Sanadin caca book 2 complete - Chapter 16
Sanadin caca book 2 complete Chapter 16: Sanadin caca book 2 complete Chapter 16. *BOOK 2* ...27...
2,962 words
*BOOK 2* ...27...
Duka da naushi Ahmad yake kaiwa Gen Buhari Bello,shima ramawa yakeyi kasancewarsa tsohon soja,ga Don 3 ya buge bindigarsa tun ɗazu. Ganin faɗan ya ɗauke musu hankaline yasa don 3 ɗauke wayar Gen BB ya fita. Sun daɗe suna faɗan kafin Ahmad yasamu nasara akansa,ta hanyar ɗaukar bindigar tasa,saita shi yayi da ita yana haki. "Miye alaƙarka da wannann kungiyar,dama tsawon lokacin nan amanar sojoji kake ci,irinkune kesa a dunga yiwa jami'an tsaron ganin marasa gaskiya koh.......(kwafɗama sa ƙasan bindiga yayi saida ya faɗi)........kaine don 2 to wanene shugaban ƙungiyar,inaso ka faɗamin yanzunnan kokuma na jajjage kanka da bindigar nan" Cikin ƙaraji da tashin hankali yake maganar. Wata dariyar baka isa ba gen BB yayi wa Ahmad,cikin sauri yasaka ƙaramar wuƙa ya yanke wuyansa da itah,yana kakarin mutuwa Ahmad ya jefar da bindigarsa ya ƙarisa wajensa da sauri. Tallafoshi yayi a razane,ga jini yanata zuba a wuyansa,abin har yakai ya kashe kansa akan yafaɗa masa wanene shugaban ƙungiyar nan? "Yaaa....rrro kenan,mai amfanin na faɗamaka tunda nasan dama mutuwa zanyi idan ta gano kasanni........bazaka taba sanin wacece itttt.......ba" "Dama macece ka faɗamin, wacece w......" Shuru yayi tareda sakinsa ya koma gefe,ganin ya riga ya mutu,abin yayi matuƙar razana shi sosai. Wayarsa ce tayi ƙara,hannunsa yana rawa ya ɗauka ganin Eemran ne. "Hello sir mungama dasu,saidai wannan shugabannasu mun sameshi yana waya da wani" "What definitely shugabarsu yake faɗawa mai ya faru" "Eh nima nayi tunanin haka,na harbeshi a kafaɗarsa da dama" "Ohh yakamata mu tafi,abin bai tafi yanda ake so ba,amma dai Alhamdulillah hakan ma mukeda nasara"
∆∆∆
"Ina jinka ka faɗamin mai yake faruwa a wajen Gen?" "Hajiya an samu matsalane ba Ogah bane,Goje ashe sojane yayi mana baɗɗa kama,yanzu haka ya gane ogah kuma ya kamashi,na samu wayarsa ne na ƙiraki" "Wayeshi ka faɗamin" "Gen ........" Kafin yaƙarisa aka katse ƙiran,kuma da alama harbeshi akayi don taji ƙarar bindiga. "Waye ka faɗamin wayeeeeee......" Ƙara ta saka tareda yin wurgi da wayar, kaltum ce ta tsugunna ta ɗauke wayar jikinta yana rawa. Kallon fuskar hajiyah Mammah nakeyi,idan ka ganta zakace bazata wuce shekara talatin ba a duniya,babu wannan sunkuyawar da yamutsewar fuskar. Mamaki abun ya bani,mai ta shafa haka ta sanja lokaci guda. Masifa tacigaba dayi tana zuwa tana dawowa,ganin abin bazai mata ba ta jawo wani akwati a ƙarƙashin gadonta,ja ne yana glowing,kana gani kasan abun tsafi ne. Hannunta ta saka ya buɗe,wani aljana ce ta bayyana a gabanta da baƙaƙen kaya,kamarsu ɗaya da itah,amma kana gani kasan ita ba mutum bace,to wacece kenan. Jikina rawa ya fara daga inda nake labe da jikin ƙofa ina leƙawa,dan karfin hali bana tsoron ma ta ganni. "Ruhina inaso kayimin bayani shin mai kasani gameda abinda yake faruwa,ƙungiyar dana kafah wadda da ita nake control na manyan ƙasar nan ta rushe,mai yasa abubuwana suke rushewa" Muryarta da bibbiyu take fita kamar wata na'urah. "Hakan dama dole zai faru,tunda dodo ya baki kashedi akai,matar da kike gudun kada ta bayyana harta haifi magajin wannan matakin tariga ta bayyana,kuma itace sanadiyyar karyewar alƙalaminki,indai ba kasheta kikayi ba to bazaki ƙara nasara ba" "Kaman ya yarinya,ni banga kowa a tareda shi ba,Mulaifah ce itama kuma yanzu sun rabu" "Hhhhhhhh duk da a zahiri kina kulada yarintarki amma hakan baya aiki a hankalin ki,shiya riga ya tsufah" "Ruhuuuuuu karki ƙara magana akan tsufah na,bazan tsufah ba bazan taba tsufah ba,wannan fatar tsufan ina nuna ta ne kawai da iyalaina,suma in suka isheni dukka zan gama dasu nayi rayuwar ƴan ci na" "To inba haka ba mai yasa kika kasa gane cewar Ahmad yayi rayuwa ba'a gabanki ba na tsawon shekara shida,bai kawomiki anan ya gamuda itah ba,sannan kuma yayi rayuwa a cikin ƙungiyar da kike karewa. Sannan ya bar mata da kuma ɗa a rayuwarsa ta baya.......munkasa gane hakanne a da dayake ta Addu'a a lokacin,yanzu dayake kan aikin ruguza ƙungiyarki bayayi sosai shiyasa muka gani......amma duk da haka bamuga hoton madubin rayuwar ba har yanzu" Jikin hajiya Mammah rawa yafara bakinta yana fitar da wani hayaƙi,ganin Kultum zata fito yasa nayi saurin barin sashen nima nawa jikin yana rawa. Me suke nufi,kenan nida ɗana mune sanadin karyewarta a yanda ta yarda,in hakane to kuwa muna cikin hatsari,sannan dole kada tasan koni wacece, matar nan ta wuce yanda nake zato. Ina cikin tafiya ina tunani naji na bangaji mutum,saurin dawowa hankalina nayi tareda kallon Fatee. "Ke ina kike gani haka, kaman wata sabuwar makahuwa,kije mommy tana nemanki " Daga haka ta wuceni tana karairaya,nidai binta nayi da ido kafin na wuce sashen hajiya Maryam. A zaune na gansu itada Neelah suna magana,ita kuma yaushe ta dawo,da alama yaune. Saida na giashesu kafin na zauna a akan kujerar,Neelah ce ta kalleni tareda cewa. "Miye ya faru haka Sumaimah naganki kaman wacce taga fatalwa,ko kema kinji labarin nasarar da Ahmad yayi akan ƙungiyar BC?" "Uhm yayi nasara amma kuma yasake buɗe ƙofar gane shirinmu,domin a yanzu haka hajiya Mammah tasan da labarin yayi rayuwa a cikin ƙungiyar BC,kuma yanada ɗa da mata,duk da batasan sunanmu da fuskarmu ba amma nasan bazata zauna ba saita gano hakan" Abinda nagani a ɗakin hajiyah Mammah na sanar dasu,duk da basu wani razana ba,amma sunyi mamakin yanda takai har haka a shu'umanci.
Mun daɗe muna tattauna,wanda duk yawanci gargaɗi hajiyah Maryam takemin akan nayi taka tsantsan, lamarin,tunda yanzu yafi nada muni,ga zaman dazan ƙarayi a sashen hajiyah Mammah,domin inkana son kama damisa dole saika shiga sansaninsa. A ranar Ahmad yadawo daga yankinnamu,anyi murna sosai da nasararsa ciki kuwa harda hajiya Mammah,kaman ba fadarta ya ruguza ba. Musamman A.M Aliyu ba ƙaramin farin ciki yayi ba da nasarar. Ana ta murna amma bandani,domin wajen zamannawa na kullum wato lambu na tafi na zauna. Zuciyata nason ganin Ahmad domin nayi kewarsa sosai,amma kuma ina tuna kashedin da yayimin na cewar kada na kuskura nasake nuna fuskata a gabansa.
∆∆∆
Bayan sati ɗaya da wannan nasarar da gen Ahmad yasamu nutsuwarsa ta ɗan dawo ba kaman da ba,saidai duk da haka yakasa tsintar kansa da jin komai ya ƙare. Koda yake dama yasan akwai sauran rina a kaba,tunda har yanzu bai kama shugabar ƙungiyar ba,amma tunda yasan macece yanzu zarginsa kashi tamanin a cikin ɗari yana kan hajiya Maryam ne,don abinda yake kwanannan kenan saka mata ido na shige da ficenta,domin ya kula tashiga cikin tashin hankali da abinda yafaru,sannan ta tsiri zama cikin busy. Biron hannunsa yake dannawa yana ɗagoshi,duk da hakan akwai wani abun da babu. "Ohhh that girl why....meyasa nake missing ɗin matar wani,kaddai na fara son matar da bazata taba zama mallakina ba kai,ahah no ba sonta nake ba,inajin haushi ne da kuma zunubin abinda na aikata mata" Cije cije yake yace wancan yace wancan shi kaɗai,a iya sati guda daya wuce gabaɗaya yaki ko gidan baya son komawa,domin yana shiga zaiji yana so ya ganta,wanda kuma yasan bazai gantan ba,shida kansa ya bata umarnin kada ya sake ganinta a inda yake. Kai inaga barin ƙasar zayyi naɗan wasu watanni ko zaiji daɗi,dama abbah yabashi hutu tunda yasamu wannan nasarar. Yana cikin wasiwasinne Eemran ya shigo office ɗin. "Eemran kayimin arrenging na zuwa hutu gobe" "Ogah anya kuwa hakan zayyi wu,don an fitar da aiki daga headquater,kuma naga hadda kai a cikin wanda zayyi supervising" "Supervising ɗin me" "Uhmm a cikin trainee ɗin aka dauka masu ƙwaxo zaku tafi dasu Russia na tsawon wata Uku" Komawa jikin kujerar Ahmad yayi tareda sakin dogon numfashi. "Yaushene tafiyar?" "Gobene ogah" "Ohk" Abin yabawa Eemran mamaki,yayi tunanin zaice bazai jeba,amma saiyaji sabanin haka,kenan so yake yabar garin kota wacce hanya. Washagari bayan an gama tsara zaman sojojin a jirgi sun tafi kafin manyan suka bisu a private jet,duk cikinsu Ahmad ne kaɗai ƙarami. Lokacin dazai taho ko ƴan gidan bai fadamusu zai tafi ba,iya Neelah ce kawai tasani sai Saleem. Masauƙinsa aka kaimasa kayansa, bayan ya watsa ruwa yasaka riga marar nauyi ta shan iska. Fitowa yayi wajen cin abinci,amma shi a hadene da sauran ƙananan sojoji. Bayan ya zauna an saka masa abinci,har zai fara cin abinci yaga wani yazo ya zauna a opposite ɗinsa,mamaki abin yabashi,dan yasandai baizo dasu Eemran ba bare su zauna. Ɗagowa yayi suka haɗa ido da wani matashi,zaiyyi shi a haife,kallon rashin sani yake masa,amma kuma sai yaji kamar ya taba ganinsa. Shima kallonsa yake ko ƙiftawa bayayi,sai can kafin yace. "Goje mai kakeyi a nan,bayan batanka kaima soja ka shiga,amma meyasa baka faɗi inda kake ba,kasan kuwa halin da Sumaimah tashiga a sanadiyyar rashinka?" Maganar da bawan Allahn yayine ta dakeshi da ƙarfi,zaro ido yayi tareda ajiye cokalin yana kallonsa.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...28...
Number dakinsa kawai yabashi tareda yimasa alamar ya sameshi a can ɗin, Yagane mai yake nufi kuwa,sai yayi shuru da zancen akan zai sameshi a ɗakin. A zaune yake da labtop akan cinyarsa lokacin da musbahu yayi sallama a ɗakin,bayan ya zauna shuru sukayi babu wanda yace komai,saida suka ɗan ja kaman mutuna kafin Ahmad yayi masa magana. "Naji kana magana akan goje,ga dukkan alamu kasanni lokacin ina a matsayinsa,kuma kasan inda na zauna" Kallom mamaki Musbahu yabi Ahmad dashi kafin yace. "Ya kake magana kaman ba kaine goje ba,shin mai yake faruwane,ka rasa hankalin ka ne a hatsarin dakayi,shiyasa ka manta komai,amma bakayimin kamada wanda ya rasa hankalin sa ba" "Eh ba hankalina na rasa ba,nayi recovaring hankalina ne,saikuma na manta rayuwar danayi a wanda kake faɗa. Kafin muce komai zanso nasan wanene kai kuma menene alaƙata dakai a rayuwar bayan. Sunana Ahmad Aliyu,General under Investigation division" Zaro ido Musbahu yayi jin matsayin da Ahmad ya faɗa. "Shin mafarki nake kokuma idan har kaine goje yaushene kayi karatu haka,a sanina dai dabanci kakeyi da kuma aiki ma ƴan siyasa. Sannan kana nufin baka ganeni bane,nine fah Musbahu yayan Sumaimah matarka,duk da bakaje wajen ɗaurin aurenba amma ai muna haɗuwa a gari san......." "Bangane wanne labari kake min ba,kaine yayan matata,kuma banje wajen ɗaurin aure ba,meyasa toh? Barina baka labarin abinda yasa bansan kokai wayeba,sannan inaso ka bani labarin abinda yafaru daga farkon rayuwata a wannan gojen dakake faɗa har ƙarshe,harma da labarin ita matar tawa."
Bayan yabashi labarin abinda yasameshi ya rasa hankalin sa har yayi rayuwa a matsayin goje,ba ƙaramin mamaki yabawa Musbahu ba. Shima labarin rayuwarsa daya sani a matsayin goje ya faɗamasa,da yanayin aurensa da kuma yanda Sumaimah tasha wahalar zaman aurensa harda tafiyar dayayi ya barta. Abin ba ƙaramin tayarwa Ahmad hankali yayi ba sosai,shin dama haka yake a rayuwar,a ina zai samo wannan baiwar Allah,mai zaice da ita irin wannan abun daya jawo mata. Kama kai yayi tareda jan numfashi,tsawon lokaci ya ɗauka yana jimamin abinda ya aikata. "Zan shirya komawa gida gobe,zamu tafi ka nuna min itah" "Ahah hakan bazai yiyu ba general,duk da nasan kai ogah ne,amma inna bika zan samu matsala a nawa training,nayi ƙoƙari sosai kafin na samu wannan matsayin. Sannan kuma ita kanta wacce kake son zuwa wajenta bata nan,ta tafi garin abuja aikatau,saboda bayan tafiyarka hatta makarantar daka biyamata kuɗinta had ta gama sun hanata certificate,duk wani abu mutane sun washe ganin an ɗau shekara baka dawo ba,shiyasa ta tafi neman abinda zata rufamusu asiri" Wani irin sanyin jikin Ahmad ya sake jin wannan batun,gabaɗaya ya rasa mai yake masadaɗi. Wunin ranar gabaɗaya ƙareshi sukayi Musbahu yana yimasa labarin goje,batun zuwa wajen Sumaimah kuwa sun barshi akan suna komawa zasu nemi inda take yaje.
∆∆∆∆
Sumaimah {POV}
Bayan wata biyu.....
