Kenza eBookz

Sanadin labarina complete novel - Chapter 3

Sanadin labarina complete novel - Chapter 3

Sanadin labarina complete novel Chapter 3: Sanadin labarina complete novel Chapter 3. Dariya sukayi shi da Jiddan, Yayan ta cigaba da sababi akan bokon,…

4,368 words

Dariya sukayi shi da Jiddan, Yayan ta cigaba da sababi akan bokon, sai ga su sun shigo part din, Amira ce ta ja hannun Jiddan ta zaunar da ita a gefen Ya Fauwaz, maryam ta tsaya daga tsaye tace

"Tun muna daki muke jiyo maganar ki Yaya."

"Ko kice daga bangon duniya ba."

"A'ah dakin dai, kina magana ko hadiyar yawu bakya yi Yaya, ki dinga hutawa."

"Tunda ki kike ci dani kike sha dani, ai sai ki gindaya min sharadi, mutum da bakin sa an isa a hana shi magana ne."

"Allah ya huci zuciyarki gimbiya Yaya, ba abin fada bane."

Tace tana zama a kusa da Amira, suka saka Yayan a tsakiya, wani iri Jiddah take ji, musamman da bata taba experiencing irin wannan rayuwar ba, sai take jin wata nutsuwa na saukar mata, a kalla zatayi rayuwa irin wadda mutane da yawa suke yi, a kalla zata san dadin zama cikin mutane tayi gogagya dasu cikin rayuwa. Sun dade a wajen Yayan har sai da Mama ta aiko su zo kitchen lokacin girkin rana yayi, bata bi su kitchen din ba, ta wuce ciki ta samu Anty tana bacci ita da Usman , sai ta shige daki ta kwanta kawai tayi lamo akan gadon rayuwar ta na dawo mata daki -daki, mataki-mataki. Bata san daga nan wanne mataki zata taka ba, Amma ko ma wanne iri ne zatayi kokari wajen kula da rayuwar ta da kanta, dan ba zata so ta sake maimaita rayuwar ta, ta baya ba. Washegari litinin suka tashi da shirin zuwa makaranta, tun asubah kowa na gidan ya mike aka hau shirin shiryawa, tana shara Anty tace ta ajiye taje tayi wanka dan tare da ita zaa tafi makarantar, fuskarta ce ta fadada da fara'ah, tayi saurin karasa sharar yayi wanka a gurguje dadi na kamata, kaya ta tarar akan gadon da skirt underwear sai half vest da kayan da Antyn ta bayar aka dinka mata, underwears din kuma Abu ta bawa ta siyo mata a kasuwa. Dauka tayi ta saka, ta shafa mai sannan ta zura sabon Hijab din da yake gefen kayan, tamkar ba ita ba, ta sauya sosai kayan sun mata kyau yar fuskar ta fayau ta sake fitowa. Hijab din da ya kasance mint green ya karbi fatarta sosai kasancewar ta fara sosai. Tana ta kallon kanta a mudubi Anty ta shigo tace ta fito su yi breakfast, sai ta tsaya tana kallon ta baki bude

"Masha Allah Jidda, kin yi kyau tabarakallah Masha Allah. Kin ganki kuwa? Lallai zaa yi kallon yan matacci anan."

Murmushi tayi ta sunne kanta cike da kunyar yabon da Antyn tayi mata, tabi bayanta, ta bata tea da bread anan falon ta, tana sha Amira ta leko tace ta fito, ta tashi da sauri bata gama ba ta ajiye kofin, ta saka takalmin da Antyn ta bata, tace

"Zamu tafi.."

"Toh Jidda, Allah ya bada sa'a, kiyi karatu sosai kinji? Shine gatanki."

Da kai ta amsa, ta nufi kofar ta biyo ta suka fito harabar gidan, Safiyya na tsaye rike da hannun Usman da Muhammad, ita tayi candy wannan shekarar, ta kalli Jiddan da suke fitowa tare da Amira rike da hannun juna, kauda kai tayi kawai bata ce komai ba, ta taimakawa yaran suke shiga motar, Maryam na ciki a zaune da Umaima, sai ga Fauwaz ya fito daga wajen su yana gyara hular da ya dora akan manyan kayan da ya saka, ya gaida Antyn sannan ya shiga gaba gefen me zaman banza. Zama Amira tayi bayan ta matsawa Jiddan itama ta zauna, driver da Baban ya samo musu saboda zuwa makaranta ya tada motar, suka fita daga gidan. Sai a sannan Safiyya ta gaida Antyn a gajarce ta shige ciki da sauri. Duk cikin yaran gidan Safiyya ce kawai bata sakewa da ita, ta kuma san dalilin yanayin da mahaifiyarta ta karbe ta ne, tana kokarin taya mahaifiyar ta kishi, shiyasa ma bata taba damuwa da yanayin yarinyar ba, sau tari tana ganin ta amma kallon kirki bata isheta ba bare ta samu matsayin gaisuwa. Tana shigowa falon sukayi kicibis da Mama, wadda ta cika tayi fam daga gani a cikin bacin rai take.

"Ina kwana Maman Fauwaz?"

"Bana son abinda kike min gaskiya, yanzu tsakani da Allah aure min mijin da kikayi be isheki ba, sai kin kakaba masa rike miki yar dan uwan da ya kasa rike amanar da Allah ya bashi, ba zaki duba shi nauyin da yake kansa ba na yaran sa."

"Me ya faru?" Tace kamar bata san maganar da Maman take yi ba

"Makarantar yaran nan da kika saka babansu ya kai yarinyar da kika dauko."

"Wai Jidda?"

Shiru tayi ranta idan yayi dubu ya baci

"Ayya kiyi hakuri, shi da kansa yayi niyya yace zai saka ta bani na nema ba, sannan naga ai d'a na kowa ne Maman Fauwaz, ba'a san wanda zai more shi ba."

Tana fadan haka ta shige ciki da sauri dan tasan tsaf yadda ran Maman yake a bace za'a iya yin batacciya. Bata san tashin hankali ko kadan shiyasa duk yadda taso suyi rigima taki bata kofa, idan ta fara ma sai tayi shigewarta daki ta barta.

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: *__SL__**

©®*_*_Hafsat Rano_*_*

Page (6)

****Fauwaz ne yayi mata duk cike-ciken da ya kamata yayi mata, ya biya kudin da komai sannan akayi mata interview, yanayin karatun ta ba irin nasu bane dan haka abubuwa da yawa bata gane ba, a jss 2 head teacher din yace a sakata Fauwaz ya roki a sata 3 tunda yanzu aka juya session din, hoping zatayi coping kafin time din, haka akayi aka sata ya rakata har kofar class din su da yake kusa da na su Amira ss1, tsayawa tayi tana kallon sa, a hankali tace

"Nagode Ya Fauwaz."

Murmushi yayi mata sannan ya tafi, ita kuma ta shiga cikin ajin. Duk suka zuba mata ido suna kallon ta, tsayawa tayi daga jikin kofar ta sunkuyar da kanta kasa, Safeera ce ta taso daga seat dinta tazo ta sameta a tsaye tace

"Taho ki zauna."

Bin ta tayi zuwa seat din dake kusa da na Safeeran ta zauna sannan tayi mata godiya.

"Nagode."

"Ba komai, ya sunan ki?"

"Jidda..."

"Nice name, ni kuma sunana Safeera, ki saki jikinki, duk wadda ta raina miki hankali ki fada min."

Murmushi tayi mata bata ce komai ba, uncle ya shigo suka maida hankalin su zuwa kansa, kowa ya mike aka gaishe shi sannan yace new comer ta tashi tayi introducing kanta, bata motsa ba dan da turanci yayi maganar sai da Safeerah ta rada mata, ta tashi da sauri a kunyace ta tsaya,ya sake maimaitawa

"What is your name?"

Tace

"Jidda."

"Hauwa'u right?" Ta daga kanta

"Ki fada har da sunan Baba." Safeera ta sake whispering mata

"Hauwa'u Ibrahim."

"Ok welcome to Jss 3 Hauwa'u, seat down."

Zama tayi jikinta a sanyaye, turancin shine babbar matsalar ta a yanzu, dan su a chan da Hausa ake koya musu yawancin subjects din. Introducing new topic yayi ya shiga bayani wanda kusan rabi babu abinda ta fuskanta, Safeera na lura da ita, har ya gama ya fita, ta kalleta bayan malamin ya fita tace

"Baki gane ba ko?"

Daga mata kai tayi alamar eh

"Zan miki bayani idan an fita break, sannan karki ji tsoro, turancin ma bashi da wahala, da kin gane shikenan."

"Nagode." Tace tana mata murmushi

"Can we be friends?" Tace tana mika mata hannu, hannun ta kalla hakan ya saka Safeera yin dariya

"Zamu zama kawaye?" Ta fada mata da hausa, gid'a mata kai tayi ta mika mata hannun itama, suka gaisa

"Friends for ever." Tace tana sake matsar da chair din ta kusa da ta Jiddan.

"Duk abinda baki gane da turanci ba ki fada min, sannan akwai dictionary ma, duk kalmar da kika ji baki gane ba, ki duba zaki ganta da meaning da komai, zakiyi mamaki yadda zaki improving sosai."

*Shikenan, nagode sosai."

Hannu ta mika mata

"Taso muje muyi break kafin a dawo class."

Mika mata hannun tayi suka fito compound din makarantar, Amira da ke zaune tare da friends dinta ta taso da sauri

"Jidda."

"Kin santa?" Safeera ta tambaya

"Gidanmu daya." Amira tace sannan taja hannun ta

"Muje kafin a koma class."

Bin ta tayi safeera tayi tsaye tana kallon su, Asiya ce tazo kusa da ita tayi dariya tace

"Daga ganin yarinya kin makale mata, gashi nan ai."

"Ina ruwan ki?" Tace tana barin wajen, taje ta siya egg rolls guda biyu da lemon cway ta ci daya ta dauki daya ta je wajen da suke zaune da amira da kawayenta, ta mika mata

"Kawata gashi."

"Ta gode taci meat pie."

Amira tace tun kafin ma Jiddan tayi magana, ran safeera be yi mata dadi ba, ta juya zata bar wajen Jiddan ta mike da sauri ta ce

"Amira bari muje aji zan karasa rubutu."

"Tsayani." Tace da sauri tabi bayan ta, hakan ya sakata sakin fuskar ta suka koma ajin suka zauna, ta karbi eggroll din taci kadan, ta ajiye sauran.

Tun daga ranar Safeera ta zama kawarta, duk da da farko bata sake da ita ba, sai da ta fara fuskantar ta da halin ta, she's very simple ba kamar sauran yan ajin nasu ba, dan ba kasafai suke mata magana ba ma musamman tunda suka gano bata iya turanci ba. Dan ma suna shakkar Safeeran ne da wani abun ba haka ba, ita take koya mata duk wani abu da tasan zai saka yan ajin su kalli Jiddan a matsayin koma baya ko kuma ba level din su bace ita Sosai ta bada himma akan karatun ta, duk kuwa da tana shan bakar wahala amma haka ta dage, ko yaushe ta zauna tana rike da littafi, babu maraya sai rago, kuma babu abinda ba zaka iya ba in dai ka saka ranka. Rabin rayuwar ta a bangaren Yaya take yin ta, hakan yasa Amira da Maryam suma ko da yaushe suna shashen, bata bin su wajen su saboda ko taje ma bata samun fuska a wajen Maman dan kiri-kiri take nuna mata bata son ta tare da yaranta, sanin haka yasa itama ta tsaya iyakar matsayin ta, bata zak'e ba bare a samu matsala. Tsakanin ta da yaran gidan musamman Fauwaz,amira da Maryam ba zata ce akwai wani banbanci da suke nuna mata ba, zuwan ta ma ya kara musu shakuwa da Anty tunda ko yaushe suna manne da ita idan basa wajen Yaya toh suna part din Antyn. Bangaren islamiyya ma alhamdulillah, da naci da dagiya tana gane komai a hankali a hankali kan nata yake sake budewa, tun bata ganewa har ya zamana ta soma dauka sosai fiye da yadda tayi tunani. Hakan yake karawa Anty Jin dadi dan tana kyautata zaton ilmin shine gatan Jiddan ba komai ba. Aikin gida duk ta hanata komai girki kawai take tayata shima saboda bata so a samu matsala ko gaba idan tayi aure. Sau kusan uku Tariq na kiranta bayan tafiyar sa, idan suka gaisa sai yayi mata maganar Jiddan duk da baya fadin sunan ta sai dai yayi alamar yadda zata gane, dariya kawai takeyi tace toh zaa yi, sau daya ta bawa Jiddan labari da ta ga bata nuna interest dinta akan maganar ba sai kawai ta share itama.

***Rayuwa ta cigaba da garawa cikin ikon Allah Jidda ta kammala jss 3 zata tafi ss1, Amira Ss2, Maryam ss3 ita da Umaima. Hutu Anty ta shirya musu zuwa chan garin su, ta fadawa Baba yace idan sun shirya zai saka driver ya kaisu amma kwana uku kawai zasuyi su dawo. Shiru tayi dan taso ace ko sati ne su yi, kallon ta yayi yaga kamar tana tunani yace

"Akwai wani abun ne?"

"Eh wai da ko sati ne."

"Kwana uku nace, ba kari kuma."

"Toh Jiddah ko zaa barta ita tayi satin saboda Yaya."

Da sauri ya waigo dan da har yayi shirin shigewa dakin sa

"Ban gane ba, an yi hutun islamiyya ne?"

" A'ah."

"Toh kwana uku zakuyi ku juya, ni ne uban Jidda ni nake da iko da ita a yanzu ba Yaya ba, idan kuma iyakata zaa nuna min toh."

"Allah ya baka hakuri." Tace tana sauke kanta a kasa, daki ya shige be sake magana ba, Mama dake tsaye tun dazu a kofa tayi tsaki ta shigo fuskarta a hade, ta kalle ta itama ta kalle ta, ta sake jan wani tsakin sannan tace

"Ki gama munafuncin ki da shishigin ki da son lallai sai kin nana masa yar da ba tasa ba, zaki wani fake da munafunci da iyayi."

Tashi tayi kawai tayi hanyar fita ta bar mata dakin, dan dama basa taba hada zama waje daya dan in dai tana wajen Baba baya ko kallon Antyn sai itace ma zata dinga kokarin sako ta a hirar su irin na kissar nan,shiyasa ta shafawa kanta lafiya take iyakar kokari wajen gujewa abinda zai dagula mata sukuni.

***A falon ta, ta same su Amira na karanta musu wani story book, Adil ne akan kafar Jiddan, Maryam kuma na ta saman kujerar tana mata tsifa, wajen kwana biyu kenan Aunty tana fama da ita akan tsifa dan da gaske ta tsani abinda zai sata taba gashin ta, shiyasa tsifa ke mata wuya sosai. Su kuma tsawon gashin nata ne yake birgesu dan ranar da ta fara bude kanta Amira da Maryam tamkar zasu lashe ta, suka dinga tabawa suna dama sune da an ga gayu, ita dai murmushi kawai takeyi dan ita be wani dadata da kasa ba. Duk sati ake basu hairstyle a school shiyasa ma take yin kitson amma shima dan ba yadda zatayi ne seniors din nan ba mutunci ne dasu ba. Satin da aka soma exams kuwa ba'a basu hairstyle din ba shiyasa ta barshi har sai da Anty tayi magana.

"Tsifar kike tayata Maryam?"

Anty tace tana zama daga kujerar dake daura da kofar shigowa part din nata dan fita zata kuma yi,

"Wai bata son tabashi, shine nace ta kawo nayi mata. Nice nake da gashin Jiddah tab, Ai da an ga gayu wallahi, bama fa shi da wahalar tsifar saboda laushin sa"

"Lallai kam, kin taimaka mata. Idan kun gama Jiddah ki hada kayanki wanda zamu tafi dasu, na fadawa Baba yace kwana uku kawai zamuyi amma."

Tashi tayi tsaye da sauri cikin tsananin jin dadi tace

"Wayyo zan je naga baffanah, yaushe zamu tafi?"

"Gobe da safe in sha Allah, ki duba abinda bashi da wanki ki wanke."

Murna ta hau yi, fuskarta ta gaza boye farin cikin da take ciki, dariya suka dinga mata, Amira ta kalli Anty tace

"Anty dan Allah zan rakaku."

"Na'am?" Sai kuma tayi shiru dan tasan ba lallai uwarta ta barta ba, ba kuma dadi tace wa yarinyar a ah, shirun ta ya saka Amiran ta zata ko ba zata da ita bane

"Dan Allah Anty."

"Ba k'i nayi ba Amira, amma ki tambayi Mama idan ta barki shikenan sai mu tafi."

"Nima zan je."

Muhammad yace ashe suna jin abinda ake cewa,

"Nima."

Usman ya fada yana mikewa yazo wajen Antyn, sai Muhammad din ma ya tashi suka tsaya mata a gaba

"Shikenan toh duk zani daku."

"Yeeeh yeeeh."

Suka hau tsallen murna, murmushi kawai Anty take cike da jin dadi, a kalla zuwan Jidda ya kara mata shakuwa da yaran sosai. Duk da tasan ba lallai Maman ta bar su ba, amma ko a hakan ita taji dadi sosai ba kadan ba. Tunanin yadda Amira zata fadawa Mama takeyi gashi har ga Allah tana son zuwa taga yadda garin yake da labarin da Jiddah take basu.

"Idan na fadawa Mama zata yarda?"

Ta tambayi Maryam, dage kafada tayi alamar oho sannan tace

"Kema kinsan wace Mama, da hakura kawai kikayi."

"Ba zan hakura ba, i will try my luck."

"Allah ya bada sa'a toh." Tace tana mikewa

"Bari kiga naje na aro wayar Ya Safiyya nayi game."

"Tab! Allah sa ta baki."

"Zata bani ai tasan nima an kusa siya min tawa."

"Sai dai haka, moha taso ka rakani wajen Mama kaji, Allah yasa ta bar mu."

Rike hannun sa tayi suka nufi bangaren Baba da suka san zasu samu Maman achan, kuma tasan in dai Baba yace yes Mama ba zata hana ba sai dai zata sha rakwashi da kallon banza, duk wannan daga baya ne in dai har sun tafi.

Sallama tayi daga kofar Muhammad ya kwace hannun sa ya shige ciki ita kuma ta tsaya tana jira a bata izinin shiga.

"Uwata shigo mana."

Baba yace yana gishingid'e yana duba wayar sa, shiga tayi kanta a kasa gabanta na dukan uku uku, ta ki yarda ta hada ido da Mama kwata-kwata, ta zauna a gaban Baban sannan tace

"Em em dama."

"Dama me? Ina jinki."

"In dai kaga Amira na haka ai akwai abinda zata tambaya."

"Ina jin ki toh."

"Dama Baba, so nake na bi Anty nima."

Da sauri Mama ta ajiye abun hannun ta, ta kalli Amiran da kanta yake kasa, ranta yayi masifar baci, ta kalli fuskar Baban ta karanci yanayin sa, fuskar sa a sake yana shirin yin magana ta rigashi

"Kin manta da bikin ummul? Ko ba zaki ba?"

"Wannan satin ne bikin?"

Baba ya tambaya yana kallon Maman

"Eh wannan ne, har sun yi anko ma fa, inaga dai ta manta,ummul ba zata ji dadi ba idan baki je ba."

"Ummul ba sa'ar Maryam bace ba? Ko Safiyya ma, ba komai sun wakilci uwata, ki shirya ki bisu kinji."

"Nagode Baba, Allah ya saka da alkhairi."

Sai ta tashi da sauri ta fita, ba tare da ta hada ido da Maman ba, tana fita Muhammad ma yace zai je, shima Baban yace toh. Kasa karasa abinda Maman take tayi a dakin, ta fice da sauri dan idan ta zauna ba zata iya rike bacin ranta ba. [11/25, 3:54 PM] Rano2: SL

*7*

©®Hafsat Rano

****A tsakiyar falon ta tsaya ta shiga kwalawa Amiran kira, a tunanin ta, tana cikin wajen Antyn, bata san direct wajen Yaya ta gudu ba dan tasan haduwar su ba zatayi kyau ba, shiyasa ta salallaba ta gudu, ba kuma zata yarda su hadu ba sai gobe , dan duk bala'in Yaya sai dai ta barta amma a wajenta zata kwana ta san kuma Mama ba zata taba biyo ta wajen Yayan ba,gaisuwa safe ce kawai take hada su kuma shima kwana biyun nan da daminar ta dan ja baya zafi ya sako kai tsakar gida take fitowa tun sassafe ta basa baza tabarma. Dakin ta, ta shige ta san duk daren dadewa zata zo ta sameta ne, bata amince ba babu in da zata bi Halima dan har yanzu bata gama yarda da ita ba, duk yaron da zaka dauke shi aiki karshe ya aure maka miji ba kuma zaka taba amince masa ba har duniya ta nade, duk da idan da zaa saka mata wuka ace ta fadi aibun ta ba zata ce gashi ba, amma ita sam bata amince da ita ba, ba kuma zata fara daga yanzu ba, ta bar yarta ta bita garin da bata san me zata tarar a chan ba. Da la'asar fita ta kamata, ta shirya ta fice daga gidan ta manta shaf da batun Amiran, shagon ta ne aka kawo kaya, abinda ya fitar da ita kenan tare da Fauwaz, wanda basu suka shigo gidan ba sai dare. Kasancewar a gajiya ta dawo bata bi ta kan ta ba, ta kwanta dan da wuri zata sake fita washegari akan ragowar kayan da basu riga sun iso ba. Shirin su suke hankali kwance, murna wajen Jidda da Amira baa magana, Maryam a kasan ranta tana son bin su Amma bata shiryawa fadan Mama ba, shiyasa kawai ta hakura tana kallon su. Kitso akayi ma Jiddan me kyau duk da tsananin santsin gashin kanta amma da ya hadu da bahijja me kitso sai gashi ta kama mata shi, yayi kyau sosai dan sai da taji kunya yadda su maryam suka dinga koda ta wai kamar kan larabawa.

Cikin dare ta kasa bacci saboda zumudin tafiyar ana kiran sallah ta mike kamar wadda aka tasa, ta hau shiryawa tana sake hade kayan da zata tafi dasu. Tun dare dama tayi shara saboda haka babu datti, sai yan kayan da ba zaa rasa ba suma ta tattare kowanne ta saka shi a in da ya dace. A haka Anty ta sameta, batayi mamaki ba dan idan da sabo ta saba da wannan, sam Jiddan bata da son jiki kuma duk abinda ta san ya kamata yi kawai take ba sai an ce ba, bare kuma yau da take da zumudin ganin baffanta.

"Sannu Jiddah, Allah dai yasa kin yi bacci?"

"Nayi." Tace sai kuma ta dan russuna tace

"Ina kwana Aunty?"

"Lafiya lou Jidda, bari na dora mana ruwan wanka dan da wuri zamu fita in sha Allah, idan kin gama kije ki ga Amira ko ta tashi."

"Toh..." Tace cike da zumudi ta karasa abinda take ta nufi wajen Yayan dan Amira ta fada mata anan zata kwana saboda Mama. Ta tashi har tayi sallah ma,amma kuma yanayin ta be nuna wa Jiddah tana cikin walwala ba, kallon fuskar ta tayi, sai kuma ta zauna a gefenta tana mata kallo me dauke da alamar tambaya

"Na fasa zuwa." Tace a cikin yanayin da yake nuna kusa take da ta fashe da kuka

"Mama?" Ta tambaye ta

Daga mata kai tayi alamar eh

"Ok kiyi hakuri."

"Dan Allah mene dan na biku? Gaba daya Mama bata so taga muna harka daku bansan me yasa ba, yanzu ta turo Safiyya wai kar na soma bin ku."

"Bakin kishin ta na tsiya ai bazai barta ta hakurar wa zuciyar ta, ta karbi abinda Allah ya riga ya kaddara ba."

Yayah tayi maganar tana shigowa dakin rike da charbi a hannun ta, duk suka kalleta sai ta dora

"Nace dai duk ba akan kishi ake wannan abun ba? Idan akan shi ne yaci ace an ajiya ko? Shekarar Halima kusan takwas a gidan nan harda arzikin Usman, idan hakan be zama ishara ba sai yaushe?"

"Ba haka bane Yaya, tace wai bamu saba zuwa irin wajejen ba."

"Uwarki ce bazan hanaki kareta ai, me zai sameku a chan da ba zai same ku anan ba? Kin taba ganin an yi wa Allah wayo? Ba hujja bace bakin kishi ne kawai."

Mikewa Amiran tayi tana jin babu dadi, bata son maganganu irin haka akan Maman, musamman daga wajen Yayah, a kullum so take taga komai ya zama normal Mama ta yi hakuri ta bar komai ya wuce

"Idan kun gama shiryawa zan shigo."

Ta wuce kawai ta bar part din ranta duk babu dadi

"Yarinyar nan ba dai hankali ba dan tafi uwarta wallahi, dama uban yan girman kan chan da safiya sune suka yo uwarsu, amma sauran ba ruwan su."

"Uhum." Jidda tace itama ta mike, tafice ta bar Yaya na cigaba da mitar zancen.

A gurguje tayi ma Usman wanka tayi nata ta shirya cikin riga doguwa ta atamfa ta sallah da Baba yayi musu ita da Maryam da Amira. A shirye ta samu Aunty tana zaune tana waya a gefen gadon ta, yadda take wayar ya tabbatar mata da Baffa ne, zumudin ta ne ya karu sanda taji Antyn tana cewa sai sun zo. Bayan ta gama wayar ne ta dauko mata sarka da dankunne me kyau ta bata ta saka sannan tace ta jirata a falo. Fita tayi ita kuma ta yafa mayafin ta ta nufi sashen Baban, ta same shi ya shirya shima, da mamaki take kallon sa

"Ba dai fita zakayi?" Tace tun daga kofa, kafin ya bata amsa Mama ta turo kofar ta shigo, ya kalle ta sannan ya maida kallon sa wajen Auntyn yace

"Tare zamu, inaso zan ga Yaya."

"Yaran sun shirya?" Yace yana kallon Mama, dan dam tayi amma sai ta kame tace

"Sun kuma chanja shawara kasan abun yara."

Gid'a kansa yayi yace

"Taimaka min da hula ta akan bedside Halima."

"Toh." Tace ta wuce ciki, yana ganin ta shiga ya maida kallon sa kan Mama yace

"Minti goma sha biyar na basu su shirya, Muhammad ma yace min zaije dan haka kar abata min lokaci."

Wani kallo tayi masa, ya daga mata kai alamar haka yace, bata ce masa komai ba ta juya ta fice daga shashen. Dakin su Amiran ta wuce ta sameta a kwance a gado ta lulluba da bargo ranta babu dadi, a kanta ta tsaya fuskar ta a hade tace

"Sai ki tashi ki shirya yana jiranku, saura ki tsaya bata lokaci yace ni na hana kuma."

Da sauri ta mike zaune, tana kallon fuskar Maman cike da zumudin murna

"Ki shirya Muhammad ma, ki daukar masa sababbin kayan sa."

Daga haka ta juya ta bar dakin, da sauri Amira ta tashi ta hau ciro kayan ta a wardrobe da ta maida su, ta saka a trolley taje dakin Maman ta dauko na Muhammad ta hada, sannan ta shiga wanka ta watsa da mugun sauri sannan ta fito ta zura kayan ko shafa mai batayi ba,ta fita zata kira Muhammad Maryam tace mata ta masa wanka har ya tafi falon Baba, komawa tayi daki da sauri ta gyara fuskar ta, ta daura dankwali sannan ta dauko kayan nasu ta fito.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull