Sanadin labarina complete novel - Chapter 4
Sanadin labarina complete novel Chapter 4: Sanadin labarina complete novel Chapter 4. Babbar motar Baban ce da ake amfani da ita idan za'a je kauye ko wani…
4,196 words
Babbar motar Baban ce da ake amfani da ita idan za'a je kauye ko wani waje tare, driver ne yake tukata sai Baban a gefen sa, kujerar baya jidda da amira suka zauna Anty kuma ta zauna a ta tsakiya ita da Muhammad da Usman, maryam kamar zatayi kuka da ta rakosu dan dai kawai bata son fushin Mama ne amma da itama sai taje, ita da Safiyya kawai suka rage a gidan dan Mama ta sake fita da Ya Fauwaz da Umaima tun dazu kuma kila sai yamma likis zasu dawo. Hanya suka dauka sosai bayan an tsaya an yi siyayyar abubuwan da zasu tafi dashi. Tafiya sukayi a hankali har suka isa, hakan ya kara zumudin jidda ganin an dauku hanyar gidan, ta zura hannunta ta window tana feeling sanyayyiyar iskar dake kadawa. Parking Baba Driver yayi a kofar gidan dan ba wannan ne karon farko na zuwan sa da Baba ba. Baffa na jin tsayuwar mota ya fito da sauri suka yi kicibis a waje. Fuskar sa tamkar gonar auduga, idanun sa suka hango masa Jiddan sa, wadda ta sauya masa tayi haske ta dan yi kiba kadan, wajen Baba ya nufa kai tsaye duk da dokin ganin Jiddan, suka shiga gaisawa da tambayar bayan saduwa,cikin gidan suka dunguma suka shiga gaba daya, akayi sa'a Lami bata nan tayi tafiya zata kuma kwana biyu, gidan a share yake tas tas, sai katuwar tabarmar da Baffa ya shinfida a tsakar gidan, suka zauna dukkan su aka shiga gaishe gaishe. Duk da zumudi da son ganin baffan nata amma sai ta makale a gefe cike da kunya, takasa cewa komai. Dariya duk ta basu Baba ya tsokane ta akayi dariya kafin ta gaida Baffan ya amsa sannan Amira ma ta gaishe shi.
Wajen awa biyu Baba sukayi, suka sha fura da nono sannan suka ci dambu da Innar su Saude ta aiko musu, sannan suka shirya komawa shi da Baba driver, Kwan zabi Baffa ya basu masu yawa ya rakasu har mota Baba ya dauko kudi ya bawa Baffan ya karba da kyar yayi godiya. Ya bude masa kofar ya shiga ya sauke glass din yace
"Yaya zan shiga siyasa in sha Allah, a tayamu da addua."
"Kai Masha Allah, Alhaji ai dama irin ku ake so a siyasar kasar nan,ka chanchanta"
"Kayya, zamu dai gwada jarrabawa mu gani."
"Toh Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Amin."
Suka sake sallama suka tafi Shi kuma ya koma cikin gidan, ya samu Anty a zaune suka shiga hirar yaushe gamo, ya dinga yi mata godiya akan jidda sannan ya bata labarin zuwan da Baba yayi aka kaishi wajen likatan kashi tun daga lokacin ya samu saukin kafar dan har gona zuwa yake. Ita bata ma san anyi ba,dan be fada ba, kuma dama tasan ba fada din zai yi ba, haka yake ko yayi abu baya so a yaba masa yafi son kawai a yi shiru.
***Kwanan su biyu sosai Amira taji dadin garin, yanayin weather din yayi mata ga fura da nono abinda take matukar so kenan, gobe zasu tafi shima da kyar Baba ya kara musu kwana daya,dan be samu me zuwa dauko su bane ba ma shiyasa, kanya suke je tare da Saude suka samo suka zauna a tsakar gidan su Sauden suna sha tana basu labarin abun dariya, tashi Jidda tayi ta ce zata dauko abu a gida ta dawo. Gidan su ta shiga ta tarar da Anty zata fita hankalin ta a tashe, da sauri tace mata.
"Jidda Muhammad yana wajen ku ne?"
Da sauri ta girgiza kanta
"A ah, tare muka bar su da Usman suna zaune."
"Na shiga uku!"
Tace tana yin gaba, da sauri jidda tabi bayan ta, suka hau neman sa, abu kamar wasa sai gashi an neme sa an rasa, iya kar tashin hankali Anty ta shiga. Sauran makota ne suka fito aka bazama nema, Usman dai yace yabi su Yaya Amira da Yaya jidda da suka fita, lokacin Anty tana sallah, su kuma sun ce be biyo su ba, kuka wiwi Anty take tana jin kamr ta hadiyi zuciya ta mutu, wannan wanne irin tashin hankali ne, ina ya shiga? Me zai faru? Yaya Mama zata ji idan wani abu ya same shi bayan da kyar ta yarda suka biyo ta, zata taba fita idan wani abu ya same shi? Ba zata fita ba ko a wajen mutane balle mahaifiyar sa. Har duhun magriba ya soma babu shi babu labarin sa, dukkan su kuka suke har Jidda da Amira da ta cika da tsoron abinnda zai faru da Muhammad din.
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: *__SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (8)
****Kasancewar karamin gari ya saka suke da yakinin ba zai bata a cikin sa ba, sai dai tabbas ana kyautata zaton ba lafiya ba, daga chan gaban gidan su Jiddan akwai wata babbar rijiya, da duk mazauna wajen suke amfani da ita. Kamar an tsikari Aunty haka ta mike da sauri duk suma suke mike
"A duba rijiyar nan, Allah ubangiji yasa ba fadawa yayi ba."
Ta fashe da kuka, jikinta na rawa sosai tamkar mazari, Baffa ne da Baffan su Saude da wasu maza biyu suka nufi rijiyar dan duk ciki babu wanda ya yi tunanin dubawar.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Kalmar da aunty ta iya ji kenan daga bakin Baffa sanda ya leka kansa cikin rijiyar, saboda tsabar kaduwa ta yanke jiki ta fadi cikin wani irin yanayi. Nan da nan wajen ya cika makil da mutane aka samo masu shiga rijiya mutum hudu biyu suka shiga suka dauko shi, cikin yanayin firgici.
***Wani irin kuka aunty take, duk rashin imanin ka sai ka tausaya mata, Jidda da Amira ma sun ci kuka sun gode Allah, suna nannade a zaune gefen Aunty Usman na jikin Amira yana kuka shima duk da kukan be san na menene ba, waya Baffa ya dauka ya kira Baba, ya koma gefe ya sanar dashi abinda yake faruwa cikin yanayin dauriya dan sai da yayi da gaske sannan ya iya kiran Baban shima saboda kiran ya zama dole ne.
"Kullu nafsin za'ikatul maut Yaya, ko da Muhammad a gaban mu yake ni da mahaifiyar sa dole sai ya mutu, bani da jahilci dan ni musulmi ne kuma na yarda da kaddara, Allah ya sa me ceton mu ne, kayi mishi dukkan abinda ya kamata a kaishi gidan gaskiya."
Jiki a sanyaye Baffa ya dawo ciki, akayi duk abinda za'a yi, a daren aka kaishi.
****Sanda Baffa ya kira Baba yana daf da shiga gida, sosai mutuwar ta dake shi duka me zafin gaske, kansa a kasa kirjinsa na masa wani iri, juriya da jarumta irin ta namiji a haka suka karasa gidan, yana tunanin yadda zai sanar da Mama. Dakin ta ya wuce kai tsaye wanda ya dade rabon shi da shiga har cikin dakin nata, tana zaune tana lissafi gabanta tray ne na abinci tana so ta kammala taci duk da tana jin kamar an dauke appetite din bakin ta ne, wani irin yanayi take jin zuciya da gangar jikin ta tamkar zatayi zazzabi, daurewa kawai take tana karfafa jikinta dan bata so ta bar aikin da take bata kammala ba. Sauri take taga ta gama dukka dan tana son kiran Tariq taji ko lafiya yake? Dan sai take jin kamar ba lafiya ba, ajiye takarda da biron hannun ta, tayi ta jawo wayarta dake saman gado ta hau dialing number sa.
