Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 1
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 1: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,410 words
[12/14, 10:03 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
*MABUƊI*
*Ina me farawa da godia ga Allah subhanahu wata'ala,da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna asama,ina roƙo ubangiji yayi riƙo da hannuna wajen rubuta dai-dai,ya kuma yafe kusakuran da zasu iya kasancewa aciki Ameen.*
*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da wannnan littafin gaba ɗayansa zuwa ga duk wata me nakasa,especially masu matsala irin na TAIMIYYAH,ina roƙo ubangiji yasa nakasan ta zame muku alkhairy da ɗaukaka a rayuwa.*
*Page 1*
Matashiyan budurwace kwance ƙudundune cikin bargo,jikinta na faman kakkarwa alamun zazzaɓi ne yai mata kamun me kyau,daga gefenta wata dattijuwa ce wacce shekarunta ya fara nisa sosai,don a ƙalla zatai shekaru sittin da biyar zuwa sama,farace tas dattijuwan me tsagen kalangu a fuskanta hagu da dama,kyakykyawace wanda a kallo ɗaya zaka zaci cewa bafulatana ce,sai dai ba hakan bane bahaushiyace ziryan,wanda ubangiji ne kawai yai mata baiwan kyau da farin fata,hannu takai tana janye bargon da budurwan ta ƙudundune aciki,cikin muryan da ke nuni da tsananin kulawa take faɗin "Tashi TAIMIYYAH ki ƙoƙarta kiyi wanka ko zaki daina wannan rawan sanyin,idan kin karya yanzu sai Sani yazo ku koma asibitin watakila waɗannan magungunan kaɗai bazasu wadatar da ke ba sai an haɗa da alluran dai da ba'a so."
Ta ƙare maganan tana ƙarisa yaye bargon da budurwan ta rufa dashi,nan take kyakykyawan fuskan budurwan da aka kira da TAIMIYYAH ya bayyana,tare da jikinta baki ɗaya wanda take sanye da rigan bacci Ash colour me kauri sosai,kamanninta da tsohuwan daya bayyana sosai zai baka tabbacin idan ba ƴarta bace to akwai alaƙa ta jini me ƙarfin gaske dake tsakaninta da dattijiyan matan,abinda kawai dattiyan zata nuna mata shine fuskan manyance ,amma hatta farin fatan nata irin na Dattijiyan ne,TAIMIYYAH ta yamutse kyakykyawan fuskanta tana sake lumshe manyan idanunta,muryanta can ƙasa dake ɗauke da ƴar shagwaɓa take faɗin "Wash! Allah Iya baki ji kaina ba kaman zai cire wallahi."
Iya ta dube ta cike da tausayi da kulawa tana faɗin "Sannu kiyi haƙury zai bari,yanzu tashi ki shiga wankan na haɗa miki ruwan ɗumi sosai da zakiji daɗinsa,Allah ya baki lafiya TAIMI na."
Budurwan ta amsa da "Ameen." Tana miƙewa tsaye da ƙyar sai lokacin na kula da cewa tana da tsayi dai-dai misali wanda bai cika yawaba,sam bata da jikin ƙiba sai dai jikin a murje yake cike da tsoka da cikan halitta me ɗaukan hankali,ta sake lumshe manyan idanunta sabida ciwan da kanta keyi,kafin a hankali takai hannunta na hagu ta dafa guiwan ƙafanta na hagun tana me fara takawa zuwa toilet ɗin dake manne cikin ɗakin,Dattijiya Iya tabi bayanta da kallo ƙaunar budurwan da tausayinta na sake ratsa ilahirin jinin jikinta,tana matuƙar tausayin TAIMIYYAH sai dai ko kaɗan ba ta nuna mata cewa nakasan da ta samu na ƙafa yana damunta domin ita kaɗaice a kullum take ba TAIMIYYAN tabbacin haka ubangiji yaso ganinta,tashi tayi tana me ficewa daga ɗakin mintoci kaɗan ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da Mug da ta ciko da zazzafan Kunun gyaɗa da yaji madara sabida sanin TAIMIYYAH na matuƙar son sa,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet,tana ɗaure da ƙaton towel da tsayinsa ya sauka har zuwa guiwanta,ƙafafunta nabi da kallo wanda na lura ɗaya ya sirance ɗaya kuma lafiyayye,ta yadda ruwa ke gangara a jikinta kaɗai zai baka tabbacin Allah yai mata baiwa da sulɓin fata,taiwa Hajiya Iya kallo ɗaya tana sakin murmushi,a hankali ta ciga da dafa ƙafanta na hagu tana takowa zuwa cikin ɗakin,da alamu wankan da tayo yasa ta fara jin daɗin jikinta,Iya ta ɗaga kai ta dubeta tana faɗin "Sannu kinji daɗin jikin ko? ga kununki nan saiki daure ki farasha kafin Ladi ta gama soya miki dankalin."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta masu haske ta dubi Iya,cikin sanyin muryanta me daɗi take faɗin "Naji daɗi Iya nagode da kulawa,amma ina ga abar dankalin wannan ɗin kaɗai ya isa,amma zuwa anjima don Allah ki min faten tsaki da kanki irin wanda kikeyi yayi ɗan tsamin yakuwannan shi kawai nake son sha." Ta ƙare maganan da shagwaɓa sosai a muryanta."
Hajiya Iya tayi murmushi me faɗi tana faɗin "To shikenan baki da damuwa za'ayi insha Allah,yanzu dai sha kunun ki sha magungunan,sai a sake kiran Sanin ku koma asibitin,ki tafi da duka magungunan sabida su gani ki kuma buɗe baki kiyi magana agaban likitan bana son wannan miskilancin naki idan kina ciwo ki ƙi magana."
Hajiya Iya ta ƙare maganan da mita,wanda hakan yasa murmushi me faɗi suɓucewa daga face ɗin TAIMIYYAH wacce ta kammala shafa mai tana ƙoƙarin saka rigan da ta ciro,ba tare da tayi magana ba har Iya ta fice ta sanya doguwan rigan atamfa Red wanda akaiwa adon zanen manyan Flawer da milk and black,yayi mata kyau sosai tare da haska kalan skin ɗinta,bata shafa komi a face ɗinta ba sai lip balm me taushi,qamshin Body mist datai anfani dashi ne ya cika ɗakin baki ɗaya domin ita ɗin ma'abociya son qamshi ce na ajin ƙarshe,zama tayi tana ɗaukan Mug ɗin da Iya ta aje tana fara shan kunun ahankali cike da nutsuwa,magungunan ta sha bayan ta shanye kunun,wani zufa ta fara ji na keto mata hakan yasa ta miƙe tana ƙara ƙarfin gudun Fan ɗin dake aiki a ɗakin,tsaye tayi gaban dogon mirrow ɗin ɗakin tana kallon fuskanta da ya rame sosai a kwanaki biyu kacal da fara ciwan nata,sai fararen manyan idanunta ma'abota haske da ɗaukan hankalin mai kallonta,domin wasu irin idanu Allah yai mata baiwansu masu ɗaukan hankali,ƙirjinta ta kalla tana me waro ido waje ganin cewa ta manta bata sanya Bra ba,gashi fita zasuyi sam bazata iya fita babu shi ba,sabida Allah yai mata baiwan cikar ƙirji,sai dai bawai irin sunyi girman da har suka rankwafa bane,kawai dai bata iya fita haka babu Bra dake tare su ajikinta,wannan sabo ne dataiwa kanta tunda ta isa sanya Bra ɗin,don haka kai tsaye wajen da take aje su ta nufa ta ɗakko tana sauke zip ɗin riganta zuwa ƙasa ta sanya,wayanta dake aje bisa gado ya fara ringing,sai ta nufa wajen don ganin me kiran,ganin sunan Sani ya bata tabbacin yazo kenan,ta ɗaga wayan tana gaida shi tare da bashi tabbacin fitowanta yanzu.
"Iya ga Sanin can ya iso zamu wuce."
TAIMIYYAH ta faɗi hakan tana kallon Hajiya Iya dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun da suke qawataccen falon nata,Iya ta ɗaga kai tana sauke ganinta akan TAIMIYYAH da ke sanye da dogon Hijab kalan Red da yai mata kyau sosai,ta saki murmushi tana faɗin "To sai kun dawo ki kula ki kuma buɗi baki agaban likitan bana son wannan miskilancin naki,kice ma Sanin idan kun dawo ya shigo ina son ganin sa."
TAIMIYYAH ta amsawa Iya tana miƙewa hannunta ɗaya riƙe da ƙaramin hand bag da ta sanya magungunan da aka ɗaurata akai,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta na hagu,wanda ke bada tabbacin sai da taimakon dafa guiwan shanyayyen ƙafan take iya takawa tana tafiya,a dukkanin cikar halittan ta babu inda ke da naƙasu sai wannan ƙafan na hagu daya shanye ya silance,kyakykyawace da ta mallaki duk wani cikan halitta me ɗaukan hankali,ahaka ta dinga takawa har ta fice daga falon Hajiya tayo waje,idanunta suka shiga ƙarewa haraban sasan Iya kallo kaman me son gano wani abu,kafin ta cigaba da takawa bisa tsarin yadda ubangiji yaso tafiyan nata ya zamo ahaka har ta fito daga sashin Iya baki ɗaya,ta iso ainihin haraban gidan me ɗauke da part guda biyu duk da na Hajiya Iya ne cikon na ukun,tafiya ta cigaba dayi zuciyanta na karyewa a lokacin da idanunta ke hango mata matar da ta fito daga ɗaya part ɗin,bayan matan wani matashi ne ke biye da ita riƙeda da wata ƙatuwar leda a hannunsa,TAIMIYYAH tayi saurin yin ƙasa da kanta tana cigaba da tafiya har ta iso dai-dai inda Hajiya Shuwa suke tahowa,hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan tana jiran ƙarisowan Hajiya Shuwan wacce suke kira da Umma,matar wan mahaifinta ne wacce taiwa TAIMIYYAN wata irin muguwan tsana.
"Ina kwana Umma."
Sune kalmomin da suka fito daga bakin TAIMIYYAH a lokacin da su Umman suka iso suna shirin gitta ta su wuce,sai dai gaisuwan da ta aikawa Umman yasa Umman dakatawa tana zubawa TAIMIYYAH ƙananun idanunta,fuskanta babu ɗigon fara'a ko kaɗan,tai mata wani malalacin kallo memakon ta amsa gaisuwan TAIMIYYAN sai cewa tayi "Ikon Allah su gurguwa kenan ance baki da lafiya,ke kuma haka Allah ya yoki irin jaraba ga nakasa ga yawan ciwo da wanne za'aji? kuma a hakan ake so wani yazo yace zai kwashi jaraba,ga gurgunta ga yawan cuta kaman sikila,to mu dai kurwan mu kur kada arasa me so ace wataran za'a cinnama lafiyayyun ƴaƴan mu gurguwa raguwan cuta."
Ta ƙare maganan da jan tsaki tana yin gaba abinta bayan ta kalli ɗan lelen ɗan nata ta maka masa harara tare da yi masa sign da ido alamun ya shige gabanta,ba tare da ta kuma kallon TAIMIYYAH da tai ƙasa da kai zuciyanta na shiga wani irin ƙunci mara misaltuwa ba,manyan idanunta tuni sun fara tara hawaye, ciwan kan da take riritawa taji ya dawo sabo,cikin ɗan hanzari ta dafa ƙafanta me laluran ta fara cigaba da tafiya,sai dai taku biyu tayi taji sassanyan qamshin turaren BENTLEY na isowa hancinta,kaman yadda kafin tayi wani yinƙuri yayi saurin tare gabanta,manyan idanunsa masu kama da nata ya sauke akanta,wani abu na yawatawa cikin maƙoshinsa,cak! TAIMIYYAH ta tsaya still bata ɗago face ɗinta ba don qamshinsa ya gama bata tabbacin ko waye domin kaf gidan shi kaɗai ne mamallakin irin wannan turaren me qamshin da ke kashe jikinta, amon muryansa me cike da ginshira taji cikin kunnuwanta yana faɗin "Kiyi haƙury Sis da halin Umma please! watarana sai labari ko kaɗan bana so kisa wani damuwa a zuciyanki haka Allah ya halicceki kuma yaso ya ganki, mu da ita babu me halitta haka kuma babu wanda isa ya sauya halittan wani face wanda yayisa,ya jikin naki?"
Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,hakan yasa TAIMIYYAH yin jarumtan maida ƙwallan da suka cika idanunta,sai dai duk yadda ta so ɓoye halin da zuciyanta ke ciki ƙaramar zazzaƙan muryanta dake rawa ya fallasata,cikin sanyin muryan da ke kashe zuciyansa take faɗin "Naji sauƙi Yah Sadeeq zazzaɓin ne yaƙi tafiya shine yanzu zamu koma wajen ganin likita,ina kwana dafatan mun tashi lafiya."
Ta ƙare maganan da gaida shi tana me ɗago manyan idanunta ta sauke akan face ɗinsa,sai dai ganin ita ɗin yake kallo yasa ta sake ƙasa da kanta,tana jin yadda idanunsa ke cigaba da yawo akanta,kafin ya furta "Okey! Allah ƙara lafiya yi maza kije tunda yana jiranki zuwa anjima zan shigo sasan Iya sai muyi magana,take care Angle."
Ya ƙare maganan da wani karyayyen sauti daya motsa zuciyan TAIMIYYAH,hakan yasa ta gyaɗa kanta tana lumshe idanunta da buɗesu lokaci guda ta cigaba da takawa zuwa parking space inda take hango motan Sani,ya bi bayanta da kallo tausayinta da matsananciyan ƙaunarta na sake kassara zuciyansa.
Ko da TAIMIYYAH ta isa wajen motan Sani baya ta buɗe ta shiga don tana buƙatan kwanciyane sabida yadda kanta ke sarawa,sam baiyi ƙorafi ba domin matsayin driver yake bashi da damuwan duk inda zata zauna ɗin,sannu yai mata yana tada motan bayan TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin amsa masa,zuciyanta na mata bitan baƙaƙen maganganun Umma wanda inda sabo yaci ace ta saba da yadda Umma ke kyaran halittan ta da kushe nakasanta tamkar itace tayo kanta a hakan,ba haka Allah yaso ganinta ba, hawaye masu ɗumi suka silalo mata ta kai hannu ta share tana son ƙarfafa zuciyanta kaman ko yaushe,don ganin maganganun basuyi tasiri a zuciyanta sosai ba,sai dai har suka isa asibitin ABU da ke zaria zuciyanta babu daɗi,zuciyanta ya sake nauyi tana tambayan kanta wai har sai yaushe ne zata daina fuskanta gorin halitta da cin fuska daga wasu cikin ahalinta akan yadda Allah ya yota? da ƙyar ta lallashi kanta ta samu ƙwarin guiwan shiga cikin asibitin don ganawa da likita.
A ƙalla ta shafe kusan awa guda kafin ta fito tana faman liliya inda akai mata alluran,domin bayan dukkanin bayanai da taiwa likitan sai ya sanar da ita dole ta amshi allura guda uku wanda zaa jera yi kullum guda ɗaya,ba don rai yaso ba ta amince domin allura na daga cikin abinda family ɗinta suka tsana akira za'aiwa ƴaƴansu tun bayan laluran data samu TAIMIYYAN wanda ta sanadin allurance ta samu wannan nakasan na shanyewan ƙafa ɗaya,wanda hausawa ke kira da shan inna wanda kuma take fuskantan ƙalubale me tarin yawa daga ƴan uwanta da wasu baren daban ma,kai kace itace ta janyowa kanta laluran da kanta ba Allah ne ya ɗauro mata ba.......
Hello! my people gani da sabon salo sabon tafiya irin wanda Ɗansabo bata taɓa zuwa dashi ba,labarin TAIMIYYAH labari ne mai cike da ban tausayi, haɗi da darasi me tarin yawa ga zallan ƙauna da soyayya me motsa zukata,kada ki bari abaki labari a wannan karon kowa ta ƙoƙarta ta mallaki nata akan fara shi me sauƙi da zan faɗi nan gaba kaɗan,ku dai ku cigaba da bibiyata a shafukan da zasu biyo baya don jin ya rayuwan TAIMIYYAH zai kasance.
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:03 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH* ❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 2*
Lokacin da TAIMIYYAH suka dawo gida daga asibitin ana ta kiraye-kirayen sallan zuhur ne,hakan yasa Sani wuce wa masallacin kusa da gidan,ita kuma TAIMIYYAH ta nufo sasan Iya jikinta gaba ɗaya ya saki ga wani zufa da ke keto mata alamun alluran da akai mata ya fara aiki sosai wajen saukar da Zazzaɓin gaba ɗaya,kaman ance ta kai dubanta ga sashen adana motoci na gidan,idanunta suka sauka akan motar Abie ɗinsu,ƙatuwar baƙar LEXUS tuni taji zuciyanta ya fara gudu wani daɗi ya lulluɓe zuciyanta,domin tayi kewansa matuƙa don sun rabu da shigowa garin shi da matansa da qanninta ,ta cigaba da takawa cikin takun tafiyanta wanda take dafe da ƙafanta na hagu,lokacin da ta sanya kanta a sashin Iya shi kuma Abie na shirin fitowa don zuwa masallaci,kaɗan ya rage suyi karo TAIMIYYAH tai baya don bashi hanya,cikin rashin sa'a hannunta dake dafe da ƙafanta me lalura ya zame,tai kaman zata kifa Abie ɗin yayi saurin taro ta yana faɗin "Subhanallah! ki dinga kula Zainab."
TAIMIYYAH da duk murnan ganinsa ya gama cika ta tai murmushin da suka bayyana kyawawan haƙoranta,cikin zallan murnan daya kasa ɓoyuwa take faɗin "Sannu da zuwa Abie,i miss u so much tare da su Ummie kazo?"
Alhaji Sameer ya gyaɗa mata kai yana sakin murmushi yake faɗin "We ol miss u too dear,tare muke ya jikin naki hope kina samun sauƙi sosai?"
Ta gyaɗa kai da shagwaɓa take faɗin "Naji sauƙi sosai Abie bari in shiga daga ciki na ga masallaci zaka sai ka dawo."
Daga haka ta raɓa shi ta wuce ya bi bayanta da kallo,yana kallon yadda take tafiya wanda shi yake ganin kaman a wahalce take takawa,tausayin ƴar sa da ƙauna irin ta uba da ƴa ke ratsa sa,sai da ta ɓacewa idanunsa sannan ya juya ya fice daga sasan baki ɗaya.
A cikin sasan Iya kuwa TAIMIYYAH na shiga falon Iya bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka fara sauka akan qanwarta Nahar,yarinya ƴar shekaru bakwai zuwa takwas,Iya da Ummie da ke zaune cikin falon ne suka amsa sallaman TAIMIYYAH,yayinda Nahar ta rugo da gudu wajen TAIMIYYAH tana faɗin "Oyoyo! Anty TAIMIYYAH."
TAIMIYYAH da tayi saurin jingina da jikin kujera don kar Nahar ɗin ta kadata,tayi saurin sakin murmushi tana ware mata hannuwanta Nahar ta shige,ta rungume yarinyan tana faɗin "Welcome My Baby i miss u."
Raudha yayar Nahar ce ta iso itama tana ma TAIMIYYAH oyoyo,TAIMIYYAH ta rungume su duka sunata murnan ganin juna,Raudha zatai shekaru goma sha ɗaya,kallo ɗaya zakai mata kasan sun haɗa jini da TAIMIYYAH,domin kamansu ɗaya da Iya har farin fatan,yayinda suka ɗakko manyan idanun Abie farare tas,sakin su TAIMIYYAH tayi tana nufan wajen su Iya,Nahar ta biyo bayanta tana faɗin "Anty har yanzu Abie ya kasa sawa a gyara miki ƙafanki ki dinga tafiya irin yanda mukeyi,kuma a daina ce miki gurguwa yadda su Anty Zuhrah ke kiranki."
Ummie ne tayi saurin buge bakin Nahar ɗin a lokacin da ta iso wajen,yayinda TAIMIYYAH tai murmushi tana duban Nahar ɗin da muryanta me raunin daya fallasa cewa maganan Nahar ya taɓa zuciyanta,ta furta "Nahar ba laifin Abie bane domin bashi ne zai iya sawa ƙafan ya gyaru ba,ni haka Allah yaso ganina karki damu kinji,ni Allah bai nufa in dinga tafiya irin yadda kuke yi bane kuma ki daina ɗaukan maganan da su Anty Zuhura ke faɗi kina sawa a ranki kinji ko?"
Yarinyan ta gyaɗa kai alamun gamsuwa yayinda TAIMIYYAH tai ƙasa tana gaida Ummie,Ummien ta amsa da kulawa duk da cewa fuskanta babu wani alamun ɗoki ko murnan ganin TAIMIYYAN,domin irin matannan ne marasa sakin fuska,sam bawai ta damu da TAIMIYYAN bane kanta da ƴaƴanta kawai tasani,shiyasa tun lokacin da Abie ɗin ya auro ta ya nuna son ta riƙe TAIMIYYAN ta bijera masa,domin a ganinta zama da irin su lalurace kawai da ɗawainiya duk da cewa babu abinda yake gagaran TAIMIYYAN a hakan babu abinda bata iyawa,hatta da ɗaukar ruwa a bucket da duk wani aikin ƙarfi gwargwado tana iyawa,babu abinda ake taimakonta dashi sai ƙalilan,sannu da dawowa Iya taiwa TAIMIYYAH tana tambayanta yadda sukai da likita,TAIMIYYAH ta sanar da ita cewa allurai aka bata uku anyi ɗaya saura gobe da jibi,Iya tai mata fatan samun sauƙi daga haka ta zame jikinta ta nufi ɗakinta don yin wanka da sallah sabida yadda take jin zufa ya jiƙe jikinta bazata iya komiba ba tare da ta sake wanka ba.
Lokacin da ta fito wankan samun su Nahar tayi sunyi ɗai-ɗai a bed ɗinta,suna faman kallon ƙaton photo album dake aje saman Bed side na gado,kallo ɗaya tai musu ta saki murmushi tana wucewa wajen kayanta,doguwar riga mara nauyi ta saka me taushi bata shafa komi ba a jikinta,ta zura Hijab ta tada sallah,bayan ta idar ne ta tasa kan su Raudha zuwa falo lokacin Abie ya jima da dawowa daga masjid,zama sukai gaba ɗaya aka shinfiɗa babban ledan cin abinci wanda aka jera manyan kulolin abinci duk da cewan zuwan bazata sukai bai hana Iya saka Ladi me aiki shirya abincika masu sauƙi ba,tare sukai lunch ɗin gunin sha'awa TAIMIYYYAH na jin farin ciki sosai na ganin ahalinta,duk da cewa sam babu cikakken wani shaƙuwa tsakaninta da Abie ɗin,amma hakan baya hana ta shiga farin ciki a duk sanda zai zo garin walau shi kaɗai ko da su Ummie ɗin,Ummie itace ta fara tashi daga wajen cin abinci tana sanar da Iya cewa zata wuce part ɗinsu,Iya tai mata Allah huta gajiya tai gaba su Nahar ko kallonta basuyi ba bare suyi yinƙurin bin ta suna nane da TAIMIYYAH domin Allah ya ɗaurawa yaran son Yayar tasu,ko don irin kulawa da ƙaunar da TAIMIYYAN ke gwada musu ne Allah masani,lokacin da Abie ya kammala cin abincin yayi hamdala tare da goge bakinsa da tissue,sai ya ɗaura manyan idanunsa akan TAIMIYYAH wacce itama ta gama cin abincin tana gogewa Nahar baki ne,cikin murya me nuna kulawa yake faɗin "Zainab yanzu kin gama NCE ɗinki sai kuma miye plan ɗinki na gaba,aure ko karatun zaki ɗaura?"
Kalman aure daya shigo cikin kalamansa yasa TAIMIYYAH saurin waro idanunta,cikin muryan da ke nuna kiɗima take faɗin "Abie aure kuma? Karatun dai zan ɗaura ni bazan yi wani aure ba waye ma zai auri gurguwa kaman yadda Umma ke faɗi."
Ta ƙare maganan tana turo baki alamun shagwaɓa,Iya da ke zaune duk tana jinsu ta ɗago tare da saukewa TAIMIYYAH harara tana faɗin "Ashe ban hanaki irin waɗannan kalaman na banza ba TAIMIYYAH,don Allah ya yoki ahaka sai akace shikenan bazaki samu masoyin da zai aureki a haka ba,to bari kiji wanda suka fiki nakasama sunyi aure har sun haihu bare ke da babu abinda ma yake gagaranki,kije gidan Malam Inuwa ki kallon gurguwan da bata ko iya tashi ta miƙe a nannaɗe take amma tayi aure ƴaƴanta goma sha biyu zar sunanan suna taka doran ƙasa,don haka ki iya bakinki ki kuma daina ƙoƙarin ja da ikon ubangiji,ita wacce kike ji abakin nata tana cewa bazaki auru ba sai ki zuba mata ido ki ga idan itace ta halicceki da zata hana Allah ikon sa,ni a nawa ma babu wani karatun da zaki ɗaura Allah ya kawo me so kiyi aurenki kawai ki huta."
Tunda Iya ta fara magana ko tari babu wanda yai har ta dasa aya cike da sababi da jin zafin Hajiya Saratu a ranta,Abie ne ya dubi mahaifiyan na su yana faɗin "A'a Iya idan har tana son cigaba da karatun kar a tauyeta,abata dama ta ɗaura idan yaso tana cikin yi Allah ya kawo me son sai ayi auren,amma zaman haka bazai yiwu ba,Zainab wani skull ɗin kike so gashi yanzu ana cikin wannan strike ɗin,ni kuma bazan so ki tafi wani gari ba sabida laluranki, karatunki a kusa da gida zaifi,don haka sai dai ajira aga janyewan yajin aikin malaman sai asan abinyi,idan akwai wani plan ɗin da kike dashi ina jinki tell me."
Abie ɗin ya ƙare maganan idanunsa akan TAIMIYYAH da daɗi ya cika ta,na jin cewa Abie ɗin bazai hanata cika burinta na son yin karatu me zurfi ba,cike da ɗoki take faɗin "Abie zan fara yin wani Computer Skull kafin a dawo daga yajin aikin,ina so in samu certificate na Computer Training ɗin,kuɗin form da na registration kawai zaka bani,a can wajen Congo ne sai Sani ya dinga kaini yana ɗakko ni ko Abie?"
Alhaji Sameer ya jinjina kansa cike da gamsuwa yake faɗin "Eh hakan ma yayi kinyi tunani me kyau,karki damu zan baki kuɗin komi da komi,amma Iya tace an baki allurai uku meyasa kika yadda aka fara,kinsani sarai bana so ko kina manta alluran shine silan laluranki Zainab."
Ya ƙare maganan da faɗa sosai wanda yasa TAIMIYYAH bashi haƙury,tare da sanar dashi magungunnan ne basui mata ba dole sai an haɗa da alluran,tare da su Raudha ya bar sashin zuwa part ɗinsu da suke sauka idan sun zo daga Lagos ɗin.Bayan fitan su Iya ta kalli TAIMIYYAH da ke ta faman murnan zata shiga Computer skull,ta maka mata harara tana mitan faɗin "Ayi dai mugani duk son karatun mutum da ƙinsa da aure indai lokacin mutum yayi dole yai auren ba."
Kafin TAIMIYYAH tace komi suka jiyo amon muryansa,wannan dai muryan nasa me cike da isa yake doka sallama daga bakin ƙofar ɗakin Iyan,Iyan ce ta amsa sallama tare da bada izinin shigowa,qamshin turaren BENTLEY ya riga isowa cikin ɗakin kafin gangar jikinsa ya shigo,idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH da ta miƙe tare da dafe ƙafanta ta fara takawa don komawa ɗaki ta kwanta,baiyi magana ba har ta shige corridor ɗin da zai sadaka da Bedrooms ɗinsu,illa ɗauke kansa da yai ya maida dubansa kan Iya yana takowa cikin falon,a kujeran 2 seater ya zauna yana fuskantan Iya ya fara gaida ta,ta amsa fuska a sake tana faɗin "Yanzu Sadeek ka dawo tun jiya sai yau zaka shigo gaida ni,to kayiwa kanka ne aiko baka shigo ba ka zo don mutuniyar ka dana tabbatar kaji bata jin daɗi ko da yake naga yanzu ƴar wasan ɓuya kuke tunda uwarka bata ƙaunar jituwan da ke tsakaninku."
Ta ƙare maganan cike da sababi hakan yasa Sadeeq sake haɗe fuska,yana wani taɓe baki yake faɗin "Ke dai Iya kin faye son nacin magana ɗaya,waya gaya miki wasan ɓuya muke ita ɗince dai bansan meyasa bata son haɗuwan mu ba yanzu ko don taga ta gama zama Big Girl ce oho."
Iya ta taɓe baki itama tana faɗin "kadai ji da ƙaryan turancinka,ya wajen aikin naku ina fata dai komi na tafiya yadda ya dace ko?"
Sadeeq ya gyaɗa mata kai kawai,kafin ya miƙe ya nufi wajen cin abinci yana faɗin "Iya akwai abincin da zan iya ci anan,cikin gida tuwon shinkafa akayi ni kuma banso,ai na ga motar Abie ashe sun shigo."
Iya ta amsa da "Eh aiko sai ga su babu sanarwa,sai ka duba akwai ragowan shinkafa da miya sai dai mayyan Salad ɗin ta juye shi ta kai fridge."
Tuni ya gane wa take nufi don haka baice komi ba sai nufan hanyan ɗakinta da yai,Iya ta bi bayansa da kallo tana taɓe baki ba yau ta gama gane jikan nata ya kamu da son ƴar uwan nasa ba,sai dai bata ji ko sama da ƙasa zasu haɗene zata bar TAIMIYYAH ta aure shi,sabida ƙiyayyan da uwansa take gwadawa TAIMIYYAN,shiyasa tai biris bata taɓa nuna musu daga shi har TAIMIYYAN tasan abinda suke ciki ba........✍🏻
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer* *Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
_Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank*
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: - Nawa aka tura?
Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN, 9Mobile Glo Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*WANNAN SHINE BAYANAN*
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:03 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH* ❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 3*