Sanadin labarina complete novel - Chapter 15
Sanadin labarina complete novel Chapter 15: Sanadin labarina complete novel Chapter 15. ***Idan tace ta san lokacin da bacci ya dauke ta, tayi karya, bacci…
4,485 words
***Idan tace ta san lokacin da bacci ya dauke ta, tayi karya, bacci tayi sosai irin wanda ta dade bata yi irin sa ba. Bangaren Tariq din ma haka ne, bacci yayi peacefully har yaso ya makara tashi. Shi ya fara farkawa ya dan janye jikin sa yana kallon fuskar ta, very cute da dan karamin lips dinta da ya dace da yar fuskarta. Duk da ta chanja masa sosai amma shi har yanzu kallon baby yake mata, dan a yanzun ma yar karama ya ganta a gabansa. Samun kansa yayi da yin murmushi ya tashi yaje yayi alwala yazo daidai saitin kanta ya shafa mata ruwan hannun sa a fuskar ta, da sauri ta bud'e idon ta, ta tashi zaune tana zazzare ido, tamke fuskar sa yayi, ya wuce gaba zuwa wajen da zai yi sallah, tashi tayi ta shiga toilet din tayi alwalar itama ta fito ta tsaya tana tunanin da abinda zatayi sallah dan mayafin kanta babu yadda za'a yi yayi sallah. Yana zaune yana addu'a tunda ta fito, bata ce masa komai ba shima be ce mata ba, tana ta tsaye har ya gama ya taso yazo ya kwanta yana kulle idon sa
"Za.. n..yi.. sallah." Ta fada a rarrabe kamar me jin tsoro
"Yi mana." Yace still idanun sa na rufe
"Mayafi na ba zai ba."
"Kinsan ba zai sallah ba amma kika yafa kattin banza da wofi suna kallanki?"
Ya fada a hasale tunowa da abinda ya faru jiya
"A cikin gida ne ai."
"Cikin gidan babu Maza? Ko muharraman ki ne? Eh?"
Yace yana tashi zaune, shiru tayi ganin daga magana har ya harzuko, kwafa yai ya tashi ya fita ya sauka kasa, ya samo mata madaidacin mayafi a wajen ma'aikata wajen, ya kawo mata ta yafa a kasa tayi rolling da nata, sannan tayi sallar. Ta zauna a wajen har gari yayi haske sosai, yana ta baccin sa hankali kwance. Baki daya hankalin sa yayi gida, tana ta sake-sakn ko ta gudu ne sai gashi an kirashi, ya sa hannu ya kashe kiran aka sake kira a karo na biyu, sai da ya dan ja tsaki sannan ya daga yana kara wayar a kunne
"Hello..."
"Tariq kana ina ne wai?" Muryar Mama ta fito ta cikin wayar har tana juyowa daga in da take zaune, dan bude idon sa yayi ya murza kansa cikin yanayin baccin dake kansa yace
"Bana gidan Mah, anjima zan shigo."
"Da gaske ne kenan" tace gabanta na faduwa dan taji Amira da Fauwaz suna maganar kasa -kasa
"Me?"
"Ba komai, kazo gida kawai inason ganin ka."
"Shikenan, I'm on my way."
Ya katse kiran yana leko ta daga wajen da take zaune, ya d'an ya mutse fuska ya mike tayi saurin dauke kanta zuwa dayan side din, kamar be gani ba, ya shiga ya gyara jikin sa ya fito yace ta taso, da sauri ta mike har tana kusan bashi dariya.
***Mama na compound din zata fita Tariq din ya shigo, idon ta akan motar tana son gasgata abinda take gani, Jidda ce a zaune kusa dashi, jiri-jiri taji yana neman kayarda ita, kafin ma su gama parking tayi saurin shigewa ciki dan bata jin ko fitar zata iya a lokacin kuma. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (31)
ASSALAM ALAIKUM DEARIES BARKAN KU DA KOKARI…. KAMAR KODA YAUSHE. WANNAN KARON MA MUNA BARAR ROKON KU WAJEN TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS DAKE MANHAJAR YOUTUBE YARO NE DAYA TASHI DA SON KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE KUMA KWADAYIN GADON ME SUNAN SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE. A KUMA YI VIEWING DA LIKING. A TEMAKA DA SHARING MA... JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO... " Assalamualaikum dear sisters and brothers. Welcome to ummu sudais YouTube channels? A channel where the Holv Quran is been recited from different Angles. Click on this link and listen to the Beautiful recitation that will melt your heart https://youtu.be/Lafgc749sK8 Your subscription to our channel is of Great important. Please help us grow our channel by subscribing and liking
**** Da sauri ta bud'e motar ta fice ya tsaya yana kallon ta, hadda d'an gudun ta, ta bude kofa sai ta waigo ta kalli wajen da yake, ta jujjuya bakin ta sannan ta shige da sauri, murmushi yayi ya rufe motar ya nufi bangaren Maman yana jin sa sakayau kamar wanda ya sauke wani baban nauyi dake kansa. A tsaye ya samu Maman tana kaiwa da komowa a tsakanin hadadden falon nata, tun kafin ya gama shigowa ta soma fada
"Ni zaka wulakanta Tariq? Ni?"
"Mama... Me ya faru?"
"Tambaya ta kake me ya faru? Baka san me ya faru ba Tariq?"
Girgiza kai yayi
"Allah Mama ban sani ba."
"Menene hadin ka da yarinyar nan?"
"Mama?"
"Eh menene hadin ka da ita? Daga ina kuke ma tukunna? Kar dai kace min? Noo ba zai yiwu ba."
"Dan Allah ni dai Mama ki kwantar da hankalin ki."
"Ya zan kwantar da hankali na wai? Hu? Taya kake so na kwantar da hankali na ina ganin ku tare? Kasan abinda hakan ke nufi? Na rasa ka kenan,."
"Ba zai lasting ba mama, just give me sometime, bana so akai na ku samu matsala da Baba."
_"I'm doing it for Baba."_ Ya fadawa kansa da kansa k'asa-k'asa amma sai yaji kamar zuciyar sa bata karbi uzurin sa ba, so yake dole ya karfafa kansa cewa duk ma abinda yake saboda a samu maslaha a tsakanin iyayen sa ne, shi he has nothing to do with her, ba daidai dashi bace sai ya karyarta ma ai, amma kuma sam zuciyar sa taki bud'e masa kofar da zai aje irin wannan uzurin da har zai samu wajen zama a cikin zuciyar tasa
"Don't go far na gaya maka toh, Halima da yarinyar are cunning, idan baka yi wasa ba you will end up..."
"Nooo Mah..." Ya katse ta
"I don't think hakan zai faru, in sha Allah hakan ma ba zai faru ba."
"I hope so, fita zan amma ganin ku tare na ji ma na fasa, we only have few days sai kayi duk yadda zakayi kafin a shiga cikin bikin, bana son kuma silly excuse dan ba zan karba ba."
"In sha Allah." Yace amma kuma sai yake jin kamar ba zai iya aikata abinda Maman take so ba, amma kuma why not? Shi ai ba son yairnyar yake ba. Fita yayi ya nufi bangaren su, yaje yayi wanka sannan yayi breakfast ya zauna yana hutuwa a falon har Fauwaz ya shigo.
***Kamar munafuka haka ta shiga part din nasu, aunty na zaune a falon taji kamar ta nutse saboda tsabar kunya, kanta a k'asa ta shiga ciki, ta gaida Auntyn tayi saurin shigewa dakin ta, tasa key ta kwanta rigingine tana kallon pop, ta kasa tantance yanayin da take ciki gaba daya,ta kuma rasa a wanne mataki zata ajiye abinda Ya Tariq din yayi, tunda ya nuna mata time kawai yake jira yayi ending marriage din nasu, kila dai kawai so yake ya dagula mata lissafi ya barta da ciwo a zuciyarta, zatayi duk yadda zatayi ba zata sake bari su hadu ba, ballantana har wani abu makamancin hakan ya faru. Message ne ya shigo wayar ta sai a lokacin ta tuna da wayar, baki daya kamshin turaren sa take kamar wadda tayi wanka da ruwan turaren, duk ya cika mata kofofin hancin ta, wayar ta dauko ta shiga message din sai taga Ya Fauwaz ne
_"I will take over daga nan, kamar yadda nayi miki alkawari Ya Tariq sai yazo da kansa ya kawo kansa wajen ki, ki barmun komai, ke dai kawai kiyi avoiding nasa."_
Murmushi tayi kawai ta goge text din, dan ita bata taba tunanin Tariq din zai yi abinda Fauwaz din yace ba, bata ki ba idan baya hayyacin sa ko kuma dai wani babban al'amari, itama tun farko tayi gangancin hada kanta dashi, banbancin su yayi yawan da zai yi wuya ya iya sakkowa zuwa level dinta. Har magriba tana kunshe a daki sau biyu Amira na zuwa suje wajn Yaya amma kemaimai taki, gobe za'a kawo musu ragowar wasu kayan kamshi na turara jiki wanda na kwana uku ne kachal zaa musu daga nan zaa shiga hidimar bikin wanda bata dauke shi yanzu da muhimmanci ba dan bata san matsayin ta a wajen wanda ake yi domin shi ba. Da safe Amira tazo su tafi wajn Yayan da k'yar sai da Aunty ta bata rai sannan ta amince amma da cewa tayi ba zata ba ta daina zuwa, duk da Amira tasan dalilin amma basu taba maganar ba dan jidda zurfin cikin ta yayi masifar yi mata yawa, ganin bata fada mata ba yasa ta ki mata maganar gaba daya. Ita aka farawa dan Ya Safiyya da Umaima basu ma tashi ba, ana gama mata ta sulale ta koma nasu part din dan tayi alkawarin ba zata yarda su hadu ba. Tana shiga Aunty ta tashi tana rike bakin ta kamshin irin mayatataccen kamshi ne me dadin gaske, kudi sosai aka kashe dan ita kanta daga wani state din tazo matar bayan wacchan ta gama musu ta tafi.
"Kinji kamshin da kike Jidda?"
Kunya ce ta kamata, ta rufe fuskar ta, da tafin hannun ta tana dariya, kod'a ta Aunty ta dinga yi ita dai kawai dariya take cike da kunyar Auntyn dan abinda ya faru jiya.
***Kwana biyu bayan sun dawo yana ta zuba ido babu ita babu alamar ta, sau wajen uku yana zuwa part din Yaya amma sai ya tarar bata nan, har sai da Yaya ta gaji tace wai lafiya yake mata safa da marwa a gida ne? Fita yayi kawai be sake dawowa ba, chan anjima ya tafi wajn Auntyn amma sai suka hadu da Auntyn a hanya zata fita, ya juya bayan sun gaisa ya samu waje ya zauna yana saka ido ko zai ga fitowar ta amma shiru har dare babu ita babu alamar ta. Be san dalilin da yasa ya damu da son ganin ta ba, shi dai kawai yaji yana so ya ganta ko ma ba zata masa magana ba. Kamar ya koma wajen Auntyn amma sai ya hakura ya fasa. Da safe ya sake saka ido amma shiru, a lokacin ne kuma gidan nasu ya fara cika da mutane, yawanci yan uwan Mama ne suka fara zuwa a ranar, silalewa yayi ya bar gidan dan baya son su ganshi kwata-kwata.
***Suna zazzaune dukka yan matan a falon farko su kuma su Mama na ciki, Salma ce tace tambaye Maryam
"Wai Ya Tariq baya nan ne?"
"Wa? Ya Tariq din zaki tambayen? Wallahi ban san in da yake ba."
"Har yanzu Ya Tariq baya son mutane, wallahi na matsu na ganshi naga yadda ya chanja."
"Ganin Ya Tariq sai kin cika Form, da dai Jiddaa ce." Amira tace tana dariya, bata fuska Salma tayi, taja tsaki tana mikewa
"Sai ana maganar mutane kuna kawo mana maganar wata chan dan Allah."
"Kinyi maganar mijin ta ai dole ayi maganar ta."
"Wai miji, tab!" Ta kwashe da dariya
"Kina mamaki ne?"
"Ba dole ba, dan Allah me ya Tariq zai ci da yarinyar nan? Yarinyar da aka taimakawa aka mayar mutum sai shegen girman kai ita ba yar uban kowa ba."
"Aiko baki san jiddah ba."
"Bana son ma na santa."
"Toh gaskiya ki bar maganar nan kar ma taji wallahi, kinga abinda kika taba yi mata din nan."
"Ai ku kome za'a ce akanta bakwa gani, sai kuyi tayi."
Turo kofar yayi, ya shigo fuskar sa a tamke,ya dan ji maganganun da suke sama-sama ya kuma fuskanci abinda suke magana akai, shi yasa ya tsani taron mata dan babu yadda za'a yi su hadu su tashi ba su tada fitina ba. Gaishe su sukayi a kusan tare duk sun rude Allah yasa be ji me suke cewa ba, be amsa ba yayi wucewar sa dan dama Mama ce tace yazo ya gaida su Aunty Nafi dasu Aunty Mimi, da ba dan haka ba, da ba zai shigo ba. A tsaitsaye ya gaishe su, ya fito yazo zai wuce Salma tayi tsagal tace
"Ya Tariq ina wuni?"
Ko kallon in da take be ba, yayi ficewar sa, yana fita su Ummi suka kwashe da dariya, kamar ta kurma ihu haka taji dan kunya. Dama Aunty Nafi ce ta saka ta, tace tayi kokarin shige masa,amma dan wulakanci ko gaisuwar ta be amsa ba bare tasa ran zai kalli in da take. Tsokanar ta suka dinga yi ta rasa ina zata saka kanta sai daki ta gudu saboda borin kunya.
***Shi baki daya baya jin dadin zaman gidan, a matukar takure yake gaba daya da zaman waje dayan gashi ba wani sanin wurare yayi a garin ba dan ma dai yana da saurin gane waje kuma yanzu an cigaba akwai map, gashi Baba yace dole sai ya kara wasu satittikan kafin ya tafi, Mama kuma ta saka shi a gaba tana so taji ya ake ciki, gashi ya rasa yadda zai ko wulgawarta baya gani sau biyu da aunty tana part din Baba yana zuwa ya murda kofar dakin ta amma a rufe zai ji, baya kuma magana yake juyowa dan baya son ta raina shi ko taga kamar ya damu da ita ne, so yake kawai yaga ta daina kukan ko har yanzu tana yi? Gashi ya rasa solution bayan yayi mata alkawari itama, gashi zuciyar sa ta hana shi kemaimai da ya fara tunanin yadda zai yi sai kawai yaga ta fara hasaso masa Jiddan. Wajen Yaya ya nufa duk da itama jama'ar ta sun fara zuwa, wanda dama duk suna burin zuwa Abujan sai kawai Baba yayi amfani da damar nan aka ce duk me son zuwa ya shirya, aikuwa suka dinga tururuwa kafin kace me gidan dame d'am da mutane. Tun a kofar shiga yaji hayaniya sai fasa shiga ya bari idan dare yayi ya dawo. Da daddare Baba ya dawo ya kirashi suka zauna yace menene shirin sa akan tarewar jiddaa, shiru yayi yana nazari har sai da Baban ya sake maimaita masa sannan yace duk yadda akayi yayi, dan jim Baban yayi da zai ce wani abu sai kawai ya fasa
"Shikenan, sai ka fara shiri, akwai gidan da zaku zauna, Incase ko baka nan dai muna kusa."
"Nagode Baba, Allah ya kara girma."
"Amin ya Allah, dan Allah Tariq karka wulakanta min 'ya, Dan Allah."
"In sha Allah."
"Kuma inaso kuje kai da ita ku gaida mahaifin ta, sai ka saka muku rana bayan sun gama bidi'o'in nasu na mata."
"In sha Allah zamuje."
"Shikenan Allah yayi muku albarka."
"Amin ya Allah."
***Duk yadda Mama taso Tariq ya yi botsare akan maganar auren nan sam yki, ta ma kasa gane in da ya dosa kwata-kwata, kamar ma so yake kawai ta kwantar mata da hankali shiyasa ma yake biye mata da nuna mata shi ma baya son abun. Babu yadda za'a yi baya so kuma ya hakura har a kawo yanzu, wanda nan da kwana biyu zata tare daga nan kuma bata san ya zai yi ba. Yanayin hayaniyar bikin da dumbin mutanen da suka taru yasa ta hakura da maganar ba wai dan ta hakura gaba daya ba, yanzu zatayi focusing kawai akan su Safiyya idan aka gama zata dawo kan Tariq din ne dan ba zata yarda a lalata mata rayuwar dan ta ba. Baki daya gidan idan ka cire bangaren Yaya kowa ya yi shirin tafiya wajen hadaddiyar dinner din da aka shirya, Mama bata nan sun fita da Aunty Mimi daga chan zasu wuce ita da wata babbar kawarta da suka hadu a taron da suke na matan ministoci. Su jidda na wani babban gidan makeup ita da su Ya Safiyya wadda da k'yar akayi convincing dinta ta yarda zaa mata amma yar kad'an dan bata son irin heavy makeup din, ita kadai take budirin ta dan me gayya me aikin kamar ma be san anayi ba, shiyasa Amira zata tsayata su tafi tare driver ya kaisu su kuma Ya Safiyya miijin kowacce ne zaizo su tafi abun su. Su Umaima ne suka fara tafiya sai Ya Safiyya ma ta tafi ya zama sai su kadai dama kuma sune karshen gamawa. Driver Amira ta kira tace sun gama ya matso da mota, yace mata ya dan fita daga cikin wajen zai shigo da Oga yana waje. Yana cewa oga ta gane Ya Tariq yake nufi dan haka yake ce musu shi da Ya Fauwaz dan dama ba bahaushe bane ba. Kin fadawa jiddah tayi sai da ya dawo ya kira sannan tace su taso su tafi.
Yana tsaye jikin sabuwar motar sa, wadda Baba ya bashi gift dinta jiya na kammala karatun sa da kuma aure, kaftan ne a jikin sa fari me hade da navy blue collar da jikin hannun, takalmi da hular kansa duk navy blue ne,dinkin da kad'an ya wuce guiwar sa. Kallon wajen yake a tsanake har suka fito, Amira ta hango shi suka nufi wajen da yake a tsaye, sai da suka kusa karasawa sannan Jidda ta ganshi, tsayawa tayi chak cike da mamakin ganin sa, juyowa yayi suka hada ido ya tako ya same su a wajen da suke tsaye
"Kije Sam ya ajiye ki,mu ba zamu je dinner din ba."
"Ok." Amira tace tayi gaba da sauri,
"Muje ko?" Yace yana nuna mata hanya
"Tafiya zamuyi da Amira fa." Ta fada idon ta nayi raurau kamar zatayi kuka
"Na sani ai, cewa nayi ba zaki je ba, babu wata dinner da zaki oya shiga mota mu wuce gida."
"Dan Allah ka barni naje."
"Ba zaki ba."
"Dan Allah." Ta sake cewa already har ta soma kukan bakin ciki, kukan ka gama saka rai a abu ace ba zaka ba, da tun farko da tace ba zata ba da sun kyale ta shikenan, amma sai da ta hakura har tazo make up sannan yace ba zata ba..
"Oya, muje ko na daga sama, kinsan kuma zan iya."
Waigawa tayi ta hango wasu saurayi da budurwa a chan gefen su, ta sake waigawa dayan barin shima wasu ne a zaune suna hira, sai kawai ta nufi motar tana had'a hanyaa. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (32)
***Kofar motar a bud'e take, taje ta shiga ta sunkuyar da kanta k'asa zuciyar ta na tururi, agogon hannun sa ya kalla ya kalli cikin motar, ya kad'a kansa ya tako zuwa wajen motar, ya rufe mata kofar ya zagaya ya shiga ya zauna.
"Ki daura seatbelt."
Yace yana jan tasa ya daura, ya kunna motar, hawaye ne ya shiga sauko mata na bakin ciki, duk kawayen su na school zasu je Amira ta fada musu Safeera ma zata wuce daga chan dan ta shigo tana gidan aunt dinta. Sake kallon ta yayi yaga bata daura seatbelt din ba, matsowa yayi jikin ta,ta dago ya kalle ta yayi mata murmushi, irin murmushiin na ci karfin ki, kauda kanta tayi ya jawo belt din ya daura mata, ya tsaya daf da ita bayan ya daura matan, k'in juyowa tayi tana jin ji daf da ita, k'ashin wuyan ta ya kalla, yaga rami, hannu ya kai ya taba ta juyo da sauri
"Har ajiya za'a iya yi a wuyan nan naki."
Yace hannun sa yana kan wajen, fuskar sa a sake yana so ya kure ta, banza tayi masa tana jin yadda yake tafiya da hannun sa akan wuyan nata, wani irin take ji amma ta fuske dan sosai take cikin bacin ran hanatan da yayi wanda bata ga dalili ba.
"Kina wannan kamshin turaren zaki shiga wajen da yake da garadan maza? Baki san darajar aure bane?"
Yace yana kokarin saka idanun sa acikin nata,
"Haramun ne, ki bari mu samu solution sai kiyi ma duk abinda zakiyi, amma dai yanzu na hana,."
"Sai ayi sauri a samu solution din, I'm sick and tired, na gaji."
Sai ya fashe masa da kuka dan ba karamin haushi maganar sa take bashi ba, kullum sai yayi kokarin shiga rayuwarta haka kullun sai ya jaddada mata jiran lokaci yake, ta gaji kawai ya yanke hukuncin da duk ma zai yanke dama ta riga ta shirya. Tsayawa yayi chak yana kallon ta, kukan take bil hakki da gaskiya, ya rasa kwakkwaran dalilin da zai saka ta dinga irin wannan kukan, be sani ba ko zama kusa dashi ne bata so, ko ganin shi ma gaba daya ne bata so. Gashi shi kuma yana jin shi very comfortable duk sanda suke tare, yanzu ma yana samun labarin zasu dinner ya taho hankalin sa ba a kwance yake ba, baya so taje wajen ayi ta kallon ta, ba kuma dan yana so ko kishin ta ba a nasa tunanin, sai dan kawai ya kare martabar auren sa da yake kanta.
"Komai kuka, kuka baya maki wahala ne?"
Ya tambaya yana maida kansa ya jingina a jikin kujerar motar yana duban ta, kamshin turaren ta, na fuzgarshi zuwa gareta, sai dai yayi matukar kokarin hana kansa, yana jaddadawa kan nasa cewa . Kokarin daidaita kanta tayi, ta goge fuskar tana hana kukan cigaba da zuwa, kukan bakin cikin abinda yake mata ya kuma nuna sam be san ma me yake ba, yanzu da tayi magana maimakon ya amsa mata sai ma ya tsaya kawai yana kallon ta, ya kuma sauya zancen zuwa wani na daban. Jin tayi shiru ne yasa shi tashi ya sake kunna motar ya ja suka fice daga wajen. Kasancewar babu nisa tsakanin nan da gidan ya saka su saurin isa, hakan ya kara tabbatar mata da ba zata je din ba kenan. Sai da ya shiga har cikin gaban part din Auntyn sannan yayi parking, bata jira komai ba, ta bud'e kofar ta fice, maimakon ta shiga nasu bangaren sai ta chanja hanya zuwa part din Yaya. Parking ya gyara ya bi bayan ta da sauri dan ya hango wasu samari a wajen suna zaune, kasancewar da sauri yake tafiya yasa yayi saurin cimmata, ya rufa mata baya yana kakkareta. Ta ganshi sarai amma tayi kamar bata ganshi ba, suka cigaba da tafiya tana daga kafa yana sauke tasa har suka shiga. Yaya na zaune ita da Gwaggo da wasu a falon ta shigo, ta shige dakin Gwaggon da saurin ta, bude baki Yaya tayi zatayi magana sai gashi ya shigo
"A ah, tare kuke ne?"
"Eh." Yace yana shigewa ciki shima bayan ya gaishe su a gajarce
"Ina wajen bikin kuma?"
"Ko har an dawo? Gwaggo tace
"A ah be isa an dawo ba, bari naje naji dan yadda Jidda ta shigo kamar ba kalou ba."
"Toh Allah yasa lafiya."
"Amin." Tace tana mikewa da k'yar dan kafarta ta fara matsa mata sosai. A tsaye ta same shi daga kofar ita kuma jiddaa na saman gadon ta rufe fuskarta, duk kwalliyar da akayi mata ta baci ga shi sai kiran wayarta su Safeera suke Aunty ma ta kirata ta kasa dagawa.
"Ya akayi me ya faru?" Yaya tace tana kallon sa
"Wai dan nace ba zata je dinner ba, shine take kuka."
"Kamar ya ba zata je b? A wanne dalilin yasa ba zata ba?"
"Menene amfanin zuwan toh?"
"Abinda suka dade ana shiryawa zaka hanata fisabillillah, gaskiya baka kyauta ba wallahi, Jidda tashi kinji, daina kukan haka nan kiyi hakuri, kai kuma sai ka gaya min kwakkwaran dalilin da ya sa ka hanata wallahi, dan ni banga dalili ba."
"Ni ba wani dalili, kawai bana so ne, ta bari taje idan babu aure na akanta."
"Ahayyye!"
Tayi shewa tana tafa hannu, kicin-kicin yayi da fuska Yaya ta rasa me ma zata ce
"Ai be kamata ba, tunda dai shi aure daraja ne dashi, kuma ni bana son irin wadannan abubuwan, ta bari a samu hanyar da za'a kawo karshen komai."
"Kai tafi chan, wacce hanya ce da ba za'a iya samar da ita ba har sai an ta maganar ta, ai kawai yanke hukunci ake idan har da gaske har zuciya ana neman hanyar, ba a fatar baki ba.".
"Tashi kinji Jidda, ki rabu dashi bakin hali ne yayi masa yawa da mugunta, idan ba haka ba a gama shirya abu dan gadara ya hanaki zuwa haba."
Tashi tayi idonta har sun daga saboda kukan bakin ciki, gaba Yaya tayi tazo zata raba ta gefen sa ta wuce ya tare hanyar yana mata wani irin kallo da idanun sa suke a shanye,
"I'm sorry."
Ya samu kansa da furtawa dan da gaske yaji babu dadin abinda yayi mata, kin amsa wa tayi zata wuce ya sake tarewa
"Please kiyi hakuri."
"Zan rungume ki idan baki hakura ba."
Kallon sa tayi da sauri, ya gid'a mata kai,
"Da gaske nake Allah."
"Na hakura."
Tace ganin yana matso ta, amma duk da haka sai da yayi hugging din nata,abinda yake taso tun dazu, yana so ya shaki kamshin jikin nata sosai amma kuma yana hana kansa, daga karshe yaga ba zai iya ba, tunda dai ba wani abu yayi ba, kuma ai ba haramci ya aikata ba. Yaya ce tayi saurin fita dan da ta labe a falon, dariya ma ya bata dan tasan dama wuyar ta yazo hannu, irin su masu sum-sum din nan sun fi kowa iya shege
"Almuri." Tace tana zama a in da ta tashi,
"Me ya faru Yaya?"
"Wai ya hanata zuwa wajen bikin dan shegen kishi."
"Abinda kake so ai shi kake kishi Yaya."
"Bar dan bantan uba, yana so yana yare, zai gane shayi ruwa ne, dama ai dan hakkin daka raina..."
"Haka ne, kina ga a yadda ya shigo fa, kamar ma da fari be lura damu ba."
"Ina zai lura so ya rufe masa ido."
"Kai Yaya."
"Allah kuwa, yaga yar karamar yarinya duk ya rude babban kwabo, da yana cika bakin shi baya so yan-yan-yan."
***A yadda yake ji kamar kafarsa ba zata dauke shi ba, gashi duk yadda taso ya kyale ta, ya kasa, sai da wayar sa dage cikin aljihun gefen rigar sa tayi kara sannan ya saketa yana matsawa baya, da sauri ta koma cikin dakin ta kule chan karshen gefen gadon shi kuma ya d'aga wayar ganin Mama ce
"Wai Tariq me kake nufi dani ne?"
"Na'am Mama?"
"Eh, Jidda bata zo wajn nan ba, sai naji labari na yawo a wajen wai kaje ka dauke ta a gidan makeup kace ba zata ba, me yasa zaka je ka dauke ta? Kuma me yasa zaka hanata zuwa? Bangane maka ba kwata-kwata."
_"Ba zan iya bari tazo wajen nan ba."_
yayi maganar kasa kasa amma duk da haka sai da taji shi,
"Ba zaka iya bari ba? Saboda kana kishin ta ko?"
" Ni? Noo ba haka bane, kawai dai tunda ba wai an riga an rabu bane, dole na kare martabar auren, shine kawai amma ba wani abu bayan nan."
"Kasan da yake kai ka haife ni TARIQ, son yarinyar nan kake."
"Mama!"
"Ka dauka ana wa namiji auren dole ne kuma baya son matar yayi hakuri ya cigaba da bin ta kamar jela, ina lura da kai wallahi, duk take-taken ka na gani."