Kenza eBookz

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 17

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 17

Sanadin caca book 2 complete Chapter 17: Sanadin caca book 2 complete Chapter 17. Bayan mun shigo gidan fita nayi daga motar ya nufi wajen parcking,ina nan…

3,048 words

Bayan mun shigo gidan fita nayi daga motar ya nufi wajen parcking,ina nan tsaye ina kallon ƙyauye naga ya wuce ta gefena,baicemin na biyoshiba nabi bayansa da sauri,wani falo muka wuce kafin mukazo wani daban. Bai shigaba da hannu ya nunamin na shiga,shikuma yayi wani wajen daban. Kaman wata baƙuwar kaza haka na kutsa kai ina rarraba ido. Wazan gani inna ce da deeja dakuma Sayyid. Suman tsaye nayi ina kallonsu,har deeja ta rungumeni banyi motsi ba,wannan wanne irin bazata ne haka. Nayi kaina tambayar,in suna haka tsaf zasu saka kaina yin kwancewa. "Innaaa......" Shine kawai abinda nasamu faɗi,dariya sukayi tare,har matar danake tunanin matar ƙanin hajiyah Maryam ɗince,wacce suke cewa Hajiya Shukurah. "To anan dasu bazaki iso ba,duk mamaki ne yanaki motsawa" Da sauri nazo inda inna take na rungumeta da ƙarfi,kukan Sayyid naji yana jan hijabi nah. Juyawa nayi na tsura masa,kama naga yanayi da hajiyah Maryam,kodan nasan yanzu jikantane,amma idon kam na ubansa ne. Tureni yake yana tiro baki,waina matsa a jikin inna. Dariya abin yabani,wannan kam halin babansa ne. Hannu nasa na ɗaukeshi,zuciyata cike dason yaron,wai dana riqeshi saina tuno labarin hajiyah Maryam,gaskiya ba ƙaramin azantuwa tayi na sosai. Kallona yake yaƙi sakin jikinsa dani,deeja tana matsowa ya miƙa mata hannu. Dariya abin yabani,wato har ya mantani kenan. Inna na kalla tareda haɗe rai. "Inna kiga ya mantani,laifinki ne bakya bashi labarina" "Ohh jimin,labarinki ma kike cewa,keda kika figeshi a nono kika gudo saboda duniya tamiki zafi,kuma ma dakike can ɗin wani rainonsa kike daya miki zafi. Kinshigo gidan mutane ko gaishesu bakiyi ba kina ta danki koh" Maganar da tayine yabani kunya,kuma fah ban gaisheda matar gidan ba. Cikin rusunawa na gaisheta,dariya tayi kafin ta amsa. "Lahh kada ki damu Sumaimah,ai kinyi kewarsune shiyasa. Dan ma kada ki damu anan zasu zauna" Kallon inna nayi da sauri,anan zasu zauna kaman yah. Ta gano wanne tunani nake,saita bani amsa. "Nice nake neman wacce zata tayani aiki,shine Anty Maryam tacemin daman tanason inna ta dawo da aiki,sune suka zauna a sashen hajiyah Mammah suka raini Ahmad itada Inna ladiyo. To bazata manta dasu ba har abada." Cikeda murna dakuma mamakin dama ashe inna tasan Ahmad tun yana ƙarami na kalleta. Murmushin manya tayi kafin tace. "Kiƙara mata godiya har deeja zata saka a makaranta,dama nayi tunanin tafiya da itah zan koma garinmu,to saiga mota wai ƙira daga hajiya,shine muka taho" Bayan na gama godiyar wani abune ya fadomin. "Inna meyasa zaki tafi garinku" "Hmmm wata shida kenan da gaji ta matsawa baba audu kan cewar ya siyar da sashenmu,yanzu haka wanda suka siya sun matsa mu tashi" Wani takaicine naji yazomin wuya nah menene haka mutanennan suke nufi. Duk kuma wajen bai zama gadon inna ba,ɗanta ya mutu ita tuminin takaba kawai za'a bata,sannna Ahmad ba ɗan ta bane. Ɗakin da aka bawa inna muka koma,anan sabon hira ya buɗe. Deeja na kalla tana shirya kayansu,hankalin yarinyar yabani mamaki,dan lokacin dana tafi ba wani har can bane,yanzu ta zama tamkar uwar Sayyid komai wajenta yake zuwa. Yau jina nake tamkar an tsundumani a aljanna,abu kaɗan saina kallesu na sake kallonsu,jinake kamar na maidasu cikina. Labari kuwa har raba dare mukayi munayi,nasu gaji da kuma gidanmu. Bayan mun gama hirar Deejah tayi bacci itada Sayyid tashi nayi na shiga banɗaki. Bayanna fito rigata na cire nayi sama da zanin,ina shirin kwanciya naji maganar inna. "Shin kun daidaita ne a tsakaninku?" "Uhmm ni dawa?" "Zaki fara wannan juyar da maganar kamar baki gane ba, mijinki mana nake nufi" "Ahah bamu shirya ba,har yanzu baisanni ba" "Baisani ba ya akayi kuma naga ciki a jikinki" Shuru nayi na rasa ma mai zance mata. "Uhm.....inna uhmm lokacin baya cikin hankalin sa ne,wata tabashi magani sai shine" Ganin na duburburcene yasa ta juyar da kanta tareda cewa. "Allah ya kyauta,ya daidaita ku bisa lokacin daya dace" Ameen nace a hankali daga nan na kwanta. Da safe bayan mun tashi nice nayi aikace aikacen gidan dukka,bayan mun gama karyawa muna zaune hajiyah Shukurah tashigo da waya a hannunta. "Sumaimah ga kira nan daga hajiyah Maryam waiki koma driver yazo ɗaukarki" Zaro ido nayi kaman zanyi kuka,dan har raina gidan ya isheni sosai,don ba yadda zanyi ne. Dan kwana ɗaya danayi dasu inna har naji daɗi,gashi bangama ganinsu ba kuma zan tafi. "Uhm hajiyah ki bata haƙuri dan Allah na ƙara" "Ahah ki koma kici gaba da aikinki,bakya tunanin a halin da kike ciki zamanki kusada su ma hadari ne,dan haka ki koma kici gaba da kula Allah yakiyaye,matsalar hajiyah Mammah tariga tasan take a matsayin wacce tasan mai take ciki,zamanki kusan danginki zaisa ta binciko dawa kike tare." Ɗaga kai nayi alamar na fahimta. Badan naso ba na shirya komawa. Naso tafiyah da Sayyid amma nasan bazan fara wannan gangancin ba mai suna gani kasheni,dan haka sallama nayi musu na dawo. Tun a hanya naji kamar banje ba. Watan su inna ɗaya kenan da dawowa,amma bangansu sosai ba,sai nayi tabi kafin hajiyah Maryam ta barni naje. I zuwa wannan lokacin cikin jikina ya fito,saboda girman dayakeyi nan da nan,don ya shiga wata na huɗu a satinnan. Ana Sayyid saida yayi kusan wata bakwai kafin yakai haka,amma shi yanzu haka yakai kusan cikin wata bakwai a matan da basa girman ciki. Kowa a gidan yanzu yasan inada ciki,saidai ban damu ba,saboda duk a zatonsu na mijina ne daya tafi rani. Ita kanta hajiyah Mammah har kyauta takemin,tareda cewa mijina bai kyauta ba daya barni da ciki yasake komawa. Nidai saidai nayi murmushi nace uhm. Bayan nayi sallahr asuba bacci nakoma mai shegen nauyi,gashi nayi wata ƙiba saboda yawan cin abinci kaman gara,cina har ya wuce na cikin Sayyid. Ummi har boye abincinta take inta ganni,inna ladiyo ce da hajiyah Maryam haka hajiyah Mammah suke bani abinci duk sanda suka ganni. Bayan na miƙe daga kan katifar madubi na ɗauka na kalli fuskata,taƙara fari da ƙiba,haka ma jikina. Ƙafafuna kam ba'a magana. Wanka na shiga ina fitowa nasaka doguwar riga,daga cikin materials ɗin da hajiyah Maryam ta ɗinkamin saboda goyon ciki,naji daɗinsu kuwa sosai ba kaɗan ba. Ummi ce tashigo ɗakin ina shafa mai,hijabi ta ɗauka tasaka da kuɗi a hannunta. "Ke kuma fah ina zuwa haka,nasan baki fiye zuwa aike ba,an fi tura mai gadi shikaɗai" "Hmmm wai Yallabai ne zai dawo shine inna tayimin lissafin abinda zan siyo,Sannan kuma ki faɗamin mai kike so zaki haɗamasa" Zaro ido nayi tareda kallonta,wanne yallabaiɗin badai Ahmad ba,gabaɗaya na manta da ashe zai dawo,bana tunashi sainazo kwanciya na rungume rigarsa tukunna. "Kinga tsaya tsaya basai kinje ba zanje" "Ke dalla kimin lissafi naga bake kika sakani ba, yanzuma daga sashensa nake na gyara,kina bacci ɗazu na ɗauki key" Kallonta nake da mamaki,nasan inna ce tasakata,itama kuma tana tausayina nasan. Rungumeta nayi ina zuba mata godiya,ba ƙaramin daɗi naji ba data gyara ɗin. "Nagode ummi,barinaje na dudduba sashen,sannan na gyara kitchen ɗin. Kafinnan zan miki lissafin abubuwan" Lokacin dana shiga sashen tsaf yake ta gyarashi koni zanyi iya haka. Saidai ɗaki da kuma banɗaki dana ɗan ƙara gyarawa. Kuɗi da yawa hajiyah Maryam tabawa inna ladiyo na abincinnasa,ni kaina shaidace yanda take ji dashi a cikin ranta. Hmmm koya zamu kaya nidashi idan ya dawo,shin wacce amsa zan bashi ne idan yayimin tambayar miye a jikina. Kitchen ɗin na gyara na fitar da abinda zanyi amfani dashi. Ina cikin haka ummi ta dawo,sosai ta tayani har muka gama aikin wajen daya na rana,lokacin kam nasan anty thing a kowanne time zai iya dawowa,da sauri muka ƙarisa nabar sashen,domin banaso ya dawo ya sameni,ban shirya ganinsa a yau ɗin ba. Lokacin da muka koma daki nayi sallah waje na samu na zauna ina haki tareda sauke numfashi,don ba ƙaramin gajiya nayi ba,jikina nauyi yakemin kwanannan. Ruwa mai sanyi ummi ta miƙomin tareda ajiye abincin mu a tsakiyar ɗakin. Saida na zuqe ruwan naja ajiyar zuciya kafin nace. "Kai gaskiya ummi a tafawa ruwa,ruwa rahama ce,mai rowar ruwa ya cika marowaci" Dariya tayi kafin tace. "Ehh lallai yau gana mai yiwa ruwa santi,haba kema da laifinki,ji yanda kika dage kina yimaza aiki kaman wani mijinki,ko wanda kike aure bakya yimasa bautar da kike masa,Sannan abinda yabani mamaki ban taba ji kince ga salary ɗin ki ba. Ko yake shima wannan mijinnaki da nice da tuni ai munyi wacce zamuyi,na taho aikatau domin mu rufawa kanmu asiri,amma shine hakan bai isheka ba ka biyoni kayimin ciki ka haɗani da wahala,inama zan ganshi da sai na tsayar masa" "Hhhhh ummi kinada abin dariyah,zaki iya tsayar masa idan na hadakun?" "Ehh mana bari ki gani Allah ya kaimu" Murmushi nayi batareda nasake cewa komai ba na saka hannuna a abinci. Muna gamawa na kishingiɗa domin na kwanta na huta.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2* ...30...

A jirgi ɗaya Musbahu suka taho shida Ahmad,zaibi normal jirgi ya hanashi akan zasu taho tare. Don a dan wannan wata ukun da sukayi sunyi sabo sosai,wanda duk sanadin labarin Matar sa ne. Bayan sun sauƙa kowa jawo jakarsa yayi suka fito. "Toh general ni daga nan zan hau motar gida" "Ahhh habadai,kazo muje gida mana ayi ka huta in yaso gobe saika wuce,sannan ya zancen .......dakace zaka haɗani da itah,gashi numberta tunda ka bani kullum saina gwada amma ban sameta ba" "Shiyasa nakeson tafiya gida ai general,saboda nasan inna tasan inda take zata bani address ɗinta. Sannan karka damu na gode da dukkan halaccinka,inna dawo nayi maka alƙawarin zanzo har gida,saimu je inda take tare." "Yaushe zaka dawo,nan da sati biyu za'ayi bikin nasararku" "Eh kafin lokacin zan dawo Inshaallah" Sai bayan da Musbahu ya shiga motar garinsu kafin driver yazo ɗaukar Ahmad zuwa gida. Sashensa ya wuce direct ta ƙofar baya,dan tun abinda ya faru yakejin kamar shida ƴan gidan basu hada wani jini na azo a gani ba. Mahaifinsa ne ɗan uwansu to baya raye,dangin mahaifiyar sa kuma na can wani gari daban,daɗin daɗawa kuma basa Ga maciji da su. Ɗan tsayawa yayi daga bakin ƙofa yana kallon yanda aka gyara ɗakin,Sumaimah ce ta faɗo masa a rai,yasan babu mai wannan aikin sai itah. Ɗaki ya wuce ya ajiye jakarsa ya watsa ruwa. Falon ya fito yana dadanna waya,daga idon da zayyi suka haɗa ido da saleem,wanda yake hakimce akan kujera yana kallon yayannasa. Hade ido yayi ya kafeshi dasu kaman shine babba,abin ba ƙaramin mamaki yabawa Ahmad ba. "Kaikuma fah ya haka' "Dole ka tambaya mana yah Ahmad,yanzu baka gidannan tsawon wata uku ka dawo amma ka wuto sashenka kawai,ƴan cikin gida nacan suna zancen" "To so what suyi maganar ma,dama sun damu dani ne,kaima in zancen dazakamin kenan to kama hanyarka kayi waje" Jijjiga kai Saleem yayi tareda jan numfashi,yana son yayannasa kuma wani lokacin baya ganin laifinsa,yanayine yasakashi zama hakan. Wajen dining ya nufah ya buɗe kulolin,ƙamshin abincine ya bugeshi saida ya lumshe ido. Zama yayi ya zuba abincin yaci yayi nak,ko ci kanka baicewa Saleem ba,yayinda shikuma ya zuba masa ido yana cin abincin kaman ya samu tv. "Hmmm kana cewa ba ruwanka da yan aiki gashinan kuma kazo ka ci abincin mai aikin gidan. Ni inaga ƙoƙarinta ma,da ciki tayi maka wani gyaran sashe da kuma abinci,saikace mijinta" Yana cikin goge bakinsa ya cakk jin abinda Saleem yafaɗa,ciki ciki kuma wanne iri . "Saleem mai kake cewa cikine da wa?" "Sumaimah mana mai aikinka,ohh da kanace budurwace,naga dama ka fara nuna kishi akanta,tun wuri gwanda ka bari,naji an ce cikine da itah,mijinta yazo ganinta sai gata da ciki,lallai wannan miji ya iya bugu sosai" Wani zimmm kan Ahmad yayi,a ransa yana ta maimaita Allah yasa dagaske na mijinnata ne bashine ba. Gumin daya keto masa ya goge tareda cewa, "Cikinnata zaikai kaman ya" "Oho nina sani,naji dai ana cewa yayi babba kawai" Duk da abinda Saleem ya faɗamasa hankalin sa bai kwanta ba. Wayarsa ya ɗauko ta gida wanda takeda layinsa na nigeria.. Ƙiranta ya farayi amma shuru bata shiga,haka har ya Haƙura don kansa. Faɗawa yayi zurfin tunani Gabaɗaya ya gagara barwa kansa cikin jikinta ba nasane,kai yasan ma nasane. Hannun Saleem yagani yana yawo akan fuskarsa,hakanne yasakashi firgit ya dawo hankalin sa. Tashi yayi zaune yayi hanyar ƙofar dazata shigar dashi cikin gidan. "Ina kuma zakaje ogah ta wannan ƙofar?" "Zan shiga na gaisar da mutanen gidanne sarkin tambaya" Sakin baki yayi saida yaga ya shige kafin yabi bayansa,a bangarensa kuwa don ya haɗu da Sumaimah zai shiga. Ba kowa a babban falon gidan sai Sameer wanda yabada hankalin sa gabaɗaya kan wayar hannunsa.. Jin shigowar mutum yasa ya ɗaga kansa,yana ganin Ahmad ne ya cigaba da harkar gabansa. "Don kana zargina meyasa bazaka zo gaba da gaba ka tuhumeni akai ba,saika dunga binciken hakan a bayan fage?" Ajiye wayar Sameer yayi jin topic ɗin da Ahmad ya ɗauko. "Hmm menene abin zuwa gabanka na faɗamaka,bayan nasan bazaka fadamin gaskiya ba. "Taya zan faɗamaka gaskiya bayan nima a lokacin bansan ta ba? Zarginka gaskiya ne amma ba yanda kake tunani bane. Nine wanda mukayi faɗa dakai harka cakamin wuƙa" Yafaɗa yana ƙarisa maganar tareda buɗe masa gefen cikinsa. Zaro ido Sameer yayi,yayinda fuskarsa ta nuna rashin jin ɗaɗin yanda yayi masa raunin,amma shima ai ya dukashi sosai. Shuru sukayi babu mai cewa komai,sai can kafin Ahmad yace. "In kanada kokwanto ka daina kawai gaba,ka tunkareni dashi" Yana gama faɗin hakan yayi masa ɗan Murmushin kwarewa. Duk maganar da suke Sumaimah na jinsu,wacce take tsaye cak tayi suman wucin gadi,jikinta rawa yake wanda ta ɗauki tiren,kaddai Ahmad ya tuna rayuwarsa ta goje,in kuwa hakane to zai ganeta tana shiga. Har ta juya zata koma taji muryar Sameer. "Yadai naga kin tsaya kuma zaki koma,ko kin manta wani abune,sauri nake fah zan fita" Shigowa tayi kanta a ƙasa,ta gefen ido tana kallon Ahmad wanda ya tashi zai fita daga falon,da alama bai san zata shigo,saidai tunda ya riga ya tashi kawai ya fice. Yazo giftawa ta gefenta tayi ƙamshin turaren datake shaƙa kafin tayi bacci a jikinsa,wannan har yafi wancar shigarta,nutsuwa da kasala ya sauƙar mata a lokaci guda,har bata san lokacin data ja dogon numfashi ba. Sai bayan ya wuce ta dawo hankalin ta kafin ta kulada Sameer wanda yake binta da kallon mamaki. "Yadai naga kin tsaya ido rufe kaman mai addu'ar kirista,idan bakya jin daɗi waye yace kiyi aiki?" Bata bashi amsa ba sai ajiye masa abincin da tayi ta fita,gaba ɗaya tunda yanxu sun gane tana aure kuma harda cikin basa yin maganar da sukeyi da,kuma ma cikin ya maidata marar magana,ga yawan gajiya. Bayan ta fito daga falon har zata wuce taga Ahmad tsaye a bakin shiga sashensa,diriricewa tayi zata yi hanyar kitchen da sauri,sai kuma taji muryasa. "Kizo yanzu ina son magana dake" Daga haka ya shige ciki. Ajiyar zuciya tasake tana bin ƙofar da kallon. Banda sunan Allah babu abinda take ambata. Tiren ta mayar kitchen kafin ta dawo zuwa sashennasa,zuciyarta cikeda zullumin yanda zasu ƙare,tasan dole yaji labarin cikinta kokuma ma yagani da idonsa. Tura ƙofar falon tayi ta shiga,yana zaune akan kujera yana kallo,amma daga gani kasan hankalin sa baya kan kallon. Ɗauke idonsa yayi daga kan tv ya mayar kanta,tasan bakomai yake dubawa ba sai yanda ta sauya sosai. Duk da hijabine a jikinta amma dole a gane hakan. Saida tazo kusada shi kafin ta zauna a tsakiyar falon tana kallon tiles.. Takai minti biyar a haka kafin ta ɗago,desame ita yake kallo har zuwa lokacin. Saida suka haɗa ido kafin yayi magana.. "Shin ban cancanci kimin bayani ba,cikin waye a jikinki. Ni kokuma mijinki? Karki bani amsar daba haka ba,domin idan kika boyemin dole zan gano gaskiya domin zanyi binciken mijinnaki a garinku nagano hakane koba hakane ba. Dan haka ki amsa min *cikin waye?*?" Shuru Sumaimah tayi bata bashi amsa ba,banda rawa da jikinta yake ba komai..saboda yanda yake kausasa mata murya. "Na mijinki ne?" Ɗaga masa kai tayi "Na wane?" Nan ma ɗaga masa kai tayi,daka mata tsawa tayi kagin tana bashi amsa guda biyu. "Ki bani amsa da bakinki cikin waye a jikinki" A yanzun bude bakinta tayi tareda cewa. "Cikinka nehhhh" Runtse ido yayi tareda komawa jikin kujerar ya lafe,shidama hakan yayi tunani,yasan babu wani mijinta,tayi hakanne domin ta boye,kuma hakan yayi domin zai ara masa lokacin mai ya kamata yayi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda yake ta maimaitawa idonsa rufe.. Kallonsa Sumaimah tayi tareda fara hawaye tana jijjiga kai. "Cikin shege dashi zan fara ajiye jinina a gidanmu,da wanne ido zan kalli mutane kenan,shin ke kanki mai zancemiki bare mijinki *KAICO NAH* (littafina na huɗu,wanda ya tara ɗumin darasi kenan mai yamin magana). Da wannan zunubi da kuma ɗanyen aiki dana aikata,shi kanshi ɗan na cuce shi na..........." "Ya isa haka" Shine abinda Sumaimah ta faɗa da ƙarfi tareda ƙara sautin kukan ta. "Kada kasake faɗin hakan akanka da kuma ɗan cikina,domin dukkanku baku cancanci wannan bayaninnaka ba sam,idan laifine ma nice mai laifin kuma na ɗauka,sannan ciki dama ban dangantaka dashi ba,duk da cewa kaine mafi kusantuwar dashi. Duk abinda kakeji akansa kanada damar kaji,amma na roƙeka kada kasake furtamin wannan kalmar. Ka ɗauka tamkar wannan abin bai faru ba,ta hakanne zaka manta dashi ka koma tamkar yanda kake. Sannan yanda kake daukan abubuwan ba haka suke ba. Zan dawo aiki gobe,saidai bazan dunga shigowa ba sai ka fita,haka kafin ka dawo bazaka ganni ba,ba'a samu wata mai aikin ba shiyasa,kafin a samu zan dena." Tana gama faɗin hakan ta miƙe daga zaunen da take tana goge hawayen fuskarta,harta kai bakin ƙofah taji maganar sa a cikin dashashshiyar murya. "Watansa uku kenan" "Eh" "Lafiya kike" "Eh" Kici gaba da jira amma dolene zan ɗau mataki akai,zan nemi mijinki akan maganar,dolene na karbi hukuncin abinda na aikata,abin yayi muni dayawa" Wannan karon Sumaimah bata bashi amsa ba ta fita,tana jin yanda muryarsa ta karye tayi raunin ba ƙaramin tausayinsu take ji ba a wannnan alaƙar,daga itah har shi...... Fatanta Allah ya bata lafiyar cigaba da kulada jaririnnasu,Sannan kuma yabata da sauƙi. Ɗazun bataso faɗa masa cikinsa bane,gudun kada yayi bincike ya gano komai ne yasa ta amsa masa da eh ɗin.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2* ...31...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull