Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 27

Sanadin labarina complete novel - Chapter 27

Sanadin labarina complete novel Chapter 27: Sanadin labarina complete novel Chapter 27. "Tafiya zan." Tace tana jan mayafin ta, hannun ta ya kama ya mikar…

4,477 words

"Tafiya zan." Tace tana jan mayafin ta, hannun ta ya kama ya mikar da ita sannan ya taimaka mata suka fito. Sai da ta shige sannan ya dawo ciki ya shinfid'a abin sallah ya tayar. Tare suka fita masallaci, achan suka zauna har gari yayi haske sosai kafin su dawo gidan yana zuwa ya tarar da kayan tea da bread sai kosai a plate an kawo amsa hade da farfesun naman zabo. Be so ya tada Baffan a tsaye ba dan yasan saboda shi yake ta hidimar da kashe kudi. Zama yayi yaci sosai kuma yaji dadin farfesun dan shi yafi ci sosai yasha ruwan Lipton. Turo kofar akayi da sallama tana rike da ruwan zafi a dan madaidacin bucket din plastic karami, ruwan wanka ta kawo masa dan ita tayi nata tun dazu har ta saka kayanta. Karbar ruwan yayi a hannun ta yana jin dadin ganin ta, yaje ya juye sannan ya dawo yace ta zauna tayi breakfast din kafin ya fito, toh tace masa ba dan zata zauna din ba dan ta lura shi sam be gane yadda rayuwar take su a wajen su ba. Yana shiga toilet din ta fice haka ya fito yaga ta gudu yayi murmushi kawai ya shirya yana gamawa Baffa yazo yace su shiga ciki ya gaisa da matan gida. Bayan ya shiga sun gaisa sai yace ta fito su tafi dan akwai abinda yake so yayi a kanon kafin su koma da daddare. Fita yayi waje tare da Baffa ya saka aka dauko manyan ledoji niki-niki aka saka musu a booth yana ta cewa a barshi amma Baffa yace ba za'a barshi ba akwai sakon Baba a ciki ma, dama jiya ya nema amma be samu ba da suka dawo shine ya sake aikawa. Godiya sosai Tariq din yayi cike da yabawa dattakon Baffan. Fitowa tayi zuciyar ta wasai ba kamar jiya ba, ta shiga motar sannan yazo ya shiga suka sake sallama da Baffa sannan suka tafi. Yar tafiya kad'an sukayi Baffa ya kira ta a waya yace su dawo Tariq yayi mantuwa a dakin, envelope ce a ajiye a saman katifar. Katse wayar tayi tana kallon sa

"Kayi mantuwa inji Baffa."

"Mantuwa?"

"Eh wai envelope akan katifa."

"Ohh! na Baffa ne ai."

"Envelope din?"

"Umm."

Ya daga mata kai, kiran Baffa ne ya sake shigowa, ta daga yace sun juyo kowa?

"Baffa wai yace naka ne." Tace tana kallon sa

"Nawa?"

"Eh Baffa."

"Ina zuwa." Yace yana sake katse kiran ya bud'e envelope din sai ga kudi sababbi kal yan dubu dubu.

"Subhallahi." Da sauri ya kira Jidda tana dagawa yace

"Akan me yaron nan zai min haka? Wannan kudin na menene?"

"Baffa bansan na menene ba."

"Bani shi a waya."

Cirewa tayi daga kunnen ta, ta mika masa ya karba yana chanja hannun da ya rike kan motar

"Wannan kudin me yawa na menene Tariq?"

"Baffa naka ne, a siya kayan abinci bamu zo muku da komai ba."

"A ah gaskiya baka kyauta min ba, shikenan kuma sai ka bani kudi masu yawa haka?"

"Ayi hakuri Baffa."

"Kash! Amma... Toh shikenan Allah yayi muku albarka ya saka da Alkhairi nagode nagode."

"Ba komai Baffa." Yayi saurin zare wayar dan godiyar tayi yawa, mika mata yayi yana maida hankalin sa kan tukin ita kuma ta saka a kunnenta tana satar kallon sa

"Kiyi min godiya kinji? Allah yayi muku albarka ya kiyaye hanya."

"Amin Baffa." Tace a sanyaye sannan ta cire wayar tana dorata akan cinyar ta

"Angode Allah ya saka da Alkhairi."

Tace a sanyaye, dan waigowa yayi k'adan yayi mata murmushi ya sake maida kansa gaba. Be tsaya ba har sai da suka isa, suka fito zuwa cikin gidan ya shiga ya dauki wasu kayan ya chanja a dan gurguje sannan yace yana itama ta chanja tazo su fita, da sauri sauri ta shirya cikin doguwar riga suka fice daga gidan. A hanya suna tafiya yace mata ina ne gidan su Safeera, kallon sa tayi ya gid'a mata kai

"Kirata kice zaki zo, idan na gama sai na biyo mu wuce."

Dadi ne ya kamata tayi saurin ciro waya ta kirata tace gata nan. Har cikin compound din gidan suka shiga sai ga Safeeran ta fito da saurin ta, ta tare ta suka gaisa da Tariq din yace zai je ya dawo, suka shiga ciki shi kuma ya fice daga gidan.

"Na zata fa da wasa kike da kika ce zaki zo gaki nan." Tace suna haurawa saman balcony

"Nima bansan zan zo ba, dawowar mu kenan fa, yace na shirya ashe nan zai kawo ni."

"Wallahi ya kyauta, sosai sosai. Kamar yasa nayi missing din best friend dita gashi akwai gist da yawa."

"Toh ai gani."

"In sha Allah wuni sur zakiyi, musha hira."

"Amin, ina Mom naji gidan shiru."

"Ai haka kullum gidan namu yake kema kin sani."

"Ku ai yan gayu ne shiyasa."

"Ba wani nan, Mom tana sama tare da Daddy Ya Isma'il kuwa tun safen wuri ya fice bank sai ni kadai da house helps din gidan, nima dai na kusa dagawa na shige daga ciki na huta da zaman kadaita."

"Ah lallai."

"Allah kuwa, muje daki kawai idan Mom ta fito kin je ki gaishe ta, yanzu sai ta kai azahar ma bata fito ba "

"Allah sarki Mom."

Tace suka karasa dakin Safeeran da aka sake gyara shi da kawata shi. Saman gadon ta haye tana cire veil din sannan ta ware gashin kanta da bata iya taje shi ba tun jiya da ta saka masa ruwa. Fita Safeera tayi ita kuma ta mike zuwa gaban mirror dinta. Drawer ta bud'e tana neman hand dryer bata ganta ba, sai da Safeera ta dawo daga kitchen bayan ta jero mata kayan ci akan tray sannan ta dauko mata hand dryer din ta taimaka mata ta gyara mata kan sosai sannan suka zauna zaman hira har Mom ta sauko taje ta gaishe ta sannan suka dawo suka dora ta bata labarin wanda zata aura Sadiq dan har an kawo kudi ma rana kawai zaa saka, tayi mata murna sosai kuma taji ba dadi dan tasan ba lallai ta samu zuwa bikin ba. Har la'asar sannan Tariq ya dawo yace ta fito, kamar kar su rabu haka dai babu yadda suka so taje tayi ma Mom sallama ta ba wa Safeera kudi ta bata da kyar ta karba suka fito sai ga Ya Isma'il ya shigo gidan a motar sa, da sauri yayi parking ganin wanda yake tsaye a jikin mota a harabar gidan nasu ya fito da sauri ya nufi wajen Tariq din ya mika masa hannu suka gaisa sai yaga ya amsa masa a sake ba kamar jiya ba.

"Dama Yayan mu wata magana ce dani."

Yace yana dan shafa kansa, murmushi Tariq din yayi yace

"Ina jinka."

"Dama neman alfarma zanyi, a shige min gaba wajen neman auren Maryam."

"Maryam?"

"Eh sister din Jidda ba,we met on social media har muka zama friends daga nan ne kuma muka zama lovers, yanzu haka har mun yi magana zan zo naga Baba, idan an amince min." Ya dan dukar da kansa irin respect din nan

"Masha Allah, congratulations. Kazo in sha Allah babu matsala."

"Nagode babban Yaya, nagode."

"Haba ba komai."

Yace idon sa na kan Jidda da suka tsaya daga baya ganin suna magana

"Baby mu tafi ko?"

Murmushi sukayi ma juna ita da Safeera ta kwaikwayi babyn da yace tana mata dariya. Ya Isma'il ne ya bud'e mata motar bayan sun gaisa, ya kara mikawa Ya Tariq hannu suka sake musabiha sannan suka matsa gefe shi da Safeera suna kallon motar tasu ta fice daga gidan.

"Rayuwa kenan." Ya Isma'il yace yana murmushi

"I'm happy for Jiddah, he's such a nice and cool guy, kuma yana son ta sosai sosai, irin mijin da ya dace da Jidda."

"Haka ne, sun dace da juna."

"Sun dace kam."

"Muje jiki kiji wani labari yarinya, I will soon be getting married."

"Are you serious!?"

"Allah kuwa,gidan su Jidda kuma zan fada."

"Amira?!!" Ta zaro ido

"Maryam."

"Wow! Dan Allah Yah?"

"Allah,maganar da muke dashi Kenan."

"Gaskiya naji dadi sosai wallahi, bata da issue ko kad'an wallahi."

"I know! Zo muje mu samu Mom, bana so a bata lokaci ban shige daga ciki ba."

Dariya suka kwashe a tare suka juya zuwa ciki, ta bud'e murya tana kiran Mom.

***Wajen cin abinci suka wuce sukayi order Chicken Mandi Rice da salad suka wuce gida. Shi kadai yaci dan ita cikin ta a cike yake daga gidan su Safeera. Bayan sallar magriba suka bar gida zuwa airport duk da sai da suka biya wani waje ya karbi sako. Suna shiga Abuja direct gidan su suka wuce dan sai after 10 suka shigo garin ma saboda delay din da aka samu kafin jirgin ya tashi.

#Ranooooo

***❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO KISHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (58)

***Tun da suka dawo Tariq ya daina zama saboda shirye-shiryen tafiya dan a cikin satin zasu tafi saura be fi kwana uku ba, gashi da shirin tafiyar sa shi kadai yayi da intention din idan yaje zai zo da wuri amma yanzu yasan idan suka shilla suka tafi shikenan kuma sai dai idan haihuwa Jiddan zatayi su zo gida duk da be riga yasan yanayin commitment din da zai shiga achan din ba amma yasan aikin su yana cin time sosai. Maryam da Amira sun zo gidan sau biyu suna wuni duk sanda suka zo tare da sakon gaisuwar Mama suke zuwa duk da jin su kawai take amma kuma hakan na mata dadi matuka, bata san halin da ake ciki tsakanin Baba da Maman ba dan yayi fushi sosai akan Maman shine take neman hanyar da zata samu ya sakko kuma a kasan ranta tana jin nutsuwa idan ta tuna Jiddan ce matar Tariq dinta ba irin Salma ba. Akan case dinta dasu Anty Nafin sai da taje Kano tayi mata tatas hakan ya jawo suka dauke kafa ma daga zuwa gidan Hajiya Babban gaba daya dan sosai Anty Nafin ta kullaci abinda Maman tayi mata. Ana gobe zasu tafi Anty tazo ita da Usman, kamar Jidda ta zuba ruwa a k'asa tasha saboda murnar ganin Antyn. Dama lokacin tana karasa hada kayan ta waje daya ne sai ga Antyn aikuwa ta tayata suka karasa tare suna aikin tana shigar da sakon da take son nunawa Jiddan cikin hikima da yadda zata kula da mijin ta, ta sake samun fada a wajen sa. Jiddan naji duk tana daukewa dan dama Antyn ce mirror dinta ita take dubawa a abubuwa da yawa saboda tasan babu abinda ya zaunar da Antyn a gidan har ta kawo yanzu sai hakuri da iya zama amma ba dan haka ba da tuni ba wannan labarin ake ba. Ya Tariq ne ya kirata bayan yaji komai lafiya sai take fada masa Antyn tazo shineyace kawai ta bita su tafi tare idan ta tashi tafiya saboda su yiwa Baba, Yaya da Mama sallama dan fitar asubah zasuyi gobe daga nan shima idan ya gama gidan zai wuce sai su dawo tare. Toh tace ta ajiye wayar ta fadawa Antyn abinda yace.

"Hakan yayi." Tace.

"Tunda tare zamu tafi ai sai mu hau shiri, komai ya riga ya shiga jaka sannan wadannan abubuwan da na nuna miki su karki wasa dasu wallahi."

"In sha Allah ba zan ba Anty."

"Yawwa, Allah dai ya kaiku lafiya, idan mun koma kika je part din Maman Fauwaz ki zauna sosai kinji? Karki ce zaki taso daga zuwa."

"Sau biyu da su amira suka zo sai suce wai Mama tana gaishe ni."

"Kai haba? Da gaske ko wasa?"

"Allah haka suka ce, na karshen ma Amira tace wai Mama tace mu fadi me muke bukata na tafiyar, shine sai yace tace mata zai zo gidan dan dama yana nan."

"Toh Allah yasa addu'ar mu ce taci ta, hakan ai kinga yafi, a kalla zamu fi samun kwanciyar hankali, kuma kinsan Allah? Maman Fauwaz bata da damuwa ita dai barta da kishi da duk mace kuma tana dashi sai dai kowa da irin yadda yake bayyana nasa, amma ko bayan wannan ba ruwanta da rayuwar ka, ko a sanda nake mata aiki bata da irin takurar nan magana ma bata cika son yi ba shiyasa ake mata kallon mara kirki, amma kishi ne kawai ya sakata yin duk abinda take amma sam babu cutarwa."

"Haka ne gaskiya."

"Allah ya kyauta yasa sakkowar tata kenan tunda dai yanzu ta zame miki dole tunda kika auri dan ta, ba'a kuma san karshen zaman da kuma yayan da za'a haifa ba."

"Ni ba zan haihu ba Anty."

"Saboda me?" Tace da sauri

"Tsoro nake ji fa."

"Kin jiki, ai sakin jiki zakiyi ki haifo mana babies Masha Allah, yadda bamu da yawan nan kinga ai ma kara yawa a daina mana gori."

"Kai Anty."

"Allah gori mana,ni da Yaya duk haihuwar daya ce kuma dama kinga mu biyu ne, dangi da yawa na da dadi wallahi sai baka dasu zaka gane, kuma dai haihuwar ce ke sawa a yi yawan."

"Tou haka ne."

"Tashi kinga kar lokaci ya kara ja mu tafi."

"Toh."

Ta mike taje ta dauko Hijab dinta ta saka suka fito, Sam na zaune suna ta hira da su Faisal sai ya taso da yaga sun fito yazo suka tafi. Bata shiga wajen Antyn ba direct wajen Yaya ta wuce daga nan sai ta je ta gaida maman ta zauna kamar yadda Anty tace. Dambu nama Yaya take ci da lemo Jiddan ta shigo, ta zata Fauwaz ne har da saurin ta zata boye Jiddan ta ganta.

"Auw ashe ba al'murin chan bane nake saurin boyewa."

"Rowa dai Yaya,."

"Allah ba rowa ba, in dai yagani sai ya dumbuza nan da nan sai kiga ya kare."

"Ai Yaya ke da Ya Fauwaz kamar Tom and Jerry kuke,ina wuni?"

"Lafiya lou, bismillah ci kad'an."

"A ah Yaya, nagode tsautsayi yasa naci ki zo kina yin mafarki na."

"Kin wa kanki yarinya."

Ta rufe robar ta tura shi gefen kujera tana karkade hannun ta

"Babar ku ce tayi min da kanta, naga kwana biyu shiri take nema da kowa a gidan nan, inaga dai tasu ce ta hado shi da Baban naku."

"Kai Yaya, saboda haka aka yi miki dambun?"

"Allah kuwa ai ina lura da komai, ina kuma shan kallo na..."

"Kuma tunda dai ina cin riba sai su karata chan." Ta dora

"Hajiya Yaya kenan."

"Uhum, ya akayi da magana ne?"

"A ah babu, zuwa nayi na ganki kuma mu tafi tare ki kwana mu raba dare muna hirar bankwana."

"Allah ya tsareni da zuwa gidan ku wallahi, Allah ya kiyaye ya kaiku lafiya."

"Yanzu ba zaki zo muje ki kwana ba?"

"Ba zani ba wallahi, kar kuma ki ishen da iyayi bayan ba har zuciyarki kike maganar tafiyar ba."

"Allah Yaya har zuciya ta nake yi."

"Toh naji, zuwa ne ba zan ba,ehe."

"Toh shikenan Yaya, amma zaki rakamu airport din ko?"

"Ko gaban gate din gidan nan ba zan rakaku ba bari kiji, salon a hada baki dake a sani a jirgin haka kurum."

"Kai Yaya ana tafiya ne ba visa ba komai?"

"Oho na sani?"

"Toh kuma ai naji zaku je Umrah wannan azumin sannan kuje hajji da babbar sallah, yanzu ya za'a yi kenan?"

"A mota zamu ko a jaki."

Tace tana gimtse fuska, dariya sosai Jidda tayi har da rike ciki. Tsinken sakace Yaya ta dauka tana sakacen tana hararar Jiddan da take mata dariya

"Jakin ne ya ban dariya Yaya, afuwan!"

"Kece da kayan haushi ai."

"Nayi shiru toh, kinga kar muyi fada tunda dai tafiya zan."

"Ba zamuyi ba ai, ya kike fama da dan dunkum din mijin ki kuwa?"

"Kai Yaya."

"Yo Allah ai sai hakuri irin su."

"Na yanzu ba haka suke ba fa Yaya."

"Toh ya suke? Ban labari."

"A ah, kawai dai suna da kirki da dadin zama in dai ka iya zama dasu."

"Ni rashin iya zama da su ne yasa nasha wuya wajen Malam kenan kike so kice."

"Ni? Bance ba Yaya, a bar maganar toh."

"A barta, dan ni ko Qurani za'a dafa ace min masu irin halin Malam na da dadin zama ba lallai na yarda ba, karshen magana kenan."

"Hahaha, karshen magana kenan kuwa Yaya."

"Ah toh "

"Bari na je na gaida Mama toh, zamu dawo muci dambun naman ni da su Amira."

"Wallahi kika gayyato min su tamu ce ni dake."

"Dan kad'an zaki sammana." Tace tana ficewa

"Karfa ki fara na gaya miki." Ta daga murya, sai kuma ta mike ta dauke robar ta shiga da ita daki ta bud'e cikin kayan ta, ta tura a ciki ta rufe har da saka key sannan ta dawo falon tana sababi.

Mama ce kadai a falon da ta shiga, tana zaune cikin ado amma kuma fuskar ta, ta nuna tana dan cikin damuwa, kallon Jiddan tayi sanda ta shigo duk sai taji kunya kafarta ta hau harhadewa ta samu ta karaso ta zube a k'asan carpet cikin tsananin girmanawa ta gaida Maman

"Lafiya lou, kuna lafiya?" Ta dora akan amsar gaisuwa

"Lafiya kalou alhamdulillah."

Jiddan ta amsa cike da mamaki doguwar amsar lafiya lou din da Maman ta baya hade da tambayar lafiyar su bayan a dah lafiya kawai take cewa shima a gajarce tana kin kallon Jiddan

"Goben da karfe nawa zaku tafi?"

"Da asubah yace."

Gid'a kai tayi

"Ga kayan ku chan da yace kuna bukata idan kun tashi sai ku tafi dasu."

"Ok tam, mun gode Allah ya saka da Alkhairi."

"Amin."

Shiru ya biyo baya kan Jidda na kasa baki daya falon yayi mata wani irin mugun girma sanyin AC yasa ta sake shiga wani irin yanayi

"Akwai wani abun kuma da kuke bukata?"

"A ah babu."

"Ok! Ki shiga wajen su Amira suna ciki."

"Toh." Ta mike ta wuce ciki Maman ta bita da kallo tana son sake gasgata Jiddan a matsayin matar Tariq din ta. A dakin su Amira ta dade suka sha shafta anan taji labarin soyayyar Maryam da Ya Isma'il tayi mamaki sosai ko daya Ya Tariq din be fada mata ba, har Isma'il din ma yazo jiya ya tafi yanzu magabatan sa zai turo sai Ya Fauwaz ma da yake so aje ayi masa tambaya. Suna kyautata zaton kuma Baba dukkan su zai hada har Amira tunda duk dama tsiran su a haihuwa ba yawa sosai Tariq ne dama tsakanin su dukka da tazara me dan yawa sai kuma Ya Fauwaz din ma hakan ne amma su matan a kusa kusa duk Mama tayi haihuwar shiyasa suka taso kusan kai tsaya gaba dayan su. A waya Mama ta kira Amira tace ta turo Jiddan, ta tashi da sauri ta zura Hijab dinta suka dinga mata dariya wai taji kiran suruka ta rikice, tana shigowa falon ta hango shi a zaune yayi crossing kafarsa yana shan abu a cikin mug, kallon k'asa k'asa yayi mata ta, ta yi saurin sadda kanta k'asa ta karasa ta zauna daga gefen Maman a k'asa tace

"Gani Mama."

"Wai tafiya zakuyi, kunce babu wani abu da kuke bukata ko?"

"Babu komai Mama, addu'ar ki kawai muke bukata nothing more."

"Toh Allah ya kiyaye ya tsare."

"Amin ya Allah."

Suka hada baki duk da Jiddan a ciki ciki tayi nata amsawar amma ba karamin dadi addu'ar tayi mata ba.

"Ku tashi kuje wajen Babanku."

Mikewa yayi rik'e da cup din ita kuma ta dan russuna tace

"Mun gode Mama."

"Allah ya bada sa'a."

***Jerawa sukayi har part din Baban suka same shi yana waya, Tariq din ne ya fara shiga kafin yace ta shigo, Anty na dakin sa taji shigowar su ta fito lokacin Baba ya ajiye wayar yana duban su

"Mutanen turai." Murmushi sukayi dukka har Anty, Tariq yace

"Baba barka da warhaka."

"Barka dai ango." Ya sake zolayar Tariq din

"Baba ina wuni?" Ta gaishe shi a nutse

"Lafiya lou 'yata, kuna lafiya?."

"Lafiya lou."

"Toh madallah, sai tafiya ko?"

"Eh."

"Toh Allah ya kaiku lafiya ya bada sa'ar abinda aka je nema."

"Amin Amin.," Anty tace

"Sai a kula sosai, rayuwa irin wannan dole sai kun hada kanku kun yi kuma hakuri da juna "

"In sha Allah Baba."

"Ka rike amana, bana so naji ko na gani dan Allah. Hauwa'u amana ce a wajen ka "

"In sha Allah."

"Yawwa, ke kuma ki rike mijinki da kyau kiyi masa biyayya iyakar iyawar ki, Allah yayi muku albarka baki daya ya kade fitina."

"Amin."

Fitowa sukayi ita ta wuce part din Anty shi kuma yaje yiwa Yaya sallama, daga nan yace ta fito suka je gidan Umaima suka mata sallama sannan suka je gidan Safiyya, anan ne kawai taga ya dan sake har ya zauna ma sun dan taba hira da mijin nata kafin suyi musu sallama suma su wuce gida.

#Ranooooo

***❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO KISHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (59)

***Alarm din da ya saita ne na karfe 4 daidai ya tashe su, kallon juna sukayi a lokaci daya sukayi murmushi

"Morning Baby."

Yace yana janyewa ya sauka daga gadon,

"Morning dear.". Tace tana maida masa murmushin. Tashi tayi ta sakko ta nufi wajen kayan su shi kuma ya fice daga dakin. Dan sake gyara kayan tayi sannan ta shiga toilet tayi brush da alwala ta fito tayi raka'atanil fajr ta zauna tana addu'a har aka kira sallar fajr din ta tashi tayi sannan ta cire Hijab din ta fito falon tana tafe tana azkar. Kitchen taje ta sake duba abinda bata sakashi wajen da ya dace ba, ta dan dauraye cups din da Ya Tariq din yasha coffee jiya sannan ta dauko wasu cups din ta dora su akan Iceland ta dafa ruwan tea tasa a flask shima ta dora a wajen sannan ta dawo kan falon a gurguje ta sake gyara shi ta tabbatar komai daidai sannan ta nufi dakin sa. Knocking ta fara yi sannan ta tura kofar bakin ta dauke da sallama. Yana tsaye gaban mirror yana rik'e da bathrobe ta shigo,.

"Yanzu zan kiraki dama." Yace yana sakin rigar wankan ya riko hannun ta.

"Muje muyi wanka Fauwaz yana hanya tare da yaran chan wai sai sun rakaki dole."

"Allah sarki yan uwana." Tace tana murmushi

"Oya." Ya kama hannun rigar zai hau cire mata tayi saurin kwacewa

"Zan iya." Tace tana dariya

"Nima zan iya ai."

"Toh na hutasshe ka, kayi wankan anan ni zanyi a daki."

"Why? Me yasa?"

"Zamu bata lokaci ne."

"Ba wani, kawai dai kinsan baki da gaskiya ne."

"A ah fa, kaga sauri muke."

"Yanzun ma saurin zamuyi, tsayawa ma maganar nan bata time ne." Ya fizgota ya jata zuwa toilet din, ba yadda taso dole ta hakura amma tasan shi ba zai tsaya iya wankan BA wallahi, aikuwa be tsaya din ba haka ya dinga shiriritar dasu har su Fauwaz suka iso, jin gidan shiru yasa Fauwaz kiran Ya Tariq din a waya daga toilet din suka ji kiran, da sauri suka karasa suka fito ya dauki wayar ya kirashi

"Muna shiryawa ne gamu nn fitowa."

Ajiye wayar yayi suka shirya a tare a gaggauce sannan suka fito yayi falo ita kuma ta koma bedroom dinta ta dan karasa abinda zata karasa sannan ta fito.

Tea kawai suka sha shima a tsaitsaye sai snacks din da ta daukar musu wanda Anty ta basu jiya suka tafi. Ita da Amira da Maryam ne a mota daya sai driver shi kuma da ya Fauwaz suma a tasu motar sai wasu motocin biyu har suka isa airport din. Wani kebantaccen wajen suka nufa masu kula da gate din sukayi saurin bud'e musu, suka fito suka shiga cikin building din dake dauke da wani falo a farko sai wani wajn me dauke da round table da kujeru. Falon suka shiga suka zauna suna zama sai ga su Baba nan sun shigo shi da wasu manyan mutane su. Mikewa su Jiddan sukayi bayan sun gaishe su suka koma dayan wajen me round table din suka zauna achan. Suna zaune suna hira kad'an kad'an ya Fauwaz ya shigo yace su taso, jikin ta ne yayi sanyi ta rike hannun Amira suka fito daga wajen, wata hanya suka bi zuwa filin jirgin ba wadda sauran mutane suke bi ba, daga dan baya duk suka tsaya Baba ya dafa kan Jiddan bayan ta durkusa a gaban sa ya saka mata albarka sannan ya mikawa Tariq din hannu suka gaisa yana dan russunawa. Hugging din Fauwaz yayi a karo na farko sannan ya dagawa su Amira da Maryam hannu da suke hawayen rabuwa da Jiddan. Ita kanta hawayen take ta daga musu hannu sannan suka juya suka soma tafiya a jere zuwa wajen jirgin. Sai da suka kai wajen matattakalar sannan suka juyo suka sake daga musu hannu sannan suka haura ciki.

"Allah ya tsare ya kiyaye." Baba yace yana murmushi

"Uwata kuka kike? Da an kwana biyu fa zaku kai musu ziyara."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull