,jini ya gani a bargon da wajen ƙasanta,wanda yasan ba shakka daga cikinta yake fitowa,saboda tsabar ƙarfin dayayi mata a jiyan.. Hannunsa dukka biyun wanda suke rawa yasaka a kansa ya dafe,domin ji yake kaman zai cire saboda tension ɗin dayake ciki,wani ihu ya fashe dashi na dana sani da kuma nadama. Hakanne ya farkar da Sumaimah daga baccin da tayi a jiyan,wanda za'a iya ƙiranshi da ƙanin suma. Iduwanta fulu fulu sukayi,badan fatar bakinta ta ƙasa inda ta cijeta tayi jawur. Yunƙurawa tayi a hankali ta tashi zaune tana cicccize baki saboda tsamin da jikinta yake yimata. Kallo tabi Ahmad dashi,wanda shiɗinma ita yake kallo tamkar gunki. Zanin dayake gefenta ta jawo ta saka akan ƙirjinta,kana ta kama gashinta daya bake akan fuskarta ta ɗaure. "Meyasa......meyasa......meyasa kika aikata haka,kinsan kuwa girma da kuma munin abinda kika sanya na........." "Kana lafiyah,maganin yabar jikinka bazai cutar dakai ba?" Shine abinda Sumaimah ta faɗa cikin dashashiyar murya. "Naji Mulaifah tana cewa zai jawo maka babbar matsala idan ta zauna dashi a haka" "Shine dalilin daya saka kika bada kanki,abinda yafi komai muhimmanci a wajenki,sannan kika saka na aikata abinda harna mutu bazan manta ba? Meyasa zakiyimin haka,bayan nace miki ki tafi mai ya dawo dake toh? Akan matsalata ki kalli abinda na aikata miki,yanzu ya zanyi kenan" Maganar cikin nadama yake ambatarta kamar zayyi kuka. Ɗan murmushin ƙarfin hali Sumaimah tayi kafin tace. "Karka damu nidama ba budurwa bace bare kace na rasa budurcina,Sannan nayi niyyar tafiya kaman yanda kace,......." "Wannan shine abinda yakamata muyi magana akai a yanzu?" Daga haka ya tashi ya shiga banɗaki. Binsa Sumaimah tabi da kallo tareda runtse ido. Shin wai yaushe zatayi tarayya da mijinta cikin salama ne,dan wannan ko kusa bazata ƙirata da kwanciya ba sam. Ƙoƙarin tashi take amma abu ya gagara,ko ranar farkonta bataji wannan azabar ba,gaskiya bazata taba yafewa Mulaifah ba. Jingina tayi da kunnen gadon,ganin duk yanda tayi bazata iya tashi daga kan gadon ba. Jin motsin takunsa ne yasakata buɗe idanuwanta,jallabiya ce a jikinsa ruwan toka,sai ruwa daya ke fitowa daga sumar kansa,alamar ya tsabtace jikinsa. Daren farkonsu ne ya faɗo mata a ranta,yanda tayi fama dashi kafin ya tashi yayi wanka. Duk da halin datake ciki hakan bai hanata yin murmushi ba,idan tace batayi kewar goje bama tayi ƙarya. Ciɗak taji ya cirata sama tareda yin hanyar banɗaki,da kallon mamaki tabishi kana dabi jikinta ma da kallon,zanin ya cire cinyoyinta duk bushashshen jini. Runtse idonta tayi wannan kunya har ina. Da sauri ta buɗesu jinta a cikin ruwan zafi,saida tasaki ƙara jin yanda ya shigeta. "Ki zauna a ciki zafinsa inya ratsaki zakiji ƙarfin jikinki ki iya gyara kanki. " Daga haka yabar banɗakin,ajiyar zuciya ta saki tareda sake jikinta a cikin bahon wankan,tasan yanzu yafijin haushinta ma fiyeda wacce tayi silar shigarsa cikin wannan yanayin. Ta daɗe a ruwan,bayan yayi sanyi ma tasake saka wani ruwan zafin. Saida taji jikinta ya ɗan dawo daidai kafin tayi wankan tsarki ta fito. Towel ɗinsa ta ɗauka tayi amfani dashi,lokacin data fito baby duvet ɗin ya cireshi,ko ina ya kaishi oho. Hijabinta ta ɗauka tayi sallahr asuba,dan rana harta fara fitowa a lokacin. Addu'o'i ta dungayi daga zaunen,ta daɗe kafin ta tashi ta naɗe sallayar. Falon ta fito domin hada abinda zataci. Idonta ne yakai kan dinning inada aka ajiye leda,tasan Ahmad ne ya ajiye,tunda jiya babu ita a wajen. Sannan abincin datayi masa jiyan shima yana wajen. Ƙarisawa tayi wajen ta buɗe ledar,magani ne na relief pain a ciki. Tea ta haɗa tasha kana ta sha maganin. Daga nan ta tafi sashensu,dan ma Allah ya taimaketa safiya ce ba mutane sosai,su inna ladiyo kuwa batada matsala dasu ,dan yi zatayi kaman ta dawo daga sashen hajiya maryam,tunda ko badan haka ba wani lokacin takan kwana a wajenta. Bayan ta kwanta akan katifar tata abubuwa ne da dama suka fara yawo a cikin kanta,shin da wannne ido kenan yanzu Ahmad zai dunga kallonta.....runtse ido tayi ko bacci zai ɗauketa.
A bangaren hajiyah maryam da taga rana tayi sosai Sumaimah bata zo ba sai hakan ya tabbatar mata da zancen da Neelah ta ƙira ta faɗamata. Safa da marwa take a ɗakinnata tarasa abinyi,so take taje taga mai yake faruwa,dan indai yana cikin magani zai iya yi mata illah sosai. "Kai wannan mutane wannan mutane,wato so take ta laƙaba masa cikin shegen da tayi?. Allah sarki koyah Sumaimah take,nasan tunda banganta ba yanzu to tasha wahala a wajensa" Waya ta ɗauka taƙira Sumaimah ɗin,saida tayi ƙira kusan sau uku kafin ta daga cikin magagin bacci. "Hello Sumaimah kina jina,kina ina ne,sashensa ko kuma naku?" "Uhmm ina ɗakinmu" "Dan Allah ko zaki daurewa kizo,idan nace zanzo wajenki hakan zai zama abin magana,ya jikinnaki?" Saida tayi jimma kafin ta amsa,wanda hajiyah maryam ɗin rasan kunya taji da kuma mamakin ya akayi ta sani,amma wannan bashine a gabanta ba dan haka ta basar. "Ehh.....zan iya zuwa,bacci ne ma ya ɗaukeni" Bayan ta kashe wayar bayan gida ta shiga,da alama wasu dabaru zata haɗawa Sumaiman saboda jikinta. Lokacin datazo ta ƙyar ta haɗa ido da hajiyah maryam,ita a dole kunyar ta takeji,ita dai bata ce mata komai ba,har ta gama wankan ta fito. Wunin ranar Sumaimah a sashen hajiyah maryam ta wuni,duk wani abu ita tayimata,tun tana noƙewa har ta saki jikinta,musamman dataga hajiyah maryam din batayi mata labarin abinda ya farun ba. A bangaren Sumaimah kuwa da tunanin Ahmad ta wuni,shin yana ina,ko ya zasu cigaba oho,shin zai sake yarda ta shiga sashensa ma kuwa? Tasan yanacan yana ɗorawa kansa laifin abinda ya aikata mata.
Washagari jikin Sumaimah ya ware,dan harta koma ayyukanta na yau da kullum,sannan kaf gidan babu wanda yasan mai ya faru sai hajiyah Maryam da kuma uban gayyar.. Bayan ta tashi saida ta gama da sashen hajiyah Maryam kafin ta wuce sashensa,har dare dai yayi bata ganshi ba,shin ya dawo ma oho. Ba kaman ko yaushe ba yauɗin da ɗar ɗar na zuciya ta buɗe sashen,yana nan kaman yanda ta fita ta barshi jiya. Abinda ya farune ya dawo mata cikin kai,amma tayi saurin maidashi ta ɗauko mopa. Tana cikin goge goge Ahmad ya fito daga ɗakinsa,yana sanye da dogon wando da kuma vest,turus yayi dan bayyi zaton zata dawo aiiki ba,haka itama batasan yana nan ba. Bakinta yana rawa haka cikin dauriya ta gaisheshi,jin bai amsa ba ya tsaya ƙyam kaman gunki yasakata ɗago idonta,haɗa ido sukayi dama ashe ita yake kallo. "Mai ya dawo dake sashennan,yanzu duk abinda yafaru dake baki ɗaukeshi a ishara ba kika sake dawowa inda nake,mai yasa bazaki tsaneni ba kuma ki zageni akan abinda nayi miki,saima dawowa dakikayi cigaba dayimin aiki....mai kike nema haka a wajena?,bakya tsoron abinda ya faru ya sake faruwa?" Ƙaremasa kallo tayi jin yadda yake sambatu cikin karayar zuciya. Idanuwansa sun faɗa gefen idonsa yayi baƙi,ga bakinsa ya bushe yayi fayau yini ɗaya kaman majinyaci,ko ita batayi haka ba bare shi. Ajiye mopar hannunta tayi ta matso kusada shi tana cigaba da kallonsa. "Karka cemin blaming kanka ka dungayi tsawon wannan lokacin,bakaci abinci ba kuma bakayi bacci ba......shin sau nawa zan ce maka ba laifinka bane,Mulaifah ce ta zuba maka magani saboda ta cimma wani ƙudirinta akan ka,bai kamata ka.........." "Idan ita tayimin haka tsakanina da ita ne,kikuma da kika shiga tsakani miye ma'anar hakan kenan" "Ohhh kafi son na barta ku aikata sabo da ita kenan,alhali inada damar magance hakan,Sannan kuma ta laƙaba maka ɗan da ba naka ba,ko kuma na barka hakan ya cutar dakai?" "Kema da kika tunkareni muka aikata hakan miye maravarsa da natan kenan,Sannan nifah nace miki ki tafi amma kika dawo" "Duk naji sannan na yarda ka saka laifin dukka akaina,amma ka daina yiwa kanka wannan hukuncin. Nina ɗauka laifina ne,amma kai ba naka bane tunda baka cikin hankalin ka. Zancennan ya wuce sannan ya tsaya iya nan,zan ɗau komai akaina" Taƙarisa maganar tana nuna kanta,hawayen dayake idonta ta share tana binsa da kallon tausayin halin da suka tsinci kansu,da kuma tsantsar kulawa. Shi har yarasama mai zaice da itah,saidai bi da ido. Haka yana nan a falon ta gama gyara ko ina ta gama abinci ta kawo masa. Duk abinda take tanajin idonsa a kanta,komai yake saƙawa a ransa oho. Bayan ta kawo masa abincin har sannann bai dawo hayyacinsa ba,shurunne yayi yawa hakan yasa Sumaimah yin tafi a daidai fuskarsa,ganin taje ta dawo amma har yanzu bai motsaba. "Mai yafaru haka?" "Sumaimah ina son na aureki idan zaki yarda" Maganar ta daketa sosai,sannan ta bata mamaki a lokaci guda. "Aure kuma? Shin saboda abinda ya faru a tsakaninmu ne yasa kake wannan tunanin?" "Eh dashi ɗin ma,amma kuma daman ina son hakan a raina" "Kayi haƙuri bazai yiyu ka aureni ba a yanzu" "Meyasa nasan abinda kikemin soyyaya za'a ƙirashi, wanda saboda hakanne nima na fara sonki a cikin raina" "Ba iya soyayyar bace kaɗai zata wanzar da aure,saida sharaɗi tukunna,sannan cewa nace maka bazayyi yuba,ba wai bazan amince ba." "Meyasa bazai yiyu ba toh,nariga na keta miki mutuncinki,zuciyata bazata juri ganin abinda namiki ya tafi haka ba,dan haka ki amincemin aurenki ta hakanne zanji na rage wani abun" "Kona amince maka baya halatta nayi aure guda biyu" "Aure biyu,mai kike nufi da hakan?" "Inada aure,harda yaro a garinmu" "Whattttttt!!!!!!!!!!!!" Shine abinda Ahmad ya faɗa tareda miƙewa kaman an tsikareshi..... "Am dama........" Tun kafin Sumaimah tace wani abun ya toshe kunnensa. "Shut up,don't say anything,banason jin komai daga bakinki,sannan kuma ki fita daga sashennan,banason ko ido nasake haɗawa dake daga yau" Taƙarfi ya faɗi hakan har saida ta razana,tashi tayi da sauri ta bar sashen tana hawaye,shikenan komai data dade tana yi ya wargaje a yau ɗin.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...26...
