Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 17

Sanadin labarina complete novel - Chapter 17

Sanadin labarina complete novel Chapter 17: Sanadin labarina complete novel Chapter 17. _"Me yasa nake kasa controling kaina when I'm with her?"_ Ya sake…

4,498 words

_"Me yasa nake kasa controling kaina when I'm with her?"_ Ya sake tambayar kansa. Tana da wani irin tasiri akansa, a kanta yake bude baki yayi magana sosai fiye da yadda take yi masa kuma shima yake yiwa kowa, baya tunanin komai da kowa a duk lokacin da take gabanta. Murmushi yayi yana jin taste din salivar dinta a cikin bakin sa, dama he has been longing for this , ya dade yana imagining kansa kissing her small lips, he never expected her to be this sweet, a dah kallon karamar yarinya yake mata wadda yake ganin ba zata iya masa ba, kuma ba zata iya da needs nashi ba, but ya fara proving kansa wrong, and he is developing feelings for her, duk da babu yawa amma kuma yasan ko yaya ne dai. Juyowa yayi da kansa yaga ta sake juyawa dayan side din, yasan kunya taji, sai ya kyale ta kawai ya juya ya rufe idon sa, ko minti biyar be kara ba bacci yayi awun gaba dashi.

***Da asubah ta riga shi tashi, ta kalle shi babu ko riga a jikin sa sai 3quater wando, duk kuwa da sanyin dakin, ta rasa dalilin da yasa ko sanyin baya ji bayan ita har hancin ta ya toshe saboda sanyi ya kure AC kuma ya cire riga, shi jin zafin nasa ma extraordinary ne, toilet taje tayi alwala ta fito ta sameshi ya tashi ya kunna hasken dakin,alwalar da tayi yasa sanyin da take ji ya karu, yazo ya wuce ta ya shiga toilet din shima, rage sanyin tayi sosai ta kudundune da blanket sai da taji sanyin ya dan ragu sannan ta tashi ta dauko Hijab din ta saka ta shinfid'a sallaya zata tada ikama ya fito da ruwa a jikin sa yana gogewa da towel alamun wanka yayi, jallabiyar ya dauka ya saka ya ciro hula irin wadda ake kira da tashi ka fiya naci fara ya dora akansa ya fice da sauri dan kar ya rasa jam'i.

Tana nan akan sallayar ya shigo dakin da sallama, ta amsa kanta na kasa bacci na fizgarta, zuwa yayi ya duka a gabanta ta dago jin shi a kusa da ita

"Baki bacci ba?" Ya kalli idon ta, da suka dan tasa, girgiza masa kai tayi

"Nayi."

"Ok, yau daurin auren yaran chan, munyi waya da Baba yanzu da wuri zan fita,dan Kano zamu a sumaila za'a daura auren ki kwanta kiyi bacci kinji?"

Ware idon ta, tayi da sauri taji ta nemi baccin ta rasa

"Ni ba zan je ba? Ba zani gidan ba?"

"Eh." Yace mata kai tsaye

"Ni kadai zan zauna?"

"Eh." Yace mata nan ma

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi tsoro nake ji, kuma duk su Amira suna nan har kayan da zamu saka yau an karbo, dan Allah ka barni dan Allah."

Sai ta fashe masa da kuka wiwi, yana durkushe akan digadigin sa,yana kallon ikon ALLAH, abu kad'an sai kuka? Me zata je tayi toh kuma? Baya son duk abinda zai faru tsakanin shi da Mama ya shafe ta, yasan nata sai yafi zafi shiyasa yaga gwara tayi zaman ta.

"I'm sorry kinji, zan turo su Amiran sai su zauna dake."

"Ba zuwa zasuyi ba, biki ake fa."

"Toh shikenan, babu abinda zai sameki ai,akwai masu aiki a waje, Fauwaz zai kawo duk abinda babu a kitchen."

Sai ya mike ya isa wajen kayan sa, ya dauko sabuwar shaddar sa fara kal da babbar riga, ya dauki takalmi, agogo da hular sa, da sauran abinda zai bukata, dan a gidan zai shirya, mota yaje ya kai ya dawo har lokacin kukan take sosai, baya so ta karyar masa da zuciya har yace taje, sai kawai ya tsaya daga kofar yace mata ya tafi, ko dagowa batayi ba, yayi jim a tsaye sai kuma ya juya ya fita dan baya so Baba ya kuma kiran sa dan babban aiki ya sashi, kuma sune zasuyi gaba kafin su Baban su iso shiyasa ma ko breakfast be tsaya yayi ba.

_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_

_08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_ [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (35)

***Kasa daga kafarta tayi daga in da take tsaye, taji kamar ana sassara mata su, tsoro ne ya shige ta, tsoron abinda zata tarar idan har ta bishi, bata yi tunanin da gaske aunty take ba,da tace yau zata tafi, sai ta dauka kawai tsokanar ta sukeyi, a yanayin da ya shigo mata ta tabbatar ba da wasa yake ba, me ya kamata tayi? Ta tambayi kanta tana tsaye rike da Hijab din gashin kanta a barbaje dan ko ribbon bata saka masa ba.

"Aunty." Tace tana kallon in da ta ajiye wayar ta da nufin ta kirata a waya tazo tunda tana part din Baba. Babu wayar a wajen, dudubata ta shiga yi amma bata ganta ba, tasan kuma a saman gadon ta ajiye ta, cigaba da dubawa tayi tana rike da Hijab din tana tunanin abinda ya kamata tayi. In da yasan zai samu Auntyn ya nufa, yayi knocking a kofar ya tsaya rataye da hannayen sa a bayan sa. Bude kofar tayi,

"Tariq?"

"Aunty zamu tafi ne dama, shine nace bari na fada miki."

Wani irin sanyi taji a k'asan ranta, tayi murmushi tana gid'a masa kai

"Ba komai ai, akwai kayanta a wata trolly sauran sai a kawo mata da safe, Allah ya tsare ya taimaka."

"Amin , Baba be dawo ba?"

"Yana hanya, zamuyi magana dashi."

"Nagode Allah ya kara girma."

"Amin Amin."

Tace ta kasa boye farin cikin ta, wucewa yayi sai da ta daina hango shi sannan ta rufe kofar zuciyar ta cike da farin cikin Jidda zata samu nutsuwa da sauyin rayuwa irin wadda take mata fata.

Tana tsaye ta gama dube-duben wayar bata ganta ba sai gashi ya shigo, be kalli in da take ba, ya saka hannu yaja akwatin yayi gaba. Yanayin fuskar sa kadai ta ishe ta ta gane ba da wasa yake ba, dole ta saka Hijab din ta tura ribbon din a hand bag dinta tabi bayan sa a sanyaye. Har ya shiga mota tunda a gaban wajen yayi parking dinta dama, ta hasken da ya haska cikin motar ta hango shi yana kokarin tada motar, kofar gaban a bud'e take, ta karaso ta shiga a sanyaye ya yi reverse suka fita daga gidan. Babu wanda yayi ko tari a cikin su, tukin sa kawai yake har suka isa gidan dake dauke da me masu gadi da securities saboda yadda rayuwar ta zama yanzu. Gida ne madaidaci wanda be cika girma sosai ba, amma kuma ya yi kyau sosai ya dace da masu gidan. Idanun ta akan compound din gidan sanda yayi parking a gefen wata mota dake fake a cikin gidan baka me kyau. Kashe motar yayi ya fita, itama sai ta fito duk da be ce mata ta fito din ba, ya mikawa wani matashi car key din sannan suka haura saman balcony zuwa kofar da zata sadaka da cikin gida. Yana gaba tana bin shi a baya suka shiga cikin falon da yake a matukar tsare, ko ina fes fes komai na ciki sabo ne kal an kawata falon da kaya kalar golden masu daukar ido. Hular dake kan sa ya cire ya ajiye a saman centre table din dake tsakiyar falon ya wuce zuwa bedroom din da ya maida shi nasa, dan tuni duk ya tattaro kayan shi daga gida ya kawo su. Cire kayan da yake jikin sa yayi ya sauya zuwa doguwar sakakkiyar jallabiya milk colour ya fesa turare a jikin sa. Ya zauna yana ciro wayar sa da tata, ya bud'e ya saka number sa ya kira yaga tata number din yayi saving sannan ya jona su a jikin chargy ya kwanta a kan sofa yana mike kafarsa. Be san ko hukuncin da ya yanke yayi daidai ba, shi dai kawai yabi abinda zuciyar sa ta fada masa ne. Kiran wayar sa akayi, ya tashi yaje ya dauko sai yaga Baba ne yake kira, nauyin Baban yake ji a yanzu dan be san yayi abin kunya ba sai da yaga kiran Baban. Kamar ba zai daga ba ganin zata katse yasa ya daga.

"Baba barka da dare." Yace yana kokarin danne kunyar da yake ji

"Barka dai Tariq, ashe kuma kun wuce sai da na dawo nake samun labari."

"Na'am..." Yace yana sosa kai, dariya Baba yayi

"Shikenan ka shigo da safe inason ganin ka, kar kuma ka manta da maganar da mukayi akan zuwa gaida Baffan naku."

"In sha Allah ba zan manta ba."

"Toh madallah, Allah yayi muku albarka."

"Amin ya Allah, sai da safe."

"Mu kwana lafiya ango."

Baba yace cikin sigar tsokana, ai be san sanda ya danna power button ya kashe wayar gaba daya ba. Sai kuma yayi murmushi tunanin abinda ya aikata na dawo masa, da kunya matuka amma ya zai yi? Hakan ya kamata dama tun farko, ya kuma tabbatar hakan ya farantawa Baban rai dan yadda yake masa magana zakaji muryar sa a sake take cike da annashuwa.

***Shiru shiru be fito ba, har ta gaji da tsaiwar ta zauna shiru, mikewa tayi tana kallon kofar da ita kadai ce a cikin falon, nan kuma taga ya shiga, yanke shawara shiga ciki tayi kawai dan ba zata yi ta zama ba. Kofar ta bud'e a hankali ga mamakin ta sai taga wani falon nan dan karami sai kofofin dake ciki, wadda take kallon ta, ta nufa ta murd'a a hankali ta tura kanta, sukayi ido biyu dashi idon sa akan kofar, saurin sakin handle din tayi zata koma muryar sa ta dakatar da ita

"Zo nan."

"Na'am?"

"Kinji me nace ai."

Shigowa tayi ta tsaya daga hanya, ya kalle ta ya kalli Hijab din jikin ta.

"Ki cire Hijab din kizo nan ki zauna."

"Ba tafiya zamuyi ba?"

"Kinzo kenan." Yace yana d'age mata kafadar shi

"Toh ai na zanje na kwanta? "

"A kaina."

Yace mata kai tsaye, saurin kallon sa tayi ya d'aga mata gira, sai ta kauda kanta daga kallon shi cike da mamakin amsar da ya bata

"Oya zo nan kafin na taso, kina bata min lokaci."

Matsowa tayi tana turo baki, ya girgiza kai yana sake kishingid'a sai da tazo daidai in da yake a kwance, sannan yace ta cire Hijab din, ta dade tana wasa da Hijab din ta kasa cirewa shi kuma yana kallon ta, da k'yar ta cire sai ta yafa shi a saman kafadarta zuwa chest din ta.

"Zauna."

Ya nuna mata saitin cikin sa tunda shi a kwance yake, dan dosanawa tayi ta zauna duk a darare take, tashi zaune yayi yasa ta a tsakiyar jikin shi, numfashi taja da sauri tana kokarin gyarawa ya sauke kafafunsa kasa ta zama dai tana gabansa a zaune kafafun sa sun sakata a tsakiya, kunya da wani irin yanayi me wahalar fassarawa ta shiga, yayi kamar be san me yake ba, ya kai hannu zuwa saman kanta ya hau shafa mata gashin kanta da ya dade yana burin tabawa. Duk ta rikice ta kasa zama sai motsi take ta cigaba da abinda yake yi.

"Ina ribbon din?"

Ya rad'a mata a kunnenta, tayi saurin bud'e jakar ta ciro ta mika masa, yayi murmushi ya kama gashin ya saka mata, be yi sosai ba tunda ba wai ya iya bane dama, tana jin shi yana cirewa yana sake maidawa a dole sai ya kama shi da kyau.

"Gashin doki ne?" Yace bayan ya gama daidaitawar a ganin shi

_"Na jaki ne."_

ta fada a ranta, amma a fili shiru tayi kawai dan ko yayi tayi motsi sai taji ta a jikin sa gaba daya. Maimakon da ya gama ya barta ta tashi sai yaki, suka cigaba da zama a haka. Ya kunna wayar sa dake gefen su, ya kira Ishaq dan dama dazu yaga missed calls dinsa yana tuki lokacin.

A handsfree ya saka wayar bayan Ishaq din ya d'aga, suka gaisa sannan ya tambaye shi amarya dan Tariq din ya fada masa in brief,

"Kana da matsala." Yace yana girgiza kansa

"Matsalar me? Daga cewa ya amarya? Ai wallahi kai dan gata ne, ga gida ga mota ga mata wallahi ka godewa Allah."

"Akace maka ban gode ba?"

"A ah kawai dai tuna maka nake ne, yawwa dazu ma Yasmin ta kirani zata dawo cikin week d'in nan har tace na fada maka."

Gaban Jidda ne ya fadi, jin an ambaci sunan Yasmin, ta yunkura zata tashi ya sake matsewa yana zagayo da hannun sa ta cikin ta.

"Karka dameni da magaanar wata yarinya pls."

"Ai dole na isar da sakon ta, ka sani ko da ita zakayi ta biyu? Yarinya me so da kaunar ka."

"Ni bana son ta."

"A ah fa, kar reshe ya juye da mujiya, ka sake tunani sosai."

"Idan ka shirya waya dani ka kira."

Ya katse kiran yana jan siririn tsaki, hannun sa dake cikin Jiddan yasa ya shafa cikin nata wanda yake flat kamar ba'a taba saka masa abinci ba.

"Bakya cin abinci ne?"

Banza tayi masa dan baki daya wayar da taji yanayi ta sakata a yanayi, gumi ne ma yake ta keto mata ta cikin jikin sa.

"Dole ki dinga cin abinci sosai, naga alamar bakya son ci shiyasa, ji cikin ki, wannan ai sai na balla shi."

"Zanje na kwanta." Tace a muryar haushi

"Oya kwanta mana, waya hanaki?"

"Dayan dakin zanje." Tace

Sakin ta yayi yana ware hannun sa, ta tashi da sauri ta fice. Lumshe idon sa yayi ya bud'e, be san dalilin da yasa yake acting haka, ko dai magaanar Mama gaskiya ce son Jiddan yake?

***Dayan dakin ta shiga, ta jefar da Hijab din da jakar hannun ta, ta zauna tana kallon kofa, "yarinya me son ka da kaunar ka" ta tuno abinda na wayar yace, "ka sani ko da ita zakayi ta biyu?" Wani kululun abu ne yazo ya toshe mata a wuya, tana son ya Tariq sosai dan bata sake gane tana son sa ba sai da ta samu kusanci dashi sosai, ya iya duk abinda yasan zai tafi da hankalin mace, in a cool and matured way, ko kallon ta yayi sai taji wani iri bare yayi mata magana, closeness dinsu shi yafi komai taba ta. Duk da tasan baya son ta kamar yadda take son shi, amma zuciyar ta, taki barin ta, ta cire shi daga cikin ranta. Tsawon mintuna arba'in tana nan a zaune a wajen, dan bata da shirin tashi ma, ta saka wannan da kwance wanchan hankalin ta gaba daya yana wajen sa, ko ya cigaba da wayar sa ko ma ya kira wadda aka kira da sunan Yasmin din duk dama pretending yake da yace baya son maganar, tasan kadan daga aikin maza,toh amma ita a matsayinta na wa da har zai yi pretending a gaban ta? Ai bata jin tana da wannan matsayin ma baki daya.

Kitchen ya nufa bayan ya fito daga dakin, yaje ya dauko yoghourt ya duba akwai ragowar cake din da yaci da safe, ya samu silver cup ya hado mata dashi ya nufi dakin nata, ya kwankwasa tayi saurin gyara zaman ta, ya turo ya shigo rike da plate din, kin kallon sa tayi ya ajiye ya kasan rug din gaban gadon ya zauna yana tankwashe kafarsa

"Ga dinner, na duba bamu da komai a kitchen din."

"Na koshi."

"Wallahi karya kike, sai kinci kuma."

"Ikon Allah."

"Ikon gaske, sakko malama, bana son iyayi." Yace yana gimtse fuska, kaamar zatayi kuka ta sakko, ya matso daf da ita har kafarshi na gogar tata,daukar cake din tayi ta soma ci cikin k'asa kasa da murya yace

"Ki cinye tatas so nake cikin nan ya dago ko kad'an ne kar kizo ki kasa daukata."

Kwarewa tayi jin abinda yace, ya tashi da sauri ya kawo mata ruwa tasha, kanta a k'asa ta dauki yoghourt din tana sha tana kallon dayan side din, gaba daya ta gama gano ya Tariq bashi da ta ido ko kad'an, idan ya fadi wata maganar sai ka rantse bashi ne yafade ta ba, kuma ya fuske kamar be yi ba. A hankali ta shanye yoghurt din, ya dauke plate din ya fita ita kuma ta shiga toilet dan ta gyara bakin ta, ta dauka idan ya tafi ba zai dawo ba, tana fitowa ta sameshi a zaune ya kunna system dinsa ya dora ta akan kafarsa, gefen sa bakin shayi ne yana fitar da tururi.

"Menene size din underwears dinki?" Ya tambaya idon sa na kan system din, jin tayi shiru ya sashi dagowa

"Zan gane size din dayan da na gani dazu a wardrobe dinki."

Yace yana mata shu'umin murmushi.

*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_

_08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_ [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (37)

***A hanya Baba ya sake kiran sa, yace masa gashi nan ya taho, ya katse kiran sai ya kira Fauwaz, yana tare da Maama lokacin tana masa magaanar daurin auren da kuma abinda take so yayi mata saboda bakin ta, manyan bakin da zasu zo gidan. Daga wayar Tariq din yayi dan dama yana so ya kirashi sai kuma wani abun ya dauke masa hankali,

"Kana ina?" Yace yana dagawa

"Wajen Mama, ka zo ne?"

"No yanzu dai zan shigo gidan, bari na karaso."

"Ok." Ya katse wayar

"Tariq ne?"

"Eh shine."

"Daga ina zaizo? Dama ba a gidan ya kwana ba?"

"Eh toh ban dai sani ba, amma inaga a gidan sa ya kwana."

"Oh okh, kace ina jiran sa fa."

"Ok ma, bari na je na karasa shiryawa dan Baba yace baya so bakwai tayi bamu tafi ba."

"Ok, shikenan."

Juyawa yayi ita kuma ta wuce kitchen taga abinda ake yi, duk da komai da za'a ci a bikin order akayi amma kuma akwai aikin da ake mata a kitchen shi zata je ta duba. Murmushi Fauwaz yayi bayan ya baro wajen Maman, dan yasan bata san Tariq ya aikata tsiyar ba, kuma yasan idan ta sani akwai matsala sosai, su dai yan kallo ne, gefe zasu koma suka yadda zata kaya. Kallon gate din da aka bude yayi, Tariq din ne, ya shigo ya samu gefe yayi parking Fauwaz din ya karasa wajen motar ya bud'e masa kofar, ya zuro kafarsa bayan ya fito rike da kayan sa, ya mikawa Fauwaz din.

"Ajiye min a ciki ina zuwa, zan ga Baba."

"Ai tun asubah be shigo ba fa, sai dai Mama ita ce take neman ka dama."

Hannu yasa ya karbi kayan yace

"Bari na fara shiryawa toh, samo min plain tea nayi warming ciki na."

"Ok."

***A gurguje ya shirya cikin shigar farar shadda wadda da akayi wa aiki da bakin zare, tea din ya dauka yana sha da hannu daya, dayan hannun kuma yana daidaita hular kansa, kiran sa akayi a waya ya daga da sauri dan yasan Baba ne, sukayi magana ya ajiye cup din ko rabi be sha ba, ya rige babbar rigar a hannun sa bayan ya saka bakin takalmin sau ciki, ya fito da sauri ya nufi bangaren Maman, part din nata a cike yake sai yaji duk ya takura, Amira da tazo zata fita yace tayi wa Maman magana.

"Ta shiga wanka." Tace tana kallon yadda kayan jikin sa sukayi masa kyau

"Ok, kice mata mun wuce."

"Ok sai kun dawo."

Har yayi gaba itama ta wuce sai ya tuna

"Amira."

"Na'am?"

"Anjima driver ya kaiki wajen Jidda."

"Tana ina?"

"Ban sani ba."

"Wallahi Ya bansan ina ba shiyasa na tambaya."

"Gidana toh."

Saurin toshe bakin ta, tayi alamun laaa, sai tayi dariya, hararar ta yayi yana kallon ta, tayi saurin daina dariyar yace

"Saura kuma ki bud'e bakin nan naki ki fada wa mama, zan yi magana da ita idan na dawo."

"Ba zan ma fada ba wallahi, ni yanzu ma zan tafi sai na dawo anjima kafin lokacin event din yayi."

"Event din me za'a yi?"

"Anan gidan ne zaa yi, itama Jiddan ta sani ai kayan da zata sa ma yana waje na."

"Ba zata zo ba, kije dai ke sai ki dawo anjima din."

"Toh shikenan bari na chanja kayana, zan ce ma Mama na je a sake gyara min gashi sai na tafi chan."

"Gyaran gashi? Aina akayi?"

"Glamorous Saloon ne, duk fa yau zamu je da Jiddan dama."

"Ok kuje tare din, a gyara mata sai ku koma gida."

"Ok tam."

"Kice mata nace ta saka Hijab idan zaku fita."

"Toh Yah." Tace tana gimtse dariyar da take neman taho mata, juyawa yayi da sauri ya bar wajen, ta kwashe da dariya ta buga tsalle.

Kaamar yadda tace masa zata fadawa Maman haka tace mata, ta dauko ATM din ta, ta bata ta fito wajen takwas bayan su Ya Tariq din sun tafi, ta samu Sam tace ya kaita gidan Tariq. Jidda na kwance a falon bayan ta gama kukan bakin ciki ta hakura gashi bata ga wayar ta ba, bare ta kira ko Aunty ce tasa ta roke shi taji ana knocking, tashi zaune tayi ta tabbatar da knocking din ake ko kunnenta ne sai taji an sake kwankwasawa, wajen kofar taje tace waye? Da sauri ta bud'e jin muryar wadda bata yi zato ba, suka rungume juna suna ihu kamar wadanda suka shekara basu ga juna ba. Zama sukayi a kujerar Amira ta kalli falon

"Haduwa, ashe kina nan."

"Dama zaki zo?"

"Gashi kuwa, Ya Tariq ne yace nazo na kular masa da matar sa."

"Ba wani nan, ni kyale ni kinsan ya ce wai bazan je gida ba, dan Allah haka ya dace?"

"Kinsan fa shi daban yake, wallahi dan zaki sha fama."

"Allah sarki ni."

"Wai yaushe kika taho? Kuma kin taho gaba daya kenan?"

"Oho nima ban sani ba, bansan me suka kulla shi da Aunty da Yaya ba, yazo ya tiso keyata a gaba har kuka sai da nayi wallahi."

"Ai Ya Tariq, sai a barshi wallahi, haka ya hanaki dinner kina ji kina gani."

"Ki daina tuna min dan Allah."

"Toh sorry, tashi zakiyi ki mana wani abu mu dan ci ko breakfast ban yi ba, yace muje a gyara miki gashin kanki."

"Gashi kuma? Ni ai bana retouching."

"Eh ai ba retouching ba, sake dai gyara mishi kayanshi zaa yi."

"Kayan shi?"

"Eh mana, baki sani ba?"

"Ke kika sani, ta yaya gashi na zai zama kayan shi tsakani da Allah kema dai banda neman magana."

"Ah toh na waye dah? Lallai ma ke din nan wallahi."

"Oho ke kika sani, babu komai a gidan nan sai dai kisha tea da cake."

"Anjima ai za'a kawo garar, wai hadda Ya Tariq a garar da Baba yayi."

Ta kwashe da dariya,

"Ko da yake yace shi yarsa yayi wa ba Ya Tariq ba."

"Allah sarki babanmu, Allah dai ya saka masa da gidan aljanna."

"Amin Amin. Muje ki shirya dan da wuri zan koma kar abubuwan su hade min, amma zan dawo da daddare idan kina so."

"Eh dan Allah ki dawo, wallahi inaso ko kwana ne ma kiyi."

"Wa? Ni? Tabdijam, Ya Tariq din ne zai barni na kwana?"

"Me zai hana?"

"Ba za'a ji mutuwar sarki a baki na ba, jeki shirya dai bari na sha tea din."

"Kyaji da gulmar ki."

Tace tana yin gaba ta shiga kofar da zata kaita dayan falon kafin dakunan nasu. Wanka tayi a gurguje ta ciro riga da skirt ta saka ta dauko veil dinta da handbag ta fito ta samu Amiran ta kunna TV tana kallo tana shan tea din

"Kira min wayata inaga a gida na barta."

"Ok."

Kitchen ta wuce ta hado tea din tazo ta zauna lokacin da amira ta kira wayar tata,

"An d'aga gashi ." Ta mika mata, karba tayi ta kara wayar a kunne

"Hello aunty?"

"Uncle ne ba Aunty ba." Da sauri ta ciro wayar daga kunnen ta, ta kalli number din, taga dai number ta ce,

"Waye?" Amira tayi mata alama da hannu

"Dama wayata nake nema shine nace Amira ta kira min ita."

"Oh okh, tazo kenan, kin daina kukan?"

"Umm.."

"Good, akwai wani abu ne?"

"Um um."

"Okh sai mun dawo." A ciki ta amsa ya kashe

"Wai wa ya daga?"

"Ya T..." Tace tana mika mata wayar ta

"Wai kina nufin da wayar taki ya tafi."

"Gashi nan, ni ban masan yaushe ya dauka ba."

"Lallai Ya Tariq, ai kamar akwai landline a hanyar kitchen din chan, na ganta a saman wani table."

"Ni wayata nake so,."

"Kika sani ko new one za'a kawo miki."

"Ai bance inaso ba."

"Malama ki daina pretending dan Allah, Amira ce fa, your best friend mene wai ban sani ba,ko yanzu kin daina son Ya Tariq din ne ake bashi I don't care attitude."

"Ni da nace miki ina son sa ne?"

"Fadawa wanda be sani ba."

"Tashi mu tafi, kar ya dawo yace ya fasa."

"Kad'an daga aikin babban Yaya."

Ta mike zata yafa mayafi Amira ta tuno da abinda yace mata

"Wallahi na tuna,yace karki yafa mayafi wallahi"

"Na shiga uku, mayafin ma?"

"Wallahi haka yace mun, kuma yana sane sai ya tambaya."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull