Sanadin labarina complete novel - Chapter 8
Sanadin labarina complete novel Chapter 8: Sanadin labarina complete novel Chapter 8. "Amin Halimatu." Yace yana murmushi, fitowa Mama tayi fuskar ta babu…
4,491 words
"Amin Halimatu." Yace yana murmushi, fitowa Mama tayi fuskar ta babu yabo babu fallasa dan farin cikin da take ciki ya danne haushin Auntyn da take ji, ciki ya shiga da nufin shiryawa ya barsu a zaune suna jiran fitowar sa, babu wadda tayi magana a cikin su, har ya fito cikin shigar manyan kaya da shadda da babbar riga,ya dora dara akan sa,ya kira Safwan tun kafin ya shiga wanka yace yazo ya kaishi airport. Sallama yayi daga kofa sai da aka bashi izinin shigowa sannan ya shigo, ya russuna ya gaida Baban,sannan ya gaida su Mama.
"Airport zaka kaini." Baba yace yana daga tsaye, Mama ce ta tashi ta dauko suitcase dinsa ta mikawa Safwan din, ya karba ya fita da ita, sannan shima ya sake musu sallama ya fita. Ya rage sai su biyu, Mama ce ta fara ficewa tana bata fuska, sannan Auntyn itama ta fita ta rufo masa part din,da bawa Usman key din tace ya kai wa Maman.
***Sati Baba daya a chan akayi komai ya saka hannu yayi approving aka saka ranar da za'a yi taron nad'a su wanda zai kama kwana biyu tsakani, be dawo ba sai kawai ya aika Mama da Aunty suka zo,sai Kawu Rabi'u da Alhaji Adamu da Malam Nura aminan Baban, sai Safwan. Jidda, Amira, Umaima da Maryam suka tattara suka koma part din Yaya, ta samu abokan yi aikuwa sukayi ta fama. Washegari suna zaune aka dauko maganar Tariq, Yaya ta zage tana fada musu matsalar sa ta rashin lafiya, ita a lallai sai ta yi convincing dinsu sun yarda ba kalou yake ba. Maryam ce tace
"Yaya fa ras yake wallahi, kawai yanayin sa ne haka yanayin Malam dinki."
"Yo wannan ai har yaci uban Malam wallahi."
"Bari dai kiga a samu wata tayi wuf da kalbinsa, ba ma zaki gane shi ba."
"Kayya, masu irin bakin halin nan fa basu ragawa kowa ba,matan nasu ma su suka fi shan wahala dasu."
"Aiko Ya Tariq zai baki mamaki Yaya, ai shi na zamani ne ba irin Malam dinki ba."
"Toh zamu gani ai, ni wallahi da ma wayata tana irin kiran nan da ake ganin mutum da sai na kirashi na sake jaddada masa maganar shan maganin nan, ku kuma duk ba waya gwara ma ni da yar karama."
"Sai dai na karbo ta Ya Safiyya." Umaima tace tana mikewa
"Yawwa karbo, kice tazo nan nace itama dole na tashi tsaye dan kusan bakin halin su daya da uban gayyaar."
"Yanayin su ne a haka." Jidda tace ba tare da ta kawo komai ba, wani kallo Yaya tayi mata sannan tace
"Eheee? Kare su kike jidda?"
"A ah Yaya, kawai dai.
"Kawai me?"
"Ba komai." Tace tana murmushi
"Yawwa, gwara ma dai karki kare shi."
"Toh Yaya."
Karbo wayar Safiyya Umaima tayi, ita kadai take bawa da taje ma bacci take sai kawai ta dauko ta taho. Ta kunna data ta kira shi ta mikawa Yaya wayar
"Idan ya daga kiyi magana, kar kuma kice ni na kira wallahi."
Karba Yaya tayi, ta mike rike da wayar tana jira ya dauka, tana kallon kanta a cikin wayar mamakin yadda al'amarin yake kasancewa na sake kamata. Ta dau lokaci tana ringing kafin a daga, fuskar sa ta bayyana a cikin wayar, dafe kansa yayi ganin fuskar Yaya ta cika screen din, kautar ta kansa yayi yana kokarin danne dariyar da ta taso masa dan duk abin mutum idan yaga fuskar Yaya a cikin wayar sai yayi dariya.
"Kana jina?" Tace tana daga murya da karfi,
"Ya Allah!" Ya motsa bakin sa, sai kuma yace
"Ina jinki?"
"Yawwa, baka iya gaisuwa bane ni wai?"
"Ina wuni?"
"Lafiya lou, naga ka kara haske ko mai kake shafawa ne?"
" A ah Yaya, bana shafa komai."
"Toh ai shikenan, baki yi min murnar Babanku ba."
"Allah ya sanya alkhairi." Yace kai tsaye dan shi fa duk abinda tace kawai ahakan yake biye mata
"Safiyya ce ta kira miki wayar?"
"A ah Umaima ce ta aro wayar Safiya ta kira min kai tunda kai ba zaka kirani ba."
"Ina Umaiman?"
"Gata." Yaya ta juyar da wayar zuwa bangaren da suke zaune
Da sauri ta dukar da kanta, Amira ma tayi kasa ya rage saura Maryam da Jidda kawai yake gani. Girgiza kai Maryam ta hau yi
"Wallahi Ya bani na kiraka ba."
Kallon su yake su biyun Yaya na sake hasko masa su a tunanin ta Umaima ce a zaune sam bata lura sun buya ba ita da Amira. Shiru yayi be ce komai ba, dan ganin figigiyar yarinyar nan ya saka shi manta abinda ma zai ce, tana nan yadda take bata sauya ba. Kashe wayar yayi kawai ba tare da yace komai ba. __SL__**
©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (16)
***Da yamma Isma'il yazo daukar su, cike da zumudin ganin jiddah, shi da Farouk suka zo yayi parking a chan gefen gidan sabo da motocin dake wajen sannan ya kira Mom a waya yana fatan su fito tare da jiddah, dan haka ma yazo da Farouk dan ya ganta a zahiri ya daina cewa ya haukace akan yar karamar yarinya. Fitowa sukayi suka tsaya a jikin motar Farouk ya kalle shi ya kwashe da dariya
"Wai duk zumudin ne haka?"
"Ba zaka gane ba, kwana biyu da ban ganta ba, ji nake kamar na shekara ban ga cute face din ta ba."
"Uhum umm, sannu Romeo"
"Ai nafi Romeo sai dai baban Romeo."
"Ah lallai, sannu."
"Yaww, idan ka ga babyn zaka tabbatar na iya kamu, ni zan raini kayata, ta tashi ta tsarin da nake so."
"Gaskiya ne kuma, amma fa ana iya samun matsala irin haka, sai kaga karshe yarinya tace bata so."
"Think positive dan Allah, in sha Allah babu abinda zai faru."
"Allah yasa."
Hango fitowar su Mom ya sakashi yin shiru, yana leken bayansu, ya hango su ita da Safeera a baya hannun su sarke da juna, ajiyar zuciya ya sauke da sauri Farouk ya kalli wajen da yake kalla. Har suka karaso idanun sa na kanta,shi kuma idanun Mom na kanshi tana nakaltar yanayin sa, Farouk ne ya zungure shi wanda saboda yadda yake kallon su yana murmushi har sai da Jiddan ta dan ji kunya, yayi saurin waskewa yana juyawa wajen su Mom
"Mom kun fito ashe."
"Ina zaka san mun fito?" Tace sai ya sosa kansa yana kallon Farouk, ya harare shi kawai ya budewa mom kofar suka shiga ita da kanwar Daddy, Safeera ta zagaya ta shiga suka sakata a tsakiya, dan russunawa jiddah tayi
"Mommy ku gaida gida, sis sai gobe a school mungode."
"Nifa jiddaaaa?"
"Hadda kai Ya Isma'il, ina wuni?"
Dadi na ya kamashi,yace
"Fine, bari mu tafi."
Sannan ya rufe kofar motar Farouk yayi kamar ya daki kafadar sa amma ya kyale, kamar ma Isma'il din ya manta da su waye a cikin motar. Matsawa baya jidda tayi, tana rike da hannun Usman suka juya motar ta daga musu hannu sannn ta juya zuwa cikin gidan.
Shiru ne ya biyo baya, fuskar Isma'il tamkar an masa bushara da aljanna, waka ya kunna a motar ya rage volume din sosai yadda ba zai damu na baya ba, ya rike wa motar wuta yana bin wakar a hankali a hankali.
"Malam ka tafi damu a hankali kar soyayya ta kwashe ka, ka zubar damu a titi."
"Kyale ni." Yace yana dariya
Aunty Yagana ce ta kasa hakuri, tace.
"Gata yarinyar me hankali wallahi."
"Wa?" Suka hada baki dukka har Isma'il din
"Jidda."
"Auw, eh kuwa." Mom tace kawai tana murmushi
"Ai jiddah wallahi tayi, ga hankali da nutsuwa wallahi." Safeera ta dora
"Bata da damuwa kwata -kwata."
"Allah dai ya bar wannan kawancen naku har girman ku, har jikokin ku ma, duk da naga yayan naki ya rikice, Allah ya tabbatar mana da alkhairi Isma'il."
"Na'am?"
Yace yana kokarin juyowa bayan dan be yi tunanin zaayi saurin gano shi ba
"Ka kula fa." Mom tace sannan ta dora
"Farouk kayi ma abokin ka fada, ya rage zafafawa, ita rayuwar nan komai a hankali ake binsa."
"In sha Allah Mom,ina fada masa ai."
"Munafuki." Yace yana hararar sa
"Wai Ya Isma'il ne...?" Sai tayi shiru tana yin murmushi
"Allah yasa hakan ya kasance,."
"Amin idan da alkhairi."
Shiru yayi be sake cewa komai ba, yasan dole Safeera ta gayawa jiddah, shi kuma be shirya hakan ba yanzu kar tayi rejecting dinsa tun kafin ya koya mata son sa. Dole ya hanata fada mata dan sai ya jira right time, yanzu da sauran su a fara musu maganar soyayya. A gida ya ajiye su be shiga ba suka juya shi da Farouk, suna fita suka hau fada shi Farouk a lallai sai ya nuna masa is too early saboda yana jiye masa karyewar zuciya musamman a hangen sa da yanzu Jiddan suka sake yin sama, da kuma yanayin kyawunta zata iya samun yayan manyan kasar suce suna son ta (tunda shi be san jiddah ba yar gidan bace) shi kuma Isma'il yaki yarda da duk wani point da zai kawo sam, ya riga yayi nisan da ba zai gane duk abinda za'a ce masa ba. Da daddare da ya dawo gida ya samu Safeera ya kwabe ta yace kar tace ma Jiddan komai, sukayi alkawarin ba zata fada ba, akan haka suka tafi, ya kasance ita ta sani amma jiddah bata taba hasashe ko kawowa ba. Tafiyar Baba da Mama ya saka gidan ya zama tamkar part din Yaya ne kawai, anan suke duk dabdalar su tunda yanzu sun rage daga Amira sai Maryam kawai, Safiyya da Umaima sun bi su tunda su dukka sun kammala karatun su ana shirin fara higher institution, rabon zaa yi haka ne admission din Safiyya ya dinga delay karshe dole sai dai su fara tare da Umaima a wata private university din a Abujan. Da farko Mama cewa tayi ba zata bar yaranta a wajen aunty ba, sai da Baba ya bude mata wuta sosai yace toh sai ta zauna ya tafi da Auntyn dan shi ba zai katse musu karatu ba sannan ta hakura, duk da haka sai da ta kawo yar uwarta ta zauna a part dinta a zuwan ta dinga kula da su Amiran, sai gashi da ita da su Amiran duk sun maida part din Aunty da na Yaya wajen zaman su, idan akaje school aka dawo anan zaa baje har dare, daki daya yanzu Amira da Jidda suke kwana, hakan yakara karfin shakuwar su sosai.
Rayuwar ta cigaba da garawa cikin ikon Allah, Jidda ta shiga Ss2 Amira ss3, anan ne Baba yace jiddan tayi waec a Ss2 din saboda yana so su taho gaba daya, jin haka ya saka Safeera tada hankalin ta, a dole itama aka kyaleta tayi a SS2 din dan ba zata iya bari jidda ta tafi, ta barta ba. Haka akayi suka zauna zaman yin waec sannan sukayi neco, bayan an gama ne jiddah ta shirya ta tafi garin su wajen Baffan ta, tayi sati uku sannan ta dawo lokacin ma Amira taje Abuja, sai ya rage sai ita kadai a gidan kamar mayya. Zaman ta da Yaya ne yake debe musu kewa dukkan su, dan idan kana tare da Yaya ba zaka taba yin hawan jini ba. Tana zaune tana kallon wata drama a wayar aunty rabin hankalin ya tattara ya koma kan kallon duk hirar da Yaya take mata bata ji ta ba, har tayi fushi ta tashi ta fito waje tana sababi
"Takwara ta koya miki wannan banzan kallon kayi ta magana ayi maka banza, mtsw kuma wai a haka ake so ka koma Habuja. Ni kawai a barni na koma kauyanmu."
"Ya hakuri Yaya, wallahi banji ki bane." Tace tana fitowa ta zauna a gefen Yayan
"Toh naga kema da muke zama muyi hirar mu kin bi hanyar yaran chan."
"Kallon da dadi Yaya."
"Duk dadinsa ya kai gidan badamasi ne?"
"A ah be kai ba."
"Ah toh, ki daina bari na ina ta magana ni kadai"
"Na daina in sha Allah."
"Yawwa yar albarka, yanzu tunda an gama makaranta sai me?"
"Sai ta gaba, Baba yace cigaba zamuyi."
"Auw kema biya musu zakiyi ke da nake ganin ki me hankali, uban me ake tsinta ne a bokon da za'a ce sai an kure shi, shi kanshi wanchan sahoramin ina nan ina jiran dawowar shi sai na wanke shi tas, in banda shirme karatu ba na Allah da annabi ba, ace kaje kayi zaman ka ko kazo ma a kanka sai wani abu vidiyo, ta nan zaa ganka kana cika kana batsewa."
"Toh Yaya yanzu rayuwar ta zama sai kayi karatun ai."
"Namiji yayi mace ma sai ace dole sai tayi? Dakin mijinku be fi muku bane wai ni?"
"Yaya karatun yafi."
"Tafi chan, aure shine birgewar mace ba ta zauna gande-gande ba a gaban iyayen ta, yanzu ji Safiya da Umaimatu dan Allah, ga Maryama gaki ga takwara, wannan ai shirme ne."
"Zamuyi ai Yaya, daga baya idan mun fara jami'ar"
"Lallai ashe zaa yi fada dani kuwa, ko naji kauye wallahi na samo muku mazaje duk na hada ku dasu naga karyar bokon."
Rufe bakin ta, tayi taba dariya, sannan tace
"Ya hakuri Yaya, zamuyi fa."
"Ko fa mashinshini baku dashi fa, wannan wanne irin abu ne? Ko wannan gattin banzan da aka zuba a waje ne yake bawa mazan tsoron zuwa su kulaku ne ni Hajara?"
Sai ta hau tafa hannu tana salallami,
"Ba zai yiwu ba wallahi, dole a sake sabon zama,ko za'a yi karatun dole kowacce ta kama miji a hannu, ba zan lamunci wannan sakarcin ba."
"Toh Yayah."
Tace tana cigaba da dariya dan ita bata ga abin ta da hankali ba, bama ta wannan tunanin ita sam wallahi, shiyasa ma bata dauki maganganun Yayan da wani muhimmanci ba.
Kiran ta Usman yazo yayi yace tazo Safeera tazo,ta tashi da sauri dan bata yi tsammanin zuwan ta ba, Yaya na mata magana bata ji ba tayi gaba kawai. Da saurin ta, ta shiga falon tana kiran sunan ta, sai ta tsaya chak ganin mutum a zaune a falon jikin sa sanye da shadda fara kal, yayi kyau sai taga baki daya ya sauya mata kamar bashi ba, fuskar sa ta kalla sai taga kamar ta kara haske akan dah,
"Ya Isma'il?" Tace tana karasowa dan bata ga Safeeran ba, ta bayan ta tayi tsalle ta dane ta, wanda ta kusa kaita kasa, suka kwashe da dariya gaba daya
"Na zata fa ba dake akazo ba."
Tace bayan ta saketa
"Ni da Ya Isma'il ne, suprise visit mukayi miki tunda aka gama examz shiru."
"Wallahi, duk ba dadi zaman."
"Ina wuni ya Isma'il."
"Lafiya lou, kina lafiya?" Yace yana dan zamowa daga jikin kujerar zuwa gaba
"Ina aunty? Tasan kunzo?"
"Eh ta shiga ciki, magana ce ta kawo mu Jidda ni da yayana."
"Toh... Zauna bari na kawo muku ruwa."
"Kyale shi, ki zauna bari naje na dauko."
Tace tana zamewa ta barsu su biyu. Shafa kansa yayi jidda ta kalle shi sai tayi saurin dauke idanun ta ganin yadda yake kallon ta, ta dade da sanin yana mata irin wannan kallon amma bata taba kawo wani abu ba, amma a yau sai taga kallon nasa yayi mata nauyin da taji duk ta takura.
"Jiddaaa."
Ya kira sunan ta cikin jan sunan wanda ya sakata dagowa ta dan kalle shi sannan ta yi saurin dauke idonta ta amsa a chan ciki kirjin ta na bugawa kamar wadda tayi tsere, tana tsoron duk abinda zai fito daga bakin sa
"Kiyi hakuri da abinda zan fada miki jiddah, ban zo ba sai da na nemi izinin Aunty, ta bani damar zuwa na fada miki abinda yake Raina.."
"Jidda na jima ina sonki, so me karfin gaske, tun ranar da na dora idona akanki ban kara samun nutsuwa ba, komai nake kece Jiddah, ina sonki fiye da yadda nake son kaina, ke din nake so Jidda, ba wani abu da kike dashi ko kika mallaka ba."
Wani gingirim taji a kanta, taji yayi mata nauyin da taji tamkar an dora mata gaba daya nauyin Nigeria akan ta, wani irin yanayi ta riski kanta wanda bata taba tunani ko hasashe ba, me zata ce masa? Ba zata iya cewa bata son shi ba ko dan Safeera, ko dan kaunar da suke nuna mata, sai dai bata jin ko digon sansa a ranta, bata jin zata so shi, ba kuma dan bashi da qualities din ba, ba kuma dan be hadu ba, bata taba kawo saurayi me jini a jiki da hutu kamar Isma'il zai sota ba ma, ba ajin sa bace ita, yafi ta komai da komai amma ya sauke kansa yake fada mata kalmar soyayya."
"Dan Allah Jidda karki ce min a ah, zuciya ta ba zata iya dauka ba, dan Allah."
Bakin ta ne ya sarke, ta shiga tari babu kakkautawa, duk ya rikice ya shiga kiran Safeera, da sauri ta fito ganin jidda na tari ta koma ta kawo ruwa ta bata tasha sannan tarin ya tsaya. Kallon ta yake yana daga tsaye yaki zama saboda yadda ya rikice,sai da ya tabbatar ta dawo daidai sannan ya zauna yana jan ajiyar zuciya.
[03/10, 21:27] Mss Xoxo: ❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [05/10, 16:20] Billyn Abdul 2: *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
**
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*
5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (17)
***Shiru ne ya biyo bayan zaman, kowa da abinda yake sak'awa a ransa. Safeera ce ta gaji da shirun ta mike
"Ya Isma'il muje sai muyi waya ko Jidda?"