A bangaren Ahmad kuwa da Sumaimah tafita,jiyayi gabaɗaya duniyar tayi masa zafi,kenan daman duk tsawon wannan lokacin matar aure yakeso,wani abu mafi munin ma wai har ya kwanta da itah,wannan lamari har ina. A daddafe ya shirya cikin kayan aiki ya bar gidan,abincin data haɗamasa ko kallonsa bayyi ba. Bayan yaje office ɗin ma shuru yayi tareda dafe kai,yarasa ma mai yake masa daɗi. Eemran ne ya shigo hannunsa ɗauke da file. Bayan yayi masa gaisuwar sojoji ne ya ajiye masa file ɗin a gabansa. "Ranka ya daɗe mun samu maboyar inda shigaban ƙungiyar yake,yana garin DABAGAYI ne amma can cikin jeji,mun samu hakanne bayan........." Bai gama bayanin ba Ahmad ya karbi file ɗin ya fara dubawa,haba no wonder shiyasa suka rasasu,suna can inda ba'a tsammani. "Eemran ku shirya private jet a yau zamuje wajen,i need to end this case da sauri,nasan koma menene yanada alaƙa da wani nawa,kuma da rayuwar danayi a baya,nagaji da zama cikin wannan duhun,i need to know everything" Yana gama faɗin hakan suka bar office ɗin zuwa headquater su.
Wajen yamma rana ta kusan faɗuwa suka shiga cikin jejin,a bakin wajen suka tsaya,basuda wani yawa don basu wuce su goma ba,saboda binciken na sirri ne,ko mahaifinsa baisan sun tafi ba. Saidai sun ɗebi makamai masu hatsarin gaske. Jejin Ahmad yake ƙarewa kallo,haka kawai ya tsinci kansa dajin kaman yasan wajen. I donsa ya rufe yaja wata iska mai nauyi,haka ido a rufen yafara tafiya a cikin jejin. Sudai sauran sojojin binsa suke a baya har suka iso bakin wani ɗutse,babu kowa a wajen,amma kuma suna jiyo motsin wasu na tahowa ta bayan dutsen. Hakanne yasa Ahmad yayiwa tawagarsa alamar suyi baya cikin duhuwar jejin su shirya kai farmaki. Yana nan tsaye ya saita duk wanda ya zo ya harbeshi,wasu mazajene manyan manya guda huɗu,kana ganinsu kaga shu'umai suka bayyana,suma tasu bingidar tana ɗane,domin da alama kaman yanda su Ahmad suka ji motsinsu suma sun ji nasu motsin. Na gabanne yafara sauƙe bindigar tareda yiwa na bayan magana. "Kai ku sauƙe ogah gojene fah ya dawo" Jin sunan yasakasu sauƙe bindigoginsu tareda matsowa,gaisuwa suka miƙa masa tareda cewa. "Ogah ya dai sai yanzu ka dawo,ai har anyi taro ganin shuru shuru baku dawo ba yasa akayi tunanin duk cikinku babu wanda ya rayu, Don 2 a ranar na naɗa sabon Don3 amma mu bayyi mana ba,dama muna fatan dawowarka" Duk maganar da suke Ahmad binsu kawai yake da kallo,sai a sannan maganar wancan barawon da suka kama ta dawo masa,da kuma maganar Sameer shida Abbansu. Kenan dai a rayuwar da yayi baisani ba a wajensu yayi aiki,Allah yasa ma ba kayan sojojine a jikinsa ba da sun ganeshi. Ɗaya daga cikinsu ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi,ta hanyar jan hannunsa zuwa cikin sansaninnasu. Suna tafe yana binsu a baya batareda yace komai ba har suka isa Wani ɗaki. Shiga sukayi ya bisu,ba ɗakin kwana bane,domin hadda kujera da table a ciki. Don 3 yaji sunce a gaisuwar da sukayiwa wanda yake kan kujerar,shima ƙatone amma bakaman su ba,saidai ya fisu murɗewar jiki. "To ogah mai guri yazo mai tabarma sai ya naɗe,ogah goje ya dawo,dama matsayinsa ne a ka baka" Daga yanda suke maganar ya tabbatar kam ba sonsa suke ba a shugabannasu. "Wanne zancen banza kukeyi haka,kunyi farautar da aka saka kune,nida idona naga goje an soka masa wuƙa,dan haka bai tsira da ransa ba" Matsawa sukayi daga gaban yayi arba da goje,wanda yake sanye da baƙaƙen kaya da bindiga a hannunsa. Firgit ya tashi yana rarraba ido,ashe da gaske sukeyi dai. Ganin yafara kame kame ne yasa Ahmad ƙarisawa gabnasa tareda yin murmushi. "Lahh ogah kada ka damu fah,ni yanzu ma inada wasu yaran mun kafa tamu ƙungiyar,saboda lokacin da abin yafaru na bugu,na manta komai na rayuwata,iya kawai sunan ƙungiyar ne yazo kaina da kuma inda take shiyasa nazo" Wani washe baki yayi tareda cewa. "Ahh toh abu yayi ƙyau sosai,nayi zaton ai kazo ƙarbar matsayinka ne" "Ahah bashi nazoyi ba,nazone dai wajen Don 2,saboda na tuna zamu haɗu dashi idan muka dawo a raye,sannan kuma nazo nuna masa mutanen dana haɗa,sun ƙware sosai a wajen iya aiki,bansani ba ko zasu samu karbuwa suma a........." "Ahah mai zai hana,dama munyi rashin mutane sosai a harin da muka kai waccar shekarar,tunda kai ka kawosu to munsan babu matsala. Kai me kuke jira,ku basu masauki mana shida mutanensa" Yafaɗa yana bawa wanda suka rako Ahmad ɗin umarni. "Goje in bazaka damu ba za'a baku masauƙi ku zauna kafin na aikawa da shugaba saƙon cewar kazo" "To shikenan bakomai,ni barina je nayima mutanennawa magana" Bayan ya koma wajen daya bar su Eemran bayani yayi musu akan plan ɗin ya sauya,zasu saje da barayinne su san komai nasu kafin su kai farmaki. Hakan kuwa akayi,dan har kaya suka sanja irin nasu,saidai ba kaman yanda sukayi tunani ba,zasu kai kusan kwana uku kafin wanda suke jira yazo.
Sumaimah (POV)
Bayan Ahmad ya koreni daga sashensa na daɗe a lambu ina tunani,ina ganin fitowarsa ya ɗau mota ya bar gidan. Tunda yanzu aikin sashensa ya ƙare,lokacine daya kamata dama na farka daga yi masa abu batareda yasan koni wacece ba,yanzu zan fara aikin da hajiyah Maryam tasakani a sashen hajiyah Mammah. Domin itace sanadin dukkan waɗannan abubuwan,da badan itaba da yanzu na faɗamasa cewar nice matarsa,wani lokacin saina kusan subutar baki sai na tuna da rayuwar ɗana,idan tagano shima tarwatsa rayuwarsa zatayi kaman ta mahaifinsa. Gyara fuskata nayi na nufi sashen hajiyah Mammah. Tana zaune akan dadduma a tsakiyar falonta,jikinta lullube da babban mayafi kamar kullum. Sallama nayi da amsa a nutse,tsugunnawa nayi tareda karkatar dakai. "Hajiya barka da hantsi ya jiki jikin?" "Lafiya kalau ƴar nan ya haƙuri da rayuwa" Hawaye na ƙaƙalo yafara zubomin,wanda bakomai na tuna na zubar dashi ba sai korar da Ahmad yayimin ɗazu. "Hajiyah ki taimakeni kaman yanda Allah ya taimakeki, Yallabai nake yiwa aiki,babu abinda banayi masa,yau da safennan ya koreni wai kada nasake nuna masa fuskata,na tambayeshi mai ya faru yacemin wai kawai ya gaji danine. Gashi inada ɗa da kanwa da innata a ƙauyenmu wanda nake tallafawa,miji kuma ya tafi nema har yanzu shuru bai dawo ba" Kuka nake kaman raina zao fice,inaji tana cemin nayi shuru amma banyi niyyar tsayawa haka ba,saina amayar duk abinda na ƙunsa kwanannan. Saida naji zuciyata tayi sakayau kafin tanafara rage kukan ina jan majina. Mai akinta Kaltum ta ƙwalawa ƙira,sai gata kuwa tafito daga wani ɗaki. "Zo kalutume ga wannan yarinyar daga yanzu zata dunga tayaki aiki anan sashen na ɗauketa aiki" "To shikenan hajiyah za'ayi yadda kika ce" "Karki damu ki dunga aikin anan sashen,saidai idan zakiyi min aiki banda gulmace gulmace,sannan banda rawar kai,duk da naga bakiyi kamada mai hakan ba dama, ki kwantar da hankalin ki zan biyaki,yanda zaki kulada ƴan uwanki,Allah yaƙara rufamana asiri" "Ameen ameen hajiya,nagode nagode sosai,kaman yanda kika taimakeni kema Allah yayi miki hakan" Nadaɗe ina kwararo mata Addu'a godiya,ina cikin hakanne kaltum tasake shigowa tareda raɗawa hajiyah Mammah wani abu a kunne. Ɗan zaro ido tayi tareda sauya yanayin fuskarta. "Kin bata maganin amma taƙi sha,mai take nufi kenan,dashi zata zauna har a sani? Kice mata ta sameni a ɗakina yanzunnan" Daga haka ta sallameni suka shiga ciki. Ko basu fadaba nasan zancene akan cikin Mulaifah,nasan dai bazata taba faɗamusu ba,in kuwa suka gane kenan ya wuce wata biyu. Ina nan zaune a wajen ina nazari naga Mulaifah tafito daga ɗakinta zata shiga na gaji Mammah ɗin,harara ta bankamin,tayi wata rama ga fari data ƙara kamar wata fatalwa. Murmushin mugunta nayi kafin na fito daga sashen,hmmmm danma bata san nina lalata mata shirinta ba kenan.
Ban nufi sashen hajiyah Maryam ba saina nufi namu,yanzu dole na rage shiga wajen hajiyah Maryam ɗin,idan har inaso nasha lafiya.
∆∆∆
Su Ahmad har sunyi kwana uku a cikin sansanin barayi,yauɗinne kuma suke saka ran zuwan shugaban kungiyar na biyu wato Don 2. Abubuwa da dama da suke shirin yi da kuma wanda sukayi babu wanda basu sanar da Ahmad ba,hakan ba ƙaramin dadi yayi masa ba,ganin ya samu dukkan labaran dayake buƙata cikin sauƙi. Abu ɗayane dai har yanzu bai sani ba shine sanin shugaban ƙungiyar na ɗaya da kuma na biyu. Wannan kaf cikinsu babu wanda ya sani. Dare ya fara,kowannne lokaci Za'a iya ƙiran Ahmad su gana da Don 2,a zaune yake shida su Eemran suna plan yanda komai zai kasance. "Ka gane Eemran ku tabbatar kun saitasu dukka bindiga,sanann gurnet dayake kakkafe yazama cikin ready,so nake mu tashi wajennan a yau bayan munkama shugaban,kada kowa ya tsira da ransa a cikinsu. "Angama shugaba" Suna gamawa aka zo ƙiransa ya fita. Wani ɗaki aka bi dashi,wanda tsawon kwanansu uku na gidan basu taba shigaba. Yanada matsakaicin girma kuma yasha ado kamar ba'a cikin kogon dutse ba. Wani mutum ne a zaune yasha suit baƙaƙe,ɗan dattijo ne domin yafara manyanta,magana yake a waya lokacin da suka shigo,sannan fuskarsa da wata baƙar mask tana sheqi. Bayan ajiye wayar cire mask ɗin yayi tareda juyowa cikin taqama. "Barka da dawowa jaki na mijin gaske goje,naji daɗin cewar kana raye,domin ko babu komai nasan jakar da muke nema tana hannun ka,sannan........." Caff ya tsaya da bayanin ganin wanda yake tsaye a gabansa.. Yana zare ido. Shima Ahmad ɗin a bangarensa tun lokacin daya juyo ɗin kafeshi da ido baya ko motsawa saboda razanar ganinsa a wajen. "Gen. Buhari Bello wanda suke cewa Uncle BB,Aminin mahaifinsu ne tun suna ƙanana,suma tare suka tashi suka gansu. Komai da AM Aliyu zayyi sai yayi shawara dashi,amma.......what yana ɗaya daga cikin wakilan ƙungiyar datake maƙiyarsu a barikin sojoji?? "General mai kake anan badai kaine goje ba??" Kafin yagama tantancewa Ahmad ya saitashi da bingida,yayinda ya danna wata makunna a hannunsa,aikuwa wajen ya kaure da ƙarar bindigu da tashin gurneti.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.