Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 25

Sanadin labarina complete novel - Chapter 25

Sanadin labarina complete novel Chapter 25: Sanadin labarina complete novel Chapter 25. "Ba sai an mana wulakanci ba zamu fita." Tace tana yin wajen kayan,…

4,491 words

"Ba sai an mana wulakanci ba zamu fita." Tace tana yin wajen kayan, zata taba Mama ta dakawa masu aikin tsawa tace bata son jira su kwashe kayan, da sauri suka suri akwatin tasu sukayi waje, Salma babu ko mayafi akan ta sai wata hula ita kuma Aunty Nafi sai mayafi suka fito Maman na tsaye suka wuce, already tayi waya gate tace sam ya sauke su a tasha suna fita aka saka musu kayan a booth Salma sai kuka take Anty Nafi kuma ta kasa cewa komai saboda yadda ran ta yayi bala'in baci.

Zama Mama tayi a nutse tana dafe kanta da yake mata kamar zai rabe biyu, bata san ta tara damuwa haka ba sai yau da Baba ya birkice mata, ta kuma san kafiya irin tasa shiysa ba zata taba amincewa ya aiwatar da abinda yayi niyya ba, da kanta zatayi kokarin ganin Tariq da Jidda sun bar kasar baki daya gwara su je su karata a chan duk da bata son Jiddan bata kuma san yaushe zata so ta ba amma gwara ita akan salma.da ta gama saida mutuncin ta a titi. Maryam ce tazo ta zaune a gefen ta, ta dago tana kallon ta sai ta girgiza kanta

"Ya akayi? Zaku je gidan Safiyya daga nan ku wu kaiwa Umaima kaya."

"Ok sai muje gidan Ya Tariq?"

"Bana son neman magana."

"Dan Allah Mama, ba zamu dade ba."

"Toh naji, idan kunje KU gaishe su "

"Har Jiddah?"

"Ban sani ba." Tace tana jan tsaki

"Wai Mama, Anty Nafi yar gidan ku ce itama Hajiya Babba ce ta haife ta?"

Girgiza kanta tayi

"Bamu da alaka ta jini ko kad'an, yar abokin Alhaji ce, zumunci irin na da da iyayen suka rasu shine aka bawa Hajiya Babba ita dan dama gida daya muke tun a dah, shine muka taso tare babu wani banbanci, amma kinga ai yanzu ta nuna min jini ba karya bane ko? Tunda na tabbata abinda tayi min Mimi ba zatayi ba, anyways, we learn from our mistakes, ya wuce in sha Allah."

"In sha Allah."

"Tashi kuje kar kuyi dare."

"Ok ina kayan suke."

"Suna cikin daki na, ki taho min da wayata na kira Dr Iman tazo tayi mun bp."

"Ok mah." Ta wuce ciki ita kuma Maman ta kurawa waje daya ido tana tuna abinda ya faru. [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (53)

***Kusan tare suka shirya a gurguje saboda saura kiris su makara, tea kawai suka sha da slice bread suka fito Faisal ya dauke su zuwa Embassy din. Da zuwan su Alhaji Tahir ya fito har kofa ya shigar dasu bayan ya rike hannun Tariq din jidda kuma ta bi bayan su zuwa wani hadadden office. Zama Tariq yayi a kujerar dake facing ta Alhaji Tahir din ita kuma ta zauna akan couch din dake baya da dan madaidacin table a gaban wajen, fridge ya bud'e ya dauko musu ruwa da lemo sannan ya karbi takardun ya dan duba su kad'an ya mike ya fita bayan yace yana zuwa. Juyowa yayi gaba daya da kujerar suka hada ido ya dage mata gira tayi murmushi tana kallon kofar shigowa.

"Sai na taso ma." Yace yana kokarin mikewa, da sauri ta hau girgiza masa kai

"Dan Allah kayi zaman ka anan."

Murmushi yayi ya girgiza kai, ya juya daidai lokacin Alhaji Tariq din ya dawo yace su taso, suka bishi ta wata kofa ba wadda suka biyo dazu ba, ya kai su wani babban office yace su shiga su zauna, suna zama Mr Biden ya shigo shima. Cikin kankanin lokaci suka gama abinda zasuyi suka fito bayan sun wuce layi me yawa a reception din wajen. Godiya sukayi masa yace su gaida Baba suka fito shi kuma ya juya zuwa ciki.

Jirgin rana zasu bi zuwa Kano, shiyasa sai da suka fara komawa gida suka karasa shiryawa, kwana Jidda take so tayi a gidansu amma taka take-taken Tariq din kamar ba zai barta ba, kwana biyu yace kawai zasuyi wai idan suka je kano yau gobe da wuri sai su tafi garin su Jiddan, su dawo da yamma, su sake kwana sai su dawo da next day, kaya ta dauka kusan set biyar incase ko zai chanja shawara ya barta, yana lura da ita da tana saka kayan a suitcase yayi kamar be gani ba dan be shirya barin ta ba, bayan yasan duk rayuwar da ta shiga a wajen Matar baffan ta, SANADIN LABARIN da ya saka masa tausayi da kaunar ta, tun ranar farko da ya fara dora ido akanta, ya samu kuma labarin ta, yake dawainiya da son ta shi kansa ba tare da yasan me yake ji ba, ya damu da ita sosai har ya zama yana tuna ta a kowanne lokaci har bayan tafiyar sa, dalilin da ya saka shi kiran Aunty a wanchan lokacin. Duk a tunanin sa tausayin ta kawai yake yi, shiyasa ya dinga chusawa kansa ra'ayi akan irin matar da yake so ya aura, yana kokarin dakushe zuciyar sa da nuna mata ai jiddah bata cikin wannan layin. Tasowa yayi ta bayanta tana ciro undies dinta a bobboye dan kar ya gani tana turawa a cikin kayan nata. Rungume ta yayi tsam yana dora kansa a saman kafadarta, da sauri ta saki sleeping dress din da ta ciro zata sake chanja mata waje cikin wanda Aunty ta aiko mata, irin fitinannun sexy nighties din nan ne dan rigar ko kusa da zuwa waist dinta batayi ba, da kad'an ta kai saman cibiya sai wani transparent pants sannan rigar ta baya a bud'e take gaba daya. Yaga sanda ta yadda rigar, sai ya cikata ya duka ya saka hannu ya dauki rigar yana dagata, kamar wadda aka dasa a wajen haka tayi ta dauke numfashi tana rufe idonta sanda ya dauki rigar ya dagata yana kallon ta idon sa a shanye kamar wanda yasha wani abun, shiru taji yayi ta dan bud'e ido kad'an suka hada ido ya kad'a mata kai yana daga mata rigar

"I love this."

"Ajiya fa aka bani." Tace still idon ta a kulle.

"Waye?"

"Em.. Ami... Ya Safiyya ce ta bani ajiya."

"Me yasa ta baki ajiya?"

"Nima ban sani ba."

"Shikenan ta zama tamu, zan biya kudin amma ba zamu bata ba gaskiya."

"A ah gwara a bata mu ba abinda zamuyi da ita."

"Ko? Mu ke da abinda zamuyi da ita ai, beside ko kyauta ne ma Sofy zata bani matata ta saka min na gani."

"Innalillahi!"

Dukawa yayi ya tura ta a suitcase din sannan ya rufe yana yin wani irin shu'umin murmushi sannan ya rufe yana daga su

"Nasan in da ake saida irin su don't worry zan siya miki kinji?"

"Ni bana so."

"Allah sai kinso, tunda ni inaso."

Turo baki tayi ya matso daidai fuskar ta yayi magana a hankali

"Inaso na dinga ganin ki cikin lingerie and bikinis. I don't mind idan ma kika zauna haka, eh kin gane...."

Ya kashe mata ido daya, da sauri ta juya tana kunshe dariyar ta.

"Common... life din is too short let's enjoy our self Baby "

Kin kallon sa tayi, ya koma ya zauna yana murmushi kasa kasa , ya dauki wayar sa ya kira Fauwaz yace yazo ya kaisu airport daga nan zai aike shi wani waje. Fita tayi daga dakin taki yarda ta kalle shi kwata-kwata shi kuma babu abinda yake sake birgeshi da ita irin kunyar ta.

Dakin Godiya taje ta sameta a kwance tace ta hada kayan ta za'a kaita wajen aunty zasuyi tafiya su, tashi tayi da yar murnar ta tunda dama mamanta tana aiki a gidan nasu ne shine aka bata yar, a gurguje ta gama hade kayan ta dauko kudi ta saka mata a kayan sannan ta dauki waya ta kira gate tace Faisal ya kai ta gida dan ta kira Aunty already tace ta turo ta tunda basa nan kuma ko sun dawo ma daga kanon tafiya zasuyi gwara kawai ta dawo tunda babu amfanin zama. Tana kokarin komawa ciki bayan yarinyar ta fita sai ga Fauwaz ya shigo, tsayawa tayi ya karaso ciki suka gaisa sai ta tuno babu ko mayafi a jikin ta, tasan kuma halin oga aka, ciki ta shiga ta bar Fauwaz din bayan tace masa tana zuwa, ta shiga dakin ta, ta chanja zuwa bakar abaya tayi rolling sannan ta same shi a dakin sa tace masa Fauwaz yazo. Tashi yayi ya fito bayan ya jawo suitcase din tasu ita kuma ta cire musu cable din wayar su ta dauki bottle water a fridge sannan ta saka abinda tasan zata bukata a cikin handbag dinta ta fito sanye da flat shoe. A tsaye ta same su daga Tariq din har Fauwaz din suna magana, tana fitowa Fauwaz yaja kayan yayi gaba shi kuma ya juyo yana kallon shigar ta kafin ya kad'a kai, babu wani aibu she looks decent dan yasan ma'aikatan wajen zasu iya kalle mishi mata ganin how beautiful she is amma a kalla if shigarta is ok ko sun kalle ta ma sun kalli Allah ya isa kawai. Shi a ganin sa ma fa Jiddan sa ta kai matsayin saka nikaf kawai saboda baya so taji ta a takure ko taga kamar ya matse ta shiyasa yaki cewa din amma wallahi da zata saka shi sai yafi kowa jin dadi, babu shegen da zai kalleta bare har yayi admiring kyauwun ta a zuciyar sa.

Hannun sa ya sarke a cikin nata suka fito bayan ya karbi ruwan ya sha kad'an. Wani ne daban a mazaunin driver sai kuma wata mota daya da Tariq din be san ta ba, itama da mutum hudu a cikin ta, fitowa sukayi da sauri suka gaida Tariq din ya gansu wasu manya fuskar su a toshe da bakin glass gefen aljihun kowannen su dauke da bindiga

"Ban gane ba."

Yacewa Fauwaz bayan ya budewa jidda mota ta shiga, kad'a kai Fauwaz yayi yana dariya

"Abokin Babana ya samo mana su wallahi, shi Baba baya so amma yaki yace yadda rayuwar nan ta zama wallahi tunda dai mun shiga circle din dole ne muyi abu kamar nasu, this two naku ne har ku wuce tare zaku tafi Kano din ma yanzu.". Ya karashe yana dariya

"This is serious, kenan mutum ba zai yi rayuwar sa ba haka nan sai da wasu? Waye ma ya damu ne wai damu ma?"

"Haka kake gani fa, insecurity din ya wuce in da kake tunani, akwai wasu ma da zaku hadu dasu kuna sauka a airport."

"Are you kidding me? Kai aka sani ai bani ba."

"Allah I'm serious, muje kar kuyi missing flight."

"Abun babba ne." Yace sannan ya shiga gefen Jidda shi kuma Fauwaz ya shiga gaba.

***A mintiunan da basu gaza awa daya suka isa Kano, suna sauka kuwa suka hadu da wasu zugar securities din suna jiran su, shi abun ma dariya yaso ya bashi, sai kuma dai ya share yace su kaisu chan main house din su Mama akwai abinda zai yi kafin su wuce masaukin su, sabon gidan da sukayi anan nasarawa gra. Zasu shiga motar kenan taji an kira sunan ta, tsayawa tayi chak muryar sa na dawo mata tar akanta. Ya Isma'il ne,

"Jiddah." Safeera ta kirata ta juyo da sauri idon ta ya sauka akan sa, yana cikin ashe colour din suit idon sa sanye da siririn medicated glasses fuskar sa dauke da murmushi

"Safeerah,Ya Isma'il!"

Ta fada a lokaci d'aya cikin jimla daya. Tsayawa Tariq yayi rik'e da murfin motar idon sa akan wanda aka kira da Ismail din da yadda yake kallar masa Jiddan sa. Hugging din Safeeran tayi sannan ta gaida Ya Isma'il din ya amsa yana matsawa ya mikawa Tariq hannu

"Oga barka da rana."

Kamar ba zai mika masa hannun ba dan sai da yayi dan jim kafin ya mika suka gaisa.

"Safeera ce da brother din ta." Tace tana murmushi

"I see!"

Yace a d'age yana sake kallon Isma'il din wanda yake ganin kamar tunda yazo wajen Jidda kawai yake kallo.

"Muje ko?" Yace

"Ok zan shigo na gaida Mom in sha Allah."

"Ya dai kamata wallahi, Ya Tariq sai anjima."

"Sai anjima." Ya maida mata

"Ok sir, ku gaida gida, Jidda bye." Ya ware yan yatsun sa guda biyu ya dagawa Jiddan su

"Ok 👌."

Motar ta shiga sannan shima ya shiga ransa na baci sosai, haka kawai yaji baya son Isma'il din.

"She's my best friend."

Tace tana kallon sa da murmushi a fuskar ta. Nodding kansa yayi be ce komai ba,shiru tayi ganin kamar mood dinsa ne ya chanja. Tunanin yadda zasu kwashe da a gidan su Maman ta shiga yi. Bata san wacce irin tarba zata samu ba, shiyasa duk jikin ta yayi sanyi ga Tariq din ya gimtse fuska yaki yarda ma ya kalli side din da take.

Wayar sa ya zaro zai kira Ishaq yaga missed calls din Yasmin kusan kullum sai ta kirashi ko tayi masa message a WhatsApp, da gaske take ba zata barshi ba kila sai ta ganshi tare da Jidda sannan zata kyale shi. Fasa Kiran Ishaq din yai ganin an zo gate din gidan su maman. Idon ta akan gate din ganin irin girman gidan bata taba kawo Maman daga irin wannan gidan ta fito ba duk kuwa da dama kana ganin ta kasan masu kudi ne amma bata kawo har haka ba, shiyasa Maman tayi mugun raina Anty dan ko kusa ba tsarar ta bace idan banda kaddarar aure babu yadda za'a yi su hadu inuwa daya. Harabar gidan zata ci motoci kusan sha biyu saboda girman sa, ga motocin nan a faffake wasu lullube wasu kuma daga gani ba'a dade da hawan su ba. Fita yayi be ce ta fito ba sai tayi zaune tana tunanin ko ba fitowa zatayi ba, har yayi gaba sai ya juyo ya ganta a zaune duk da an bud'e mata kofar bangaren ta. Dawowa yayi da baya yace ta fito, ta fito tana satar kallon fuskar sa. Hanya ya nuna mata yace tayi gaba ya take mata har suka main entrance din. Door bell ya danna jim kad'an aka zo aka bud'e. Da sallama suka shiga dukkan su cikin falon da yake dauke da kujeru set uku saboda tsabar girman shi. Hajiya Babba na zaune a falon ta dago idon ta sanda taji sallamar kamar ta Tariq, shi din ne kuwa sai taga ya kara girma sosai. Al'amin ne yayi karaf din cewa

"Wa nake gani kamar Captain?"

Murmushi yayi wanda ya tsaya iya saman labbansa yace

"Ni ne."

"Ah lallai yau nazo a sa'a, Hajiya Babba kinyi babban bako mutanen turai da basa ziyartar yan uwa."

"U r not serious!"

Yace suna karasowa tsakiyar falon in da second set din kujerun suke kuma in da Hajiya Babban take tana karatun Qurani akan dan katakon ta.

"Sannun ku da zuwa." Tace tana rufe karatun ta yunkura da dan k'yar ta mike daga k'asa idon ta akan Jidda dake ta sunne kai cikin taraddadin abinda zata tarar

"Bismillah, zauna mana Hauwa'u."

Ta kira ainahin sunan nata da Baba ne kawai yake fada mata a yanzu sai ko course mates dinta, nutsuwa taji kad'an ganin a kalla tasan wacece ita har ta kama sunan ta haka radau. Zama tayi a k'asa Tariq kuma ya haye kujerar sai ya dan zamo kadan yace

"Hajiya barka da gida."

"Ba zan amsa ba." Tace tana kauda kanta, ta dawo kan Jidda tana share shi

"Dalilin ki Tariq yazo gidan nan,dan rashin kirki."

Sunkuyar da kai Jidda tayi ta danyi dariya kad'an

"Ba zaki kulani ba granny?"

"Ba dan ni kazo ba, yanzu ace Tariq gidan nan kamar baka san hanya ba,yaushe rabon ka da kazo? Itama uwar taka da laifin ta wallahi."

"Ayi hakuri Hajiya kinsan turawa basa san mutane sosai."

"Kana da matsala."

Yace yana kallon al'amin din

"Sai su ci kansu ai." Tace tana daga wayar dake gefe da take communicating da duk ma'aikatan gidan

"Nayi Baki." Tace ta katse

"Malam ya gida ya aiki? Ya kwana da yawa?"

"Alhamdulillah wallahi, aiki ana lallabawa gashi nan ba dadi, kai fa?"

"Toh gashi nan dai, zan koma ne ma cikin next week in sha Allah."

"Kace zaka sake guduwa sai an kuma ganka kenan."

"A ah fa."

"Ai naji aikin naku ne kullum kuna tafe shiyasa, ina wani time na irin wannan ziyarar."

"In sha Allah ma.zanzo, zan shigo gidanka ma kafin mu bar kano muzo mu gaida madam."

"Da ka kyauta kuwa."

"In dai Tariq ne ba zuwa zai ba fa, shi in dai harkar mutane ne toh babu shi a ciki sam."

"Haba Hajiya ba haka bane ba."

"Fadawa wanda be sanka ba."

"Hauwa'u, tashi ki zauna sosai kinji?"

"Nan ma yayi Hajiya "

"Toh bari na shiga ciki na turo miki Nu'ayma, idan kuma zaki shigo cikin ne toh."

"Nu'ayman tazo Hajiya."

Yayi charaf ya amsa kamar dashi ake.

"Ok toh, ka biyo ni inason ganin ka."

"Dollars zaki bani ko pound sterling?"

"Duk wanda kake so."

Dariya sukayi shi da al'amin ta shige ciki, maimakon ya tashi ya bi bayanta sai ya kasa dan ba zai iya barin ta daga ita sai al'amin din me shegen surutun tsiya ba, jira yayi sai ga Nu'ayma ta fito da fara'arta, ta gaishe su sannan yace ta kai Jiddan dakin su. Tashi Jiddan tayi ita kuma ta daukar mata snacks da juice din da aka kawo mata suka shiga ciki, sai sannan ya tashi yabi bayan Hajiya Babba ya bar al'amin din shi kadai! [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (54)

***Sun jima a gidan Hajiya babba fiye da yadda tayi zato ko tsammani, suna daki sai ga aunty Mimi ya shigo cike da murnar ganin Jiddan wadda ita tayi duk kokarin ta wajn wayarwa da Hajiya Babba kai akan Jiddan da yanayin halin kirkin ta, a dah su Nafi sun fanfa ta amma da Anty Mimin ta yi mata bayani sai taji ta sauka sosai, har ma tana son Jiddan shiyasa da tazo tayi mata tarbar da Jiddan batayi tunani ba. Sun fito zasu tafi bayan an saka mata kyautar Hajiya Babba a booth suna sake yin sallama sai ga Anty Nafi da Salma sun shigo a motar Anty Nafin driver ya kawo su, kallo daya Tariq yayi musu suna shigowa ya dauke kansa ya shiga motar sannan ya zuro kafafuwan sa waje yana zaro wayar sa, maganar da Hajiya babba tayi masa kenan a ciki akan maganar Anty Nafin da abinda ya faru yayi mata bayanin komai shine ta kira tace su zo ita da Salma sai gasu sun iso dan dawowar su kenan ma daga Abujan ko kaya basu chanja ba suka fito dan dama ko hajiyar bata kirata ba tayi niyyar zartowa tazo ta fada mata irin wulakancin da Mama tayi mata akan Tariq. Mamakin ganin Tariq din da Jidda a gidan yasa ta fitowa da dan sauri bayan ko gama parking daidai driver be ba.

"Tariq dai kaki barin Jidda da tayi zaman ta anan ai, Hajiya ma zata ji dadi."

"Anty zamu dawo, yanz akwai in da zamuje daga nan ne."

"Toh shikenan, sai kun dawo din."

"Sai anjima Anty Mimi."

"Sai anjima Jidda, bye."

Baya ta shiga shi kuma dama yana gaba tare da driver sai dayar motar da take bin su, suka fita daga gidan yana kallon mirror din gaba yaga sanda Anty Nafin ta karaso tana kallon motar tasu ita ma yar iskar yarinyar idon ta akan motar. Shafa kansa yayi yana jin wani dum kamar wanda yayi wani babban aiki. Direct gida aka wuce dasu daga nan. Gidan da ma'aikata masu kula da gidan dan yanzu yawanci Baba anan yake weekends kuma mafi yawancin lokuta tare suka zuwa da Mama dan itace me sabgar yi ga shagunan ta dan ma fauwaz shine karfin kula da duk wasu business dinta shiyasa ko yaushe yana tsakanin Kano din da Abuja yana duba yadda abubuwan suke tafiya. Daga bq ta fito ta bawa Jidda key din part din nasu da aka sake gyara shi dazu, mika masa tayi ya karba yana amsa waya ya bude sannn ya matsa mata ta shiga sannan shima ya shiga yana jan suitcase din su zuwa ciki yana cigaba da wayar sa. Ta rasa gane dalilin sauyawar sa lokaci d'aya, duk da haka suna yawan had'a ido amma sai ya fuske yana cigaba da wayar da take tunanin kamar da gayya yake jan hirar. Kayan nasu ta dauka tayi ciki tana kallon sanda ya bita da kallo. A gefe ta ajiye kayan tana karewa bedroom din kallo me dauke da hadadden royal bed din da aka sakawa red bedsheet me zanen heart. A gefe ta zauna ta fito da charger ta, ta jona wayar ta sannan ta nufi toilet din dake manne a falon. Wanka ta fara yi sannan ta dauro alwala ta fito daure da towel Babba. A wajen kayan su ta ganshi yana duba abu, tayi kamar bata ganshi ba saboda rashin kayan dake jikin ta, kad'an ya kalle ta sai tayi tunanin zai mata magana amma kuma sai ya cigaba da abinda yake kamar shima be ganta ba. Juyawa yayi ya fita, jiki a sanyaye ta shirya ta yi sallah sannan tazo ta dauki wayar ta,ta kira Safeera dan taga kiran ta sanda suna gidan Hajiya Babba . Suna cikin wayar ya shigo sanye da dogon wando fari da t-shirt kamshin turaren sa ya cika dakin daga gani wanka yayi babu ko tantama. A gefen ta ya zauna ya saka hannu ya zare mata wayar daga kunne sannan ya katse kiran yana kallon ta

"Haka ake lallaba miji?"

Ya kalle ta rike da wayar bayan yaga da wadda suke yin wayar.

"Na'am?" Tace a dan kaikaice tana kokarin hana idanun sa tasiri akanta

"Eh, haka akeyi? Baki san fushi nayi ba?"

"Fushi? Me yasa?"

"I'm jealous, kishi nake and you just pretend as if baki gani ba ma."

"Kayi hakuri."

"Ai kinji... A dake ka a hana ka kuka, ayi maka laifi a yi saurin baka hakuri da kazo zakayi yar mitar ka."

"I'm so sorry ba zan kara ba.”

“Ni ba zan hakura ba!”

“Please…”

“Sai da sharadi idan kinaso na hakura.”

Kallon shi tayi ya kashe mata ido

“Sai kin saka min rigar nan kin yi fashion parade sannan zan hakura.”

“Innalillah!”

“Yea! Idan ba haka ba nayi ta fushi na daina kulaki!”

Ya juyar da kansa gefe daya yana turo baki kamar karamin yaro.

“Shikenan zanyi, amma sai dai anjima!”

Juyowa yayi yana murmushi

“Why not now? Me yasa sai anjima?”

“Ni dai kawai.”

“Shikenan I will wait! Amma karma kizo min da wani excuse wallahi. Inaso naga matata ehe.”

“Tell me, waye wannan ismail din? How much did he know about you?”

“Ba zamu kyale maganar ba?”

“No it’s better ayi ta kawai Jiddaaaa.”

“Ok, yayan Safeera ne, both of them helped me alot a rayuwa ta, sun so ni a yar kauye ta da rama ta, basu taba kushe ni ba ko aibata ni.”

“OMG!” Yace yana kokarin rike ta, ta dan matsa kadan tana kin kallon sa

“He nuna interest akaina and I said no, be takura min ba, he left daga nan aka daura min aure, and I waited for good 1year, since then ban sake ganin sa ba coz dama a time din ya tafi karatu, this is the first time bayan long time da na ganshi, and yasan nayi aure, kuma nasan babu wani abu a ransa.”

“Jiddah!”

Ya kira ta ganin yadda mood dinta ya sauya. He misunderstood everything yazo yana ta fushi akan iska. Kin kallon sa tayi saboda yadda idanun ta suka cicciko zatayi kuka. Juyowa da ita yayi suna kallon juna, tayi saurin sauke kanta kasa ya sa hannu ya tallafo fuskar ta.

“I’m so sorry kinji? Dan Allah Kiyi hakuri ki daina tuna abinda ya wuce, nayi kuskuren fadan abubuwan chan Amma wallahi wallahi ba har zuciya ta ba, I was just looking for an excuse to hold on to, ba nayi ne don cin fuska ba, dan Allah forgive me! Wallhi nayi regretting, I regret everything har rashin dawowa ta,forgive me dan Allah!”

Kuka tasa masa ya jawota jikinsa ya rungume zuciyar sa na wani irin zafi, yasan zata dade bata manta ba, bayan ka zauna zaman jiran mutum ba shekara daya amma ya dawo yace baya son ka, dole da ciwo ontop of that kuma ma ya hada da kushe ka, dama zai iya dawo da lokacin baya ya goge duk abinda yace din, Amma Yanzu kam it’s too late. Ta dan dade tana kukan kafin tayi shiru sai ajiyar zuciya da take a hankali, tana da saurin kuka karamin abu yanzun nan zai sakata kuka sosai, bayan ta yake tapping a hankali ya kasa ce mata komai har tayi shiru din. D’ago ta yayi yana kallon yar fuskar tata, hannun sa yasa ya goge mata ragowar hawayen da take ya shafi saman lips dinta da yake ganin shine kawai last option dinsa da zai yi amfani wajen sake bata hakuri.

“I’m sorry.”

Yace muryar sa ta shige ciki sosai. Sai ya matso da fuskar sa daf da tata, ya dora hanci sa a saman nata yana gogawa kadan kadan yana kokarin saka mata idonsa a cikin nata saboda taga how sorry he is, a hankali ya kai bakin sa saman nata ya hade su waje daya, sannan ya sa hannun sa ya zagaye ta cikin ta ya matso da ita so so close. Kusan minti biyu ya dauka yana kissing dinta a hankali, kafin ya cikata yana maida kansa ya hade goshin su waje daya, idon ta a rufe yake jikinta yayi wani irin sanyi, ya riga ya gano lagon ta. Kissing aaman

“Please Kiyi hakuri, ki daina tunawa kinji? Ya wuce ba zan sake ba. I love you so very much, bansan irin son da nake miki ba wallahi! Kukan ki is one of my weaknesses dan Allah ki daina kinji?”

G’id’a mishi kai tayi, ya rike hannun ta yana mata murmushi

“Did you love me?”

Ya tambaye ta for the first time cike da tsoron kar tace masa a ah.

“Umm? Kina son Ya Tariq dinki?”

“Eh…” ta daga kanta kunya na cikata

“Yes! Say it naji, pleaseee.”

Kasawa tayi, ta boye kanta a kirjin sa tana dariya kadan kadan

“Kunya kike ji?”

“Umm…”

“Ni dai sai kin fada min naji.”

“Ba zan iya ba.”

“Zaki iya, pleaseeee!”

Yawun bakinta ta tattaro fuskar ta har lokacin na cikin kirjin sa,

“Na rufe ido na, inajinki fada mjn, tell me you love me.”

Dagawa tayi kadan taga ya kulle idon sa, kallon fuskar ta dinga yi tana admiring din ta, ta dan kai hannu kadan ta taba gefen sajen sa, ya rike hannun yayi kissing dinsu still idon sa na a rufe

“I’m waiting…”

“I love you so much.” Tace da sauri kamar wadda aka tunkuda. Dariya ta bashi amma sai ya kanne ya bude idon sa

“Wow! I love you more baby.” Yace yana mata murmushi [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (55)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull