Sanadin labarina complete novel - Chapter 5
Sanadin labarina complete novel Chapter 5: Sanadin labarina complete novel Chapter 5. Yace a gajarce sannan ya katse kiran. Dama kira yayi su yi magana da…
4,435 words
Yace a gajarce sannan ya katse kiran. Dama kira yayi su yi magana da Auntyn akan abinda ya faru, yayi magana da Mama dazu, ya kuma san itama tana cikin zulumi dan kai tsaye Maman ta nuna masa Auntyn ce ma ta kashe Muhammad din, shine ya hanata yin komai, ya kuma roke ta akan kar ta tashi hankalin ta, ta kuma tashi na kowa ya nuna mata haka Allah ya tsara dama chan, dan dole ta hakura ta kuma yiwa su Aunty Nafi magana suka hakura dan da sun shirya ciwa Auntyn mutunci sosai. Tunanin sa ne ya tsaya akan yar ficikar yarinyar, wadda be taba gani ko jin mutum me ramar ta ba, shi mamaki yake da yaji har tana magana radau haka kamar ba ita ba, a fili idan batayi magana ba zaka rantse ko kwakkwaran motsi idan tayi zata iya faduwa. Shafa sumar kansa yayi da ta soma taruwa dan ya kwana biyu be rage ta ba, ya shaki iska ya fezar yana tattare dukkan tunanin sa a waje daya, sannan ya mike daga gaban reading table dinsa ya tashi zuwa wajen system dinsa ya dauko ta ya jona a jikin socket ya kunna sannan ya shiga duba wasu publication yana kokarin dauke hankalin sa da abinda ya faru, duk da a chan kasan zuciyar sa yana tare da tausayin yaron, wanda ba zai dorar da wani abu ba game da rayuwar sa, duk rashin sakewar sa da mutane yana da matukar son yara, shiyasa yayi sabo da shi da Usman idan yana nan suna yawan zuwa dakin sa su manne masa, basu da rashin ji da hayaniya irin ta yara dai dan abinda ba zaa rasa shiyasa suke dadewa a wajen sa basu gundire shi ba, da zarar yaji zasu fara damun sa sai ya kunna musu kallo ya shige daki ya barsu wani lokacin har sai sun yi bacci sannan ya saka Safwan ko Safiyya su dauke su. Tattare aikin yayi ya ajiye dan baya jin zai iya, ya zaro socks me kauri sosai saboda sanyin da ake zugawa ya saka a kafarsa ya rufe ta da katoton takalmi ya dora rigar sanyi me kauri sosai ya fice daga gidan.
**** Kasancewar karamin yaro ne ba a zauna wani zaman makoki ba Baba yace babu bukatar hakan, idan kaga Mama zaka dauka jinya tayi saboda yadda ta zabge lokaci daya haka ma Aunty, dukkan su basu da lafiya dan sai da Baba ya kira Dr Bashir yazo har gida ya duba su ya basu magani. Sati kusan biyu da faruwa abun amma babu wani sauyi a yanayin gidan, idan ka shigo gidan zaka rantse babu mutane dan ko su Amira da suke ziryar shiga part din Auntyn yanzu basa yi saboda maman, sai dai su hadu idan zasu tafi islamiyya amma ko zaman falon wajen duk sun daina, tafiya ta kama Baba satin sa guda kenan bayanan shiyasa ko zaman cin abincin ma sun daina dama shi yake assasawa shima kwana biyu kafin ya tafi ya rabu dasu dan baya son tashin hankali kuma zaman su waje daya sai iya haddasa abinda yake ta gudu.
*** Tsaki Yaya taja a karo na ba adadi, lalle take kwabawa zatayi kunshi, duk gidan ya isheta so take ta yi tafiya amma tasan Baba ba zai barta ba, gashi yan hirar tata sun daina zuwa dama Jiddah ce take kawo su amma yanzu gidan kamar an yi ruwa an dauke shiru kake ji, bakin ta kaikayi yake mata kusan kwana uku kenan tana neman wanda zasu yi hira dashi amma ta rasa, Abu da take shigowa tayi mata wasu ayyukan kwana biyu taje ganin gida sai ya zama sai ita kadai. Kunshe kafarta tayi bayan ta shafa lallen a dukka kafar abinda ake kira da dungulmi ko tsohuwa ta fada kwata, ta saka leda da tsumma irin yadda tsofaffi suke, sai ga Safwan ya shigo. Sakin baki tayi tana kallon sa kafin tace
"Kai nifa na zata baka duniyar nan."
"Kai Yaya, ina zanje? Ina nan."
"Amma ko gaisuwa? Saboda ba uwar ku bace ace babu me leko ni."
"Kiyi hakuri sarauniya, kinsan yanayin da ake ciki, shiyasa amma ki basu yan kwanaki zasu ware, ni bana zama ne kwata-kwata ga kula da shop din Mama ga zuwa school?"
"Menene shup?"
"Shop ba shup ba Hajjaju."
"Ko ma uwar menene dai."
"Shago ake nufi, shine shop da turanci."
"Yanzu shagon ne kuka maida shi shap saboda tsabar iyayi da kinibibi ni Hajara?"
"Haka yake ai, yawanci fa kalmomin turanci ne bahaushe ya sata."
"Ummm, karyar banza."
"Allah Yaya, yawanci kalmomin na turanci ne."
"Kaga idan kana da kati a wayar ka, kira min yayanka inaso nayi magana dashi."
"Wai Ya Tariq?"
"Shi, kira min shi."
"Missing dinsa kike Hala?"
"Musi?" Tace tana bata fuska
Dariya ya kwashe da yace
"Eh mana..."
"Kai ka sani, idan ma zagi na kayi ruwanka,kira shi tambayar sa zan ko yana shan maganin sa, dan jiya nayi mafarkin sa wallahi."
"Magani? Wait wai bashi da lafiya ne?"
"Baka sani ba? Ai ba kalou kansa yake ba, shiyasa nayi yadda nayi na tabbatar ya karbi rubutu ya soma sha, kar abun yayi tsamari azo a aura masa yarinyar mutane ya bada wahala kamar yadda kakanku ya wahalar da rayuwa ta, kai gayen nan yaci ubana daidai gwargwado,me zaa yi da miskilin mutum ne wai?"
Dariya sosai ta bawa Safwan, ya shiga kyakyatawa har da kusan zamowa daga kujera, tsaye tayi hannun ta nannade da leda da tsumma tana kallon shi, bata cika son dariya ba nan da nan tayi kicin kicin da fuska, da kyar ya samu dariyar ta tsaya, ya rike bakin sa ganin ta bata fuska,
"Ya hakuri Hajiyata, afwan wallahi kece kika bani dariya, wato kema kinsan gaye?"
"Ban sani ba, tashi kayi gaba, idan ba zaka kira min shi ba, bari ubanku yazo ai shi na isa dashi sai yakira min Shi."
"Maida wukar your excellency, ni ban isa ba wallahi, bari na kirashi amma ba lallai ya daga ba, kinsan da banbancin lokaci tsakanin mu."
Shiru tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, ciro wayar sa yayi, ya shiga WhatsApp yayi dialing video call dan hakan ne kadai zai wanke shi a wajen Yayan. Jidda ce ta shigo sashen daure da food flask me dauke da alala da Auntyn tayi wa Yaya, da sauri Safwan ya mike ya karbi flask din yana mata murmushi [11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (10)
***
"Karka kuskura ka bude min kwano."
Tayi saurin cewa ganin har ya zauna rike da flask din
"Hajiya Yaya rowa dai babu kyau, gani zan me muka samu kinsan fa ni da ke akwai amana."
"Yanzu na gama saka abu kaki yi, wacce amana kuma."
Ta harare shi tana tabe baki, da sauri ya dauki wayar da ya manta yayi kira, yaga har Tariq din ya d'aga har ya katse kiran ma
"Kinga har ya d'aga fa, na manta na kira."
"Ina zaka tuna kaga kwano."
Dariya Jidda tayi, ta gaida Yayan ta zauna tana kallon d'aurin da tayi a kafarta
"Yaya kunshi kikayi?"
"Eh yar albarka, kinsan mu bama iya barin kafarmu kod'ai kod'ai ba lalle, kiga kafa fara kal babu kyawun gani, wannan sai yaran zamanin nan, mu ina."
"Yaya gashi ya daga, video call ne ma."
Matsowa tayi da sauri, ta zauna a kubin sa sannan tace
"Hasko min shi, kaga ba hannu."
Matso da fuskar ta tayi, Tariq dake tsaye rike da water bottle jikin sa sanye da riga armless, hannun sa da yake a murde Yaya ta kalla, sai kuma ta kalli fuskar sa da take kamar kowanne lokaci tace
"Menene haka kake zaune babu kaya?"
"Babu kaya?" Yace a kasa sosai, amma duk da haka sai da taji, sai kuma ya kalli kanshi
"Eh wannan ai sakarci ne."
"Bamu gaisa ba fa Yayah, ina wuni?" Yace yana kin biye mata
"Lafiya lou, kana lafiya?"
"Eh, kefa?"
"Oho ban sani ba."
Kallon ta yayi, ta harare shi yayi saurin dauke idon sa, yana barin wajen da yake, yana jin ta tana magana da Fauwaz k'asa -kasa, yayi kamar be ji ba ya cigaba da zare igiyar takalmin dake kafarsa,
"Kana ji ko? Kana shan maganin naka kuwa?"
"Magani?" Sai ya tuna da sauri yace
"Eh ina sha."
Washe baki tayi,
"Ka kyauta." Sai kuma ta rage murya ta kalli Jiddah dake zaune a dayan gefen nata tace
"Maganin ya fara masa aiki.".
Ya jita sarai sai yayi kamar be ji ba yace
"Yayah zan fita school, zan kiraki idan na dawo."
Yace bayan ya gama zare takalmin
"Toh babu damuwa, ka dai cigaba da shan maganin kaji? Karka yi wasa dan aljanu mugaye ne wallahi, duk abinda kake yi nasan ba yin kanka bane aljanun gado ne."
"Bye."
Yace ya katse kiran,sai kuma yayi murmushi kadan, matar baki dayan ta drama queen ce, zatayi kyau da acting.
Sai ya sake murmushi ya girgiza kansa yana ajiye wayar
Haushi ne ya tirnike Yaya ganin bata gama bayani ba ya katse kiran, har Jiddah taso a bawa su gaisa gashi tana son ta masa wata magana amma dan wulakanci shine yace mata wani bye ya kashe
"Uwar bye din, mtsw!" Tace tana mikewa
"Kar ya makara school ne fa Yaya, Amma zai kira nasan yana dawowa, baki ga alamun ya chanja ba? Ai maganin yana aiki sosai."
"Allah?"
"Da gaske baki gani ba?"
"Umm na gani fa."
"Ehen, da kansa ma zai fara kiranki ne da maganin ya gama bin jikinsa."
"Eh gaskiya kuma haka ne, toh shikenan yanzu ka tashi ka je, tunda yar fillon nan tazo sai muyi zaman mu.*
"Abincin fa Yaya? Yunwa nake ji." Ya kai hannun sa akan flask din da sauri tace
"Karka kuskura ka taba min funfulaye (foodflask) kaji na fada maka."
Zare hannun sa yayi ya mike, ya daga hannun sama yace
"Ban taba ba, bari naje na samo balangu me zafi da lemon exotic naci kayana nima."
"Tsaya, balangu zaka siyo?"
Tace tana washe baki
"Eh ba, amma ko guntu ba zaki ci ba."
"Haba kai kuwa, wasa fa nake maka, dauki kaci ka rage min, sai kaje ka siyo mana naman amma nawa kar su saka yaji ulcer, lemon ma bana son me gas kaji?"
"An gama."
Ya dawo ya dauki plate ya zuba rabin alalar ya zauna ya cinye tas, ya sha ruwa yayi gyatsa, sannan ya mike yana zura hannu a aljihu
"Tunda dai ciki ya dauka, bari naje na dan yi siesta."
"Wajen me naman ne sita?"
"Eh eh, nan ne kuwa, bari naje." Yace yana kunshe dariyar sa
"A dawo lafiya."
Tace dadi na kamata, ba zata ci alalan ba har sai ya kawo balangun ta ayyana a ranta. Ido daya ya kashe wa jidda sannan ya fice yana dariyar mugunta.
Shiru shiru babu shi babu alamar sa, tun da zata cire kunshin take cewa safwanu shiru, har ta gama Jidda ta zuba mata ruwa ta wanke shiru be dawo ba.
"Jeki dubo min shi jidda, kar dai yaron nan wayo yayi min."
"Toh." Tace tana mikewa, ta fito tana tunanin ina zata dubo shi, part din Aunty taje ta kira Usman tace ya dubo mata Ya Safwan a bangaren su, yaje ya dawo yace mata bacci yake, komawa tayi ta fada ma Yaya aikuwa ta dinga balbalin masifa da kyar ta hakura tayi shiru amma ta shirya rama abinda yayi mata.
****Washegari Baba ya dawo, kai tsaye part din Yaya ya wuce ya tadda ita tana zubawa kadangaru ruwa da abinci me manja, kasancewar part din nata ginin kurzu kurzu ne ya saka wajen ya zama matattarar gadangaru shikenan take zuba musu ruwa da abinci kullum. Shigowar Baban ya sakata dakatawa.
"Sannu da aiki Yaya?"
"Yawwa, dawowar Kenan?" Tace tana ajiye kwanon hannun ta,
"Eh wallahi, saukar kenan Yayah, mun sameku lafiya?"
"Lafiya lou ba lou ba."
"Me ya faru Yaya?"
"Bari na kawo maka ruwa kasha."
Tace tana nufar randar ta da ta saka aka kawo mata tun daga chan wai tafi ruwan firij sanyi, kawo masa tayi ya sha yayi hamdalah sannan yace
"Me ya faru Yaya?"
"Uhum. Menene ma be faru ba? Gida ya zama kamar kango babu me yi da wani, fisabillillah, abinda ya riga ya faru ai ya riga ya faru ko?"
"Haka ne."
"Ni gaskiya bana son shirun nan, ita Halima tana jin cewa bata kyauta ba ita kuma Aishatu tana jin ba'a kyauta mata ba."
"Duk nayi magana dasu wallahi Yaya, na kuma nusar da kowaccen su akan hakuri da daukar kaddara, amma ba komai zan yi maganin abun."
"Yawwa, gwara duk su yi hakuri sannan su kyale yara su cigaba da rayuwar su kamar dah, shirun ya ishen baki na har doyi yake saboda zaman kadaita, na gaji."
"Zaa gyara in sha Allah."
"Yawwa Allah yayi albarka, shi kuma me babban suna Allah yasa me cetonmu ne."
"Amin Yayah."
"Bari na shiga ciki Yaya,babu wata matsala dai ko?"
"Babu sai guda daya take, yaron nan ni yayi wa wayo yace zai siya min balangu, na saka rai yazo ya hanani, wallahi har mafarkin balangun nan nayi."
"Kai Kai kai, be kyauta ba, yanzu yanzu zaa kawo miki balangu da tsire da kuma me?"
"Leman bawo da yar ayaba."
"Shikenan an gama."
"Allah yayi albarka, yasa kaima yarannan su rama maka."
"Amin ya Allah."
***Maimakon ya wuce part dinsa sai ya nufi bangaren su Fauwaz din ya kwankwasa masa kofa ya kira sunan sa, tashi yayi da sauri jin kiran Baba ya bude.
"Mutanen garin ku, shine ka sakawa uwata rai kasan ba bata abu zakayi ba ko?"
Dariya yayi shima Baban ya saka dariya
"Maza kaje ka samo mata balangu da tsire, ka hado mata da lemo da ayaba masu kyau, kayi sauri kuma."
Ya mika masa kudi, hannu yasa ya karba sannan yace
"Ok tohm."
Juyawa Baban yayi shi kuma ya koma daki ya chanja kayan jikinsa ya fito, ya dauki motar ya tafi siyo mata abinda Baban yace, tun ranar be je part dinta ba dan yasan haduwar su ba zatayi kyau ba.
Part din Mama ya wuce kai tsaye, dan ba wanda ya san ya dawo, yaran duk suna falon a zaune maimakon yadda suke zama a main falon gidan tun bayan abinda ya faru Mama ta hana suna kunshe a part dinta, shigowar Baban ya sakasu duk mikewa Safiyya dake waya da saurayinta Mahfouz tayi saurin katse kiran. Bin su Baba yayi da kallo dukka yana nazarin maganar Yaya
"Sannu da zuwa Baba."
Suka hada baki dukka suka fada a tare, be amsa ba sai ya gid'a kansa kawai yana wucewa bedroom din Maman. Jikin su ne ya basu sai suka tashi suka shige bedroom dinsu.
Umaima ce tare da Maman tana tayata jera wasu sabbin kaya da tayi a wardrobe sallamar Baban ta iske su,ajiye rigar dake hannun ta tayi, ta russuna ta gaida Baban sannan tayi saurin ficewa daga dakin.
"Sannu da zuwa." Mama tace tana ajiye kayan hannun ta, ta nufo wajen Baban
"Yawwa Maman Yara." Yace cikin shigar tsokana
"Banji dawowar ka ba Sam."
"Ai ban dade ba, na fara zuwa wajen Yaya ne, kuma dai Malam Basiru be shigo da motar ba akwai sakon da zai karbo min shiyasa."
"Sannu da hanya."
"Yawwa, a bani wajen zama Maman Yara."
Da sauri ta jawo babban carpet din da take sallah akai me taushi ta shinfid'a masa a gaban gadon, ya zauna itama sai ta nemi gefen sa ta zauna.
"Yawwa ko kefa, a bar matafiyi a tsaye?"
"Ban dauka zaka zauna ba wallahi, bari na dauko ruwa da abinci."
"Barshi tukunna, babu yunwa dan tun rana muka dawo na tsaya ne dai a government House, kuma Yaya ta bani ruwan randar ta me sanyi nasha."
"Masha Allah, fatan an samu abinda aka je nema."
"Alhamdulillah, gaskiya."
"Toh Masha Allah."
Sai ya gyara zaman sa
"Ya karin hakurin mu?"
Fuskarta ce ta sauya nan da nan, ya yi murmushi yana girgiza kansa
"Alhamdulillah." Tace bayan wasu yan dakiku
"Toh Alhamdulillah, Allah ya kara mana hakuri."
"Amin." Tace tana jin abun na taso Mata
"Abu daya nake so daga gareki dan Allah, ki cire komai ki barwa Allah, ki sani Muhammad ya tafi ba zai dawo ba, kiyi masa addu'a dan ita kadai yake bukata,maganar yaran nan da kika hana su zuwa ko ina har wajen mahaifiyarta na soke shi, ki barsu su yi rayuwar su yadda suka saba, duk wannan ba shine zai hana abinda zai faru ya faru ba sai dai idan har Allah be kaddara ba."
Shiru tayi, ranta ya sosu, tasan dole Yaya ce ta fada masa, dan tasan hakan ba halin Aunty bane ko me ya faru tsakanin su bata taba fadawa Baban, tayi mata wannan shaidar sai dai kawai ba zata fada bane.
"Kinji ko? Ayi hakuri a barwa Allah komai."
"In sha Allah."
Tace tana sauke kanta kasa, Abu daya da yake kara birge Baban da ita kenan, bata taba ketare maganar sa sai dai idan be yi ba, shiyasa yake respecting dinta sosai domin tayi masa abubuwa masu tarin yawa a rayuwar sa,da ba zai iya mantawa ba. Mikewa yayi yana karkade jikinsa, sai ta daga kai tana kallon sa
"Dama dalilin zuwan ka kenan?"
"A ah, zuwa nayi naga matata, uwargida sarautar mata!"
Murmushi ne ya subce mata, ta tashi ta rakashi har kofar falon, sannan ta dawo ciki shi kuma ya nufi bangaren Aunty.
[03/10, 21:27] Mss Xoxo: ❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [05/10, 16:20] Billyn Abdul 2: *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*
5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (12).
***Daidai gwargwado yaran sun fara dawowa kamar da duk ba dukka ba amma suna shigowa wajen jiddan ko su hadu a wajen Yaya, saura kwana uku a koma school sai ya zama kawai shirye-shiryen komawa suke tunda sabon session ne. Text books din Ss1 amira ta bawa jidda ita kuma ta karbi na Maryam a kalla an samu sauki. Duk da Baba babu laifi alhamdulillah harkoki na kara bud'e masa musamman da yanzu siyasar ta juyo kansa da gaske yake yin ta,ana kuma saka ran zai samu babban matsayi a gwamnatin tun kafin zabe yazo. Gidan da yake jikin nasu akayi masa talla bayan Maigidan ya rasu ya zama na magada, siyewa yayi ya fashe ya shigo dashi cikin gidan nasu dan so yake ya fitarwa da kowa part dinta me zaman kansa tsakanin Mama da Auntyn yadda kowa zata ci gashin kanta, sannan yana so ayi gyaran part din Yaya itama. Ana jibi zaa koma makaranta Safeera ta kira wayar aunty daga cikin wayar Mom dinta tace zato zo, kwatance aunty tayi ma Maman Safeeran bayan sun gaisa tace zata saka a kawota dan tun da akayi hutu take maganar jiddan. Ita ma jiddan tana maganar ta amma tasan ba kamar Safeeran ba dan ta damu sosai da ita, ta kan kira a wayar Aunty su yi magana. Wanka jidda ta tashi tayi, ta sake gyara dakin ta ta zauna zaman jiran bakuwar tata ko wajen Yaya bata je ba, tana zaune Usman yazo ya kirata yace tazo in ji Aunty wai kawarta tazo, da sauri ta fito ta samu Safeeran a zaune a kujera ita da wani saurayi wanda zai yi sa'an Ya Fauwaz ko ya dan girme shi, da sauri Safeeran ta tashi ta rungumeta, cikin farin ciki, dariya suka bawa su Aunty da saurayin da ya gaza boye farin cikin sa
"Sannun ku da zuwa." Tace bayan sun saki juna sun zauna a tare
"Yawwa."
Yace idanun sa na kan jiddan, be taba ganin yarinya me kyawun ta ba, take tashiga ransa duk da shekarun ta basu kai shekarun da yake jin ya kamata ta san soyayya ba, tashi yayi bayan sun gama gaisawa yace zai je ya dawo anjima ya dauki Safeeran, har ya mike tace
"Ya Isma'il dan Allah ka bari sa dare."
"Ko? So kike mom ta hanani shiga gida kenan."
"Ba zata ce komai ba Allah."
"Da yamma dai zan dawo."
Bata fuskar ta, tayi kamar zatayi kuka, ya juya ya fice yana jin dukkan wani karsashin da yake dashi yana gushewa, love and first sight kenan, zai iya jira a yadda yake ji, zuwa lokacin da ya chanchanta. Da kyar yayi driving kansa zuwa gida ya shiga falon ya tarar da Mom da wata Aunt dinsu kanwar Daddy, gaishe su yayi, ya shige dakin sa ya kwanta rigingine yana kallon sama.
"I'm in love." Ya furta a hankali yana lumshe idanun sa.
Gidan su Safeera babban gida ne sosai kuma suna da kudi dan Baban su babban dan boko ne kuma business man, su biyu iyayen suka haifa daga ita sai Ya Isma'il, suke nan su daga kansu Mom bata sake haihuwa. Rayuwar su suke cikin jin dadi sosai, gashi sun shaku da Ya Isma'il ko yaushe suna tare da junan su, yau ma da driver ne zai kaita gidan su jiddan amma sai yace zai kaita dan shima yaga jiddan da kullum take maganar ta, sai gashi abinda be yi tunani ba ya faru, a cikin dan kankanin lokaci ya kamu da soyayyar yar karamar yarinyar da ba dan kar yayi karya ba sai yace Safeera ma zata iya girman ta, be sani ba amma ko yanayin jikin ne dan mafi akasari fulani basu da girman jiki. Juyi ya dinga yi shi kadai ya rasa abinda yake masa dadi sam,har sai da Mom ta biyo shi jin shiru be fito ba, a tunanin ta bacci yake amma sai ta ganshi a kwance, ta tambaye shi abinda yake damun sshi, kamar ya fada mata gaskiya sai ya kasa ya girgiza kai kawai yace hutuwa yake, fita tayi sai ya tashi kawai ya bi bayan ta dan zaman haka ba zai amfane shi da komai ba.
****Zuwan Safeera yayi ma jiddah dadi sosai, ta ware sosai har ta bawa Aunty mamakin yadda ta sake da Safeera bata sake da kowa haka ba, tare suka ci abinci sannan ta ja ta wajen Hajiya Yaya, suka dade anan har Amira tazo itama tayi joining dinsu, suka saka Yaya a gaba ta dinga biye musu ana dariya. La'asar din farko farko sai ga Ya Isma'il yazo, suna part din Yayan Usman yazo kiransu, Safeera bata so ta zata zai kyaleta sai daren, dan idan sun koma gidan ma babu abinda zatayi gashi ba kowa. Turo baki tayi sanda suka shigo falon Auntyn yana zaune a kujerar dake facing hanyar shigowa, idanun sa akan hanyar yana jiran ya ga ta in da zasu bullo, ajiyar zuciya ya sauke da karfi sanda suka shigo wanda har da Aunty ta kalle shi, ya waske da sauri yana mikewa
"Nace fa sai dare Ya Isma'il."
"Ni kuma nace dama da yamma zanzo ai."
"Muna shan hirar mu."
"Wai haka jiddaaaah?" Ya ja sunan batare da ya san yayi ba
"Eh." Tace tana murmushi, murmushiin shima yayi mata sannan yace
"Zamu sake dawowa aunty, akwai in da zanje anjima ne shiyasa nazo yanzun."
"Ba komai Isma'il, itama Jiddan zatazo in sha Allah."
"Yaushe?" Ya fada da sauri, sai ya hau sosa kansa bayan yayi maganar
"Ko weekends dai, tunda an koma school."
"Ok, Allah ya kaimu."
"Amin."
"Ungo jidda, rakasu."
"Tohm."
Ta karbi yar madaidaciyar ledar suka fita tare, ta rakasu har wajen mota sannan ta mika ma Safeera ledar da Auntyn ta bata, ta karba tana leka ciki sannan tace ta gode.
"Wai kuwa kuna da hoto tare ku biyu?" Ya tambaya bayan dogon nazarin da yayi, girgiza kai Safeera tayi ta fasa shiga motar
"Yawwa Yah snap us dan Allah."
"Ok." Ya ciro wayar sa, ta dafa kafardar Jiddan ya dauke su tare, yana lura da yadda kunya ta kama jiddan, yayi murmushi yace
"Bari ayi ma kowacce ita kadai, na tarihi."
"Yes, fara dani."
"A ah bari na fara da jidda "