Yana zaune a gajiya yake tikis bayan ya dawo daga motsa jikin sa, so yake ya watsa ruwa kafin ya duba wasu papers da zai, amma kuma ya gaza tashi yana kishingid'e kansa na dan sara masa wanda ya san stress ne na karatu da baya ko hutawa dan a sati weekends ne kawai yake samu ya huta kamar na awa hudu amma sauran ranakun sam bashi da hutu. Wayar sa dake yashe a saman dan madaidacin table dake cike da manyan text books dinsa ce tayi kara, duk da baya expecting Kira daga kowa amma sai ya mike yana dora idon sa akan table din har ya karasa ya dauki wayar ganin sunan Mama ya sakashi dagawa ya zaune a kujerar dake gaban table din yace
"Hello..."
"Hello Assalamu alaikum."
"Wa alaikisalam." Ya amsa yana dan motsa kafarsa kafin ya gaishe ta, ta amsa sannan ta dora
"Lafiya kake ko?"
"Me faru mah? Lafiya ta kalou."
"Naji muryar ka haka-haka, hope dai babu wata matsala."
"No, stress ne kawai, da na dan samu na watsa ruwa zan warware ."
"Ok!" Tace a gajarce, shigowar Baba dakin ya sakata rike maganar da zatayi, ta zuba masa ido tana karantar yanayin da ya shigo mata, zama yayi a gefen ta, sai taga kamar idanun sa sun kada
"Rike wayar Tariq."
Tace tana zare ta daga kunnenta, tashi yayi shima bayan ya cire wayar daga kunnen sa ya nufi wajen kayan sa, ya shiga cire kayan jikinsa.
"Me ya faru?" Tace tana kallon sa
"Aisha!" Sai gabanta ya ce ras jin ya ambace ta da sunan ta kai tsaye, kamar wadda aka zare wa laka haka taji, ta saddakar babu lafiya amma kuma ta gaza hasaso komai akai
"Kinsan cewa rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko? Haka kinsan cewa bawa baya taba wuce kaddarar sa, kiyi hakuri, kiyi hakuri duk me rai mamaci ne."
"Dan Allah me ya faru?" Tace hannun ta na rawa
"Muhammad ne..."
Sai ta mike da sauri,
"Me ya same shi?"
"Zauna dan Allah." Yace yana riko hannun ta, kasa zama tayi ta hau girgiza masa kai
"Me ya same shi? Me ya sami d'ana."
"Ya fada a rijiya, Allah yayi masa rasuwa."
Kara ta kwalla da karfi,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shikenan an kashe min d'a."
Sai ta fashe da kuka me karfi, kukan da ya kai attention din Tariq kan wayar dake hannun sa yana kokarin zuba tea a cup,a kunne ya saka wayar da sauri yana sauraren abinda Maman take cewa
"Sai da na nuna bana so yaran nan su je, ka dage dole sai sun je, shikenan ta kashe min shi,an raba ni da d'ana, Wayyo Aallah na."
Riko ta Baba yayi, ta kwace tana matsawa baya, kamar zata zauce haka take ji, da sauri Tariq ya katse kiran sannan ya sake kira at the same time, Baba ne ya dauki wayar, ya daga
"Muhammad ne Allah yayi mishi rasuwa yanzu."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, rashin lafiya yayi?"
" A'ah, tsautsayi ne ya gamu dashi,ka kwantar da hankalin ka zan kira ka."
Sai ya kashe wayar, yayi saurin fita ya bi bayan Mama da ta fice da gudu tana kwala ma yaran kira. Da sauri Safiyya, Maryam da Umaima suka fito a kusan tare, Yaya dake part dinta itama ta fito a gigice, Safiyya ce ta rungume Maman da take kuka tana kiran ta kashe mata shi, kamar wadda zata zauce haka ta koma, duk suma suka saka kuka ganin Maman na kuka sosai, daka musu tsawa Baba yayi ganin sam sun maki sauraren sa, yana kokarin yayi magana amma suna kuka Maryam hadda kururuwa, shiru sukayi duk suka koma kuka kasa-kasa, yace su wuce zuwa falo, sannan ya juya, suka bi bayan sa banda Mama da ta tsaya a wajen, sai da Safiyya ta rike ta sannan suka koma ciki, duk suka zauna suna fuskar su a cikin kafafunsu suna kuka kasa kasa , Yaya ce kawai a zaune a kujera, Mama na daga kofa taki zama, Baban ma a tsaye yake ba zaka iya tantance yanayin halin da yake ciki ba, Muhammad yaro ne me matukar shiga rai, shiyasa ya shiga ransu sosai duk da karancin shekarun sa,
"Dukkan mu zamu mutu babu Wanda zai zauna a duniyar nan sai dai in har lokacin mu be yi ba, amma idan yayi dole ne mu tafi, babu kuma wanda ya isa ya hana, kowanne bawa da yadda Allah ya kaddaro masa SANADIN mutuwar sa, Muhammad lokacin sa ne yayi,ko yana gaban mu ne bamu isa mu hana ba wallahi, kukan ku ba zai dawo dashi ba kuma ba zai chanja komai ba sai ma sabawa Allah da kuke kokarin yi ta hanyar kin yarda da kaddara."
"Allah ya gafarta masa yasa me ceto ne."
Yaya tace a sanyaye ita kanta mutuwar ta kad'a ta, dan hawaye take yi duk da bata bude murya ba,
"Kiyi hakuri Aisha, kiyi masa addu'a kawai, idan Allah ya kaimu da asubah zamu tafi in sha Allah."
Daga haka ya juya da sauri ya bar falon,zaman dirshen Mama tayi a wajen ta cigaba da kuka me cin rai, zuciyar ta taki amince mata ba an shirya cutar mata da yara bane dama tun farko shiyasa bata amince da tafiyar ba, waya Safiyya ta dauka ta kira gidan su Maaman, cikin kankanin lokaci sai gasu sisters da brothers din Mama har da Hajiya Babba, babu wadda ta yarda a cikin su cewa lokacin Muhammad ne yayi, dukkan su sun tafi akan shiri ne, wasu ma gani suke Aunty ce ta jefa shi a rijiyar dan sun yarda babu abinda kishiya ba zata iya aikatawa akan yayan kishiyar ta ba. A gidan duk suka kwana Hajiya Babba kawai aka mayar gida zaa dawo da ita gobe, kusan duk basu rintsa ba.
Bangaren Aunty kuwa sosai jikinta ya rikice da mugun zazzabi, tun bayan da aka kaishi aka dawo ta tabbatar da gaske ya rasu ba mafarki take ba, bata san wanne kalar tunani mutane zasuyi akan ta ba amma ta tabbatar ba zata taba fita ba, me zata cewa Mama ta yarda da ita ne wai? Me kuma zata ce wa Baba da saurin yaran su yarda babu sakacin ta?
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Ta furta da karfi sai kuma ta fashe da kuka, rike ta Innar su Saude tayi tana bata Baki
"Kiyi hakuri, haka Allah ya kaddara babu makawa sai ya faru."
"Me zan ce wa duniya? Me zan fadawa mutane su yarda bani da hannu a ciki? Su yarda ba sakaci na bane? Me yasa wai ma ba Usman bane ya mutun?"
Da sauri ta rufe mata baki tana bata fuskar ta sosai
"Karki yi sabo wallahi."
"Astagfirullah."
Ta hau fada da sauri da sauri, jidda da Amira dake kusa dasu suka kara tsananta kukan su, har wani jaja-jaj fuskar jidda tayi saboda kuka, fuskar su ta daga sosai, su ya bi, Usman yace su dawo shi sai ya tsaya yace zai jira su,ya akayi har ya je wajen rijiyar ya fada babu wanda ya lura shine abinda yafi damun Baffa.
Gidan baki daya babu wanda ya rintsa saboda zulumi da tashin hankali, da asuba, Baba, Safwan da abokin Safwan Jamil, neighbors suke sai abokan Baba su biyu Alhaji Adamu da Malam Nura sai driver Baban suka dauki hanya, suka isa wajen 7 lokacin su Baffa sun fita har an shinfida tabarmi suna zazzaune cike da zulumin tashin hankalin da ya same su, tunda Baffa ya hango motar su Baban gabansa ya fadi, haka ya daure ya taro su, suka hadu suka zazzauna, gefen Baban Baffa ya zauna jikin sa a sanyaye, lura da yanayin Baban ya sakashi yin shiru dan da so yake yayi masa bayani amma sam Baban ya nuna babu bukatar hakan. Sun dan jima a zaune har rana ta fito sosai, sannan suke ce zasu tafi. Baffa ne ya nemi Baban ya shigo ciki su yi magana da aunty dan sosai take cikin wani hali, tashi yayi yabi bayan Baffan zuwa cikin gidan, suna zazzaune a tsakar gida da sauri Amira ta tashi tayi wajen Baban tana fashewa da kuka, rike hannun ta yayi be ce komai ba, ya isa gefen tabarmar da aka shinfida masa ya zauna sannan ya amsa gaisuwar matan dake wajen tare da Aunty duk suka tashi suka shiga ciki ya rage daga shi sai Aunty, kukan ta ne ya tsananta har ta gaza furta kalma daya ,yana jin ta be ce komai ba, har sai da ta dauki lokaci dan kanta ta rage ta shiga jan hanci.
"Kin gama?" Yace yana kallon ta, girgiza masa kai tayi da sauri
"Toh ya ishe ni haka, kin isa ki hana abinda ya faru ya faru ne? Ko kuma zaki iya chanja abinda Allah ya riga ya kaddara?"
Girgiza kanta tayi da sauri, ya gid'a kansa sannan yace
"Bana son shiririta, abinda ya riga ya faru ya faru, Allah ya jikan sa yasa ya huta, kar ku bata mana lokaci tare nake da mutane, ku fito mu wuce."
Yana fadan haka ya mike, ya fice daga gidan, jikinta a sanyaye ta tashi itama, taje suka dauko kayan su, suka fito Jiddah dauke da Usman ,Amira ta rike musu kayan, Iya Lami da tayi dawowar safe na tsaye daga gefen bayan gida ta zuba musu ido,tana hasashen yadda zaa kwashe da uwar d'an idan an koma, zata so ace da ita zaa yi tafiyar dan kawai taga yadda Halima zata wulakanta dan ta tabbatar ba za'a kwashe kalou ba dan ma mijin nasu babban mutum ne me dattako. Sallama sukayi mata,ita da Innar su Saude da sauran matan, ta amsa kamar ta damu da abinda ya faru, ta rakasu har zaure tana bawa Auntyn baki, babu wanda ya kulata suka fice dan kowa ya riga ya san karya take kawai dai dan kar ace bata yi bane. Motar da Fauwaz da Jamil da Driver suka shigo ita su Auntyn suka shiga sai Jamil ya koma wajen su Baba ya zauna a gaba. Baffa na tsaye da sauran mutanen unguwar, sai matan dake mammakale a katanga, daga musu hannu su Baffa sukayi sanda aka tada motar, idanun sa akan Jiddah da itama shi take kallo, har suka bar unguwar tasu. Ajiyar zuciya Baffa ya sauke yana fatan komai yazo wa Haliman da sauki dan ya hangi tashin hankali shinfide acikin kwayar idanun ta, ya kuma san abinda take gudu da tsoro wanda har ya haifar mata da zazzafan zazzabi wanda baya raba daya biyu daga jiya zuwa yau Jinin ta yayi mugun hawa.
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (9)
***Dukkannin su suna zaune a falon, Mama na daga side din part dinta a kasa sai wata kanwar ta Anty Mimi da take ta fama da ita akan tasha ko tea ne, dan tun jiyan bata saka komai a cikin ta ba. Motar su ce tayi parking a kofar gidan da ke dauke da yan tsiraren yan uwan Baba a zaune a kasan rumfa, wajen su, su Baba suka nufa Safwan kuma da su Aunty suka shiga cikin gidan. Dukan uku uku kirjin Anty yake har suka dangana da kofar da zata sadaka da falon nasu, takalman mutanen da ta gani ne ya sakata sauya akalar ta zuwa shashen Yaya, duk nan din ma bata da yakinin abinda zata tarar, kanta a kasa hannun ta kunshe a cikin Hijab dinta ta shiga da sallamar ta wadda sai kayi da gaske zaka ji muryar ta da take a dashe sosai. Da ido Yaya ta bita bayan ta amsa sallamar har ta durkusa a gabanta, kanta a kasa tana kokarin tattaro ragowar kalaman da suka rage akan harshen ta
" Karki ce komai, idan har kikayi magana akan abun da ya faru toh lallai baki san kaddara ba, ba kuma zaki ci jarrabawar ki ba, Allah ya kan jarrabi bawa ta hanyar da be yi tunani ko zato ba dan ya gwada imanin sa, ki daure ki ci wannan jarrabawar."
"Nagode Yaya, nagode nagode da kika fahimce ni."
"Jahili ne kadai mara tauhidi zai zarge ki, ki tsarkake zuciyar ki, karki kula kowa da maganganun mutane ki tsaya akan gaskiyarki."
Shiru tayi tana jin nutsuwa na saukar mata, a kalla mutane biyu masu kusanci da Muhammad bayan mahaifiyar sa sun fuskance ta, sun kuma gamsu cewa ba zata cutar dashi ba. Sai da ta tabbatar da samun nutsuwar ta wajen kashi hamsin sannan ta bar shashen Yayan ta nufi nasu. Ta shiga duk suka bita da kallo, kallo me dauke da tarin manufofi, gaban Maman ta karasa, ta durkusa cikin yanayin da yake nuna tsantsar yanayin da take ciki, zatayi magana ta daga mata hannu dan dama tunda ta shigo bata kalle ta ba,
"Bana son jin komai,cuta dai kin riga kin cutar dani, ba zan kuma taba yafe miki ba idan har cutar da Muhammad kikayi da gayya, ki fita daga harkar yayana da komai naki, bana son ko bude ido na ganki."
"Allah baya barin wani dan wani yaji dadi Maman Fauwaz, kuma Allah shine shaida ta, da shi da Usman duk daya suke a wajena, ba zan taba yin abinda zai cutar dashi ba, Allah ne shaida ta, wallahi wallahi ban san ya fita ba, ina sallah a lokacin, ban kuma san baya tare da su Amira ba."
"Babu abinda zaki ce fa malama, dan Allah ki tashi ki bamu waje, zaman ki anan ma matsala ce babba."
Anty Nafi tace tana jan dogon tsaki
"Maman Usman kije part dinki, ba komai.". Anty Mimi tace a kasan ranta tana jin babu dadi, tana kuma tausayin Haliman dan tasan ba zata taba aikata abinda yan uwanta suke zargin ta dashi, rabon ayi hakan ne ya saka har yace zai bisu, ajali ne yake kiran sa Allah ya kaddaro a chan kasar sa take. Jiki a sanyaye ta mike, ta wuce su tana jin wasu na maganganu kasa kasa, ta wuce part dinta ta shiga ta samu Jidda da Usman a zaune sunyi jigum tamkar wadanda sukayi jinyar satittika, kar ma Jidda da ramar ta sake fitowa sosai ta dashe tamkar wadda bata da jini. Karfafa kanta tayi ganin halin da yaran suke ciki, ta shiga da karfin ta tana kokarin aro jarumta ta dora a saman fuskarta wadda ta boye ainihin abinda take ciki. Zama tayi itama a gefen Jiddan, wadda take jin su kadai suka ragewa juna a duniya, sun dan jima a haka kafin Auntyn ta mike ta nufi dakin ta, sai a lokacin wayarta da take cikin jaka ta sake daukar kara a karo na kusan hudu kenan, tun bata shigo ba aka kira Jiddan na tsoron ta fita ta kai mata taga ana ma Auntyn wani abu sai ta hakura kawai, ganin an sake kira yanzu ya sakata ciro wayar ta tashi zata kaiwa Auntyn daga cikin dakin Auntyn tace
"Daga Jiddah kice bana kusa."
Tsayawa tayi ta daga wayar, ta kara a kunnenta, muryarsa ta shiga chan cikin kunnenta, wani irin dum taji saboda yadda karfi da amon muryar sa ta doki kunnenta, sake maimaita Hello Aunty yayi jin ba'a yi magana ba, zare wayar tayi da sauri daga kunnen ta, sannan ta sake mayarwa a hankali cikin siririyar muryarta tace
"Bata kusa."
Shiru ne ya biyo bayan har ta zata ko an katse kiran ne, dubawa tayi taga yana kan layi sai ta sake maimaita wa
"Bata kusa Auntyn."
Samun kansa yayi da kwaikwayon muryar ta a chan kasan makoshin sa da ta tuna masa da sirantar ta,
"Ina Auntyn?" Ya tambaya
"Ta shiga ciki, idan ta fito zan fada ?mata."
"Ok, an kaiki asibiti?" Ya tambaya yana son ji
"Asibiti?" Tace sai kuma ta hau girgiza kai
"A ah, ai ni lafiya ta kalou."
"Ok!"