Sanadin labarina complete novel - Chapter 9
Sanadin labarina complete novel Chapter 9: Sanadin labarina complete novel Chapter 9. "Toh ai Yaya abin ne, nasan halin ya Tariq da taurin kai, kar ya bata…
4,492 words
"Toh ai Yaya abin ne, nasan halin ya Tariq da taurin kai, kar ya bata ma yarinya lokaci azo ba'a barta ta zabi miji da kanta ba shi kuma yazo yace ya fasa."
"Ai wallahi ina me tabbatar maka be isa ba, kai dai kawai kayi abinda nace, sauran ka bar komai a hannu na, Dijengala nake me abun mamaki "
"Toh Allah ya taimaka dije."
"Ka fadi sunan uwarka."
"Hahaha, Allah sai na fasa taimaka miki."
"Yi hakuri toh."
"Ban hakura ba, sai kince please."
"Ni zaka wulakanta dan zaka taimaka min?"
"A ah, amma sai kin bani hakuri da turanci."
"Kasan dai bana son shegen turancin nan? Kaga ana ciccize baki wai a dole ana turanci, mtswws! Aikin bur inji tusa."
"Shikenan tunda bakya son taimako na, kuma sai na fadawa Ya Tariq abinda kike shirya masa idan yaso ya hawo jirgi yazo ya sameki."
"Yazo din mana, tsoron sa nake? Karka taimaka din idan baka taimaka ba ai ubanka zai taimaka tunda shi na isa dashi."
"Calm down My heart beat, wasa fa nake miki, ai ban isa naki abinda kike so ba, yanzu zanje na fara aikin ki."
"Yawwa dan albarka, yi maza ka gama kai ma na samo maka taka ko a karkara ne."
"Wait what? Wallahi kar ma a fara dan ina da fine babe dita idan ba haka ba kuwa zan bar gari na hada kayana na tafi karkashin gada."
"Ka tafi bangon duniya ma, dan nema."
"Maimakon ki lallaba ni,o matar nan."
"Ba zan lallaba din ba, nima ba uban da ya lallaba ni da za'a auran min dunkum din kakanku."
Da sauri ya sa hannu ya toshe bakin sa saboda yadda ta bashi dariya sosai, ya mike ya fice dan idan ya biye mata ba zata gaji ba sam.
Tsohon part dinsu ya shiga, ya ciro sabuwar wayar Jidda ya bude ta, ya tura hotunan Ya Tariq masu yawan gaske sai nasu dasu Amira dan kar ta kawo komai, sannan ya kashe ta, ya maida ita kwalinta, ya nufi bangaren Auntyn. Jidda na kwance a daki tayi rigingine taji usman na ihun ya Fauwaz, da sauri ta duro ta fito ta same shi a tsaye ya daga Usman sama yana dariya.
"Ya Fauwaz." Tace ya sauke Usman yana mata murmushi
"Jidda ce tayi kiba haka?" Yace a sigar tsokana, dariya ta saka
"Kai Ya Fauwaz yaushe ka ganni last zaka ce nayi kiba."
"Allah kuwa, idan na ganki a hanya ma ai ba zan gane ki ba."
Dariya kawai take dan tasan hadda tsokana, duk da tasan tayi mugun chanjawa sosai dan baki daya jikinta ya murje duk ramukan nan sun ciko sai wanda ba za'a rasa ba. Bangaren chest da bayanta a lokaci daya tayi su dan bata taba ma tunanin zata yi ba, girman lokaci daya yazo mata shiyasa yanzu koyaushe da Hijab dinta take yawo a cikin gidan saboda ma'aikatan da masu gadin gidan. Ledar wayar ya mika mata ta karba tana leka ciki, tayi tsalle cike da murna,
"Sakon Baba,."
"Mungode Allah ya kara budi."
"Amin Amin, Amira ma jiya aka bata tata, number ta na ciki tace ki kirata kina kunna wayar akwai gist."
"Toh shikenan, yau ba zan iya bacci ba, kusan kwana zamuyi muna hira nasan."
"Lallai gandoki, zaku yi ku bari ne, ina Aunty ta shiga?" Ya waiga yana kallon bangaren bedroom din Auntyn
"Tana part din Baba."
"Ok, gidan shiru,kuma ku tattara ku dawo ma dinga zuwa hutu kawai."
"Aikuwa."
"Shine, dama akwai plan din Baba, amma wannan zuwan nasan har da magaanar tafiyar ma, kinga ya maida hankalin sa waje daya ya dinga zuwa ko duk after two weeks ne, yanzu kuwa yana chan hankalin sa na nan."
"Ai kamar Yaya ce bata son tafiya ko?"
"Haka zata hakura, an gama.mata part dinta ma fa."
"Lallai dole ta hakura."
"Aikam, in baki labari." Yayi kasa da murya
"Nayi new babe wallahi."
"Dan Allah, aina take?"
"A chan Abujan ne."
"Lallai, Masha Allah."
"Ki bari kawai, zuwa zan na shige daga ciki, na bar Ya Tariq tunda shi ya tsaya kure wa boko guda."
"Be gama ba har yanzu? Ya dade."
"Ya gama wani course yake, kinsan pilot ne."
"Wai, ban ma sani ba ai."
"Aiko yana chan ya kusa ma, dazu muka gama waya ma."
"Allah sarki, idan kunyi waya ka gaishe shi."
"Gaki da sabuwar wayar ki, na ma saka miki number kowa har tasa, ki kirashi kawai."
Zaro ido tayi
"Wai... Tsoron sa nake ji, ba zan iya ba wallahi."
"A ah zaki iya mana, menene abun tsoro?"
"Uh um, ka gaishe shi kawai."
"Toh shikenan, zaiji."
"Nagode."
"Bari na dubo Jamil mu gaisa, zan dawo idan aunty ta fito."
"Ok sai ka dawo." [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (18)
***Tunda suka shigo mota be kara magana ba, tsoron sa daya kar Jiddah taki shi, be san ya zai yi da rayuwar sa ba idan har tace bata son shi. Da kyar ya kaisu gida suna zuwa yayi saurin yin hanyar dakin sa, jiki a sanyaye itama Safeeran tayi nata dakin tana fatan kar a samu matsala dan ta san yadda Ya Isma'il yake son Jidda. Tunda ya shiga dakin ya kasa zaune ya kasa tsaye,duk da ba wai tace bata son shi bane, amma kuma ai be kamata ta rikice haka ba, ya kamata ko yaya ne ta bashi amsa. Wayar sa ya dauka ya kira Farouk yace ya shigo dan Allah, nan da nan sai gashi, ya kwashe komai ya fada masa , shiru yayi yana nazari kafin yace
"Kila shock ne, kasan har yanzu fa da sauran su, kila bata taba tunanin hakan ba shiyasa tayi acting haka, give her some time, in sha Allah Khair."
"Kana ganin ba matsala, tari ne fa ya sarketa kamar zata shid'e."
"Calm down, ina ji a raina ba matsala bace gaskiya, ka bata time ka barta da Safeera suyi magana, kawarta ce tafi kowa sanin ta, hopely zata iya convincing dinta ma."
"I hope so, I'm just nervous ne, ba zaka gane ba. I don't think zan iya daukan rejection."
"Ba matsala fa, ka kwantar da hankali ka, as you come fine like this akwai wata babe da zata ki ka ne?"
"A ah fa, banda irin Jidda."
"Hadda wadda tafi Jidda ma."
"Kana dai fasa min kai ne kawai."
"Da gaske fa "
"Toh naji, bari na duba me akayi a kitchen yunwa nake ji yau ko breakfast ban ba."
"Kaji ko?"
"Bari kawai."
Yace ya fita shi kuma ya mike kafarsa yana tausayin Isma'il din idan har aka samu matsala.
***Zaman jiran Baba yayi tayi har bayan isha, sannan ya shigo a gajiye duk da haka sai da ya tsaya a wajen Yayan dan yasan tana nan tana jiran sa, a zaune kuwa ya sameta tana kallo tana dan gyang'adi, sallamar sa ta sakata wartsakewa ta mike da sauri
"Yaya baki bacci ba, Allah yasa bani na rike ki ba nasan da wuri kike kwanciya."
"Kai nake ta jira wallahi, sannu da hanya."
"Yawwa, ai da kin kwanta idan Allah ya kaimu da safe sai muyi maganar."
"Ba zan iya hakura bane ai, magana ce me muhimmanci."
"Toh, Allah yasa lafiya "
Yace yana zama a kasan carpet din,daga gefen kafarta, baya taba zama kujera da mahaifiyar sa tunda ya taso, yana bala'in so da kaunar Yaya dan baya hada duk wani abu da ya shafe ta da kowa har kuwa da yayan cikin sa, shiyasa duk abinda take so shi yake mata. Gaba daya ya tattaro hankalin sa waje daya ya kara tankwashe kafarsa, dan yasan idan ba fada masa matsalar Yaya tayi ba ko baccin kirki ba zata iya ba.
"Maganar yaran nan ce Alhaji."
"Ina jinki Yaya."
"Ajiye 'yaya mata a gaba haka be kamata ba, ba daya ba har su biyar rigis, wanda duk cikin su babu wadda akayi wa aure ba zata zauna ba, abun nan kullum dashi nake kwana nake tashi, ya zama lallai duk su fito da miji ko da za'a yi karatun dai ya zama akwai maganar aure."
"Haka ne Yaya, dama dai akwai maganar Safiyya da Umaima a k'asa."
"Ah toh Masha Allah, ai ban sani ba, sai ayi abinda ya kamata, daga su sai azo maganar na k'asan."
"Wai da suma su fara jami'ar, tunda Maryam ta fara yanzu tana ajin farko, Amira da Hauwa'u kuma zasu fara suma bana,sai a hade su, su uku idan sun kai ajiye biyu ."
"Hakan ma yayi, amma ni ina da wata alfarma da nake nema a wajenka, buri na kenan idan ka cika min burin nan ka gama min komai."
"Babu alfarma a tsakanin mu Yaya, me kike so ayi? Fada kawai zakiyi ni kuma zan cika miki da yardar Allah."
"Magaanar yaron nan ce Tariq, da yarinyar nan Jiddah."
"Na'am!"
"Na duba na dubo gaba daya dangi kaf banga wadda ta dace dashi ba, sannan na gamsu da tarbiyyar yarinyar nan dari bisa dari, ina kaunar ta har cikin raina bana so mu rasa ta, shine nake so ka kaini wajen mahaifinta na nema wa Tariq auren ta."
"Toh Yaya, duk yadda kika ce haka za'a yi, da ni da yaran nan duk ikon ki ne."
Washe baki tayi cikin tsananin jin dadi tace
"Allah yayi maka albarka,ya raba ka da duniya lafiya, ya sa yaran nan su rama maka."
"Amin Yaya."
"Yanzu yaushe zamu je?"
"Toh Yaya, ko wani satin idan Allah ya kaimu, sai muje."
"Toh shikenan, Allah ya kaimu."
"Amin ya Allah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Amin Amin,sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya."
***A daki ya samu Aunty, ta tare shi da fara'arta, ya fara watsa ruwa ya zura sabuwar jallabiyar sa sannn ya dawo falon ya zauna, abinci ta kawo masa wajen da yake zaune, yaci kad'an dan cikin sa a chushe yake, ta tattare ta kwashe ta maida kitchen sannan ta dawo ta zauna a gefen sa, zuciyar ta na azalzalarta da maganar Jiddah, kallon ta yayi yaga kamar akwai abinda zata fada masa, sai ya ajiye remote din hannun sa ya tattara hankalin sa ya bata yana fuskantar
"Ya akayi Halimatu, kamar da magana a bakin ki."
Murmushi tayi ta sauke kanta k'asa,
"Yanzu na baro wajen Yaya, tazo min da wata magana me girman gaske, duk da na amsa mata da toh dan dole a lallaba ta, amma kuma ina hasaso gaba, duk da ni kaina na dade ina hasaso dama hakan ta kasance a raina, amma na share saboda sanin halin yaran yanzu ba irin mu bane, kar kayi musu abu su ga kamar ka takura musu, shiyasa nayi hakuri na bar magaanr a raina, amma kuma sai ga Yaya tazo da maganar, kuma ga dukkan alamu idan har aka ki yi mata abinda take so za'a samu matsala."
"Toh, Allah yasa ba wani babban abu bane."
"Babba ne a wajen yaran idan har aka samu akasi, amma kuma idan suka hada kansu zan fi kowa farin ciki da wannan hadin."
Kanta ne ya kulle bata gane in da Baban ya dosa ba, ganin bata fahimta ba ya saka shi yi mata gwari-gwari.
"Yaya ce take so muje mu samu Yaya, a nemawa Tariq auren Jidda."
Wani gingirim taji kanta yayi, ta kalli Baban sannan tace
"Tariq kuma?"
"Eh."
Ranta ne ya dan sosu, har Baban ya fuskanci bata ji dadin maganar ba, duk da bata ce komai ba amma fuskar ta, ta nuna rashin jin dadinsa. Ido ya zuba mata cike da mamakin yadda ta karbi maganar, a tunanin sa zata fi kowa murna da hakan dan ko ba komai Tariq dan dakin tane, sannan be yi tunanin zata ki jinin sa ba, tunda duk tsiya ai Tariq dan sa ne, kuma idan da kara itama ai dan ta ne
"Akwai matsala ne?"
Yace mata fuskar shi na sauyawa zuwa bacin rai, girgiza masa kai tayi kawai. Sai ta mike ganin ba zata iya rike abinda take ji ba, ta fice daga dakin ya rakata da ido cikin tsananin mamaki. Daki taje ta zauna ta rasa abinda yake mata dadi, bata taba kin Tariq ba, ba kuma zata taba kin sa ba, amma Mama fa? Ya rayuwar Jidda zata zama a auren wadda mahaifiyar sa bata so ko kaunar ta? Har ga Allah tafi wa Jidda sha'awar Isma'il, tunda shi da mahaifiyar sa duk suna san jidda, zata fi samun nutsuwa dasu dan zasu tallafi rayuwar ta, sannan zata samu uwa da zata dubi lamuran ta. Safa da marwa ta dinga yi a tsakanin dakin ta, shiyasa Yaya dazu ta bata rai kenan akan maganar, shine tayi saurin fadawa Baban, da tasan hakan ne zai faru da bata yi mistake din fara sanarwa Yayan ba, dama ance ciki ba dan abinci kawai aka yi shi ba, da ta sani ta rike sirrin su ya zama tsakanin ta ne kawai da Jiddan har zuwa sanda zasu fahimci juna daga nan duk abinda za'a yi sai ayi. Yanzu ya zatayi? Zata cewa Baba a ah ne bayan abinda yayi wa Jiddan da bashi da maraba da abinda yayi wa Yayan cikin sa, ko zasu ki dansa Tariq ne bayan shi be kyamace su ba. Ko kuwa Baffan Jidda zai hana dan Baba auren Jidda ne? Bata da mafita, mafita daya ce idan har jidda taki, amma kuma tayaya ma Jidda zata ki? Baba ko Yaya su nemi alfarma a wajen ta, ta kasa yi musu. Ai da ta cika babbar butulu kuwa. Har kusan awa daya bata koma dakin Baban ba,tana ta sakawa da kwancewa har bata san lokaci yaja haka ba, dakin Jiddan ta shiga a tunanin ta ko tayi bacci dan tana da baccin wuri, ga mamakin ta, idanun ta biyu tana kallon hotuna a wayar ta, akan hoton Tariq take, jin Auntyn ya sakata saurin kifa wayar amma duk da haka Auntyn ta riga taga abinda take yi, maimakon tayi abinda ya kawo ta dakin sai kawai ta fice ta jawo mata kofar. Tashi Jidda tayi dan tunda ta zauna take kallon hotunan Ya Tariq dake cikin wayar, har sai da Auntyn ta shigo sannan ta dawo senses dinta, takashe wayar ta makala ta a charge ta kwanta ta rufe idanun ta, maimakon tayi bacci sai ta samu kanta da tunanin sa, ta dinga juyi tana so baccin ya dauke ta amma sam, haka tayi ta fama har dare ya tsala sosai, da kyar bacci ya dauke ta. Tashi tayi da safe idanun ta a kumbure saboda rashin bacci, ta gyara dakin ta dan yanzu part din Auntyn baki daya masu aike ne ke gyarawa. bayan ta gama ta fito falo ta zauna kenan tana kallon TV Ya Safwan ya shigo, ta gaishe shi ya amsa yana nuna mata fuskar ta
"Me ya faru da face dinki?"
"Bacci ne wallahi."
"Wai da gaske kike dama da kika ce raba dare zakuyi da Amira kenan."
"A ah, wajen 9 fa muka gama waya da ita, sai kuma baccin yaki zuwa."
"Kina me? Kallo ko?"
"A'ah, hotunan daka saka min na zauna ina ta faman kalla ashe har dare yayi ban sani ba."
"Ah shiyasa, kinga ai kin more kallo."
"Kai Ya Fauwaz."
"Allah kuwa."
"Fauwaz." Aunty ta kira sunan sa tana shigowa, kallon kofar yayi dan jiya be dawo ba, da yaga dare yayi sai kawai yace ya shigo da safe.
"Ina kwana aunty?"
"Lafiya lou, ashe tare kuke jiya da Baba."
"Eh wallahi, wajen Jamil naje kuma sai muka tafi wata sabgar sai dare muka dawo."
"Lallai, an kwana biyu ai ba'a hadu ba."
"Wallahi."
"Ya kowa da kowa?"
"Duk suna lafiya suna gaishe ku."
"Muna amsawa."
Sai ta wuce ta dauki flask ta fita zuwa part din Baba, dama abinda ya shigo da ita kenan. Ko da ta koma jiya da daddare Baban ya kwanta, da safen nan kuma ba'a tada maganar ba, a ransa yaji babu dadin yadda tayi amma kuma ya mata uzuri sosai, tunda ko da Mama ce haka zatayi itama, tunda yanzu ko a hakan ne yasan akwai kalubale a gaba ma, shiyasa kawai ya bar maganar yaga abinda Allah zai yi. Ko da yaushe idan Ya Fauwaz ya shigo sai yayi mata maganar Ya Tariq, duk kusan rabin hirar su akan sa yake mata, yana sanar da ita duk kyawawan halayen sa, hakan ya saka ko bayan da ya tafi ta kasa mantawa da duk magangan da sukayi,ta dinga bitar su kamar wadda take bitar karatu [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (19)
***Kusan sati guda kenan da zuwan su Isma'il amma babu wani information daga wajen Jidda, sun yi waya da Safeera da sabuwar number ta amma ba wadda tayi wa wata maganar a cikin su, hakan ya kara tada hankalin Ismail ya samu Safeera da magaanar sai kawai ta bashi sabuwar number din Jiddan da bata so ta shiga abun nasu sosai azo a samu akasi tazo tana jin haushin Jiddah. Samun number ya dan rage masa damuwa ya koma daki ya kirata sai dai har ta gama ringing bata daga ba, tana chan kitchen tare da Aunty ta bar wayar a daki tunda dama babu me kiranta daga Amira sai baffan ta, sai kuma Safeera idan tana so tace mata tazo WhatsApp suyi hira. Sake kira yayi ya dinga jera kiran tunanin sa tana gani ba zata dauka bane dan shine, sai kuma wata zuciyar ta tuna masa ai bata da ma number dinshi bare taki dagawa saboda shi ne, shafa kansa yayi yana mata uzurin kila bata wajen yana kokarin hana waccan zuciyar tashi ta farko tasiri a tunanin sa. WhatsApp yayi login sai ya duba number din yaga tayi registering WhatsApp din sai kawai ya shiga kai ya tura mata kalamai masu dadi da sanyin gaske, hoping zata duba ta bashi time suyi magana ko da a wayar ne ba sai a fili ba. Cigaba da zama yayi rike da waya yana dakon kiran ta ko kuma zuwan ta online wanda yasan tabbas za'a yi dayan biyu, ko ta biyo kiran ko tazo online. Dakin ta shigo bayan sun gama aikin da Aunty, ta dan gaji dan abinci sukayi na mutane da yawa da za'a fita dashi waje duk da akwai masu aiki amma kuma ya zame musu jiki duk irin wannan aikin tare sukeyi da ita da aunty, kasancewar aunty zata je taga Baffa duk da bata fadawa Jidda in da zata din ba dan bata so tace zata shiyasa ta bar mata aikin ta cigaba da kula dashi ita kuma taje ta shirya, ta fito ita da Usman suka tafi tare da Driver. Gama aikin kenan an zuzzuba a manyan kuloli ta baro wajen tasan Abu zata karasa sauran aikin a fidda shi, wanka ta fara yi tana shiga dakin, ta maida doguwar rigar dake jikin ta mara nauyi sosai ta kwanta lamo tana jin kanta na dan sara mata, tasan alamun period dinta ne shiyasa duk take moody ga wata irin kasala da take ji, farko da bata gane ba sai da Safeera ta fada mata sannan ta ganar da ita duk abinda ya kamata ta gane ta sani. Pillow ta daga ta ciro wayar ta duba, missed calls din da ta gani rututu ya sakata saurin cire lock din sai taga bakuwar number, da saurin ta, ta kira number back dan tasan duk wanda zai kirata ya san tane sosai kuma irin wannan missed calls din da yawa sai kaji tsoron ko ba kalou ba. A firgice ya dau wayar da take ajiye da a saman chest dinsa yayi rigingine yana jiran kiran gashi yana da fita zai je ya samu Daddy a office dinsa amma duk sai yaji baya son fita kwata-kwata. Yadda yayi mata saving sunan haka ya bayyana akan allon wayar sa, ya daga ba tare da bata lokaci ba yana manna wayar a kunnen sa sannan yace
"Bari na kiraki Jidda."
Sai ya katse kiran, muryar sa tar a cikin kunnenta, bata kawo shi zai daga ba kwata-kwata, sai tayi sakalo da wayar sanda ta dauki burarin shigowar kiran nasa, ganin zata katse ya sakata katsewa ta dan karata kadan a gefen kunnen ta kamar me tsoron shocking tace
"Assalamu alaikum."
"Jidda ,wa alaikisalam. Ashe zaki daga."
"Ina wuni?"
"Lafiya lou, kina lafiya? Ya gida dasu Aunty?"
"Alhamdulillah."
"Ina kika shiga ne, aka bar wayar bawan Allah tana ta neman agaji."
"Ina kitchen ne."
"Ah kice dai ashe da babbar chef nake magana, shikenan kinga ni lafiya lou."
"Uhum." Tace
"Me kika dafa mana? Nazo na karba dan nasan zai yi bala'in dadi."
"Abincin sadaka ne da akeyi."
"Oh okh, next time sai ace muzo muyi tasting ko? Nasan komai kika dafa zai yi dadi sosai."
Dan gajeren murmushi tayi me dan sauti, hakan ya sake bashi hope ya cigaba da zuba kamar be san yanayi ba, so yake dole sai yayi impressing dinta, ko ba komai a hankali zata saba dashi ta saki jikin ta dashi, shawarar da suka tsara kenan shi da zuciyar sa, ya fara kokarin saba mata da kanshi kafin komai ma yazo daga baya, duk maganganun da yake a gajarce take masa masa kanta na cigaba da tsananta mata da ciwo gashi bata so ta katse shi amma kuma maganar tashi ta ishe ta, sai da yayi ya gaji dan kansa sannan ya hakura yace zai kira anjima. Da sauri ta rigashi katse kiran ta kwanta tana tura kanta cikin filon ta yadda zata rage ganin hasken da yake kara mata ciwon kan.
***Ran Baba a bace yake sosai har Aunty ta gama masa bayani da abinda take so yayi idan Baba yazo masa da maganar Jidda, sai da ya bari ta gama tsaf sannan ya kalleta yace
"Kin gama?"
Sai a sannan taga yanayin fuskarsa, sai taji kamar an dake mata guiwowi, ta tabbatar ba zai goyi bayan ta ba kenan duk da yadda tayi ta kokarin tsara masa maganganun yadda zai fahimce ta
"Kin bani mamaki Innajo, kin bani mamaki sosai."
"Na'am?"
"Yanzu har kece zaki budi baki kice na hana Alhaji auren Jidda? Kenan ma Jidda tana da wani uban bayan shi ban sani ba?"
"Yaya baka fahimce ni ba."
"Bana so na fahimce ki, ni ba butulu bane mara godiyar Allah, me Jidda tafi shi yaron da har zaki dage kai da fata? Wacece Jidda ma? Ke kina ganin ke da yar taki har kun kai wani matsayi da zaku yi abinda kuke so ko me?..."
"Bari na tuna miki idan har ke kin manta, sanda Alhaji ya aure ki ke kanki kinsan ke ba sa'ar auren sa bace, haka yace yaji ya gani ya aure ki ya rufa miki asiri da ni kaina, sannan kika dauki yar taki da kike ganin karan ta ya kai tsaiko da har zaku butulce, kika kai masa ya karba ya rike babu banbanci da Yayan cikin sa, ko akwai banbanci?"
Yace yana kafe ta da ido cikin bacin rai
"A ah." Ta girgiza kai da sauri duk kwalla ta cika mata ido dan bata taba ganin bacin ran Baffa irin yau ba
"Sannan karki manta adalcin Alhaji lokacin da ya rasa Muhammad, kina ganin idan wani mahaifin ne ba shikenan ba kuma maganar auren ku ma zata iya lalacewa akan haka, amma me yayi? Shine ma yake kokarin kwantar miki da hankali ya kuma hana uwar yaron nan yin wani yinkuri, wannan shine mutumin da kike kin dan sa kike ganin be dace da yarki ba tunda ita din yar gwal ce."
"Dan Allah Baffa kayi hakuri, dan Allah."
"Ki barni na gama tuna miki tunda ke kin manta, sanadiyyar waye na samu lafiyar kafata? Idan kin manta sai ki tuna, dan haka..."
Ya nuna ta da yatsa
"Jidda ba 'yata bace, haka kike ba taki bace, yar sa ce dan haka yana da damar yayi duk abinda yaga dama akan rayuwar Jidda, ke ko mutuwa nayi wallahi ba zan yafe muku ba idan kuka kiyi masa biyayya."
"Dan Allah kayi hakuri Yaya, nayi laifi babba, amma dan Allah kayi hakuri."
"Toh kar na sake jin wannan maganar kin daga ta, sannan idan kinsan kin bata masa rai saboda magaanar nan, lallai lallai ki bashi hakuri, sannan ita ma Jiddan zan saba mata idan har tace zata zo min da shashanci."
"Ita bata ma san da maganar ba."
"Idan ma ta sani din, kuma ko yanzu Alhaji yake so ayi auren sai anyi."
"Allah ya huci zuciyar ka Yaya."
"Amin."
Yace a kufule, sum sum sum ta tashi ta fice zuwa gidan su Saude, daga nan bata wani jima ba tayi sallama ta tafi, dan da tasan ma abinda zai faru ne da bata zo ba, sai bayan Baffan ya karanta mata duk abubuwan da ta manta sannan ta dawo hankalin ta, tasan bata kyauta ba kuma dole zata bawa Baba hakuri akan maganar.
***Baba na zaune a hadadden falon sa na ciki wanda ke cike da ababen more rayuwa, news yake kalla hankalin sa baki daya yana kai har wayar sa ta gama ringing sam be ji ba. Mama ce tazo ta zauna a kubin sa, cikn shigar alfarma kamar ko da yaushe, kamshin turaren ta ya cika ilahirin falon. Dan juyowa yayi ya dube ta, yayi murmushi kawai itama ta maida masa ya cigaba da kallon news din har zuwa sanda aka gama, juyowa yayi ya dauki wayar sa zai yi kira sai yaga missed calls din Tariq, kwana wajen biyu kenan basuyi magana ba, yana taso ya kirashi dama yaji progress din training din nasa dan baki daya yayi dedicating lokacin sa akan son yayi achieving hours din nan, yawanci ma yanzu ya fiyi saboda yanayin busy din da yake shiyasa ya tsirga sosai duk da giant ne a tsaye yake amma hatta idanun sa sun fada saboda rashin isashen lokacin da baya samu. Ko waya ma da Baba kawai sukeyi shima kuma duk maganar akan training din nasa ne sai jefi-jefi yake kiran Mama ko ta kirashi yaga missed call ya kirata idan yana free. Yanzu ma fitowar sa kenan daga cikin wajen yana cike da farin cikin akwai yiwuwar in less than a year da ta rage masa sai iya hada hours din, shiyasa ya cika da murna ya kira Baba dan ya fada masa amma kuma be dauka ba. Cigaba da tafiya yayi zuwa in dai zai hau train dan yau akwai in da zashi ba kai tsaye gida zai koma ba, yana so yaje yayi siyayya kafin a shiga cikin sati ya zama so busy ya kasa siyan abubuwan da bashi dasu. Kiran Baban ne ya shigo, ya daga yana rataya rigar sanyin dake rike da a hannun sa a saman kafadar sa, suka gaisa ya tambaye shi yadda ake ciki, ya sanar masa da duk progress din da aka samu, yayi masa murna sannan yace yana so ya nemi alfarma a wajen sa
"Inaso nayi maka wani katsalandan a rayuwar ka, duk da bazan fada maka ko menene ba, amma ina neman amincewar ka, idan har ka amince shikenan, ina me tabbatar maka da ba zakayi nadama ba."