Sanadin labarina complete novel - Chapter 28
Sanadin labarina complete novel Chapter 28: Sanadin labarina complete novel Chapter 28. Yace yana son kwantar musu da hankali. Murmushi sukayi dukka sannan…
4,377 words
Yace yana son kwantar musu da hankali. Murmushi sukayi dukka sannan sukayi wa Baban sallama dan daga nan gombe sukayi zasu duba wani aiki.
Harabar wajen na cike da mutanen da suka yo wa su Baban rakiya, saukin ta motar tasu tinted ce sai kawai suka hade a mota daya sauran motocin suka bi su a baya suka sulalle daga wajen.
***Personal welcoming suka samu a cikin jirgin kasancewar a first class zasuyi tafiyar me full suite dake hade da private bathroom daga nan akayi musu introducing flight attendant din idan suna da bukatar wani abu. Kujerar su irin wanda ke dauke da pod ne da zaka iya converting dinsa zuwa flat bed hade da fluffy duvets. Gefe kuma amenity kit ne da pyjamas sai slippers. Tafiyar almost 13hours ce zuwa Toronto, kanta na saman kafadar sa cikin yanayin gajiya da kosawa saboda bata taba irin wannan doguwar tafiyar ba, an kawo musu menu sun zaba abinda zasu ci amma bata wani iya ci sosai ba sai juice kawai da sandwich. Gyara musu kujerar yayi suka mike sosai ya lullube su da duvet yana sakata jikin sa sosai. Bacci take ji duk da tana tsoro amma kuma kasancewar tare dashi ne sai taji ta sake sosai har ta soma baccin a jikin sa. Ta jima sosai tana baccin kafin ta farka daidai kusan lokacin da saura kad'an su isa. Gyara mata gefen idon ta yayi da hannun sa ya taimaka mata ta tashi zaune sosai shima ya zauna yana mika mata ruwa tasha kad'an ta maida kanta jikinsa tayi lamo. Bayan wasu mintuna da tashin ta akayi sanarwa isowar su da kuma shirin saukar su. Yanayin fuskar ta ne ya sauya ta nuna farin ciki dan batayi tunanin tayi dogon bacci irin haka ba, ta zata sai ta kara wani zaman sannan zasu iso dan tayi matukar gajiya dan ba akwai comportability a tafiyar amma duk da haka ta jigata sosai amma shi ko kad'an be nuna gajiya ba saboda ba yau ya fara ba.
***Wani irin mugun sanyi taji sanda suka fito waje, dunkulewa tayi tana sake tura hannun ta cikin katotuwar rigar sanyin da ya saka mata. Kafadarta ya kama ya rik'e ta sosai a jikin sa zuwa motar da zasu shiga daga train station din zuwa gida bayan sun bar airport din train suka hau zuwa garin su sannan suka iso. Ko kad'an bata wani ganin gaban ta lafewa tayi kawai a jikin sa sanyin na cigaba da ratsa ta. Tafiya kad'an suka isa gidan nasu da yake a sama, hannun ta duk ya kankare duk da handsocks din da ta saka har guda biyu, shi ya rike mata jakar hannun ta, da sauran kayan nasu, suna kokarin shiga lift Ishaq ya cimmasu shi da Yasmin da suke ta sauri. Wani kallo Yasmin din tayi ma Jidda itama ta dan kalleta kadan kafin ta yi gaba kawai suka shiga cikin lift din dukka. Ishaq ne ya tayashi da kayan.
"Welcome back Captain" Yasmin tace tana kallon fuskar sa
"Thank you." Yace a gajarce, ya mika wa Tariq hannu alamar ya bashi card din kofar, mika masa yayi yace
"Idan kun huta zamu dawo mu gaida Anty amarya."
Banza Tariq yayi masa dan ba karamin kular dashi yayi ba, akan me zai taho da Yasmin bayan yasan baya so kuma yasan hakan zai yi hurting din Jidda? Tura kofar yayi ya matsa mata ta shiga ciki sannan yatura kayan nasu yana tare kofar ganin kamar Yasmin din neman shiga take yi
"Yasmin muje mu barsu su huta."
"Ok."
Tace tana kada kanta ta juya cike da tunanin wacece suka zo da Tariq din nata tunda ko da wasa Ishaq be gaya mata yayi aure ba.
Suna shiga Jidda tayi saurin hayewa saman gadon ta ja katoton bargo ta lullube har saman kanta saboda yadda take jin kamar ta kankare. Ajiye kayan hannun sa yayi ya karo karfin room heater din nan da nan dakin ya dau dumi sosai a hankali a hankali taji sanyin na barin ta. Zama yayi a gefen ta yasa hannu ya bud'e mata fuskar ta suka kalli juna
"Are you feeling better?" Yace yana taba saman forehead dinta
"Yes I'm ok, wai sanyi kaman mutum zaiyi freezing?"
Dariya yasa
"Haka suke kuma kinzo a lokacin sanyin ne shiyasa, amma zaki saba."
"A hakan? Ba zan iya sabawa ba."
"Zaki saba, baki ga su Ishaq ba? Kamar ma ba sanyin ake ba."
"Matar sa ce dayar?" Ta tambaye shi tana kallon fuskar sa
"Itace Yasmin!"
Yace yana dago kanta ya dora a saman cinyar sa, shiru tayi tana hango haduwar Yasmin din da mugun wayewar ta. kamshin turaren ta har yanzu yana mata yawo a hanci kana ji kasan irin designer perfumes din nan ne masu shegen tsada da kamshi.
"Don't worry zan yima Ishaq magana akai, I don't want any problem."
Bata ce komai ba, tana jinshi yana zare mata scalf din kanta, sannan ya janye kan nata ya dora a saman pillow ya mike ya wuce toilet yaje ya hada ruwa me zafi a cikin tub yazo ya mikar da ita
"Muje ki rage gajiyar nan."
Tashi tayi ya ja hannun ta zuwa toilet din duk tayi sanyi sosai, shi da kansa ya cire mata kayan jikin ta ya bar mata na cikin kawai dan baya so ya kara mata wata gajiyar akan wadda take ciki. Fitowa yayi ya barta a ciki tayi wankan ta fito ta shafa mai ya taimaka mata ta saka kaya masu dumi sosai sannan ya shiga toilet din shima yayi wankan hade da alwala yazo sukayi sallah daidai lokacin da order din da yayi ta iso ya fita ya karbo ya kawo musu suka ci abincin. Bacci kawai take so tayi dan idon ta har lumshewa yake tana gama cin abincin taje tayi brush tazo ta kwanta ya dan kalleta yana Jona system dinsa dan yana saka sim din sa har ya samu kira amma be daga ba sai ya jona system din ya zauna yana dubawa abubuwan da suka turo masa wanda zai fara gobe as early as 8am. Cikin bacci taji ana gyara mata kwanciyar ta, ta dan bud'e ido kad'an ya rungume ta yana rufa musu blanket din dukka jikinsu.
*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350
2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_ 400 *(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_ 400 *(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_ 400 *(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_ 400 *(Mamu gee)*
5... _BABU SO_ 400 *(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/25, 3:55 PM] Rano2: _SL__**
©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (60)
***Tun da sukayi sallar asubah ta koma bacci, be fada mata zai fita ba dan yaga alamar a gajiye take tikis har lokacin sai bin gefen gado take karshe ta haye tana jan duvet ta rufe kanta nan da nan kuwa tayi bacci. A nutse ya shirya cikin shigar farar shirt me layin baki daga saman shoulder din, navy blue dogon wando sai light blue tie. Be saka jacket da cap din ba sai ya ajiye su a gefe ya gyara zaman waist belt dinsa sosai ya shiga dan madaidacin kitchen dinsu ya samo coffee yasha kad'an sannan ya fito ya saka dark blue din sau ciki ya dauki briefcase dinsa ya dora cap din akan sa ya rike jacket din a dayan hannu ya zo daidai kanta ya durkusa kad'an yayi mata peck a gefen kuncin ta, ya ajiye mata note a gefen gadon ya fice da dan sassarfa. Cikin bacci taji kamar ana taba kofa, ta bud'e idonta kad'an tana wurwurga idon ta a dakin tana neman sa, baya nan sai ta sakko da sauri ta fito falon nan ma baya nan. Kofar taje ta bud'e a zaton ta ko shine ya dan fita sai taga Yasmin a tsaye taci uban kwalliya rike da basket me kyau a hannun ta.
"Goodmorning." Tace mata tana rabawa ta shiga cikin gidan kai tsaye, sakin kofar Jidda tayi tabi bayan ta tana jin duk ta muzanta dan ko brush batayi ba bare wanka.
"Captain fa?" Tace tana kallon falon
"Oh yau fa dole ya fita da wuri na manta, oops ya akayi na yi late har ya fita? Allah yasa ma yayi breakfast dan nasan yau kam zai zama so busy."
Kallon ta kawai Jidda take bata ce komai ba amma maganganun ta sun dan taba ta, kenan fita yayi amma ta share baki tana bacci babu wanka bare tayi tunanin samar masa abinda zai karya.
"Kanwar sa ce ke amma ko?"
Tace tana zama bayan ta gama karewa falon kallo
"Umm." Jidda tace tana kokarin barin wajen
"Very beautiful kamar shi, amma fa ya fiki kyau."
Tayi dariya, yak'e Jidda tayi ta wuce kawai ciki ta barta a falon bakin ciki na tirnike ta, daga zuwan ta? Sai ta fara cin karo da irin wannan masu budadden idon? Tana daki tana jin motsin ta a falon ko me take yi oho, wanka ta tashi ta shiga ta dauko wani kaya da take tunanin da BA zata iya sawa ba saboda da kunya amma da taga irin shigar da Yasmin din tayi cikin wani matsattsen jeans da riga ta saka turban kawai akanta ko mayafi babu yasa ta ji itama zata iya. Wankan tayi ta fito ta shirya cikin rigar da ta kasance red colour ta shafa kalolin turarurruka masu kamshin gaske harda wani hadin khumra da Anty ta siya mata a wajen wata mata. Rigar da kadan ta wuce guiwar ta sai ta saka socks me dan tsawo ta gyara gashin kanta ta saka hair band ta fito da gashin ta tsakiyar kan. Light makeup tayi ta shafa red jan baki sosai wanda ya sake fito da sihirtaccen kyawun ta. Rigar daga saman wuyan an dan tsaga ta sai ta dora farar karamar rigar sanyi irin me gashin nan. Yunwa take ji sosai, ragowar abincin da sukayi order jiya ta tuno ta fito falon, Yasmin na zaune tana kallo a TV tana danna waya ta saki baki ganin Jiddan, kin kallon ta Jiddan tayi ta wuce kitchen din da yake cikin falon Yasmin din na kallon ta tunda ba wai a rufe yake ba, fridge ta bud'e ta dauko abincin tayi warming dinsa a microwave ta zubo a plate tazo ta zauna a kujerar dake facing dinta ta shiga cin abincin a hankali.
"Ya sunan ki?"
Dagowa Jidda tayi ta kalle ta,
"Na'am?"
"What is your name? Sannan menene alakar ku da Tariq?"
"Jidda, alakar mu kuma wannan shi zaki tambaya ai."
"Me yasa?"
"Zai fi iya fada miki ai."
"But baya tsayawa ya saurare ni ai, ni kadai nake son shi amma shi ko kallo ban ishe shi ba, please i need your help."
Wani kallo Jidda tayi mata irin kallon baki da hankali din nan, sannan tayi dariya kawai tana cigaba da cin abincin ta dan ta lura sam Yasmin din bata da hankali.
"Please kanwar mu, wallahi inason shi sosai."
"Naga alama ai, ki sameshi kawai kiyi masa magana nima tsoron sa nake ji."
"Ba zaki iya ba?"
"No ba zan iya ba."
Tace tana mikewa, taje ta wanke plate din ta gyara wajen ta dawo falon ta zauna tayi connecting wayarta da wifi ta kira Amira facetime, lokacin su kusan biyar din yamma. Bata daga ba sai kawai ta mike ta dan kalli Yasmin din tace
"Ki gaida gida ni na shiga ciki."
"Tafiya zan nima, idan ya dawo kice nazo, ga breakfast dinsa nan hade da lunch zan kawo dinner."
"Chef ce ke?"
"Yes." Tace tana murmushi
"Ok yayi."
Tace tana yin gaba, ita kuma Yasmin din ta mike sai gashi ya turo kofar ya shigo, tsayawa chak Jidda tayi jin an budo kofar wanda ta tabbatar da shine, kayan jikin ta, ta kalla kunya na kamata amma sai ta daure ta cije ta juyo tana fuskantar sa., Takalmi yake kokarin cirewa ya lura da Yasmin din dake tsaye a falon nasu, sai Jiddah ta ya kalleta ya sake kalla kafin ya tabbatar da itan ce ko wata ce daban saboda tsabar kyawun da yaga tayi masa. Da wani irin salo da bata san ta iya shi ba, ta nufe shi ta karasa da dan sassarfa ganin yadda yake bin ta da wani irin kallo, rungume shi tayi da sauri ya saki jakar hannun sa yana kankame ta sosai a jikin sa.
"Welcome home baby." Tace tana ciro kanta daga kirjinsa, kin cikata yayi yana shakar kamshin turaren da take yi cikin wani irin yanayi
"I missed you so much."
"Ba kai ne ka tafi ka barni ba?"
"I'm so sorry kinji? Bana so na tashe ki ne naga kin gaji sosai, shiyasa amma dama ba dadewa zan ba."
"Tom shikenan na hakura." Tace tana masa murmushi
"You look very beautiful."
Yace yana kallon kayan jikin nata, murmushi tayi ta duka ta dauki briefcase din tasa ta rike hannun sa
"We have a visitor."
Tace tana nuna masa Yasmin dake tsaye kamar gunki.
"She's not welcome here." Yayi mata whispering a kunne.
"Yasmin welcome, meet my beautiful wife Jidda."
"Oh,okh yayi, Allah ya bada zaman lafiya. But she's young!"
"Young and sweet." Yace yana kissing hannun Jiddan da ke cikin nasa.
"Bari na wuce, Allah ya taimaka."
"Amin mun gode." Jidda tace tana mata murmushi
"Kin manta basket dinki." Tace mata ganin zata fice, banza tayi ta karasa ficewa da sauri. Kicibis sukayi da Ishaq sai kawai ta fashe masa da kuka
"Subhallahi, me ya faru Yasmin?"
"Ishaq Tariq sam bashi da tausayi, ashe aure yayi? Duk yadda nake son shi me yasa baya so na? I'm I ugly? Or what?"
"Calm down, kinsan akwai differences tsakanin ki da Tariq, beside be taba furta miki kalmar so."
"Na sani, kuma I'm 100% ok with that hoping zai iya so na ko gaba ne, amma saboda tsabar wulakanci kaga abinda sukayi min shi da so called wife din shi?"
"Kiyi hakuri please, bari zamuyi magana dashi."
"There no need Ishaq, na hakura wallahi."
Sai ta juya da sauri ta bar wajen. girgiza kai yayi ya fasa zuwa wajen Tariq din kawai ya bi bayan ta.
***Yana zaune kamar sarki ta cire masa tie din ta kawo masa ruwa yasha sai ya jawota kan kafarsa ya manna kansa a jikinsa
"Kin yi kyau Jidda na,and naji dadin yadda kika fahimce ni, kuma kika yi treating Yasmin yadda ya kamata ba hauka ba zubar da class, she mean nothing to me kuma itama ta sani, Ishaq ne duk yayi complicating abun yana bata false hope bayan yasan ba haka bane ba"
"Allah sarki, sai dai tayi hakuri."
"Tariq naki ne ke kadai ko?"
"Yes!" Ta gida masa kai
"Good." Yace yana dariya
"Mine and only mine."
Ta dora tana tashi daga jikin sa rike da tie din nasa. Jawota yayi ya maida ita ta zauna
"Then give me cin hanci idan kinaso na zama yours baki daya."
"Me kake so?"
"Anything special."
"Ok an gama ranka ya dade."
"Wow! Sai ni dan gata." Yace yana matso da fuskar sa tata, yasa baki akan lips dinta ya shiga tsotsa a hankali in a passionate way.
***Rayuwa me dadi da inganci suke yi a tsakanin su cike da kaunar Jun, Tariq baya shakkar nunawa kowa irin kalar soyayyar da yake mata musamman yanzu da suke kasar masu jajayen kunnuwa da babu wanda zai damu da abinda kake ciki ko kayi. Tare suka je ya bawa Yasmin hakuri dan ko yaya ne mutumin da yace yana son ka yafi wanda yaki ka, ashe ma tun ranar da abun ya faru Ishaq ya shigar da kansa wajen ta, and she accepted saboda dama sun shaku sosai. Duk da busy schedule din Tariq haka yake kula da Jiddan sosai kuma kullum a gida yake kwana tunda har yanzu be fara zama irin so busy din nan ba. Duk abinda zai yi within kasar yake ya dawo amma dai daf yake da fara fita wasu kasashen anan ne kuma dai dole Jidda tayi hakuri, be taba jin yana da second option a aikin nasa ba sai da ya tabbatar dole watarana ya dinga tafiye tafiye sosai kuma ba tare da Jiddan tasa ba. Wajen taran dare ya shigo gidan a gajiye tikis yana hanya sukayi magana da Fauwaz akan maganar auren sa da aka tambaya wanda Baba yace dukka zai hada harda su amira tunda itama ta samu mijin maryam dama Ya Isma'il ne, da murnar sanar mata ya shigo gidan amma sai ya sameta a kwance ta lulluba da bargo tana rawar sanyi, da sauri ya yaye mata bargon ya durkusa a gaban ta
"Subhallahi, menene?" Yace yana dagota jikin sa
"Zazzabi nake da amai."
Tace tana rufe idon ta saboda tsabar yadda ta galabaita dan kusan sau ashirin tana amai.
"Shine baki kirani ba? Kinga yadda kika galabaita?"
Yace yana cire blanket din saboda yadda zazzabi ya rufe ta sosai. Ruwa ya debo a tap me dumi yazo ya rurrufe dakin sosai yazo ya jawota jikin sa ya janye rigar ta ya shiga goge mata jikin da yayi zafi sosai. Sai da yaga zazzabin ya dan daidaita sannan ya shiga ta wayar sa yayi booking appointments na ganin Dr ya zabi 1hour sannan ya gyara mata jikin ta suka tafi asibitin. Suna zuwa akayi mata duk gwaje-gwajen da za'a mata aka tabbatar she's pregnant, tsabar murnar be san sanda ya dagata sama ba, dariya Dr din ta dinga musu sannan ta basu maganguna suka dawo gida. Tun daga lokacin shikenan kuma laulayi ya fara me matukar wahalarwa, duk sanda zai fita kamar zai mata kuka saboda tausayin ta,amma sai ta karfafa masa guiwa ta samu ya fitan baya dadewa sosai yake dawowa sai kuma washegari. Da haka har cikin yayi kwari sosai,daidai lokacin bikin su Ya Fauwaz, be so ba dole yace ta fara shiri ya kaita gidan saboda shima aikin nasa ya fara matsawa sosai dan zai iya tafiya yayi kwana biyu ko uku ma baya nan, kuma ko ya dawo ba zai fi yan awowi ba zai sake tafiya. Murna sosai ta hau yi dan batayi tunanin zasu je gida nan kusa ba, shi kansa be yi tunanin hakan ba amma gwara gidan da ta zauna anan din babu kowa shima ba zama yake ba ga ciki kuma.
***Kwana biyu da maganar tafiyar ya siya mata ticket ita kadai dan bazai samu damar zuwa ba kuma, duk bashi da walwala ganin haka yasa ta nuna murnar ta duk da itama a gefe daya bata san yadda zatayi coping idan babu shi ba, ya riga ya saba mata da caring dinsa haka dole zata sha famar rashin shi. Ana gobe zata tafi ya kanainaye ta dan tun magriba ya dawo gidan ya hanata sakat duk in da ta motsa yana manne da ita, ji yake kamar yace ya fasa aikin nasa kawai su tafi tare su koma gida suyi normal rayuwar su amma ya zai? Da k'yar ya barta ta karasa hada kayan da zata tafi dasu suka yi dinner yace bacci yake ji ta san sarai kuma ba wani bacci rigima ce irin tasa gashi ita yanzu sam bata san abinda yake so din amma shi kamar wanda aka kara ingizowa baya taba barin ta abu kad'an tayi sai yace tayi turning nashi on, haka dai take daurewa yanzun ma haka ta daure dai dan ta lura da duk take-taken sa zai iya canceling tafiyar yace sai wani lokacin shiyasa take ta lallabawa tana bin sa yadda yake so din. Ita ta fara tashi da safe bayan sun yi sallar asubah maimakon ya barta ta karasa abinda zata karasa kafin su tafi amma ya ki barin ta, ya rike ta kam yana tura kansa cikin rigarta wajen da tafi komai daukar hankalin sa yanzu a jikinta saboda yadda suka kara girma sosai. Bata hanashi ba duk da ta kai karshe amma haka ta taimaka masa ya samu abinda yake so sannan sukayi wanka tare suka shirya. Zai wajen azahar sannan suka fita zuwa airport din suna zuwa yayi mata duk abinda zai yi, ya rakata har cikin jirgin yana rik'e da ita, sai da ta zauna sosai tana kallon sa yayi hugging dinta so tight a hankali ya rad'a mata
"Ki kula min da kanki da babyna "
"In sha Allah."
"I love you so much Jidda nah."
"I love you too."
"Allah ya kiyaye, call me da kun isa dan Allah "
"I will, in sha Allah."
Tashi yayi ya juya ya fice ganin saura kadan jirgin ya tashi, yana tsaye daga gefen wajen jirgin ya soma tafiya a hankali a hankali har ya daga sama, ya sauke ajiyar zuciya yana komawa ciki dan shine zai dauki next passengers din da zasu tashi zuwa Manchester.
***Kasancewar ba wannan ne tafiyar farko ba sai taga dan saukin tafiyar duk da shima ta galabaita, san gefen ta akwai wasu couples da yaran su,su biyu kuma yan Nigeria ne sune ma suka zama kamar yan uwanta. Matar me suna Amrah da Mijinta Sultan (Abinda Ke Cikin Zuciya) sai yaran su biyu, sun burgeta sosai saboda yadda suka shaku da junan su kuma yadda sukeyi ita da mijin nata ya kara sa mata kaunar Ya Tariq dinta tana hasaso suma sun zama haka watarana. Exchanging contacts sukayi da matar daidai lokacin da suka iso filin jirgin na Abuja. Mama ce da kanta tazo daukar ta, tunda ta samu labarin cikin Jiddan take cike da matukar farin ciki, sun dade da shiryawa da Baba kuma tsakanin ta da Anty babu laifi kadaran kadahan Yaya ce dai take shan gata daidai gwargwado a wajen ta. Mamakin Jiddan ne ya dadu sanda suka fito taga Maman a tsaye tare da Amira da Usman suna jiran ta, da sauri Amira ta taho zata rungume ta Mama ta daka mata tsawa
"Baki da hankali ne? Baki ga halin da take ciki bane ba?"
Kunya ce ta kama Amiran ita kuma Jidda ta dinga dariya ta karaso ta russuna zata gaida Maman tace Maza Maza ta mike ba'a son me ciki da durkuso,tashi tayi a kunyace ta gaida Maman ta amsa tana kallon cikin nata.
***Rayuwa ce ta cigaba da garawa cikin ikon Allah har cikin Jidda ya shiga wata tara, an yi bikin su Amira Wanda Jidda ta zama itace akan komai dan hatta Mama ita ta barwa ragamar komai duk abinda zatayi sai ta nemi shawarar Jiddan wanda take cike da kaifin tunani hakan ya sa ta kara shiga zuciyar Maman sosai. Yaya ce tazo ta zauna da ita da k'yar sanda ta shiga wata takwas dan sai da Baba yasa baki sannan ta yarda tazo suka zauna. Waya suka gama kenan da Ya Tariq yace ta tashi ta fita ta dan zazzagaya gidan saboda tace masa bata jin dadin jikinsa. Yunkurawa tayi da nufin tashi taji wani abu ya soke ta da sauri ta durkusa ta kwala kiran Yaya. Tare suka shigo da sabuwar me aikin ta da mama ta kawo mata bayan Godiya, da sauri ta fita tace a kunna mota dan har Jiddan ta kai kasa saboda wani irin murdawa da cikin ta yayi ga wani irin ciwon mara da ya taso mata gadangadan. Yaya ce ta riketa tana mata sannu, Godiya taje da sauri ta sau waya ta kira Aunty ta fada mata, sai ta aika Usman tace ya fadowa Mama aikowa mayafi kawai ta yafa ta fito, kafin taje sun wuce asibiti sai ta bisu chan din. Cikin ikon Allah ana zuwa ba'a fi minti talatin ba Jidda ta haihu haihuwa me sauki kuma lafiya lou dan ko karuwa batayi ba. Murna a wajen Mama tayi saurin kiran Anty t fada mata sannan ta kira Baba shi kuma ya kira Tariq yana tsaka da shirin tahowa dan ranar zai baro kasar sai ga kyakkyawan labari. Sujuduj shukur yayi yana kara godiya Allah da ya sauke ta lafiya.
Mace aka samu me kama daya sak da Jiddan har farin kamar dai yadda Tariq din kullum yake jaddada mata me kama da ita yake so. Nan da nan asibitin ya cika da su Anty, Amira, Ya Safiyya da babyn ta haka ma Umaima, Ya Fauwaz da matarsa. Maryam ce kawai bata nan tana Kano amma an kirata an fada mata. Baba ne yazo yaga sabuwar amaryar tasa wadda Yaya ta rike ta kam ta hana kowa sai dai Ka kalle ta a hannun ta, Baba kawai ta bari ya dauka shi da abokin sa amma daga su bata sake barin kowa ba. Kasancewar kalou aka haihu yasa basu kara awa daya ba aka sallame su. Gida aka wuce da ita part din Mama in da dama tun kafin haihuwar tasa aka gyara mata dakin dan so take ta kara wanke kanta a wajen Tariq din da Baba har ma da Jiddan.