Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 24
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 24: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,484 words
"Yah Zuhurah mutumiyan namu na ga duk ta sake wani sanyi ne,da alamu ta gama saka rai da zata mallaki handsome Nass ɗinta ne,sai kuma uwarsa tai mata cikas, wallahi duk na ƙosa akai stage ɗin da zai tako ƙafarsa gidan nan ayi me kankat ɗin.Kin san yanzu lallaɓashi nake tayi muna chart tamkar babu wata manufa a zuciyata akansa,nuna masa nake yi ina bala'in tausayinsu daga shi har gurguwar tasa,shiyasa ya saki jiki dani har yake sanar dani irin tarin damuwan da yake ciki akan rabuwarsa da TAIMIYYAN. Ashe wai uwarsa ce masa tayi ko a waya ya kirata bata yafe ba,don tafi so kwata-kwata ya shafe babinta a zuciyarsa.Amma fa da gaske ba ƙaramin so yake wa TAIMIYYAH ba,zan yi aiki kafin in mantar da zuciyarsa ita koda na mallakesa."
Basmah ce ke wannan maganan suna zaune tare da Zuhurah a falonsu,bayan sun kammala cin abincin dare. Zuhurah ta ɗaga kai ta kalli Basmah tana cewa, "Ai baki sani ba,TAIMIYYAH yadda kika san tana da wani magic na farin jinine a tare da ita,ki duba kiga yadda babu wuya ta shiga ran mutane,shiyasa ai duk wanda zai so ta ba zai mata so na wasa ba,nima duk na ƙosa in ga yadda waɗannan idanun nata za su yi randa ta ganki da Nass ɗin,ba dai jibi Umma za ta tafi bikin ba,sai mu jira dawowarta mu ga yadda za a kaya.Nima cikin wata satin Ameeru yace iyayensa za su turo a tsaida lokaci kawai."
Basmah tayi wani farr...! Da ido tana cewa, "Wow! kinga idan lokacin an tunkuɗomin ƙeyarsa mun jone sai kawai a sanya lokaci ɗaya ayi bakinmu tare a huta kawai,tunda shi Yah Sadeeq ya ƙi wa Umma hannu har yau bai je wajen Nadeeyan ba bare a san abinyi."
Ta ƙare maganan da taɓe baki Zuhurah kuma ta sanya dariya,suka cigaba da tattauna yadda zasu ƙuntata zuciyar TAIMIYYAH duk randa ta gane cewa Basmah ta kwace mata Nass ɗinta.
Basmah ta lumshe idanunta azababben soyayyar Nass ɗin na sake kama zuciyarta.Tana kuma sake jinjina wayonta da kaifin ƙwaƙwalwanta, na yadda aka yi ta janyo hankalin Nass har ya saki jiki da ita.
Ta shiga tuna yadda tayi ta nuna masa cewa, ta ɗauke sa tamkar matsayin Yayanta ne tunda yana son TAIMIYYAH.Koda wasa bata taɓa nuna masa cewa suna da ƙiyayya da abar sonsa ba,sai ma nuna masa da take yi kullum cewa kar ya cire rai da samun TAIMIYYAN.......✍🏻
_Lallai Basmah kinyi ƙoƙari inji Ɗansabo,shiyasa aka ce ka rabu da mutum kawai inda ka gansa,sheɗancin wasu mutanen yafi gaban kwatance,to masu karatu kunji ta inda Basmah ta ɓulla har ta fara samo hankalin Nass yana magana da ita,ko me zai faru a gaba? Sai mu cigaba da bin labarin sannu a hankali don jin cikakken ya rayuwar TAIMIYYAH zai kasance baiwar Allah_ 😰
#Ɗansabo ce#[12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*43*
*Kano*
Kwance yake akan gadon ɗakinsa idanunsa duka a rufe, babu abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke kwaɗayi irin ya ji ɗumin jikin TAIMIYYAH a cikin jikinsa. Gaba ɗaya tunda ya ɗaura ido akan tsiraicinta, hannuwansa suka jiye masa laushin fatarta,sannan bakinsa ya ɗanɗano masa wani irin ɗanɗano me garɗi a mounth ɗinta ,ya rasa dukkanin sukuni da nutsuwanrsa.
Ya fi kowa sanin sabida shine TAIMIYYAH ta tattara ta bar garin baki ɗaya, don ta tsorata da maitarsa da ya fitar a fiki akanta.Ya buɗe idanunsa yana Janyo wayansa tare da zubawa lambobin wayarta ido,wanda tun ɗazu yake gwada kiranta,amma sai yaji ya kasa don bai san me zai ce mata ba idan ya kira ɗin.
Gabaki ɗaya tunda ta bar garin kaman ana sake ninka masa, sha'awan son kasancewa da ita ne.Duk neman matansa bai taɓa jin kwaɗayin mace irin na yau ba,kuma babu wacce yake ji zata iya kashe wutan dake ci a zuciyarsa sai TAIMIYYAH. Ya sauke wani numfashi me zafi maransa na sake wani irin ɗaurewa, tsabagen wutar jaraba dake cin zuciyarsa.Ya cije lips ɗinsa yana shahadan danna mata kira, tare da fatan ta ɗauka ko muryanta ya samu ya ji ko zai samu relief.
Sai dai har kiran ya gama ɓurarinsa ya tsinke ba a ɗaga wayar ba.Sai kawai yayi jifa da wayar yana tashi da ƙyar ya nufi toilet,bai jima ba ya fito yana nufan ƙofar fita daga ɗakin baki ɗaya,don zuwa ya haɗo tea me lemon ko zai rage masa nauyin da maransa yayi. Zuciyarsa na kimsa masa tunanin akan kawai ya samu Mamie a gobe, ya sanar mata cewa ya amince zai iya auren TAIMIYYAH. Har ya kai part ɗin Mamie tunanin dake yawo cikin kansa kenan....
___________
*Zee Town (Zaria)*
TAIMIYYAH na zaune tana danna system ɗinta, a lokacin da kiran Emran ya shigo wayarta. Tunda kuma ta ɗauki wayar ta ga baƙuwar number ta ji a jikinta cewa shine,shiyasa ta share kiran bata ɗauka ba har ya tsinke. Ta saki ƙaramin tsaki tana saka wayan a fly mode, ta cigaba da abinda take yi zuciyarta cike da ɓacin ran rainin hankalin da ke son shiga tsakaninta da Yah Emran ɗin.
Har ta gama abinda take yi ta kashe system ɗin, don yin shirin kwanciya barci zuciyarta bata daina tunani,akan abinda ya shiga tsakaninta da shi ba. Lokacin data ɗauro alwala don kwanciya bacci, sai da ta gabatar da sallar wuturi kafin ta nufi gado ta kwanta,bata ɗauki dogon lokaci ba bacci ya sure ta.
Washegary ya kama monday tunda wuri TAIMIYYAH ta tashi, don tana son ganin Baba Sani kafin ya wuce Kano wajen aikinsa.Shiyasa ƙarfe takwas ta isa Sasan su Umma ,a ɗakin Baba Sanin suka gaisa da Umma wacce ke fifita masa tea da zai sha.
Ya gama shirinsa tsaf yana zaune yana cin chips da aka soya masa,TAIMIYYAH ta tsuguna ta kwashi gaisuwa tana sanar masa da buƙatarta. Baba Sani ya amsa cike da kulawa,yana me kai hannu cikin aljihunsa ya irgo adadin kuɗin da take buƙata ya miƙa mata.
Ta amsa tayi godia tana miƙewa ta fito daga ɗakin,Umma na biyo bayarta da mugun kallo.
Lokacin da ta shigo Sasan Iyah ta tadda har Iyah an sha wanka an fito karyawa.Ta saki murmushi a lokacin da ta isa gaban Iyah tana cewa, "Iyah barka da fitowa ina kwana."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH da manyan idanunta tana cewa, "Lafiya lau Zainabu, daga ina kike da wuri haka?" TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe face tana ba Iyah amsa da cewa, "Daga wajen Baba Sani na amso kuɗi ne kinsan yau an koma skull, ina buƙatan kuɗi a hannuna har zuwa sati me zuwa."