Gid'a mata kai jidda tayi, tana kallon Safeera taje tayi wa Aunty sallama tazo suka fice ita dashi tana zaune kamar wadda aka dasa a wajen. Aunty ce ta fito ta sameta a zaune a wajen kamar wadda aka ce karta motsa daga wajen, kunyar Auntyn ce ta lullube ta, ga wani irin yanayi da take ciki me wahalar fassarawa
"Jidda ba dai korar su kikayi ba ko?"
Girgiza kanta tayi sannan tace
"A ah Aunty."
"Toh ya akayi? Bani labari."
Dariya ta bawa Jiddan yadda ta zauna tana kallon ta, tana jiran ta bata labari
"Ni suka fara samu da maganar jiddah, da farko ma mamaki nayi a tunani na Ismail yafi karfin ki, ban taba kawo hakan ko a hasashe na ba, kina ganin zan bari wannan babbar damar ta wuce mu?"
"A ah." Tace a sanyaye
"Shiyasa na bashi dama kuyi magana duk da nasan halin ki, ba lallai ma ki bashi wannan damar ba."
"Uhum."
"Muyi addu'a mu nemi zaɓin Allah, idan da alkhairi Allah ya tabbatar mana."
A ciki ta amsa, ta tashi ta shiga ciki dan tana bukatar zama ita kadai tayi tunani sosai.
***Tun bayan tafiyar su aunty take jujjuya maganar a ranta ta rasa Wanda zata fadawa, a yau take saka ran zuwa Baban, weekends yake zuwa Kano sai yayi kwana biyar a Abuja, ta gama duk abinda zatayi tunda tasan ko yazo ma sai ya gama da mutanen sa a waje sannan yake shigowa ciki, jidda tayi kulewar ta a daki yan miskilancin sun motsa sai ta kyale ta tayi nazarin abun sosai. Yanke shawarar zuwa wajen Yaya tayi kawai ta rage zaman kadaitar, ta yafa mayafin ta ta nufi shashen Yayan, ta sameta a zaune ita da aabu suna zare ganyen zogale daga jikin sa, sa hannu tayi aka cigaba tare da ita suna hira har aka gama tas abu ta dauka ta tafi kicin ta dafa mata. Fitar abun ya saka Auntyn yin shiru tana tunanin sanarwa Yayan abinda yake faruwa da yake ya nukurkusar zuciyar ta, yanke shawarar sanar da Yayan tayi kawai dan idan abu na cin ka idan baka fada ba baka taba jin dadi.
"Yaya kin gane kawar Jidda Safeera ko?"
"Na gane ta, bikin ta yazo ne?"
"A ah, su ai yan boko ne Yaya."
"Ai sai ayi tayi dai, yaran nan jiran Alhaji nake yazo ayi wacce za'a yi, ko zasuyi karatu sai sun fara fidda miji, dazu muna maganar da jiddah dariya ma ta mayar da abun."
"Gaskiya ne yaya."
"Toh Allah,zaka bar zagada-zagadan yan mata ne a gabanka haka? Wannan ai shirme ne."
"Ita Jidda dama maganar da zan miki kenan, Yayan kawarta ta, Ismail yazo yace yana son ta."
Da sauri Yayan ta kalle ta kamar bata shirya jin hakan ba, kamar kuma ba ita ke maganar a samu miji yanzu ba
"Ita Jiddan ce tace yazo?"
" A'ah, shine dai ya sameni da maganar, shine nace bari na fara fada miki."
"Toh ita Jiddan tana son shi ne?"
"Wallahi Yaya ban sani ba, amma dai kinga yadda suka shaku da kanwar sa, kuma suna son Jiddah sosai har mahaifiyar su wallahi, shiyasa nayi mata sha'awar shi."
Shiru Yaya tayi, ta bata fuska nan da nan tayi kicin kicin, hakan ya bawa Aunty mamaki ta rasa dalilin hakan daga Yayan, kasa hakuri tayi tace
"Baki ce komai ba Yaya."
"Toh me zance? In dai tana so kuma an tabbatar da halin sa ai shikenan."
Shiru duk sukayi, ganin kamar ran Yayan ya baci sosai ya saka Auntyn tashi ta tafi, tana fita Yayan ta mike itam
"Ai ba zata sabu ba wallahi, gida be koshi ba a kai dawa, yarinya me hankalin zan bari ta kubce mana ina, bari ubansu yazo."
A fili take maganar tana tsaye, sai ga Fauwaz kamar wanda aka jeho hannun sa rike da ledar wayar Jidda da Baba ya siya musu ita da amira na gama school, sai kuma sakon snacks da Mama ta bayar a kawo ma Yayan. Tafiya yayi da dan sassarfa kamar zai rungume Yayan ta goge tana dariya
"Shakiyin banza, shakiyin wofi, rungume ni fa zakayi da ko?"
"Eh wai irin na turawa ba, irin nayi missing din nan naki."
"Allah ya shirye ka kaji, zuwan Kenan?"
"Wallahi Yaya, zuwan kenan dan Baba ma ya tsaya wani meeting ga wata gaisuwa da zasu kawai nayi gaba dan na matsu naga my heart beat."
Ya tallafe zuciyar sa, bugu ta kai masa ya zille yana kyalkyala dariya
"Zo ka zauna dama neman wanda zan fadawa damuwa ta nake sai gaka."
"Faduwa tazo daidai da zama, ga sakon ki inji Hajiya Mama, part din ki kuma ya kusa kammaluwa na daina missing dinki."
"Toh ajiye nan tukunna, an gode."
Ajiyewa yayi ya zauna, itama ta zauna tana tattaro hankalin ta waje daya kana gani kasan magana zatayi me muhimmanci
"Ya labarin Yayan ku?"
"Lafiya kalou, ya gama ai har ya fara training, kinsan wasu awowi ake so ka hada kafin ka zama babban matukin jirgi."
"Shi kuma abin da ya dame shi kenan, saboda tsabar rashin son mutane shine ya zabi bangaren da ba zai dinga zama ba kenan koyaushe yana sama kamar tsuntsu."
"Da dadi fa Yaya, babban aiki ne."
"Kai ka sani, ni ba wannan ba, zaka iya kira min shi yanzu?"
"Yanzu nasan baya kusa dan dazu muna magana ma ya kashe zai kirani."
"Toh shikenan, wai kuwa yana da budurwa ni Hajara?"
"Tab! Ba dai Ya Tariq ba, karatun ya saka a gaba idan fa ba gani yayi ya karbi cert dinsa a hannu ba, toh fa ba zai nutsu ba, yana da naci duk abinda yasa a gaba."
"Toh Masha Allah, wani tunani nayi. Zan je takanas na roka masa auren Jidda a wajen mahaifin ta."
"Jidda kuma Yaya?"
"Ita, dan Malamin da ya bashi rubutu ya fada min, idan aka basshi haka sakaka toh ko auren ma ba zai ba, haka zai kare rayuwar sa, ni kuma sai na duba kaf dangi babu me halin Jidda, ita kadai zata iya taimaka mana ta rufa mana asiri."
"Amma Yaya Jiddah fa, da Ya Tariq?"
"Menene a ciki?"
"Ba komai, amma a fara jin ta bakin ta kar ayi mata dole."
"In sha Allahu ma babu wata matsala, ina ji a raina zasuyi rayuwar aure ingantacciya."
"Toh yanzu ta yaya hakan zata kasance?"
"Ni dai kai zaka taimaka min, ka sami Jiddah da maganar naga kuna shiri sosai, ni kuma zan fadawa Baban KU."
"Toh Ya Tariq din fa?"
"Karka fada masa, irin matsalar sa ai baa fada musu sai dai kawai ayi dan aka daka ta tasu wallahi ba za'a yi ba."
"Auren dole kenan za'a masa."
"Dallah ana kaika."