Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 24

Sanadin labarina complete novel - Chapter 24

Sanadin labarina complete novel Chapter 24: Sanadin labarina complete novel Chapter 24. Ya hau kicin-kicin zare mata Hijab din ta rike kam tana girgiza…

4,424 words

Ya hau kicin-kicin zare mata Hijab din ta rike kam tana girgiza masa kai, rike ta yayi a jikin sa ya karasa zare Hijab din ya zama daga ita sai undies din, da sauri ta rukunkume shi ta chusa fuskar ta a tsakanin kirjin sa wata iriyar matsananciyar kunya na lullubeta hade da tsananin tsoron abinda zai iya aikata mata. Ji tayi ya daga ta sama chak, ya sumbaci saman lips dinta sannan ya nufi kofar barin dakin da ita, chusa fuskar ta tayi a kirjin sa taki dagowa har suka dangana da dayan dakin sannan ya dire ta yana kashe dukkan hasken dakin dama curtains din a rufe suke kasancewar masu kauri ne ya saka duhu ya mamaye dakin gaba daya sai dan haske kad'an. Rage kayan jikin sa yayi ya kwanta yana hade jikin su waje daya, ya shiga kissing din ta a hankali tun daga saman goshin ta har zuwa wuyan ta, cikin wani irin salo da ya kusan mantar da ita a wacce nahiya take, shi kansa yana daurewa wajn bin ta a sannu ne saboda tausayin ta da yake yi amma he's eager , so eager fiye da first time dinshi wanda shi kansa yasha wahala musamman da first time dinshi kenan, sai da ma ya wahala sosai kafin ma ya gane in da ake dosa gaba daya. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (51)

***Da kansa yake driving din hannun sa daya akan steering while dayan na rike da hannun ta dake saman kan gear yana murza shi a hankali. A haka suka karasa gidan da yake dan cike da mutane saboda dawowar Baban. Sai da ya shiga ciki sosai sannan yayi parking. Da dan saurin ta, ta kama handle din zata fita ya riko ta, ta juyo yayi kissing din lips dinta sannan ya cire mata lock din, murmushi me tsada ta sakar masa, ya maida mata sannan ta fita, yana kallon ta har ta shige ciki, kashe motar yayi ya fito yana saka bakin shade ya toshe idon sa.

Da Usman ta fara cin karo ya dane ta yana kiran Ya Jidda. Da sauri Aunty ta fito sai ta tsaya tana kallon Jiddan cike da mamakin ganin ta

"Wa nake gani?"

"Aunty nice." Tace a kunyace tana rike hannun Usman din da yake cike da murnar ganin ta

"Lallai sannu Tariq, shine ya sako ki a gaba kuka taho gida?"

"Kai Aunty, ina wuni?"

"Lafiya Lou, toh ai gaskiya ce, kwana nawa yau dududu."

"Ai an daina irin wannan aunty."

"Lallai, toh kuna lafiya dai ko?"

"Eh aunty." Tace a dan kunyace tana tuna abubuwan da suka faru tsakanin ta da gogan nata

"Ya targaden?"

"Alhamdulillah, yayi sauki."

"Masha Allah, Allah ya kara sauki, na zata ma fa gobe Tariq din zai tafi. Shiru kuma ban ga yazo ba."

"Nima dai ban ga yana shirin tafiyar ba."

"Ok kila ya d'aga, anma naga ya karbi passport dinki? Ko tare zaku tafi ne?"

Ta dan bigi cikin ta, girgiza kai jiddah tayi

"Nima dai ban sani ba, ranar dai yace min wai zan bishi?."

"Sai kika ce a'ah?"

"Ban ce komai ba."

"Kaji sokuwa, me zaki zauna kiyi bayan zaman jiran sa da kikayi a baya? Sannan ke ba kin huta da kowa ba, ba'a ganki ba bare a kafa miki kahon zuk'a."

Shiru Jiddan tayi, dan ita har hango tafiyar tasu take tare kawai dai bata son nunawa auntyn ne

"Kin je kin gaida Maman Fauwaz din ne?"

"A ah nan ya fara kawo ni, yace zai ga Baba ne."

"Ok, sai kuje da Usman ki gaishe ta, Yaya ma tana nan tana jiranki, kun mata laifi wai."

"Innalillahi, Hajiya Yaya."

"Zakuyi mata bayani tana nan tana jan maganar dan sosai ranta ya baci wallahi."

"Ni wallahi bani bace Ya Tariq ne."

"Sai kije ki bata hakuri, dan shi kam dama sun saba."

"Taso Usman ka rakani."

"Bari na karasa shiryawa kafin ku dawo."

"Ok." Tace ta kama hannun Usman suka fita bayan ta gyara yafen mayafin ta sosai dan ta lura baya so

***Wajen Mama suka fara shiga bata nan tana part din Baba, tana zaune bata ma san Maman bata nan ba Maryam ta fito da murnar ta sai ga Amira ma sun fito tare da Salma. Chak ta tsaya tana kallon Jiddan dake zaune suna magana da Maryam. Wani kululun abu ne ya zo mata makoshi, ta karaso tana yamutse fuska ta zauna a kujerar dake gefen su tana dauke kanta ta dauki remote tana kokarin chanja channel. Babu wanda ya kulata a cikin su duk sun rude da ganin Jiddan a ganin ta ma kamar sun kasa zama waje daya musamman Amira da take tsokanar Jiddaan da tayi fresh ta kara haske ita kuma tana cewa taji tsoron Allah. Tsaki taja wanda ya jawo hankalin su kanta, ta tabe baki tana kallo TV

"An bi an ishe mu da ihu kamar yau kuka taba ganin ta."

"Ina ruwanki?" Maryam tace tana hararar ta

"Kinsan ta Mero, wai Ya Tariq fa take so ashe shine duk tasa wa Jidda kahon zuk'a."

Gaban Jiddan ne ya fadi maganar ta dan tsorata ta, Amma sai ta daure tace

"Ayya abun tausayi, ai Baby nawa ne ni kadai, ta gama haukan ta, ta hakura na tsare gaba na tsare baya."

"Correct my girl." Maryam tace sai sukaa tafa da Amira suna kwashewa da dariya

"Zan baku mamaki wallahi dukkan ku. Mtsw!"

Ta mike sai gashi ya shigo, ita kadai ta ganshi dan su suna kallon ciki ne basa ganin me shigowa, kuma ta kofar baya ya shigo alamun daga wajen Baba yake

"Allah nasan irin su Ya Tariq ba dai iya love ba, kinsa masu shiru-shirun nan wallahi hmm, bomb!!!"

"Ba ruwana idan yaji ke kika sani." Tace tana musu dariya, Maryam ce ta karbe

"Ai gaskiya ce ,Allah sa nima Salim dina ya iya soyayya, mu soye mu rakashe abun mu."

"Amin wallahi."

"Ehem ehem."

Yayi gyaran murya yana gimtse fuskar sa, yaji duk abinda suka ce tun daga farkon hirar da Jidda ta kirashi da baby da kuma wadda suke yi yanzu, dadi daya yaji da Jidda tayi hankalin boye sirrin su, wanda mata da yawa yanzu suke bayyana sirrikan su ga kawayen su bayan haramun ne Allah ya hana. Diriricewa Amira da Maryam suka yi dan basu taba kawo zai shigo shashen ba, idon sa akanta tayi saurin sadda kanta k'asa l

"Ya Tariq sannu da zuwa, ina wuni? A kawo maka ruwa?

" Ko juice?" Maryam ta ce

Duk sun rikice musamman da suka san ya ji komai da dukkan alamu

"Munafukai." Yace a hankali, zamewa sukayi suka gudu ya zama daga shi sai Jidda sai Salma dake tsaye kaamar wanda aka dasa a wajen

"Come here baby." Yace yana nuna mata gefen sa da yake zaune, pretending kamar be san da zaman Salma a wajen ba, wanda yake ji zai iya tashi ya jata har waje sannan yace securities su yi mata shegen duka ita da uwar ta. Har ba zata taso ba saboda kar Mama ta fito sai kuma ta tuna da Salma dake falon, tashi tayi a nutse ta isa wajen nasa maimakon ya barta ta zauna a gefen sa sai kawai ya dora ta akan cinyar sa, wani irin waro ido tayi tayi kamar zata tashi ya zagaye ta da hannun sa ya hanata tashin yana kashe mata ido daya

"Maama?"

Tayi kamar a hankali wanda shi kadai zai iya ji, yasan Mama ba zata shigo yanzu ba shiyasa ma yayi hakan.

"Nayi missing dinki, so much."

Yace yana saka hannun sa ya gyara mata lipstick din bakin ta yana kallon yadda lips din ta suke shining kamar yayi kissing dinsu.

Da sauri Salma ta juyo yaji sanda ta bud'e kofa ta shige ya saki murmushi yana gid'a kansa. Yunkurawa tayi zata tashi again ya sake hana ta

"Karki kara kokarin tashi idan bani nace ba."

Kofar ce ta sake budewa sai kuma salati ya biyo baya da karfi, Aunty Nafi ce Salma na bin bayan ta

"Tariq menene haka? Wanne irin rayuwa ce wannan?"

Yi yayi kamar be ji ta ba, ya kusanto da bakin sa daf da na Jidda da kunya ta hanata ko da motsi ne, bata san dalilin sa nayiin hakan ba,ji tayi yayi mata peck a gefen kuncin ta, zuwa lips dinta na sama, yayi kamar zai hade bakin su waje daya da sauri Aunty Nafin ta tura Salma suka koma dakin ganin abin na Tariq yafi karfin tunanin ta. Cikata yayi ta tashi da sauri tana kin kallon sa,shi kuwa murmushii kawai yake idon sa a toshe da bakin glasses.

"Kananan marasa mutunci."

Yace a zuciyar sa yana relaxing sosai a saman kujera. Hanyar fita tayi ta dago ya kalle ta

"Baby ina zaki?"

"Wajen Yaya."

"Ok bari na zo muje." Ya mike tayi saurin cewa

"Dan Allah kar muje tare."

"Why? Ke da babyn ki?"

"Ni dai dan Allah."

"Me yasa toh?"

"Kunya zaka sa ni ji."

Dariya yayi k'adan ya koma ya zauna

"Shikenan sai kin dawo."

Juyawa tayi ta fita shi kuma ya cigaba da zaman jiran Mama wadda ya baro su suna fafatawa da Baba akan abinda ya faru.

**Kaamar munafuka haka ta shiga wajen Yayan tana labewa, Sarai Yaya ta ganta amma ta maze ta tsuke fuskar ta tana yin kamar bata ga Jidda ba

"Assalamu alaikum." Tayi sallamar tana shiga gaba daya

"Amin." Yaya tace a gajarce

Kusa da ita Jiddan ta zauna ta kauda kanta gefe ta koma dayan gefen ta sake dauke kanta,

"Dan Allah Yaya kiyi hakuri."

"Da akayi me?"

"Komai ma, dan Allah wallahi ba laifi na bane Allah Yaya, dan Allah."

"Ba dai kin zabi miji ba? Ke dadi miji ko? Har kike rawar kai ki shige dakin miji da tsakar rana kiki fitowa ko?"

"Na shiga uku."

"Kiyi hakuri dan Allah."

"A ah ai ba komai, ba komai kinji? Masu hali irin Malam ma kaza aji ya ka cika bare kana bin su, ni da zan siyar miki kima da darajar wajen sa shine kika watsan k'asa a ido kika shige daki kukayi mukus ko? Dadi aure "

"Na shiga dari ma ba uku ba." Ya furta a hankali, sai kuma a fili tace

"Ba haka bane Yaya, kiyi hakuri ni dai dan Allah."

Noke kafardar ta, tayi

"Dan Allah Yayarmu, Hajiya Yaya ikon Allah, ki taimaka kiyi hakuri ko na zauna na fasa komawa."

"Ki zauna a ina?

"Anan."

"Kaji mukafukar yarinya, ni zaki ma kinibibi?"

"Da gaske Yaya."

"Wasa kike ko?"

"Da gaske mana."

"Toh ma hakura,."

"Ni idan bakya so sai nayi zamana anan din kawai."

"Nace miki na hakura, ba in da zaki zauna da ya wuce dakin mijinki, na bar maganar ma kwata-kwata, shikenan?"

"Toh shikenan Yaya, amma da..."

"A bar maganar, samo min yoghurt a firij na dan sha."

"Hajiya Yaya da cin dadi."

"Arzikin d'a, ke ma ki zage jiki ki zazzago su baka san wanda zai jikan ka ba."

"Nawa ma kikayi Yaya?"

"Sha hudu nayi."

"Wai!"

"Biyar ne suke raye a yanzu."

"Masha Allah."

"Haka mukayi haihuwar nan da wahala ma ba irin ta yanzu da gata yayi muku yawa ba, wai tsabar lalacewa wai da miji ake jego, mu zamanin mu ka isa? Ai kai da miji sai kayi arba'in har ba irin Malam masu bakin hali ba."

"Zamanin ne ya chanja Yaya."

"Ai na gani, sai a shige daka da miji a bar me zaman dabaro tana hamma da zare ido, yaran yanzu sam basu da ta ido wallahi."

"Zamanin ne fa Yaya."

"Ai sai ku karata ga ku nan gasu, shiyasa ni ba gidan wadda zanje zaman dabaro kin ganni nan, kowa ya karata chan."

"Uhum." Jidda tace tana hasaso yadda zata kaya idan akace wai itace da ciki ko zata haihu.

***Fada sosai Baban yake ya dauki waya ya kira Tariq yace ya dawo, dama cewa yayi ya basu waje zai kirashi, sai gashi nan ya shigo ya kalli Mama da take cikin tsananin tashin hankali, ta so ita ta fara sanar da Baba maganar tayi masa bayani yadda zai gane amma sai akaci rashin sa'a ya sani wanda bata san ta wajen wa ba, amma kuma yace text akayi masa shiyasa tayi tunanin Nafi ce ta tura masa text din, bata san haka zata mata ba, gashi ta kara sata a matsala dan Baba yace babu ruwan sa tunda har ta iya tura Yara gidan Tariq din duk da tasan rashin dacewar hakan shima kuma ba zai iya komai ba illa ya tursasawa Tariq din auren Salmar kamar yadda yace Maman na so tunda da bata so ba zata fara tura su ba, babu irin bayanin da batayi masa ba akan Nafi karya take amma fafur yaki yace dama ai ya gaya mata tun ba yau ba, ta fita daga harkar gidan Tariq amma taki, shikenan tunda har ta zabi hakan dama kuma bata son jidda sai ya auri Salman dan ya gaji da halin ta. Gefen Baban Tariq ya zauna Baba ya kalle shi ya nuna sa da hannu sannan ya nuna Maman

"Ga uwar ka nan, tasan duk abinda yake faruwa saboda son zuciyar ta, ta jawo maka matsala da kanta, bani da abinda kuma zan yi akan wannan maganar dan ko zuwa sukayi suka fadawa duniya sun bata min suna, babu kuma wanda zai yarda da mu, duk da su kansu illa zasuyi wa kansu babba amma mutane basa gane hakan idan har suka rasa abun da suka kwalla fa rai akai basu samu ba, toh sai su yi kokarin shafa maka bakin penti, yanzu zamani ne na social media kuma duk abinda aka ce siyasa ta shigo zakayi kokarin kare mutuncin ka da martabar iyalin ka dan abu kad'an sunan ka zai karade ko ina, bani da niyyar tursasa maka aure a wannan lokacin, amma tunda har ban isa na saka ko na hana mahaifiyar ka ba, shikenan gata nan,kaje ka fara shirye-shiryen auren Salmar, idan yaso sai ka ajiye Hauwa'u a gida kaamar yadda take so, ka dauki matar da ta zaba maka ku tafi"

Da sauri Tariq ya dago kansa da yake duke, ya kalli Baban

"Sai ka fara shirye-shirye dan babu lokaci, abinda mahaifiyar ka take so ne, tunda ita Hauwa'u ba 'ya bace a wajen ta,amma ta sani, tana da 'yaya mata duk abinda kayi wa dan wani kaima sai anyi wa naka."

Kan Tariq a k'asa ya kasa motsawa dan be yi tunanin abinda Baban zai ce kenan ba, bayan yayi masa duk bayanin da zai masa kuma ya gamsu ya amince, amma kuma sai yaga Baban ya chanja baki daya kamar bashi ba, tashi Mama tayi dan tasan ko me zatayi ba zai saurare ta a lokacin ba, shiyasa kawai taga gwara ta fita zuwa sanda zai huce, sannan taje ta samu Nafi suyi duk wacce zasuyi dan wallahi da Tariq ya auri Salma gwara ta hakura da Jidda duk da bata son ta.

Yunkurawa Tariq yayi zai bi bayan Maman bayan yayi godiya a ciki ciki Baban ya dakatar dashi yace ya zauna, zama yayi ya tankwashe kafarsa

"Na kira wani a embassy, yace ku shiga gobe da safe, idan yaso daga chan sai ku wuce kanon."

"Na'am?"

"Eh, sannan akan maganar da mukayi yanzu..."

"Baba dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya auren yarinyar nan ba."

"Na sani, kuma nima ba zan bari ka aure ta ba ,inaso mahaifiyar ku tayi hankali ne, ta ajiye duk makaman yakin ta,ta rungumi Jiddah dan idan aka tafi a haka ko 'yaya kukayi zata iya kin su, tunda tana kin uwarsu."

Ajiyar zuciya ya sauke me karfi wadda har sai da ya bawa Baban dariy

"Jairi, kannen ka mata ne suka sanar dani duk abinda yake faruwa tun ranar da uwata suka zo gidan, nayi shiru ne ina bibiyar komai,."

_"Ashe yaran nan suna da rana."_ yace a cikin zuciyar sa, godiya ya sake yiwa Baban yayi masa sallama ya fito ya wuce kai tsaye wajen aunty dan yasan anan zai tarar da ita [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (52)

***Abinci ta zuba ta zauna tana ci a k'asan carpet suna hira da Aunty sai gashi ya turo kofar ya shigo bakin sa dauke da sallama. A ciki ta amsa Anty kuma ta amsa a fili tana masa maraba. Yanayin da ya ganta a zaune sai ya tuna masa ita ranar da ya fara ganin ta da muryar ta kamar usur wuyanta kamar mirikin lema.

"Barka da rana Aunty."

"Barka dai Tariq, ya gida?"

"Alhamdulillah Aunty."

"Madallah, ya shirye-shiryen tafiyar?"

"Ana kan yi, Visa din Jiddah ce dama zata dan mana delay kad'an."

Ya karashe yana kallon fuskar ta, tunda ya shigo ta daina cin abincin da take ci yana lura da ita

"Masha Allah, toh Allah ya bada sa'a ya taimaka."

A yadda Antyn tayi maganar zaka gane cewa ba karamin farin ciki tayi ba da tafiyar Jiddan, abinda dama take ta hangowa kenan dan indai ya tsallake ya tafi shikenan kuma kashin ta ya bushe a wajen Mama da Nafi dan ta lura Nafin ce take sake zuga Mama akan Jidda,yanzu kuwa idan suka tafi ba shikenan ba?

"Bbyna..." Yayi maganar yadda aunty ba zata ji ba, dago kyawawan idanun ta tayi ta sauke su kansa, ya motsa bakin sa a hankali yace

Kin gama?"

Girgiza masa kai tayi ta cigaba da juya spoon din

"Ok, ki karasa sai mu tafi."

Gid'a masa kai tayi, yayi murmushi kad'an ya zare glasses din idon sa yace

"Aunty, gobe zamu je embassy daga nan zamu wuce Kano in sha Allah."

"Kai dama na biku kawai mu tafi wallahi."

"Aunty mu tafi kawai toh mana."

"A ah, babanku ma ba zai yarda ba, nima kuma tsokanar ku nake duk da inason zuwa din amma zan bari cikin next week in sha Allah."

"Toh Allah ya kaimu."

"Amin ya Allah.'

Mikewa Jidda tayi da plate din dan babu kuma in da abincin zai cigaba da shiga dan gaba daya ya hanata sakat da kallon shi duk da idon sa yana cikin bakin glass amma tsaf ta gano kallon ta yake kuma ta san shi sarai zai iya bata kunya a wajen auntyn dan shi kam babu ruwansa ko a jikin sa.

"Jidda dai wannan cin abincin na wasa me wallahi."

"Shiyasa bata kiba ai aunty."

"Aikuwa, a haka ma ai jiddah tayi kumari, sosai."

"Yanzun ma da sauran ta." Yace k'asa-k'asa amma sai da taji, ta juyo ta dan kalle shi ya motsa bakin sa yana mata murmushi ta shige kitchen din ta wanke bakin ta sannan ta fito ta wuce tsohon dakin ta, bin bayan ta aunty tayi suka barshi a zaune tana shiga ta zauna tace Jiddan ma ta zauna, rike da hisnul muslim dinta da counter sai yar jakar da sarka da abun kafar nan suke ciki da ta dauka a cikin kayan ta tazo ta zauna kusa da Auntyn

"Akwai abinda yake damun ki ne?"

Ta tambaye ta tana kallon yanayin Jiddah da yadda take abu very cool duk da dama chan haka take amma yau sai taga ya karu. Girgiza kanta tayi

"Babu komai aunty."

"Akwai in da yake miki ciwo ne?"

"Ba ko ina."

"Toh na tura miki text tun ranar kin gani?"

"Na gani aunty."

"Yawwa, ki yi hakuri kowacce mace da kika ganta a haka ta fara, girman kenan, ke dai banda gardama dan ita ke jawo ma mutum matsala, dama dai chan kinga ba wasu uban magunguna aka narka miki ba, mafi a'ala dai shine maganin sanyi, idan aka kwana biyu da kanki zaki nemi karin wasu abubuwan ba sai wani ma yaji ba, yanzu dai ki daure kiyi hakuri na lokaci ne da ya wuce shikenan, ki gyara jikin ki da mijin ki sannan kiyi masa biyayya iyakar iyawar ki."

"In sha Allah Aunty, nagode sosai Allah ya saka miki da gidan aljanna, ba dan ke ba aunty, da bansan ya rayuwata zata kasance ba, da nasan yanzu ina chan cikin wahala da tashin hankali, bani da abinda zan yi na biya ki Aunty."

"Abu daya zakiyi ki biyani, duk runtsi duk wuya karki taba bijirewa mijinki, kiyi kokarin kyautata masa sannan ki sani, soyayya karamar abu ce a zamantakewar aure, kuma ita kadai bata iya dorar da aure, hakuri da addu'a sune babban makami domin akwai kalubalai masu tarin yawa da zasu taso miki, wanda zasu bude miki ido kisan mecece ma rayuwar."

"In sha Allah aunty."

Tace cikin muryar kuka, ita kanta tasan akwai kalubale sosai a rayuwar aure tunda taga yadda ita kanta Auntyn tayi hakuri kafin yanzu da komai ya wuce sai dan abinda ba zaa rasa ba, ta kuma ga yadda Baffan ta yasha wahala a wajen Iya Lami , sannan ga yadda Yaya a kullum take labarin wahalar da tasha a rayuwar auren duk da ba lallai dan abu ya samu wane kai ma ya same ka ba, amma idan ka sawa ranka Allah zai iya jarrabarka shikenan zaka zauna lafiya kuma cikin shiri.

Hawaye Aunty take amma bata bari Jiddan ta gani ba, tasa bayan hannun ta, ta share sannan tace ta je su tafi kar yayi ta jira, zata aiko da sakon Baffa da zata tafi masa dashi. Tashi tayi jikin ta yayi matukar sanyi ta jawo mayafin ta har saman fuskar ta yadda ba zai ga fuskar ta ba har ya gane kuka tayi ba. Waya yake ta fito tana kallon k'asa, ya zura mata ido yana so ya gano wani sauyi a tare da ita, yanayin tafiyar ta ya nuna kamar she's down, katse wayar yayi bayan ya ciro ya daga kunnen sa, ya mike tsaya ya zura ta a aljihun gaban rigar sa, ya riko hannun ta yana leka fuskar ta, hawaye ya gani yayi a kwance a fuskar tata, yasan definitely wata maganar sukayi da aunty amma be san wacce ba, baya fatan tasan maganar Salma da abinda yake faruwa wanda yayi tunanin Auntyn ma bata sani ba, tsoro ne ya darsu a ransa kar dai ko auntyn ta sani shine ta fadawa Jiddan

"Menene?"

Yace ciki nuna tsantsar kulawar sa, gefe daya kuma yana jin tsoron amsar da zata bashi dan be san a yadda zata kalli abun ba, tunda yanzu ne ta fara sanin sa bare ta banbance abinda zai iya da wanda ba zai iya ba.

"Ba komai."

"Tom ki daina kukan kinji? Muje mota sai ki fada min menene."

Da ka ta amsa masa, ya karbi yar jakar daga hannun ta ya rike mata dayan hannun suka fita daga falon. Motar na nan in da ya ajiye ta dan haka kawai bud'e mata baya yayi ya taimaka mata ta zauna sannan shima ya shiga da sauri, ya jawo ta baki daya jikinsa da yake motar tinted ce, kukan shagwaba ta saka masa ya rikice ya rasa yadda zai yi, ita bata san baki daya kukan ta rikita shi yake ba, kuma shine babban weak point dinsa, tapping bayan ta ya dinga yi a hankali har ya samu tayi shiru, ya zaro tissue daga saman dashboard ya goge mata fuskar bayan ya dago ta daga jikin sa

"Menene?"

"Ni Baffa na."

"Kike so ki gani? Shiyasa kike kuka?"

"Eh." Ta gid'a masa kai, ajiyar ya sauke da karfi jin ba waccan magaanar bace yace

"Zaki ganshi gobe in sha Allah."

"Sai me kuma?"

"Babu komai."

"Ok..." Ya zare jikinsa a hankali ya fito ya dawo mazaunin driver yaja motar suka bar gidan.

***Masifa aunty Nafi take Salma kuma na ta gursheken kuka, tsabar wulakancin abinda Ya Tariq yayi musu ace a gaban su sai dinga romancing matar sa, gashi wallahi ita da gaske take tsananin son sa da kaunar sa take kamar ta je ta shake Jidda har lahira, ita kanta Aunty Nafi taji haushin wulakanci da yayi musu ai ko ba komai ita matsayin uwa take a wajen sa, amma saboda wulakanci shine zai maida su yan iska yana rungumar mace a falon mahaifiyar sa. Banko kofar akayi Mama ta shigo tana huci kamar zakanya, tashi aunty Nafi tayi tana kallon ta da mamaki

"Ki tattara yarki da tsummokaran kayan ki, ki bar min gida na, kuma wallahi wallahi Tariq ba zai taba auren Salma ba, tunda ke muguwa ce makira, baki duba karfin alakar mu ba, har ki kala wa dana sharri saboda kawai son zuciya."

"Ban gane sharri ba, kina nufin Salma sharri tayi wa Tariq kenan, kuma kin goyi bayan sa?"

"Eh sharri kikayi masa bakar muguwa, wallahi sai kin tafi bani ba ke kuma wallahi."

"Ahayye! Tab Amma sannu Aisha, kina nufin zaki rabu dani akan danki? Yaran yanzu da ba shaidar su ake ba?"

"Nayi, kuma kema kinsan duk abinda kuka fada akan sa karya ne, toh wallahi ko ku tafi da kafarku ko securities su fidda ku."

"Aikuwa wallahi ba zai yiwu ba, a dake mu a hana mu kuka, ba za'a bata min yarinya kuma ace zaa kore mu ba, wallahi ba inda zamu ko Tariq ya karbi Salma ko kuma zance ya karada dukka kasar nan."

"Idan kin ga dama ki dau loud speaker ki zaga kaf duniyar nan kina fada, babu abinda zai faru illa kanki da zaki WA illah, dan ko a yanzu babu me karbar yarki da wannan banzan halin nata ballantana son zuciyar ki yasa ki bata suna, kinga zata kare a haka ba aure."

Mamakin yadda Maman take kokarin wargaza musu plan dinsu ya saka jikin ta sanyi, amma sai ta hana ta gane halin da ta shiga tace

"Ai akwai hukuma ko? Wallahi sai naje sun bi min hakkin 'ya."

"Kije binnin sin ma, kuma wallahi ko a hanyar gidan mu na chan Kano na sake ganin ki sai na saka an rufe min ke an jefar da mukullin."

"Naji duk abinda kuke fada ke da yar taki kuma nayi recording din komai, dan haka sai a bi wani sarkin ,tunda baki san halacci ba."

Shiru Aunty Nafi tayi ganin dai da gaske Maman ta gano plan din su, kenan ta ji maganar ko dai so take ta sakata fara feeling quilty?

Juyawa Maman tayi ta fita, jim kad'an sai gata ta dawo da wasu masu aiki daga bq su biyu kedaru majiya karfi,suka shigo dakin tace su kwashe kayan su Anty Nafin su fitar mata dasu, tsoro ne ya shigi Anty Nafi, tana so tayi magana amma kuma tana tsoro dan bata taba ganin bacin ran Maman haka ba sai yau, dan komai akayi mata bata cika tankawa ba, shiyasa tayi tunanin zata iya amfani da wannan damar ta cutar da Maman ta kakabawa Tariq Salma ta samu hankalin ta ya kwanta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull