Sanadin caca book 2 complete - Chapter 18
Sanadin caca book 2 complete Chapter 18: Sanadin caca book 2 complete Chapter 18. Anyi sati guda da Ahmad ya gane cewar Sumaimah tanada cikinshi,kuma har…
3,154 words
Anyi sati guda da Ahmad ya gane cewar Sumaimah tanada cikinshi,kuma har zuwa yanzun hankalin sa bai kwanta ba,har mafarki yake mijinta yasaka masa wuƙa a wuyah,abinda yake bashi mamaki kuma mijinnata kamarsu ɗaya dashi,saidai yana zuwa masane a salo na daba. Yau ma tun Dare abinda ya kwana yanayi kenan,da asuba bai koma bacci ba,karatun qur'ani yayi tareda neman gafarar Allah bisa wannan dumbin zunubi nasa. Da wuri ya fita daga gidan, gabaɗaya abubuwa sun isheshi. Lokacin dayaje office babu kowa a headquarter sai masu shara da gyare gyare,aikin dayake kansa ya dauka ya fara,ko zai rage abinda yake cikin ransa. Wajen misalin ƙarfe sha biyu yaga kira a wayarsa,sunan Musbahu yagani,dama yana expecting kirannasa tun jiyah amma shuru. Yana ɗagawa sallama sukayi yace masa. "Yah Musbahu naƙira ka baka ɗaga ba,gobene fah za'ayi bikin baku matsayin" "Oga wanann yayan da kake ƙirana dashi na kasa sabawa dashi,gani fah a ƙofar headquater bansan office ɗin ka ba" "Okay ka tsaya ganinan zuwa yanzu" Ajiye aikin dayake yayi ya fita daga office ɗin,binsa wani squad na ma'aikata sukayi,dama yana ciki,babu wanda yaga ya fito tunda suka zo. Da sauri sauri ya fita harabar wajen,daga nesa ya hango Musbahu a tsaye wajen da ake parking motoci. Tun daga nesa daya ganshi ya taho daga wajen suka yi gaisuwar musabaha. "Barkanka da zuwa muƙarisa" "Lahh ogah da basai ka shigo bama,in ka yimin kwatance ma zanzo" "Ahah karka damu ƙarisa,bayan abinda yake tsakaninmu inayi maka kallon aminina ne" Tafiya suke suna tattaunawa har suka isa,ruwan sanyi yabashi don shine abinda yakeda shi a office ɗin. "Ga ruwa kasha hanya,barina ƙarisa wannan saimu tafi gida kaci abinci" "Zan sha ruwan dai abinci kam daka barshi,dan har nayi booking na hotel,muna gaisawa zanje na sauya kaya sai mu haɗu. Har yanzu ina kiran wayar ta ma baya shiga,bansan meyasa ba. Hmmm inaga akwai matsala........." Jim Musbahu yayi daya faɗi hakan,wanda hakan yasa Ahmad bashi dukkan nutsuwar sa donjin wacce matsala ce. "Basa garin,daga innan da Deejah dakuma Sayyid,na tambayi matar gidan kuma tana cemin wata baƙar motace tazo ta daukesu wancan watan zuwa nan abuja,bansan waye ba ,amma jikina na bani ko gidan da Sumaimah take aikine" "Amma kana gani wanne wajene haka,mai ya faru dukka suka tafi gabaɗaya,basusan inda suke ba address ɗinsu?" Cikeda damuwa Ahmad yake tambayar,gaba ɗaya hankalinsa ya tashi. Ji yake duk laifinsa ne dabai nemeta ba,gashi har ta shiga duniya neman aikatau saboda rashin abinyi. Rarrashinsa Musbahu ya fara yi ganin yanda hankalin sa ya tashi,don yasan kansa yake ɗorawa duk laifin abinda ya faru. Shikansa ba ƙaramin tausaya masa yayi ba,ace ka yi rayuwa da mata harta haihu amma baka sani ba,to amma meyasa ya kasa tunawa. Shine wasi wasin da Musbahu yakeyi,wanda shima Ahmad yayi irinnasa. Sun dade suna zance duk akan matar tasane,saikuma wanda yake damunsa aransa na Sumaimah. "Bakomai Musbahu karka damu,Inshaallah Allah zai bayyana su. Yanzu dai muje gida tukunna daganan sai mu wuce gidan tv bada information ɗinsu,da kuma radio,maybe idan sunji ko wani yasansu ya ƙira. Ga matsalar babu hotunansu." A motar Ahmad suka fita daga headquater zuwa gidansu. Direnct sashensa ya wuce dashi basu shiga cikin gidan ba. Shidai Musbahu binsa yakeyi a baya,don ya damune ma yabiyoshi,sannan shima yana da buƙatar son ganinsu,musamman Deejah wacce yakejin kaman nauyin kulada itah a kansa yake. A falo yamasa iso ya zauna,motsin mutum yaji a kitchen,sannan kuma babu abinci a dinning,sai sannan ya tuna ya rage awa guda hadda rabi akan lokacin dawowarsa,ajiyar zuciya yayi yasan abinci take,koba komai zata fiddashi kunya,da har yayi niyyar kuwa hanata yi masa aiki,yanzu ma daga ya samu matarsa sai Yanda zayyi da case ɗinta. Kitchen ɗin a yashiga ya sameta a kan stool tana wanke kwanukan da tayi amfani dasu,a gefe kuma ta jera kayan abincin a kan tire,da alama tagama gyara wajen take kafin ta tafi. Aikinta take a hankali ko kuladashi batayi ba,hakanne yabashi damar ƙare mata kallo,tayi fari tayi ƙiba fiyeda da,wanda kuma yasan cikinne ya sakata,don gashinan yafito a jikinta,dayake doguwar rigace a jikinta,kuma ta fara kamata saboda cikin. Kyau tayi masa a hakan,inaga matarsa take masa wannan hidimar da cikinsa a jikinta. Inama matar dayake ta nema ce. Wani runtse ido yayi tareda jijjiga kai,ahah wannan matar wani ce wanda yaci amana. Tabon dayake zuciyarsa na abinda ya aikata ne ya dawo sabo. Jinginar dayayi a jikin ƙofar kitchen ɗinne yasaka ƙofar yin ƙara,wanda kuma ya ankarar da Sumaimah wacce kanta yake sunkuye,kallonsa take da alamar mai ya dawo dashi a lokacin. Lokaci guda ya tsime tareda yin gyaran murya. "Nayi baƙo ne mun dawo dashi,zan ɗauki cup ne na shan ruwa,sannan idan kin gama abincin ki kawo shima yanzu" Yana gama faɗin hakan ya ɗauki cup biyu a inda ta jera ya fita,itadai da kallo kawai tabishi tareda tabe baki. Gabaɗaya ya dagula mata lissafi da ƙamshin jikinsa,wanda yake rikitata,aman da take ji ɗazu ma yakoma. Bayan ya fita cigaba tayi da wanke wankenta,saida ta gama kana ta ɗau kwanukan abincin da saka su plate da komai zata kai musu. Lokacin data shiga da Ahmad suka haɗa ido,saboda shine yake facing kitchen ɗin,shikuma baƙonnasa ya bawa kitchen ɗin baya,magana taji sunayi akan yaɗa labarinta ko za'a sameta,har zuwa taje ta ajiye kayan abincin akan dining table, juyowar da tayi zata tafine idonta ya sauƙa akan Musbahu,yayinda shima itan ya kalla a lokacin daidai yakai gorar ruwa bakinsa. Dawowa yayi dashi da sauri tareda zare ido. "Sumaimah!!!!" "Yah Musbahu" Itama ta faɗa cikeda mamakin ganinsa a nan ɗin. Ahmad ne ya kalleshi tareda cewa. "Kasanta ne?" "Itace fahh dama kuna tarene tuntuni?" "Itace wa,muna tareda itah a ina?" "Mai kake nufi,bakasan wacece ba,ko aljana ce kai ni kaɗai nake ganinta,Sumaimah ce fah matarka wacce ka bari ka tafi. Itace muke nema" Da wani mungun sauri Ahmad ya kalleta a razane,ganin kallon dayayi matane yasakata sauƙe idonta,wani kuka ne da batasan na menene ba ya kufce mata,dama abinka da yanayinta ya koma na kukan. Zuba mata ido sukayi dukka ganin yanda take ta kuka kaman an daketa. Musbahu ne yayi ta mazan yi mata magana. "Mai aka miki kuma kika fara kuka,zo nan ki faɗamin mai yake faruwa" Takawa ta farayi kaman wacce ƙwai ya fashewa a ciki,ta gaban Ahmad ta wuce zuwa inda Musbahu yake,shidai binta yayi da kallo kaman ya samu tv. Tun daga tambayar ko kwaƙwƙwaran motsi bai ƙara ba. "Miye ya faru da wayarki nayi ta ƙiranki bata shiga,ya akayi kike zaune da mijinki amma bai san ke bace,yana can yana nemanki. Ina kuma su inna suke,domin dana koma gida an ce suna garinnan?" "Uhm uhm wayar ta baci banda wata kuma,su inna kuma suna gidan Hajiyah Shukurah ƙanwar hajiyah Maryam. Ta ɗauki inna ne aiki,kawu audu ne ya koresu bayan tafiyarsa (tafaɗa tana kallon Ahmad kafin ta ɗauke idonta). Tunda wai dama wajen ya zama nasa. Ina baba yake dasu Ammi?" "Baki ƙarasa bani amsata ba Sumaimah,meyasa dakika haɗu da mijinki baki faɗamasa ke wacece ba,ko rashin ganeki da yayi ne yasa kika ƙullaceshi akan sai sanda ya sani da kansa?" Jijjiga kai tayi da sauri tareda cewa. "Ahah ba haka bane,ba a son raina naƙi faɗamasa ba,saidan yazama dolen,mutanen da suka yi sanadiyyar zamansa a goje suna tareda shi,idan suka sanni wacece bazasu ƙyaleni na dakuma shi,shiyasa ban faɗamasa ba" "Mut......." "Dan Allah kada ka tambayeni dalili yah Musbahu,inasu baba da ammi baka faɗamin ya suke ba.......baka ga Deejah ba tayi hankali kaman ba itah ba" Tayi hakane domin ta kawar da maganar ɗazun,duk da tasan hakan bazayyi yu ba. Ganin kallon da Ahmad yake yiwa Sumaimah mai cikeda abubuwa da dama yasa Musbahu cewa.. "Suna nan ƙalau,yanzu dai bani address ɗin inda su inna suke,ni yanzu zan tafi,kina buƙatar yin magana dashi" Jimm tayi jin abinda yace,amma haka ta bashi ba yanda zatayi. Kitchen ta koma tanajin fitarsu shida Ahmad ɗin. Hannu ta ɗora akan zuciyarta wacce take bugawa fatt fatt. A bangaren Ahmad kuwa da Musbahu yace zai tafi kasa hanashi yayi,domin a yanzu burinsa ɗaya shine jin bayani daga bakin Sumaimah,na akan me ta ƙi faɗamasa matsayinta a wajensa. Ganin har suna shirin rabuwa Ahmad baice komai ba yasa Musbahu cewa. "To ni zan tafi gen. Ga yanda abu ya kasance,amma ni abinda nake gani ka bita a sannu ta faɗamaka mai yake faruwa,ni kaina shaidane akan irin son da take maka a lokacin baya,bata haɗaka da komai,duk da mutane suna jin tsonka amma kaine wanda take burin komawa gareshi idan tayi nisa dashi" Da kalamai masu dadi cikin hikima ya taushi Ahmad kafin ya tafi ya barshi,yana musu fatan shiryawa mai ɗorewa. Kaman jira yake yana tafiyah ya koma sashennasa,bai sameta a falon ba,har yaji babu daɗi kaddai tafiya tayi,sai kuma ya gano ƙofar kitchen a buɗe. A kaban kitchen table ɗin take tsaye tana kallon window,ta bawa ƙofar baya. "Can you explain your self please?" Tajishi sarai amma bata juyo ba,wani kukan tasake fashewa dashi har yafi na ɗaxu. "Am sorry am sorry please i....i can't..........."
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...32...
"Am sorry am sorry please i....i can't..........." Bata gama bayanin ba taji ya rungumeta ta baya. "Relax" Shine abinda ya raɗa mata a kunne cikin sanyayyar murya. Rage sautin muryar kukan tafara tana jan zuciya a hankali. "Ki daina wannan kukan ya isa haka,tun ɗazu kikeyi zai iya affecting ɗinki, nasan kina tunanin cewa zan takuraki ne saikin faɗamin dalili,bazanyi hakan ba zan baki lokaci daga nan idan kin kwantar da hankalin ki ki faɗamin gaskiya. Yanzu godiya kawai zanyi ga Allah daya warwaremin matsalata a kusa,Alhamdulillah daya kasance kece." Nagode da fahimtarka da kuma daɗaɗanan kalamanka,Inshaallah zan sanar dakai dalilina nayin hakan,kuma nayi ne saboda lafiyarka tawa da kuma ta ɗana,amma bawai don son rainaba" "Uhm naji,amma duk da haka bazan gamsu ba sainaji mai nene dalilin. Sannan koba komai ni shaidane na kuladani da kikayi da kuma bin hanya mai hatsari wajen ganin kin karemin mutuncina,duk da nasan hadda kishi a lamarin" Ƴar dariya tayi kaɗan a cikin kukan tareda ɗora hannunta akan nasa,daidai lokacin kuma cikinta yayi motsi. Daidai wajen ya ɗora hannunsa tareda sakin ajiya numfashi. "Am sorry for calling you illegal blood.....ƙanin sayyid koh,inada yaro amma bansani ba" Ɗaga masa kai tayi tareda murmushi. "Kayi haƙuri hakan Yazama dolene,nagaji da tsayuwa zan tafi idan na huta in mun sake haɗuwa zan faɗamaka mai yake faruwa,amma kafin sannan dan Allah kada ka faɗawa kowa ni wacece indai ba Neelah ba" "Taya kikasan Neelah?" "Labari mai tsayi" Juyowa yayi da itah tareda share hawayen kan kumatunta. "Dama haka kike da saurin kuka,shine ya ceceki da kuma tunawa danayi halinda kike ciki,amma da sai raina ya baci sosai" "Kaima kanada laifi" Tafaɗa tareda kallon cikin idonsa. "Wanne laifi nayi,saboda nakasa ganeki?" "Ahah ba wannan ba,kafin lokacin da hankalin ka yadawo,na daɗe ina zaune a gefenka tareda jiran ka tashi,amma daka tashi baka tasheni ba sai kawai gani nayi baka nan ka tafi ka barni. Kuma nasan ka ganni a wajen gadonnaka" "Naganki kam,kuma na yarda laifina ne,amma na amshi hukuncina tunda na zauna da matata tsawon lokaci bansan ita bace" Ɗan yin baya tayi zata faɗi ya riqota tareda tambayar miye. "Jiri nake ɗanji ne,barinaje na kwanta" Hannunta take ƙoƙarin cirewa daga nasa,amma yasake riƙota. "Ina zakije barina kaiki ɗaki ki kwanta,kinci abinci ma kuwa?" "Naci saidai inna tashi a bacci na ƙara,ahah ka bari na tafi ɗakinmu,inna zauna anan za'a zargi wani abun,nayi maka alƙawarin zan dawo daga na tashi" "Nikuma banmiki alƙawarin barinki ki tafiba,domin hankalina bazai kwanta ba. Muje ki kwanta kuma anan sashen,bake ba komawa can kin dawo nan. Har sai kin faɗamin dalilin dayasa karna faɗawa kowa ke matata ce" Yana gama faɗin hakan ya cirata sama zuwa ɗakinsa. Tun tana mutsu mutsun ya sauƙeta har tayi shuru ta haƙura. (Ku tashi mafarki ne😀😀😀) _____Tashi tayi daga kan kujerar tareda yin hamma,da Ahmad suka haɗa ido wanda shima itan yake kallo,duk da kafin sannan hankalin sa nakan system ɗin dake gabansa. Tun lokacin daya raka Musbahu ba direct yashigoba ya tsaya yin waya daga wajen aiki,yana shigowa ya sameta tayi bacci a inda suka barta. Ta gaji amma tasan dole zai tambayeta wani abun saboda baƙon lamari dayaji. Shine a cikin wannan yanayij harta samu damar yin bacci? Harda mafarki? Haba no wonder hakan yake mata kaman bashiba,ashe bada gaske bane. "Sannu da tashi" Ya faɗamata yana kallonta. Kunya ce ta kamata ganin abinda tayi. "Kayi haƙuri" Tafaɗa a sanyaye,itama tayi mamakin yin baccinnata yanzu,daga kuka kawai sai bacci. Tashi tayi ta gyara rigar jikinta tareda ɗaukar hijabinta zata tafi. Har ta fara tafiyah taji maganar sa. "Na zauna tsawon awa guda ina jiran ki tashi domin ki faɗamin dalilinki nayin haka,amma daga tashi saiki tafi?" "Zanyi sallah ne nasan lokaci yayi" Ba wani sallah kawai don ta samu excuse ɗin fitane. "Nan sashen baya sallah,ki shiga kiyi sallahr idan kin gama kuma kizo" "To" Tace ba musu tareda nufar ɗakinnasa. Daidai lokacin data idar yashigo ɗakin,a bakin gado ya zauna. "Uhmm fara bayani ina jinki,kince kinada dalilinki wanne daliline?" "Uhmm zaka ɗan iyah bani lokaci kafin........." "Babu wannan maganar,dolene ki faɗamin mai yake faruwa,hajiyah maryam tasan ke matata ce" Ɗaga masa kai tayi da eh. "Sannan nasan itace tace kada ki faɗamin,shiyasa kwanaki tayi barazana dake domin hanani yin bincike akan ta. Kuma itace ta hanaki faɗamin ko?" Tashi yayi a zuciye yana faɗin. "Barina je wajennata na tabbatar tunda ke ta hanaki magana,kuma kaman yanda bataso kowa sai yasan matsayinki a wajena" Jin abinda ya faɗa Sumaimah batasan lokacin data tashi tariqoshi ta baya ba. "Karkaje na roqeqa kada ka rushe abinda muke tsarawa,rayuwar mu na tangal tangal akai. Ba hajiyah maryam bace take aikata abinda kake tunani,hasalima duk duniya idan da wanda bazai cutar dakai ba itace." Juyowa yayi yana yiwa Sumaimah kallon tana da hankali kuwa. "Eh inada hankali kuma nasan mai nake,na roqeka kabi komai a sannu,makashinka na tareda kai amma ba hajiyah Maryam bace" "Taya kike tunanin zan yarda da wannan maganar taki,keda bakisan mai yake faruwa ba" "Saboda ita ɗin......ita ɗin mahaifiyarka ce wacce ta haifeka. Hajiyah Mammah ita ke ƙulla maka komai Tundaga farko. Shugabar kungiyar BC ma da kake nema itace,inada shaidar hakan domin ni jiyau ce ba ganau ba. Nasan lokacin da kake ƙungiyar a matsayin na ɗaya daga cikinsu dan haka tun ranar dana shigo ɗakinnan na farko naga takaddu akan kungiyar,anan nagano kana bincikene akai. Sannan a ranar naci karo da hajiyah Mammah itada mai aikinta sun shigo ta jikin bangon gidannan. Ko lokacin dakuka ci nasara akan BC an ƙira an faɗawa hajiyah Mammah abinda kayi a wajen,wanda yanxu haka babban bincikenta nakan ta gano rayuwar dakayi a bayane. Nasan hakanne saboda aikin baɗɗa kama danake a sashenta. Batun mahaifiyar ka ma hajiyah Maryam duk itace ta rabaku,ta ƙwaceka tun kana jariri a wajenta,Sannan tace idan tafaɗawa duniya kai danta ne saita kasheka........duk wanann bazaka gane ba saina baka labarin mai ya faru. Ta gargaɗeni da kada na faɗamaka,amma ka riga ka gano wacece ni,dan haka banida zabi daya wuce na faɗamaka mai yake faruwa...." Labarin abinda tasani tunda ga zuwanta gidan ta sanar masa har zuwa yanzun. Tun sunayi a tsaye har ta samu waje ta zauna,amma shikam bai zauna ba,ya kafeta da ido tunda tafara har zuwa yanxun,jin abinda take faɗamasa yayi kaman almara,garin ya hakan ya faru amma bai sani ba....... Ya tafi dogon tunani lokacin data gama bashi labarin tayi shuru,sai bayan taci gaba ne tukunna ya dawo da hankalin sa kanta. "Wannan shine dalilina na ƙin faɗamaka ni wacece,amma tsawon wannan lokacin ina cutuwa da rashin sanina da bakayi ba,musamman abinda Mulaifah tayi maka,shiyasa na jefa kaina ba tareda tunanin abinda zai faru ba. Haka ma hajiyah Maryam tana cutuwa da nesanta kanta daga gareka tsawon wannan lokacin,bugu da ƙari ga jinyar da take fama da itah tsawon shekara da shekaru,jiya ma saida aka ƙara mata jini. Jikinta yayi tsanani sosai,abinda hajiyah Mammah take ya kamata a dakatar da itah haka. Takowa yayi a hankali ya zauna a inda take,kana ganinsa kasan jikinsa yayi matuƙar sanyi. Hannunta ya kama tareda riƙewa a cikin nasa. "Shin mai zance dake,kwata kwata ma miyasa ban ɗago ba da ya Musbahu yacemin sunanki Sumaimah,ban taba kawo kece matata danake nema ba shiyasa. Kinyimin abubuwa a rayuwata ta baya,haka ma kinyimin a wannan. Abubuwan da kikayimin bazan taba misaltasu ba,dan haka godiya ma bazata iyah fitowa daga bakina ba,domin tayi kaɗan. Kuɗin matane da samunsu a cikin al'umma zayyi matuƙar wuyah,nagode da kare min mutuncina da kikayi,nagode da karemin mutuncinki da kikayi,nagode da haifamin ɗana na farko duk da bana tareda ke,Sannan na goɗe da ɗaukamin yaro na biyu duk da bana a cikin hankalina da kuma sani. Nayi miki alƙwarin nuna miki so da kuma ƴaƴana,zan nuna musu kulawar da ban basu ba a da. Nagode da shigowarki rayuwatah Sumaimah. Har ma da haƙuri dakikayi dani bansan mai zance ba,nasan ba halina da nagartata ce takai ba da har Allah ya hadani dake babu abinda zan.........." Jijjiga masa kai takeyi ganin maganganunnasa da yawa. "Karka ce haka,ka wuce duk yanda kake tunani a wajena,kai ɗin na dabanne. Koda kana a lokacin baya kana mutunta inna a matsayin mahaifiya,lokacin da banida lafiyah ka tausayamin ka,ka siyamin magani ka sakani a makaranta dana faɗamaka ina so. Sannan da muka shirya kamar sauran ma'aurata kai ɗin namijine wanda yasan yadda zai bi da mace. Ko daren mu na farko ma ba.........." Hannu ta saka a bakinta tareda yin murmushi. Fitar da hannunnata yayi tareda cewa. "Mai nayi a ranar faɗamin" "Ahah bazan faɗaba gaskiya,ka ƙyaleni" Riqota yayi ganin tana ƙoƙarin guduwa. "Ina zakije bazaki faɗamin ba wai?" "To ka sakeni zan faɗamaka" Yana sakinta ta tashi da gudu,tana dariyah. "Bazan faɗa maka ba,kayi zuciya ka tuno,abu ɗaya zaka sani shine .......kaƙi ka tashi kayi wanka da kyar na tasheka" Binta yayi da sauri kafin ya fitah har ta kai bakin ƙofah. Takalar baƙin ƙofah tayi,cikin zafin nama ya tareda kafin takai ƙasa. Numfashi take fitarwa sama sama don ta tsorita sosai. "Habibteee pay attention,kidaina wasa da rayuwarki da kuma na yaron cikinki kinji" Ɗaga masa kai tayi da toh. "Rungumeta yayi,sun daɗe a haka kafin ya ɗagota dayaga hankalin ta ya dawo kanta. Kallon idonta yakeyi cikeda so da kuma kulawa. Itama shiɗin take kallo cikeda so da burgewa. "Kayi haƙuriii!!!" Tafaɗa cikin siririyar murya. "Okay ya wuce amma ki kula nan gaba sosai,muje ki rakani wajen hajiyah maryam ina so nayi magana da itah" "Toh"
SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...33...