Sanadin labarina complete novel - Chapter 7
Sanadin labarina complete novel Chapter 7: Sanadin labarina complete novel Chapter 7. ***Kwanan sa hudu yana avoiding yarinyar, ta shiga rayuwar sa sosai…
4,412 words
***Kwanan sa hudu yana avoiding yarinyar, ta shiga rayuwar sa sosai komai yake ko ina yake sai ta bishi, gashi shi mutum ne da baya son a shiga rayuwar sa idan har ba shine ya gayyato mutum ba. Nacin ta shi yafi komai damun sa gashi sam bata da zuciya duk yadda ya kai da nuna mata baya son yadda take bin sa amma bata ganewa, shi ko sunan ta be sani ba sai ranar da ta fada masa da kanta, daga ranar be kuma sake tuna sunan nata ba ya manta. Zaman sa ya cigaba da yi a daki duk da yana da lectures amma baya son ya fita su hadu shiyasa ya hakura ya zauna yana bin lecture din online yana following komai, baya so ko kadan ya dauke idanun sa daga kan system din baki daya ya tattara hankalin sa waje daya yana yi yana jotting down key words din. Door bell dinsa ce tayi kara alamun yana da bako, ya daga kai ya kalli agogon dake makale a saman table din nasa, be san wanda zai kawo masa ziyara a irin wannan lokacin ba, duk da yasan bazai wuce Ishaq ko xuo kaiy ba, amma kuma ya san suna class a wannan lokacin kuma babu abinda zai fito dasu, sake kad'a bell din akayi, ya tashi yana jan siririn tsaki, ya shiga takawa kafarsa sanye da white socks zuwa kofar dake gaban dan corridor kafin main cikin gidan. Budewa yayi ya kalleta cike da mamakin ganin ta, basket ne a hannun ta me kyau, ta sakar masa murmushi ya dan saki fuskar sa kadan yana tsaye still akan kofar
"Zan iya shigowa?" Tace tana kallon cikin gidan, da sauri ya girgiza mata kai
"Ba zan iya ba?"
"Eh." Yace kai tsaye, dan jim tayi a tsaye, shima ya cigaba da tsayawa a wajen sai tayi murmushi ta mika masa basket din
"Lunch nayi maka naga baka fita school ba"
Sai ta mika masa ya miko hannun sa ya zai karba hannun su ya hadu da na juna, da sauri ya janye yana bata fuska saura kadan basket din ya fadi abinda yayi matukar bata mamaki.
"Shikenan?" Yace yana rike da basket din a kaikaice, kasa magana tayi dan tsabar takaici, ta daga masa kai alamar eh
"Ok, thank you."
Yace ya juya rike da basket din, ya tura kofar sa ya barta a tsaye a wajen kamar wadda aka dasa saboda tsabar mamakin sa. Kusan minti biyar ta dauka a tsaye a wajen ta gaza aiwatar da komai, kafin daga bisani cikin yanayi na bacin rai ta bar wajen fuuuu.
A gaban kofar ya dire basket din, yai gaba abinda ko budewa be yi ba bare yaga abinda yake cika.
[03/10, 21:28] Mamuh: _ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_* _MamuhGee_
*_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_* _Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_*
_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_
_4 BOOKS 4500_ _3 BOOKS : 3500_ _2 BOOKS : 2500_ _1 BOOK: 1500_
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇 09134848107 [05/10, 16:20] Billyn Abdul 2: *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*
5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (15)
***Shiru yayi bayan ya ajiye wayar, mamakin sa na karuwa idan ya tuna yanayin yarinyar, tsaki yaja ya mike ya rasa dalilin da yasa shi damuwa da al'amarin ta har haka, ya kuma rasa dalilin da duk lokacin da ya ganta sai ya ji duk maganar dake dauke akan harshen sa ta dauke. Tsaki ya sake ja a karo na biyu yana dan murza saman goshin sa. Tunawa yayi da abinda yake kafin shigowar wayar, kashe datar sa yayi dan kar a sake damun sa ya cigaba da duba takardun sa har zuwa lokacin da yaji ya gaji sosai sannan ya hakura. ID card dinsa ya dauka da wayar hannun sa ya fito, ya bi ta wajen office din masu apartment dinsu da suke zama kullum Monday to Friday, jinin su ya hadu da ogan dan sosai yake son shi suna ganin shi suke fara murna shiyasa yake yawan tsayawa idan zai fita su gaisa. Ogan ne yau shi kadai a office din yana duba sabbin washing machines din da za'a kawo. Daga jikin kofar ya dan yi knocking, ya taso da sauri
"Hello James."
"Hello Tariq, please come in." Yace yana nuna masa ciki
"No thank you, just want to check on you, i'm on my way."
"Ohh, not bad."
"I'll see you later."
"Ok Tariq, i sent you an email, see ya."
"Ok , bye."
Wayar sa ya bude ya shiga mail dinsa, sai yaga wai ashe gift card ne me dauke da £80 suka bashi a matsayin lucky winner na duk yan gidan da suke bayarwa duk karshen wata, murmushi yayi kawai ya maida masa reply da
"Thank you, I hope it's not cheating."
Dariya James yayi dan da gaske cheating din ne, wata baturiya ce taci dan shi Tariq ko participating be yi ba amma ya bashi, reply yayi masa
"It's cheating bro. Lol😅"
Murmushi Tariq din ya sake yi kawai, ya maida wayar yana kara sauri akan tafiyar da yake a dah. A dan garden din cikin school din ya hangi Yasmin suna zaune da wani dan kasar ghana, so close kamar zasu shiga jikin juna, tabe baki yayi yazo zai wuce su ta tashi da sauri tana kiran sa
"Tariq please ka tsaya."
Dan rage tafiyar yayi har ta daidaita dashi, yaki kallon ta suka cigaba da jerawa har zuwa cikin building din, I'd card dinsa ya ciro yasa a kofar itama tasa nata suka shiga still be kalle ta ba suna dai tafiya a tare, sai da yazo in da yake son kaiwa sannan ya ja ya tsaya yana mata kallon me faru?
"Please magana nake so muyi."
"Ina jinki."
Yayi folding hannun sa a kirji ya jingina da bangon wajen
"I want us to be friends, pleaseeee."
"Kin taba ganin friendship mace da namiji?" Yace yana kallon ta
"Na'am?"
"Yes, kin taba gani?"
"Sosai, ina da friends both maza da mata, and I see nothing wrong with it."
"Ok, ni I'm exceptionally different, bana friendship da other gender, it's haram in Islam, sorry."
Yayi gaba abin sa ya barta a tsaye cike da takaicin wulakancin sa, juyawa tayi taga babu kowa a wajen sai su biyu, ta yi saurin barin wajen tana jin kamar ta kwala ihu, bata taba ganin dan rainin hankali irinsa ba, but ba zatayi given up ba zata cigaba da gwada sa'ar ta.
***Kanwar Yaya ce wadda ake kira da Gwaggo tazo dan taya Yayan murnar Baba ta kuma yi kwana biyu, halin su daya sak da ita da Yayan wajen surutun su, sai dai ita tafi Yaya sauki wajen fada dan Yaya akwai masifa bata ragawa kowa duk girman ka sai dai idan baka tabo ta ba. Kwanan su Mama biyar suka dawo suka bar Baba achan, a ranar kaf yan uwan Mama suka zo taya ta murna, tamkar ana shagalin biki haka aka taru Yan uwan da abokan arziki aka ci aka sha. Aunty da jidda suna bangaren Yaya anan suke nasu zaman su isu dan basu da hurmin shigarwa Maman abu. Amira ce ta kawo abinci a yar madaidaciyar kula inji Aunty Mimi tace a kawo ma Auntyn, sai kuma na Yaya shima daban.
"Zo muje part dinmu, su salma sunzo duk muna dakin mu."
Amira tace wa Jidda, kallon Aunty jidda tayi alamun taje? Ta daga mata kai dan ba zata iya hanata ba dan ita tun dama chan bata taba hanata zuwa ba ita dai Jiddan ce bata so,. Tashi tayi ba ason ranta ba dan dai kawai kar Amiran taji babu dadi ne shiyasa. Ta bita suka shiga part din nasu. Duk suna zazzaune a falon an baje ana ta hira suka shigo sai duk suka bi Jiddan da kallo, aunty Mimi ce tace
"Amira kawarki ce tazo?"
"A ah Jidda ce fa, ta gidan nan."
"Ku wuce malama."
Mama tace tana bata rai,
"Wacece?" Suka tambayi Maman bayan su jiddan sun wuce ciki
"Yarinyar chan ce ta dauko ta, yar brother dinta ce daga kauye."
"Inyee samun waje tusar asuba."
Aunty Nafi tace tana rike haba
"Tubarkallah Masha Allah, me kyau da ita wallahi."
Aunty Mimi tace tana kokarin dauke maganar Nafin
"Ai ke Mimi bansan wacce irin zuciya ce dake ba, har wani kod'a kyawunta kike a gaban Yaya."
"Toh laifi ne Ya Nafy? Ni fa ban ga abin tada hankali ba anan, beside har yanzu fa Ya Aisha ce a sama wajen his excellency, ko wannan kadai ya isa ai mutum ya hakura, wasu in sun yi auren ai wulakanta da gida suke, amma kiga fa ko tafiya Abujan nan Mama ce fa zata koma, tsakani da Allah mu ajiye son zuciya muyi maganar Allah, menene laifin Halima?"
"Mimi bana son maganar nan dan Allah, a barta ranar farin ciki ce bana son abinda zai bata min rai."
Mama tace tana mikewa
"Nayi shiru." Ta rufe bakin ta, tabe baki sauran sukayi dan duk basa goyon bayan Anty Mimi kawai dan dai babu me ce mata komai kowa yana respecting dinta dan kaf gidansu babu kamar ta a kirki da son yan uwanta.
***Duk suna zazzaune wasu na danna waya wasu kuma na hira Amira ta shigo tare da jiddah,
"Maryam yau ga jidda na sakata shigowar dole."
"Kai Amira da kai na fa nace zan biyo ki."
"Ban yarda ba wallahi." Umaima tace tana dariya
"Wace ita?"
Salma da tun shigowar ta taji sam yarinyar batayi mata ba, in dai taga wadda ta fita kyau a waje sai kawai taji tana jin haushin ta, tafi so duk in da taje ta zama ontop
"Jidda ce, yar gidan Auntyn mu ce."
"Daga kauye take kenan." Tace tana dariya
"Salma." Ya Safiyya dake gefe tana chatting tace tana bata fuska
"Bana son irin wannan maganar, jiddah shigo ki zauna."
Ta dora tana yi wa jiddan murmushi abinda yayi matukar daure mata kai, toh ko dan dama bata cika magana bane shiyasa Jiddan ta zata ko bata da kirki ne? Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Maryam, sai Salma ta tashi fuuuu ta fice daga dakin.
"Yarinyar nan bata da hankali, amma zan yi maganin ta."
Safiyya tace tana mikewa, ta bar musu dakin ya rage daga Jidda, Amira, Umaima, Maryam sai yar gidan Aunty Mimi Nu'ayma. Sukayi zaman su har jiddah ta saki jikinta sosai dan dama Salma ce tasa ta darare da farko, tare suka ci abinci a dakin sukayi zaman su har lokacin tafiyar su Nu'ayma yayi Salma ta shigo tana kumbure-kumbure tace tazo su tafi. Biyo ta sukayi ya rage saura jidda a dakin tayi zaman ta, suna fita suka ji Aunty Nafi na fada
"Akan wata bare Safiyya zata wulakanta yar uwarta yanzu Ya Aisha"
"Kiyi hakuri zamuyi magana, duk wannan ba abin tada hankali bane dan Allah."
Mama da bata cika son irin wannan abubuwan ba, ta fada tana kallon gefen da Safiyya take akan dinning tana duba wata magazine kamar ba da ita ake ba. Ashe biyo Salman tayi ta rar rankwashe mata kai tace kuma kar ta sake musu irin haka, shine harda kukan ta, ta fadawa uwarta shine ita kuma taji haushi take ta banbami.
***Babban Album jidda ta hango akan wata akwati, ta tashi ta dauko ta bude ta fara kalla, hotunan su ne tun suna yara zuwa girman su, sosai wasu hotunan suka bata dariya, ta dinga dariya tana kalla, har tazo kan hotunan Ya Fauwaz da Ya Tariq, tsayawa tayi tana kallon hoton idanun ta akan sa, fuskar sa kamar sanda yazo part din Antyn a duk hotunan, kamar dole akayi masa baya so. Taba kofar dakin taji anyi, ta tsaya da abinda take tana kallon kofar, turo kofar Safiyya tayi ta shigo tana kallon hannun Jiddan
"Kina ciki dama jiddah?" Tace tana zama daga gefen ta, cikin rashin sakewa Jiddan tace
"Ina ciki hotuna nake kalla."
"Kin ganmu muna yara kanana ko?" Tace tana murmushi
"Amira duk tafi bani dariya."
"Ai Amira muguwar mummuna ce taana yarinya, ni da Ya Tariq ne kawai dama masu kyau."
"Gaskiya."
Tace tsakanin ta da Allah dan safiyyan kamar su daya da Tariq din hatta yanayin shirun su da yadda suke magana.
"Bari kiga sabon Album din kwanan nan." Ta tashi ta dauko mata sabon da suka yi ranar graduation din ta, ta dora akan kafar jiddan ta bud'e mata
Shine a farkon page yana sanye da dogon jeans da farar t-shirt, fuskar sa sake yayi murmushi wanda yayi matukar yi masa kyau,
"Dama yana murmushi?" Ta samu kanta da tambaya
"Kai sosai ma, sai dai ba kowa yake ma ba, wannan ma ni na saka shi yi wallahi."
Bata ce komai ba, ta bude next page ta cigaba da kalla, kusan dukka hotunan su ne shi da Safiyya, sai wanda Safiyyan da su Amira amma nasa yafi yawa. Hotunan sun yi kyau dukka kamar zaka yi musu magana su amsa ta ciki dan yadda ya dauku sosai.
Dawowa sukayi daga rakasu suka tarar da jiddan tana kallon hotunan suka zauna aka cigaba da kalla tare ana tuna baya,wanda zaa yi dariya ayi
"Kinga na Ya Tariq yana karami?" Maryam tace tana dariya
"A ah." Ta girgiza kai
"Ya Sofy ina album din Ya Tariq dan Allah."
"Salon kuyi masa dariya,ajiya ya bani ba zan baku ba."
"Dan Allah jidda ce zata gani, Yaya boss yana karami."
"Noo ba zan ci amana ba."
"Jidda kice kinaso ki kalla zata dauko, musha dariya"
" A'ah kar a dauko ni dai ba ruwana."
"Kin kwafsa, da mun sha kallo wallahi."
"Dan dai baya nan ne, kunsan da baku isa ba wallahi."
Ya Safiyya tace tana dariya, abinda ya sake bama jiddah mamaki ganin yadda ta sake tare dasu kamar ba ita ba.
Har bayan magriba tana wajensu,dan ji tayi ma kamar tayi ta zama a chan yadda taji dadin yinin ranar. Sai da Aunty ta turo tazo sannan suka rankaya tare da Amira suka koma wajen aunty, basu ga Mama a falo ba kamar ma bata nan dai.
***Kwana biyu Baba ya kara ya dawo cikin rakiyar mutane da yawa, a hanya sukayi magana da Tariq dan tun ranar be samu kansa ba, tare yake da sababbin masu kula dashi DSS har su hudu, sai wasu motocin, dole zaman sa a unguwar ba zai yiwu ba musamman yanayin aiki dole ya zama yana kusa da Mr President sannan kuma da yanayin yadda kasar ta zama dole yanzu sai an samu wadanda zasu zauna da family dinsa su kula dasu kafin ya tattara su dukka su koma chan saboda security purpose. Gidan a cike yake taf, Baffa da Iya Lami sunzo duk da be so tahowa da ita ba amma ta nace a dole sai tazo ba yadda ya iya suka taho tare har da Innar su Saude da Sauden, duk sun zo taya Aunty murnaz Baffa kuma Baba. Kafin isowar Baban gidan ya cika ba masaka tsinke hatta bangaren Yaya a cike yake da yan uwanta da na Malam, Mama ma wajen ta aciken yake da kawaye da yan uwa. Mom din su Safeera ma tazo da kanwar Daddy da Safeeraan. Aunty ce fa gayyato su duk dai dan itama bangaren ta kar ya zama babu kowa tunda su ba yawa ne dasu ba, ba kuma ta san mutanen anan din ba Duk girke-girken da akayi Mama ce ta saka akayi order ta fitar ma da Yaya na part din ta haka ma aunty sannan ta bar nata a wajenta. Ta shirya cikin shiga ta alfarma wadda tayi bala'in karbar zubi da tsarin ta, dama Mama yar gayu ce tun da bare yanzu da likafa ta daga ta zama matar minister wadda take jin a yanzu ne tayi daidai da level dinta. Itama Aunty tayi shigar ta daidai da ita tayi kyau kuma abinka da dama chan kyayyawa ce sai ta fito fes sosai. Iya Lami tana ta zak'ewa a wajen Auntyn duk da taki yarda sam da ita, Jiddah kuwa daga gaisuwa ko kallon ta bata sake yi ba, tayi zaman ta a daki ita da Safeera. Part din Yaya, Baban ya fara shiga kamar yadda ya saba ya gaggaisa da mutane. Yaya kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha, dan farin ciki. Daga nan ya shiga wajen Mama itama da nata mutanen suka gaisa sukayi masa Allah ya sanya alkhairi, sannan ya shiga wajen Aunty a karshe. Daga nan ya dawo wajen su Baffa da aka saka rumfa a harabar gidan suna zazzaune a wajen. [11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (14)
***Da sauri ya karasa gaban table din,ya zauna yana jawo system din, ya cigaba da bin lectures din har zuwa sanda malamin ya gama, ya zare headphone din dake kunnen sa ya mike ya tattare komai ya ajiye a gefe ya kashe system din ya zare flash din dake makale a jiki, ya nufi wajen da kayansa suke ya dauko dambun naman da ya taho dashi ya ajiye sannan ya samo chilled juice ya hada ya zauna yana ci yana browsing a wayar sa. Ya dade a zaune a wajen har lokacin sallah yayi, ya mike bayan ya zare socks din dake kafarsa ya nufi toilet yayi alwala ya fito ya wuce zuwa dan madaidacin masallacin da yake kusa da apartment din nasu, yana cikin dalilin da ya sakashi karbar apartment din saboda kasancewar masallacin da yake kusa da wajen, baya taba missing sallah duk da ba wai ana kiran sallar bane amma kuma yana amfani da wayar sa yaga time din idan yayi yaje yayi sallar. Ajiye takalmin sa yayi a cikin wasu lockers sannan ya dauki wani na shiga cikin masallacin ya saka ya haura sama in da ake sallah, ka'idar su ce baa cika cikin main building din da takalmi sai dai ka ajiye shi a farkon shigowa in da aka tanadi lockers masu kyau kowa ya ajiye nasa a wajen tunda ba wai yawa ne dasu ba, Ishaq ya hango a gaban sahu ya karasa kusa dashi sukayi sallar sannan suka fito a tare, anan yake tambayar sa abinda ya hanashi zuwa lectures yau, shafa kansa yayi kafin yace
"Haka nan naji bana so fita yau."
"Manyan kwari dama ai haka ne, ko basu yi attending class ba lafiya lou."
"Ba wani, kuma ma nayi following online, banbancin mu kawai zama a class din ne."
"Eh haka Mr David yace, kayi joining class din tun daga farko."
"Eh." Yace suna cigaba da tafiya.
"I'm hungry wallahi, ko kana da wani abun naci?"
"Muje ba za'a rasa ba ai."
Yace sanda suke haura stairs din maimakon lift, ba ko yaushe yake bin lift din ba musamman idan ranar be wani yi exercise sosai ba sai ya hau stairs din kawai ko ba komai ya motsa jinin sa.
"Da lift da komai amma ka bamu wahala,."
"Ka motsa jini ai."
"Duk wanda nake yi kullum."
"Ka kara wani." Yace yana manna card dinsa a jikin kofar, ta bude suka shiga ciki, kallon basket din Ishaq yayi kafin yace
"Wannan fa?" Ya nuna basket din
Tabe baki yayi kafin yace
"Yarinyar nan ce ta kawo."
"Yasmin?"
"Oh eh ita."
"Wai kace nazo adaidai, har abinci take kawo maka kenan."
Juyowa yayi da sauri ya harare shi
"This is the first and last time, nasan ba zata sake iyayin kawowa ba."
"Baka da kirki sam, yarinyar nan fa she's serious akan ka."
"She's not my type."
"Then wace type dinka? Kowacce kace she's not your type, sai ka fada mana type din naka muji ai."
Zura mishi ido yayi, be ce komai ba kawai ya girgiza kai
"Ehen ina jinka, fadi muji type dinka."
"Ok, since you insist."
"Ina ji?"
Ya bude basket din ya shiga fito da kayan dadin da Yasmin ta aiko yana jin kamar an sashi a aljanna, ko kallo basu ishi Tariq ba, ya kishingid'a akan couch din dakin yana yin kasa sosai da idanun sa
"I'm all ears."
Hannun sa ya ware kamar me shirin lissafi yace
"Bana son mace ta cika rama da yawa haka kuma bana son tayi kiba."
"Yasmin is average.".
"That's not all."
"Ok ina jinka "
"I want a shy girl, me kunya sosai bana son wadda idanunta suke a bude,bana son yarinyar da zata ce tana so na, nafi son yarinyar da zata zama very very hard to get, bana son cheap girl"
"Ehen."
"Very beautiful with a soft and long hair, me addini sosai, mara son yawan magana da hayaniya, wadda ta iya girki me dadi...."
"Allahu Akbar."
Ishaq yace yana tura lomar chicken biryani
"Allah ya cika maka burin ka, amma fa banda hard to get din nan, dan za'a iya samun matsala."
"Haka nake so ba wata matsala."
"Toh Allah yabada sa'a Capt."
"Amin." Yace yaja bakin sa yayi shiru dan dama ba kasafai ya fiya doguwar hira ba idan ba da Ishaq din ba. Kallon sa ya dinga yi har ya gama cinye abincin tas ya sha ruwa yayi hamdalah sannan yazo suka shiga karatu wanda yawanci Tariq din ne yake guiding dinsa a duk abinda be gane ba, ya bala'in iya mathematics da physics shiyasa ma ya zabi bangaren aviation yana so ya gama yayi training din zama pilot in two years ya hada 1500 hours ya samu Airline transport pilot certificate. Target din shi kenan, kuma ya dauko hanyar cimma shi. Sai dare sosai ya kwanta bayan sun gama karatun Ishaq din ya tafi.
***Sabon part din da Baba ya siya aka soma ginawa wanda ginin yake sauri sosai, duk da cikin gidan aka shigo da ginin amma zai zama basu da wata alaka kowa zata zama tana bangaren ta. Mama ce zata koma sabon part din kowa ma yasan wannan, Aunty bata damu ba sam, tunda itama part din Maman za'a gyare mata a hade da main falon duk cikin nata, sai kuma a bawa su Fauwaz part din Auntyn. Sosai ginin yake sauri dan Baba so yake a gama da wuri Mama takoma a kalla ya san hakan zai rage wata matsalar. Suna zaune tare da Malam Nura da Alhaji Adamu a harabar gidan, aka kira Baba a waya, ya daga ganin number ce ta PA din Mr President wanda ya kasance class mate din sa ne, tunda ya zama shugaban kasa yake kokarin jawo Baba jikin sa amma sam Baban yaki yarda har sai da ya gamsu dari-bisa dari da yanayi da tsarin mulkin nasa sannan ya amince har aka saka sunan sa a cikin sababbin ministocin da za'a nada, babu wanda Baban ya fad'awa ya dai ce musu zai shiga siyasa su taya shi da addu'a. Daga wayar yayi suka gaisa sannan yace an aiko masa da invitation ta email sannan an yi masa booking flight zuwa Abuja a ranar shima an tura masa e-ticket din. Tashi Baban yayi bayan ya sanar dasu dalilin wayar sukayi masa fatan alkhairi sannan ya shiga gida. Wajen Yaya ya wuce kai tsaye ya sameta da maganar. Rawa ta shiga takawa cikin farin ciki, dariya Baban ya dinga yi har sai da tayi rawar ta gama sannan tace
"Allah ya tabbatar da alkhairi,ya bada sa'a, ya raba ku da sharrin makiya ya baku ikon sauke nauyin da aka dora muku."
"Amin Yayah, Amin ya Allah. Adduar kenan."
Daga nan ya wuce cikin gida ya kira Aunty da Mama zuwa falon sa ya sanar dasu, tashi Mama tayi ta rungume shi da sauri saboda tsabar mamakin maganar, minister fa? Baban matsayi ne sosai wanda yayi daidai da ita, ya kuma dace sosai da ita. Murmushi kawai Aunty take duk kunya ta kamata, sai da Mamaan ta sake shi sannan Aunty tayi masa Allah ya sanya alkhairi. Ya amsa ya saka musu albarka gaba daya, sannan yace Mama ta hada masa kayan da zai tafi dasu kasancewar ita ke girki ranar, dakin sa ta shiga ta barsu su biyu, ya nuna mata kusa dashi yace ta dawo, ta koma ta zauna ya kalle
"Har yanzu akwai abinda yake damunki ko?"
Girgiza masa kai tayi,
"Babu komai."
"Gobe Safwan ya kaiki asibiti a sake duba ki a duba bp dinki, ban yarda da yanayin ki ba."
"Allah ba komai."
"Toh shikenan, in sha Allah kafin na dawo zaa yi kokarin a gama gyara gidan nan, sai kuyi min duk list din abubuwan da zaku bukata, duk da nasan yanzu zaman namu anan ba zai dade ba, amma dai bari muga abinda Allah zai yi."
"Allah ya taimaka ya bada sa'a."