Sanadin caca book 2 complete - Chapter 20
Sanadin caca book 2 complete Chapter 20: Sanadin caca book 2 complete Chapter 20. A bakin get Ahmad ya sauƙe Sumaimah,bayan yabata nata abincin,yaso rakata…
3,154 words
A bakin get Ahmad ya sauƙe Sumaimah,bayan yabata nata abincin,yaso rakata har sashensa,dan shi a son ransa yafison ta kwana a can, amma taƙi yarda,haka yayi mata sallama ya juyah. Sashensu ta nufah,ummi da inna ladiyo sunata hira sun kunna fitila kasancewar sannan aka ɗauke wutah,ba a kunna generator ba. Sallama tayi tashiga ɗakin,shuru sukayi suna kallonta,ganin yadda take tafiyah kaman an yi mata mutuwa. "Ke kuma daga ina haka tun rana,kikaje kika ɗebo damuwa?" Zama tayi tareda ɗora kanta a kan cinyar inna ladiyo. "Inna ciwon hajiyah Maryam ya tashi,wannan karon har yafi nada,inna bakiga ba kaman bazata waye safiyar gobe ba,duk da rai da mutuwa na hannun Allah" Hannunta ta ɗora akan Sumaimah tareda jan numfashi. "Tana ganin jarabawa kam a gun matar can,amma in Allah yasa da sauran kwananta sai kiga komai yazo da sauƙi. Ki kwantar da hankalin ki,Inshaallah zata samu sauƙi" Da haka inna ladiyo ta lallami Sumaimah taci abincin ta tazo dashi,hankalin ta kuma ya ɗan kwanta ba kaman nada ba.. Dare ya fara kowa ya kwanta,amma Sumaimah gabaɗaya ta kasa bacci,sai juye juye take,tunowa da wani abu tayi. Zumbur ta tashi Zaune tareda saka mayafinta. Lallabawa tayi a hankali ta bude ɗakinnasu saboda karsu ummi su jita. Ko tsoro bataji ba haka ta nufi sashen hajiyah Mammah ga duhu. Tafiyah take kaman wata mai shiga ɗakin fatalwa jikinta yana rawa,amma taurin kai ya hanata juyawa da baya.
SADI-SAKHNA ce 09035784150
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...35...
Motsi kaɗan taji saita haska,kuma dayake tasaka hakan a ranta har muryoyi takeji suna amsa mata kuwwa. Key ɗin falon ta ɗakko,dan dama tana dashi saboda tana yi mata aiki. Abinda zai bata cikas shiga ɗakin hajiya Mammah ne,wanda batasan yana buɗe ba kokuma a rufe. Murɗa ƙofar tayi,amma wannan kam babu zancen zai buɗe a lokacin. Hankalin ta ya tafi wajen buɗe ƙofar,bata tsammata ba sai muryar Mulaifah taji a bayanta. "Ke kuma mai kike anan wajen da wannan daren" Cikin alamar maye take maganar tana tangaɗi,kana ganinta kasan ta hau air. Ganin hakanne yasa Sumaimah wata dabarar ta faɗo mata. Gyara fuskarta tayi alamar damuwa kafin tace. "Am dama hajiyah Mammah ce tace na gyara mata ɗaki,to kuma na manta ne sai yanzu nazo,gashi bata nan banaso tazo taga ban gyaraba" "To kuma gyaranne zakiyi shi yanzu,ina Mamman taje ta?" "Dare bayyi bafah sosai bakya ganine,ita kuma taje asibitine hajiyah Maryam batada lafiyah. Dan Allah kozaki buɗemin na gyara mata,yanzunnan zan gama" Shuru tayi kaman mai tafiyah tunani kafin ta gyara tsayuwarta. "Uhm banida key ɗinta,amma nasan tana ajiyewa a Drawer tv stand dinta,amma fah ba ruwana in kika ɗauka,don ta hana" Tafaɗa tana saka hannun ta a baki,kana ganinta kaga marar hankali. Murmushi Sumaimah tayi jin barin zancen da Mulaifah take,kai dole ace giya haramunce,Sannan tana saka mutum yin komai da aka hana. Bayan ta shige ɗakinta wajen data kwantanta mata ta nufah. Cikin sa'a kuwa saiga key ɗin,guda uku ne saida ta gwada dukkansu kafin ta samu wanda ya shiga. Ɗakin duhune ƙirin,baka ganin komai,ga batada wayah bare ta haska. "Kince zaki gyara ɗaki amma bakida haske a hannunki,ga fitila ki gyara mata kizo ki fitah,dan bawani sonki nake ba kinsani. Ohhh" Tana cikin maganar tasaki amai a ɗakin. Matsawa gefe Sumaimah tayi tana kallonta,itah harta manta tana gidan ma,rabonta data shigo gidan ta kusa wata uku,yau mai ya dawo da itah oho. Ga nan cikin jikinta ya fito sosai. Miƙowa Sumaimah fitilar tayi tareda yin Murmushin masu shaye shaye. "Ahhh abinka da mai ciki tana shaye shaye,so nake ba ya mutu kar yazo da rai,banason haifarsa ko kaɗan" Taƙarisa maganar tana jijjiga hannunta alamar ahah. Karbar fitilar Sumaimah tayi ta koma gefe tana kallonta,duk rayuwar data tsinci kanta taji tausayin kanta,amma wannan ta damata ta cinye akan wacce za'a tausayawa. Bayan ta gama magangunun ta fita jan ajiyar zuciya Sumaimah tayi tareda rufe ƙofar. Dube dube takeyi ko zata samu wani abu daya sabawa hankalin ta a ɗakin,amma bata gani ba har ta shafe wasu mintuna. "Wayyo Allah nah shin ina take ajiye abubuwan ta ne? Ohh ƙarƙashin gado,anan naga wannan fatalwar ta fito" Tsugunnawa tayi ta leƙa ƙarshin gadon,har nishi take saboda girman da cikinta ya fara. Ido biyu tayi da akwatin,batayi wani tunanin ba ta jawoshi waje. A buɗe yake sai wasu kwalabe guda biyu a ciki. Ɗayar a bude take ba komai a ciki,sai kuma ɗayar da wani jan abu a ciki. Ɗaga su tayi a hannunta tana kallo. "Wannan kuma mai nene,ya nagansu a buɗe,ina abin cikin?" Motsin mutum taji,ga fitilar da Mulaifah ta bata tana ta rawa,itama kuma jikinta yana rawa. Dan muryar kaltum babu makawa taji,mai ya dawo da itah yanzu. Bakin ƙofar tazo a garin tafiyah tayi tuntube kwalbar hannunta guda ɗaya ta faɗi,taji fashewarta kuma a lokaci guda ta taka bata saniba. Zafine ya ziyarci ƙafartata har cikin kanta,bata tsaya duba ciwon ba ta fito daga ɗakin,daidai lokacin da kaltum tashige ɗakinta,hakanne yabawa Sumaimah damar ficewa daga sashen. Muryar Kultum taji tana fadin. "Waye anan,Mulaifah kece?" Gudu Sumaimah ta fara jin Kultum ta biyo bayanta,wani lungu ta shiga da wasu fulawowi a wajen. Ban nishi babu abinda takeyi,tana cikin wannan halin aka kawo wuta wajen ya ɗau haske,Allah ya taimaketa Kultum ɗin ta wuce. Kwalbar da take hannunta da kallah,sai yanzu ta gane ainihin kalarta,baƙace samanta a tsuke. Wani baƙin zarene a cikinta an cika shi tamm. Zarewa takeyi tana zubarwa har saida ta cireshi tass tukunna ta mayar kwalbar ta rufe ta nufi sashensu.
___A bangaren Kultum kuwa ganin tabiyo sawu bataga komai yasa ta koma,a hanyar juyawar tata aka kawo haske. Jini tagani ya tako tun daga cikin ɗakin hajiyah Mammah zuwa waje,zaro ido tayi tareda shiga ɗakin da gudu. "Yau waye ya shigo sashennan?" Shine abinda ta faɗa a razane,musamman da taga akwatin da yafi rayuwar hajiyah Mammah kanta daraja a ƙasa a buɗe,hannu ta ɗora a ƙirjinta ta dafe. "Nashiga uku waye ya shigo cikin ɗakinnan haka" Waya ta ɗauka hannunta har rawa yakeyi ta ƙira hajiyah Mammah. "Hajiyah hajiyah akwai babbar matsala fah,wani ya shigo ɗakinki ya buɗe akwatinki na ƙarƙashin gado" "Akwati kuma dama a bude na barshi,waye yasamu key ɗin dakina,babu wanda ya sani banda Mulaifah,ita kuma batasan inda na saka akwatin ba" "Hajiyah babu komai a cikin akwatin,sai wata fashashshiyar kwalbar an takata ɗakin duk jini" "What jini kuma? Ganin nan dawowa yanzunnan,akwai kwalba biyu a ciki ina suke?" "Ga ɗaya mai zan abu ta fashe,ɗaya kuma bata nan" "Wayyo nashiga uku,ganin nan dawowa yanzunnan driver zai dawo dani a darennan,amma ba Mulaifah bace tayi?" "Ba ita bace,tana bacci a ɗakinta, wani ne fah ya shigo,na bishi ma yagudu ɗazu" "Kuma mai kike da kika daina binsa,koma waye sai ya karbi hukuncin lalatamin shirina na tsawon shekara da shakeru,ganin zuwa idan wanda ya ɗauka ya lalata kwalbar ko wanne lokaci hajiyah maryam zata iyah tashi" "Mammah keda waye kike magana haka naji hankalin ki a tashe?" Maimuna ta tambayeta ganin yanda take haɗa gumi,itah mai sunan tazo wajen jinya amma gabaɗaya hankalin ta na wani wajen daban.. "Inason komawa gidane yanzunnan ƴar nan,an samu matsala,ciwon zuciya na ya tashi,dama yakan yimin idan naga mai jinya. Ko zaku kulada itah kafin......." Lahh karki damu Mammah kije gidan kawai,sha ɗaya tayi bazan iya tuƙin dare ba,amma bari na faɗawa Saleem ya maidaki gida" Godiya ta dungayiwa Maimuna har tagama ƙiran Saleem ya kaita gidan. Shiga tayi wajen hajiyah Maryam wacce akayi wa allurar bacci tana kwance tamkar gawa,kuka tayi a gunnata da kuma wasu surutai kafin ta fito suka tafi.. Sai sannu suke jeramata tana saiƙe nishi ɗaɗɗaya.. Har bakin sashenta Saleem ya rakota kafin ya wuce nasu part ɗin,dama jini ya bata masa kaya daya taimakawa likita wajen sakama hajiya Maryam na'urar iska. Tana ganin yabar wajen ta jefar da gyalen jikinta tareda miƙewa tsaye. Kultum wacce ke falon a tsaye sai ganin tayi kamar an jefo ta ciki. Hancinta ta ɗaga sama ta shaƙi iskar ɗakin kafin ta buɗe ido.. "Koma wacece zata gane kuranta,abinda ta ɗauka yafi ƙarfin sata" "To amma hajiyah wannan data fasa babu komai,Sannan wacce ta tafi da itah inta fasata fah itama" "Wacce ta fashe aikin dana yiwa Maryam ne,a yanzu bazan ƙara amfani da jininta na dawo da ƙuruciyata ba,Sannan ina buƙatar ƙarin ƙarfi da gaggawa,domin idan wani abu yafaru da kwalbar Harsheelah nasan kaina zata dawo,domin kullum burinta shine taga raunina" Buɗe hannunta tayi a iska saiga wani ƙoƙo a cikeda jini ya bayyana. Jinin da Sumaimah ta yanku a tsakiyar ɗakin ta dandala kana ta ɗiga a cikin na ƙoƙon. Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara zaro mata bayi kamar rediyo.. "Macee macecee da ciki a jikinta,itaceeee wacce ta kasance masomin alƙadarinki,surukar gidannan ta wannan da'rar mai samun nasara akanki idan baki kawarta ba, Sannan kuma itama jinin gidannan ce" "Me.....me kike faɗi Matiful duluk. ......wacce matar kenan badai matar Ahmad ba danake nema ruwa a jallo,dama tana gidannan ne? Kuma jinin gidannan ce ta yaya kenan?" "Hhhhhh aiki ya ganki uwar gijiyar Harsheelah,dolene ki dage in kinason cigaba da aiki da dodo,idan ba haka ba ƙarshenki ne kema yazo kamar yanda na wanda suka wanzu kafinki ya wuce" Ganin sun fara mata dariyar ƙeta ne yasa ta kawar da ƙoƙon ,domin bashine a gabanta ba yanzu. "Kultum ƙiramin Mulaifah inason in tambayeta,nasan dole tasan wanda ya shigo ɗakina tunda har ya samu makullina" "Amma hajiyah da alama tayi shaye shaye yauma,ba lallai tah.........." "Ban tambayeki yin ja'inja dani ba,babu ruwana da shaye shayenta,inta kama zan zaqulo duk abinda ke cikinta ciki kuwa harda shegen ɗan da ya baje koli a mahaifarta idan zan samu amsata. Mtsw matsama kiga naje da kaina" Bangaje Kultum tayi ta nufi ɗakin Mulaifah,tana kwance tayi ɗaɗɗayah,ko takalminta bata cire ba. Hajiyah Mammah na zuwa ta nuna hancinta wani hayaƙi ya fita,aikuwa cikin firgici Mulaifah ta tashi ta zauna tana sosa hanci da atishawa. "Maza faɗamin wa kika faɗawa inda key ɗin ɗakina yake?" Ganin wacce take gabanta kamar kakar tata amma kuma tafita yarinta yasa ta murza ido. "Mtsw saida Sport G yacemin dama zanga abinda hankalina bazai ɗauka ba,amma hadda zafi a hanci kaiii" "Dallah ki ware kokuma namiki abinda yafi na hanci,don tsabar rashin sanin daidai kinada ciki kike shaye shaye koh,in kika mutu ai ke kika sani,na rasa uwarki ma ballantana ke. Ki faɗamin akan shashancinki wa kika bawa bayani ya shiga ɗakina?" "Uhm na'am ni.....bansani ba iya kawai gyara tace zata miki na kaya shiyasa nace ta shiga amma ni baruwana. Saboda ta gama miki da wuri har na bata fitila. Saboda kullum kina cewa na zama mai kirki" "Wacece itah baki santa bane?" "Nasanta mana,wai granny mai ya shiga kankine,na ganki ma kaman wata sa'a ta fahhhh" Wani wawan hawa hajiyah Mammah tayiwa gadon Mulaifah tareda cafkar wuyanta. "Faɗamin wacece ita,kokuma na ƙarisaki yanzunnan,matacciyah kawai" "Wayyo Sumaimah,Sumaimah cefah mai laifina danna barta tashiga ɗakinki,naga dai tanayimiki aiki sosai" Sakin wuyan Sumaimah hajiyah Mammah tayi tareda daskarewa a wajen,meyasa ma bata taba zarginta ba duk zamanta a gidan. Kenan.......kenan......mijinnata wato Ahmad ne,kenan itace matarsa daya aura a rayuwarsa ta shekara biyar.......jinin mace mai ciki Matiful duluk ya faɗa,kuma tanada ciki.....kenan tasan mai nake ƙulllawa tsawon wannan lokacin,kallon ayaba kawai takeyi mata. Wata dariyar takaici hajiyah Mammah tasaki lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai ƙaman hadarin marka marka mai shirin zubar da ruwa........
SADI-SAKHNA ce 09035784150
*SANADIN CACA* -BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA* 09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2* ...36...
Bayan ta dawo daga sashen hajiyah Mammah banɗaki ta wuce,anan taga ciwon dataji da kwalbar data fashe,tafin kafarta ne ta dama ya tsage, Wankewa tayi ta ɗaure wajen kafin tazo ta kwanta,ɗaya kwalbar kuma dagata tayi tana kallonta. "Ko itama na fasata kaman yanda ɗayar ta fashe kai?. Ahah idan na fasata kuma wani abun ya shafeni fah?" Ruwa ta tara a cikin roba ta karanta ayoyin karya sihiri a ciki,bude kwalbar tayi ta juye ruwan a ciki ta rufe. "Bansani ba kozai karya abinda yake ciki ko ahah,amma Allah ina roqonka Allah yasa yayi aiki" Ajiyewa kwalbar tayi a cikin kayanta kafin ta kwanta. Bayan ta kwanta ta daɗe bacci bai ɗauketa ba,shin abinda tayi daidaine kokuma saka kanta tayi a haɗari. Rufe idonta keda wuyah taji wata iska ta zagayeta,da guguwa ta taho amma ƙarfinta ya ragu kafin ta iso gareta, tana gudu haka ta ɗauketa zuwa wani waje mai duhu. Buɗe idanunta tayi daga mafarkin,saidai sabanin ɗakinsu a wani waje ta tsinci kanta mai matuƙar duhu,dagane ba ɗakinsu bane saboda jin tana kwancene rairayi. Hannunta takai kan cikinta,yana nan babu abinda ya sameshi. Tasbihi da fara da salati duk wanda ya samu zuwa bakinta. A haka tana wannan halin har haske yafara fitowa da gabas. Tunda ta tsinci kanta a wajen take zaune bata motsaba har zuwa wannan lokacin. Motsin takun mutum tajiyo yana zuwa,ɗauke numfashinta tayi har zuwa lokacin da aka dalleta da wani abu mai haske. "Hmmm wai dama kece ashe? Kinyi wasanki yanda ya dace,amma bari kiga naki ƙarshen yanzunnan" Kultum ce take maganar cikeda jin haushin Sumaimah. Jin wanda yake magana maimakon taji tsoro sai maida martani da tayi. "Kinyi mamaki ne da kikaganice,zatonku ku kaɗai kuka iya shiri,komin ƙanƙantar allura ƙarfece,dan haka ba abar rainawa bace kuma akan iyalina babu abinda bazanyi ba. Ganin baku kasheni ba duk da kunsan ni wacece to aikin danayi a sashennata ita shugabar taki yayi mata illah sosai koh?" Wani mari Kultum ta bawa Sumaimah mai ƙarfi. "Hmmmm zatonki dan kinyi wannan ke wata shegiya ce,jira tazo tasameki kiga yanda zata gama da ahalin da kike komai dominsun. Ke kuma zakiga baƙar wahalar da zaki sha kafin mutuwarki" Dunƙule hannunta tayi tareda faɗin wata kalma,nan da nan wani tururi ya kunnu a dukkan ilahirin jikin Sumaimah,tana jin zafin kuwa ta fasa wani ihu mai cikeda ban tausayi.
A asibiti kuwa hajiyah Mammah na tafiyah Ahmad ya shigo asibitin. Anan suka kwana a wajen hajiyah Maryam ɗin har gari ya waye. Har zuwa lokacin hajiyah Maryam bata tashiba,sai kace matacciyah haka take. Ƙarfin allurar ya ƙare yaci ta tashi amma har yanzu shuru. A.M Aliyu ne ya kwana a kujerar da take gabanta,iyah dare ɗaya amma damuwar da take fuskarsa bazata misaltu ba. Su Sameer Ahmad da Maimuna suna tsaye a gefe guda,babu mai cewa komai kowa da abinda yake sakawa. Sallama akayi a ƙofar shigowa ɗakin,Saleem ne ɗauke da kayan karyawa,sai kuma su inna larai itada Hajiya Shukurah. Gaishe gaishe akayi na kwanan mai jiki. "Gashi wannan inji inna ladiyo wai na Sumaimah ne,itace mai san ɗanwake" Ya faɗa yana ajiye wata ƙaramar coolar a gefe. "Sumaimah kuma,jiya fah yah Ahmad ya maidata gida,ko ba gida ka mayarta ba kai?" Fatee ta faɗa cikeda mamaki tana kallon Ahmad. Shima da mamakin yace. "Gida na mayar ta mana,saida ta shiga ma kafin na wuce" "Eh ta koma gida,amma inna ladiyo tace wai bayan sun gama fira sun kwanta,data tashi ƙarfe biyun dare bata kanta ba. Tayi zaton ko tana wajenka shiyasa bata nemeta ba" "Nida ban kwana a gidaba taya za'ace tana wajena,Sannan side ɗina ma a kulle yake,kuma batada key ɗin wajen yanzu. To ina taje kenan?" Ahmad yayi tambayar a razane. Kowa hankalin sa ne yadawo kan wannan sabon lamarin,kafin kace me Ahmad yafice da gudu daga ɗakin. Saleem ne yabi bayansa suke tada mota zuwa gidan. A ƙanƙanin lokaci suka isa,tareda security na gidan aka shiga nemanta,amma babu ita babu labarin ta a gidan. Don ba kowa a gidan daga su inna ladiyo itada ummi sai kuma hajiyah Mammah wacce a cewarta ta kwana batada lafiya ciwon zuciyarta ya tashi. Wasa wasa har dare babu Sumaimah babu alamarta,ga hajiyah Maryam ma har yanxu bata motsi,saidai ta buɗe idonta tana kallon sama kawai,daga haka babu abinda takeyi. Yanda sukaga rana haka suka dare aka waye,kowa in ka ganshi kaman ya tashi a jinya saboda tashin hankali. Ganin sun raba kansu a asibiti da kuma gida ga ciwon hajiyah Maryam an tabbatar musu bana asibiti bane,hakan yasa suka dawo da ita gida aka malamin da zai mata na islamic. Suna dawowa gidan da safe sai gashi yazo,yasha manyan kayansa wai hajiyah Mammah ce tayi masa Magana akan zai fara mata magani. Maimuna ce da Fatee kawai a gidan saisu inna,sauran mazan dukka basanan suna wajen case ɗin neman Sumaimah,wanda aka watsa a media ma amma har yanzu babu takaimaiman labarin ta.. A zaune yake ya zurawa waje ɗaya ido,bai taba sanin haka take a cikin ransa ba sai yanzu,bai san wanne irin so mai zurfi yake mata ba sai yanzun,gaba ɗaya nutsuwarsa bata tareda shi saboda batannata. Wayarsa ya ɗauka ya danna ƙiran Maimuna,don itace mai kulada hajiyah Maryam ɗin. "Hello y kuke ya jikinnata,ta farka ne?" "Ahah bata farka ba har yanxu,mai maganin da aka turo ma yazo ya fara yimata" "Waye kuma ya turo mai magani?" "Hajiyah Mammah ce mana,dama tun a asibiti da Likitoci suka ce ayi na gida tace zata nemo mai magani" "What mai magani daga wajenta,ganinan zuwa yanxunnan,zan taho da mai maganin,munyi magana dama dashi. Ki tabbatar baki bar mutuminnan shikaɗai da ita ba,Sannan kada ki kuskura ki bari ya tabata har sai nazo tukunna" Cikeda mamaki ta amsa masa da toh. Yana kashe wayarsa ya ɗau key ɗin motarsa zuwa gidan. Kaman yanda yace Maimuna jansa tayi da wani abun har ya iso gidan. Suna zaune an saka masa shayi yana sha,ga babbar riga yasaka ƙatuwa. Jiran gwashin dayace a kawo yakeyi,wanda Maimuna ta ɗau lokaci da gangan tana kawowa.. Da sauri Ahmad yashigo cikin ɗakin,wanda saida ya razana malamin. "Kai waye ya aikoka?" "Uhm ni malamin sayyada ne kakarka,tana ɗaukar karatu a wajena,to har aikin maganin aljanu ma nakanyi sosai,shine tace surukarta batada lafiyah nazo naga abinda zan iya yi akai" Ya ƙarisa maganar yana Murmushi. "Kaine malamin,a ina ka zama Zambilu? Garin ya takasa gane mai kake aikatawa har ta kawoka kayi wa wata maganin aljanu?" Zumbur yayi ya tashi da suka haɗa ido da malam Hadi,wanda Ahmad ya taho dashi. Tsakaninsu kar tasan kar ne,dan zambilu riƙaƙƙen ɗan tsubbune mai aiki da aljanu sosai. Malamai sunsha haɗa ire irensu suyi musu wa'azi amma abu ya faskara. "A ina kuka haɗu da itah harta aikoka kayiwa wata magani?" Ahmad ne ya tambayeshi cikin kakkausar muryah. "Iyee kunga tunda abin yazama haka inaga na manta gidan daya kamata nazo ne,sai anjimanku ni nayi nan" Yazo da sauri zai wuce ta bakin ƙofah Ahmad ya tareshi. "Malam zamu tafi dashi headquater,kai kuma ga nan Maimuna zata taimaka maka ku fara aikin" "To shikenan mashaallah Allah yabamu ikon yin nasara" Ahmad yana gama magana ya danƙi hannun Zambilu zuwa waje,kana ganin riƙon da yayi masa kasan babu mutunci a lamarin.