Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 16

Sanadin labarina complete novel - Chapter 16

Sanadin labarina complete novel Chapter 16: Sanadin labarina complete novel Chapter 16. "Amma Mama ba haka bane, ni ba haka bane, ba spec dina bace ba, no…

4,486 words

"Amma Mama ba haka bane, ni ba haka bane, ba spec dina bace ba, no ba haka bane gaskiya."

"Sai kayi kuma, na bar baki."

Ta katse kiran, rike wayar yayi saroro a hannun sa yana jujjuya maganar da Mamsn tayi masa a ransa. Duk maganar da sukayi tana ji kuma ta san akan ta ne, kekashewa taji zuciyar ta, tayi lokaci daya, babu amfanin cigaba da zubar da hawayen ta akan mutumin da ya cika da son kanshi, tasowa tayi tazo har gaban sa, ta tsaya sannan tace.

"Kayi sauri ka kawo karshen wannan drama din, kaga sai ka samo daidai da kai din."

Daga haka ta wuce shi kawai ta fice daga dakin, ta wuce part din Aunty ta shiga dakinta,tayi kwanciyar ta,tana hana kanta sake kuka akan sa. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (34)

***Wajen Yaya ta nufa dan tasan itace kai tsaye zata saka Baba ko ta hanashi. Ta kuma san ta yadda zata bullo mata ta daina ragawa Mama dan ta lura shirun ta yasa take ganin har yanzu tana da ikon taka ta. Bedroom din Yayan ta shiga ta sameta a kwance tana hutawa bayan ta idar da sallar walaha, tashi tayi zaune suka gaisa sannan tace magana tazo su yi

"Ina jinki Halima, mecece matsalar? Dan nasan dole akwai magana."

"Yaya dama akan maganar Jidda ce, ni a gani na tunda har Tariq ya dawo Jidda ya kamata ta tare a gidanta, dama taron bikin ake so ayi kuma ya nuna baya ra'ayi ni a ganina kawai ta tare shine mafi a'ala."

"Ni kaina nayi wannan tunanin kuma jiran Alhaji nake ya shigo, dan na ga alama dan ku bashi da ta ido sam, gwara su je chan su karata."

Dariya ta saka Yayan ta cigaba da bayani

"Al'muri da yake munafuki ne ai kinga yadda yake ko? Irin masu halin nan ke dai kawai ki kalle su, sun fi kowa iya shakiyanci."

"Yanzu ki barmun komai, a yau ba sai gobe ba zata tare, dan babu amfanin zaman."

"Allah ya kaimu Yaya, dama dai maganar kenan abun ya soma damuna."

"Ai dole, yarinya ma tayi hakuri ki bari zanyi maganin shi a yau din nan, sai kisa ta shirya duk abinda zatayi zuwa anjima."

"Toh bari naje Yaya, Allah ya kara girma."

"Amin kinji? Allah yayi albarka."

***Komawa tayi ta saka jiddah a gaba, da Safeera da ita suka taimaka mata ta hade koman ta waje daya, hannu bata saka ba ita a lallai ba in da zata tunda be san worth din ta ba, babu wadda tabi ta kanta musamman Safeera da tasan munafurci ne kawai ba har zuciyar, take maganar ba. Falo ta dawo tayi zaman ta, tana kissisima yadda zata kaya a zaman nasu, duk da kaso hamsin tana tsoron Mama amma kuma sauran kason na kwadaituwa da son zama dashi din. Fitowa Safeera tayi ta sameta a falon suka cigaba da zama sai ga Isma'il ya kirata, dagawa tayi jidda tayi kamar bata gane da wanda suke waya ba, suka dan jima suna magana daga karshe ta kashe tana murmushi

"Ya Isma'il ne, kinsan ya kusa zuwa gida."

"Allah sarki, Allah ya taimaka."

"Amin, ni tunda tafiya zakiyi ma ai ba amfanin zama na, zan koma gidan Aunty Sajida kawai."

"Wai waye yace miki tafiya zan? Ki jira mana ki gani, nasan ba in da zanje."

"Toh zamu gani, yarinya gwara ma ki saka ranki tafiya dole."

"Idan nace ba zani ba ai babu me daukata. "

"Wallahi tsaf zai dauke ki din, tab!"

"Ke kika sani."

"Ke ma kin sani ai."

***Ran Mama ya kai karshe a baci, dawowar ta kenan daga wajen Yaaya da ta turo aka kirata ta fada mata yau matar Tariq zata tare, da k'yar ta amsa da toh ta taso tazo ta fadawa su Aunty Nafi, suka kuwa hau fanfata akan karta yarda. Kiran TARIQ tayi be daga ba, sai ta kira Fauwaz shima sai da ta katse sannan ya biyo kiran tace masa ina Tariq yazo maza-maza, baya nan dan tun safe da ya fita training be dawo gidan ba, gidan sa ya wuce a chan yayi wanka ya shirya sannan ya koma bacci dan yasan idan be more baccin sa ba ya koma sai ya samu matsala, shiyasa har Maman ta kira be ji ba. Sai da rana tayi sannan ya tashi ya dan sake gyara jikin sa sannan ya hau mota ya dawo gidan. Tun a hanya dama Fauwaz ya fada masa Mama tana neman sa, shiyasa yana zuwa part dinta ya wuce tana ganin sa tace ya shigo suka shige chan dakin ta in da babu kowa.

"So nake ka saki Jidda a yanzu ba sai anjima ba."

Kawai tace masa ko zama bata iya yi ba. Kallon ta yake hankalin sa a tashe, ta hade rai taki bari ko kad'an yaga saukin ta, kasa furta komai yayi, ya dinga kokarin tattaro kalaman bakin sa amma ya gaza furta su, idan har yace zai iya sakin Jidda yayi karya, duk da ba wai yana mata son da ba zai iya rabuwa da ita ba, amma ba zai zo ya samu matsala da iyayen sa akan ta ba, haka kuma ba zai taba so hakan ta shafi iyayen sa ba

"Mama dan Allah mu bari mubi komai a sannu, dan Allah "

"Babu wani bin komai a sannu, yau kwana nawa kaana min alkawari amma ka gaza cikawa sai bin yar karamar yarinya a baya kamar wanda aka gama dashi."

"Wai Maama waye yace bin ta nake?"

"Kasan ni yarinya ce ai, bansan me nake ba."

"Ba haka bane Mama."

"Toh naji, duk ba wannan ba, bana son zaman ku karkashin inuwa daya, dan haka sai ka sawaake mata tunda ka kasa samun mafita."

"Baba fa? Zai yi fushi dani sosai."

"Ka barni dashi kawai, kai dai kayi abinda nace, ba zan iya jure ganin ta a matsayin sirikata ba."

"Amma Mama, mesa kika tsaneta haka?"

"Tambaya ta kake?"

" A'ah, kawai dai naga kamar yayi yawa ne mama, kiyi hakuri dan Allah mubi komai a sannu, Dan Allah muyi wa Baba biyayya kar muzo muyi abinda zai bata masa suna shi yanzu da yake a idon duniya abu karami zaki ji ana yi dashi."

"Ba zan ba, akan yarinyar nan zan iya batawa da kowa, idan har jinin Halima ce zata auri jini na, na gwammace komai ya faru."

"Mah?"

"Idan har na isa da kai, ka rabu da ita."

"Menene laifin ta a gareki Mama?"

"Babu komai, ba abinda tayi min kawai bana son ta ne."

"Shikenan mama, zanyi abinda kike so, amma ina zuwa Dan Allah."

Fuskarta ce ta fadada da farin ciki, t

"Dan Allah da gaske kake?"

Daga mata kai yayi

"Toh madallah, ka gama min komai Allah yayi maka albarka."

"Amin Ya Allah."

Ya juya ya fita ita kuma ta koma wajen su Aunty Nafi zuciyar ta cike da farin cikin zata kuntata wa Auntyn dan dama tayi alwashin sai ta mata abinda zata dade tana jin ciwon sa.

Ko da ya fita sai ya rasa abinda yake masa dadi, ko giyar wake yasha ba zai iya aikata abinda Maman take so ba, dan ba itace akan gaskiya ba, Baba yafi ta gaskiya dan haka dole ne yasan yadda zai yi be bata wa daya daga cikin su ba. Iyaye dole ne ka bisu kayi musu biyayya kuma mahalifiya tafi karfin wasa shiyasa yake matukar yi mata biyayya domin samun rabauta. Amma kuma a wannan gabar be san me yasa ba, baya jin yana tare da Maman. Zaman sa yayi a waje tare da masu gadin gidan lokaci zuwa lokaci yana dan saka musu baki a hirar dan yadda gidan yake cike da mutane bazai sake shiga ciki ba, tunda dai hankalin Maman ya kwanta for now zai tafi da ita a haka kafin yasan abun yi. Sai da akayi la'asar sannan ya tashi daga wajen, ya shiga cikin dakin su ya hau tattare muhimman takardun sa waje daya, ya zuba su a yar karamar jaka ya saka a bayan mota, sannan ya tafi kiran Yayan da ta turo tana neman sa. Chan cikin dakin ta, ta kule dan ba kowa take so yasan maganar da zasuyi ba. Mamakin ganin ta a nutse a zaune yasa shi shan jinin jikin sa

"Lafiya Yay?"

"Lafiya ta kalou wallahi."

"Menene ya faru?"

"Takardr jidda zaka ban?"

"Takarda kuma Yaya?"

"Eh, tunda baka son ta ba, ka sakar musu 'ya taje ta auri wanda yake son ta."

"Wanene?" Ya bata fuska

"Ina ruwan ka? Wani ne yazo tun kafin ma ayi maganar ka, wai mu masu shishigi da son gwaninta muka ce gida be koshi ba,ashe zaka zo ka watsa mana ido?"

"Aina yake shi din?"

"Oho ba zaka ji ba, ka bata takardar ta ba sai ta sake kwana da igiyoyin auren ka akanta ba."

"Kuma ita ma tana son shi?"

"Kaji mun yaro, ina ruwanka da wannan kuma? Kai tunda ba da gaske kake ba, ai sai kawai ka yanke hukunci Amma ba zai yiwu ka hanata kula kowa ba kai kuma baka so."

Mikewa yayi ransa a baci ya fice be sake cewa komai ba, dariya suka kwashe da ita, Fauwaz dake makale ya fito suka tafa da Yaya

"Kinsan ta kan tsiya Yaya."

"Ni din ta wasa ce? Sai shegen kishi amma girman kai ya hana shi gane halin da yake ciki."

"Ya sani fa Yaya, kawai yana hana kansa yarda da hakan ne, bari muga abinda zai yi kuma, bari naje naji yadda ake ciki."

"Karka manta kazo ka fesa min."

"Akwai amaana ai ni dake tawan."

"Amanar kad'an ce, tunda ka kusa kashe ni na dawo daga rakiyar ka, bakin mugu."

"Ai ya wuce sai zamu Kano sallah, da kafarki zaki taka ki shiga jirgin ma Hajiya Yaya."

"Bana so, babu kuma shegen da zai saka ni shiga."

"Zamu gani dai, bari naje nagano."

"Munafuki." Tace tana kallon sa, be ji me tace ba, ya fice dan da yaji sai ya dawo sun yi ta da ita.

Kai tsaye part din Aunty Tariq ya nufa ransa a bace fuskar nan tasa a hade tamau, babu kowa a part din Aunty na side din Baba, ita kadai ce sai Usman da yake wasa a falo yana kallon Disney World, tasowa yayi da sauri yayi hugging din Tariq din, ya d'aga shi sama yana kokarin daidaita fuskar sa

"Wasa kake?" Yace yana sauke shi k'asa

"Eh tare muke yi da Yaya Jidda tace zatayi sallah."

"Ina Aunty?"

"Ta fita."

"Ok zauna kayi wasanka ko? Ina zuwa."

Yace ya nufi dakin Jiddan, ta idar da sallah kenan taji rigar dake jikin ta, ta takura mata, sai kawai tayi deciding ta cire ta, data raka Safeera ne ta sakata amma dama bata iya zaman gida da ita, riga da wandon ta ciro na bacci masu dan kauri rigar iya guiwa sai dogon wando, ta saka tana gyara gashin kanta da ya barbazu akan nata ya murd'a kofar ya shiga da sallama muryar sa a chunkushe kamar wanda ya saka wani abu a makoshin sa ya tokare wajen. Kasa dagowa tayi tayi tsam a wajen da take ya shiga takowa yana karewa dogon gashin nata kallo. A daf da ita ya tsaya ta kalli kafarsa dake sanye da takalmi sau ciki. Muryar tasa a ciki-ciki yayi magana

"Ina Hijab dinki?"

Bata amsa ba, dan bata ga amfanin tambayar ba, wurwurga idanun sa yayi tayi a cikin dakin ya taka zuwa wajen da kayan ta suke, ya bude wardrobe din yana kallon jerin kayan dake gyare a cikin wardrobe din.

"Lefe." Ya fado masa a ransa, hannu ya sa ya ciro Hijab guda daya a cikin jerin kayan, pant dinta ne ya fado, ya sunkuya ya dauka ya kalli wajen da take a tsaye, da sauri ta kautar da kanta kunya matsananciya na kamata, ciki ya mayar ya rufe ya dawo ya mika mata, sannan ya dauki wayar ta dake ajiye a saman gadon, yace tasa Hijab din.

"Ina zamu?" Tace rike da Hijab din bata saka ba

"Gidan Mijinki zaki." Ya amsa mata kai tsaye, yayi hanyar barin dakin sai da ya kai karshe sannan yace

"Karki bata min lokaci." [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (33)

Be iya motsawa daga wajen ba, maganganun Mama da nata na cigaba da yi masa yawo akai, toh ko dai son nata yake? Ya tambayi kansa. No ba haka bane. Wata zuciyar ta rad'a masa, tausayin ta kawai kake ji, ya sake jin wata zuciyar ta tunasar dashi.

"Eh haka ne, tausayi ne kawai nothing more."

Yayi assuring kansa yana samun hujjar da zai rike, kad'a kansa yayi ya fito daga dakin, duk da maganar ta, ta bata masa rai amma kuma ba zai yi abinda suke so ita da Maman ba, sai yayi istikara sannan ya samu gamsashishiyar hujjar da zai rikewa Baba ya yarda dashi. Wani kallo Yaya tayi masa da ya fito, yayi kamar be ganta ba yayi ficewar sa, ta yi dariya tana girgiza kanta, tasan akwai sauran drama amma kuma a chan k'asan zuciyar tana tausayin Tariq din, dan tasan irin su so be iya yi musu da dadi ba.

Tunda ta shiga dakin take juyi a gado, kamar ta tattara kayan ta, ta tafi wajn Baffa haka take ji, baki daya babu abinda yake mata dadi, tana nan kwance har aka soma dawowa, su aunty ne yan farkon tahowa suka taho tare da Safeera da zata kwana a gidan. Tana jin su ta fito da sauri, suka rungume ita da Safeera idon Aunty akanta, sai da suka zauna sannan Auntyn tace

"Jidda me ya faru ne wai?"

Turo baki tayi cikin yanayin rashin jin dadi tace

"Hanani yayi."

"Tariq hoo, amma me yasa?"

"Nima ban sani masa ba, kawai mugunta ce wallahi."

Tace kwala na sake taruwa a idon ta dan ko tunawa tayi sai taji hawaye

"Karki kara cewa mugunta duk tsiya mijinki ne, kuma duk abinda yace shi zakiyi."

"Aunty amma kinsan be kyauta ba ko?"

"Toh me zan ce jidda, tunda shine yake da ikon barki ko hanaki."

"Aikuwa, kuma dole ayi biyayya."

Safeera tace tana dariya, duka Jidda takai mata, tace ta taso su shiga ciki, suka bar Aunty ita kadai sai itama kawai ta wuce dakin ta dan watsa ruwa ta dan warware gajiya.

Bayan tayi wankan tana zaune a falon akayi knocking, kasancewar duk masu aikin gidan idan dare yayi basa shigowa suna bq yasa ba kowa sai ita kadai a falon, tashi tayi ta bud'e kofar sai taga Tariq a tsaye, matsa masa tayi ya shigo sannan ya rufe kofar

"Aunty yunwa."

Yace yana zama idon sa akan hanyar dakin Jidda

"Bari naga ko zaka samu wani abun a kitchen."

"Aunty Indomie nake so, tunda nazo banci ba, a kira sai ta dafa min karki wahalar da kanki."

"Aikuwa Jidda gwana ce, dan tafi ni ma, suna ciki da kawarta Safeera bari na kira ta."

"Nagode Aunty."

"Ah ba komai ai, bari na turo ta."

Tayi gaba tana murmushi, a kalla yanzu ta tabbatar da Tariq yana son Jiddan ta, abinda dama yake daga mata hankali kenan, sai gashi duk kowa ya gama gano shi duk da shi be gama gano kansa ba, he's so obsessed with her. Knocking tayi musu daga kofar ta dan bud'e tace

"Zo ki dafawa Tariq Indomie yunwa yake ji."

Zaro ido tayi,

"A daren nan Aunty?"

"Eh yana falo yana jiran ki, ni kwanciya ma zan dan na gaji sosai, sai da safe Safeera."

"Sai da safe aunty."

"Jiran ki yake." Ta maimaita mata ganin tana zaune ko motsi batayi ba, tashi tayi ta dauko Hijab ta zunbula har k'asa sannan ta zura slippers ta fito tana zumburo baki Safeera na mata dariya,

"Idan naji kin dade zan rufe kofa ta "

tace mata tana dariya

"Allah ya kiyaye na dade, sama-sama zan dafa masa na dawo daki, a daren nan ace ka wani dafa abinci kawai dan a kuntata maka."

Tayi maganar bayan ta rufo dakin yadda Safeeran ba zata jiyo ta ba, yana tsaye jikin bangon corridor din duk yaji me tace, kallon sa tayi gaban ta, ya fadi, ya kad'a kansa yana nuna mata hanya

"Wuce na fasa Indomie din ma, sakwara nake so."

"Wallahi ban iya ba." Tace da saurin ta, dariya taso bashi ya kanne yana nuna mata hanya

"Ita mijinki yake so dole kuma ki yi masa abinda yake so ko na fadawa Aunty."

Tafiya ta cigaba da yi zuwa kitchen din ya take mata baya, ya samu jikin freezer ya tsaya yana folding din hannun sa, tsayawa tayi tana kalle-kalle kamar me neman wani abu,

"Dafa indomie din amma kikayi min sama-sama sai kin daka min sakwara da tiny hands din nan naki."

Indomie din ta dauko ta, ta dora yana kallon ta,

"Bana son jagwalgwalo kuma."

"Ni bana iya abu idan aka sakani a gaba."

"In fita kenan?"

"Eh."

Tsalle yayi ya haye saman deep freezer din

"Karewarta ma kenan, kiyi sauri kuma karki sa yunwa ta kama ni."

Bata sake magana ba, ta cigaba da abinda take yana kallon ta, waya ya ciro ya hau dannawa ta juyo kad'an taga hankalin sa na kan wayar, yaji ta dauko ta kara a Indomie din ta rufe duk be gani ba. Ta gama ta saka masa chicken a ciki amma sai yace ta soya masa egg, nan ma kamar ba zatayi ba ta soya egg din ta hada komai a tray amma sai yace mata saura oat, kamar tace ba zata dama ba amma dai ta daure dan ta lura shi kamar zaman shi a kitchen din be dame shi ba. Dining ta wuce ta dora akai bayan ta gama, ya duro yana maida wayar aljihun sa, ya tako zuwa wajen dining din, yaja mata kujera daidai in da ta ajiye abincin

"Zauna." Yace yana rike mata kujerar.

"Na'am?"

"Sit down!"

Zama tayi ya tura ta ya maida kujerar jiki yana tsaye daga bayan ta

"Oya, cinye tatas."

"Bana jin yunwa."

"Wallahi sai kinci, ina kallo kika zuba mun yaji ai, so kike na mutu ko?" Ya zuro mata kansa ta bayan kujerar

"Ai me yaji tafi dadi."

"Oya, ci."

Daukar fork din tayi ta fara ci, wani masifaffen yaji ya shiga har cikin kwanyar kanta, bata son yaji komai kankantar sa, shishi ta fara ya yi murmushi yana cije kasan lips dinsa,

"Yaji ko?"

"A ah kwarewa nayi."

"Ok sannu, oya eat maza-maza."

Jujjuya fork din ta soma yi, ya ja kujerar gefen ta, ya zauna yana tallafe fuskar sa. Narai-narai tayi da fuska kamar zatayi kuka amma ya fuske, ya dauki oat din ya fara sha, yana kallon ta.

"Dan Allah kayi hakuri ba zan kara ba."

"Me kikayi?"

"Yaji na saka maka."

"Me yasa?" Ya tsare ta da idanun sa, sauke kanta tayi kasa da sauri

"Oya tell me, me yasa kika cika min yaji?"

"Nima bansani ba."

"Toh karki sake."

"Ba zan sake ba."

"Good girl, kije ki kwanta toh, sweet dreams"

Da sauri ta mike, dama jiran kad'an take, tayi gaba ya bita da kallo ya girgiza kansa, yayi sauri ya karasa shan oath din ya tashi ya bar part din.

***Washegari da safe Aunty na dakin ta, Rasheeda tazo ta sameta wai Mama na falo tana magana da ita, abin ne ya bata mamaki dan tunda ta dawo Abujan sau daya Maaman ta shigo shashen ta shima rashin lafiya tayi har da karin ruwa shine tazo a tsaitsaye ta duba ta. Tasowa tayi cike da mamaki ta fito sai ta sameta a zaune tana karewa falon kallo, tana ganin Auntyn ta fito ta mike tsaye

"Ina kwana Maaman Fauwaz?"

"Lafiya, ina Jidda?"

"Jidda kuma? Me ya faru?"

"Bani da damar kiran Jidda kenan?"

"A ah ba haka bane, bari na kira ta."

Tace, girgiza kafa Maman tayi bayan ta koma ta zauna wajen da ta tashi, zuwa tayi ta kira Jidda, suka fito tare. Ganin Maman a zaune yasa ta samu k'asa ta zauna ta gaishe ta cike da girmamawa, amma maimakon ta amsa sai ta shiga aiwatar da abinda ya kawo ta

"Me kikayi wa Tariq?"

"Na'am?"

"Me kikayi masa? Wanne kalar asirin akayi ma d'ana da har ake so ya zama wani sulobiyo yana bin ki kamar wani jela?"

"Kamar ya wai?" Aunty tace

"Kamar yadda kuka sani,nasan idan har ba wani abun kukayi masa ba wallahi Tariq yafi karfin ya dinga bibiyar ta haaka."

"Haba Maman Fauwaz, mu babu abinda mukayi masa wallahi, me zamuyi ma?

"Oho, wallahi ba zan dauka ba, ba zai yiwu a maida min yaro wani gashi nan ba, tun wuri ki sani wallahi, dan wannan karon da karfi na nake, kuma zan yi komai na karya wannan kaddararren auren."

Sai ta mike,

"Ki shirya bugawa dani a wannan karon, dan bana hada Tariq da kowa saboda haka ba zan taba bari ba wallahi."

Sai ta juya ta fice kamar kububuwa, dariya Aunty tayi bayan ta fice jiddah da ta tsorata ta kalli Auntyn

"Share ta Jidda, wallahi ba abinda zata iya duk barazana ce, kuma idan ta isa sai ta hana Tariq din ko? Amma ba ke zata zo tana fadawa magana ba,na daina yi mata shiru wallahi, duk abinda tazo dashi a shirya nake nima, Tariq kuma in sha Allah sai kin haifa masa yayan da zata goya a bayan ta."

"Aunty ni tsoro nake ji, dan Allah ko a hakura."

"Akan me? Wallahi ba a isa ba, ki zauna shekara guda kina jiran sa ya dawo sai ace a hakura? Saboda mu ne bamu da galihu ko? Toh ba'a isa ba wallahi, kuma a yau ba sai gobe ba, zaki tattara ki tafi gidan ki ai an gama komai, ban ga zaman me kike ba ma."

"Bari kiga." Tace ta dauki veil dinta ta rufa kanta ta fita, tashi Jidda tayi ta koma dakin ta duk babu dadi, bata son tashin hankali kuma bata so Aunty ta yi abinda da batayi ba akanta.

*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_

_08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_ [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (36)

***

"Na shiga uku." Tace tana jin kamar k'asa ta bud'e ta shige ciki,

"Fada min ina so na sai wasu kaya ne."

Turo bakin ta tayi gaba, ta wuce taja kujerar mirror ta zauna, murmushi yayi ganin dabi'ar tace turo bakin,ya kuma san maganin ta, cigaba da duba kayan yayi ya zabi dogayen riguna da kiyasin tsayin ta da nasa amma dan ya sake tabbatar wa sai ya janye system din ya mike ya nufi in da take a zaune ya saka hannu biyu ya mikar da ita, sannan ya karata a jikin sa, yar karama take tashi a duk sanda suka tsaya a tare, saboda shi yana da tsayi sosai.

"Menene tsayin doguwar rigar ki?"

"54."

Tace tana kauda kai ganin kamar leken wuyan rigarta yake yi wadda take v-shape, duk a takure take

"Ashe daidai nayi guessing, nasan ba zaki fi hakan ba, little Jiddah."

"Little?"

"Yes." Ya d'age mata gira,

"Zo kiga wani abu." Yaja hannun ta, ta kalle shi da sauri shima ya kalle ta saboda yadda sukayi wa juna shocking

"Like charges repel, unlike charges attract."

"Na'am?"

"Haka akace a physics."

"I'm not a science student."

"I see, amma zaki iya fadamin?"

"Me?" Tace tana daga kanta ta kalle shi, shiru yayi kamar ba zai magana ba, sai kuma yace bayan ya rike mata hannun kakam

"Size of your underwears."

"Wayyo Allah na, Dan Allah ka daina."

"I need to know, ina siyan kayan lefe ne."

"Lefe?"

"Yes, ba ana lefe ba idan za'a yi aure ba."

"Aure zakayi?" Ta samu kanta da tambayar sa, gid'a mata kai yayi

"Aure zan, shiyasa zan hada lefe kuma ke zaki tayani zaba."

"I can't." Ta janye hannun ta fuskar ta na chanjawa nan da nan, kallon ta yake yana karatar yanayin ta,ya kuma hanata kwace hannun nata, shafa kansa yayi da hannu daya yayi murmushi yace

"Muje ki fara zabar min masu kyau kuma kar amarya tace ban iya zabe ba."

Wajen da ya ajiye system din ya jata, ta haye gadon ya zauna a gefen ta yana saka system din a tsakanin su, ya shiga nuna mata kayan tana kallo, duk wanda ya nuno sai tace be kyau ba, har suka dau lokaci a haka ba tare da ta zabi kowanne ba, sunan Yasmin ne kawai yake mata yawo aka, tasan ta gama haduwa iya haduwa dan tasan Tariq bazai kula yarinya kamar ta ba. Zamewa tayi ta kwanta bayan ta dan matsa zuwa dayan side din gadon, ta rufe idon ta taja duvet ta rufe har kusan kanta. Tattare system din yayi da wayoyin su ya dora a saman chest of drawers, ya karo sanyin dakin ya kashe wutar ya hawo gadon ya kwanta a wajen da ya tashi, ya bar space a tsakanin su. Juye-juye suka dinga yi dukkan su, kowa da abinda yake sakawa a ransa

"Little Jidda?" Ya kira sunan ta yana matsawa zuwa tsakiyar gadon,amsawa tayi ciki-ciki, ya saka hannu ya juyo ta suka kalli juna ta dan hasken da ya shigo ta corridor din dakin

"Tell me about you, everything about you kinji?"

Dan motsawa tayi ya sake jawota sosai zuwa jikin sa,

"Fada min, bani labarin Jidda."

"Yanzu? Bacci nake ji fa."

"Ba wani, inajinki kina ta juyi, kin kasa baccin."

"Ni da gaske bacci nake ji har na fara ma."

"Oh okh, to bari na saka ki wartsake."

Sai ya matso da fuskarsa wajen tata, ya rufe idon sa ya hade bakin su waje daya. Kamar yadda ruwa yake idan ya dauke haka tunanin jidda ya dauke, ya kwasheta ya sauke ta a wani bigire na daban, kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, tana jin shi cike da mamakin sa, sai da ya gaji dan kansa, sannan ya matsa da kansa baya ya dora shi a saman pillow yana kallon saman daki,

_"Me ya same ni ne?"_ Ya tambayi kansa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull