Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 18

Sanadin labarina complete novel - Chapter 18

Sanadin labarina complete novel Chapter 18: Sanadin labarina complete novel Chapter 18. "Gaskiya ni wallahi."

4,445 words

"Gaskiya ni wallahi."

"Haka zaki hakura, dole abi miji dan a zauna lafiya."

"Ke kika sani." Ta

suka fito, Sam yana zaune tare da gate man yana jiran su, suka shiga motar yaja suka bar gidan. Ita aka fara yiwa sannan akayi Amiran, sai sheki gashin yake da kyalli musamman ita da take da gashi sosai, ita kanta me salon din sai da ta yaba da tsantsi da yalwar gashin ta, duk da bashi da cika sosai tsayin da tsantsin ne gashi baki sosai.

A gate aka ajiyeta Amira tace ba zata shigo ba su Salma suna ta kiran ta, kamar zatayi kuka haka ta shiga gidan tana cike da jin haushin Tariq din.

*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_

_08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_ [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (38)

***Bayan la'asar suka dawo, yana shiga gida ya dauki motar sa ko ciki be shiga ba dan yasan Maman ma tana cikin mutane ya wuce nasa gidan, baki daya wunin ranar tunanin ta yayi tayi, shiyasa suna sauka yayi gidan ya huta gaba daya a chan duk da anjima dole ya dawo gidan nasu kafin a tafi kai yaran. Horn yayi aka bud'e masa ya shiga da motar ya samu gefe yayi parking sannan ya fito, hannun sa rataye da babbar rigar da bata fi awa daya a jikin sa ba ya cire ta dan duk a takure yake. Key din ya mikawa faisal ya haura, ya murd'a kofar yaji ta a rufe sai yayi knocking. Idar da sallar ta kenan dan bacci tayi tun da tayi azahar ta kwanta sai lokacin ta tashi, tayi sallar tana zaune jigum tana tunanin yanzu su Amira suna chan ana shan shagali ban da ita, da tuni tana part din Yaya ana ta harka. Knocking din ya sake yi ta tashi daga wajen da take ta nufi kofar ta bud'e ta, yana tsaye hannun sa rike da wayar ta da tashi sai babbar rigar dake sakale da dayan hannun, matsawa tayi ta bashi hanyar ya shiga ciki ta rufe kofar ta juyo ciki. Har ya zauna a kujera ya ajiye wayoyin a gefen sa, ya cire hular kansa yana dan kishingid'a saboda yadda yake jin gajiya. Bata ce masa komai ba, ta wuce kitchen ta dauko ruwa da cup ta kawo masa sannan ta mike ta shige ciki, ruwan ya dauka yasha ya dauki remote ya kunne TV ya mike kafarsa sosai sannan ya karo AC falon. Dakin taje ta zauna kurum tayi shiru tana tunanin me ya kamata tayi,shima kuma kamar wanda aka kullewa baki be ce mata komai ba, sai duk taji babu dadi dan ta dauka zai yi mata magana tunda dai shi ya ajiye ta. Ta dan dade a zaune sai kawai ta tashi tace bari ta watsa ruwa duk da tayi da suka fita da Amira, amma kuma baccin da tayi taji tana bukatar ta watsa ruwan dan duk zuciyar ta a jagule haka ta tashi. Tana shiga wankan ya shigo dakin, ya zauna a gefen gadon rike da wayar ta da ya kawo mata, motsin ruwa yaji a toilet ya gane tana ciki, maimakon ya fita sai yayi zaman sa idanun sa na kan kofar toilet din yana danna wayar sa. Sam bata ji shigowar sa ba, shiyasa ta fito kai tsaye daga toilet din daure da towel din da yayi amfani dashi dazu, kanta a rufe da karamin towel saboda kar ruwa ya taba. Sai da tazo kusan rabin dakin sannan ta ankare dashi, tayi diri-diri duk ta diririce kamar zata koma sai kuma taga shima komawar da kunya, tsayawa tayi chak kawai a wajen da take ta sunkuyar da kanta k'asa

"Ga wayarki."

Yace yana daga mata ita sama idon shi na kan ta

"Zan dauka." Tace tana jan towel din a kokarin ganin ta sake rufe jikin ta sosai

"Zo ki karba, ko na koma da ita."

"Ni ba amfani zan da ita ba."

"Ba wani, Aunty ta kira ki, sannan Amira tayi miki text wai zasu zo, na kirata nace bana neman su."

"Toh ka fita idan na saka kayan zan fito sai na karba."

"Ba in da zani."

Yace yana gyara zaman sa, motsawa tayi daga in da take tsaye a hankali har ta isa wajen wardrobe dinta, ta zaro Hijab zata saka ya mike ya iso ya rike Hijab din yana mata kallon cikin ido

"What are you try to hide?"

Shiru tayi dan yadda ya matso so close da ita, ya hana ta motsawa yana kuma yi mata kallon k'asa-k'asa.

"I'm asking you, me kike boye wa, show me."

"Dan... Allah... Kayi hakuri.".

Ta fada a rarrabe ganin ya rike jikin towel din, murmushi yayi yana cije saman lips dinsa, ganin yadda duk ta firgice ta shiga tashin hankali.

"Kema wai kin girma ko?"

"Dan Allah ni dai kayi hakuri."

"I can't, haram ne?"

"Eh." Tace da sauri ba tare da tasan ma ta fada ba. Kallon ta yayi da sauri still yana rike da gefen towel.din itama ta rike kakam

"Ta ya akayi ya zama haram?"

Ya kai hannun sa saman kanta ya cire towel din da ta daura ta rufe gashin

"Wow." Yace yana ya saka hannu ya shafa gashin

"Ta ya akayi ya zama haram? Fada min."

"Sanyi nake ji, ka tsaya nasa kaya na, dan Allah."

"Ok, ok.. Saka toh." Ya cika towel din ya jingina da jikin mirror yana folding hannayen sa

"Kaje waje."

"Ba in da zani, idan zaki sa kisa idan kuma sai na taimaka miki fine, I will be glad to help."

"Na shiga uku."

"Da saura ma yarinya." Ya kad'a kai yana murmushi. Doguwar riga ta dauko ta dora ta akan towel din sannan ta zare towel din ta kasa, ta saka Hijab din akai. Dariya ta bashi yadda take ta sauri ta gama ta kai towel din ciki ta sakashi a washing machine, sannan ta fito

"Kin manta baki saka abinda na gani a cikin wardrobe dinki ba, da twin dinsa."

"Bra and pant." Ta fada a zuciyar ta,

Da sauri ta fice daga dakin dan ta gano Ya Tariq so yake sai ya hanata sakat a gidan. Dariya ya saka, ya mike daga jinginar da yayi yabi bayan ta, ya sameta a kitchen kamar be neman abu. Hannun sa zube a cikin aljihun sa ya tsaya a kofar kitchen din yace

"Kije ki shirya sosai, ki sameni a mota."

"Gida zamu?"

"Oho, don't waste my time."

Da sauri ta koma dakin, ta dauki underwears din ta koma toilet ta saka sannan ta saka riga da skirt sakakku ta dora veil akanta me dan kauri dan bata so yace mata lallai sai ta saka Hijab. Flat shoe ne a kafarta duk da bata da tsawo chan amma shine raayinta, shi ta saka ma yanzu ta fito ta same shi a zaune a mota yana amsa waya ta cikin kunnen sa dake sakale da Bluetooth. Tana zama ya dora mata wayarta akan cinyar ta, ta dauka ta jujjuya ta, sannan ta kunna ta hau whatspp dan ganin me yake faruwa. Wayar yake tayi idanun sa na kan titin ko sau daya be juyo ya kalle ta ba, har suka karasa gida, da murnar ta,ta kalle shi shima a daidai lokacin ya juyo bayan ya gama wayar wadda da dukka alamu akan aikin sa ne.

"Ki ajiye wayarki kusa dake, zan kiraki." Yace bayan ya samu waje yayi parking zata fita, gid'a masa kai tayi ta fita daga motar yana kallon ta, sai da taga ta fita sannan ta kalle shi

"Ba zan koma ba."

Sai tayi gaba da sauri ta shige part dinsu, dariya ta bashi ma, ya kada kansa yana hasaso yadda zai ciccibeta idan har tace zata masa gardama. Fita ya sake yi daga gidan dan zuwa ya samu Baba a chan guess house dinsa.

Babu kowa a part din nasu sai masu aiki duk suna chan bayan gidan in da ake taron bikin kafin azo kai amaren gidajen su, Amira ta kira a waya tace ta kawo mata kayanta, sai gata ita da Nu'ayma, ta saka suka fita Amira na tsokanar ta. Aunty ce ta hango su da suka taho wajen, ta kalli chan in da Maman take taga tana wani abun bata lura da Jiddan ba, tashi tayi ta riga su isa ta kama hannun Jiddan tace musu tana zuwa. Chan wajen da ba mutane suka je Jiddan ta gaishe ta, ta amsa cike da murnar ganin ta

"Ashe da gaske yake da yace zai kawo ki."

"Kece kika ce ya kawo ni?"

"Eh nice, sannan Baban ku ma yana son hadaku gaba daya yayi muku magana har Maman Fauwaz, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, duk abinda zai je ya dawo ki rike mijinki kinji? Karki ji tsoron kowa."

"Aunty menene? Akwai matsala ne?"

"Babu ko daya, nasan ba lallai ta amince da tarayyarku ba, musamman yanzu da duk muka gane Tariq yana son ki, zatayi kokarin baki matsala dole sai kin jajirce sannan ki hada da addu'a,."

"Wallahi ni Aunty tsoro nake ji."

"Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin ki."

"In sha Allah, nagode."

"Muje ciki, kije ki gaishe su ki dake kuma, mahaifiyar mijinki ce ta zama dolen ki."

"Toh." Tace a sanyaye, suka koma ciki Mama ta hango su, ta gimtse fuska sai taga Jiddan na tahowa in da suke a zaune da manyan kawayen ta harda matar gwamnan adamawa da matan manyan koshoshin kasar

"Jidda." Aunty Mimi ta tare ta tana kusa da in su Maman suke dan suna jin su ma

"Laaa, ina wuni?"

"Lafiya Lou, ban ganki ba gaba daya a kwana biyun nan, har Amira na tambaya tace kina nan."

Murmushi tayi bata ce komai ba,

"Karasa wajen su Maman ki gaishe su."

"Toh." Tace tana matsawa wajen su, ta russuna har k'asa ta gaida su, suka amsa a sake banda Mama da ta juyar da kanta gefe tana magana.

"Matar Tariq ce, shine babba a yaran Mama." Aunty Mimi tace musu tana murmushi

"Ah Hajiya Aisha har suruka ce dake amma bamu sani ba? Gata nan Masha Allah wallahi."

"Kun sani yanzu ai."

Tace tana dariyar yak'e, gefe kuma kamar ta jawo Aunty Mimi da Jiddan ta hada tayi musu shegen duka haka taji, tashi Jiddan tayi ta koma chan wajen su Amira, kafin daga bisani ta fice daga wajen ta tafi dubo Hajiya Yaya.

Da murnar ta,ta shiga kamar wadda ta dade bata ga Yayan ba haka taji, itama Yaya na ganin ta, ta dire abinda yake hannun ta

"Wa nake gani kamar matar malam nabahani."

"Kai Yaya?" Ta kwashe da dariya

"Toh Badamasi."

"A ah Yaya, ba ruwana wallahi."

"Ah gaskiya, kya tarewa miji wai ke dadi miji daga kwana daya har ya hure miki kunne ko?"

"Kai Yaya!"

"Allah kuwa, kin yi luf dake a dakin miji, yar kumama an san dadin aure."

"Na shiga uku, Yaya daga zuwa na?"

"Zuwan kenan?" Tace tana dariya

"Eh Yaya."

"Ai da naji shiru nace munafukan yara kaji su luf kamar basa duniyar nan.".

"Tsokanar mu dai kawai kike Yaya."

"Yo Allah ,shima munafukin yana fuffukar baya so baya so ashe duk munafurci ne."

"Me zan samu ne Yaya? Yunwa nake ji."

"Na shiga uku ni Hajara, ba dai horon yunwa yaron nan yayi miki ba, kai ni sai naga ma daga jiya zuwa yau kin fada sai uban fari da kika kara, gaya min gaskiya me yayi miki?"

"Innalillahi, Yaya ba komai fa, kawai dai abincin gida nake son ci, shiyasa, amma a kwana daya Yaya sai mutum ya chanja? Jiya ma fa muna tare."

"Toh ai abun nasa ne, kinsan kan sa da motsi har yanzu, sai kin yi hakuri dai."

"Hajiya Yaya kenan."

"Iya gaskiya ta na fada miki, tashi ki duba kitchen akwai flasks din abincin da Babar taku ta aiko, sai ki zuba ki cika cikin ki."

"Yawwa yanzu naji batu."

Ta mike ta shiga kitchen din ta zubo fried rice da chicken tazo ta zauna tana ci a hankali suna hira da Yaya. Har magriba tana wajen Yayan sannan su Amira suka shigo suke cewa Baba ya dawo ya saka a kira masa Ya Safiyya da Umaima part din sa, dan yi musu final nasiha tunda har masu zuwa daukar amaren sun fara zuwa. Kira ne ya shigo wayarta, ta kalli screen din taga an rubuta Capt.T, kai tsaye ta gane shine, ta daga a kasalance ta saka a kunnenta

"Ina kofar part din Baba."

"Na'am?"

"Kizo."

"Ok."

"Ba zai shigo nan din ba? Ko da yake ina yaga idon da zai hada dani? Ai be isa ba."

"Hajiya Yaya ta Ya Tariq." Amira tace tana dariya

"Na Jidda dai, wace ni?"

"Ai kece ta karfen."

"Jeki dai dadi miji, daga kira har kin mike jiki na rawa, ba dan jan ajin nan, ko ni da nake ba yar zamani ba na iya jan ajin nan tun zamanin kakanku, shima yasan Dije ba ta wasa bace, shiyasa ya kasa yi min kishiya."

"Yo ai ke Yaya surutun ki kadai sai ya kori kishiya."

Amira tace tana dariya, ita dai jidda fita tayi ta bar su suna gamzawa, ta hange shi tsaye a kofar part din Baban tsaye shi da kaamar Mama, suna magana amma idonsa na kan ta tunda ta nufo su, a tsorace take dan bata yi zaton zai kirata Mama na wajen ba, bata san me zata tarar ba, shiyasa ta dinga jan kafar ta, har ta isa wajen kanta a k'asa tayi sallama, shi kadai ya amsa ta kalli Maman wadda fuskar ta, take a matukar hade kana gani kasan ranta ya kai kololuwa a baci, bud'e kofar tayi ta shige, ya girgiza kai kawai yana kallo na, fuskar sa babu yabo babu fallasa amma ya nuna kamar ransa babu dadi.

"Muje." Yace yana nuna mata hanya, a tunanin ta part din Baban zasu shiga, amma sai taga ya nuna mata hanyar wajen da akayi parking motar, jiki a sanyaye tabi bayan sa, ya bud'e mata bayan motar ta shiga sannan shima ya shiga, sam yazo ya shiga wajen driver ya tada motar suka bar gidan. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (39)

***Cikin yanayin bacin rai Baba ya rufe ta da fada, ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, sosai ran sa ya baci akan abinda Maman tayi, shiyasa ya ki bari a kira Jiddan yace kuma Tariq ya dauki matar sa su wuce gida, ya kuma kafa masa sharadin duk abinda ya faru da ita sai ya basu mamaki shida mahaifiyar sa. Ranta a bace yake matuka bayan ta dawo ciki dan da Tariq din ya fita bin bayan sa tayi, ta tambaye shi dalilin da zai wulakanta ta haka har ya dauki Jiddan ba tare da sanin ta ba, hakuri kawai ya bata dan be san me zai ce ba, bata sake magana ba ganin Jiddan ta nufo su, sai kawai ta koma ciki in da ta tarar da Baban na yiwa Safiyya da Umaima nasiha. Tana shiga yace su tashi su tafi Allah yayi musu albarka, sai kawai tabi bayan su, suka fito yayi kwafa yana cike da haushin Maman, dan ta kaishi makura a yau zai kuma nuna mata shi yake da iko da ita da Tariq din, ba zai tsaya ta zubar masa da girma akan son zuciyar ta ba. Tafiya akayi dasu kowacce a nan Abujan zata zauna, duk da bacin ran da Maman ke ciki haka ta daure har aka tafi dasu, sannan tunanin ta ya dawo kan abinda ya faru, da irin maganganun da Baban ya gaggasa mata a gaban yaran. A daki suka sameta bayan sun dawo daga kai amaren, Aunty Nafi ta zauna a kubin ta, tana kallon yanayin ta

"Wai Yaya me ya faru ne? Ko duk tafiyar yaran ce?"

"Rai na ne a bace Nafi, wallahi."

"Me ya faru?"

"Kinsan wai ashe Tariq tun jiya ya dauki yarinyar nan suka wuce gidan sa?"

Zaro ido tayi

"Ba dai Jidda ba?"

"Ita, ace ya kasa fada min sai yau zanji a wajen ubansu, tsakani da Allah me Tariq yake so ya zama ne?"

"Gaskiya ba haka aka bar shi ba, Tariq din da muka sani daban wannan Tariq din daban, gaskiya an samu matsala, kema Yaya kin yi sanyi da yawa har kika bari haka ta faru, yanzu suna ina?"

"Sun tafi."

"Kika bar su kuma?"

"Ya zan? Baban su yace wallahi komai zai iya faruwa idan nace zan wani abu."

"Tab! Amma gaskiya da matsala, shikenan haka zamu zuba ido kishiya ta mallake miki babban d'a?"

"Ba zai yiwu ba ai, wallahi ba zan amince ba, duk tsoratarwa kawai yake shima, dole na tashi a tsaye."

"Gaskiya dai, ai ba zai yiwu ba."

"Menene shawararki?"

"Eh toh, tunda dai a yanzu ran Honourable ya baci sosai, zai iya aikata komai, ta karkashin kasa zamu biyo musu, tunda dai ke bakya son dan tainakon nan na wajen malamai."

"A ah bana so, wani abun dai daban."

"Yaushe Baban zai yi tafiya?"

"Jibin nan zasu tafi tare da Halima."

"Wannan karon kuma? Ah lallai kinyi sake wallahi."

"Ni duk wannan baya gaba na, ta d'ana nake."

"Toh kawai mu tura musu Salma da Amira gidan, tunda dama hutu suke dukkansu, sauran aikin sai mu barwa Salma tasan me zatayi duk zan dora ta akan komai."

"Kina ganin hakan zai yi? Amira fa bata da aminiya irin ta."

"Duk wannan ba matsala bace ai, ke dai ki bar komai a hannu na."

"Shikenan, dan Allah ayi duk yadda za'a yi, kafin ma a samu matsala wani abu ya shiga tsakanin su, yazo shima ya tattara ya tafi dan inaga a karshen satin nan zai koma Canada, dan naji Baban yana maganar suna ta masa mail ya ma kara sati,."

"Toh kinga in da aikin ki zai shigo, ki masa lamfo-lamfo ki nuna masa komai ya wuce zaki kula da ita ko baya nan, daga nan ita kuma sai mu nuna mata shege."

"Shikenan zan daure, yanzu ke yaushe zaki koma?"

"Ai ban ga ta tafiya ba, sai naga yadda aka yi, ba a barki ke kadai ba, amfanin dan uwan kenan."

"Toh kar mu bar Mimi taji maganar nan, zata bata komai."

"Wa?* Ta kama bakinta

"Ba zata ji komai ba, uwar iyayi sai ta hau fada mana magaana, kyaleta kice wani taro zan rakaki."

"Shikenan, Nagode sosai, sai kuyi magana da Salman, shi kuma Tariq din nasan yadda zan masa, Dan ba karamin aikin sa bane suna zuwa ya koro su wallahi."

"Zai aikata, musamman yanzu da baya ganin kowa sai figaggiiyar yarinyar nan, me zubin yunwa."

"Wallahi ko ganin ta kusa dashi bana son yi, dan dai yaran yanzu ne, baka isa dasu ba."

"Ba a hayyacin sa yake bane aj."

"Toh Allah yasa ya dawo hayyacin nasa, kar a samu matsala kiji ana amai an samu juna biyu."

"In sha Allah hakan ba zata faru ba, ina Allah ma ya kiyaye."

"Toh Amin." Tace a sanyaye

***Tunda suka dauki hanyar babu wanda yace uffan, shi gaba daya hankalin sa na kan abinda ya faru da yake ta gudu tsakanin iyayen sa, gashi be san yadda Mama zata dauki abinda ya farun ba, gashi shi kansa be san dalilin da yasa ya kafe ba har yake ganin Baban yafi ta gaskiya. Be so hakan ta faru ba, yafi so duk su fahimci juna tunda an riga an daura auren. Yana parking ya fice daga motar be ko kalli in da take ba, a hankalin ta bud'e kofar ta fito, jikin ta da yayi matukar yin sanyi taja zuwa cikin gidan tana ayyana abinda ya sashi a cikin yanayin da yake ciki. A tunanin ta zata ganshi a falo, sai taga wayam alamun ya shige ciki, mayafin jikinta, ta ajiye a saman kujerar ta nufi kitchen tana kallon hanyar dakin nasa, ta leka store taga an kawo musu kusan komai an lode, kayan abinci na ban mamaki dan kar tayi karya da sai tace babu ce kawai babu a ciki. Wucewa still idon ta na kan bedroom din nasa, ta bud'e nata ta shiga, ta ajiye komai a mazaunin sa sannan ta sauya kayan jikin ta zuwa riga 3 quarter da dogon wando wanda ya dan tsuke daga sama ya bud'e daga kasa, headband ta dora akan ta fito zuwa kitchen dan sama musu abinda zasu ci, tayi kuma amfani da damar wajen zuwa ta gano halin da yake ciki dan ko motsin sa babu. Dankali ta dauko ta feraye ta soya ta hada da fresh chopped tomatoes, peppers, carrot da onions, tayi mixing tayi seasoning nasa sannan ta dama masa oat dan taga alamun yana so sosai. A tray ta dora komai ta nufi dakin nasa, har taje kofar zata yi knocking sai tayi wani tunani, fasawa tayi ta wuce nata dakin ta ajiye tray din a gefe ta dauki turare ta feshe jikin ta dashi sannan ta yafa matsakaicin mayafi a kan kayan jikin ta, sannan ta dauki tray din ta nufi dakin nasa. Yana zaune akan sofa be cire ko takalmin dake kafarsa ba, gaba daya tunanin sa ya kare ya rasa me yakamata yayi, wa kuma ya kamata dole yayi wa biyayya ya farantawa a cikin su, kowanne a cikin su idan yayi masa ya bar daya be kyauta ba, zai kuma saka kansa a matsala ne, gefe daya kuma baya jin zai iya rabuwa da ita kamar yadda Maman take da bukata ba, sosai yake jin ta a ilahirin gaba daya zuciyar da ruhin sa, kamar idan ya rasa ta yayi wani babban rashi me girma a cikin rayuwar sa, sai yake jin kamar ta dade da shiga rayuwar tasa sani ne be yi ba sai yanzu. Idanun sa akan kofar sanda ta kwankwasa, ya kasa motsawa ballantana ya bud'e baki yace a shigo, sake knocking din tayi a hankali kaamar me tsoron taba kofar, cikin muryar sa da ta shige chan ciki yace

"Shigo."

A hankali ta murda handle din sannan ta turo kofar ta shigo rike da tray din, idanun su suka sarke waje daya, ita tayi saurin janye nata dan hango wani irin abu kwance a cikin kwayar idon nasa, wadda ta kasa fassara yaren da yake kwance a cikin ta. A gabansa ta durkusa ta ajiye abun hannun ta, sannan ta mike zata juya yayi saurin riko hannun ta.

"Ina zaki?" Yace yana mata kallon k'asa-k'asa

"Kitchen, na manta ruwa da lemo."

"Akwai ruwa a wannan fridge din."

"Toh juice din fa?"

"Bana bukata, sai dai idan zakiyi wani abun."

"Eh zanyi."

Tace da sauri, cikata yayi ya zamo kasa gaban tray din, ya bud'e plate din ita kuma ta juya ta bar dakin da tunanin ko zai dakatar da ita, amma sai taji be ce mata komai ba. Falon ta koma ta dinga zagaye haka kawai ta rasa me zatayi, daga karshe ta hakura ta wuce dakin ta, idon ta akan nasa dakin. Sai da ya gama cin dankalin da yayi masa dadi sosai, yasha oat dinsa ya wanke bakin sa da mouth freshner me dadin kamshi kamar mint, sannan ya jawo cable din system dinsa ya jona a chargy ya shiga kan mails din da akayi masa yayi replying wanda zai iya sannan ya duba available flight na karshen satin wanda zai bi, ya dade yana dudduba abubuwan da tsare-tsaren abinda ya kamata yayi kafin ya ajiye komai yaje yayi alwala yayi shafa'i da wutri, sannan ya cire kayan jikin sa ya rage dashi shi sai boxer da farar singlet ya nufi dakin nata. Rashin ganin haske a dakin ya sa ya gane tayi bacci kenan. Time ya kalla a wayar sa yaga sha daya har da mintuna, be san ya dau lokaci haka ba. A kanta ya tsaya ya dan haska fuskar ta da hasken wayar sa, bacci take tsakanin ta da Allah, gashin kanta da yazo har kusan rabin fuskar ta, yasa hannu ya gyara mata, ya durkusa a gaban ta yana kallon yar karamar fuskar ta gaba daya, so yake ya dan ja baya kad'an har ya samu amsar abinda yake so ya samu, ya kuma samu hanyar da Mama zata yarda ta amince da bukatar sa, baya so ya sabar mata da kanshi azo a samu matsala shiyasa yake son ya bi abun daki-daki. Saman kanta yayi kissing sannan ya gyara mata pillow da ke kanta a hankali yadda ba zai tashi ta ba, sannan ya mike ya fita daga dakin ya ja mata kofar. Da safe ta farka a tunanin ta zata ganshi a dakin, sai taga babu alamun ya shigo dakin ma kwata-kwata, tashi tayi jiki a sanyaye tayi abinda zatayi ta fito falon, tana fitowa yana shigowa sanye da kayan motsa jiki ya hada zufa sosai, damtsen hannun sa ta kalla tayi saurin dauke idonta, murmushi yayi k'adan ya zo saitin ta ya wuce ta gefen ta, ya shige ciki. Ajiyar zuciya ta sauke ta matsa tsakiyar falon tana duba abinda ya kamata ta sauya masa wajen zama, duk da babu datti ko kad'an amma sai da ta kara gyaran falon sannan ta shiga kitchen din. Toilet ya wuce kai tsaye yayi wanka ya fito yana goge jikin sa wayarsa tayi kara,ya sa hannu ya dauka ganin sunan Mama ya saka gaban sa faduwa, tattaro jarumtar sa yayi sannan ya daga.

"Ina kwana Mama?" Yace bayan ya amsa sallamar ta

"Lafiya lou, kun tashi lafiya?"

"Alhamdulillah."

Yace mamakin tambayar na kama shi

"Toh Yayi, yaushe zaka fito?"

"Anjima k'adan da nayi breakfast Mama."

"Toh ka zo inason ganin ka."

"Toh in sha Allah..."

"Madallah..."

"Mamma abinda ya faru jiya...?

"A bar wannan magaanar, ya wuce kawai, ka cigaba da shirye-shiryen tafiyar taka, Allah ya taimaka ya bada sa'a "

"Amin Mama."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull