Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 2
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 2: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,493 words
Yana sanya kansa cikin ɗakin sassayan qamshin daya kama ɗakin ya doki hancinsa,ya ɗan lumshe idanu yana jinjina tsafta da son qamshi irin na TAIMIYYAH,halayyanta da ke sake saka shi jin ta aransa sosai da yaba ƙoƙarinta akan kula da kanta, duk da laluran ƙafanta sam bata da ƙyuiya da son jiki,kwance ya hange ta tayi ruf da ciki tare da tokare hannayenta da pillow waya riƙe a hannunta,sam bata ji sallamansa ba sai qamshin turaren BENTLEY da ya buɗe ɗakin,hakan yasa ta saurin tashi zaune tana sauke manyan idanunta akansa,fuskanta a sake take faɗin "Yah Sadeeq shigowa kayi,ina yini."
Harara ya zabga mata yana takawa zuwa wajen stool da ke gaban madubi ya janyo ya zauna,idanunsa ya mayar kanta kafin ya buɗe baki cike da ginshira yake faɗin "Wannan yarinyan kin girma da yawa kin fara raina mutane ko? Ba kina kallo na shigo ba amma ki kai tahowanki sabida baki ƙaunar haɗuwan mu yanzu ko? to yau sai kin gaya min yadda akai na zama dodo har da kike guduna."
Ya ƙare magana babu alamun wasa ko sassauci a face ɗinsa,hakan yasa TAIMIYYAH sake dubansa ya sake jefa mata harara,ganin hakan yasa ta tsuke baki tana faɗin "Kayi haƙury ni fa ba gudowa nayi ba,kasan banda lafiya to kwanciya na shigo yi ina jin jiri ne."
"Allah ya sauƙe ya baki lafiya,amma meyasa tun wancen week ɗin dana shigo kika ƙi bari mu haɗu har na koma?"
Yadda ya tsare ta da ido yasa ta kauda kanta,ba tare da tace komi har sai da ya sake maimaita tambayansa sannan ta ɗago ido ta dube sa kafin ta shagwaɓe murya tana faɗin "Umma ce fa tace in daina shige maka inba haka ba duk randa ta sake ganina da kai saita ƙarisa ɗayan ƙafan nawa na zama gurguwan me sosai."
Yadda ta ƙare maganan muryanta na ɗan rawa yasa jikinsa yin sanyi,cikin taushin muryansa me kauri yake faɗin "Amma sau nawa zance ki daina damuwa da maganganun Umma,haba Baby meyasa kike son kafa Hujja da Umma ni kuma kina azabtar da zuciyata why?"
TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta ta ɗago tana ƙoƙarin danne hawayen da ke son zubo mata,cikin rawar murya take faɗin "Dole in saka maganganunta araina Yah Deeku,Umma bata so na bansan miye laifi na don na kasance gurguwa ba,bani nai kaina ba inda ana ba ɗan Adam zaɓin ya zaɓi yanda yake son halittansa ya kasance bana ji akwai wanda zai zaɓi nakasa,amma ita sam ta kasa gane bani ce na zaɓi zamowa a haka ba,yanzu ba da bane Yah Deeku nasan ciwan kaina a yanzu,maganganunta suna ƙona zuciyata kaman yadda wuta ke ƙona itace,dole in kiyaye duk abinda zai dinga janyo min gorin halitta,kayi haƙury Umma uwace a guna amma zuciyata bazata iya juran yawan aibantani da takeyi ba,shiyasa tunda ta nuna bata son shaƙuwan dake tsakaninmu dole mu koyi nisanta da juna."
Zuwa lokacin da TAIMIYYAH takai ƙarshen magananta tuni hawayen da take dannewa sun ɓalle,suna zarya a saman kyakykyawan face ɗinta,Yah Sadeeq da tunda ta fara magana ya tsura mata ido,ransa yai matuƙar sosuwa da hawayen da take zubawar,ya sani tafi shi gaskiya domin kaman yadda ta faɗi ne babu wanda yasan ciwan kansa da zai so jin yadda Ummansu ke kyaranta tana aibanta nakasanta kai kace TAIMIYYAN irin guragunnan ne da basa ko iya tafiya,cikin muryansa da ya bayyana raunin da zuciyansa shi ma yayi yake faɗin "Yanzu kina nufin sabida Umma ne zaki daina kulani bayan kinsan zuciyata ta riga ta kamu da ƙaunar ki Zainab,ya kike so inyi da wannan sabuwan ɗabi'an da sam bazan iya jure masa ba?"
Sanin bazata amsa masa ba yasa shi kai tsaye cigaba da faɗin "Lokaci yayi da zan fito fili insanarwa da Umma ke nake so,so kuma da aure ko hakan zai tabbatar mata da cewa alaƙanmu dake ya wuce shaƙuwa na ƴan uwantaka,zallan soyayya ce mara algus."
Kukan da TAIMIYYAH ta sanya masa ne yasa shi tsura mata ido cike da mamaki,baki buɗe yake kallonta wani abu na yawo a cikin zuciyansa,cikin muryan kukan take faɗin "Ka dubi girman Allah Yah Sadeeq karka faɗawa Umma wannan maganan,wallahi kasheni zatayi nina sani,don Allah karka shigo da abinda kasan bazai taɓa yiwuwa ba,alaƙanmu ta tsaya iya na ƴan uwantaka, ka riƙe girmanka na Yayana wanda nafi so da shaƙuwa dashi,me sharemin kuka na da bani dukkanin ƙwarin guiwa,don Allah kada ka rusa wannan alaƙan ka shigo da batun da bazai taɓa yiwuwa ba illa jefa rayuwata cikin garari."
Kuka takeyi sosai zuwa lokacin domin ita kaɗai zata iya gayawa duniya irin tsanan da Umma tai mata,ba ta ji ko za'a tashi duniya zata iya amincewa da Yah Sadeeq ɗin ya zama abokin rayuwanta,ta sani yana son ta don ya riga ya jima da fallasa mata sirrin zuciyansa,ita ɗince har yau ya kasa jin taƙamaimai miye a zuciyanta game dashi,baya hango kowace irin soyayya a idanunta daya wuce na ƴan uwantaka,irin na wanda shaƙuwa ya shiga tsakani,cikin tsananin ɓacin rai ya daka mata tsawan da yai saurin sata sake rushewa da kuka me ƙarfin gaske,ta kai hannu tana toshe bakinta ganin yadda ya taso yana nufota,ta shiga matsawa da baya-baya tana cigaba da toshe bakinta kuka nacin ta,zama yayi daga bakin Bed ɗin yana kai hannu ya janyota baki ɗaya zuwa jikinsa,kafaɗunta duka ya kamo yana girgizata yake faɗin "TAIMIYYAH me kike nufi da waɗannan kalaman,kina so ki gaya min tuntuni ni kaɗai nake haukata ke zuciyanki bata kamu da soyayyata ba? Ki sanar dani ni kaɗai nake shirme na kome?"
Yadda yake magana yana ɗaga murya da sake jijjiga kafaɗunta yasa TAIMIYYAH sake rushewa da kuka,sai dai kafin tayi wani yinƙuri sai shigowan Iya suka ji cikin ɗakin,ta tafa hannu tana salati tana faɗin "Me zan gani Saddeeku dukanta kai bata da lafiya kome,ko kaima ka fara kurɓe kurɓen zamanin nan da samari keyi ne bamu da labari? To sakarta tun ranka bai ida ɓaci ba,ka kuma sanar dani tun farko ma uban mi ya kawo ka ɗakinta?"
Sadeeq da ransa ya gama ɓaci sai ya saki TAIMIYYAH yana ballawa Iya harara yake faɗin "Bansani ba miye naki na shigowa nan ɗin kaman an kiraki."
Iya takai hannu ta bige bakinsa tana faɗin "Yi min shiru mara kunya,kuma ka gaya min me tai maka da zaka tasa ta agaba kana jijjiga kaman ka biya sadakinta sabida tambaɗa da fitsara,to ahir ɗinka ka kiyayeta ince dai soyayya ce kakema wannan haukan,to inma son ta kake tun wuri ka cire bazata so ka ba,inma ta fara dole ta daina kowa yai ta kansa,indai ina raye TAIMIYYAH ba zata aure ka ba uwar ka taje can ta zaɓo maka matan aure amma ba dai Zainab ba,wuce ka kabar min sasa tun bansa an kira min uwar ka da uban ka sun maka iyaka daga shigowa nan ɗin ba."
Yadda Iya ta rintse ido tana yayyafin masifa yasa Sadeeq ficewa cikin zafin nama,zuciyannan kaman ya faso ƙirjinsa sabida ɗaukan zafi,Iya ta bishi da tsaki kafin ta koma kan TAIMIYYAH tana lulluɓeta da faɗa kaman zata duke ta,cikin faɗan take cewa "In banda ke ɗinma banza ce uwar sa har nan tazo tai miki iyaka da ɗanta,amma shine zai lallaɓo ya tasaki agaba har da kama jikinki yana girgizawa baki fito kin bar masa ɗakin ba,yo ko dai kema son nasa kike? Aiko da kinyi asaran duniya kin kuma ba mutane kunya me zakici da mutumin da uwarsa bata da aiki saina aibanta halittanki tana kyaranki,to ahir ɗinki wallahi idan kika biyesa har ya yaudari zuciyanki sai dai ku mutu da son juna amma bazaki aure sa ba indai ina numfashi kuma na isa dake,shashashu kawai marasa hankali."
TAIMIYYAH dai kuka kawai takeyi ba tace uffan ba har iya ta gama bambaminta ta fice,sai ta zame ta kwanta tana cigaba da kuka me tsuma zuciya,ita sam bata taɓa jin cewa zata iya son kowani namiji bama bare Yah Sadeeq ɗin,meyasa Iya zata ɗauki zafi da ita har haka? ta cigaba da kukanta zuciyanta na ƙuna ,kiran wayanta da akai ne yasata tsai da kukan bayan ta ɗauki phone ɗin ta ga cewa qawarta Haneefa ce me kiran,basu jima suna magana ba sukai sallama da juna,TAIMIYYAH ta nufi toilet ta wanke face ɗinta ta fito,dogon Hijab ta zura ta ɗauki phone ɗinta ta fito,a falo taci karo da Iya har lokacin bata fasa ƙananun mitanta da ta saba idan ranta ya ɓaci ba,kallo ɗaya taiwa Iyan ta ɗauke kai tana takawa zuwa ƙofan fita falon ba tare da tayi niyyan tankawa Iya ba,ganin da gaske fita TAIMIYYAH zatayi ba tare da ta kula ta ba,ya sanya Iya ɗaga murya tana faɗin "Au binshi zakiyi don na kore sa,ko kuwa gidan ubanwa zaki kina fama da kanki?"
TAIMIYYAH da takaicin Iya ya gama cika ta,ta juya ta balla mata harara kafin ta furta "Ni part ɗin Abie zani tunda yau abin naki akaina zaki sauke shi."
Yadda TAIMIYYAN tayi magana cike da shagwaɓa da jin haushi yasa Iya sakin murmushi,tana faɗin "Oh'oh'oh me yai zafi daga faɗin gaskiya kuma ƴar nan,dawo kije ki kwanta tunda ba lafiya ne dake ba,ni ina jiye miki ne yadda uwarsa ta tsaneki me zaki ci dashi Allah na tuba,ko da kike a haka ai kinfi ƙarfin ajinsa ke ɗin matar manya ce."
Wani hararan TAIMIYYAH ta ballawa Iya tana juyowa ta dawo cikin falon,kujeran kusa da Iya ta nufa ta kwanta tana faɗin "Nidai Iya wallahi fitinanki idan ya tashi yana bani tsoro,yaushe rabon da kika ga na kulasa amma sabida son ɗauramin laifi har da faɗin ko na fara son sa ne,ni bana son sa kuma bazan so kowa bama bare aje ana min gori,auren ma bazanyi ba ko zanyi kuma zanyi fatane Allah ya bani me nakasa irin tawa ta yadda ƴan uwa da danginsa babu wanda zai min gori,amma Yah Sadeeq bazan taɓa iya bashi zuciyata ba Iya don Allah ki kwantar da hankalinki,ni abinda kawai zakiyi ki birgeni ki samu Abbah da maganan kice masa baki son sake jin shi Yah Deekun ya tada maganan."
Iya da ta tsurawa TAIMIYYAH ido tsananin tausayin ta na faman ɗawainiya da ita,ashe dai TAIMIYYAN na son auren gori take gudu sabida nakasan ta,zuciyan Iya ya motsa da wani irin yanayi me wuyan fassara,ji take da komi nata zai ƙare akan TAIMIYYAN ƙafanta ya dawo dai-dai da zata iya sallamawa,sai dai ita ɗin shaida ce akan irin yawon manyan asibitocin ƙashi da sukai tun TAIMIYYAN na ƙarama har kawo yanzu,amma ba'a dace ba ƙasar waje ne kawai ba'a fita da ita ba,ita da kanta TAIMIYYAN da ta gaji da wahala ta roƙi a ƙyaleta haka ubangiji ke son ganinta,Iya ta furta "To shikenan karki damu zanyi magana da Sanin,ni dai abinda nake so kisawa ranki gorin da ake miki bazai sauya komi ba,akan duk abinda Allah yai nufin kasancewansa,kada kisawa zuciyanki lallai sai me lalura irin taki zaki bawa dama,ina fa lura da dake sarai kina samun masoya kece kike kore su ashe sabida wannan manufan ne dake ranki? To wallahi ki kiyayeni angaya miki sai me lalura ne irin taki kaɗai zaki aura ki samu kwanciyan hankali da soyayya? Wannan shirmenki ne kawai ke dai ki dinga addu'an Allah yai miki zaɓi mafi alkhairy kawai."
TAIMIYYAH kai kawai ta gyaɗawa Iya alamun gamsuwa da kalamanta,daga haka suka kulle wannan babin,Iya ta ɗakko mata zancen aminiyanta Hajiya Juwairiyyah,wacce suka rabu da saduwa da juna,cikin hiran Iya ke sanar da TAIMIYYAH da zaran ta sake samun sauƙi zasu kaiwa Hajjajun ziyara,ita dai TAIMIYYAH jin Iya kawai take yi amma sam a ranta bata son zuwa ko'ina, ita sam tafiye-tafiye basu dame ta ba.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer* *Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:03 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 4*
Kwanaki biyar da suka biyo baya TAIMIYYAH ta samu sauƙi tayi garas,don ta gama amsan alluranta har tana harkokinta,tun safiyan yau da ta tashi tana jin cin Meat pie,sai dai basu da nama ya ƙare dole sai ta aika an siyo gashi Nura almajirin Iya kwana biyu bai zuwa ya tafi gida,bayan tayi wanka ta shirya wajen ƙarfe sha ɗaya har da rabi,ta samu Iya a ɗaki don sanar mata zata fita cefanan yin Meat pie ɗin ta dawo,don kuɗi sosai take dashi a hannu,sabida duk idan Abie zai koma yana barin mata kuɗi sosai a hannunta,gefen gadon Iya ta samu ta zauna ganin Iyan akan dadduma alamun idar da sallan walhan ta kenan tana addu'a,wayanta da taji yana ring acikin ƙaramar jakan hannunta ta ciro,ganin sunan Mubarak yasa ta share kiran tare da maida wayan silent,Mubarak wani course mate ɗinta ne da sukai NCE tare,shi a dole son TAIMIYYAH yake da gaske sai dai ita kuma bai taɓa birge taba,mutuncinsa da take gani da irin taimakonta da yake yi akan karatu yasa ta kasa blocking ɗinsa,Iya ta waiwayo ta zubawa TAIMIAYYAH idanu,wacce ke sanye da Hijab kalan Pusha Pink daya haske farar fatanta,tayi kyau ƙwarai duk da cewa babu komi akan face ɗin illah manyan fararen idanunta da ta sanyawa kwalli,sai bakinta da sai ka kalla da kyau zaka gane ta goga lip gloss,wani kuma zaiyi zaton pink ɗin janbaki ta saka domin pink lips gareta.
"Sai ina kuma da hantsinnan TAIMIYYAH?"
Iya ta jefa mata tambayan har lokacin idanun Iyan na kan TAIMIYYAH,TAIMIYYAH ta dubi Iya tana sanar da ita inda zata da abinda zai kaita,Iya ta gyaɗa kai tana faɗin "To shikenan sai kin dawo ki kula da kyau,ni bana son yawan zuwa kasuwan da kike da Nura na nan ma babu inda zaki gaskiya,ga ɗari biyu can saman madubi idan kinga Goro me kyau ki siyo min."
TAIMIYYAH da ta miƙe tana me dafa ƙafanta ta fara tafiya take cewa"Bar shi Iya akwai kuɗi sosai a hannuna bayan Goran ma har Gautan Yalo idan na gani duk zan siyo miki."
"To Allah yayi albarka TAIMI na,Allah fito min da suruki nagari."
Cewan Iya tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,cike da so da ƙauna haɗi da tausayinta me zurfi,a ciki TAIMIYYAH ta amsa addu'an Iya tana cigaba da takawa har ta fice daga ɗakin,lokacin da ta fito haraban gidan sai ta dubi part ɗin Abie da ke kulle,ta cigaba da tafiya tana jin kewan su Nahar na ratsata don kwanaki biyun da sukai ba ƙaramin ɗebe mata kewa da sanya ta farin ciki sukai ba,sam bata kula da fitowan su Zuhura daga Sashin su ba,sai da ta kusa fita daga gate ɗin gidan sai ji tayi kawai an janyo Hijab ɗinta ta baya,ta waiwayo tana sauke idon ta akan Basma,kafin ta buɗe baki don musu magana Zuhura ta riga ta da faɗin "Dallah! Malama bamu waje mu wuce sauri muke kinzo kina wannan shegen tafiyan naku na guragu,salon a bangajeki ki faɗi ki janyo ma mutane masifa,yanzu gaba ɗaya na ga wani tashen girman kai kike ji tunda Yaya ya zubda ajinsa yace ke yake so,ko mai zaici da gurguwa bansani ba,ko da yake kila kyawu da dirin jikin yake mawa,inma hakan ne banda abinsa idan Kyan da nonuwan ke ruɗansa ga lafiyayyun ƴan mata nan da suka haɗa komi mitsuww!"
Zuhura ta ƙare maganan da jan dogon tsaki,Basma na taya ta yayinda TAIMIYYAH da suka ja gefe tayi saurin durƙusawa ƙasa,tuni hawaye sun fara zarya a face ɗinta,har suka fice daga gate ɗin ta kasa koda motsawa,kanta na duƙe tana ji zuciyanta na mata wani irin zafi kaman ya kama wuta,ko kaɗan bata fiya ganin laifin su Zuhuran akan duk irin cin mutuncin da suke mata ba,tafi ganin laifin Umma domin a wajenta suka fara gani,itace ta koya musu hakan duk da cewa TAIMIYYAN age mate ɗin Zuhura ne watanni biyu kacal ke tsakaninsu,amma ace har Basma da take qanwan bayanta ta san taci zarafinta akan kawai ta kasance me nakasa,wasu hawayen masu tsananin zafi suka sake wanke face ɗinta,tayi saurin buɗe jakanta tana ciro hanki da ke ciki ta shiga share hawayen ,tana rarrashin kanta kaman yadda ta saba,don wannan ba shine karon farko ba,idan zasu haɗu so dubu to tana da tabbacin sai sun goranta mata sunci fuskanta,taso fasa fitan kawai ta koma amma sai tayi tunanin Iya zata tsare ta da tambaya,da zaran ta gaya mata yadda sukai da su Zuhuran kuma to abin bazai kyau ba domin Iya wanke ƙafa zatai ta je taci mutuncin Umma da su kansu su Zuhuran,wanda hakan bakomi yake sake janyowa TAIMIYYAN ba sai tsantsan tsana,don haka kawai ta miƙe duk jikinta yayi sanyi ta cigaba ta kawa har ta fice daga gate ɗin gidan,idanunta sun rine sabida kukan da tayi amma bata da zaɓi haka ta cigaba da tafiya bisa yadda Allah ya nufeta da takawa,ta miƙo layin nasu sosai tana cigaba da tafiya,wasu yara da suka zo wucewa ne suka zuba mata ido suna kallonta,ƙaramin cikin su ne ke cewa "Laah! Gurguwa ce kunga yadda take tafiya." Ya ƙare maganan yana kwatanta ma ƴan uwansa yadda TAIMIYYAH ke dafe guiwanta tana takawa,TAIMIYYAH da ke cigaba da tafiya duk tana jinsu yadda suka biyo bayanta suna ta kwaikwayon tafiyanta,idan tace zuciyanta baya shiga ƙunci to tayi ƙarya ,sai dai babu yadda ta iya haka ubangiji ya nufe ta da kasancewa,kuma bata isa ta hana a kwaikwayeta ba,sai dai tunawa tayi da cin mutuncin da ƴan uwanta na jini sukai mata a yanzu yanzu,yasa takaicin yaran raguwa a ranta domin tana ganin gara su yara ne masu hankali ma sunyi bare su,har ta iso bakin layin su inda zata iya samun abun hawa zuciyanta a cinkushe yake babu daɗi sam,bata wani jima a tsaye ba ta samu abin hawa tai gaba abinta.
___________
*GRA,Zaria.*
Babban gida ne wanda tun daga nesa me kallo zai san gidan na manya ne masu hannu da shuni,tsananin haɗuwan ginin da tsaruwansa zai sa me kallo yasan cewa ƙwararru a harkan ginin zamani ne suka zana asalin taswiran ginin,ginin upstairs ne da tsayawa misalta tsaruwansa ɓata lokaci ne,daga cikin ƙaton parking space na gidan motoci manya guda uku ne aje,za kai tafiya me nisa kafin ka isa asalin main entrance na shiga cikin gidan.
Daga ciki gidan babban falo ne a ƙasa,mai ɗauke da ɗakuna guda uku kowanne manne da toilet a ciki,an zuba kaya na alatu wanda ƙwararrun Interiors ne suka tsara komi bisa muhallin daya dace,yanayin yadda aka tsara falon da irin kujerun dake cikinsa da sauran kayan decor na ɗakin,zai tabbatarwa me kallo ba ƙananun kuɗi aka narkar ba, daga hannun hagu wanda nan ne aka aje 3 Seater,wani kyakykyawan magidanci ne ma'abocin kyawu da cikar haiba,Black Beauty ne wanda fatarsa ta rine da hutu da jin daɗin rayuwa,hakan ya haifar ma lafiyayyan fatansa da wani irin fresh,yana da dogon hanci zar tare da manyan dara-daran idanu,abinda ya ƙarawa kyawunsa armashi shine gashin giransa baƙi siɗik wanda suke a cinkushe,kame yake cikin kujeran ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya,a shekaru bazai gaza shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas ba,daga saman cinyansa ƙaramar laptop ne yana faman latsawa,dukkanin nutsuwansa yana ga aikin da yake a cikin computern,sanye yake cikin wata Farar Jallabiya,wanda kana kallo zaka san manyan kuɗi aka aje kafin a ɗauke ta,dukkanin wajen ya cika da qamshin turaren RALPH LAUREN,takun takalman dana fara jiyowa daga ɓangaren matakalan benan dake kallo cikin falon yasani kai dubana wajen,idanuna suka fara hango min fuskan matar da ke sakkowa daga stairs ɗin sanye cikin kayan bacci riga da wando da suka fiddo suranta a fili,baƙace sai dai tana da matsakaicin kyawun fuska,don kai tsaye bazaka kirata kyakykyaba,haka kuma bata da muni akwai ta da cikar halitta me ɗaukan hankali,ko kaɗan bata da makusa,matashiyace da bazata gaxa shekaru ashirin da takwas ba a duniya,amma duk wanda yai mata kallo ɗaya zai iya bata shekaru ashirin da biyu sabida yanayin kula da gyara da jikin ke amsa a kowani lokaci,gaba ɗaya tunda ta doso tsakiyan falon qamshin turarukan da tai anfani dasu masu sanyi da daɗin qamshi suka cika wajen,abinda yasa magidancin tsayawa cak! daga latsa Cumputern da yake ya ɗago manyan idanunsa masu cike da kwarjini ya zube akanta,fuskansa babu yabo ba fallasa yai mata kallo biyu yana me ɗauke kai ya cigaba da aikinsa,ita kuma ta cigaba da takowa cikin takun da ke nuna yanga da kwarkwasa don janyo hankalin wanda akeyi dominsa,ko da ta iso inda yake kai tsaye ta zauna kusa dashi tamkar zata shige jikinsa,gaba ɗaya gangar jikinta ya gama mannuwa da tasa,ta miƙa hannu da nufin ɗauke Laptop ɗin dake bisa cinyansa,yayi saurin kai hannunsa yana dafe nata hannun, tare da ɗago ido ya zuba mata,fuskansa na tsukewa hakan yasa ta janye hannun nata,cikin muryanta me cike da iyayi ta fara faɗin "Haba A.Maleek magana fa mu ke daya kamata ace ka bani lokacinka ka saurareni,amma shine zaka sakko nan ka zo ka zauna kana faman sabgan gabanka,meyasa yanzu ni bani da ƙima da darajan da zaka xauna ka saurari matsololina? A gaskiya A.Maleek na fara gajiya da halin ko inkulan da kake nuna min."
Tunda ta fara magana ya tsaida abinda yake ya zuba mata idanunsa dake rikitata,yana jifanta da wani irin kallo da ita kaɗai tasan ma'anansa,kafin amon muryansa ya fito cike da Isa da izza yake faɗin "Suhailah ni za ki zo ki tasa kina ɗagawa murya,si'anki ne ni ko ni ɗin ɗanki ne? karki bari ki fusata zuciyata a wannan karon har kija in ɗauki matakin da ba zai mana daɗi ba,ke kike ɗaukan maganan da kika zo dashi tana da muhimmanci,ni a wajena maganan banzace tunda bazaki bi abinda nake so ba,don haka ki barni inji da tarin matsololi da ciwan kan da kike bani,oya tashi ki bar nan wajen tun raina bai ɓaci ba,kuma wannan ya zama karo na ƙarshe da xaki sake zuwa min da raini makamancin wannan."
Ya ƙare maganan yana nuna mata hanyan inda ta fito,idanunta ta sauke akansa kaman zatayi magana amma yanayin yadda ta ga ya haɗe fuska yana jifanta da kallon da ta fi tsana a wajensa, yasa ta juyawa da sassarfa ta nufi hanyan stairs ɗin,da bibbiyu take takawa har ta haye,ya bita da wani mugun kallo kafin yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa tare da ɗaukan laptop ɗinsa da wayansa ya rufa mata baya zuwa saman,ɗakinsa direct ya nufa yana aje Laptop ɗin da wayansa,ya fara cire jallabiyan jikinsa yai jifa dashi bisa Bed,ɗakin yabi da kallo zuciyansa na ɗaukan zafi,sam Suhailah bata damu da gyaran ɗakinsa ba,abinda kawai tasani ta ciyo wanka tazo ya biya mata buƙatanta su sha bidirinsu ta kakkaɓe jikinta tabar masa ɗakin,sai lokacin da ta busa iska sannan zatai gyaran ɗakin,idan kuma tayi sai ta ɗauki wani dogon lokacin kafin ta sake,sai dai shi idan yana gari ya dage yai gyaran ɗakin da kansa,don bai lamunci wani ƙato ko ƙatuwa su shigo masa ɗaki da sunan gyara ba,Bathroom ya nufa don yin wanka kaman yadda saba baya iya bacci idan baiyi wanka ba,lokacin da ya fito kintsa jikinsa yayi ya sanya wasu kayan bacci masu taushi ya zura slippers ya fito,kai tsaye kitchen ɗin dake nan upstairs ɗin ya nufa,don haɗo shayin da zai sha kafin ya kwanta,da kansa ya tafasa ruwan zafin ya zuba duk abubuwan da yake buƙata,cikin Mug ya juye bayan ya tafasa ya fito zuwa wajen dining ɗin da ke manne da corridor ɗin shiga Kitchen ɗin,Sugar ya ɗiba da slice bread guda biyu ya nufi ɗakinsa,bayan yayi ma ƙofan shiga ɗakin Suhailah kallo ɗaya ya ɗauke kansa,koda ya kammala shan shayin nasa bakinsa ya je ya wanko yazo ya kwanta,ba tare da yana jin cewa zai bi takan Suhailah wajen nemanta zuwa ɗakinsa kaman yadda yakanyi a wasu lokutan ba,don shi yana ɗaya daga cikin irin mazan da sam basa son raba shinfiɗa da matansu koda sun samu saɓani ne,sai dai yana ganin a yanzu lokaci yayi daya kamata ya fara biris da lamuranta ko zata saitu tasan abinda ya dace da ita,addu'an kwanciya bacci yayi ya shafa yana fata yau yayi bacci ba tare da yayi mafarkin da ya saba yi a ƴan kwanakin nan ba,mafarkin dake tsaya masa arai ya kuma rasa gane kan inda mafarkin ya dosa,lumshe idanunsa yayi bayan yaja blanket ya rufe jikinsa........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer* *Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:03 PM] +234 703 769 7050: *TAIMIYYAH*❤️
©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
*Page 5*
_________ Ƙarfe goma da rabi na dare TAIMIYYAH ce ke zaune tana kallo a falon Iya,ita da Ladi me aiki ne da yake nan take kwana Ladin tana da ɗakinta daga waje,wayan TAIMIYYAH ne ya fara haske alamun kira na shigowa sabida ta sanya wayan a silent,ta kai hannu ta ɗauki wayan tana ganin sunan Yah Deeku ɓaro-ɓaro kaman yadda tai saving number ɗinsa,ƙaramin numfashi ta sauke kafin ta danna received takai kunni,zuciyanta na sauya bugu domin rabonta da shi tun ranan da yabar part ɗinsu a fusace,muryansa ta jiyo yana faɗin "Hello!" sai ta lumshe ido tana amsawa da faɗin "Hello! Yah Sadeeq ina yini."