Yau tun safe na tashi da tashin zuciya,abu kaɗan sai naji zanyi amai,da sabuluna nafarayi a banɗaki. Bayan rana tayi har sannan ban saka komai a cikina ba,saboda banajin son komai. A zaune muke nida ummi bayan mun gama aikin ranar,inata magana niban kulaba ashe kallona takeyi,ɗaga mata gira nayi da alamar lafiya. "Lafiya kalau,kawai naga kin sauyaminne kwanannan,duk da ke farace amma ƙin ƙara fari,ga wayan bacci dakikeyi,komai inkin fara saikice kin gaji" Maganganun da ummi tayi dukka nima na kulada su,amma babban abin tashin hankalin shine abinda na zarga,wanda ban kawo shiba sai yanzun. Wani zabura nayi nai banɗakinmu da sauri,a gaban madubi na tsaya ina kallon kaina,mamana na kalla wanda naga sun ƙara girma,rabonsu da haka tun inada cikin Sayyid. Zaro ido nayi tareda shafa cikina,rabona da al'ada wata biyu kenan,wayyo mai nake tunda ban kulaba sai yanzu. "Innalillahi yanzu ya zanyi kenan,kenan ciki na samu a ranar? Mai yasa dukka biyun suka faru a rashin saninsa,nasan wannan zaisan nasane,amma da wanne zai kalleshi shine tashin hankalina,ahhhhh" Ƙarar danasaka ne yasa ummi yin magana daga cikin daki. "Sumaimah lafiyarki kuwa?" "Ba komai ummi" Fitowa nayi daga bnaɗakin ina rarraba ido,yanzu wazan tunkara da wannan zancen kenan,nasan hatsarin danake ciki nida wannan cikin Allah ne yasan iyakarsa. Don yanzu su hajiyah Mammah babban burinsu shine gano ni wacece,tunda yanzu babu komai ya ruguje. A bangaren hajiyah Maryam kuwa kullum ƙara rauni takeyi,Neelah kuwa batada lokacin kanta tunda Ahmad ya tafi ya barmata ragamar hidimominsa. Hanyar sashennasa na nufah,haka kawai na tsinci kaina dayin hakan. Buɗewa nayi na shiga,alamun rashin mutum duk sun nuna a wajen,har ƙura ta taru a falon. Ina shiga naji wani ƙamshi a falon,wannan wanne turarene haka dayaƙi washewa tsawon wata biyu. Ɗakin na bude na shiga,nan kamma har yafi falon,dan ji nayi wata nutsuwa tana sauƙamin. Duddubawa nakeyi ina neman turaren,saida na shinshina dukka turarensa amma ban jishi a ciki ba. Wardrobe ɗinsa na buɗe,inda ya lanƙaya kayan daya saka a gefe,a jikinsu turaren yafi yawa,ɗakkosu nayi ina shinshinawa,na daɗe ina abu ɗaya,sai daga baya nagane ina abu tamkar kuliyah. Kuma mai wai tsaya,kenan ba turare hancina yake shinshinowa ba,guminsa ne,yaushe na zama mai iya shinshino yanda gumin mutum yake?. Ajiye sauran kayan nayi na ɗauki riga ɗaya na boye,kan gadonsa na faɗa,ahhh nan ma jinayi kamar yana kai. Nice nake kewarsa kokuma ɗan cikina duk bai shafen ba,tunda naji daɗin kwanciyar bacci zanyi kawai. Bacci nayi na ƙoshi sai don kaina natashi,amma duk da haka banji ya wani isheni ba,mitstsike ido nayi,sai sannan na hango gari ta window yafara duhu. What bacci nayi na kusan tsawon awa shida ko biyar. Banɗakin sa na faɗa da sauri nayi alwala,mayafin kaina na yaye nayi sallah kafin na fito zuwa kitchen ɗinsa ko zan samu abinda zai iya shiga cikina. Tundaga lokacin dana gano inada ciki,sai yazama kamar hurashi akeyi,tsorona ɗaya nasan zayyimin girma fiyeda na sayyid,dan daga ganinsa ma. Nashiga damuwa sosai da lamarin,ga banida waya ta faɗi a ruwa bare na ƙira inna na faɗa mata. Kullum inna tashi da safe sainayi shiri mai kyau,gashi na tsiri saka hijabi da kuma ɗaurin zani akan cikin. Sati uku da fara laulayin har na rame na yi fayau. Fitowa nayi daga wanka kware kwaren danayi,to wankane babu sabulu,towel ne a jikina ina gogewa ruwan,kullum a banɗaki nake shiryawa,amma yau dayake naji su ummi suna aiki a babban falo shiyasa ban yi a banɗakin ba. Motsin tafiya naji,hakan yaa na rarumi hijabina na saka. "Dama kin ajiye hijabin,wannan boye boyen ya isa haka,nariga nasan cikine dake malama,inna tacemin wai ai mijinki ya kawoki ziyara,shine daga bada tsarabar ciki sai ya tafi,bazai tsaya a gaisa ba?" Sauƙe ajiyar zuciya nayi bayan naji bayanin ummin,kenan daman sunsan inada ciki,musamman abinda inna ladiyo tafaɗawa ummi,yayi min daɗin matuƙa,kuma ya kareni daga amsa tambayoyi. "Miye kikayi wani tsaye kamar gunki,kije sashen hajiyah Maryam wai tana nemanki,inna ladiyo ce tace na faɗa miki" Karisa shiryawa nayi cikin doguwar riga ta atamfa,nasaka hijabina na tafi. Kafinnan saida nabi ta wajen inna ladiyo tukunna tana kitchen. "Inna dama kinsan......." "Haba ƴar nan,muna tare a ɗaki ɗaya har mu kasa gane halinda kike ciki? Abinda zan faɗamiki shine ki daina wannan boye boyen haka,wanda yasani yariga yasani,wanda baisani ba kuma zaki jawo hankalin sa ne yasaka ayar tambaya" Ɗaga mata kai kawai nayi batareda nace komai ba,kuma maganar tata haka ne. "Kije hajiyah Maryam tana nemanki a sashenta" "Toh" Shine kaɗai amsata kafin na wuce can din,sai a lokacin naji rashin kyautawa ta,don rabona da sashen nayi sati biyu,wasan buya nayi tayi da ƴan gidan,saboda karsu gane inada ciki. Magana naji sunayi tun kafin na shiga,da waye haka suke surutu. tura ƙofar nayi na shiga,wani saurayine amma ba zai wuce shekara sha bakwai ba. Daga yanda suke maganar zaka gano cewar ɗan uwanta ne. "Wai huzaif yayar babanka nake fah ba kakarka,tashi to ku tafi gatanan ta shigo" Dukkansu kallona sukayi itada shi,kallo ɗaya mutum zayyi masa ya gano kamar da suke da hajiya maryam,tunda tace yayar banbansa to ɗan Taheer ne kenan,babban dansa. "Okay ni barina je waje,ki sameni a mota" Rabawa yayi zai wuce tagaba na hajiyah Maryam tayi masa magana. "Kai banason sakarci,bata girmeka bane da bazaka gaisheta ba" Cikin ɗaɗɗagawa irinta masu sabuwar samartaka ya gaisheni,nidai na amsa a taƙaice ya fice. Ƙarisawa nayi muka gaisa da hajiya Maryam,sunkuyar da kaina nayi,don naji kunya sosai. "Hhhh yau kuma kunyata kikeji,kijr zai kaiki gidansu ne akwai wanda zaki haɗu dasu,bansan ko ki kwana ba ga wannan ki riqe,amma ki tabbatar ki dawo gobe. Kije maza Allah ya tsare,ki kula sosai dan yanzu ba kaman da ba,na fadamasa kada yayi tuƙin ganganci" Nidai da toh na amsa mata dakuma godiya. Saikuma kaina a ɗaure shin dawa zan haɗu a gidan da ban taba zuwa ba.. A haka dai na bi bayan wanda taƙira da huzaif ɗin zuwa motarsa. Ina shiga ya tayar da itah ya hau hanya ko magana bayyimin ba.
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...29...