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Hakane amma da kin min magana ma na riga na tanadar miki kuɗin duk buƙatunki, kamar yadda Sameer ya saba turo miki lokacin yana raye."
TAIMIYYAH da mood ɗinta ya sauya, fuskarta ya nuna tsananin kewan Abie ɗin, ta dubi Iyah tana cewa, "To ai ban sani bane Iyah sabida shi yace min lallai duk abinda nake buƙata in dinga sanar masa." Iyah ta jinjina kai tana cewa,
"Hakane babu laifi ai, yanzu yau ɗin zaki fara zuwa makarantar, ba zaki bari sai zuwa gobe ba?"
TAIMIYYAH tayi saurin duban Iyah tana cewa, "Sai gobe zan fara zuwa tunda yau aka koma, bama lallai kowa ya je a yau ɗin ba,don Zee cewa tayi ma sai zuwa Wednesday za ta fara zuwa."
"A toh nima dai haka na gani gara ki bari zuwa goben,kin sake hutawa ma."
Cewan Iyah tana faman cin soyayyan dankali da egg da Babah Ladi ta soya,ta cika cup da kunun gyaɗa daga gefe guda. TAIMIYYAH ta fara takawa don komawa ɗakinta,tana cewa Iyah, "Iyah bari in koma in kwanta zuwa tara zan tashi,yau ni zan yi mana girkin rana idan na gama kwaleman ɗakina."
Iyah ta bi bayanta da kallo tana cewa, "To madallah a tashi lafiya,sai Ladi ta taya ki kwaleman don rage miki wani wahalan."
Ita dai TAIMIYYAH tuni ta shige ɗaki abinta,kuma tana aje kuɗin da ke hannunta kwanciyar tayi,don da gaske baccin take son komawa. Sai ƙarfe tara da rabi sannan ta tashi ,ta yo wanka ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi na material,bata shafa komi akan face ɗinta ba, ta fito zuwa falo don yin kalacin safe.
Lokacin da ta kammala karyawan Iyah ce taiwa Ladi magana akan ta taya TAIMIYYAH suyi kwaleman ɗakinta. Hakan ko aka yi cikin lokaci kaɗan suka kammala,wanda rabin aikin Ladin ce kawai tayi ma,don taki bari TAIMIYYAH tayi komi,in banda shirya kayanta da tayi cikin drawer.
11:30am TAIMIYYAH ta wuce zuwa kitchen don fara shirin ɗaura musu lunch,sabida da wuri suke gama girkin rana su.
Tuwo Iyah tace tana so ayi amma na dawa da miyar Kukah,don haka TAIMIYYAH ta fara da ɗaura miyan ne kafin ta ɗaura ruwan tuwan. Cikin nutsuwa da ƙwarewa take aikinta har ta kammala tuƙa tuwan, ya silala ta sauke don fara kulla su a leda.Koda Ladi ta shigo don taya ta wani abin ,sai ta amshi kulla tuwan ita kuma TAIMIYYAH ta ƙarisa miyan ta juye shi cikin cooler.
Store ta nufa ta ɗakko doya madaidaici ta feraye shi,don tana son yin Yam balls ne. Bayan kammala feraye doyan sai ta wanke shi tas ta ɗauka a wuta. Ta nufi wajen fridge ta ɗebo carrot da green pepe ta aje su a gefe,sannan ta ɗebo tattasai da tarugu haɗe da albasa me yawa duk ta gyarasu.
Zuwa lokacin da doyar ya dahu duk ta gama yanke-yanken da zata yi, nasu carrot da green pepe ta aje a gefe guda,sai ta tsane doyar a colander don barinsa ya huce.
Kafin doyar ya huce ta tafasa nama ta baiwa Ladi ta ɗan daka mata,sai ta juye doyar tasa whisker ta dagargajeshi.Ta juye su carrot da green pepe haɗe da kayan miyan da tai grating,ta zuba albasa me yawa da ta yanka, duk ta haɗe su cikin doyar da ta dagargaje ta zuba spices da maggi yadda take so. Zuwa lokacin Babah ta kawo mata dakakken naman, shima ta juye akai ta saka hannu ta motsa, naman yabi ko'ina sannan ta fara mulmulasu zuwa shape ɗin balls.
Babah Ladi dai tsaye tayi kawai tana kallon yadda TAIMIYYAH ke kominta gunin sha'awa. Bayan ta gama maida su balls ne ta fasa egg ta kaɗashi,ta zuba garin corn flour sabida idan aka saka corn flour egg ɗin yafi kamawa ya yi kyau sosai.
Tunda TAIMIYYAH ta fara suyan yam balls ɗin,qamshi ya cika ko'ina hatta Iyah dake falo sai da ƙamshi ya fitineta,ta gane cewa bayan yin tuwon dawan sai da TAIMIYYAH ta ƙirƙira yin wani abin kenan.
Tana kammala komi ta wuce zuwa ɗaki don gabatar da sallah.Babah Ladi ita ce ta ɗauki kulolin abincin ta kai falo, ta jere su inda a ke zaman cin abinci.
TAIMIYYAH ta idar da sallah kenan tana cikin ninke Hijab ɗinta, wayarta ya fara ring ta isa wajen wayar tana kallon sunan Yah Deeku dake rubuce a jikin screen. Tayi receiving call ɗin tana saka wayar a speeker.Muryan Yah Sadeeq ya fito tar lokacin da yake furta,
"Hello! Baby kina jina?"
TAIMIYYAH ta zauna daga gefen gadon tana cewa, "Ina jinka Yah Deeku ina yini,kana lafiya?"
Sadeeq yace "Lafiya lau Zaynab kin dawo daga Kano ɗin ne ko kina can? Dis week ban samu shigowa weekend ba."
TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe murya kaman yana gabanta tace, "Na dawo jiya Yah Deeku,ai tunda na ga ban ga motarka ba na san baka samu shigowa ba."
Sadeeq da ke sauraran muryarta yana jin nutsuwa na sauka a ransa, ya lumshe ido yana faɗin, "Eh Babe! Ban shigo ba yanzu me kike yi ina so ki hau online na tura miki wani pic ne ki gani,but idan kin gani ki gaya min gaskiya tayi ko bata yi ba,tunda ke an hana min ke bayan zuciyata har yanzu ke kaɗai take muradi."
TAIMIYYAH dake saurarensa ta sake yin ƙasa da muryarta tana cewa, "Okey Yah Deeku bari in hau online ɗin."
Sadeeq zai yi magana kenan ya ji tayi cuting call ɗin,sai kawai shima ya hau online ɗin. Lokacin da TAIMIYYAH ta buɗe pic ɗin, idanunta ne suka sauka akan kyakykyawar fuskar budurwar dake jikin hoton,ta tsura hoton ido kaman me son gano haƙiƙanin kyawun budurwar.Sai kawai ta fara typing tana tambayar ya Deeku budurwansa ce? Dai-dai lokacin shi ma ya hawo online ɗin, ganin tambayar da TAIMIYYAH turo masa yasa shi murmusawa ya fara typing shi ma,yana bata amsa da cewa,
"Yes Baby tayi ko bata yi ba?"
TAIMIYYAH ta saki murmushi kaman yana gabanta,kafin ta tura masa cewa, "She's very cute Yah Deeku,gaskiya tayi Allah tabbatar da alkhairy." Sadeeq ya karanta abinda tace, sai ya aiko mata da emoji na kuka yana rubuta cewa, "Baby daɗi ma kike ji zan rasaki ko kishi ma ba zaki nuna ba ko?"
TAIMIYYAH ta aika masa da emoji na dariya kawai, ba tare da tace komi ba. Sai kawai Sadeeq ya sauka daga online yana kiranta vid-call,suka jima suna magana yana sanar da ita cewa sunan yarinyar Safiyyah. Ƙanwar wani abokin aikinsu ne suna zaune a Badarawa Kaduna.
Ita dai TAIMIYYAH sai suka gama wayar fuskarta na blushing, don har cikin zuciyarta tayi farin ciki da Yah Sadeeq zai fitar da matar aure.
Tana kammala cin tuwan da ta zuba kaɗan,ta nufi kitchen ta ɗauki bowl ɗin da ta zubawa Ummie yam balls, ta fito zuwa falon Iyah. Bowl ɗin ta aje tana ɗaukan wayarta, sannan ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah za ni Sasan Ummie in kai mata yam balls ɗinnan."
Iyah ta dube ta tana cewa, "Madallah ki gaishe da Inna Larai."
TAIMIYYAH amsa tana yin gaba, hannunta ɗaya dafe da ƙafarta me laluran, ɗaya hannun riƙe da bowl ɗin da wayarta. Babu kowa cikin falon Ummien lokacin da TAIMIYYAH ta shiga,sai ta aje bowl ɗin tana zama cikin seater, dai-dai lokacin da kira ya shigo wayarta.
Ta tsurawa lambobin idanu har kiran ya yanke bata ɗaga ba,wani kiran ya sake shigowa sai ta ɗaga tana kai wayan kunni. Jin muryan Yah Emran yasa ta saurin yin hanging up,tana yin blocking lambar baki ɗaya.
Ta aje wayan mood ɗinta na canzawa,ɓacin rai ya mamaye zuciyarta. Ummie ce ta fito daga ɗaki ganin TAIMIYYAH yasa ta ƙariso cikin falon, fuskarta ɗauke da murmushi take cewa, "Zaynab ke ce dama kika shigo shine kika zauna a falo, maimakon ki shiga har cikin ɗaki." TAIMIYYAH ta maida mata martanin murmushin tana cewa, "Laah! Ummie yanzu na shigo ba wai na jima bane,na tsaya amsa call ne,ga yam balls na kawo miki ɗazu nayi sa."
Ta ƙare maganan tana ɗaukan bowl ɗin yam balls ɗin ta kai gaban Ummien,lokacin da Ummien ke cewa, "Kai! Aiko kin kyauta Zaynab nagode sosai,ke kam kinji daɗi kina da son girke-girke, kala-kala baki ko jin wuyan aiki duk da laluran ƙarfar taki."
TAIMIYYAH ta saki smile tana cewa, "Haka kowa ke cewa bana jin wahalar aiki,wallahi kam bana ji indai har zan haɗa komi waje ɗaya shikenan,yawan kai kawo ne kawai ke sani inji na jigata a aiki,amma indai za a aje min komi waje ɗaya inyi aikina daga zaune shikenan."
Ummie ta saki murmushi tana kai yam balls ɗin ɗaya baki, ta gutsira tana cewa, "Allah sarki duk da haka dai ke ɗin ba mai kyuiyan aikin bace kawai,gashi ko yayi daɗi sosai egg ɗin ya kama jikinsa.Za ki yi mana a nan sasan wataran in ga yadda kike yi yake yin daɗi haka."
TAIMIYYAH tayi ɗan ƙaramin dariya tana cewa, "To shikenan Ummie duk sanda kika so a yin sai kiyi magana."
Daga haka suka ɗan taɓa hira kafin TAIMIYYAH ta baro sasan Ummie.
Ta shiga sasan Iyah kenan ta zauna, saƙon text message ya shigo wayarta,da wani baƙuwar lambar na daban. Sai ta buɗe text ɗin ta fara karantawa,tana gama karanta saƙon, ta fahimci daga Yah Emran ne,yana mata magiya ne akan tayi picking call ɗinsa,sai ta share text ɗin baki ɗaya,ta sake tayi blocking wannan line ɗi daya turo saƙon da shi.
Memakon ta cigaba da zaman falon sai ta nufi ɗaki kawai ta kwanta,tana jin wani ɓacin rai na taso mata,don ta kasa gane me Yah Emran ke son ɗaukarta da har yake tunanin zata iya saurararsa,bayan duk irin tozarcin da yayi mata.
Ta lumshe idanunta tunanin Nass na kutsowa cikin kwanyarta,haka kawai taji wasu hawaye masu ɗumi na sauka suna biyo ƙuncinta. Soyayyarsa da ke can ƙasan zuciyarta ke son tasowa baki ɗaya,sai ta rintse idanunta sosai tana tunanin, 'Ko a wani hali yake yanzu,shikenan Mum ɗinsa tayi nasaran tarwatsa duk wata soyayya da ta gudana tsakaninsu kenan?" Ta kai hannu tana share hawayen dake zubowa daga idanunta,tana jin zuciyarta na wani irin ƙuna da shiga ƙunci me tsanani. Ta gama sallamawa cewa ta rasa Nass har abada, tunda mahaifiyarsa bata sonta sabida kawai ta kasancewa gurguwa.
TAIMIYYAH ta jima tana kuka da hawaye kafin ta rarrashi kanta tayi shiru,tana faman sauke ajiyar zuciya, kewan Abie na taso mata.Tana hasaso cewa da yana raye da ta kira shi taji koda muryansa ne,amma ya riga ya tafi inda bazai dawo ba.
Wani kuka me ƙarfi ya sake kwace mata lokacin da take tuno sautin amon muryar su Nahar,da yadda suke yawan yin vedio call suna ɗebe mata kewa,yau gashi duka babu ko ɗaya a cikinsu.
Sai kawai ta kifa kanta a jikin pillow tana rushewa da kuka,tamkar za ta haɗiyi zuciyarta ko za ta huta da jin irin ƙuncin da take ji a yanzu.
Bayan ta rarrashi kanta tayi shiru daga kukan,sai ta zame tana gyara kwanciyarta bisa bed,bata jima ba sai bacci ya yi nasaran ɗaukar ta,bata kuma farka ba sai la'asar........✍🏻
#Ɗansabo ce # [12/14, 10:10 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*44*
_____________
Kwanakin TAIMIYYAH shida da kenan da dawo daga Kano,ya kama ranan Saturday. Ta dawo daga makarantar haddah kenan a gajiye,tana shigowa falon Iyah hancinta ya shaqo mata ƙamshin turaren SAUVAGE DIOR. Sai tayi tsaye daga bakin ƙofar bayan Iyah ta amsa sallamar da ta yi cikin sassanyar muryar ta.Manyan idanunta ta ɗaga a hankali, tana me sauke su akan bayan Emran da ke zaune yana facing Iyah,don haka ita da take tsaye daga bakin ƙofa ya bata baya. Cikin slowly ta dafe ƙafarta ta cigaba da takowa zuwa cikin falon,jikinta ya gama bata koma waye a zaune tun kafin ta ga face ɗinsa ma.
Emran da tun fara takowan TAIMIYYAH cikin falon ya zubo mata ido,sai ya cigaba da kallonta har ta ratso tsakiyan falon ta isa wajen Iyah tana cewa, "Iyah na dawo,Yah Emran barka da zuwa." Daga haka sai ta miƙe ta cigaba da takawa har zuwa ɗakinta. Tana jikinta na jin tasirin kallon da Emran ya biyo bayanta da shi,zuciyarta ta ji ya ɓaci tunda ta ci karo da face ɗinsa,ga kuma wani fargaba da zullumi da ke dukan ƙirjinta. Tambayoyi masu yawa suka dinga kutsowa cikin zuciyarta,tana tambayan kanta, 'Me Yah Emran Zaria? Don tafi kowa sanin haka kawai, ba kasafai suka cika yo tafiyayya zuwa Zaria su gaida Iyah ba,sai in da wani dalili suka fi zuwa daga shi har su Yah Anas ɗin,da wacce ya zo,kar dai a ce tafiyayya ya yo sabida ita?" Waɗannan su ne tarin tambayoyin da suke addabar zuciyarta TAIMIYYAH har ta gama cire Hijab ɗin da ke jikinta,ta aje Qur'aninta saman drawer.
Shigowar Iyah ɗakin nata ya saka TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Iyah,tana me amsa sallamar da tayi.Iyah ta tako zuwa cikin ɗakin tana kallon TAIMIYYAH cikin ido,tare da cigaba da nazartan yadda duk tayi wani sanyi daga ganin Emran da tayi. Ta ɗan tsuke fuska kaɗan tana cewa, "Zainabu sai ga Emran kaman daga sama ya biyo sahunki,yace yana ta kiran wayarki kin rufe shi baya iya samunki,meyasa zaki haka TAIMIYYAH? Ke da ɗan uwanki don ya nuna yana da ra'ayi a kanki sai ya zama abin wulaƙantawa? Ya gaya min komi, yace sabida ya bayayyana miki cewa yana son ki, shine dalilin da kika matsa sai kin dawo,to maza ki canzo kaya ki fito ki samesa ni yanzu zamu fita da Sani,zani Rimi amma zan dawo kafin ya wuce,na saka Ladi a shirya abinci sai ki shiga ku yi aikin tare, ki ɗan masa wani abin na birgewa cikin girkunan zamani da kika Iyah."
TAIMIYYAH da tunda Iyah ta fara magana ta shiga shock...Sai ta ɗaga manyan idanunta ta dubi Iyah,tana ma rasa abinda zata ce,don tsananin mamaki da tsoran maganan da Yah Emran ɗin ya shiryawa Iyah,ya gama daskarar da ita a zaune.Amma sai tayi ƙarfin halin cewa Iyah, "Toh shikenan Iyah za a yi duk yadda kika ce,sai kin dawo ma yi magana,amma ni ba sabida shi na dawo ba wallahi."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da shagwaɓa da raunin murya,wanda ya saka Iyah hararanta tana cewa, "Koma dai miye ki tashi maza ki same shi bari in je nasan kila Sani na waje ya ƙariso."
TAIMIYYAH ta bi bayan Iyah da kallo lokacin da take ficewa daga ɗakin,ba tare da ta jira cewan TAIMIYYAH ba.
TAIMIYYAH ta sauke wani zazzafar ajiyar zuciyar, tana ji tamkar ta saki kuka ko zata ji sanyin takaicin da ya tokare maƙoshinta.Ta cigaba da zama daga bakin gadonta bata da niyyan tashi ta fito zuwa wajen Emran ɗin, kamar yadda Iyah ke buƙata don ita ya riga ya gama sire mata, ta kuma tsane shi tsana me tarin yawa,sai dai ta sani tunda ya riga ya tako zuwa nan ɗin,dole ta fuskancesa ta ji da wacce ya zo?
Sai ta miƙe ta isa bakin mirrow ta tsaya, bayan ta dogare ƙafarta da jikin stool ɗin.Kallon kanta tayi daga sama har ƙasa, tana sanye ne da doguwar rigan material me irin Silk ɗinnan,anyi masa ɗinkin boubou da yai mata kyau sosai a jiki.
Fuskarta babu komi sai man leɓe da ta goga tun safe da zata fita zuwa haddah,ta juyo zuwa wajen kayanta ta ɗauki ƙaramin Hijab ta sanya, ta fita zuwa falon Iyah fuskarta babu ɗigon annuri ko kaɗan.
Tunda ta fito Emran da ke zaune ya kafe ta da ido,ya ji zuciyarsa na amsawa da tarin begenta da tsananin soyayyarta da ke fisgan zuciyarsa.
Sai dai ya fi kowa sanin zallar sha'awarta ne ke haifar da zazzafar soyayyarta da yake ji a cikin zuciyarsa,ya cigaba da kallonta har ta samu waje ta zauna cikin kujeran da ke nesa da shi.
Shiru ya ratsa a cikin falon sai sautin TV da ke kunne ke tashi a hankali,ko kaɗan TAIMIYYAH ba tayi gigin kallonsa ba,tana dai jin tasirin na shi idanun a jikinta, kafin amon muryarsa ya ratsa kunnuwarta inda yake cewa, "Zainab gani na biyoki tunda rashin kunyarki har ya kai,ki sanya duka numbers ɗina a black list ko?"
TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska tana me sake jin tsanansa na mamaye ruhinta,ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa,sai lokacin kuma ta kula da shigan da ke jikinsa.Yana sanye ne da wani haɗaɗɗen Filtex material na maza,kalan Blue Black da yai masa mugun kyau,don yana da hasken fata ba za a kira shi baƙi kai tsaye ba, sai dai a kira shi da wankan-tarwaɗa. Ta ɗauke kai daga dubansa, ganin irin kallon da yake bin ta da shi kamar tsohon maye,tayi magana cikin sanyin murya tana cewa, "Rashin kunya kuma Yah Emran?"
Emran ya dannan mata harara yana cewa, "Yes rashin kunya mana da raini,sabida kin fahimci cewa tunda na ga halittarki kin tafi da zuciyata,to gani na biyoki har inda kike.Kuma na zo ne in baki haƙury akan kalaman da nayi a kanki,da abinda ya faru tsakaninmu a Kano, yanzu son ki nake ji sosai cikin zuciyata Zaynab,don haka ki amince da soyayyata mu yi aure, dama shine burin Mamie.Ta son ganin na yi auren zumunci kuma ke ta zaɓa min,zaki amince da Yayanki ya zama mijinki Zaynab?"
Yadda ya kai ƙarshen maganan cike da narke murya na zallar iya yaudara,yasa TAIMIYYAH saurin kallonsa with so much shock...! Bakinta har wani rawa yake muryarta na harɗewa lokacin da take faɗin, "Soyayyah Yah Emran,kana nufin ni kake so a yanzu wai? Kamanta cewa ina nan a gurguwata har yanzu, wacce ba za ka iya nuna ta a matsayin matarka abokanka su raina ka ba.Ina nan a musakata ban warke ba, ba kuma zan warke ba har abada idan haka Ubangiji ya so ganina,don haka ba ni kake so ba Yah Emran tun wuri ma ka gyara kalamanka,kuma kada ma ka cigaba da yaudaran zuciyarka a kaina,kace kawai jikinki nake so Zaynab amma bani kake so ba."
TAIMIYYAH na maganar ne hawaye na fara sauka a saman kyakykyawar fuskarta,hakan yasa Emran tashi zai isa inda take zaune, amma sai TAIMIYYAH tayi saurin dakatar da shi,cikin tsananin ɓacin rai take cewa, "Karka kuskura ka ƙariso inda nake Yah Emran,in ba haka ba wallahi zan maka ihu Babah Ladi ta fito,don bamu kaɗai bane a gidan, karka ɗauka don Iyah ta fita zaka maimaita irin akuyancin da kai min a Kano."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan cike da gargaɗi tana ɗaga masa murya,yasa Emran daskarewa a tsaye yana kasa koda motsi,sai idanu da ya zuba mata kawai yana ji tamkar ya nufeta ya rungumeta da ƙarfin tsiya,kalmar akuyancin da ta furta cikin kalamanta na ƙona zuciyarsa.
Kaman TAIMIYYAH ta san tunanin da ke ransa sai ta miƙe don bashi waje,sabida zuciyarta wani irin tafarfasa kawai take yi da zallar tsanan Emran ɗin. Emran ganin da gaske TAIMIYYAH tafiyarta za ta yi ta bar shi, yasa shi cire murya ya kira yi sunanta Zaynab! Ya ɗaura da faɗin,
"Don Allah ki tsaya ki saurareni Baby wallahi da gaske son ki nake yi,ina sonki a gurguwan da kike Zaynab,kuma nayi kuskuren sakin kalaman dana furta miki wancan lokacin, amma kiyi haƙuri a yanzu zuciyata azabtuwa take yi da ƙaunarki me tsanani Sis Zaynab."