Kenza eBookz

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 19

Sanadin caca book 2 complete - Chapter 19

Sanadin caca book 2 complete Chapter 19: Sanadin caca book 2 complete Chapter 19. Sumaimah ce tafara shiga ɗakin,hajiya Maryam na zaune a bakin…

3,188 words

Sumaimah ce tafara shiga ɗakin,hajiya Maryam na zaune a bakin gado,hannunta na riqe da ƙirjinta,sai tari take wanda kana gani kasan wahala take sha. Da gudu ta isa gabanta tareda riqe ɗaya hannunnata, "Hajiya yadai jikinne ko zamu koma asibitinne" "Ahah bazan komaba Sumaimah,kozan koma ma yanzu bazayyi ba,jikina yanzu ya daina regulating baƙon jini,is no more lokaci na yayi haka,ki kulada kanki da kuma mijinki Sumaimah,yanzu na maida komai kanki ina miki fatan ki samu nasara ke. "Ahah dan Allah karki ce haka,zamu samu mafita,nasan abinda yake saka miki wanann matsalar,wannan akwatin nata ne,in muka wargazashi shikenan" Duk abinda suke Ahmad na tsaye yana kallonsu,inda Sumaimah bata bashi labarin abinda ya faru ba da bazai san mai suke faɗa ba. Hajiyah maryam ce ta fara ɗaga ido ta ganshi,sai kuma Sumaimah. A razane da kalleshi,domin tunda take dashi bai taba shigowa ɗakinta ba,maida kallonta tayi ga Sumaimah,tareda alamar biɗar ƙarin bayani.. "Sumaimah mai...,..." "Eh yariga yasan mai yake faruwa,yasan matsayinki da kuma matsayina a wajensa" "Meyasa meyasa kin kuwa san kasadar da kikayi, abubuwan suna tafiyah ba yanda muka tsaraba,the more mutane na shigowa the more hatsarin hakan yana ƙaruwa" Matsowa Ahmad yayi kusada Itah tareda tsugunnawa. Ɗauke kanta tayi idonta yana zubar da hawaye,tayaya ne zata iyah haɗa ido dashi ita kuwa,bayan abinda tamasa da bazai misaltu ba. "Um.....mmeee" Runtse idonta tayi jin kalmar daya kirata da ita,abinda bata taba zato ba a rayuwarta. Ita kanta Sumaimah tayi mamakin furucinnasa sosai. "Shin bazaki amsa ba,wannan shine sunan danake ambaton mahaifiya ta dashi a cikin Addu'a ta,yanzu kuma tunda ga mai sunan a gabana shiyasa na ƙirayeki dashi,shin bazaki amsa ba?" Kuka hajiyah Maryam ta rushe dashi. "Bazan amsa ba bazan iyah ba,bai dace dani ba sam,nagaza nakasa,nayi zaton zan iya amma ashe ba haka bane" "Ke kuwa kika kai ummeee,abinda kikayi ba kowacce uwace zata iya ba,ko a da dabana ganinki a matsayin mahaifiya ta,amma nasan keɗin jajirtacciyar mata ce. Nine na gaza na kasa,da har ban iya kallo soyayyata a idanunki ba,sai yanzu nagane da kinada niyyar cutata da tuni kin cutar dani ina yaro,saidai kullum ki dunga treating ɗina. Dan Allah ki juyo ki kalleni." A hankali take juyo da kanta har suka haɗa ido,da alama bataso hakan ba,amma roqon da ɗannata yake yi mata abune da bazata iyah riqewa ba sam. Kafeshi tayi da ido har sannan bata daina kuka ba,hannayenta takai kan kumatunsa,tamkar tasaka ƙaramin yaro a gabanta. Shafah kumatunsa takeyi wanda rabonta data taba tun yana jinjiri. "Ah...ahhmadd kayi haƙuri ka yafemin,shayarwa iyah na wata biyu kawai nayi maka,girman da yaro yake a gaban mahaifiyarsa duk baka samu ba, saboda wani yankyakykyen hukuncina". Duk kasancewar sa namiji mai dauriya,amma ganinta a gabansa tana roqonsa sai ya tsinci kansa da kasa riqe kansa.. Rungumeta yayi kaman zai shige cikinta inda ya fito,wata soyayyarta ne ke shigarsa Tamkar an jonawa tanki bututun ruwa. Sun daɗe a haka Sumaimah ta zuba musu ido. Hawayen idonta ta share,data tuna cewar itama bata san tata mahaifiyar ba,kuma tasan bazata taba ganinta ba,tunda ta koma ga mahaliccinta. Jikinta ne ya shika,hakanne yasakashi ɗagota domin yaga menene,idonta a rufe tamkar bata numfashi.. Jijjiga ta yakeyi amma shuru,waigawa yayi inda Sumaimah take. "Sumaimah ya zanyi bata motsi fah" "Jinin jikinta ne ya ƙare,inaga muyi gaggawar kaita asibiti yanzu" Tashi tayi shikuma ya ɗauketa irin bridal style ɗinnan suka fitah,tashin hankalin daya shiga ya dade baishiga irin sa ba. A hanyar fita suka haɗu da Maimuna tana magana da Fatee wacce tafito daga motar Saleem sun dawo daga ɗakkota a makaranta. Ganin Ahmad ɗauke da hajiyah Maryam kaman bata numfashi yasaka su sakin baki suna kallonsa. Abu ɗayane yazo ransu shine wani abu ya aikata mata. Saleem ne yasha gabansa cikin bacin rai. "Yah Ahmad mai kayiwa mommy" Kallonsa yakeyi da idanunsa wanda ya kaɗa yayi ja. Ya kasa bude bakinsa balle ya bashi amsa. Ganin hakanne yasa Sumaimah shiga tsakiyar su tace. "Babu abinda yayi mata dama bata da lafiyah,kaita asibiti zamuyi kubiyomu a baya,amma bayan Sameer kada ku faɗawa kowa mai yake faruwa a gidannan" Maganar da Sumaimah tayi ne cikin alamar roqo yasaka Saleem matsawa Ahmad ya wuce da hajiyah Maryam a hannunsa. A gidan baya ya ajiyeta inda Sumaimah tashiga,sai kuma shi ya shiga wajen driver. Sai bayan sun fita daga gidan kafin su Maimuna suka bi bayansu. Asibitin gidan marayunta suka nufah,amma a hanya saida suka ƙira babban likita tukunna,wanda suka yayi mata magani na ƙarshe. Ɗakin karbar mutum na gaggawa aka shiga da itah suna isowa,daidai lokacin kuma su Maimuna suka iso,harda Sameer wanda sukayiwa bayani dama yana kusada wajen. Babu wanda yake magana a cikinsu,amma kana ganinsu kasan suna buƙatar ƙarin bayani. Likitanne yafito daga wajen cikin sauri. "Am duk da jinin ta A+ ne bashida wuyar samun donor,amma kasancewar an daɗe ana bata jini dayawa,yanzu jikinta bazai ƙarba ba sai wanda DNA yayi ɗaya wato jininta" Yana gama bayanin Sameer da Saleem sukabi bayan sa,Sumaimah tana ganin haka ta kalli Ahmad akan yaje. "Kaje mana dan Allah,wataƙila sai naka yafi kamancece niya da nata" Su Maimuna suna jin abinda take faɗa,amma basu fahimce ta ba.. Shiga yayi wajen ɗaukar jinin yabada sample ɗin nasa shima ya fito. Suna nan tsaye bayan an karbi sample ɗin Sumaimah ta riqe kunkuminta,wani irin kamawa taji yayi mata. Duk abinda take Ahmad yana kulada itah,cikin wani ɗaki ya shiga ya ɗauko kujera,wajen babu gun zama,yasan kuma in yace taje wajen zama bazata tafi ba. A gabanta ya ajiye kujerar tareda kama hannayenta ya zaunar da itah. Da mamaki take kallonsa,kenan yasan ta gaji,hakan yayi mata daɗi sosai,amma taji kunya ganin su Saleem suna kallonta. "Yah Ahmad matar wani ce fah kake taba jikinta,yanzu kai......" Wani kallo yayi mata dole ta haɗiye abinda yake bakinta. Wata nurse ta fito da wata takarda a hannunta. "Ana ƙiran Ahmad Aliyu,ka shigo wai naka yafi zama iri ɗaya da nata" "Ohk" Daga haka ta koma ciki. Da Murmushi Sumaimah ta kalleshi wanda shima ita ɗin yake kallo. "Kaga abinda nake faɗamaka koh?" "Uhm nagani,barina shiga kada ki tashi ki tsaya,ki zauna yanzu zan fito. In kina jin kishirwa Saleem ya nemo miki wani abun uhm?" "Uhm naji ka shiga Allah ya taimaka yavata lafiya" Ahmad yana shigewa Fatee ta matso inda Sumaimah take. "Ke bangane ba mai yake faruwane,shine zai bawa mommy jini a wanne dalilin,wani shirin kuke haɗawa saboda ku kasheta koh? Ke kuma mecece alaƙarki dashi kina matar wani,nake ganin kaman ta Allah ashe........." "Ke Fatee miye kike hakane,meyasa duk abinda yazo zuciyarki shi kike faɗane. Mahaifiyarki na ciki batada lafiya amma kin gulma" "To laifinta ka gani,ai dole ta tambaya,nima abin ya ɗauremin kai,miye tsakanin mommy da yah Ahmad da har zai bata jini,wai kuma kuda kuke ƴaƴan ta naku bayyi daidai ba sai nata?" Maimuna ce tayi maganar cikin kasa gane mai yake faruwa. Duk abinda sukeyi babu wanda Sumaimah tasaka baki,da abin yayi yawane ma tace musu waƙa a bakin mai ita tafi daɗi.

Bayan an gama jan jinin an ɗaura mata kafin aka barsu suka shiga. Zuwa lokacin anyi mata allurar bacci. Fatee ce a zaune a gefen kanta sai su Sameer a tsaye,Sumaimah kuma na gefe a zaune. Can kaman an ɗan daɗe ta fara juya kanta kaɗan kaɗan. Fatee da Maimuna ne suka ɗan ɗagota tareda saka mata pillow ganin tana ƙoƙarin tashi. Idonta akan Ahmad ya sauqa wanda shima ita ɗin yake kallo cikeda soyayya irin ta ɗa da mahaifi. Sannu sannu su Sameer suka mata,fatee kam rungumeta tayi tana kuka. "Mommy bakida har haka amma baki faɗamin ba har kwanciya fah kikayi" "Kin damu ki sani ne,miye ya dameki banda kanki uhm" Hajiyah Maryam tafaɗa tana dafa kanta.. "Habadai mommy you know i love you" "Umm naji i love you too,yanxu dai ɗagani bake kaɗai bace a ɗakin koh?" Ƙin matsawa tayi saida ta tureta tukunna,sai turo baki take kaman zai faɗi. "Sannu Ummee jikinnaki yanzu" Ahmad yafaɗa a nutse cikin kulawa. Murmushi tayi tareda ɗaga masa kai. "Ummee ya jikin?" "Alhamdulillah Sumaimah....kinci abinci kuwa?" "Ahah" "Tabb Ahmad ka ɗauketa ku tafi gida taci abinci,batayin awa uku ma bataci ba,cikin jikinta mai neman abincine" "Ahah yau banajin yunwar zan zauna har a sallameki saimu tafi" Cikeda rigima tayi maganar,wanda hakan yasaka hajiyah Maryam haɗa rai. "Ahah ku tafi nima yanzu zan tafi idan jininnan yaƙare,uhm yau kuma a wanne bawan Allah aka ɗauka?" "Mommy yah Ahmad ne yabayar,yaushe kuka shirya dashi da har yabaki jini kuma ya kawoki asibiti,ga waccar mai aikin sai wani kula kike da ita kamar wata mai muhimmanci" "Buge bakin Fatee hajiyah Maryam tayi tareda cewa. "Ƙaniyarki da ce mata ƴar aiki,tunda har kunga ya haka yakamata kusan mai yake faruwa. Ahmad ɗanane na fari kafin na haifi Maimuna,sannan ita kuma matarsa ce wacce ya aureta a lokacin da yayi shekara biyar baya nan. Tanada ɗa mai sunan mahaifin Ahmad kuma yayan babanku wato Muhammad,ana ƙiransa da Sayyid.. (Ta faɗa tana kallon Sumaimah. Wannan suma itan suka kalla cikeda mamaki) Wannan shine abinda baku sani ba,sauran boyayyun labaran kuma sai daga baya. Sannan wannan maganar banaso tabar wajennan,akwai wanda sanin hakan a wajensu daidai yake da shiga hatsari dukkanmu"

∆∆∆

"Sani kuma na nawa Maryam,lallai kin raina wayona da kuma abinda zan iya sosai" Hajiya Mammah ta faɗa wacce take zaune gabanta dauke da ƙwaryah wacce take ganin abinda yake faruwa a ɗakin asibitin.

Muje zuwa..........

SADI-SAKHNA CEH 09035784150 ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.

*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)

Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150

Bismillahir-rahmanir-raheem

Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.

*BOOK 2* ...34...

Ciza yatsa tayi tareda jan hannunta a iska ƙwaryar ta bace. "Ba abinda ta faɗamusu daya danganceni,ita kuma waccar matar Ahmad wacce na daɗe ina nema naganta amma ya ƙi nuna fusakarta har yanzu,saidai neman ta daga baxayyi wahala ba,tunda nagano tana tareda su" Kaltum ce ta kalli hajiyah Mammah tareda cewa. "Meyasa to ba'a ganin fuskarta,da alama wajen da muryar ta ɗaukema sunan ta aka ambata,ko wata shu'umar ce kai itama?" "Ahah ruhinane yayi rauni,kullum hakan zai cigaba d kasancewa idan ba ban kawar da waɗannan mutanen ba" "Ki shirya yau inada meeting,zan ɗora wani a kujerar bello" "Toh amma shugaba ya za'ayi da neman matar shi ........." Wani dariya tayi tareda cewa. "Ki ƙaddara na sameta,tunda har duk yaran gidan da kuma ita kanta Maryam tasan wacece,to samun bazai mun wuyaba,samota kamar nayine" "Gobe zamu koma gida, sannan ina so darennan na kafe ruhin Maryam,ƴaƴan ta su zaba,ko rayuwarta kokuma su rufe wacece matar Ahmad" Wata ƴar tsana ta ɗauko a gefenta, an caccaka allurai a tsakiyar ƙirjinta,ga kuma zarruka an ɗaureta dasu. Zaren tafara ja tana wasu kalamai,lokaci ɗaya ɗakin ya turnuƙe da duhu. Kultum na ganin haka ta fita daga ɗakin da gudu,saboda tasan idan wannan ruhinnata ya fito daga akwatin suka haɗa ido,kwana zatayi tana mafarkin sa. Zagaya ta yakeyi yana wani ƙugi,yayinda itakuma idonta ya rufe tana ta karanto wasu surkulle. Can kaman wani lokaci ta tsaya da abinda take tareda da fara tari har jini yana zuba. Wani rishi ruhinnata tayi wacce kamarsu ɗaya da itah. "Hahahhaha nace miki kin tsufah ki musamu,banda kina aiki da jini domin maida ƙuruciyarki da tuni bazaki kai wannan shekarun kina aiki damuba. Kuma kinsan dokar aiki,duk ranarda kika kasa iyah damu to jininki mallakinmu ne.......uhmmm zayyi daɗi kuwa,munasan gubataccen jini ahhhhhhhh" Tana cikin maganganunnata mai kamada raɗa hajiyah Mammah ta daka mata tsawa. "Ƙarya kike,banga ranar da zaki fi ƙarfina ba,ke baiwata ce kaman yanda dodo ya bani saboda ki yimin aiki. Dolene saina gama cika burina,sai na gama ɗaukar dukkan fansana tassss" Tana faɗin hakan ta ɗakko wata kwalba a cikin akwatin,ja ce wani abu yana juyawa a cikin ta yana walwali. Baki ta saka ta zuqo abun zuwa cikinta. Lumshe ido tayi jin ƙarfin dayabi jikinta. Buɗe ido tayi jajaye dasu suna fesar da wani jan haske. "Yanzu na umarceki daki je ki riƙemin Maryam,ruhinta nake so yakasa sukuni a jikinta sam" "Ahhhhhh ruhinki ya amshi buƙatarki kuma zai cika" Tana gama faɗin hakan ta bace a iska, Sauƙe ajiyar zuciya hajiyah Mammah tayi tana kallon kwalbar da take hannunta. "Ina so na kasheki,amma saina samu wanda zan cigaba da zuqar jininsa tukunna. Yanzu dolene ki kasance a wannan halin har sai nagama da wannan yarinyar tukunna." Maida kwalbar tayi cikin akwatin kana ta maidashi cikin ƙarƙashin gadonta ba tareda ta rufe ba,saboda wanda take rufewa a cikin akwatin baya ciki.

∆∆∆

Bayan gama bayanin tashi Ahmad yayi akan zai mayar Fatee da Sumaimah gida,in yaso gobe saisu dawo. Sun fita kenan sukaji hajiyah Maryam tafara jijjiga kamar zata karya gadon da take kai.. A rikice dukka suka juyah kanta tareda da daddane sassan jikinta.. Sukam su Fatee kuka suka fashe dashi ganin abinda takeyi. Jini ne yake fita ta hancinta,yayin idonta kuma ya koma fari soll kamar ba'a taba halittar ƙwaya daga cikinsa ba. Ahmad ne yayi ƙarfin halin yin magana a wajen, sauran daga mai kuka sai wanda yayi suman tsaye. "Saleem maza ƙira likita yanzunnan" To yace cikin karyayyiyar murya ya fita. Tun kusan magriba suke abu ɗaya har dare ya fara. Mazanne sukaje sallah,matan kuma anan gidan marayun sukayi sallah,an basu abinci ma amma babu bakin ci. Bayan sun dawo daga masallacin wata mota suka gani ta shigo wajen baƙa. A.M Aliyu ne ya fito daga cikin motar a razane zuwa cikin asibitin. Ahmad ne ya kalli su Sameer. "Waye ya sanar dashi,yaushe ya dawo garin?" "Bansan yaushe ya dawo ba,amma ai dole dama zai san mai yake faruwa ba,abin yayi zafi sosai wanda da alama sai an fita da itah wata ƙasar" "Uhm uhm ba abinda ya shafi wata ƙasar bane,da sannu zamu samu mafita" Karisawa sukayi inda yake,yana ganinsu yazo inda suke da sauri,in mutum ya ganshi bazaice shine dakyakykyen sojan nan ba,lallai ba ƙaramin so yakewa hajiyah maryam ɗin ba. Hannun Saleem ya kama tareda cewa. "A ina aka kwantar da itan,ya jikinnata. Fatee tace wai ta daɗe batada lafiya ana ƙaramata jini,yaune yayi tsanani sosai" Ganin yanda yake maganar a gigice ne yasa Ahmad jijjiga kai,wato Fatee ce ta faɗamasa mai yake faruwa,duk da an hanata,this thing is no more secret,dolene su ɗau matakinsa da wuri. Abin tsoronsa ɗaya wacce ake tsoron da sani tariga ta sani,abin sauƙin ɗaya batasan sunsan wacece ita ba. "Eh batada lafiyah Abbah,ɗazu kam da sauƙi har tayi magana,daga baya abin ya rikice sosai,amma dai likitoci suna kanta domin yin nasu ƙoƙarin" "Tun ɗazun jikin ya rikice amma ba'a sanja asibiti ba,mai yasama aka kawota wannnan wajen,yakama ta in fitane ma an fara shirye shirye zuwa yanzun" "Itace batason zuwa wani asibitin,saboda batason asan batada lafiyah,Sannan da alama jinyarta kaman bai shafi asibiti kaɗai ba,hadda na musulunci za'a haɗa,wato islamic medicine" "Eh to sai ayi ai dukka,yanzu dai barinaje naga jikinnata" Yana gama faɗin hakan ya nufi cikin asibitin,waya ya ɗauko daga cikin aljihunsa,jin ya ambaci sunan Mammah yasa Ahmad runtse ido tareda barin wajen. Shikenan is no more sceret,duk da yasan tasan dama mai yake faruwa. "Salam Mammah muna asibiti ashe maryam ce badata lafiyah,nima dawowata garin kenan nasani......eh ba lallai ki sani ba wai bataso a sanine........ya kawoki wannan gidan marayun data gina anan aka kwantar da itan. Eh shi to shikenan Allah ya kawoki lafiyah" Daidai ya isa wajen da su Fatee suke ya kashe wayar,duk sunji abinda ya faɗa. Zaro ido Sumaimah tayi tareda haɗiyar yawu,batason ko yaya hajiyah Mammah tazo ta sameta a wajennan. Tashi tayi ta gyara mayafinta kana ta kalli su Fatee. "Anty Maimuna ni zan koma gida naji cikina yana........." "Ahh dama yakamata ki koma gida,kar hakan zaman ya miki illah gaki bake ɗaya ba,kije gida kici abinci ki hutah" "Tom barina leƙata kafin na tafi,dan Allah idan hajiyah Mammah tazo karkuyi mata zance nah please" Murmushi Fatee tayi tareda cewa. "Karki damu matar bro bazamu ce komai ba,dama mai kamata kowa ya saniba sai mommy ta warke muyi miki official introduction,kina kirki kin dace da yah Ahmad,Allah ya barku tare" "Ameen ya Allah nagode,Allah ya bawa ummee lafiya ya tashi kafaɗunta" "Ameen ya Allah" Fatee tafaɗa cikin rawar murya tana shirin kuka. Tashi tayi zuwa wajen windown da take ciki. An bar A.M Aliyu ya shiga inda taken,har sannan jijjiga takeyi,kodaga nesa ka gani kasan tana jin jiki sosai. Hawayen idonta tashare tareda cewa. "You are not deserve this,Allah ya baki lafiyah ya saka miki. Da sannu sai taga sakayya akan abinda takeyimiki......ina miki fatan samun sauƙi" Sakin ƙarfen windown tayi tabar wajen. Inda su Sameer suke ta nufah,Ahmad baya wajen. "Saleem ina Ahmad yayi?" Ta tambaya cikin ƙaramar muryah. "Yaje yin wayah ne yanzu,gashi can" Ya nuna mata ɗan gefensu kaɗan. Ɗaga kai tayi tareda nufar inda yake,daidai lokacin ya gama wayar,kansa ya ɗora akan saman motarsa yayi shuru. Cikeda tausayawa take kallonsa, a yau yagane matsayinta a wajensa,a yau kuma yake ganin kamar zai rasata,ganinta cikin wannan hali ma abune da duk wani ɗa sai yayi da gaske ya daure. Takawa tayi a hankali zuwa bayansa,hannunta tasaka ta saqalo ta bayansa kana ta ɗora kanta a bayannasa. Shuru sukayi na wasu mintunan kafin ya ɗaro nasa hannun akan nata. "Lafiyah kike,kin gaji koh,ko yunwa kikeji,yanzu nake shirin tafiya neme muku wani abun" "Ahah ba wannan bane,inason tafiya ne kafin hajiya Mammah ta tarar ni a nan wajen.....bayan haka ƙalau nake,kaifah ykk nasan kana cikin damuwa,amma ka daure ka jure. Kowanne tsanani yana tareda sauƙi. Sannan bawa bazai zama mai miƙa lamuransa ga Allah ba face ya jarrabeshi da gurare da dama. Idan ka jure kaci sai komai yazo da sauƙi" "Uhm naji bayaninki,nagode da samunki. da Sannu zan cigaba da yimata addu'ar samun lafiyah,itakuma da take ba daidai ba Allah ya yi maganinta." "Ameen ya Allah" "Muje na saukeki a gida" Hannayenta ya kama ya buɗe mata motar ta shiga kafin ya zagaya ɗaya bangaren. Tafiyah suke babu wanda yake cewa komai,kawai hannun ta yakama yana tuƙin,ɗan Murmushi tayi,dan ya kula yanason kama hannunnata.

Sun barin wajen driver ya kawo hajiyah Mammah itada Kultum,lokacin tara na dare yayi. Ta ɗau wani glass tasaka,tana tattakawa a hankali. Hannun A.M Aliyu yakama suka shiga inda take. Tana ganin halinda hajiyah Maryam take ta fashe da kuka tana gogewa da gefen zaninta. "Allah sarki baiwar Allah,wannan wacce irin wahala ce haka kika gamu da itah ƴar nan?" "Wlh nima Mammah bansani ba sai yanzu,a she ciwon yaci ya yacinyeta. Naso ma fita da itah,amma su yaran sun ce yakamata ayi na islamic ma,saboda abin yana kama da kamun aljanu" "Eh to hakane kam kace wani abun,amma kasan fah akwai wani lokacin da ciwukan zamani sai kaga kaman na aljanu,sai anke asibiti kaga ashe zallan kamen ciwone" "Wasu kam suna zuwa da haka,abinda yasa na yarda da maganar su likitocin munyi magana dasu,sunce wai basuga komai ba a jikinta,ko ɗagawar da kirjinta yake sunce basuga komai ba." "Hasbunallah,shikenan sai a yi na musuluncin,akwai wani malami zanyi masa magana akan matsalar" "Hakan ma yayi,Allah ya bata lafiyan ya tashi kafaɗunta" A.M Aliyu ya faɗa cikin damuwa. Kallonsa hajiyah Mammah tayi tareda cewa ameen cikin ƙasan maƙoshinta.

∆∆∆

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull