Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 19

Sanadin labarina complete novel - Chapter 19

Sanadin labarina complete novel Chapter 19: Sanadin labarina complete novel Chapter 19. Yace muryar sa na bayyanar da tsantsar farin cikin da ya shiga. A…

4,462 words

Yace muryar sa na bayyanar da tsantsar farin cikin da ya shiga. A gaggauce ya karasa shiryawa, be tsaya ko abinci yaci ba ya tafi. Tana kitchen taji fitar mota daga gidan, ta fito da sauri amma tuni ya bar gidan shi da Faisal. Wani iri taji ta tsaya rike da spatula tana jujjuya abinda yake faruwa a kanta.

"Ko dai ya gama deciding rabuwa da itan ne?" Ta tambayi kanta, tunda dama ya fada ba sau daya ba sau biyu ba, ita ba spec dinshi bace ba, yanayin yadda ya d'an sakar mata shiyasa har ta fara samun hope, amma kuma idan ta tuna wasu mazan players ne na karshe, kuma zasu iya komai sai taji duk an dauke mata karsashin ta. A kasalance ta gama abinda take a kitchen din wanda take yi don shi yayi tafiyar sa ba ko sallama, juye komai tayi akan dinning ta wuce daki bayan tasha ruwan tea kad'an. Missed calls din aunty ta gani da ta koma dakin, ta kira ta bayan sun gaisa tace ta aiko Sam ya kawo musu abinci, tayi godiya suka ajiye wayar ta kwanta tana sake-sake a ranta har dai lokaci ya dan ja, sannan ta tashi tayi wanka ta saka wani silky material ta dan gyara fuskar ta da powder da eye liner sai lipstick ta dawo falon ta zauna tana kunna TV. Knocking akayi ta mike ta bud'e, yarinya ce ba zata wuce shekara goma ba, rike da flask sai wani babban basket a ajiye a gefenta,basket din Jidda ta dauka suka shiga ciki tana mata kallon rashin sani

"Ya sunan ki?" Tace bayan ta karbi kayan hannun ta, ta ajiye a saman dinning

"Godiya."

"Sunanki kenan Godiya?"

"Eh."

"Ok..." Tace tana gid'a kanta,

"Tace ki kirata wai."

"Aunty?"

"Eh."

"Ok."

Ta dau wayar ta kira Aunty, wai ashe sabuwar me aiki aka kawo mata, tunda Aunty taji Tariq din ma tafiya zai a karshn satin shine ta samo mata me aiki daga kauyen Abujan, ita Jiddan ma bata san tafiya zai ba, godiya tayi wa Auntyn tace yarinyar ta taso, ta zagaya da ita ta kitchen daga gefe kafin bq akwai daki da toilet a ciki, dakin yana da kofa ta cikin falon farko amma ginin kitchen ya dan boye ta,ta nuna mata a matsayin dakin ta. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (40)

***Kunsan sha biyu na rana tana zaune jigum har lokacin be dawo ba, abincin da tayi masa da safe ma sai Godiya ta bawa ta kai gate wajn masu gadi, sannan ta kara musu da wanda aunty ta kawo, taci ta zubawa Godiyan ta zauna tana kallon wani American movie har dai aka gama. Mikewa tayi a saman kujerar da nufin yin bacci taji an shigo gidan, da sauri ta tashi ta leka sai taga motar shi ce, tana tsaye jikin curtains din tana jiran fitowar sa sai taga Yaya ta fito tana magana tana kallon gidan, da sauri ta bud'e kofar ta fita, tayi tsalle ta rungume Yayan tana dariya

"Yaya sannu da zuwa." Ta sake ta bayan ta tureta tana dariya

"Bansan yaushe zaki hankali ba Jidda, karki zama kamar sauran shashasun chan mana." Tace

"Murnar ganin ki ce fa Yaya, wallahi duk na gaji ni kadai kamar mayya a zaune."

"Aure kenan yarinya, tukunna ma, akwai ciki da goyo."

"Innalillahi Yaya."

"Toh ai gwara ki sani, wuce ki kaini ciki kin barni a tsaye haka."

"Laa na manta wallahi." Tace tana kama hannun ta

"Dole ki manta, kai kuma idan ka gama zaman motar sai ka shigo ko?"

Waigawa Jiddah tayi da sauri, yana zaune a motar ya zuro kafafun sa waje yana kallon su, kallon ta yayi daga kasa har sama haushin a yadda ta fito na tirnike shi, shiyasa yaki cewa komai dan kamar ma tunda ta fito bata ma lura dashi ba. Da sauri taja hannun Yayan suka shige ciki, gajeren tsaki yaja ya fito daga motar ya rufe yabi bayan su. Be shiryawa surutun Yaya ba, gashi ba zai iya hanata biyo shi ba da tace zata zo, so yayi ma ya kwanta ya danyi bacci kafin la'asar amma yasan honourable Yaya ba zata taba barin sa ba. A tsakiyar falon ya tarar dasu Yayan ta zauna tana bayanin gidan da abinda be mata ba, ita dai jidda dariya kawai take taje ta kawo mata juice da ruwa ta zuba mata dan tasan minti kad'an aka kara Yayan zatayi complain. Zama yayi a daya daga cikin kujerun falon, ya bude hannunsa sosai yayi relaxing yana kallon TV

"Muje ciki Yaya, sai kin fi sakewa."

"Wa? Ni Allah ya raba ni da shiga dakin mijinki, naje nayi ubanme toh? Haram ba dani ba."

"Kai Yaya, bafa nan ba."

"Ko Ina ne ba zani ba wallahi, dakin ku zanje nayo me toh? A wanne dalilin ma? Kul naga kina kwasar mutane kina kaisu, baki ga yadda baban ku yake ba shi da yake da girma aka ma."

Turo baki tayi duk kunya ta rufe ta, ita matsalar Yaya bata shiru sai kayi niyyar mata gwanin ta sai ta gwasale ka, yana jin su be tanka ba, yayi biris kamar baya wajen sai da Yaya ta gama sababin ta sannan ya dago ya zauna sosai yana kallon Jiddan, kallon kinyi min laifi, sauke kanta k'asa tayi yace

"Yaya? Menene hukuncin mace ta dinga fita ba hijabi wajen wadanda ma Muharraman ta ba?"

"Haramun ne, babu kyau ai."

"Good." Ya fada har lokacin idon sa na kanta,kin dagowa tayi sarai ta gane da ita yake da kuma dalilin yin maganar.

"Yo mu a zamanin mu ma ina muka isa? Kaya ne za'a yi maka su zani da riga da mayafi duk na atamfa, dinkin manya-manya haka muke sasu kuma."

"Bari na kunna miki kallo Yaya."

Tace tana son dauke maganar, tayi saurin chanja channel din zuwa arewa24 aka ci sa'a kuwa ana favourite film din Yayan, sai ta maida hankalin ta kan kallon ta manta da batun da ake magana akai. Mikewa yayi hannun sa zube a aljihun sa, yace ta kawo masa abincin sa daki ya shige ciki, kallon Yaya tayi taga itama kallon ta take, a hankali murya k'asa k'asa tace

"Sai kin koyi jan aji fa, kina kai masa ki dawo nan."

"Toh Yaya."

"Yawwa yi maza, dan naga kanki rawa yake ke dadi miji, masu irin halin Malam baa musu irin wannan rawar kan "

Jidda na jinta ita dai tayi gaba zuwa kitchen ta hado abinda zata hado ta zo ta wuce ta shiga ciki, baya dakin ta dai ji motsin ruwa a toilet sai kawai ta ajiye masa ta fice kafin ya fito ya tsaida ta har Yaya taga ta dade. Tana komawa Yaya ta kalle ta

"A kofa kika ajiye masa abincin Hala?"

"A ah na kai har ciki."

"Amma ko sakwan biyu fa bana jin kinyi."

"Ba kince kar na dade ba."

"Eh amma ai ba ina nufin kina shiga ki fito ba."

"Hajiya Yaya, bari na koma toh."

"Ban ce ba, karo min naman nan."

"Toh." Ta kara mata ta zauna suna hira, tana fada mata yadda take so tayi bata son rawar kai, dariya kawai jiddah take dan tasan halin Yaya anjima k'adan sai ta chanja zance shiyasa ma take biye mata a duk yadda tazo. Bayan la'asar driver yazo daukar ta, har lokacin Tariq ko lekowa be sake ba, shiga Jidda tayi dan ta fada masa, ta same shi yana bacci, baccin la'asar da bashi da amfani, har gaban gadon ta karasa tana kallon fuskar sa, dan jim tayi a tsaye kafin ta juya da nufin barin dakin ya riko hannun ta, ta juyo da sauri still idanun sa na rufe har lokacin,

"Mene kike kallo na."

"Na'am? Ni?"

"Am dama Yaya ce zata tafi shine nazo zan fada maka naga kana bacci shine zan fita."

Fuzgo ta yayi ta fado kan gadon, ya gyara mata kusa dashi yana kallon fuskar ta, runtse idon ta tayi taki yarda ta bud'e, murmushi yayi ya matse mata hannun da ya rike tayi saurin bud'e idon ta,

"Yanzu ma a hakan zaki sake fita wajen?"

Ya rike gefen rigar jikin ta, da sauri ta girgiza kanta

"Ba zan sake ba, dan Allah kayi hakuri Yaya na jira na."

"Ba zaki fita ba toh." Waro ido tayi da sauri

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi tace kar na dade."

"Ni kuma mijinki nace ba zaki fita ba, itama in banda abinda menene na zuwa gidan newly weds, idan ta gaji zata tafi gobe ba zata dawo ba."

"Na shiga uku, ka rufa min asiri dan Allah."

"I'm serious, ba in da zaki."

"Na shiga uku, Amma..." Hannu yasa ya rufe mata bakin ta, tayi tsit tana zaro ido, shafa lips dinta ya shiga yi a hankali yana zagaya hannun sa akan dan karamin bakin nata.

"Kina sake magana I ll kiss you."

Rufe idon ta, tayi kirjin ta na bugawa da sauri da sauri, ta rasa dalilin da yasa yake mata haka, kallon ta ya cigaba da yi bashi da niyyar kyale ta, kuma yana sane sarai yasan shikenan sun tabo Yaya, zai so yaga yadda drama zata kare dan yau sai ta kusan kasa bacci akan hakan. Shiru ne ya biyo bayan maganar da yayi, ta dan bud'e idon ta kad'an taga ya rufo da kansa saman fuskar ta, so close da ko yaya ta sake motsawa fuskar ta zata taba tasa, juyar da kanta tayi dayan barin da nufin tayi magana

"Dan Allah..." Ai bata karasa ba ya tallafo fuskar ta da hannayen sa biyu ya juyo da fuskar ta yana hade bakin su waje daya.

Shiru shiru babu jiddah babu alamar ta, dan daga murya Yayan tayi ta kira sunan ta amma shiru, kama baki tayi cike da mamakin Jiddan, wato itama A ce tana mata kallon sum-sum ashe munafuka ce irin Tariq din, kwafa tayi ta fita fice tun a mota ta fara yiwa Isyaku da Sam mita, su dai jin ta kawai suke Isyaku yana bata hakuri ya samu suka kaita gida sannan ta kyale su. A compound din suka hadu da Fauwaz aikuwa ta fara fada masa wulakancin da Jidda da Tariq sukayi mata dan taje gidan su

"Ashe Jiddan ma munafuka ce ban sani ba? Ta koyi halin mijin nata ni zasu wulakanta?"

"Ai kema Yaya ban da abinki, ai ba'a zuwa gidan sabon aure yanzu, ba irin Malam dinki bane na zamanin dah, dan ma Ya Tariq din ne idan nine da police dog zan hada ki su rarakamin ke."

"Sai dai su raraka ubanka bani ba, bakin mugu."

"Allah kuwa, zuwa zaki ki hana mu shan soyayyar mu."

"Idan kunga dama ku cinye juna tsabar soyayya, kuma ba gidan Tariq ba ma babu wanda zai sake zuwa gidan sa a cikin ku bare ku cimin mutunci, ba dai akwai ciki da goyo ba, muna nan zaku zo har in da nake."

"Allah ma kar yasa muzo rokon abu wajen ki Yaya, wallahi dan zaki wulakanci ba dan kad'an ba."

"Zaka maimaita wannan maganar, kuma ko kafarka na sake gani a gida na sai ka gane baka da wayo."

Tayi gaba shi kuma ya cigaba da kyalkyala dariyar da yake, sosai ta shaki abinda Fauwaz din yai mata ga mamakin Jiddah, duk sai ta kasa zaune ta kasa tsaye ta dinga mita ita kadai.

***Sakin ta yayi bayan yaji tashin motar su Yayan, juyar da fuskar ta tayi haushin kanta da kunyar Yaya na kamata, toh da wanne ido ma zata kalli Yaya yanzu? Me yasa duk abinda ya fada akanta ta kasa dake masa a duk sanda irin haka ta faru sai ta bada kai bori ya hau, daga baya kuma tazo tana jin haushin kanta. Da kunnenta taji yana cewa ita ba spec dinshi bace ba, amma kuma why? Maganganun da ya fada ranar da ya fara dawowa, da wanda ya maimaita daga baya ne suka shiga dawo mata daki -daki, mikewa tayi tana bata fuskar ta, ya bita da kallo ganin yadda ta sauya lokaci daya

"Menene?" Yace yana zuro kafafun sa ya sakko daga gadon

"Ka bari idan ka samu spec dinka sai kayi yadda kake so,ni ba type dinka bace ba."

"Jidda?" Yace yana mikewa, sake bata fuskar ta tayi sosai dan ma kar ya samu dama akanta,

"Me kike son cewa?"

"Nace ni Jidda ba type dinka bace, ka samo daidai da kai ni nayi maka siranta da yawa, kuma maganar aure ba zata taba yiwuwa a tsakanin mu ba."

"Subhallah, me ya faru? Why are you saying all this?"

"Abinda kace kawai nake maimaitawa, please ka kyale ni ka samu daidai da kai."

Kallon cikin idon ta yayi, be hango komai ba sai iya gaskiyar ta akan maganar da take yi, yana tsaye ya rasa abinda zai ce dan be yi tunanin taji duk abinda yace wa Fauwaz ba, be rikice ba a zahiri sai dai a badini wani irin tsoro ne ya shige shi, ya shiga takowa zuwa in da take a tsaye, da sauri ta tura kanta ta fice daga dakin, ta nufi dakin ta ta shige ta rufe da mukulli. Tsayawa yayi a falon yana kallon kofar da ta shiga, ya dade a tsaye sai ya juya ya samu kujera ya zauna yana jiran fitowar ta. Dama wajen goshin magriba ba ne, saboda haka yayi alwala a toilet din falon ya sake tsayawa ko zata bud'e amma har akayi kiran sallah bata bude ba, masallaci ya wuce ana idar da sallar ya sake dawowa amma still dakin a rufe yake, gashi be san ta in da zai fara yi mata knocking yace ta bud'e ba. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (42

Mota ya koma ya dauko bakin glass dinsa ya saka sannan ya shiga wajen Yayan, share shi tayi har ya zauna yana kallon ta, ta cikin glass din yana so yayi dariyar yadda ta turbune fuska ta kautar da kanta a dole ba zata kalle shi ba

"Ina kwana?"

Shiru

"Yaya ina kwana?"

Nan ma shiru kamar ba da ita yake ba, waka ta fara tana karkada kanta tana habaici abinda ya bashi dariya yayi k'adan yana mikewa

"Tunda ba zaki kulani ba bari na tafi."

"Da uban me ya kawo ka? Ko ka nuna min ku tantirai ne kaida Jiddan?"

"Me mukayi?"

"Oho, duk abinda ma mutum yayi dan kansa."

"Kizo mu tafi ki bini toh."

"Idan na bika ba suna na Hadiza ba kenan, ni da gidanku ai har Abada, Allah ya taimaka ya bada sa'a."

"Toh kiyi hakuri kinji?"

"Ni kyale ni, sum-sum dakai kamar mutumin arziki, har ita Jiddan ashe itama munafuka ce, za tazo har in da nake ne."

"Kunfi kusa." Yace yana mikewa

"Sai kinzo Yaya."

Ya zura hannayen sa cikin aljihu ya fice, ya nufi wajen masu gadi ya zauna yana sauraron hirar da suke duk da be saka musu baki ba, hakan ba karamin dadi yake musu ba, sam yaran gidan kaf basu da girman kai ko kadan haka ma fauwaz da yafi Tariq din magana yake zama dasu har suyi hira sosai. Ana haka shima Fauwaz ya dawo ya sameshi a wajen zai zauna yace su je ciki. Tashi yayi yabi bayan sa suka jera yana tambayar sa karfe nawa su Baba suka tashi. Suna shiga ciki ya kama hannun Fauwaz din ya murde shi ya baya, ya fara ihu

"Washhh!!! Da zafi fa."

"Me yasa mukayi magana kaje ka fadawa J..."

"J?"

"Jidda."

"Oh wacce magana?"

"Maganar da mukayi ranar da na dawo, how comes ta sani idan ba fada mata kayi ba."

"Oh tab! Ai tana tsaye time din tazo kawo maka ruwa da juice taji komai."

"Shit." Ya sake shi yana dunkule hannun sa

"Me ya faru?"

"She's punishing me."

"Kamr yaaya?"

"Tace na kyale ta, naje na nemo type dina, and since then ta daina kulani."

"She's right, shine zaifi sauki."

"But ai da ba haka take acting ba, tana min magana ko da kadan ne, yanzu fa ko kallona batayi, kaamar ma ta tsane ni."

"Abun ya dameka sosai?"

"Sosai, yadda baka tunani, I'm thinking of not going again, bansan idan na tafi ko zata ce ta fasa ba."

"Then kayi mata bayani."

"Na me?"

"Kace mata mistake ne ba abinda kake nufi ba, ka fada mata you want her so bad baka so ka rasata, da dai irin wannan stuffs din, ka dai gane."

"Wa ni? Noo ba zan iya ba, kawai dai bana so ta daina min magana, amma ni ba zan iya karya ba."

"Karya?"

"Ehen, na fadi abinda nasan ba haka bane."

"Tirkashi, then ka kyaleta kawai, tana da every right da zatayi fushi ta daina kulaka, let her be, zan mata magana idan Baba yazo sai ta same shi nasan zai fahimce ta, kai kuma sai ka samo type dinka, a think hakan yayi."

"Idan ka fada mata haka wallahi zan iya fasa bakin ka, ni ba haka nace maka ba,I just need a solution ne kawai."

"Toh Ya Tariq ya za'a yi? Baka son ta, she's not your type, dan babu bukatar cigaba a zaman ku tare, free her Dan Allah, nasan zata samu..."

Ai be kai karshe ba yaji ya bige bakin sa, ransa a bace ya balbale shi da masifa, kar ya ya sake ya kuma sako maganar wani, sai da ya gama sannan Fauwaz din yace

"Kayi tunani dai, if not zaka rasa Jidda."

"Idan Mama ta dawo kace mata nazo, I'm going."

"Ok."

Juyawa yayi ya fita shi kuma Fauwaz ya zauna yana mamakin ace wai Ya Tariq din ba zai iya gane halin da yake ciki da kansa akan jidda ba, ko kuma dai ya gane kawai dai tsabar ki fadi ne be sani ba, shafa bakin sa yayi Allah yaso be fasa masa shi ba a garin kishi dan yau zai je wajen Hidaya da yamma.

Da hannu daya yake tuki dayan yana danna counter kansa a gaba yana kallon titin da yake dauke da tsirarin ababen hawa, gida ya nufa tunda ya baro gidan su yayi zaman sa a central mosque sai da akayi magriba sannan ya nufi gidan kansa cike taf da maganar Fauwaz da ya wuni yana bitar ta ya kasa gano in da ya kuskure, a tunanin sa baya bukatar ya bude baki ya fad'awa Jidda komai, ba kuma ya jin zai iya nan kusa amma kuma ya kamata ace ta masa uzuri ta gane yadda ya damu da ita sosai, sau wajn goma a yinin ranar yana gwada kiran wayarta sai tayi kamar zata shiga sai ya katse yana maimaitawa kansa babu amfanin kiran. Horn yayi Yahaya ya taso da gudu ya bud'e get din ya shigo yayi parking sannan ya fito ya jefawa Faisal key din, ya gaji da tuki ba zai sake ba har sai ya dawo, Kano zasu je jibi kuma a jirgi zasu duk abinda zai taso ma a cikin garin Faisal din ne kawai zai kaishi

"Akwai baki a gidan ne?"

"Eh Amira ce da wata."

"Ok." Yace yana yin gaba, sai kuma ya juyo

"Ka zama a kusa ko yaushe zan iya kiran ka, a wanke black car din chan da ita zan fita gobe in sha Allah."

"Ok sir, an gama."

Haurawa yayi zuwa kofar da zata sadaka da cikin gidan ya sa key ya bud'e, suna zaune su uku a falon Jidda da Amira na zaune a kujera daya sai Salma dake kwance tana danna waya, da sauri ta tashi zaune tana gyara zaman ta, riga da skirt ne a jikin ta da suka dan kamata babu ko mayafi, tunda tazo uffan bata cewa Jiddan ba, itama bata kulata ba suna ta hirar su da Amira har Ya Safiyya ta kira Amiran tace ta bawa Jiddan ta tashi daga wajen taje sukayi wayar ta dawo ba tare da sun ji me suka tattauna ba. Mikewa tayi tana fadada fara'ar fuskar ta, ta nufe shi daga in da yake tsaye yana zare takalmin kafarsa daga tsaye, kallon ta yake tana karasowa har tazo daf dashi, ta dan russuna kad'an tace

"Sannu da zuwa." Fuskarta dauke da murmushi, murmushiin ya maida mata yace

"Thank you." Yana mika mata hannun shi, dan noke kafadar ta tayi ta mika masa hannun a kunyace duk nauyin shi da su Amira dake zaune a wajen na cikata, amma dole tayi bayan wayar sa sukayi da Ya Safiyya dan ba zata taba bari Salma ta samu galaba akanta ba. Idon sa akan lips dinta da yasha jan janbaki me kyau da sheki, kamshin turaren da tayi amfani ya cika ko ina ya sashi a wani yanayi. Hannun ta sarke da nasa suka karasa shigowa tsakiyar falon

"Ya T... welcome." Salma tace haushin Jiddan da abinda ta aikata na tike ta

"Yawwa." Yace yana kallon Amira da kunyar zuwan musu gida duk ta cikata

"Welcome Yah."

"Kece munafuka ko?" Yace yana hararar ta

"Allah Ya ba ruwana wallahi."

"Naji."

Yace suka wuce zuwa kofar da zata kaisu dayan falon, yasa hannu ya bud'e musu ska shiga, suna shiga tayi saurin janyewa tana kin kallon sa, tsayawa yayi saroro yana duban ta, dakin ta, ta shige ta barshi a tsaye a wajen cike da mamakin ta!

*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

_(Where every flavour tells a story .....)_

*_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_

_08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_

_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_

_MU NA YIN:_

*_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_*

*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*

*_LOCAL DRINKS:_*

_HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_

_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._

_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._

_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_

_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_

_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*

5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (41)

***Ya dade a zaune a falon dan anan ya kusa cinye fiye da rabin daren sa hoping ko zata bud'e amma har ya gaji ya tashi ya shiga ciki ya gyara pillows din dake kan doguwar kujera dake dakin ya kwana dan baya jin hawa gadon. Juye -juye ya dinga yi yana tunanin maganganun, ya fadi dukka kuma ko kad'an yasan be kyauta ba, ya yi kuma dana sanin furtasu duk da be yi tunanin Fauwaz zai fada mata ba, tunda shi dai ba a gabanta yayi waccar magaanar ta farko ba, ko shine dole yaji babu dadi ita ta ma yi hakuri sosai. Kunya ce ta lullube shi tunawa da yadda ya gama cika baki kuma yazo yana kissing din yarinyar mutane bayan ta san duk abinda yace a kanta. Fauwaz ne ya cuce shi tunda dai da be fada mata ba fuskewa kawai zai yi duk da ya taba fada taji ya san kuma taji din amma maganar bata kai munin wannan din ba. Da wuri ya tashi bayan ya samu yayi baccin kad'an, ya fito falon ya zauna sanye da jallabiya me gajeran hannu yana jiran fitowar ta. Bayan kusan awa daya da zaman sa sannan yaji ana murd'a key din dakin, yayi saurin dauke kansa daga kallon dakin ta fito fuskar ta a gaba bata ko kalli bangaren da yake ba, ta fice zuwa dayan falon na farko in da ta shiga kitchen ta duba abinda zata duba ta dora ruwan tea, falon ya dawo ya zauna idon sa na kan kitchen din yana jin motsin ta, ya kunna TV pretending kaamar yana kallo ne amma rabin hankalin sa yana wajenta. Godiya taje ta kirawo tazo ta tayata ta soya musu doya da egg sauce ta dafa ruwan tea me kayan kamshi ta jera akan saman Iceland din ta zuba ma Godiya nata tace taje taci sai tazo ta gyara kitchen din. Karba tayi ta fita daga kitchen din ita kuma ta d'aga cikin wajen oven din zata saka ragowar man da tayi amfani dashi ya shigo ya tsaya daga jikin island din yayi folding hannuwansa a kirjinsa yana kallon bayan ta. Dagowa tayi ta juyo ta ganshi tayi saurin dauke kanta ta dau plate din da ta zuba nata rike da cup tazo zata wuce shi. Saurin tare hanyar yayi ta dan ja baya da sauri

"Goodmorning tunda baki iya gaisuwa ba."

"Ina kwana?" Tace a gajarce ta nuna masa hanyar

"Zan wuce."

"Fushi kike dani?"

Girgiza kanta tayi,

"Ni ba fushi nake ba."

"Toh menene, kika chanja all of a sudden."

"Ba komai, zan wuce."

"Ba in da zaki, sai kin fada min."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull